Sadi Sakhna
Stories
1
Chapters
34
Words
150.2 K
Comments
0
Reading
12 h, 31 m
-
Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa. Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata. A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta'ba mantawa ba. Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan…
-
Kwatancen da mai masarar ya gwada mata tabi tiryan tiryan har ta samu kanta a ƙofar gidan su goje. Tsayawa tayi a bakin dangar gidan ta riƙe kunkumi tana kallon gidan. "Hmm wai nan gidan baba yakeson nazo na zauna na ƙare rayuwata,nida nakeda burin fita daga nahiyar nan,shine zanzo wannan wajen na zauna,lallai baba yanzu na tabbatar ya rainamin hankali ba kaɗan ba,shi bayyi zaman irin gunnan ba saini Bombee?" Maganar ce daga bazata kaita ba,dan haka kawai tasaka kai cikin gidansu goje babu ko…
-
Bugun ƙofar da ake ne yafarkar da ita daga baccin gajiyar daya ɗauketa. A hankali take buɗe idonta har ta waresu akan rufin ɗakin,wanda aka haɗa da zare da kuma jarida. Tashi tayi ta zauna a tsakiyar gafon tareda yin wata kyakykyawar hamma,kaman wanda ta shekara bataci komai ba. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayiwa ɗakin,ta tabbatar dai ita kadaice ta kwana a ɗakin kenan,angonnata bai shigoba da alama,to mai yahanashi zuwa ta faɗa a ranta,ganin hakan zai bata mata lokacin yasa ta bar ma…
-
Bayan shekara biyu............. Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi ɗamara da wani jan ƙyalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama. Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma ƙwarewa. Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata. Sai can kaman da daƙiƙa uku ta tsayah…
-
"Nayi wa headmaster ɗinku magana,kan cewar zakije kosake rubuta common,tunda wancan din sun bata miki ita saboda tantirancinki,na roƙeshi ya yarda,dan haka ki shiryah kije ki rubuta,idan kinci zan turaki makarantar kwana" "Baba waini bokonnan dolene ne,duniyar ma fah takusan tashi kowa yasan inda zai shiga" "Yanzu duk abinda nayi haka kika ce,wai tukunna ma kinji mai nacene. Idan duniyar ta tashi ai irin bakwa cikin rabo,ki faɗamin wane abin arziƙi kikeyi guda ɗaya da za'a shaideki da ita" Yamutsa…
-
A zaure mlm ya hadu da Bombee tashigo gidannasu,shikuma zai fita sallahr magriba. Kallonta yayi na ɗan sakanni kana ya jijjiga kai,inda duka da faɗa suna yin aiki,da sunyiwa Bombee a ƴan watanninan,amma abinnata gaba gaba ma yakeyi kaman ana watsawa wuta fetur. Shuru tayi taji mai zaice,saidai ga mamakin ta,waucewa yayi batareda yace mata komai ba,sauƙyƙyƙyiyar ajiyar zuciya tasaki,dan dama hakan takeso kada yayi mata maganar. Kao tsaye ɗakinsi ta wuce tacire kayan jikinta,ta canza wasu daban,sallah…
-
Dukkansu sakin ajiyar zuciya sukayi na takaicin sakarcin Bombee ɗin,saidai babu yadda zasuyi ba laifinta bane,tunda kowa yasan ita yarinya ce,sannan a yanda take da kasada,da kuma yanda goje ya farmaketa,koma waye iya abinda zayyi kenan. Malm Ahmadu bashida zabi illah ya ɗora kusan dukkan laifin a kansa,tunda shine ya aurarta batareda tasan komai ba. Shiryawa yayi shida su jauro suka nufi asibitin,domin ganin jikinsa tanan kuma zasu wuce police station akan case ɗin. Bombee kuwa ganin kowa ya dauke…
-
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin ɗakin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata. Labulen ɗakin ta ɗauke ta rataye ,hasken rana yashiga ɗakin,domin yabawa ɗakin ishashshen hasken dazata ganta dakyau. A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba. "Bombee" "Na'am ta amsa a dake" Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita. "Shin menene ya farune kika…
-
Saka ƙafa yayi yaƙara takata a ƙasa haɗeda cije baki. "Faɗamin ina so ki amsa cewar ke mayyace,baƙar mayyah babu abinda ya dace dake sai duka dakuma hantara,kar ma ki sake gigi cigaba da zama a ajinmu. Kunkoroki munyi miki komai amma kinƙi barin ajinmu ko,saboda ki nuna mana halinki na mayu,to idan muka koma gobe naganki a cikin ajinmu sai dakaki" "Zulaiha ce taƙarisa faɗin hakan,ƙanwar bello abokin sule. Da Bombee a primary 5 A take,saboda yanda suka maidata kaman jakarsu,yasa mlm Ahmadu yaroƙi…
-
Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah. Lylah ce ta kulada ita tace. "Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?" "Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daɗinsa ko kaɗan" "Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan" Hajiya Zeena ta faɗa tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi…
-
Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska. Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta. Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature…
-
Buɗe ido tayi ta kalleta a wani ɗaki mai rufin zana,saidai yanayin zanar wata kalace daban mai ƙarfi da kuma adon rawaya rawaya. Abinda ya farune yafara tariyowa cikin ranta. Kama daga fitowarta daga gida neman wacce zatayi mata maganin lubna,harma da kuma shigowarta wata duniya sabuwa da tayi. Zabura tayi ta miƙe tareda ya mutsa fuska,jikinta yayi tsamin kaman anyi mata dukan tsiyah. Tambaya tafarayi a cikin ranta,akan nan ɗin inane,batakai ga samun amsar tambayar ta ba,kokuma son tunowa yaushe ta…
- Previous 1 2 3 Next
