Janafty
Stories
1
Chapters
57
Words
384.6 K
Comments
0
Reading
1 d, 8 h
-
Sanda su Ma'u suka ɗau hanyar gidansu da ke Rijiyar zaki. Zaune ta ke a bangaren mai zaman banza, kamar ba ita ce ta gama kuka wurjajan ba. Wannan karon mirmishi ne da Annuri ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyan Ma'u kuma har ya ke iya bayyana a saman fuskarta. Mijinta Alhaji Mustapha na tuki, sai ya waiwayo da hankalinsa zuwa kanta a tunaninsa har a lokacin ba ta bar kuka ba, amman ga mamakinsa sai ya ganta zaune tana mirmishi. Cikin mamaki ya ce"Har kin huce kenan Hajiyata? Kallonsa ta yi ta na ɗan…
-
384.6 K • Completed
-
-
Tun ranar farko da na fara ganin Yusuf na ji a raina tabbas na haɗu da namijin da ya gama cika zaɓina. Sannan na san tabbas zai iya yin katanga da cikar burina na sai na gama Jami'a na samu aiki zan yi aure. Saboda in na bari ya suɓuce mini samun kamarsa zai yi mini wahala Tun da gashi tuntuni ina tsumayen shi. Shi wanda ya dace ɗin amman ban samu nasaran haɗuwa dashi ba sai a wata ranar laraba. Daga cikin BUK na ke mun gama lacture tun safe har yamma na sha wahala ina tafe kamar zan faɗi, ba zan…
-
384.6 K • Completed
-
-
Present. Da safen tea muka sha gabaɗayan mu amman ban da Yallaɓai saboda kamar akwai gajiya a tare dashi. Tun bayan da ya dawo daga sallar asuba ya kwanta yana ta barci sai na ƙyale shi tun da na ga har wayarsa ma sai da ya kashe. Da wuri Saude ta zo na saka Jidda ta fito da kayan na su. Daga kitchen ɗina akwai wata kofa dake fidda mutum ta can baya in da muke yin wanki ko shanya. Ko tara ruwan sama can na ce su je su yi wankin har da Baby da ta saka rigiman sai ta yi na ce a ƙyaleta ta yi. "Umma ba…
-
384.6 K • Completed
-
-
Aminu kano Teaching Hospital. Gynecologist Unit. Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai. Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi…
-
384.6 K • Completed
-
-
Mutuwa ɗaya ce haƙiƙa na tausaya mata ganin ko shekara biyu ba ta rufe da auran ba. Yallaɓai a ranar suka tafi Abuja tare da Uncle Abba da Nene, da Anty Maimuna Anty Bahijja za ta taho daga baya. Sai Hajiya iya Maman farko kaɗai aka bari a gida. Can suka kwana Tariq da Farida daga kaduna suka tafi. Ni kuma ranar litini na je ganin likita sai ranar na je lab na karɓo sakamakon test ɗina na kai mata shima ta ce lafiya lau ba wata matsala. Sai muka je matakin gaba na A transvaginal ultrasound. Ta ba ni…
-
384.6 K • Completed
-
-
Shirye shiryen biki Yaya Usman kawai ke kan layi yanzu saboda bikin ya rage saura kwana takwas. Kuma da ya ke bikin anan Gwammaja za a yi ita kuma Amarya a Kaduna gidan kakkaninta wanda ya haifi mahaifinta. Shima tsohon Soja ne mai ritaya amman ya rasu. To nan za a ɗaura aure ranar asabar amma taron biki ranar jumma'a ne asabar da an gama ɗaura aure amarya da tawaganta za su sauka a Kano sai ranar litini ango zai ɗau amaryansa da iyalansa su hau jirgi zuwa fortacol Kuma auran daman na yan boko ne lefe…
-
384.6 K • Completed
-
-
Azumi ya raba tsakiya, mun gama goma na marmari mun shiga goma na wuya kamar yadda hausawa ke faɗi. Yau in muka kai azumi mun kai sha biyar kenan, a duka shekarun da muka kwashe da aure ni da Yallaɓai na saba duk watan ramadana Yallaɓai ba ya kaiwa dare a waje a gida ya ke yin buɗe baki tare damu haka ya sabar mana kuma nima haka na saba. Amma wannan azumin sai al'amarin ya ɗan sauya. Saboda ya samu kwangila gina ma'aikatan nan na kaduna gabaɗaya ma'aikatan shi suna can kaduna shima yana zuwa har…
-
384.6 K • Completed
-
-
Mun yi azumi ashirin da tara 29 ɗaya ga watan shawwal ya kama ranar asabar ne a ranar muka sallaci salla ƙaramar salla. Mun je idi mun sallaci salla tare da al'ummar Musulman duniya gabaɗaya ni da Yallaɓai da yara sai Marwa da ta yi salla tare da mu. Bayan mun dawo idi na saka Marwa ta dafa jallop ɗin shinkafa mai nama. Tun a daran jiya muka gama duka soye soyen mu Saude da Marwa sun taimaka mini ƙwarai shi ya sa jiya da Saude za ta tafi da daddare Musabahu ya zo gidan da shi na haɗa su na ce ya kai…
-
384.6 K • Completed
-
-
Rahila ce jirgin danƙaro ita ce karshen zuwa har sai da na yi mata tsiyan tana kusa amma itace ƙarshen zuwa. Tana dariya ta ce " Ni fa na ɗauka ni ce ma farkon zuwa kawai sai na ga gida ya cika." Muna ta mata dariya ni da Ya Balki. Amina ta kira waya da ta ji gida cike kowa da kowa na nan kamar ta yi kuka ta ce ta yi missing. Ta so zuwa amma ba ta samu dama ba sai dai ta ce sallar layya in sha Allahu da ita za a yi. Ya Auwal kuma ni na kira shi a waya ya ce sun ɗan fita da laila ne da yara gidan shuru…
-
384.6 K • Completed
-
- Previous 1 … 4 5