Page 1 to 10.
Bismillahi Rahmani Raheem!
Masoyana Ina baku hakuri akan rashin zuwan littafin MUGU BAI DA KAMA. Wannan ya farune saboda bayanai da nake tattarawa akai. Kapin zuwanshi ina maku sallama da wannan takaitaccen littafin nawa mai suna Akan social media (yanar gizo)
K’arar sakon daya shigo a wayantane yasata yin firgigit ta miqe dga zaune da take ta d’auki wayanta, sunan da tai saving dashi na “My one” ya fitah akai. Wani d’an karamin tsaki taja saboda wasu guntayen hawayen da suka zuba mata a fuska. Kanta ta kifah akan guiwowinta ta fara shiesiehkar kuka.
Dea2 wannan lokacin wata yar matashiyar mata ta shigo gidan, baqa mai matsakaicin tsaye, mai kyau da itah.
“Keko fadila mai yasa ki cikin wannan yanayin? Tun d’azun naketa rafka sallama gaki zaune kin kasa amsawa”?
Hawayenta ta share ta d’aga idanunta ta dubietah, cikin muryar kuka mai d’auke da nadama ta furta
“Farry ina cikin hatsarin ruwa, na shiga ukki na lalace”
Zaunawa farry tai ta dubeta cike da d’umbin damuwa
“Ke kuwa fadila mai yasa? Dan Allah ki deana fad’ar haka, kisani fa cewan komai na Allah ne, kuma duk abunda ya sameki Allah ya kamata ki miqawa ai”
Hawayenta ta k’ara shareware, ta dubie farry
“Farry na cuci kaina, naci amanar mijina da iyayena da kuma rayuwata gabad’aya”
Hannunta farry ta kama
“Look! Fadila idan bazaki fad’amin damuwarki ba billahil azim tafiyana zanyi”
Idanunta ta saukar kasa tare da tashi tsaye ta juya bayanta
“Farry, tun kapin inyi aure ina chatting da wani mai suna Adnan”
Farry ta tari numfashinta
“Adnan dai wanda nasani”
“Eh shi farry, tun muna chatting a 2go, facebook, muka dawo whtsapp, hr muka fara imo dga nan sai video call farry”
Dakatawa fadila tai tacigaba da cewa
“Adnan ya kasance abokin firata a online idan banga adnan ba bana iya yin komai, ya kasance ya fara jan ra’ayina muna video call, haka adnan zaisani in cire kayana tas shima ya cire nashi muna video call, babu abunda muke fad’a inba maganganun batsa ba”
Kuka yaci karfinta ta dakata ta cigaba da cewa
“Farry, tun banyi aure ba gashi ynxn nayi aure har na shekara d’ayah, amma na kasa deanawa. Duk ranar da banyi video call da adnan ba, farry ji nake kamar zan mutu. D’aki nake shigiewa inyita kuka har garin Allah ya waye, gani da miji amma bana bari muna kwana a daki d’ayah, wayata ko ina security code ne da itah”
Komawa tai ta zanah ta maida kallonta ga farry data saki baki take kallonta
“Farry bazan iyaba, dan Allah ki taimakeni inaso in deana, dan Allah”
Hannunta farry ta rike da itama d’in kukan takeyi
“Fadila! Dan Allah kicemin mafarki nakeyi ne ba gaske neba”
“Wallahi farida iyakar gskyr kenan, ki taimakeni dan Allah”…