Sadi Sakhna
Stories
1
Chapters
34
Words
150.2 K
Comments
0
Reading
12 h, 31 m
-
Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi…
-
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika…
-
A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah…
-
Sauri take tayi cikin duhun dare,da alama fitsarine ya kamata sosai. Tazo daidai hanyar shiga banɗakin taga alamar wulagawar mutum a sashen goje. Ƙiftawa ido tayi tasake ƙiftawa,dan zaton ko aljani tagani,saidai kuma ta kawar ta hakan a ranta ta wuce banɗakin. Bayan tafito harta nufi ɗakinsu saikuma tashi alamar motsi a sashen kumadu. "To waye ne yashige sashen goje,shekara biyu kenan yadaina kawo mata,tunda kowa yasan babu abinda zai iya yi musu,to waye kuma a sashennasa?" Harzata shiga ɗakin kuma…
-
"Uhm karki ce mai yasa na tambayeki,amma menene haka kike nema a wajen wannan yarinyar,abinfah ya wuce yanda kike zato. Bayan bacewarta daga garinnan komai yafara tafiyah normal,saidai kuma mahaifiyar ta inna Danejo bata manta da batan ƴar ta ba,dakuma mummunan zagin da ake binta dashi. Hakanne yasa abin yafara damunta da kaɗan kaɗan,ga kuma dama ciki mai wahalarwa. Ba a tashi sanin mai ya faru ba har saida tazo haihuwa matsala ta tashi gadan gadan. A nanne mlm Ahmadu ya kaita asibiti amma tagagara…
-
Muryar wani mutum taji daga bayanta yana cewa. "Ku shiga ciki ku ɗauresu,sannan ku zubaminsu a bayan mota,karku manta da ɗauremusu fuskokinsu" "Okay toh" Mutane guda biyune suka shigo motar tareda ɗaure musu hannayensu da igiyoyi,bakin kyalle aka saka a fuskokinsu,daga aka tasa ƙeyarsu zuwa cikin wata motar. "Maza kai toro jawo motar tasu ku tafi,zamu miƙasune ga itah,sai sun faɗi dalilin dayasa suke nemanta,sannan kuma wanene ya aikosu" Daga haka su Hajiya zeenah basu sakejin komai ba sai gungurawar…
-
Sauƙe ajiyar zuciya tayi ganin ashe akwai ƙaramin wando a cikin dogon daya cire,saidai kuma an gudu ba'a tsira ba,gani tayi wandonnasa yana ɗagawa kaman wani abune yake motsi a cikinsa. Dariyah ya kece dai ta ganin inda idonnata ya sauƙa,wato kan hajiyar sa. "Hhhh ƙwaila kenan,tun ba akai ga komai ba harkin fara karayah,ima tsiwar taki da aka bani labari toh,ki shiryah yanzu zanyi miki abinda nake wa sauran ƴaƴa wanda kike ji da kunnenki a gari. Naji dama ance kinzo gidannan neman sanin wayeni…
-
Bombee ce tashigo ɗakin,ta iske innar tata zaune cikin tunani,batasan mai take saƙawa ba,amma tasan bazai rasa nasaba da auren da baba yake shirin yimata ba. "Inna......inannnaaaa" Zabura Daneji tayi tareda ɗagowa ta kalli Bombee wacce take tsaye akanta. Alamar itama damuwa ce akan tata fuskar,don duk abinda take bata son kuma abinda zai saka innarta cikin damuwa,musamman idan yazamo wani ne taban yayi sanadiyyar hakan,kowaye shi saitayi maganinsa. Kasancewarta ba babba ba,amma tana maganin manyan ta…
-
Wulgawar Bombee innayi tagani tana cin abinci, yaukuma ta dawo da wuri.innayin tafaɗa a ranta,kullum sai yamma liƙis take dawowa idan ta tafi makaranta,wani lokacinma sai dare yayi tukunna.Sau uku mlm Ahmadu yana kamata yana dukanta,amma ko kuka batayi,sannan kuma bata faɗi inda take zuwa ba,sannan kuma bata fasa kaiwa daren ba. "Inna Daneji Addah Bombee tadawo tana ɗakinmu" "Yauɗin kotaji magana babannku kai,amma a wanne yanayi tashigo" "Uhm hannun duk jini har ya bata mata uniform ɗin…
-
Wani yarone ya shogo gidan da takarda a hannunsa cikin envolope,Innar iyani ya fara gaisarwa,wacce take zuzzuba abinci a kwanuka. "Uhm dama watace ta aikoni gidannan wai nabawa Hajiya zeenah abinnan" Iyani tanajin haka tayi saurin karbar takardar tareda cewa. "Wacece matar,tana waje har yanzu?" "Tasaka nikaf,tana bani takardar tajuyah ta tafi" "To shikenan jega an gide,bari dama zan kaimata abin karyawa saina tafi mata dashi" "Wani kallon mai kuke ƙullawa innartata tabita dashi,ganin bazai kaitaba ta…
- Previous 1 2 3
