489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa. Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi. Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi. Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan. A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya…
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-nine
A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai. Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka. Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin. Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska. Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty
Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Sixteen
Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirty-two
Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun. Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah. "Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba" Zaro ido muruje yayi tareda cewa. "Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi" Fita muruje yayi daga cikin motar yakama… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Seventeen
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Three
Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Nineteen
A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty
"Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana" "Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga" "Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene. Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za'a shaideki da ita" Yamutsa… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-two
Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje. Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan. "Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?" Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko… -
Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa. Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata. A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta'ba mantawa ba. Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan…
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-four
Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa. A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida. Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma… - Previous 1 … 10 11 12 … 30 Next
