Al’amarin Maryam Na Rahamatullah Muhammad
*BISMILLAHIR* *RAHMANIRRAHIM*
~wannan~ ~qirqirarran~ ~labarine,~ ~banyi dan cin xarafin wani ko wata ba, cin karo da rayuwar wani ko kamanceceniya da yanayin rayuwar wanine wannan~ ~”arashine~
”Wasu Yarane guda biyu mata, na hango a tsakar gidan, sun takure cikin filin tsakar gidan, daga can lungu babu kowa saisu,
Yar babbar bazata fi shekara goma ba xuwa sha daya, while qaramar yar shekara hudu, suna gun Har rana ta fara zafi, garin ya fara dan zafi zafi, suna takure a wurin, can naga wata mata ta fito ta dubi shashin da yaran suke ta hade rai,, tace ke fati! dan munafurci kunanan zaune a wurin nan salon ki jawowa mutane magana? Yarinyar da aka kira da fati ta dago cikin firgita, saboda jin muryar matar da ta kira sunanta, tace a a Umma,
anty ce tace mu fito xata gyara dakinta, oh⦠ta furta tare da yin gaba,
wacce aka kira da Fati tai saurin dauke kan qaramar yarinyar daga kan cin yarta,
tare da cewa Mimi xauna naje na karbo miki magani gurin Umma, ta miqe tabi bayan umman, tana xuwa akofar kicin din ta tsaya, cikin jin tsoro,, tace Umma Mimi ce bata da lfy, jikinta da kanta yayi xafi sosai, dan Allah idan kinada magani ki bani na bata, umma ta watso mata harara, tace to uwar kinibibi, nida kikaxo wurina kika fadamun chemist gareni? Ko ni na dora mata ciwon? Sai ki bari idan ubanku ya dawo ki fada masa, taja tsaki tace wuce kiban wuri, fati tace toh π sannan ta koma gurin yar uwarta ta tallafo kanta ta mayar a cinyarta ta kwantar, tare da cewa Mimi yi hakuri kinji Baffa ya kusa dawowa, zai kaiki chemist kinji?
” a Haka suka yini a tsakar gidan, duk inda inuwa take sai su koma can, idan wannan inuwar ta jaye su koma wannan har xuwa sallar magriba, Kuma sai lokacin ne Baffansu ya shigo gidan, direct dakinsa ya shiga, fati da tun rana take dakon shigowarsa tayi saurin binsa, ta durqusa har qara tace Baffa sannu da xuwa,yace yawwa fadimatu, sai tace Baffa dama Mimi ce bata da lfy, zazzabi take da ciwon kai, Ya dago ya kalleta cikin rashin fahimta,
yace wacece kuma Mimi?
Can ya nisa⦠sannan yace au wai MARYAMU kike nufi? Tace eh Baffa, sai baffa yace wai yarinya da sunanta kun saka mata can wani sunan banxa, sunan gunki, yace tafi gurin ummanku idan tana da magani ta bata, sai fati tace Baffa tun daxu na tambayeta tace bata dashi.
Sai yace toh jeki gurin antyn ku, ya fada tare da shigewa cikin bedroom dinsa, saita tashi ta tafi gurin anty, Koda taje gurin daya matar gidan wacce suke kira da Anty, ta fada mata saqon Baffan xaginta ta dungayi, ta uwa ta uwa,,
kamar wata sa’arta, kuma dama can tafi tsanar yaran da saurin daukar xafi akansu , yayin dasu kuma suke bala’in tsoronta tamkar mala’ikan daukar rai,, da gudu tabar gunta tadawo ta rumgume Mimi wacce jikinta ya qara xafi, ko tuwon da aka miqo musu Sun kasa ci, duk ta rikice ta shiga damuwa sosai sbd halinda Mimi take ciki, Sam fati takasa cin tuwon,
mimi kuma sbd zafin ciwo ko bude idonta takasa yi balle taci abinci, π
” Wararen 8:30 pm fati taga jikin Mimi yayi tsakani, kuma babu wanda keda niyyar taimakonsu a cikin gidan nan, hakan yasa ta goya mimi ta fita waje, tana tafiya cikin anguwar kadan kadan, tana cikin tafiya ta hadu da Ahmad, (wani maqocinsu ne wanda baifi 15-16 yrs ba) ya tsayar da fati , tare da cewa… Fatima Mesa kika fito a wnn lkcn? Ta share wahayen dake fuskarta, sannan tace Mimi ce bata da lfy, kuma nakasa samun magani a gidanmu,
yace to yanxu ina xaki da ita? Tace chemist xan kaita, sai yace to kinada kudi a hannun ki? Tace a a fadane tana xubar hawaye, to yi haquri muje inada kudi danake tarawa na makaranta danake ragewa Ina ajiyewa, muje saimu kaita chemist, tace to ya karbi mimi ya dorata a kafada suka qarasa chemist, mai tsaron chemist din ya dubata tare da yimata allura, sannan ya bata magunguna, suka bashi kudi har suka samu raguwar canji, dake lokacin duniya na kwance, ya rakasu Har cikin gida, tare da ledar maganin,
ya bawa fati sannan ya juya, tayi masa gdy, ta zauna ta bude magunguna ta bata kamar yadda yake a rubuce, sannan suka nemi gurin kwanciya, Tym to tym fati takan tashi ta duba ta tataba jikin Mimi, har saida taji jikin Ya danyi sanyi, sannan tasamu nutsuwa, daganan bacci yayi awon gaba da ita tana mai godema Allah,
~Mrs Muhammad~ π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: π·AL ‘AMARIN MARYAM π·
3β£
Fadima xaune ita da yar uwarta khadija wacce take kira da Adda Khadija, suna tattauna batun auran fadimar da ake shirin yi, Khadija ta dubeta nidai na fadawa Baba ya qara jaddada masa maganar karatunki kya samu sauqin wani abun inkina ficewa kina barin gidan, ta danyi murmushi ta Kalli Adda Khadija, Adda dan Allah kar kubari auran nan ya dau lokaci saboda wlh na matsu na koma kusa da yayana Kullum cikin mafarkinsu nake acikin mummunan yanayi. Khadija tace to fadima in shaa Allah baxai wuce sati ba.
Jamila (anty) kamar yadda yaran gidan ke kiranta xaune kan kujerar roba a tsakar gida ta harde qafa tana bawa fati wacce ke wanke wanke order, yarinyar jikinta sai rawar sanyi yake ga kuma uban tsoron antyn da takeji uwa uba jibgin wanke wanken da yafi qarfinta gashi koyaya tayi kuskure ko avunda bai gamsar da Anty ba sai ta dako mata tsawa tare da xagin uwarta har ubanta na kabari bai tsiraba daga xagin anty, ana cikin hakane Baffa ya shigo gidan da yake yau juma ‘a baya fita da wuri sai an sakko daga masallaci. Ya dubi fati sannan ya Kalli shashin da jamila take yace ya haka? Ina sauran yaran gidan? Duk wannan aikin ita kadai? Eh ita xatai ta furta cike da isa, ko kana nufin ban isa sata aikin bane? Kafin yakai ga furta wani abun Umma ta fito daga dakinta kamar anjehota ta tsaya tana watsawa mijin nasu harara cike da takaici sannan ta furta kema dai jamila, ai sabida tsinanniyar uwarsu ta amince da maganar auransa shiyasa yake wannan abun, ai wlh kaji kunya matar qaninka xaka Aura dan cin amana, itama shegiya yar akuya ta kwanta da qani yanxu tana harin kwanciya da yayansa. Jamila tayi saurin katseta dakata Hajara itafa bata da laifi, saboda yayanta ta amince da auransa tunda ya hanata yayanta da yabata su ai da ai hakaba, dama tun dan uwansa na raye yake qulafacinta shiyasa da dan uwan ya mutu ya fake da cewa bazaibar yayan dan uwansa suyi agolanci a wani gidanba, inkuma tanasan xama da yayanta taxo gidansa a matsayin matar aure ta zauna dasu. Baki Baffa ya bude jin sharrin da jamila tai masa na cewa yana qulafacin matar Al amin tun yana raye, ransa yayi mutuqar baci da wannan maganar hakan yasa yace wlh duk matar tada kuma fadar wata magana kuma naji akan aurannan wlh saina saketa. Sannan ya juya batare daya shiga dakin da yayi niyyar shigaba yayi gaba. Tsit sukayi saida suka tabbar ya fita sannan jamila ta furta andaiji kunya raqumi ya shanye ruwan dan tsako, Hajara kuma tace ke kuwa anga jar mace shiyasa yaketa wannan bare baren. (yan iskan qarya da kufada mana agabansa π). Tun bayan amincewar fadima da auran Baffa yayanta suka kuma shiga takura har abunda ba ayi musu ada yanxu anai musu kamar hanasu abinci da duka xagi kuwa ba a magana domin da yana fitowa da jikinsu ya cika taf da xagi. Yanxu ma hakace ta kasance fati na duqe tana wanke wanke kamar yanda aka dora mata safe da yamma, Mimi tace yaya fati xanyi fitsari tace to Mimi matsacan kiyi ta nuna mata nesa da inda take wanke wanken tatafi taje ta tsuguna, itadai batasan yanda akaiba sai jitayi anyo jifa da Mimi cikin kayan wanke wanken ta dago a firgice yayin da mimin tasaka wata uwar qara cike da azaba da firgita Zainab ce tsaye akansu tana huci, tace da fatin ke dan kutumar ubanki acikin kayan wanke wanke xakisa tai masa futsari saboda ke jakace? Tace a a anty Zainab wlh acan gurin tayi ba a cikin kayan ba, Zainab ta tsinketa da mari tare da furta qarya nai miki kenan? (Zainab nada daga cikin yan matan gidan kuma yace a gurin amaryar gidan wato anty) hayaniyarsu ce ta fito da mutan gidan, Anty Adawiyya ke tambayar meyafaru Zainab ta mayar musu da inda akai, anty tace yayi kyau gara da kika hukuntata ita kuwa umma ko hmm bataceba ta juya daki hakama ragowar yaran gidan sai Adawiyya ce ta tsaya tanaiwa Zainab fadan abunda tayi, zainab cike da fitsara tace kinga malama babu ruwanki ke ko kishin iyayenki bakyayi idan uwarsu ta shigo gidannan mallake Baffa xatai kamar yadda ta mallake uncle, inba dan Umma na taka miki birki ba da ba asan abunda xaki akan wadannan mayun yaranba. Adawiyya ta bude baki da nufin bata amsa umma dake jinsu daga daki tace wlh Adawiyya inbaki fita harkar yarannan ba saina tsine miki, inaso ki xama yar kallo a harkarsu kamar yadda kowa ya zama, ni duk cikin yayana kece bakisan ciwon kanki ba babbar banxa. Haka fati ta gama wanke waken sannan ta wankewa Mimi jikinta da saboda ruwan daudar wanke wanke ya bata mata kaya tanayi tana shidewa saboda sanyin ruwan ga kuma yanayin sanyin da ake ciki, tana gamawa tajata suka fita daga gidan, wannan dalilin yasa koda dangin mahifiyarsu sukazo kafin kayan daki basu gansu har suka gama suka tafi, kuma basu tambayesu ba saboda gudun fitina dan matan gidan da yayansu sai yadda magana suke da waqewaqen habaici nasan a tanka musu ayi tashin hankali, har suka gama gyara mata daki tas suka tafi. Bangaren su fati kuwa sai magriba suka baro gidan maqociyarsu amarya da suke shiga, tunda aka kawota take jansu a jiki kasan cewarsu yara masu gashi takurar da suke ciki tasasu sakin jiki da ita (dan ma tana tsoron masifar su zainab da babu abunda bazatai musuba) iyakacinta dasu ta kunna musu kallo ta basu abinci ko wanka tai yunqurin yiwa Mimi su zainab xasu taso mata da bala’i. Koda suka shigo gidan babu wanda ya damu dasu balle ya tambayi daga inda suke.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: π·AL ‘AMARIN MARYAM π·
2β£
Haka rayuwa taci gaba da tafiya babu abunda ya canja na dangane da rayuwar yan marayun Allah Fatima da MARYAM haka suke rayuwar kara xube babu ilimin arabi bare na boko domin makarantar bokon tuni suka dena xuwa saboda a cewar matan gidan wai makarantar da suke tayi nisa babu me lokacin kaisu, amma nasu yayan suna da me kaisu da dakkosu makarantar islamiyya kuma har yanxu mai gidan baisamu sakasu saboda bai cika xama ba sai dare yake dawowa daga harkar kasuwancinsa bare matan gidan da suka tsani rayuwar yaran a gidan. Lokaci xuwa lokaci fati ke fakar ido tayi wanka tayiwa Mimi saboda duk gidan babu mai yadda su daukar musu soson wanka, sai kace wasu kutare π, wanki kuwa ba a taba hadawa da nasu ba duk da kuwa akwai mai wanki a gidan sai dai suyi tasa kayan suna cirewa suna tarawa, ( dan ma sunada suturar) kansu kuwa wata kalba ce manya manya da Umma tasa anty Adawiyya tayi musu saboda tun kawosu ba ai musu tsifa ba da fati tagaji da susa ta tsefe nata ta kuma tsefewa Mimi, gashi Allah yayi musu baiwar sumar kai sosai (gashi) da Umma taga susar da suke tayi yawa tasa aka siyo fiya fiya ta bulbula musu a kansu wai a fadarta kwarkwata garesu sannan tasa anty Adawiyya daya daga cikin yayanta kuma yan matan gidan tai musu kalba, domin itace wacce bata tsananta qiyayyarsu a cikin yayan gidan, domin duk yaran gidan kyara da hantara ke hadasu dasu mimin kamar yadda suga iyayensu nayi musu, agurin Adawiyya kawai suke samun sauqi sai ko yayan gidan maza wadanda basu cika xama ba balle har su takurasu, abinci kam basu da matsalarsa Sam domin ko almajiran gidan bazasice suna yunwa ba baresu akan basu duk sanda aka gama insuka rage fati ta ajiyewa Ahmad inya shigo yaci, batun rashin lfyr Mimi kuwa injiki yayi sauki saiya dawo kuma dama Mimi a halittarta mai yawan laulayice, yau da gobe tasa fati ta koyi ajiye yan kudin da Baffa ke basu kan ya fita kullum, (yakan bawa duk yaran gidan kudin kashewa kullum) ta saiwa Mimi paracetamol ta dunga jiqa mata tana bata in ciwon ya motsa. Cikin abunda bai gaxa wata 2 ba yaran sunyi fututu Sun rame sunfita kamaninsu Kai bakace yayan gatane adaba bazaka taba hada kamaninsu da fati da Mimi na wata biyu a baya ba, bazaka taba yarda yayan AL AMIN da FADIMA bane.
Misalin qarfe biyu da kwata na dare 2:15 am fadima kwance kan gadon dakin mahifaiyarta wacce suke kira da hajia, tana mafarki kamar yadda ta saba a yan kwanakin nan. Kamar kullum yauma mafarkinta ya nuna mata Mimi ta fada rijiya fati kuma nata ihun a temaka a ciro mimin amma babu wanda ya kalkesu balle yayi yunqurin temaka musu, sai dai yau sabanin sauran Mafarkanta na baya, ayau sai taga AL A MIN ya ciro mimin ya kwantar a gefe ga alamu babu rai a tare da ita, AL amin din bai furta ko kalma daya ba ya bacewa ganinta. MIMIii! Ta farka a firgice ta sunan mimin a bakinta, ihunta ne ya tada hajia tayi kanta tana tambayarta lfy? Wlh hajia Mimi bata da lfy dama Mimi Me yawan laulayice bare ta hadu da rashin kulawa, nasan duk qarfin xuciyar fati baxata iya kula da Mimi ba uwa itace kawai xata kula da me lalura kamar Mimi, tana furta wadannan maganganunne cikin tsananin kuka, ta dora dacewa hajia ki temakeni zasu kashemun yaya anrabani da yayana ankaisu gurin maqiyana an watsar, πππ Uwar ta kamata tare da rungumeta yi haquri auta kinji kema da naki lefin da kin amsa buqatar yayan mijinki da tuni kina cikin yayanki duk uwa tana sadaukar da rayuwarta dan ta cece rayuwar yayanta. Hajiya nasan auran soyayya ya qaremun tunda narasa Al amin, kuma naqi auran Baffa ne saboda inaganin hakan kamar cin amana ga Al amin daga mutuwarsa ko wata 3 beyi a qasa ba Na auri yayansa uwa daya uba daya? Hajia duniya xata xageni kuma koba a fada ba wannan auran cin amanane. Hmm yaro dai yaro ne, fadima banda abunki ai babu abunda xakiyi mutane basu xagekiba, yayin da wani yake ganin kinyi dai dai wani tym din yake gani baki dai dai ba. Kuma inkubuta a wurin ubangijinki basai kin kubuta a wurin mutum ba. Allah bai haramta auranki da yayan mijinki ba yakama kijewa wannan auure kodan yayanki. Tunda takabarki ta cika a dalilin haihuwar da kikai babu rai. Na yarda hajia wlh na amince xanje inkula da yayana bazan bari su wulaqanta ba in ina numfashi xan xame musu uwa kuma uba. Yawwa autata kokefa π da wannan suka rufe chapter suka kwanta.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌAL ‘AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌ
Writing & story by rahman Mohammed (hajia)
Editing by mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS {F S W }
Page 5β£
NOTE : ina bawa makaranta haquri da kuskuren da nayi wajen sunan yar uwar fadima ADDA KHADIJA, asanin sunan da tasarin labarin yazo dashi shine ADDA HALIMA. Saboda haka daga yanxu xamuji sunan ya koma Haleema memakon khadija, nagode ayi haquri π.
Yau ta kama Monday Wanda yayi dai dai da kwanan fadima uku a gidan auranta, xuwa wannan lokaci bataga koda giftawar me gidan nata ba balle ya mata magana, matan gidanma babu wacce ta taba nuna tasanta balle ta bata abinci, bata damuba dan babu abunda ba a kawota dashiba na bangaren kayan abinci, da yan kudadenta da yan uwanta suka hada mata dan haka hankalinta kwance yake kamar tsumma a randa. Tayiwa yayanta shirin makaranta tsaf cikin uniform, 7:00 ta fita ta kulle dakinta da nufin kaisu makaranta, taxi ta tara da yake awancen tym din babu a daidaita sahu, ta kaisu har cikin afoshin shugabar makarantar ta basu haqurin rashin ganinsu ta aka dade ba aiba ta fada musu mahaifinsune ya rasu, tayi mata gaisuwa ta kuma tausayawa yaran dama yaran Sun Shiga ranta saboda tsaftarsu da yalwar gashinsu, da yake sai shida na yamma suke tashi makarantar hade take da islamiyya tace xata dawo ta daukeso, ta raka Mimi ajinsu nursery 1 sannan ta raka fati dake ajin qarshe na primary.
Da yamma ta koma ta dakkosu kamar yadda tayi alqawari, ko takan mijin nata batabi ba balle tambayarsa izinin fita, tunda ya kwada mata xaman kanta xatai a gidan itama ta quduri aniyar hakan. Taxi na saukesu a qofar gidan ta dakko kudi da niyyar bashi saiga motar Baffa da alama dawowarsa daga kasuwa kenan daga kasuwa, ya kalleta cike da mamaki sai kuma duk ya
diririce ya shige cikin gidan
,atsakar gidan duk mutanen gidan na tsaye batasan dalilin tsaiwarsuba itadai ta bude dakinta ta shige.
Da daddare bayan isha tana tsakiyar yaranta tana koya musu home work, Ahmad yayi sallama ya shigo, ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa itadai tana qaunar yarannan musamman data fuskanci matsalar matar uba da yake fuskanta, uwarsa ta mutu wajen haihuwar qaninsa, mahaifinsa alh Nasir me kudin gaskene kuma dan boko ya auri wata matar wacce ta mallakeshi tamaida Ahmad bawanta kuma ta rabashi da ubansa, ta katse tunaninta tare da cewa Ahmad idonka kenan? Sai yanxu? Ko makarantar sai yanxu aka tashi? Ya sunkuyar da kansa tare da cewa a’a mama yau hajiya ce tasani wankinta tun safe sai yanxu nagama ko makarantar ma banjeba (yana nufin matar babansa) ta kalleshi cikin damuwa tace bakaje makaranta ba Ahmad? Kayi kokari ka dunga xuwa makaranta inka dawo sai kai mata aikin, ko bakaso na baka auran Mimi? π inbaka xuwa makaranta bazan baka auran uwata ba, yayi dariya tare dayin qasa da kansa yace mama ni fati nakeso, Mimi qanwatace, tayi dariya tace toooo π, itama fatin inbakai karatu ba bazan bakaba, fati dake gefe tayi tsagal tace mama ni ko baiyi karatuba ina sansa a haka. Gaba daya suka saka dariya har Mimi da bata cika dariya ba sai murmushi. Mama tagabarta masa da abinci yaci, har xuwa taran dare sannan yai sallama yatafi, mama tace da safe inyayi shirin makaranta yaxo ya karya , tai shirin bacci suka kwanta tare da yaran a kan gadonta kasancewar tai musu tarbiyyar rashin fitsarin kwance tundaga yaye suke dena fitsari, tuni sukai bacci sai ita ta rage, taji sallama tare da shigowa cikin dakin, ssukai ido 4 dame me gidan nata, yayi saurin sunkuyar da kanta ga alamu nauyinta yakeji, “kixo dakina inasan ganinki yanxu ” yana gama fada ya juya ya fice. Taiwa yayanta adduar bacci ta lullubesu da blanket ta dora hijab kan kayan baccinta tanufi dakin mijin nata. Koda taje bayan kwane-kwane na borin kunyar rashin kulata da halin da taga yayanta a cikin gidan, sai maganar ta dunga hada yaran cikin motar gida ana kaisu makaranta bai amince mata qara fita bada ixininsa ba, da yake namiji dai sunansa namiji sai jin hannunsa tai a jikinsa alamu haqqinsa na aure yake nema, π tunda ya fara bata dago kanta ta kalkeshiba balle ta tayashi abunda yakeyi, har yakai ga kwantar da ita akan gadonsa alokacin tayi yinqurin hanashi abunda yake wanda shi kuma alokacin yakai matuqa wajen San cimma burinsa hakan yasa ya samata qarfi ya fiya buqatarsa. Tayi kuka a wannan dare kuma ta tabbatar da tarasa Al amin har abada, tun kafin asuba tabar dakin nasa takoma nata tai wanka ta kwanta. Tsahon daren intace ta runtsa tayi qarya.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌAL ‘AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌππΌππΌ
Writing & story by rahma Muhammad {hajia}
Editing by mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Page 6β£
BAYAN WANI DAN LOKACI.
Xuwa wannan lokacin tuni fadima wato (mama) ta zama yar gida agidan Baffa domin ta ware ta fuskaci qalubalen rayuwar dake tunkaro ta. Yayanta Kullum suna jikinta, babu abunda ke fitar dasu gidan sai xuwa makaranta, har Ahmad da yake qaunar yayanta shima ta jima da maidashi dan gida, tana qaunar yaron kamar ita ta haifeshi kuma tana tausaya masa kwarai da gaske, safe har xuwa dare yana da kwano a wajenta ma ana tana bashi abinci ta dauke hidimar karatunsa tsaf kamarsu bashi kudin makaranta dinka masa uniform da kuma tilasa masa xuwa makarantar. Da yake dan halak ne yaron, yana mutuqar girmamata da yi mata biyayya kamar ita ta kawoshi duniya. Duk da baqar maganar da takesha a cikin gidan nacewa ta samu dan daba nata ba tayi ruwa tayi tsaki a harkarsa . Bata taba kulasuba saboda dan Allah takeyi kuma aranta takance Da da dukiya ai ba ai musu mugunta, kuma da basai wanda ka haifa ne lallai yake jin qankaba .
Xaman gidan Baffa xamane na kowa kansa ya sani, saboda ko su matan ajunansu ba jituwa sukeba kullum fada suke kamar masu ganin hanjin juna gasu da ido akan yayansu, baki isa koda kauda buta kisa dan wataba sai dai kisa naki. Amma auro musu fadima da akai sai yasa suka hada kai saboda su yaqeta. A Kullum cikin goranta mata suke me yawon aure aure ta auri qani ya mutu ta auri yayansa, gashi abun takaicin Sun koyawa yayansu wannan dabi a tayi mata rashin kunya da yi mata habaici, yayansu maza ne dai babu ruwansu domin bazatace ga ranar da wani aciknsu yayi mata wani abu na batanci ba. Duk sanda xatai girki a gidan babu mai tayata da koda dauke cokali ne haka xatai girkin ta gama a wahale kasancewar bata saba girkin gidan yawa ba. Yayanta kuwa ganin idonta baisa anfasa dukansu ko xaginsu da aibatasuba, amma abun burgewar shine bata taba nunawa tasan anai musu hakan ba balle tayi magana, wannan ya qara baqanta ransu domin anayine domin tayi magana ko ranta ya baci, kawai dai abunda tasani shine bata yarda tabar yayanta da qazanta ba ko yunwa ko jahilci ta tsaye musu tsayin daka akan wadannan abubuwan. Agabanta xa a dakesu kuma asakasu aikin da ko ita data haifesu bata sasuba saboda aikin yafi qarfinsu amma saita kau da kai. A irin hakan wata rana Adda Halima yayar fadiman taxo ta tarar Anty jamila na dukan Mimi kamar xata kasheta wai kawai dan ta aiki mimin siyan omo kanti ita kuma mimin tace Mata mama tace babu kyau mata suje kanti sai dai maza, shine ta kamata tana duka Lamar ita takawota duniya babu wanda yayi yunqurin ceton mimin har uwarta dake can falonta tana dinki a kan keke tayi burus kamar ba yarta ake duka ba, sai Faty daketa kuka tana ihu tare da kiran azo atemaketa Anty xata kashe mata yar uwa. Ana cikin hakan Adda halima ta shigo gidan Kai xaye taje ta angaje jamila ta kwace Mimi tare da dauke Jamilan da Mari, sannan ta dora da cewa me wannan yar ficiciyar yarinyar tai miki kike mata irin wannan dukan? Shiru Anty jamila tai saboda Marin da akai mata ya shigeta, sai Faty ce ta mayarwa da Adda halima yadda akai . Tace yayi dai dai akan taqi xuwa aikenki kike mata wannan dukan? In gaskiya ne abun naki meyasa baki aiki naki yayanba? Ta juya ta kalli ragowar mutanen gidan da suka fito kallo sannan tace wlh tlh ku kiyayi taba yaran nan, marayun Allah kun hanasu sakat, me suka yimuku? Magana ta farko kuma ta qarshe wlh duk Randa wani acikin ku da yayanku ya qara sa hannu akan yayan fadima wlh kotuce xata rabamu. Tana kaiwa nan ta kama hannun Mimi da Faty tayi waje dasu ta xubasu a motar da aka kawota driver yaja suka tafi, kotakan fadima batabi ba saboda da ranta ya baci kuma tasan fadiman najin abunda akeyi tayi shiru.
Bangaren fadima kuwa sukuku tayini Baffa na dawowa da magriba taje ta sameshi da kukanta akan yakaita gidan Adda halima, ganin tana kuka yasa bai tambayi baasiba saboda ya dauka addan ce ba lfy yasata a mota suka tafi. Koda sukaje addan kin kulata tai ta hangi su Mimi da Faty a dining Sunayin dinner tare da yaran Adda da kuma dady mijinta tuni Sun sake cikin yara da yake yawanci akwai sa anninsu acikin yaran addan. Fadima taje ta riqe hannun adda tare da saka kuka, tace yi shiru fadima aini bakimun komai ba face amanar yaya da Allah ya baki kika kasa kula dasu kuma na kwashesu inke bakiso ni inaso, sai alokacin Baffa yaji abunda ke faruwa, wasa wasa dai adda ta hana fadima Yaya tun ana ganin wasa takeyi har dady da Baffa sukasa baki amma ta qeqashe qasa tahana, da yake ance da uwa sai Allah koda Mimi tagamacin abinci ta kyalla ido taga mamanta ai saitai gurinta da gudu ta kwanta jikinta, da haka Baffa yace tabar yaron ta taso su tafi ta miqe ta yafa gyalenta Mimi ta riqe hannun uwarta xata bita adda ta bita ta dauketa ta saka ihu, ta ajiyeta Tare da cewa maxa bita dan gidanku uwar taki da batasan ciwonki ba tana xaune xa a kasheki tai shiru, Faty take gefe taga suna shirun fita tace da Adda mummy nima xanbi mama, ta riqe baki tace au kema? π€ to ai kun kunyatani xo kibita in ankasheku ta huta. Da haka ta bawa fadima yayanta tare da ja mata kunne sosai.
To tundaga wannan lokaci akasamu sauqin abun domin suna shayin Adda halima sosai domin itadin bata barin ta kwana kuma tsaf Sun san xata aikata abinda ta fadadun koma fiye da haka. Tundaganan babu wanda ya qara yunqurin dukan yayan fadima sai dai kyara da hantara da xagi. Ni kuwa nace zagi ai zagawa yake kuyi tayi π.