Search
You have no alerts.

    489 Results in the "Hausa Novels" category


    • by Sadi Sakhna A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah…
    • by Sadi Sakhna "Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana" "Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga" "Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene. Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za'a shaideki da ita" Yamutsa…
    • by Sadi Sakhna Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba. "Inna......inannnaaaa" Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa. Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta…
    • by Sadi Sakhna Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje. Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan. "Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?" Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko…
    • by Sadi Sakhna Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa. Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata. A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta'ba mantawa ba. Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan…
    • by Sadi Sakhna Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa. A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida. Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma…
    • by Sadi Sakhna Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba'a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa. Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa. "Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari. Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni…
    • by Sadi Sakhna Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan. Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba. Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin. Bombee kuwa ganin kowa ya dauke…
    • by Sadi Sakhna Kwanaki sunzo sun tafi,a ƙallah Daneji ta samu shekara guda babu kaɗan gidan malam Ahmadu,kuma har yanzu babu wata matsala data fito tsakanin ta da mijinta,ko kuma kishiyarta. Tana binta ta sau da ƙafa,itama kuma tana kyautata mata a matsayinta na babba. Tun bayan watanta uku a gidan Malam Ahmadu yafara zaton samun ɗa,amma ganin shuru shuru yasa shi dole ya bar zancen. Daga lokacin yafara zaton wataƙila wata matsala ce daga gareshi. Hakanne yasa ya nunka kulawar dayake basu fiyeda a lokacin baya,domin…
    • by Sadi Sakhna Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature…
    • by Sadi Sakhna Babu 'bata lokaci daneji ta shirya domin su tafi asibitin,har sannan Bombee na hannun mahaifinta,motsi kaɗan idan tayi ya leƙata,gani yake tamkar ƙwai ne a hannunsa,zai iya fashewa a kowanne lokaci. Ƙosawa yayi darashin shiryawar tata da sauri,dukkuwa da yanda take iya ƙoƙarinta wajen yin saurin,gani yake kaman jinkirinta a lokacin wani abun zai iya faruwa. Fitowa sukayi daga ɗakin tareda yiwa Inna laari sallama kana suka kama hanyar asibitin a mashin ɗinsa. Yana tafiyah yana waiwayen ƴar…
    • by Sadi Sakhna A haka suka koma gida cikeda ta'ajjibin abinda aka faɗa musu. Sannan kuma Daneji tacigaba dayi mata wankan maganin da mlm Alwasu yabasu. Bayan sati daya dayin hakan suka sake komawa,aka yi yankan sadaka da kuma sauƙar karatu,sannan ya kuma basu wani maganin wanda za'ayi mata. Sai a sannan ne hankalin su mlm Ahmadu ya kwanta,amma ba duk ba,saboda har yanzu idonta babu abinta ya sauya daga shi,saidai sun samu kwanciyar hankali jin cewar ta rabu da aljanun da suke jikinta. Wasa wasa abu yayi ta tafiyah,har…
    Note
    error: Content is protected !!