Search
You have no alerts.

    492 Results in the "Hausa Novels" category


    • by Sadi Sakhna Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan. Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba. Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin. Bombee kuwa ganin kowa ya dauke…
    • by Sadi Sakhna Bayan shekara biyu............. Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama. Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa. Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata. Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah…
    • by Sadi Sakhna Miƙewa tayi gwiwa a sabule jin abinda innar tata tafaɗa. Hanyar waje tafita kanta a sunkuye,tana jiyo maganar mutane a bakin kofar gidan,wanda tuk yawancin maganar ta ne da abin tirrr da Allah wadai datayi. Sauri take tayi nesa da maganganun,dan ba komai suke kara mata ba sai dake daskarar mata da zuciya,maimakon suyi tasiri wajen saka zuciyar laushi. Sai dare yaraba tukunna tashigo gidannasu,sassafe kuwa kafin kowa yatashi ta fice a gidan. A gari taji labarin an kai mahaifinta asibiti jininsa ya…
    • by Sadi Sakhna A hankali take bude idanuwanta wanda sukayi mata nauyi tamkar anɗora mata dutsi akai. Saurin yunƙurawa tayi zata tashi,amma saitaji jikinta tamkar an ɗaɗɗauresu da wasu boyayyun zarurruka. Ɗakin haskene dashi amma bana hasken rana ba ko kuma fitila,sai na tsabar farin fentin cikin ɗakin. Alamar motsi tafaraji a kanta,a hankali take daga kannata harta sauƙeshi akan fankar datake wainawa tana bawa ɗakin wadatacciyar iska. Baki tasake cikeda mamaki ,dan tunda take bata taba kallon waje mai irin haka…
    • by Sadi Sakhna Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma…
    • by Sadi Sakhna "Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato. Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa. Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara…
    • by Sadi Sakhna Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun. Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah. "Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba" Zaro ido muruje yayi tareda cewa. "Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi" Fita muruje yayi daga cikin motar yakama…
    • by Sadi Sakhna Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika…
    • by Sadi Sakhna Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa. "Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu" "Okay toh" Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar. "Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu" Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar…
    • by Sadi Sakhna Wulgawar Bombee innayi tagani tana cin abinci, yaukuma ta dawo da wuri.innayin tafaɗa a ranta,kullum sai yamma liƙis take dawowa idan ta tafi makaranta,wani lokacinma sai dare yayi tukunna.Sau uku mlm Ahmadu yana kamata yana dukanta,amma ko kuka batayi,sannan kuma bata faɗi inda take zuwa ba,sannan kuma bata fasa kaiwa daren ba. "Inna Daneji Addah Bombee tadawo tana ɗakinmu" "Yauɗin kotaji magana babannku kai,amma a wanne yanayi tashigo" "Uhm hannun duk jini har ya bata mata uniform ɗin…
    • by Sadi Sakhna A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah…
    • by Sadi Sakhna "Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana" "Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga" "Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene. Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za'a shaideki da ita" Yamutsa…
    Note
    error: Content is protected !!