489 Results in the "Hausa Novels" category
-
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Six
"Saki kuma ummah?" "Eh saki haka nace,ko baka jiba kurmane kai nasake maimaita maka,ka rubuta sakinta ka bata tabar gidannan,bana sonta a cikin gidannan" Yawu ya haɗiya mai nauyi kafin yakai hannunsa zuwa kan takardar,tambayoyine suka fara kwaranya a cikin ƙwaƙwalwarsa,meyasa sai shine,meyasa komai shikaɗai zai dunga faruwa dashi? Daga ya fita cikin wanann ifila'in sai kuma yasake shiga wani. Koyaushe shidai bazai daina fita daga chaƙwakiyar mata oho. Biro ya ɗauka tareda takardar baya ya dawo daga… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Seven
_________________________ GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria. Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Eight
Hasashen sa kuwa bai tafi a banza ba,dan Hajiya zeenah tanajin an fara gangara ta mulmulawa toro ashar. "Kai kuwa wanne ɗan rashin arziƙine,kashe mu zakayi bayan ka karbi kudi,wannan wane irin wajene na kawo kaina ni zeenatu,akan wata biyan buƙata ta duniyah. Juya juya damu na fasa zuwa garin waje saikace hanyar aljanu" Juyowa toro yayi yana dariyah,tareda ƙarewa mutanen cikin motar kallo kafin yace. "Ai hajiya tunda har muka ɗau hanya tofa sai munkaita casss,kuma banda abinki hawa ɗaya fah muka… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Ten
Har suka fito daga cikin gidan su bombin babu wanda yacewa wani komai,saboda ɗumbin abin mamakin da suka gani. Magana suka ji a gefensu,suna waigawa suka ga ashe saurayin daya rakosu gidanne,yana jingine a bakin motar tasu. "Sannunku da fitowa,na tabbatar masu samu amsar abinda kukaje nemaba" "Taya kasan hakan,ko shiyasa ka tsaya kana jiran mufito,kenan kasan inda take?" "Eh to nasani bankuma sani ba,kunsan ance ba'a aikin banza,zan nuna muku hanyar dazaku bi ku sameta dai. Amma daman batun ku tsaya cikin… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Eleven
Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba. Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen. Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi. Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Thirteen
Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci. Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa. Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa. Yana tafiyah yana waiwayen ƴar… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Fourteen
A haka suka koma gida cikeda ta'ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu. Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za'ayi mata. Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta. Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Fifteen
Tun safe inna laari take abu ɗaya a ɗaki,Allah ya haɗata da doguwar naƙuda. Danejo kadai ke kai kawo a tsakar gidan,sai Bombee wacce take wasa a zaure,fuskarta bushe da hawaye tayi sabbabben nata wato kuka,a rana tayi kuka yafi sau a kirga,wani lokacin har zazzabi takeyi. Larai ce tafito daga ɗakin inna laarin ɗauke da ledar mabiyya a hannunta,saida tatsayah tayi shewa tayi guɗa kafin ta kalli inda Danejo take. "Mashaallah yarinya ta faɗo duniya,kyakykyawa fara jinin fulani usul,kuma Alhamdulillah… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter One
.........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaɗan ,daure daure ga nan kan ina hangoshi" Nurse ɗin take fada,wacce ta haɗa gumi sharkaf saboda firgici. "Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!" Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar ɗin matsayi,dan kayansu ma ba iri ɗaya bane. ""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24" "Toh ranki ya daɗe" Ta faɗa tareda zubawa dagudu.… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Two
Ƙwana uku baya............ ________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba. Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita. JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan,… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Four
Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan. Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta. Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye. Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a ɗakinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar. Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a… -
Chapter
Bakar Ayah – Chapter Twenty-two
Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje. Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan. "Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?" Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko… - Previous 1 … 9 10 11 … 30 Next
