“`Bismillahir rahmanir Rahim
*Alhamdulillahi Ubangiji ya nufa mun dawo a daidai wannan lokacin me tarin albarka. 15/12/2023 na fara, Ya Allah ka bani ikon isar da wannan sakon da na dauko Ya Allah ka bani damar sauke nauyin da na dauka, ina muku
Fatan alkhairi
Ga Jamilah Janafty wacce bata gajiya da dimbin alkharinta a gare ni da sauran marubuta baki ɗaya.
Wannan labarin wani ɓangare na Labarin ya faru da gaske wani ɓangare kuma kwaskwarimar daliban ilimi ne.“`
Sadaukarwa ga BINTUN BATUL
Wannan labarin na kudi ne!
BAARE GOLDEN EMPIRES.
Niamey. Niger republic
02:30pm
Ta zubawa kofar yalwataccen ofishinta idanuwa, kamar kullum da rana zata fito har ta fadi ba tare da ta jira zuwan Yaranta ba, sai dai yau kamar har sun wuce ka’idar lokacin da suke zuwa mata, wayar landline da ke gefenta tayi kara. Ɗauka tayi cikin sanyi ta saka a kunnenta. “Assalamu alaikum!” Ta faɗa cikin sassanyar murya wanda yake cike da dattako. “Ina magana da Chairwoman ne na BA’ARE GOLDEN EMPIRES?”
“Eh” ta amsa zuciyarta na rawa, domin daga jin harshen da aka mata magana tasan daga nigeria ce, domin da harshen turanci ne. “Yawwa Ma’am Captain MJ Mamman Ba’are ya ce a gaya miki ba zai samu zuwa ba, har…”
“Ok ba damuwa!” Ta faɗa cikin sauri da wani raunanen murya, idanunta cike suke da kwallar bakinciki, idan tace bata ji dadin rashin ganin MJ ba tayi karya. Yau shekara shida kenan rabon da ta saka shi a idanun, MJ ba yaro bane balle a ce sai an tuna mishi nauyin da ya rataya akanshi na iyaye, sauke ajiyar zuciya tayi lokacin da aka kirata a wayarta ta ɗauka harshenta yayi nauyi. Amma a zuciyarta addu’a take mishi, a duk inda yake Allah ya kare mata shi.
“Madame ga Amaan Mamman Ba’are yana son shigowa.”
“Ya shigo!” Ta faɗa tana dauke kwallar da yake idanunta da wani tissue. Da sallama ya shigo hannunshi dauke da wayar iPhone 14pro. “Barka da rana Hajiya!” Ya faɗa yana kai wayar kunnenshi. “Barka dai Amaan Mamman Ba’are!” D’aga mata hannu yayi, ta kura mishi idanu. A hankali ta kai hannunta kan wata sandar ƙarfen gold, kafin ya ankara ta make hannun da sandar ta watsa mishi harara. “Auch Hajiya, waya me muhimmanci nake son yi?” Ya katse kiran yana kallonta, tare da tura baki. “Fisabilillahi Hajiya daga na dan yi miki alamar ina zuwa sai ki make min hannu?”
“Allah ya shiryaku! Ka gaya min wacce uwar ce zata yarda ka mata haka?”
“Tow Hajiya me nayi?” Ya tambaye ta kamar zai yi ihu, wayarta ce ta kuma kara, ta dauka. “Madame ga Aryan Mamman Ba’are yana son ganinki.”
“Ya shigo!”
Ta faɗa tana kallon agogon hannunta, can kuwa sai gashi dogo sambal kamar Amaan Mamman Ba’are, Kyakyawan buzu sak da dan uwanshi, niman wuri yayi ya zauna yana gaida ta a sanyayye. “Sannu Hajiya ya aiki?” “Alhamdulillahi, ya takwarata da Nabeeha?”
“Suna lafiya!” “Hajiya shine ni baki tambaye ni ba, wato don an tsane ni. Ko Yarana ba za’a tambaya ba!”
“Da kazo ka bani damar tambayarka?”
“Amma Hajiya fisabilillahi waya nake fa”
“Wayar tafi ni muhimmanci ne?” Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa, shi har ga Allah Hajiya bata mishi gentle, gashi wannan dan iskan Yaron yana zuwa ta wani tsaya tarairayarshi.
“Hajiya kin yi waya da Hamma MJ?” Murmushin takaici tayi, ta ce mishi. “Aryan MJ ba zai sami zuwa ba”
“Amma Hajiya kuri’ar mu ba zata wadatar ba, dole sai da Hamma, ko zan tafi Port Harcourt din ne?”
“Kasan idan na cika matsawa gudu zai sake yi, daga Port Harcourt zuwa wata ƙasa kyale shi.”
“Tow Hajiya idan yaki zuwa ki basu abinda suke so mana, tunda shi aikinshi yana gaba da kome”
” Wani lokaci idan kayi magana, kamar baka san zaman aji ba, anya Hajiya ba asarar kudin tara kika yi ba?” Inji Aryan Mamman Ba’are, “Hajiya ki gaya mishi ya fita hanyata, ba da shi nake ba. Dake nake ina ruwanshi da ni.”
Lumshe idanun tayi ta bude akanshi, idan da sabo ta saba da halin Amaan, wani lokaci idan yayi abu kamar ba ita ta haife shi ba, idan ta tuna past ɗinta sai ta ga kaman da gayya yake mata wani abu, domin yasan duk yakin da take yi ai domin su ne baki daya, ko makiyinta bata fatan ya ga irin rayuwar da tayi balle masoyinta ko ɗan da ta haifa, amma halin Amaan ya zame mata kamar jinin jikinta ne, yana ganin kamar tafi son Yan uwanshi akan shi, bayan shi bai san bakiɗayansu kaunarsu take ba, tana damuwa da MJ ne ba don kome ba, sai don rashin lafiyarshi. Shi kuma Amaan gabbo ne bai da hankali sam, yayinda Aryan ya kasance mai matukar hakuri amma bai iya faɗa ba, Majeed shine daidai da su, hatta Hajiya Turai kakarsu shakkarshi take, kaf Ba’are estate babu dodo sama da Majeed. “ba zan sallama musu tsinke daga kamfanin nan ba, duk abinda kaga ya faru dama can rubutaccen al’amari ne. Yaushe ka samu duniyar da har ka manta da asalinka? Ka manta nayi aikin tuwo-tuwo domin ka rayu?” Dafe goshi Aryan Mamman Ba’are yayi hawaye na zuba mishi, wasu abubuwan akan idanunsu wasu abubuwan kuma kafin a haife su, past din Hajiya yana da alaka da nisan da MJ yayi. Har ya koma Nigeria da zama duk da dama can Nigeria ita ce inda suka rayu, daidai lokacin da suke buƙatar taimako.