Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • by Sadi Sakhna Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya. Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta. Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi. Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah. Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta…
    • by Sadi Sakhna Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan. Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba. Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin. Bombee kuwa ganin kowa ya dauke…
    • by Sadi Sakhna Bayan shekara biyu............. Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama. Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa. Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata. Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah…
    • by Sadi Sakhna Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature…
    • by Sadi Sakhna Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa. Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi. Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi. Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan. A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya…
    • by Sadi Sakhna A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai. Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka. Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin. Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska. Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka…
    • by Sadi Sakhna Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma…
    • by Sadi Sakhna Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi…
    • by Sadi Sakhna Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun. Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah. "Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba" Zaro ido muruje yayi tareda cewa. "Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi" Fita muruje yayi daga cikin motar yakama…
    • by Sadi Sakhna Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika…
    • by Sadi Sakhna Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi…
    • by Sadi Sakhna A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah…
    Note
    error: Content is protected !!