Janafty
Stories
1
Chapters
57
Words
384.6 K
Comments
0
Reading
1 d, 8 h
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min yaudaran su na maza…
-
384.6 K • Completed
-
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Tun da cikin Gimbiya ya kai watan fitowarsa duniya Yallaɓai ya tattara gabaɗaya hankalin shi a kanta. Da a ce ya ga fuska zai ce ne na bashi dama ya koma can da zama har sai ta haihu tun da ga shi anguwan zoma. Sai dai bai samu wannan fuskar ba, ko da ya ke mene ne maraba da abin da ya ke yi. In ya na gidanta ba koda yaushe ya ke leƙomu ba sai dai ya kira waya in ko ya na gidana kwana kawai ke kawo shi tun…
-
384.6 K • Completed
-
-
Duk da na bar ma Yallaɓai ɗakin sai da ya ƙara biyo ni falon. Ina zaune ina cin dankalin hausa ɗanye kitchen na shiga na ga Jidda na ferewa wai shi ta ke sha'awa za ta soya ta ci nima nan take na ji ya shiga raina sai na ce kawai ta fere da ɗan yawa sai mu ci gabaɗaya. Shi ne kafin na taho na ɗauki wanda ta feren ƙarami na wanke na taho da shi falon Yallaɓai na zauna ina gutsira a hankali ina jin daɗin sa a bakina da cikina gabaɗaya. "Aa Hajiyar mota nan kuma a ka dawo? Wani kallo na yi masa…
-
384.6 K • Completed
-
-
Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen sha ɗaya na safe su Jidda ma shi dai ya fita suka gan shi suka gaishe shi. Daman ba sa jira na yanzu sun girma komai na buƙatunsu, su suke yi ma kan su. Sai alokacin na samu damar yi ma Yumna wanka sannan nima na shiga wankan kuma na bar mishi Yunma kwance a gefen shi shi kuma yana duba abu a cikin laptop ɗin shi. Ina fitowa ɗaure da Towel a ƙuguna na iske sa har ya gama abin da yake yi ya ture laptop ɗin gefe. Tambayarsa…
-
384.6 K • Completed
-
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* "SADIYA.." Wannan karon a yanayin yadda ya kira sunana sai da na ji jikina ya amsa da ya sa kaina na ƙasa sai da na ɗago na kalle shi. Tabbas a cikin idanuwansa na hango kamar hawaye sun cika masa kwarmin idanuwa kuma na hango gajiya da haƙuri harda kunya a lokaci ɗaya. "Sadiya.." Ya sake furtawa cikin wani irin rauni. Raunin da har ina jin sautin fitar shi daga muryansa. "Sadiya.." "Ta.." Ya sake faɗa…
-
384.6 K • Completed
-
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Ƙarfe tara da rabi na dare sai ga Yallaɓai ya dawo shi kaɗai ya ce min ya ba ro su Tariq a gidan mai za su saka mai amotar shi kuma sai ya hau adai daita ya taho gida ya yi wanka ya shirya kafin lokacin sun taho sai su raka shi can gidan Gimbiyar. Kamar ya sani bai ko neme ni na haɗa masa ruwan wanka ba, ba domin in ya ce na yi ba zan yi ba sai domin zuciyata a lokacin ba ta cikin sukuni, muna gama maganar…
-
384.6 K • Completed
-
-
Ranar alhamis su Jidda suka yi hutun makaranta. Jidda daman ita ce ta ke ɗaukan first postion a ajinsu Baby kuma Third, sun karɓo kyatuttuka tunda an yi speach and prize giving day ban je ba amma Yallaɓai ya je musu tare ma suka dawo. Ko da suka dawo mai kitso ta zo, da mai ƙunshi har an yi min ƙunshi saura kitso. Marwa daman ta na nan domin ni na ce ce ta tattaro, ta dawo wajena sai an gama biki, Amina ma ta iso tun azahar Hauwa da Munnira suna gidan suma tun safe sai zlZaitunan yaya…
-
384.6 K • Completed
-
-
Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata. Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daɗe a jikinsu ne ba a sani ba alhalin…
-
384.6 K • Completed
-
-
Da sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi. Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne. Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma kan kujera na zauna sai na…
-
384.6 K • Completed
-
-
Kamar a zahiri kallonsa na ke yi amma a baɗini ba shi na ke kallo ba. Hankalina da tunani ya yi nisan kiwo. Jikina gabaɗaya ya saki sai na ke jin kamar ba zan iya ba, kamar za'a ga gazawata in tafiya ta yi nisa. "Kin yi shuru ba ki ce komai ba Sadiya." Shi ya katse min tunani da ya sa na dawo hayyacina. Ajiyar zuciya na sauke kafin na maida hankalina zuwa ga kallon ƙasan cafet ɗin da ke gefen gadon. Ina so na yi magana amma sai na ji kamar an ɗaure min baki zuciyata ta yi wani irin nauyi sannan…
-
384.6 K • Completed
-
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* Yallaɓai fa miliyoyi sun dira a cikin account ɗin sa na banki ba zama. Tun safe ya fita ya ma riga yara fita saboda sauri, bayan kuma tun asuban fari ya fara waye waye da mutane bakinsa ya kasa shuru. Ni fa tun a farkon auran mu tun ina mamakin halin Yallaɓai har ya zame min jiki, in ya yi wani abin na daina ganin sa a sabo a wajena. Tun da na san shi, shi ne mutun ƙwara ɗayan da zan ce na sani mai bayyana…
-
384.6 K • Completed
-
-
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE* RANAR ƊAURIN AURAN GIMBIYA DA YUSUF. Ya ji tsoro da kiran Nene shi a tunanin shi kiran gaggawan da ta yi masa ko jikinta ne ya tashi, kuma ta ce ya zo gida da gaggawa tana neman shi sai ya firgita shi ya sa ya fita ko ƙaryawan da Sadiya ta matsa ya tsaya ya yi bai yi ba ya ce sai dai in ya dawo. Bai taɓa kawo ma kansa hashashen ga in da kiran Nene ya dosa ba saboda a yana hanya ma kafin ya ƙariso gidan sai…
-
384.6 K • Completed
-
- 1 2 … 5 Next