489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Ten
Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani. Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu. "Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba" "Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?" "Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai. Amma daman batun ku tsaya cikin… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Eleven
Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba. Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen. Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi. Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twelve
Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirteen
Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci. Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa. Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa. Yana tafiyah yana waiwayen ƴar… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Fourteen
A haka suka koma gida cikeda ta'ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu. Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za'ayi mata. Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta. Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Fifteen
Tun safe inna laari take abu ɗaya a ɗaki,Allah ya haɗata da doguwar naƙuda. Danejo kadai ke kai kawo a tsakar gidan,sai Bombee wacce take wasa a zaure,fuskarta bushe da hawaye tayi sabbabben nata wato kuka,a rana tayi kuka yafi sau a kirga,wani lokacin har zazzabi takeyi. Larai ce tafito daga ɗakin inna laarin ɗauke da ledar mabiyya a hannunta,saida tatsayah tayi shewa tayi guɗa kafin ta kalli inda Danejo take. "Mashaallah yarinya ta faɗo duniya,kyakykyawa fara jinin fulani usul,kuma Alhamdulillah… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Sixteen
Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter One
.........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi" Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. "Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!" Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. ""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24" "Toh ranki ya daɗe" Ta faɗa tareda zubawa dagudu.… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Two
Ƙwana uku baya............ ________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba. Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita. JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan,… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Three
Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Four
Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan. Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta. Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye. Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar. Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Five
"Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke" "Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana" Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al'ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba. "Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu… - Previous 1 … 10 11 12 … 31 Next
