Maryam Farouk (Ummu Maheer)
Stories
1
Chapters
60
Words
247.6 K
Comments
0
Reading
20 h, 38 m
-
Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin. "Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce "Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?" "Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya…
-
247.6 K • Completed
-
-
Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara ko ina sai jiran…
-
247.6 K • Completed
-
-
Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne. Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya…
-
247.6 K • Completed
-
-
Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 *KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta tura mun kuɗi na a asususun…
-
247.6 K • Completed
-
-
Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da…
-
247.6 K • Completed
-
-
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽 A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce "Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya…
-
247.6 K • Completed
-
-
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽 Cike da ƙaguwa da zancen ya ce "Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?" "To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce "Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama…
-
247.6 K • Completed
-
-
Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar. Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake…
-
247.6 K • Completed
-
-
ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi. "Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya. Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida. Kallonsa ta ringayi har ya…
-
247.6 K • Completed
-
-
HALIMA Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida. Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje…
-
247.6 K • Completed
-
-
Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace "Ina kika tafi tun ɗazu?" Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa "Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita. A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce "Get in".…
-
247.6 K • Completed
-
-
Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita. Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙalau lokaci ɗaya…
-
247.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 4 5