*Labarin gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
*Labarin nan ya faru a gaske, sai dai a wurare daban daban, amma na canza garuruwa da sunaye, domin tak’aitawa kar gidajen suyi yawa yasa zan had’a labarin a gida d’aya.*
*Nagode da gudummuwarku gareki*
_Bismillahir rahamanir rahim_
_1_
Kamar saukar aradu tsohuwar nan ta d’aga hannu ta gaure matashin saurayin dake gabanta da mari, cikin d’aga murya da b’acin rai ta nuna shi da yatsa tana fad’in “Wallahi ko zaka mutu ba zan tab’a bari ka auri karuwar nan ba, *Junaid* ko ubanka dana haifa bai isa nace ga yanda za ayi ba yace a’a bare kuma kai daya haifa, in zaka auri wacce na zab’a maka ka aura, in kuma ba haka ba to ka sani zaka mutu a matsayin wanda bai b’ata aure ba har abada.”
A hankali ya d’ago daga sunkuyar da kan da yayi tare da d’auke hannunshi akan kumcinshi ya kalleta, kyakyawa ne sosai wanda ya had’a komai da komai, abun mamaki kuma shine wasu matasan guda biyu dake tsaye daga bayanshi wanda suke matuk’ar kama, sai dai kaman wad’ancen matasan tafi k’azanta matuk’a da alama ma ‘yan biyu ne, cikin ladabi yace “Hajia kiyi hak’uri idan abinda zan fad’a zai b’ata miki rai, amma a gaskiya ina son *Maryama* kuma ita nake so na aura, Hajia munyi iya k’ok’arin mu wajen yi miki biyayya, mun bar abinda muke so saboda ke, na zama malamin makaranta ba dan raina na son haka ba, amma a gaskiya yanzu abune da zaiyi wahala, dan magana ce ta aure, rayuwa ce da ake saka rai idan har anyi to sai mutuwa ce zata raba, kenan taya zamu yarda mu auri wanda ranmu baya so? A gaskiya ni dai ba zan iya ba, kuma iyayena sun amince na aure ta haka ma Alhaji ya amince.”
Wuyan rigarshi ta finciko ta tilasta mishi kallon fuskarta tace “Junaid ni kake kallo kake fad’awa wannan maganar, to ka sani ni ce shugabar gidan nan sai abinda nake so akeyi, daga kai har uban naka zan iya tsine muku albarka idan kuka ce wannan yarinyar zaku shigo min da ita a cikin gidan.”
Sakin rigarshi tayi har saida yayi baya amma ya tsaya cak yana kallonta, gyara tsayuwarshi yayi yace “Shikenan, tunda haka kika ce ni zan bar gidan nan naje can na auri wacce raina yake so, kuma wallahi…”
Bai k’arasa ba mahaifiyarshi *Zeinabu* ta d’auke shi da wani sabon marin tana fad’in “Kayi mana shiru anan.”
Sake dafe kunci yayi yana kallonta da mamaki, ita ma kallonshi tayi duk da tana goyon bayan wacce yake so ya aura, amma dole tayi haka saboda k’arshe abin kanta zai koma, da yatsa ta nuna mishi k’ofar fita tace “B’ace min da gani, kuma kar na sake jin motsinka a gidan nan idan bani na neme ka ba.”
Ya juya zai fita wata kyakyawar tsohuwa wacce fuskarta ke d’auke da tsaga wacce ake caccakawa sai tayi bak’i ga kumatu da kuma gefen bakinta, cike da dattako tace “Kai Junaid, zo nan, ba kamata yayi ya fita ba, mafita ya kamata a samu a game da matsalarshi, ba wai mu barshi haka ba.”
Mahaifin Junaid d’in wanda suma na gani su biyu duk kamarsu d’aya, kuma abin sha’awar ba zaka ce sun haifi kamar wannan zargadan zargadan matasan ba saboda yanda suke tsaye da kyau zaune da kyau, saidai mahaifin Junaid d’in jikinshi yafi murd’ewa kasancewarshi *soja* a cikin sojojin ma *colonel* ne, kamar baya son magana saboda yanda yayi maganar yace “Ku barshi ya tafi kawai tunda saiya mana rashin kunya ne zamu yarda da k’udirinshi.” *colonel Hussein Suley Hassan Gaga* kenan wanda ko wajen aiki akafi kiranshi da Hassan Gaga.
Mai kama dashi ne sak mai sunan *Hassan* wanda shine babba yace “A’a d’an uwa ba ayi haka ba, ya kamata a tattauna a tsanake dan duk yanzu kowa zuciyarshi tafasa take.”
A harzuk’e kyakyawar tsohuwar nan wacce kallo d’aya zaka mata kasan asalin buzuwa ce tace “Babu wani tattaunawa da za ayi game da maganar nan, na gama magana dan haka babu buk’atar sake taso da ita, ba zai tab’a auro karuwa ya kawomin a cikin zuri’a ba.”
Tana fad’in haka ta wuce zuwa inda zai sadata da nata d’akin baccin kasancewarsu a babban falon gidan, sai lokacin kad’ai wani santalelen tsoho dake zaune yana kallon kowa ya bita da kallo da wani murmushi a fuskarshi, uwayen ma duk barin wurin sukayi rai a jagule, tsohon kad’ai ya rage sai matasan nan guda hud’u, Junaid ne ya juya zai fita tsohon yace “Junaid, kaje ka ci gaba da k’ok’arin samun yardar Maryama, zaka aureta, wannan alk’awari na ne gareka, kaji ko?”
Da murmushi a fuskarshi yace “Nagode Alhaji, Allah ya saka da alkairi.”
Juyawa yayi ya kalli yan uwanshi, cikin farin ciki biyu suka rumgume shi sai d’aya da yace “Ko ba komai zakayi bacci cikin farin ciki, nima Allah yasa ta amince da zab’i na.”
Murmushi sukayi sosai sai Junaid d’aya rad’a mishi a kunne “Ai kai ahalinta ce kake so, zata amince da gudu ma, idan bata amince ba ka mata bore irin nawa.”
Dariya suka sake sakawa sai d’aya daga ciki daya juya ya kalli wanda ke zaune yana latsa wayarshi alamar shi duk matsalolin nan ko a kwalar rigarshi, girgiza kai mai matuk’ar kama da shi yayi yace “Yanzu yaya *Ammar* kai ko ka tayashi farin ciki ma.”
Tabbas saurayin da gani kasan akwai shan k’amshi da d’acin rai da kuma miskilanci, dan ido kawai ya zuba mishi ya kalleshi take kuma ya d’auke ya ci gaba da abinda yake, d’aya saurayin ne yace “Kunga barshi da halinshi, watak’ila allurar sojojin ce ta motsa.”