đ« SANYI DA ZAFIđ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 4ïžâŁ
She just wished all this ayyukan wahalan da suffering da yarinyarta yar karama keyi just to take care of her itane keyi mutane bazasu gane rahama ne Allah yamaka lafiya sannan yabaka karfin nema ba gashi tana neman wannan karfin ita tafita tayo aiki ta kula da diyarta daya tak a duniya tarasa, Rasheeda ce zuwa ayyukan shara da wanke bayuka, da wanke wanke just to get paid suci abinci ga school duk ita kadai dan yanzu ma suna hutun school, yarinyarta batasan menene dadin rayuwa ba tunda ta taso sai wahala, Rashida doesnât deserve to be born like this, ta zaman ma yarta bakin tabo arayuwanta waye zai taba auren Rashida yanzu? Ko anzo ma gulman yan anguwan nan koransu suke, babu kalan sherin da baâa musu, kowace budurwa irin Rashida nada kawaye ita batadashi kota fara kawance iyayen yaran zasu raba abotan sabida ansan diyar mai HIv ce, yar fasika ne gantalalliya dan haka babu iyayen dakeson yaransu suyi muâamala da yarta, hawaye masu dumi ne suka gangaro daga idanunta dasauri takai hannunta ta share fuskan tass tareda sauke ijiyan zuciya ahankali tace âAllah na yarda ka kasheni da ciwon nan, Kama karomin cuta daban daban duk na yarda, amman Ya Allah kabama diyata farin ciki arayuwanta, Ya Allah ka kawomata karshen wahalan nan, Ya Allah idan mutuwata zai zamto abinda zaisa Rashidana tadena aikin wahalhalun nan just to take care of me Ya Allah ka dauki raina dudda banson na barta, Ya Allah spare my daughter this harsh way of living and take me insteadâ tasake share hawayen dasuka zubomata sai kawai tadaura kasan rigan atampanta kan fuskanta tai shiru takai 2min ahaka sannan ta mike taje inda take tallabota tayi tace âRaudah oya muje ki kwantaâ ina batamasan anayiba baccin yayi nisa gajiya kuma kesata baccin kaman tamutun nan, kamata Mama tasakeyi tace âtashi muje kinji Rish-rish din Mamaâ Mama tai maganan tana dagata da kyar ina bamata iya tafiya kaman matatta, kakkamata Mama tayi tasata ajikinta tana tafiya da ita ahankali tanajan kafa kaman irin wacce tasha giya tai tatil din nan, uwar dakin babu komi banda wata yar katifa datake a gyare akasa sai kuma manyan ganamasgo guda biyu na kaya sai dan rio na kayan kwalliya da wasu kodaddun hodon makeup da gorunan turaren humra suke ciki saikuma wata benci haka da littafai ne cike na school akai saikuma lab coat da aka makala a nail na bango jikin aljihun an rubuta Dr Rash ajiki Mama ta kwantar da ita ahankali.
Karfe 4:30 daidai tabude idanunta adduan tashi daga bacci tayi sannan takalli Mama wacce taganta kan dadduma idan da sabo ta saba agurguje ta tashi waje taje tahura wuta tadaura ruwan wanka sannan tashare tsakar gidan taje ta wanko bayi ta watsa ruwan sanyi ita tafito tai alwala tazo ruwan yayi zafi tahadama Mama a bucket tadawo daki dan kaita bayin dan kafafunta na balaâin damunta tace âMama muje kiyi wankaâ tana rike da Mama har bayi Mama tace âkarki jirani jeki sallaâ batai musu ba salla taje tayi sannan tafito ta daura tuwo a wuta ta kwashe kayan da Mama tasa sharp sharp ta wanke ta shanya tasake wucewa hanyar bayi tadawo da Mama dakin dahar ta gyara tafita waje takarasa tuwo tai miya tazuba komi a kula takawo daki sannan ta shirya cikin wani dogon rigan abaya baki wanda stones din duk sun ciccire tadau gyalen zata yana kenan ta tuna jiya saitahau dariya Mama dake shafa mai tace âke lafiyanki kike dariya ke kadai?â Dasauri tajuyo ta taho wajen Mama tace âMama wani dan gayun mutumi nasa a bola na zuzzubamai shara bakiga yanda yake makyarkyata ba kaman da zinare aka yishi ba kasa baâ yanda take murmushi tana dariya yasa Mama tace âwa kikasa a bola Doctor?â Dan tsagaita murmushin tayi tabama Mama labari kunnenta Mama taja tace âRauda wai mesa bakiji ne inda sun kasheki ke fa dakike musu rashin kunya ina kikeso nasa raina why mesa you are always putting yourself in trouble ne eh? Mesa bakiji wai kin dauka wani karfi gareki wai sabida wani baitaba chasaki ba koâ kaman zatai kuka tace âMama yakuri to kisaki kunnenaâ sakejan kunnenta Mama tayi dudda bada karfi sosai ba tace âsaina cireshi duka, wai mesa bakiji eh? Why wat if wani abu yasameki?â Ganin yanda takeyi da fuska kaman zatai kuka alamun jan kunnen namata zafi yasa Mama tasaki kunnen ahankali saikuma takama kafadanta cikeda damuwa sosai tace âDoctor kinason duk idan kin fita yanzu hankalina yadena kwanciya ne?â Dasauri ta girgizakai, ahankali Mama tace âto yimin alkawari u will not put kanki in any trouble againâ murmushi tayi tace âI promise Mama bazan karabaâ ijiyan zuciya kawai Mama tasauke dan tasan is impossible cus Rashida and trouble are besties, tashi tayi tawuce takarasa shiryawa ta yana gyalen akanshi ta kwashi uniforms nata tasa ajakan ta sannan tazauna tahada zanen tasaka musu frames Mama sai kallonta take kawai saida tagama tass sanan tazo kusada Mama lokacin 7 daidai tace âMama maganin safeâ tadauko magani bama Mama maganin tayi sannan tacire yar wayanta daga chaji tadauki earpiece dinta tace âMama bari injeâ cikin kudin data kawo jiya Mama tazare 1k tace âga wannan kihau abin hawa kidena tafiya da kafa hotel din nan da nisaâ dasauri ta girgiza kai tace âMama ki ijiye duk nazuwa asibiti ne next week ni dakafata zan taka ai ba nisa ko ciwon kai kikaji ki kirani zanbar kome nakeyi na dawo zanyi aiki a hotel har karfe daya biyu yau ba airport zandaiga alert, sai karfe 4 ina wajen Maman miwa bye Mama naâ dasauri Mama tace âto baxaki daure ko Lipton kisha ba tunda baki iyacin abinci dasafeâ dukowa tayi ta rungume Mama tace âMama zanyi latti ne nakai zansha a hotel din ai ana bamu coffee da biscuit bye Mama kinjiâ ta shafa fuskan Mama tana kallonta saikuma ta manna ma Mama kiss a goshi tace âMama kinyi kyau wlh atampan nan zaki bani itaâ dan maketa kadan Mama tayi tace âba Dr yace kidena min irin abubuwan nan ba saina shafamiki ciwoâ haderai Rashida tayi sosai tai sauri zata tashi hakan yasa Mama tarike mata hannu tace âzo to fushi kikayi banso kibar gida da fushi yakuri bazan kara miki maganan baâ hawaye idanunta suka tara saikuma tahadiye hawayen saikawai ta rungume Mama tsamtsam kaman yar yarinya tace âMama ko duka ciwon duniya kikedashi ni zan fiso su dawo kaina ke naganki lafiyanki kalau, Mama kome kika dawo ko menene ajikinki you will always be Mama na nikadai, koda zan samu I donât mind ni ko mutuwa yazo nafiso mu mutu tare maâ dasauri Mama ta daki bakinta tace âbazaki mutu yanzu ba sainaga yaranki jikokinaâ turobaki tayi tasaki Mama tace âMama ni banson maganan nan I hate maza to the core bazan taba aure ba, dana auri miji irin wanda kika aura danni ba Babana bane gwara na mutu ahaka banyi aure ba, matsiyacâŠâŠ.â âDoctor!â Mama takirata azafaffe hakan yasa tai shiru tadauke fuska, ahankali Mama tace âkarki kuskura ki zagi Babankiâ kallon Mama tayi irin why are you still protecting him sai kawai tayi hanyar fita daga uwar dakan cikin sanyin murya Mama tace âheâs your fatherâ jakanta tadauka ta goya tace âMama heâs not my father ko sunanshi dakikasa nake amfani da dan babu yanda zanyi ba, Mama na tsani mutumin nan and I hate all men naduniya, nidai mudaina maganan banmasan maisa kikemin maganan maza ba to mezasumin? Akwai wani hanyar neman kudi daban iyaba? Mama namafi mazan karfi laaaa nama manta ban daga karfe ba yauâ tajuya dasauri zata fita daga dakin Mama tace âkika daga karfen nan saina mammakeki wlh waike namiji ne yau naga balaâi a hannun yarinyar nanâ dariya Rashida tayi ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Mama tace âMama bakiga saisa babu me kawomin raini ba sabida ansan inada karfi Mama dan Allah kibari nadaga kinji Mama 2minsâ da hannu Mama ta nunata tace âwlh zanci kaniyanki, sokike ki mummurde ki koma namiji? Wannan harkan karfen wlh bazan yarda dashi ba jira nake rannan lahadi idan Lawali yazo ince yatafi dashiâ dasauri Rauda tace âwlh Mama karki bayarmin da abuna da kyar nasamu mutanen garejin nan suka saidamin da abin nan dubu ukuâ baki Mama tabude tace âyanzu bakisa dubu uku kin sayi sutura ba sai karfe kikaje kika saya agareji tafi aiki ki dawo zaki gamu dani wlh agidan nanâ dariya tayi sosai saikuma ta buga kafa tace âto kice bazaki bayarba wlh Mama kowa kikaba sai naje na karbo abuna kota katanga ne saina hauraâ haba Mama tarike tace âto wani daban zan bamawa ba Lawal ba sai inga idan tsafi zakiyi ki gane wana bamawa, wuce kitafiâ tace âbye Mama na, Mamana kyakkyawa mai gashi, Mama haryau gashina yaki kamo naki narasa maisaâ kaman jira Mama take tace âsabida kin soma daga karfe ne saisaâ dariya Rashida tayi harda kama ciki tace âlaaaa Mama wlh wannan zuki tamallo neâ baki Mama tasaki tace âni Mamanki ke karya Doctorâ? Dan sosa kai tayi kaman mara gaskiya tace âuhnnnâ kwapa Mama tayi tace âwuce kitafi zan gamu dake kika dawo ai anan zakizo ki sameniâ nokekai tayi tana danne dariya tawuce tafita Mama itama tai murmushi ta daga murya daganan daki tace âayi adduâa dai kafin afita daga gida Allah bada saâaâ tsayawa tayi tai adduâa sannan tabude kofa tafita abinta tana rike da frames na artwork datayi guda uku ga jaka abayanta sheâs just a young lady da kana ganinta kaga strong, bright hardworking young lady, Nisan daga gidansu zuwa hotel din kusan tafiyan awa daya cur tabar gida bakwai takai hotel din by 8, Babban hadadden hotel ne shima gyare gyaran daki take da da bayika su wata wata suke biyanta 30k office na wajen da uniform nasu taje ta chanza kayanta taciro uniform din tana sawa Riga da wando ne tana kokarin saka karamin farin hijabinta wata tashigo dakin hakan yasa dasauri tajuyo hada ido sukayi da yarinyar tana ganin gashinta tace âInnalillahi Rashida kinasa attachment neâ? Dan zaro manyan idanunta Rashida tayi dan bama tasan gashinta ya warware ba hannunta yarinyar tadaura kan gashinta bakin kirin gashi da sulbi ga tsayi sosai tace âwlh gashin kine Woww Rashida hala ku ba yan Nigeria baneâ fizge gashinta Rashida tayi kaman fada tashiga parking tace âkada ki kara tabaniâ baki yarinyan tasaki tace âohhh nidai bantaba ganin masifaffiya irinki ba daga na yabi gashinki Rashida sai fadaâ saka hijabinta tayi tace âaiki kikazo yi ko yabon gashiâ? Tana maganan ta kwashi frames din tabar wajen yarinyar tabita da kallo har cikin ranta tanason tai kawance da Rashida but Rashida irin mutanen nan ne mafadata and too protective is as if batason mutane su shigo space nata because she donât wanna get hurt oho, u canât complement her, u canât say anything to her fada but batada neman tsokana, bata shiga mutane ba ruwanta da kowa itadai tazo tayi aikin datazo yi lokacin tafiya nayi ta tafi ko minti daya bata karawa.
Sosai manager ke kallon zanen saikuma ta kalli Rashida tace âanya kene kikai zanen nan kodai satowa kikayiâ? Zaro manyan idanunta tayi tace âtunda nake bantaba sata arayuwana ba idan baki yarda ninayi ba bani paper da pen da color namiki exactly irinshi agabankiâ murmushi manager tayi takalli abin saikuma tace âzan saya akan 10k each sannan ki dingayi kina kawomin ko guda nawa ne zan sayaâ bakaramin dadi Rashida tajiba dudda zanen zane ne da har 100k zaa iya saya awani waje but bata damuba 10k is huge 30k ta kirgo tabata sosai Rashida taji dadi bata taba sanin zata iya saida zanenta ba kaman fa wasa taji ana maganan sayan frames tace ta iya manager tace takawo tagani jibi anbata 30k akan guda uku anatse tace ânagode Ma Allah kara arzikiâ dan tabe baki matan tayi tace âtafi kifara aikin kiâ wucewa tayi tafita manager ta kalli frame din tace âzan gayawa Oga 150k each nasaya wayyooo this girl is talented bata sani ba inhar Oga yasosu zance muyi ma all rooms na hotel namu nabama yarinyar tamin I will be fucking billionaire nabata 10k each ni na karbi 150k for each awajen Oga wow look at her workâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 5ïžâŁ
Ahankali yake bude idanunshi kadan kadan sama sama yaji ance âSonâ dudda idanunshi akulle but ahankali bakinshi ya furta. âMommâ shafa mai kai matan tayi ta duko ta manna mai kiss agoshi cikeda tsantsan so tace âgani nan yarona open yourself Riyad no one is gonna hurt you againâ gently yake bude idanunshi kafin ahankali ya saukesu akanta gently ya yunkuro ya shige jikinta kaman dan karamin yaro yace âMommmâ bayanshi ta shafa tana murmushi tace âmeya sameka what happen? Who did this to youâ? Murya chan kasa yace âwasu mutane wanted to kill meâŠ.â Kankameshi tayi sosai tace âbabu wanda ya isa ya cutarmin dakai ko yadauki rayuwanka as long as ina raye, u are safe already ana investigating abun sai inda karfina yakareâ takara kankameshi kaman dan karamin yaro tace âI love you Riyad kaine kadai sanyi idanuwa naâlumshe idanu yayi saikuma ya yunkuro yatashi daga jikinta yakalleta da muryanshi da bata fita sosai yace âBabaâ? Kallonshi tayi saikuma ta sauke dan ijiyan zuciya tace âtashi kaje kai wanka ka shirya kafito ka gaggaisa da mutane idan zaka iya, sannan kaje kama Babanka adduâa a makwancin saâ dan runtse idanu yayi abin yamai ciwo yaso Ya sallaci mahaifinshi, fuskanshi Mom ta taba hakan yasa yabude idanunshi dasukai ja yakalleta murmushi kadan tamai tace ânasan yanda kakeson mahaifinka but heâs in a better place yanzu trust me, all abinda yake bukata awajenka is adduâa, jekai wanka zaâa kawo maka kayayyakin dazakasaâ gyadamata kai yayi agajiye yace âMom please ke kikawomin banson hayaniyan kowaâ tsayawa tayi ta kalleshi ahankali tace âtom zan kawo maka da kainaâ dagoshi tayi yatashi tsaye ahankali yawuce bayin dake nan bedroom din, girman bayin yayi girman wani gida, wanka yayi yayi brush yadaura towel yafito yana kallon saman gadon inda tundaga kan takalmi har zuwa kan agogo an jeramai akan gadon tsaf dazai saka wasu kayan sarauta ne masu kyau sunsha aiki, anatse yake komi ya shirya cikin kayan da aka musu aikin royalty ya feffesa turare yadan juya yakallo kanshi amadubi yayi wani irin kyau na ban mamaki hulan dayasa yasake maidashi wani cikakken mutum bude kofa yayi yafito daga bedroom din wasu bayi ne maâaikata a falon suna ganinshi suka duka dukansu. âTakawanka lafiya Yarima Riyad, taho a sannu dan kwalisa abin begen Sarauniya Maryama, barka da fitowa, Allah yakara maka lafiya, makiyinka fadawanka, duk wanda yaja dakai ya shirya yasha kasaâŠ.â Wucewa yayi fuuuu yafita danshi bayason wayan nan surutun nasu, da Munir yaci karo yana kokarin shigowa flat dinsu hakan yasa ya tsaya yahade rai kaman suna fada Munir yace âkatashi, are you feeling better can you walkâ? Gyadama Munir kai yayi yay gaba kawai, Munir yabishi abaya direct inda aka binne sarki yayi yana zuwa ya shiga wajen batare da an hanashi ba yayi shiruuuuu idanunshi sukai ja, almost everyday indai Mai Martaba baida wani uzuri saiya kirashi da daddare yaji yayake ina kuma yake, kullum cikin fada yakemai daya daina yawon kasashe yakan yawan cemai yanda yake gudunma gidan nan da alamu shine wanda gidan nan zai rike kuma gam, ana cewa sarakuna basu da lokacin yaransu shidai mahaifinshi nada lokacinshi, Baba ya fara koyamai business how to make 1naira yakoma billions, Baba guides him through everything, duk business dazai fara saiya kira Baba, sai Baba ya amince zai farayi, kuma bai taba takura mishi ba, hawaye yaji sun taru a idanunshi da sauri ya runtse idanun yana fuzar da iska dan baiso suma zubo but heâs deeply hurting, da ace yasan Baba zai rasu dabaiyi tafiyan nan ba, sosai yama mahaifinshi adduâa sannan yafito Munir yagani awajen da Kabeer dasu Shaibu yan uwanshi dukansu yajiki sukamai ya amsa sai kallonshi suke Kabeer yace âkasha magani kuwa you still look sick? Ko zaka koma ka kwanta neâ? Gyadamai kai yayi ahankali yace ânasha, Iâm fine thank youâ dannewa Kabeer yayi ganin yanda yakemai magana kaman alfarma yakemai dayake amsashi yadai daure yace âto mutafi fadaâ atare dukansu suka wuce fada, sauran yayyinsa da yan uwansa natamai hira da uhm aâa kawai yake amsasu cus gashinan ne kawai, gaida mutane sukayi sai yima Riyad gaisuwa ake ana kiran sunanshi shi baimasan ya akayi akasanshi hakaba dan baicika zama ba, su Waziri dai duk suna kallon komi, kowa yazo saiyamai gaisuwa amai yajiki, yanda ma ake kallonshi sai abin yasa yaji sabon zazzabi na nema ya lullubeshi.
Mom nazaune afalonta tana jan charbi ita dawasu kawayenta wanda suke mata Sarkin daga wasu garin dasuka kawo mata gaisuwa aka shigo flat din Matan Waziri ne da babban diyarta Haleema da ake kira da Lims, tana sanye da doguwan riga abaya black ta yana gyalen akanta, tanada tsayi da dan jiki kadan duka duka bazata wuce 24, 25 ba, tana shiga dasauri tawuce wajen Mom kafinma Mamanta tai gaisuwa tace âMom ina kwanaâ takalli sauran matan wajen cikeda girmamawa tace âina Kwanan kuâ amsawa sukayi Mom tamata murmushi tace âHalima ba kina school ba yaushe kika dawoâ? Mahaifiyarta tace ânima ganinta nayi agida da safen nan ta iso daga London wlh na aika driver yaje yakawota tunda taji rasuwan Mai Martaba hankalinta yakasa kwanciyaâ sosai Mom ke kallonta akunyace Haleema ta sunnar dakai Mom tace âschool fa idan kikai missing exam ko test faâ Maman ta tace âproject ma fa takeyi this month zasu gama komi da komiâ babu wasa kan muryan Mom tace âkibi first available flight ki koma school gobe kinajinaâ gyadama Mom kai tayi ahankali tace âto Momâ Mom bata sake cewa komiba tacigaba da magana da manya, ahankali Haleema kebin dakin da kallo gabanta na faduwa adduâa take Allah yasa suhadu ta ganshi, Allah yakawoshi side din nan dudda tasan ba lallai yadawo ba barinma yaji da baki adakin amman tasan inhar yana gari yafi zama wajen Mom da bangarensu na samari.
Kallonta Mamanta tayi tace âtashi kije wajen su Batul manaâ juyowa Mom tayi takalleta tace âtashi kije wajen yan uwankiâ batai musu ba tashi tayi tawuce tafita Matan Madaki tabita da kallo tace âyarinyar akwai natsuwa ga kunya ga kawaici ta dace da Riyad sosai yanda shima baida maganan nanâ wani kalan dadi Matan Waziri taji Mom tai dan murmushi batace komiba.
Ahankali take tafiya ita kadai tana danna wayanta kamshin turaren dataji yasa ta dago kanta dasauri Riyad tahango yafito daga fada yana shigowa nan compound din Mom wlh kusan duka yaran sarki tasansu da yaran yan uwa dan afadan nan aka haifeta anan ta girma bata taba ganin yaro mai kyau da farin jini da aji irin Riyad ba kap gidan nan babu wanda yakaishi kyau, ga tsayi ga gayu ga jidakai ga miskilanci ga kudi kudinshi na kanshi bawai kudin Baban su ba dan babu wanda yakaishi kudi a yaran sarki, gashi Mai Martaba na sonshi, ga kakanshi na bangaren Mom Attorney General yafi kowa tsatso mai kyau da gata ayaran sarki.
Faduwa gabanta yayi sosai amman tadaure ta tsaya awajen jikinta har bari bari yake, tahowa yayi wajen batare daya kalle inda takeba zai wuce dasauri tace âYarima Riyad!â Tsayawa Riyad yayi chak batare daya juyoba dasaurinta Halima taje ta gabanshi ta tsaya adan kunyace tace âina yini ya hakuri?â Dan kallonta yayi trying to remember waye ita, shifa wasu kannin nashima ba saninsu yagamayi ba dan baya shiga lamarin gidan nan baison komi game da sarautan, dauke kanshi yayi ganin yanda take murmushi tana kallonshi, kaman ance dole yayi magana yace âwho are youâ? Wow the way he talks is super adorable, da kyar ta iya controlling zuciyanta dake neman fitowa ta danne kome takeji tace âHaleemaâ dan kallonta yayi irin kallon okay but still baigane ta ba and he doesnât care din nan yajuya zai wuce dasauri tace âYa Riyad sabida kai nazo gobe zan koma schoolâ dan tsayawa yayi wannan karan yajuyo kalleta da kyau shifa har yanzu bai santaba and sabida shi tazo? Akan wani dalili? Are they related in anyway? Infact baida karfin bude baki ma yayi all this questions hakan yasa yadan tabe baki yace âthanksâ kawai yawuce ya shiga flat din MomâŠâŠ
Jin akwai baki abangaren Mom yasa yajuya yagazaya ta baya yashigo gidan yaje ya kwanta.
**
Yana zaune adakinshi dashi da Munir har yanzu bai gamajin sauki ba yana sanye dawani 3quater da singlet wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Mom yasa yadauki wayan kai tsaye tace âkazo dakina ina son ganinkaâ ahankali yace âokay Momâ tashi yayi ahankali Munir dake taba wayanshi yace âina zaka?â Slippers yashiga sawa yace âMoommâ yadauki wani farin t-shirt yasaka kawai yawuce Munir daya gane abinda yake nufi wato Mom nakiranshi hakan yasa yacigaba da abinda yakeyi ahankali yabude dakin Mom tana zaune kan couch din dake dakinta ganinshi yasa tanunamai gefenta tace âtaho nanâ shigowa yayi ya maida kofan dakin yarufe yataho wajen kujeran zama yayi saikuma ya kwanto yayi filo da cinyanta heâs really feeling mutuwan mahaifinshi so duk walwalanshi bayanan, hannunta Mom tadaura saman kanshi ta shafa tai shiru kafin tasauke ijiyan zuciya tace âkasha magani kuwa? Dr zai zo anjimaâ ahankali yace ânashaâ dan ijiyan zuciya tasauke tace âda banson namaka maganan nan yanzu cus nasan kanajin mutuwan Babanka, I know how much you love mahaifinku Riyad but I have to dan kowace matan sarki maganan da datake ma danta maza kenan, nima dole nama nawaâ dan dago idanunshi yayi ya kalli Maman nashi baice komiba, ahankali tace âinaso kai aure Riyad!â dawani irin sauri Riyad yatashi zaune daga jikin ya kalleta yama kasa magana cus maganan yazo mishi ne bagatatan, Mom dake kallonshi itama looking damn serious tace âand bakowace kalan yarinya nakeso ka auromin ba Riyad, inaso ka auri yarinyar da zuciyana ta aminta da ita yarinyar da nice na zabeta, all yammatan zamanin nan yanzu burinsu is suyi aure su raba yaro da mahaifiyarshi I will never allow you marry such girls, I have a girl a mind dina gaskiyaâ haderai yayi kana ganin fuskanshi kasan bama yason maganan dasauri yace âMom aure!â? Wani mugun kallo tamai tace âkaga Riyad banson shirme donât even start all abinda kakeso kace, I supported you duk yawace yawacen dakake kana touring round the world bantaba hanaka ba dan nasan itâs your hubby, bantaba takuraka ba dudda normally normally ba tun yau yakamata kai auren ba, but yanzu lokaci yayi itâs an order you have to settle down, aure zakayi and i have a girl danakeso ka aura diyar Waziri Haleematu, ita nakeso ka aura!â Wani kalan tashi yayi dasauri yamike tsaye yana kallon Mamanshi da babu wasa akan fuskanta itama tabishi da kallo tazubamai idanu rass aka tace âkaine the most successful child acikin yaran sarki, youâve archived alot Riyad at a very young age, ga ilimi kwali daban daban gareka, ga businesses da companies daka bude, ga natsuwa ga kamala ga kwarjini, naji kishen kishen dama mai Babban daki kaine zabinta sabida yanda mahaifinku ke sonka, Waziri shima nasan kodan yanda diyarshi ke sonka kuma yana mata kwadayinka kaizai dangwalamawa, to yaji maganan kuma kanason auren diyarshi komi yazo cikin sauki idan yana bangaren mu zai mana aikin yima sauran manyan fada maganan a zabeka, instead of su Kabir yan uwanka ko kannen babbanku dake neman kujeran sarautan, gwara kai dana kaikafi kowa chanchanta and bazan hutaba saina maidakai sarki, ai tsoron kada ka zama sarki yasa daga shigowanka garin suna neman halakamin kai amman Allah bai basu iko ba, kuma naji dadin abinda yafaru hakan yanunama jamaâa cewa an tsaneka ana tsoron kada ka zama sarki saisa har anfara yunkurin kasheka, saisa saida na tabbatar kowa yasan abinda yasamekaâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 6ïžâŁ
Wallahi kanshi ma sarawa yafarayi jin maganganun da Mom kemai, first of all duk wani abun na sarautan su bayaso saisama baya iya zama agarin, baison hayaniya baison how they do things cus is always fighting, makirci and politics, and baijin tunda ya girma yatabayin cikakken 2months like good 60days agidan ba bini bini yabar country, lokutan salla ne yasan dole yake dawowa sabida yanda Baba ya maida abin mandatory yanason duka yaranshi to be home sabida hawan salla and other activities na alâadu, shi mutum ne da baisan mulki he prefer business nashi, he derive joy a business, it gives him purpose, for aure kuma dudda yasan culture nasu ne amaka aure abaka mata but shi kwata kawata baitaba sanin Mom zatamai hakaba cus Mom is highly educated and expose, itama bata cika biyema culture ba saisa ma take barinshi to live his dream life, ko kadan bai shirya aure ba cus bayason commitment for now, his plan is nan da 2yrs zaiyi aure yanzu kawai aure baya lissafinsa, dukawa yayi ahankali gaban Mom yadafa kafanta kaman zaiyi kuka yace âMommmmmâ ahankali itama Mom tana kallonshi tace âRiyaddddd! You donât have to say abinda zaka fadi kasan nasanka sama da kowa aduniya ko?â Gyadamata Kai yayi Mom tace âI know how you despise sarauta, mulki infact bakamasan komi akaiba, I know for auren zakace baka shirya ba bakasan damuwan mace da sauransuâ sai kawai takai hannuwanta tai cupping face nashi cikin tattausan lafazi tace âdama akwai abinda zan taba so aduniyan nan dabaza ka iyamin ba Riyadâ? Ahankali Mom tace âI thought nine number 1 dinka like you always sayâ? Dasauri cikin raunin murya Riyad yace âMom u are my number 1 kema kin saniâ kai tsaye Mom tace âinhar nine number one din naka then karka karamin gardama kan maganan nan itâs an order allow me to do everything am I clear?â Yadade yana kallonta yanda take kallonshi babu wasa kan idanunta yasa ya sauke kanshi kasa alamun dai baiso but baice komiba, baya iyama Mahaifiyarshi gardama, cikin fushi Mom tace âkamin shiru? Ban isa dakai bane ko ban isa nace maka haka nakeso kayi kayibaâ? Tai maganan tana shaking leg in anger, abu yahadiye awuyanshi har saida taga motsin adam apple nashi asanyaye yace âokayâ tsayarda shaking leg din tayi tai murmushi sai kawai ta matso ta mannamai peck agoshi tace âI wish kowacce uwa zata sami dâa mai mata biyayya kaman Riyad dina data zama very very lucky, Allah maka albarka kaji, Haleema is a good girl tana matukar sonka tun tana yar yarinya, she will keep my son happy Iâm sure of that, so karka damu, zancen sarauta kuma I will teach you everything and you will do well kajiâ? Gyadamata kai yayi zuciyanshi duk ba dadi duka duka kwanan Babanshi nawa da rasuwa but kowa is after kujeranshi, look at matayensu kaman ba mazajensu ne suka rasu ba dukansu kokarin daura yaransu kan Sarautar suke sunma manta da rasuwan shima yanzu yazama sarkin one day haka matarshi zatayi kenan itama yana mutuwa all focus dinta will be yanda danta zai gajeshi bamatada lokacin yimai adduâa tashi kawai yayi yajuya yayi kofa.
Mom tabishi da kallo ranta fess, dolema Riyad dinta yadinga intimidating kowa, yafi duka yaran sarki kyau ga kwarjini ga haiba ga natsuwa, ga jan aji, ga kudi, ga rashin magana, ga rashin shiga mutane, gashi baida kallon mata shi kadai keda qualities na sarki and bazata hutaba saita maidashi sarki wannan alkawari ne!.
Dakinshi yashiga Munir dake danna laptop yabishi da kallo ganin yanda mood dinshi ya chanza tashi daya, Wucewa yayi yafada gado yakife cikinshi tareda lumshe idanu Munir baicemai komiba yacigaba da abinda yakeyi abinshi.
Yana fita Mom ta daga wayanta takira matan Waziri da ake kira da Mariya ringing daya ta daga wayan tace âranki shi dade Uwardakina, Allah yaja zamaninki Umman Riyadâ dan murmushi Mom tayi kafin cikeda isa da jiji dakai tace âdole gobe Haleematu zata koma makaranta neâ? Dasauri Mariya tace âai Uwardakina ko makarantan kikace karta kara zuwa saita zaunaâ jinjina kai Mom tayi tace âtom inaga bazata tafi goben ba dan zan turo Riyad yazo ya ganta inaso nahada su aure inyaso bayan yaganta zata iya tafiyaâ wani ihu Mariya tayi cikin waya saikuma ta zube kaman tana gabanta tace ânagode nagode Uwardakina da wannan karamci naki, kidubi kowa na gidan nan amman kuka zabinma Yarima Riyad Haleematu nagode, namiki alkawari bazaki taba samin matsala damu ba, I will forever be loyal to you, Haleema zata bautamiki Uwardakina, kuma da yardan Allah kujeran sarautan nan ta Yarima Riyad ce ai naji jita jita, da yardan Allah shine magajin sarkiâ dan murmushi Mom tayi tace âWaziri ya shigo yakiraniâ tana maganan ta katse waya wani ihu Mariya tayi tamike da gudunta tafice zuwa dakin Haleematu kai tsaye tabude kofan yarinyar na zaune sanye da rigan bacci tana kokarin hada kaya Maman kawai ta dagata tana juyawa tana rawa abinma saiyasa Haleematun dariya tace âMommy menene kike murna hakaâ? Cikeda jin dadi tace âyanzun nan Sarauniya Maryama takirani tace tanason hada aurenki da Yarima Riyad gobe ma zata aikoshi gidan nanâ wani kalan zaro idanu Haleema tayi she canât believe abinda taji tun tana yar yarinya takeson Yarima Riyad yahadu ne over wlh, lips nata rawa suka fara farinciki yahanata magana tace âMommy mekikace? Yarima Riyad mene? Dan Allah maimaitaâ?Kyalkyacewa da dariya Mama tayi tace âdalla cewa nayi zaâa aura miki Riyad zaki zama matan sarki dan ina mai tabbatar miki shi zaâa bawa Sarautanâ ihuuuu tayi tareda wani kalan tsalle ta rungume Mamanta sai kawai tahau tsalle sosai lekowa dakin Waziri da shigowan shi kenan yayi ganinsu yayi murmushi waya na kunnenshi Mama zatamai magana yadaga hannu yace âinajinki ranki shi dadeâ wucewa falo yayi yazauna Mama da Haleema suka biyoshi a speaker yasaka wayan dashi da Mom ke magana suna shirya komi kaman ba mutuwa aka musu ba, planning auren da yanda zasu sami kujeran suke hankali kwance.
**
Wuraren 10 yafito daga dakinshi yana sanye cikin wani farin yadi da akamai dinkin jumper yamai kyau sosai sai kamshi yake zubawa kaman zaije gasan turare, binshi da kallo Mom tayi tana murmushi tace âSon katashi? Munir yashigo yakai sau uku nacemai bai isa yatasheka ba, bayan kunyi sallan asuba tare a mosqueâ karasowa yayi yazo kusadab da ita yazauna ahankali yace âmorning Momâ as usual pecking nashi tayi a goshi tareda shafa kumatunshi tace âmorning Riyad, yaya jikin? Zakai breakfast yanzu neâ? Girgiza mata kai yayi alamun no, dasauri tace âto maza je Gwaggon ku ta aiko dazu akiraka kadawo saikai breakfast kafin kafita fada koâ? Dan gyadamata kai yayi yatashi ahankali yayi kofa haryasa hannu zai bude kofan tace âidan tamaka maganan auren Haleema kai naamâ dasauri yajuyo da kanshi ya kalli Mom dauke kai tayi kafinma yamata wani maganan, dan jim yayi sannan yabude kofa yafita maâaikata fada sun cika wajen yawanci Mom bata barinsu falo so anan waje suke yashe kaman kaya, gaishe gaishe da kirari sukahau mai ya wuce abinshi ko kadan baison zuwa wajen Gwaggo shi kadai hakan yasa yaciro wayanshi daga aljihu dailing number Munir yayi ringing daya yadaga yace âkanaâinaâ? Daga dayan bangaren yace âganinan daure da towel wanka zan shigaâ dan yatsine fuska yayi yace âbe fast toâ ya katse wayan baiso ya koma ciki dan baiso Mom tasan baijeba kuma baison yayita tsayawa awajen hakan yasa yawuce flat din su Munir wanda da dan tafiya sai gaidashi ake bai amsa kowa har gaban flat din tsayawa yayi jimmm awajen sai chan yasa hannu yabude kofan da sallama ahankali hada idanu yayi dawata mata dake zaune a falon sanye da hijab da charbi a hannunta kaganta kaman ita tai kakinshi ta tofar sunyi kama sosai, itama tanada haske kaman shi, sauke kanshi yayi kasa da sauri sannan ahankali yashiga ciki tareda maida kofan yarufe yama kasa magana, tadade tana kallonshi sannan tasauke kanta kasa tace âMunir nasama kaje ka sameshiâ gyadamata kai yayi sai chan kaman me tsoron magana yace âina kwana Mamiâ batare data kalleshi ba tace âyajikinka dafatan basu maka komi baâ? Dan dago kanshi yayi yakalleta ganin kanta akasa yasa shima ya maida kanshi akasa yace âIâm fineâ daidai lokacin Munir yaleko daga sama daure da towel yace âina fitowa daga bayi naji kamshin turarenka wlh daukomana breakfast kataho dashiâ mugun kallo yamai saikuma kawai yawuce dinning din yazauna yana bude warmers din saman table din, ganin shayi dayaji kayan kamshi mai zafi dasauri ya zuba a cup ya debi waina da pepper soup yadade rabon dayaci traditional food kawai yahauci bini bini Mami na dago kanta tana kallonshi dudda yabama falon baya, sosai yakecin abincin dan yanada ci yana cikin ci wayanshi yahau ringing ganin Mom yasa yahadiye wainan bakinshi da sauri yakai wayan kunnenshi kafin yayi magana cikin kakkausan murya strictly Mom tace âkana ina Riyad?â Kasa magana yayi yay shiru cikin masifa sosai Mom tace âokay sabida na barka tareda Munir shine yanzu gidansu kake zuwa kasan nida matan nan bamayin juna but you keep going there kana ganin gidan nan kowani yaro najin maganan uwarsa ni ban isa kaji nawaba ko ai shikenan kayi duk yanda kakesoâŠ..â âMommm!â dip ta katse wayan dasauri yatashi yajuyo sauke kanshi kasa yayi cikeda girmamawa yace âMami bari naje in Munir yafito yasameni awajen Gwaggoâ ahankali Mami tace âokayâ kofa yayi dasauri yabude yafita tabishi da kallo sai kawai ta sauke ijiyan zuciya, wajen Gwaggo yawuce, Babban flat ne uwa gari guda, ga hayaniya ana shiga da fita masu aiki sai gaidashi ake kaman anga sarki amman ko kallon mutum daya baiyiba harya shiga dankareren falon Gwaggo, dudda dakin yacika da mutane yana shiga Mai Babban daki ta sallami kowa falon yarage daga ita sai shi yawuce wajenta yazauna yayi shiru, fuskanshi Gwaggo ta taba sannan takama hannunshi tabi da kallo tana dube dube tace âyaro jiki uwa na baturai kai kenan baka isa kaga kazanta baâ murmushi yayi ya fizge hannunshi yace âGwaggo ni na warke kidena dubamin jiki dan Allahâ tsuki tayi tareda hankadeshi tace âkaga shashashaâ Hararanshi tayi tace âni shiga dakina ka dauko huran dana dama maka daga babanka sai kai kap cikin jikokina keson furanaâ jikinta yayi sanyi shima haka sai yayi shiru ganin yanda yayi yasa da sauri tai murmushi tace âbance kamin fuskan mara lafiya ba, Allah shiya bani babanku kuma shiya amsa Alhamdulillah dâana yayi abubuwan alkhairi da dama aduniya yayi shukoki daban daban, ya gina makarantu, rijiyoyi, gonaki dan haka banda nadama Allah ubangiji yakai haske kanarinsa jeka daukoâ tashi yayi ahankali yadauko kwaryan fura yazo yazauna yafarasha anatse tana kallonshi harga Allah itama zatazo Riyad yazama sarki cus yarone mai tausayi mara hayaniya ga kwarjini ga biyayya sannan ga kwazo, baida sa ido, shine yaro na farko kap yaran sarki daya fara neman nashi da kanshi, tun ana gulma ana cecekuce but marigayi yace abarshi yayi abinda yakeso dudda kalan kudi dayake dashi baitaba raina wani ko yadingaji yafi kowaba gashi da tausayi ya tsani yaga wani na fushi ko kunci sanadiyanshi dan haka itama Riyad ne zabinta daman tariga ta jefamai kuriâa. Ahankali tace âzabinka ne diyar Waziri ko zabin Mamanka Maryama dan nasanta da tsinannen taurinkai, dason saka kabi raâayinta sabida taba Allah ya yoka me biyayya, kaika zabi Haleematuâ? Abu yaji ya tsayamai awuya but ya daure ya gyadama Gwaggo kai batare dayayi magana ba, Gwaggo tace âai shikenan zaâai magana idan anyi bakwai na babanka muji, zanma Baffan ka Muji magana nama kirashi damanâ daidai nan Munir yashigo yana zama akai sallama Mujitapha yashigo yana sanye da manyan kaya daya fito da katon teban daya ijiye sai kyalli shaddan jikinshi yake kana ganinshi kasan yasha kudi ya koshi waje ya samu ya zauna hakan yasa daga Munir har Riyad suka gaidashi atare. âIna kwana Baffaâ binsu yayi da kallo shikebin mahaifinsu yanason yaran wanshi baida matsala dasu, yanason ya gaji sarautan but then again idan baisamu ba no big deal idan any of yaran wanshi suka samu, adai dauko wani sarki ne daga cousins nasu da sauransu shine bazai yarda ba, anatse yace âkai yajiki? Kasami lafiya?â Gyadamai kai Riyad yayi Baffa yace âhar yanzu ana kan investigation koma su waye sukai kokarin kasheka zaâa kamasu, so donât worry, itâs good zakai aure koda bakai maganan ba ma yana cikin plan dina nace kafito da mata you need to settle down shi lokaci baya jiran kowa mutuwa ake kullumâ Munir ya kalla daketa sunnar dakai yace âkaikuma fa yaushe zaka fito da taka matar?â Dasauri Munir yadago kanshi saikuma ya nuna kanshi foolishly yace âBaffa niâ akufule Baffa yamai dakuwa yace âaâa niâ Gwaggo ta zubamai rankwashi tace âdan kaniyanka kaima kafito da mata akaceâ kabar da hannun Gwaggo yayi yana turo baki yakalli Baffa yace âtoh Baffa zan fara nema daga yanzuâ gyadamai kai Baffa yayi yace âkutashi kuje toh lemme speak to Mamaâ tashi sukayi suka fice daga dakin.
Direct dakin Mom yayi yana bude kofa Mom tace âget out Riyadâ gaban kofan ya tsaya yace âsorry Mommy please Munir naje kirafa yarakani wajen Hajiyaâ
Cikin fushi Mom tace âtell me Riyad akwai abinda kataba so daban maka ba? You showed me duk cikin yan uwanka Munir kakeso dudda ban shiri da mahaifiyarsa but nabarka dashi but na gayamaka kadena zuwa side dinsu banso banso yare nake maka daka kasa fahimtata eh?â Ahankali yafara tafiya yakai inda take sai kawai ya rungumeta ashagwabe yace âI am sorry Mommyyyy bazan karaba kinga banda lafiya karki fushi dani please am missing Dad already abin zaimin yawaâ shiruu tayi saikuma ahankali tace âokay nahakura but baka ba ita that woman is the reason har Babanku ya rasu baya shiri dani she come between ni da shi, allow me to plan your wedding and coronation in peace kajiâ sakinta yayi sai kawai ya daura kanshi kan cinyanta ahankali yace âMom kimin auren na yarda but please Mommy banson nazama sarki dan Allah I am too young to be Sarki, Mom I want to tour round the world with my wife in peaceâ cikeda fada tace âkaje sama da 58 countries wani tour round the world ne yarage bakayi ba? Is time kayi taking responsibility naka Riyad, you are royalty Riyad, kai Royal blood ne ba normal samari out there ba, duk wanda aka haifa a royal family akwai high possibility zai iya zama king so accept your calling, and Babana zai turo bodyguards dazasu dinga binka anywhere and everythingâ dasauri yatashi yace âMom banso wlh bansoâ wani kalan kallo tamai tace âdid you even know su waye da waye ke kokarin kashe ka?â Kallonta yayi yace âsuwaye?â Tana kallonshi tace âI donât know but my gut is telling me Yayanku from the way yake eye service dan heâs everywhere, da yarinyar nan bata cecekaba I donât know what wouldâve happenedâ dan ijiyan zuciya Mom tasauke cike da damuwa tace âkullum bana baccin dare sabida tunanin wasu out there are trying to kill my sonâ dan lumshe idanu Riyad yayi ahankali yace âMom lemme see the footageâ iPad dake gefenta agadon tadauka ta bashi daidai lokacin akai sallama yar aiki ta gayamata tai baki tashi tayi tawuce tafita shikuma ya kwanta ahankali kan gadon tareda playing footage din da aka samo daga airport din yana kallo kusan footage biyar ne daban daban tun na shigowan shi arrival hall dana elevator saina bayin wanda shine na ukun, tsare cleaner yarinyar da ido yayi, a lokacin da abin yafaru bai wani kalleta ba dan yana cikin tashin hankali sai yanzu yake kallonta on this footage dudda is not that clear video karkar dinnan but yanda ta turashi cikin sharan yakala da yanda tarufe da how she handled everything ahankali yace âwho is this feisty gurlâ? The way takebin music yake kallo, he was actually watching the footage to see kozai gane criminals din but yana fara kallo attention nashi kawai yadawo kan cleaner, har footage data kaishi wajen dumping shara yakala da yanda take tafiya sai kawai yayi pursing video tareda zooming face nata yace âwho are you? You saved my life.â
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
HAPPY JUMMAâAT GIFT đ
EPISODE 7ïžâŁ
Zaune suke dukansu afada, dan kowa yanzu is at home babu wani maganan zuwa aiki ko wani abu zaman makoki suke, yawanci Kabir ke attending, Riyad na zaune inda yake hardly yake magana, wayanshi ne yahau ringing ganin Mom yasa yadauka yakai wayan kunne batare dayayi magana ba, Mom tace âcome nayi arranging private outing dakai da Munir da 2 security personnel da Doddo (Baban Mom Attorney General na Nigeria) ya aiko maka dashi daga Abuja kuzo kuje kaga Haleema gobe zata wuce schoolâ jiyayi kawai ranshi yabaci amman yadaure ahankali yace âokayâ yazare wayan daga kunne, kallon yayinshi yayi yace âMom nakirana bari najeâ gyadamai kai sukayi banda Kabeer dako kallonshi baiyiba, tashi yayi a tsanake yana gyara zaman milk jumper rigan dake jikinshi nawani attajirin yadi, fadawa sukahaumai kirari. âTakawanka lafiya Babban mutum! Yariman dashi kadai aka haifa agarin Riyad mai martaba yabashi suna Riyad, dan kwalisan zakaran da ya riga yayi chaâŠ..â wucewa yayi dasauri yafice dan baiso yawuce side na Mom a falo yasameta ita kadai tai murmushi ta taso dasauri tana gyaramai gaban wuyan riganshi tace âMasha Allah, yarona akwai kyau wlh, bama saika chanza kaya baâ ashagwabe kaman zaiyi kuka yace âMommmmâ dan hararanshi tayi tace âshagwabanka will not work nabiye maka u will never get married ko Doddo yayi naâam da decision dinâ ahankali yarike hannun Mom din kaman dan yaro yace âbut Mom I donât even know the girl balle na sotaâ dan shiru tayi tana kallon yanda yake mata wanda halinshi ne duk girmanshi idan bayason abu haka yake mata shagwaba at this point so take ta lallabashi dan batason tasake fada da yaronta datakeso sama da komi aduniya cikeda so tace âSon you are from royal family yawanci haka ake aure, first wife din Baban ka Maman su Kabeer da 2second wife dinsa Maman su Munir duk auren hadine baya sonsu, mai Babban daki ta zabamai su ya aura dan bayaja da maganan mahaifiyarsa, daga kan Maman su Shuibu dakuma ni last wife dinsa ne matan da marigayi yaso yakumayi soyayya damu is a normal thing haka abun yake, gidan sarauta kenan with time zakaso Haleematu sheâs a good girl duk agaban mu nan ta taso and she really loves you kaman kamata asiri dâana badai farin jini baâ Mom tai dan dariya dayasa kawai ya rungumeta tareda daura kanshi kan kafadanta wlh zaka dauka karamin yarone murya chan ciki yace âto Mom at least Baba yayi koda 7days ne kafin nafara zuwa neman wata, Mom I am still moaning my father I am not in the right state of mind to meet any girl ko talk to herâ cikeda lalama Mom ta shafa kanshi tace âI know but do it for me kaji ko akwai abinda bazaka iyamin ba ni Maman ka?â Ahankali yace âbabuâ murmushi tayi tace âyauwa dan albarka, Oya tafi jeka shiga mota suna jiranka abayaâ gyadama Mom kai yayi yasaketa ahankali wani kalan murmushi Mom take tabishi da kallo tana kara wani son yaron nata da alfahari dashi wucewa yayi yazaga baya budemai bayan wata mahaukaciyar tinted jeep akayi ya shige security yarufe kofa kallon yanayinshi Munir yayi ahankali yace âchill kawai being born from this family I guess comes with all this abubuwanâ fuzar da iska Riyad yayi yakalli gefe baice komiba aka tada motan fita daga gidan sukayi tawani secret gate basu da nisa nan da nan sukakai gidan Waziri lafiyayyen kayattacen iso aka musu aka kaisu wani lafiyayen falo suka zauna wayanshi yaciro yana dannawa kawai, Maman Haleema ce tafito cikeda farinciki tace âsannunku da zuwa Yarima Riyad da Munir sannu sannunkuâ anatse Munir yace âina yini Antyâ anatse shima Riyad kanshi na kasa muryanshi baya fita sosai yace âina yini Antyâ washe baki tayi kaman ta yaga zuciyanta sabida farin ciki tace âaahhh Riyad call me Mama ai yanzu anzama daya sannunku da zuwa bari naje gatanan zuwaâ tashi tayi tabar falon bata wani dade da fitaba Haleema tafito tana sanye dawani ubansu exclusive atampa an mata dinki Riga da skirt daya kamata dam ajiki, ta yano karamin gyale tayi makeup tai matukar kyau da black beauty ce abinta mai kyau tana kamshi, kallo daya tama Riyad zuciyanta yakusan tarwatse, gogan yayi masifan kyau yayi wani zama kaman shugaban kasa yana danna waya abinshi batare daya nuna alamun yamasan an shigo falon ba, zama tayi kujeran dake facing nasu cikin murya mai laushe da dadi tace âbarka da zuwa Yarima Riyad ina yiniâ ganin Riyad wayanshi yake dannawa yasa da sauri cikin barkwanci kartaga kaman yamata wulakanci Munir yace âauu ni zaâa watsama kasa a ido ni hoto ne a falon nan ko Riyad kadai kika ganiâ? Dan murmushi tayi tace âai kaima zan gaidaka kawai nafara gaida wanda zai kasance mijinane kuma uban yâayâana nan bada jimawa baâ âuh uh uhmmmmâ Munir yayi gyaran murya yana kama baki sai kawai yamike cikeda wasa yace âbari naje waje abuna tunda abun hakane, nima Allah yabani tawa uwar yâayanâ yataba Riyad ganin yaki dena taba waya yace âina wajeâ gyadamai kai Riyad yayi yawuce yatafi zai cigaba da danna waya dasauri cikin murya mai sanyi Haleema tace âbismillah yallabai ga abinci da abunsha na ijiye maka a dinningâ dan dago idanu yayi ya zubamata su dasauri tasauke nata idanun kasa dan bazata iya jure kallonshi ba, idanunshi kaman an wanke da madara, tana wani irin jin dadi aranta kaman an gama biya mata bukatunta na duniya, daga sama zuwa kasa ya kalleta yaune rana na farko dayake kallonta baiga wani makusa ba sheâs fine, educated classy but shi baiji that feeling of love da akace anaji in his heart ba, his heart is not racing, daya ganta his heart didnât flutter, infact zuciyanshi is beating normal, breathing nashi bai chanza ba, ya kalleta and he donât feel like looking at her again, sheâs fine but batai making heart nashi fine ba, heâs not having butterflies nor goosebumps acikinshi da jikinshi, heâs not finding her intriguing dudda tai makeup etc, nothing about her is enticing his aura, he read alot barinma lokacin PHd nashi, he knows the signs of love and baiji ko daya game da itaba, he sees her just the way he sees kowace diya mace aduniya nothing special nothing different, all this look and assessment yayishi ne in secs na kallonta kawai ya dauke kai yacigaba da danna wayanshi ayangance batare dayace mata uppan ba har lokacin.
Toshi yanzu mezai fadamata? He doesnât even know what to say, watsapp yashiga yama Mom magana yace âMomâ nan da nan Mom saiga reply tace âya akayi yaron Mom kunkai?â Da sauri yayi typing. âyes but I donât know what to say to yarinyar Momâ reply Mom tamai da âstart conversation ask her to tell you about herselfâ reply yamata da âYaya zan fada?â Mom tace âHaleema tell me about yourselfâ kaman zai fashe da kuka yace âtoo long Momâ salati Mom tabuga a chatting din tace âzan bata maka raifa tell her now!!!â Da dago kanshi yayi yakalleta karaf suka hada idanu dan kallonshi take kaman tasami video dasauri yadauke kanshi murya ciki ciki ba yabo ba fallasa yace âtell me about yourselfâ wani irin murmushi tayi na jin dadi tace âokay but bari nakawo maka drinks tukunna tunda bakaso kaje dinningâ batare data kalleta ba still yace âno bansoâ wani abu taji yanda yayi maganan bako kara amman tadaure takoma ta zauna tace âwhere do I even start, okay I am 24yrs, nayi sauka last 2yrs, ina karanta international relation a Oxford, ina final semester zan gama nan da 1month, ina business I have a cafe and na iya makeup but banama mutane kaina nakemawa, I love traveling too like youâ tayi maganan tana kallonshi expecting reaction amman ko motsi baiyiba tace âI love having fun celebrations irin su biki, zuwa wedding dinner friends and I love shopping and I love reading novels mostly english ban iya karanta hausa books ba I think basically thatâs all, ohh I have plenty friendsâ daga wayanshi yayi yama Mom typing tagama gayamin about herself Mom natafi ko? Dasauri Mom tace âcommon tell her about yourself tooâ ahankali yace âMom I hate sharing u know ni nagaji i want to come back home I donât like their house is making me feel sickâ kawai yafito daga whatsapp din kafin Mom tace wani abu yamike zumbur yace âbyeâ kallonshi tayi kaman tahanashi tafiya tadai daure tace âtom nagodeâ so take yabata numbers shi koda shi bazai karbi nata ba amman bemayi maganan ba.
Yana fita yashiga mota Munir yabishi da kallo yanda yake cire boturan wuyan riganshi da sauri sauri sai kawai yahau dariya yace âbanda business da yawo gari gari banga uban abinda ka iyaba Riyad wlhâ wani juyowa Riyad yayi yamai mugun kallo baice komiba Munir ya kyalkyace da dariya zaiyi magana wayan Mom yashigo yakalli wayan kaman zaiyi kuka yadafe kanshi yace âohhhh Mom nadamuna wlhâ murmushi kawai Munir yayi baice komiba daga wayan yayi Mom tace âkana inaâ? Ahankali yace âmuna hanyan dawowaâ katse wayan kawai tayi jin ana kiranta adayan wayan ganin batamata rai Riyad yakeson yi da ranan nan, ganin Waziri ne ke kiranta yasa tadauka cikin barkwanci yace âInlaw Inlaw to Alhamdulillah, yanzun nan Maman Haleematu ke gayamin Yarima Riyad yaje yaga Haleematu da alamu akwai nasaraâ murmushi Mom tayi tace âeh haryama fara dawowa wai kunya, kasan fa Riyad akwai miskilanci da shegen kunya har yanzu abu yake kaman karamin yaroâ dan dariya Waziri yayi yace âabinki da auta, yaro kwallin kwal, ai saisa yayi farin jini awajen kowa ina mai tabbatar miki yawanci yan kwamitin nada sarki idanunsu akanshi suke nadauka zanmasha wahalan convincing nasu amman bahaka ba wlh sunason Yarima Riyad sabida yacika sharuddan zama sarki, nafarko ga tsatso mai kyau jininshi gaba da baya asalin sarauta uwa da uba, banda haka baida any criminal record ko wani case da police ko wani abu, ga ilimi boko da islamiyya ga business daya bude dake kawoma Kano cigaba sosai dazun nan Gwamna ma yakirani kinsan Meyace mini?â Dasauri Mom tace âaâa meyace?â Dariya Waziri yayi yace âcewa yayi cikin yaran sarki waye mai manya manyan hotels din nan da gidajen mai din nan nacemai ai Riyad neâ dan dariya Mom tayi tace âai Dodo ma nakirashi nasa yama Gwamna magananâ Waziri yace âai ina mai tabbatar miki kaman Riyad yagama dawowa sarki dudda naga take taken Baffan su Mujitapha dakuma Kabeer amman Riyad yamusu fincikau dole ki tashi tsayeâ dasauri Mom tace âtuni natashi kaga yanda ake sauka akanshi ne, duk nasamai magungunan tsari a abincin danake basa da kaikayi koma kan mashekiyaâ Waziri yace âyauwa hakan kinyi daidai, ranan da sarki yacika bakwai zaâa sa ranar da zaâa nada sabon sarki sai ayi bikin Sarautar da aurensu tare koyaya kuka ganiâ? Mom tace âkwarai ai duk inda zan shiga saina shiga na tabbatar Riyad yagaji sarautan nan yarona kadai ya chanchanci mulkin nan bayi yanda naga damaâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 8ïžâŁ
BAYAN 1YR!!
Cikeda natsuwa wasu manya manyan fadawa ke bude wani hamshakin kofa da girmanshi zaiyi girman wani karamin gate daidai karfe sha daya na safe, sannan dukansu suka fadi suka zube suna daga hannu irin yanda dai fadawa ke gaisuwa suka fara zuba kirari.
âLafiya jakadan Baba Ali dan Baba Ali! Lafiya mai kiran gabas da yamma! Lafiya jinjirin wata sha kallo! Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa! Lafiya Garkami Wandon Karfe! Lafiya jijigen addini! Lafiya toya matsafa! Lafiya baya goya Marayu! Lafiya toron giwa! Lafiya tufaniyar gabas! Lafiya jinjirin wata shakallo! Taaaakawanka lafiya sarkin mu sarkin Riyad zakaran gwajin dafi mai hasken zuciya da hasken aura!, lafiya dan lellen Mai Babban dakiâŠ..â
Tunda suka fara kirarin nan kusan good 10min sai yanzu wani dogon mutum yafito yana sanye da wata milk kokuwar alkyabba dahar walkiya takeyi tsabagen kyanta ga rawani dawani white yadi mai kyau dake walkiya akamai, inda farare tarrr na idanunshi kake iya gani, hannunshi yarike wata sanda mai kyau, rabon da mutanen gari da yan fada suga fuskanshi shekara daya kenan, tun kafin yakaraso inda suke turarenshi yagama gauraye wajen da kamshin dadi dake dauke da yalwataccen niâima, ahankali yake tafiya kaman baiso yataka kasa, wani irin kwarjini shiganshi ke dauke dashi da bamaka iya kallonsa, har ya iso inda suke ya tsaya chak na kaman 5secs ya kallesu one by one to check idan kowa is healthy fine and present wanda hakan yana daga cikin abinda yasa jamaâa ke sonshi, kaman baiso ya furta magana yace âkun tashi lpyâ? Kaman jira suke. âLapiyanmu kalau Sarkin mu mai adalaci, sannu sannu toron giwa tsintsiya madaurinki daya!â yanda jikinsu har rawa rawa yake sunamai kirari suna yabashi ya kalla sannan kawai yawuce duk suka biyoshi abaya, direct fada suka shige inda mutane suke cike makil wajen zama yayi ya zauna, batare daya hada ido da kowa ba this is mostly method dayayi adopting dayake samai natsuwa cus dazaran ya shigo fada he sees love hatred envy a idanun mutane da dama barinma yayanshi Kabeer, but koda wasa baitaba disrespecting yan uwanshi ba, and so far so good Kabeer din has been supportive bai bashi wani matsala ba haka ma yayyin babbanshi da Waziri ana koyamai komi everything is going smooth Alhamdulillah.
Munir sai kallonshi yake bayan yazauna, yadade baiga sarkin da mabiya keso kaman Riyad ba, anason Baban su but son da akema Riyad daban ne, har lakabi akamai da Sarki me farin jini, dudda akwai yan adawa but wlh ana sonshi barin yan cikin gari, cus kafin ma yazama sarki yana taimako sosai yasaka yara a school da dama, yanzu kawai dan heâs not happy about zama sarkin sai the whole abu yasa he hardly talks, yakara miskilanci da wulakanci fiye da da, heâs so angry sabida heâs feeling kawai responsibility akasamai akai da baya so, responsibility daya tsaya and funny enough heâs doing so good da leadership din saisa har yanzu an kasa fadin wani negative abu akanshi ko kokafadi babu wanda zai yarda ma though yasan alot of people na jiransa to just make a mistake ne and he pray dan uwanshi will not make that mistake dasukeso suke kuma jira yayi.
Almost 2hr yayi afadan sannan aka tashi yakoma side nashi, bayan an bude katon kofan nan kaman gate still akwai tafiya kafin asalin babban gininshi, baya mulki like others, he hardly let anyone a side nashi, daga Muneer sai Mom da Haleema.
Shida Muneer suka jera fadawa na binsu abaya ana kaiwa gate din kowa ya tsaya dan babu bafaden dake shiga ciki ko matarshi bata isa tashigo side dinba without izininshi, sake bude another door sukayi that will lead them to compound din da interlock ya cika koâina ga bishiyan mango dake wajen da flowers koâina sai wata arniyan jeep bulletproof dake compound din gawani secret gate dayake wajen any private outing tanan yake fita.
Shiga mainflat din sukayi WANâı irin crazy sitting room ne dakeda fadi na balaâin yasha funitures that are very beautiful, zama Muneer yayi yadauki laptop dake kan table yace âalmost 2yrs bake leka hotel ba Riyad, its only right kaje manaâ wucewa sama yayi dan yaje ya cire kayan nan dasuka isheshi.
Binshi da kallo kawai yayi kafin ya shiga replying mails, kai tsaye aka shigo falon dasauri Muneer yadago kanshi dan mamakin waye ya isa yayi hakan ganin Mom tana sanye da wani alkyabba da akayi da crystal yasa yadan taso yace âina yini MoâŠ.â Baima karasa gaidataba tawuce stairs tai sama fuuu.
Riyad yariga yasaka wandon wani yadi brown da farin singlet ajikinshi yana kokarin saka rigan aka bude kofan bedroom nashi, dago kanshi yayi suka hada ido da Mom data haderai kana ganinta kasan ranta abace, dan lumshe idanu yayi yakarasa saka rigan Mom takaraso ciki har zuwa gabanshi dab dashi ta tsaya cikin tsananin bacinrai tace âyau kwanan ka nawa rabonka da shiga turakan Haleema Riyadâ? Hannu yamika ya dauki agogo daga saman bed yana kokarin sawa yace âMom kinsan Iâve been busy dealing with lot of things, my business, this sarki thing, everything maâ âand so?â Mom tai maganan da fushi tana daga murya tace âsabida business da sauransu bazaka kula matanka ba kusan 1months da 1week baka shiga gidan ta ba, and baka bari ta shigo nan ba, sai gulma ake tell me menene banbancinka da su Muneer da basu da mataâ? Dan yatsine fuska yayi still baice komiba yadauki links na hannun riganshi yana kokarin sawa Mom ta fizge links din cikeda masifa tace âRiyad wlh zan mugun sabamaka I hate this new attitude din naka, Iâm talking to you baka kulani, ka shiga turakan Haleema koka kirata tazo nan your choice, people are watching and you know that, 1yr kenan kunyi aure ba ciki and itâs all thanks to you, ni bantaba ganin mai gudun mace har mace ba sai kai, badadan na tambaya tacemin kalau kake functioning ba dana fara tunanin kokai mace ceâ sauke kanshi yayi kasa yayi shiru why will Mom be asking Haleema irin this kinds of question? Ahankali kanshi na kasa yace âkiyakuri Momâ cikin fushi tace ânayakuri nayakuri me? Get your wife pregnant nagayamaka dagayau nakaraji kun raba kwanaâ ta ijiye links din akan gado tajuya zata wuce hartakai wajen kofa zata fita ahankali yace âMomâ juyowa tayi tamai wani mugun kallo saikuma ahankali ta tako zuwa gabanshi ta tsaya tana kallon kwayan idanunshi, ahankali takai yatsanta tadaura kan kirjinshi cikin kakkausan murya tace âni mahaifiyarka na umarceka dakai tarayya da matarka, make her pregnant within period na this sabon month da aka shiga, inba hakaba wlh saika gamu da fushina sosai Riyadâ tajuya fuuuu tafice yadade tsaye ahaka idanunshi sunyi jaaa mode nashi ya chanza, he hates yanda Haleema tells Mom literally everything about marriage nasu, koma yace he hates yanda Mom ask everything akan aurensu, he hates both kawai, yana balaâin son sirri, he loves everything about shida matarshi nazama about them, anytime yakalli Haleema he doesnât even feel like shine mijinta, he feel like Mom ne mijinta, kokarin saita muryanshi yayi yadauki wayanshi dake kan gadon, Munir yakira cikin muryanshi da bata fita sosai tsabagen bacin rai yace âka aika akiramin Haleema plsâ yana maganan ya katse wayan, tashi Munir kawai yayi yafice bayan yabada sakon yashiga mota yabar gidan cus yaji komi da Mom tafadi he just pity his brother, Mom is just over controlling Riyad, sheâs in his matter, and baya iya cemata no, itakuma Haleema akanme zata dinga gayama Mamanshi komi gameda aurensu? Sabida taga baya iya tsallake maganan Mom ne, haba itâs annoying mana, Riyad dakeda kunya tagama fallasashi, it doesnât matter koda Mamanshi ne some private mata barinma harkan auratayyan su baikamata Mom tama sani ba, the girl is sick wlh batasan menene boye sirrin mijinta ba, dashine matarshi tamai haka Allah he will deal with her, yayi tsaki aranshi.
Office yawuce abinshi inyaso yasameshi daga baya.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 9ïžâŁ
Zaune take a arnen falonta takara kiba yanzu ba kaman da datake so skinny ba, tayi bulbul taciko alamun Riyad ya iya kiwo tasami kwanciyan hankali, wasu bayi ke gyara mata farcen kafa jakadiya ta shigo zubewa tayi tace âGimbiya Mai Martaba ya aiko akiraki chan bangaren saâ wani irin farin ciki daya lullubeta batasan sanda ta karbe kafanta ba ta mike da sauri tai sama bedroom nata ta shiga tana kiran wayan Mom awayanta kiran iPhone 15, ringing daya Mom ta daga Haleema tai wani ihu tace âMom I love youuuu, youâre the best Mom, Mom wlh ina sonki sama da tawa Mamar ma, Mom dabanda ke da narasa gata, dana shiga uku, kinga Mom yanzun nan Mai Martaba ya aiko akirani kinmai magana ne?â Dan murmushi Mom tayi mai sauti kanta nawani swelling yanda Riyad baya tsallake dokanta, she just wish kowace uwa zatasami yaro mai taushin zuciya da jin maganan mahaifiyarshi irin Riyad kawai baya jure fushinta ko kadan ne, koyaya tace yayi abu kobayaso sai yayi, shi kawai baison commitment ne da nauyi akansa baison damuwa baison hayaniya but tace yayi kaza saiya yayine, murmushi tasakeyi tana wani ji da kanta tace âMadallah! sai a kimtsa aje, ki farantamai raiâ gyadama Mom kai tayi cikin mugun farin cikin dan tana mahaukacin son Riyad tace âMom banda kamarki me sharemin kukana, Mom thank you for making my husband to call me, bye Mom I love youâ katse wayan tayi itakuma Haleeman cikeda jin dadi ta shiga shiryawa, tasha wasu magungunan da Jakadiya ke hada mata ta shiryata tsaf cikin wani hadadden atampa golden, ta daura Al kyabba akai ta feffesa turare sannan sauko kasa, Jakadiya da kuyanginta jaka biye da ita har zuwa side dinshi dayake da dan tazara tsakaninsu, tana zuwa dayake ansan da zuwanta aka barta ta shiga ciki Jakadiya da kuyangin kuma suka tsaya waje, shiga flat nashi tayi koâina na falon kamshin shi yake, murmushi tayi ta maida kofa tarufe sannan tacire Al Kyabban ta ijiye kan kujera tawuce sama tsayawa tayi gaban bedroom dinshi tai knocking.
Kusan 2min tayi wanda inda sabo ta saba jira haka duk sanda tai knocking, chan taji muryanshi ciki ciki cikeda isa yace âcomeâŠ..inâ bude kofan tayi gently ta maida kofan tarufe ta shiga dakin dakin tana tafiya ahankali sabida duhu gaske but tana iya ganinshi zaune bakin gado ya tsareta da idanu dake shinning even in the dark saida gabanta yafadi tadai daure ta maida takaraso zuwa gabanshi cikin yar kankanuwan murya dake cikeda yanga da iyayi tace âbarka da warhaka Mai Martaba, kayi aike akirani ganiâ mikewa tsaye yayi yazuba mata ido, chan yace âhow many times nagaya miki kidena kaima Mom maganata?â Faduwa gabanta yayi ta daure bata nunaba, cikeda makirci tace âni kuma?akanme zankai karan mijina?â Wani kallo dayake mata yasa batasan lokaci da lips nata yashiga rawa ba, ganin yariga yagane ita tafadi tace âyes nagayama Mom baka zuwa wajena kuma ko nazo baka bari a barni na shigo? Kayakuri nayi kuskure bazan karaba, wlh bana iya bacci ne, narasa yanda zanyi dakainaâ saikuma asanyaye tace âi need youuâŠâ wani kallo ya mata yace âand sabida hakan saki hadani da Momâ? Ahankali tace âmagananta kadai kakeji saisa nagayamata amman kaya kurâŠâ bata karasa maganan ba yawani kalan hankadata kan gado dasauri ta juyo ganin yana bude mazariyan wando wlh har cikin ranta taji kaman tai ihun dadi tadai daure tai shiru tana jiranshi, kafafunta yaja cikin fushi yace âyou reported me sabida this I hope nabaki shikenanâ ya kwashe skirt nata sama yadage rigan sama adduâa yayi yashiga ciki, runtse idanu Haleematu tayi tanaji kaman zata shide, wata daya babu abinda ya shiga tsakaninsu sai yau.
Almost 1 good hour yayi cur akanta not because of kanshi but her, ya sauke hakkinta daga kanshi tunda harta fara kai karanshi, saida yaji ta bushe ya tabbatar idan yacigaba zafi kawai zataji sannan ya kyaleta sannan yatashi zaune kafin chan yamike tsaye yawuce bayi ya barta kan gadon wani mugun bacci na daukanta tana numfashi haryau takasa gane kan Riyad, zai iya 2month bai nemeta ba yawanci saitasa Mom a case nasu yake nemanta and heâs so damn good in bed Innalillahi! The way heâs this quiet bazaka taba tunanin zai iyacin mace ba, but en anytime yayi having wani abu da ita jitake kaman sheâs the luckiest gurl on earth, Riyad is good on bed, she donât even know how to explain, yana wasa da jikinta wani kalan dirty play fa, yauma haushin abinda tayine yasa bai tattabata yanda ya sababa, wlh haryau takasa gane yanajin dadin ta ko bayajin dadinta oho ko gurnani bayayi bai tabayiba, heâs just super wired guy data kasa fassara halinshi haryau, and wiredness dinshi ke kara mata sonshi sosai aranta wlh, ahaka tana lumlumshe idanu bacci yayi awon gaba da ita.
**
Around 5 Mama ta tadata daga bacci, da kyar ta tadunma Mama, Mama tace âke yarinya sai nauyin bacci kaman wani kato, tashi kin manta yau zaku koma makaranta eh? Hope kin dauki permission wajen aiki an baki shift na yammaâ? Gyadama Mama kai tayi cikin gajiyan bacci, hannu Mama tasa tadagota ta taro kafadanta hakan yasa Rashida tasauke kanta akan kafadar Mama tana kara lumshe idanu still cikin bacci, dan jijjigata Mama tayi tace âRashidaâ ahankali tabude idahunta tass takalli Mama dasu Mama tace âI think drop most of ayyukanki tunda kin koma school kinga yanzu year 5 kike you need to study well, nakosa naga diyata tazama likita, saura 1yr yanzu, Allah ya aramin rai, ranan super wax zan saka amin combination da super laceâ dan murmushi kadan Rashida tayi tanason taji Mama na maganganu haka it makes her happy, Mama tace âyanzu dai kinga kina bukatan lokacin hutawa da lokacin karatu bakiga yanda kike gajiya ba da kyar kike tashi, ki saki sauran ayyukan ki rike na hotel din nan kadai tunda anfi biya, su Maman Miwa da sauran wajajen nan ki sakesuâ dan murmushi tayi sai kawai tahau yunkurin tashi ahankali dan muryanta baya fita sosai sabida daga bacci ta tashi tace âMama so kike na bar aiki sabida mudinga karban abincin sadakan da yan anguwan nan suke kawo mana out of pity?â Tadanyi shiru daidai takarasa mikewa tsayen batare data kalli Mama ba tace âthis year is clinicals, zamuyi aiki a pediatric da obstetrics&gynecology, I can manage everything Mama trust me, Alhamdulillah kome aka koyamin sau daya ya zauna akaina, sannan daga yanzu koda ranan Sunday ne zan dinga zuwa library duk sati sau daya nayi murajiâan duka abinda aka koya mana na that week, I can study Mama, I can do my duties na kula dake da siyamana kayan abinci da kudin magunguna, I can manage my work alsoâ tana maganan tayaye labule tafita daga dakin tawuce waje saida tafara sa abinci awuta sannan tawuce bayi tayi wanka tafito lokacin har sanwan yayi tazuba taliya sannan takoma daki tashiga saka kaya Mama na zaune kan dadduma tana kallonta, tana kallon yanda taketa ciro kayan ghana masgon dasuke agoge daga gani kasan dan kaya mai kyau take nema na zuwa school abu Mama taji ya tsaya mata a wuya sai kuma ta daure kawai ta dauke kanta daga kallonta.
Wani doguwan rigan atampa maroon ta zaba ta maida gefe, taciro lab coat nata dayake a goge shima ta ijiye gefe sannan ta maida sauran kayan ta shirya tsaf tawuce tafita tasake juya taliyan sannan tadawo tasa hijabi ta kabbatar salla.
Tana idarwa bata tsaya yin azkar ba ta fita ta juyo taliyan a kula tasama Mama ruwan zafi na wanka sannan tadawo tasake zama kan dadduma tafara azkar tana gamawa ta kalli Mama dake kallonta tace âGood Morning Mama na nikadai, Mama naji dadi nikadai kika haifa nake moreki banda kanni dazaki dinga raba attention naki akanmuâ most time tana maganan ne idan taga abu na damun Mama dan tasata tai murmushi, ganin Mama batai murmushi ba yasa takama hannunta tarike dasauri ahankali tace âMamaaaaaaaâ tai maganan ashagwabe tana lankwasa kai, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace âbabban burina arayuwa shine ki zama likita Rashida, banson wani abu dazai hanaki zama, kina bukatan lokacin dazaki karatu, banson ki fadi, banson ki sami carry over, nasan kinada kokari but dudda haka karatu yanada amfani, kina all this ayyuka bazaki sami lokacin yi ba, ki manta da kula dani Allah daya tsaga mana baki bazai hanamu abinda zamusa abakin ba, after this year next year zaki gama, please Rashida kibar ayyukan nan and focus a karatuâ tunda Mama ke maganan take kallonta batason sata cikin damuwa hakan yasa tace âto naji Mama amman tunda kinga satın nan muka koma karatu da practicals bazasuyi serious ba kibari nayi aikin zuwa karshen wata abiyani kudina saina dena kinji, zancen night shift ai HOD mu tasan dani bata taba sani a night shift ba sabida ke Mama, so ko yanzu ma bazan bazanyi night shift ba, kinga na karbi albashina saimu ijiye, kuma Mama kidena damuwa yarki ta dauko brain dinki bazan fadiba In sha Allah bayan kinamin adduâa, to yanzu kin hakura na karasa zuwa karshen watan nan duk sai na saki aikin nabar na hotel din?â Shiru Mama tayi tana kallonta Rashida da taurin kai da kafiya hmm, ijiyan zuciya tasauke tace âokay! Yau sha uku ga wata, karshen wata zaki sallame kowa, next month banson ganinki kina zuwa ayyuka nanâ gyadama Mama kai tayi tace ânajiâ tashi Mama tayi tace âai shikenanâ tawuce sip wani akwati zata dauko dasauri Rashida ta tashi tace âMama stop ki kirani na dauko mikiâ dasauri tasa hannunta tadauki akwatin tasaukar dashi kasa Mama tazo wajen ta zauna itama Rashida ta zauna gaban box din tana jiran tadauki abinda zata dauka tasake daukan akwatin ta maida sama, wata yar jaka Mama tadauko acıkın box din tamika mata tace âgashi ungoâ dasauri Rashida ta kalli jakan data bata tace âna menene Mamaâ? Tasa hannu tana karba, zage zip din box din Mama tashigayi tace ânaki ne kibudeâ da sauri taciro bakin ledan data gani cikin jakan dayake a kulle tashiga budewa saiga crocs a ledansu pink color mai kyau ba asalin designers one dinba but irin normal wanda ake saidawa a market yan 5k-7k dakuma stethoscope pink shima mai kyau, da mamaki take kallon kayan dakuma murmushi akan fuskanta tama kasa cewa komi Mama ta kalleta tace âbakiso ne oya bani kayana, last month danaje clinic wata Hajiya tarabamana kudi a envelop naduba naga 20k ne shine na shiga kasuwa na siya miki crocs naga shi likitoshi kesawa a clinic dimu duka likitocin wajen shine akafansu shine na shiga kasuwa na sayomiki ashe haka takalmin keda tsada dubu takwas aka saidamin na hada miki da wannan abun gwajin nace nima yâata tai kaman yan gayun likitocin danake gani a clinic dinmuâ hawaye ne yacika idanun Rashida tana kallon Mama na bata labarin Mama takare da ânazo naboyesu nace bazan baki ba sai ranan dazakuyi resuming schoolâ daidai lokacin hawaye ya sauko daga idanunta Mama tace âke mehaka kuka kikeminâ? Kawai rungume Mama tayi da gudu ta kankameta ahankali tace âthank you Mama thank youâ shafa bayanta Mama tayi tace âgabaki dayan rayuwanki Rashida nine na cinye miki ita, bakida lokacin kanki, komi kika samu ni, kome kikeyi sabida nine, konace ki sayawa kanki abu bakiyi saisa na saya miki kema ki shiga sahun yan gayu aga yâata fess fess akara kallonta sabida yanda tai kyau, Allah yakawo miji na gariâ cikin shagwaba ta ture Mama tace âni bazanyi aure ba Mama, bazan taba iya barinki baâ baki Mama ta kama tace âke kodai zan kaiki gidan zumane amiki rukiya kaman me aljanu bazaki aure baâ gyadama Mama kai tayi tadauki takalminta tana budewa daga leda tace âinhar ban samu mijin dazai yarda na daukeki muje gidanshi tareba ina ganinki ina baki kulawa wlh gara na kare rayuwana ahakaâ da sauri Mama tamata dakuwa tace âkinci mai garinku Rashidaâ dariya Rashida tayi sosai tace âwlh Mama da gaske nake bazan taba rabuwa dake ba Allah Mamaâ ganin Mama zatai magana yasa ta tashi da sauri tace âbari nasa takalminaâ fararen kafanta ta zura cikin crocs din sun mata balaâin kyau Mama tace âMasha Allah Tubarkallah komi kema yarinyana kyau wlh, kinga kafanki aciki kuwa dudda kafan fara ba lalli amman yayi kyauâ wani juyi tayi cikin takalmin tace âMama inason takalmin thank you so much Mamaa, bari na tafiâ tawuce tasa doguwan rigan data fito dashi yakamata ya nuna her flat tummy sosai da very full chest nata cus she has boobs kaman Mama, itama Mama harda rama yasa baâa ganin nata yanzu, dan kwali ta daura tayafa gyalenta tai arranging lab coat nata a bag pack da books da stethoscope da Mama ta siyamata da komi ciki ta goya abaya tasa yar wayanta a aljihun riganta da earpiece tace ânatafi Mamaâ Mama tace âdan Allah kici abinci kinji kada ki mantaâ dasauri tace âto Mama zanci, bye Mamaâ Mama tace âubangiji Allah bada zaâa Allah ya taimaka Allah ya tsareki Allah yakuma baki miji nagariâ.
Shagon Maman Miwa taje ta gayamata ta koma school da safe zata dinga zuwa aiki, nan da nan tayi wanke wanke ta share koâina tai mopping after 8 tagama komi Maman Miwa tabata 2k saikuma ta bata 200 tace âkihau adaidaita kitafi makaranta baki takabaâ murmushi kadan tayi tace ânagode Maman Miwaâ sannan tawuce tafito MamanMiwa tabita da kallo tace yarinya ga kyau har kyau ba miji.
Adaidaita sahu ta tare ta shiga sai BUK direct department dinsu ta wuce staircase tahau tana tafiya daidai lokacin wani guy da wata young lady kaman mate na Rasheeda suna sanye da kayan gida lab coat a hannunsu na saukowa hada ido Rashida tayi da guy din da sauri ta dauke kai tacigaba da tafiya abinta tana hayowa su suna saukowa hade fuska yarinyar tayi tace âBilal yaushe zaka fadamin inda kahadamin suprise birthday partyâ? Gabaki dayan hankalinshi nakan Rashida dake hayowa abinta batare data kara kallon inda suke ba, mintsilin shi yarinyar tayi abaya hakan yasa yakalleta da sauri yace âsorry Layla come again me kikaceâ? Abu taji ya tsaya mata awuya sai kawai tawuce da sauri tana sauka da sauri yabita da sauri yace âLayla wait commonâ tuni tafice dan tsayawa yayi daidai Rashida tahau staircase din dayake kai yabita da kallo sabida kyau datamai doguwan atampan riganta yamata kyau over, dudda ko man baki babu a lips nata balle hoda ko kwalli ahankali yace âweâre going to clinic you donât need to go up kasa zamuâ kaman bada ita yake magana ba kala bata cemai ba kawai ta juya tashiga sauka da sauri yabita yace âwai mesa bakimin magana Rashy?â Chak ta tsaya saikuma tajuyo ta kalleshi tace âkada ka sake kuskuren kirana da sunan nan only those that are dear to me ke kirana dashi not youâ ta juya, dasauri yabita yace âI donât understand why exactly youâre angry with me, I told you nace miki ina sonki ne banda knowledge na your motherâs illness, agidanmu bazaâa taba barina na auri yar wacce takeda HâŠâŠ.â âBilal!!!!â Rashida takirashi da karfi ta daga hannu zata kaimai mari ranta abalaâin bace tace âthe next time bakin nan naka zai ambato mahaifiyata wlh saina zubar da hakoranka! Nataba cemaka wani abu? Nace ka aureni dama? I donât even know kana existing so go to hell!â Tana maganan tajuya fuuuu yabita da kallo kowa na department nasu yasan Rashida da masifa but shi he just said it badan rashin mutunci ba he was trying to tell her bazaâa bari ya aureta agidansu ba knowing Mamanta nada HIV, bazaâa taba bari ya auro diyar unholy mace ba, still he was trying to tell her su zama friends dan he was feeling guilty yanda yagama cewa yana sonta last year dan last year yayi joining nasu dan transfer ya karba daga former school dayake medicine a Sudan, sun fara soyayya sosai yan aji sukamai gulma Mamanta nada HiV bai yarda ba dan bata taba fadamai ba saida aka kirashi akace yazo ga Mamanta tazo clinic itama tana wajen Maman shine yaje ko yagani daga ranan yayi ghosting nata yaki kiranta yadaina daukan wayanda kotamai magana a class yayi banza da ita saima yazo yana kula yan matan class nasu sosai danya bakanta mata rai, saikuma during this 2weeks holiday saiyaji wani irin soyayya ta na tasomai yau daya ganta saiyaji tafi ko yaushe kyau sonyayyan yadawomai fresh azuciye kaman yahadiyeta dan wlh duk department nasu baiga me kyanta ba kawai dai no one can approach her ne sabida masifan ta da fitina.
Koda yafito yaga harta shige bus nasu ta zauna taciro yar wayanta ta makala earpiece tasa a kunne sabida yanda zuciya ta ke tafarfasa, ahankali yasauke ijiyan zuciya yawuce wajen motar shi inda Layla take a tsaye tana hararanshi yabude yana mata murmushi yace âwai ke lafiyanki common shiga mota mujeâ yashiga mota yatada yaja motan Rashida ta kalla sannan tasake sauke ijiyan zuciya taso Bilal last session nasu sabida she thought shine mutum na farko daya sota for who she is dan ta dauka yasan waye ita kowa na department nasu ai yasani so tadauka yasani, tun bata kulashi tafara kulashi sabida yanda yake shige mata, she really liked him suna waya but rana daya kawai yadaina kulata yadaina amsa wayanta yana kula yan matan ajinsu agabanta yana cemusu yana sonsu just to hurt her, abin yamata ciwo sabida tanada kishi but bata taba nunawa ba, bata taba nuna tadamu ba saima daina kallonshi datayi da kallon inda suke cus sheâs even blaming herself data budemai zuciyanta bayan tasan duk wanda zatai soyayya dashi baya going anywhere, idan ba lectures gareta ba earpiece zatasa a kunne tana karatu tanabin everything da aka musu, sheâs a fast learner na ban mamaki, takoyama kanta rayuwan sheâs enough for herself, she doesnât need people cus gani take kowa yimata kallon yar mai HIV ake diyar fasuka, babu abinda baâa kiran Mama dashi har anan ajinsu su ana cewa Mama karuwa ce cus gata kyakkyawa daman, batason wata ko wani yashigo space nata and hurt her saisa sheâs always always protecting her space bawai batason tayi kawa bane ko kawance baya burgeta bane, no kawai she donât wanna get hurt, kawayenta na layinsu duk iyayensu sun raba yaransu da ita saisa ta maida kanta and centered her life to be just she and her mom.
Yan ajin always sees her as mafadaciya ko magana kama Rashida zai iya koma muku fada saisa suna avoiding nata suma but during group work ko wani abu zatai participating that is idan bamata daukin nauyin yin aikin gabaki dayaba dan tanada balaâin kokari haka dai rayuwan ta yake.
Sunkai asibiti dudda sun saba da hospital din still saida akai orientation sannan aka nuna musu roaster gobe zasu fara taduba taba bata night, daga 8 ne shift nata zuwa 1 kullum banda asabar da lahadi all thanks to HOD nata! Sheâs so happy da roaster sukai few abu by 11 suka tafi direct hotel din ta wuce takai wajajen 1 tawuce wajen changing room nasu tabude locker dinta taciro uniform nata tashiga chanzawa daidai tagama chanza kayan tana kokarin saka karamin farin hijabinta aka turo door aka shigo changing room din wata cleaner na ce Joy tai murmushi tana kallon gashinta dasauri Rashida takarasa saka hijabin Joy tace âHi kinzo muje Madam zata mana magana kafin mufara aiki a seminar roomâ maida locker Rashida tayi tarufe tadauki wayanta da earpiece tasaka a aljihun wando tawuce tafito Joy tabiyota abaya wani babban hall sukaje da kujeru ke cike su kusan 34 cleaners din na afternoon zama sukayi Madam dinsu dake tsaye gaban hall tace âI called for this meeting sabida na sanar daku Oga na gari he can come anytime, alot of you dakukai joining this hotel like 2yrs ago baku sanshi ba, he can come at any moment or day idan yaga dama, baya tolerating the slitest of dirt dan haka kuyi aiki dakyau, Rashida!â Dago kanta Rashida tayi takalleta Madam tace âsince kina afternoon duty yanzu anytime kika shigo before ki goge anywhere ki tabbata kinzo wajena kin amshi key kin goge office din Oga, for afternoon kene mai gyara office din da safe kuma Kola, abubuwan mop na gyaran office dinshi is different dana general gyara after the meeting you will follow me ki karbaâ Gyadamata kai Rashida tayi tace âYes Maâ tunda take aiki yau ne rana na farko dataji anyi maganan mai hotel dinma kusan shekara biyu kenan bai taba zuwa ba ko kuma yataba zuwa bata sani bane oho dai, addressing nasu tayi na kusan 20mins sannan tace âdismiss follow me Rashidaâ binta Rashida tayi abaya suka wuce office nata tamata handing over key card da sabon bucket mop su air freshener da sauransu a cleaning trolly tace âgashi maza maza 5th floor ai kinsan office dinâ Gyadamata kai Rashida tayi tafice daga office din tawuce elevator ta shiga zuwa 5th floor din, wani special corridor akebi aje office din da shi kadaine a hanyan corridor din, key wanda take kati ta manna a kofan kofan yabudu hakanan kawai gabanta yafadi batasan mesa ba hannunta tasa ta tura kofan ahankali ciki duhu dan an kashe wuta, hannu tasa tafara kunna wutan Babban office ne sosai daya hadu bana wasa ba, akwai dogon sofa banda table da chair ga babban tv ga desktop gawani mini library da akayishi design na tree kowani branch anyi naming nashi countey ga books na garin awajen saikuma wasu kofofi guda biyu daban daban ahankali tasa kafanta ta shiga ciki sannan ta maida kofan tarufe tana kallo dudda bawani datti, sauka idanunta yayı kan zanenta dake bangon office din dayayi wani irin mahaukacin kyau she canât believe she drew this, daina kallo tayi tashigo ciro brush na cire cobweb.
SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE đ
EPISODE đ
Cobweb tafara ciccirewa kafin tafara shara da vacum cleaner sannan tafara goge goge tundaga kan su desktop din, frames na bango, admiring design da komi na office din kowaye maishi really shows love nashi ma simplicity and art, gyara koâina tayi har labule saida tai dusting sannan tabude first kofan data gani ga mamakinta saitaga bedroom ne ga lafiyayyen gado awajen ga closet gyara komi tayi sharp sharp tai moping har bayin dake dakin sannan tafito tabude dayan kofan taga nan ma bayi ne ta gyara kusan 1hr tabata sannan tagama komi tafito takoma station nasu, kafin akira waya anason tazo room 456 ta gyara ta wuce taje ta gyara haka dai tai aiki had 5 sannan ta tashi.
Changing room takoma ta chanza kayan aikinta ta maida atampanta na safe tasaka pink crocs dinta na safe tana murmushin tuna Mama data siyamata sanan ta goya jakan nata tafito tana tafiya ahankali receptionist dinsu dake wajen tana ganinta cikeda faraâa tamata waving hannu tace âbye beautiful Rashyâ dan kallonta Rashida tayi hatta daga hannu zata mata waving itama saikuma tasauke hannun like a weirdo, tadan kyafta ido sau biyu kafin tace âthanksâ tawuce da sauri tafita dayan receptionist din tace âwhen will you stop throwing kanki on Rashida? Ko Madam dinmu tasan yarinyar is a weirdoâ dan murmushi tayi tace âis because sheâs like that nake sonta, I donât want normal people irinmu as friends inason irinsu Rashida as friends, the girl is lovelyâ tabe baki dayan tayi tace ânidai nawuce asha night duty lafiya see you in the morningâ.
Tana fitowa waje ta tsaya saikuma ta juyo jakanta da sauri zuwa baya tana kallon jakanta taja zip tashiga budewa tana kokarin ciro wayantaâŠ.
Ahankali yasauko da kafanshi dake sanye dawani Bottega veneta coffee color takalmi mai tsinannen kyau daga cikin motan, kumbunan shi farare kal kal agyare kaman an musu fenti tsabagen sheki dasuke, kafin gentle yakarasa saukowa yafito daga motan, dogone sosai yana sanye dawani coffee color soft yard na yan Malaysia mai balaâin taushi anmai simple aiki a wuyan, idanunshi sanye da bakin glasses na Cartier, glasses din yasa baka ganin idanunshi sai pink lips nashi dayayi so pinkish gawani irin lafiyayen bakin saje dayabi fuskanshi zuwa gemunshi da gashin baki daya karama fuskan shi kyau sosai da kwarjini da haiba kaman wani balarabe, hannunshi na daure da agogon Cartier shima latest collection dinsu, his entire body speaks luxury, he looks squeaky clean kaman ka lashesa,
daidai taciro wayan tana kokarin manna earpiece a kunnenta dan Mama takeso takira kawai taji sahun gudu gudu sauri sauri dasauri tajuyo dan taga meke faruwa, daidai lokacin itama Mirabel data fito daga cikin hotel din tazaro ido tace âOga yazo OMGâ tai parking space dagudu itama same with sauran maâaikatan dake waje, kallon inda sukayi Rashida tayi har tana dage but still bama ta iya hango wanda ake kira da Oga sabida yanda maâaikatan suka zagayeshi cikeda farinciki sunamai sannu da zuwa, dauke kanta kawai tayi takarasa makala earpiece din tafara tafiya abinta tana dialing number MamaâŠ.
Shifa he hates too much attention, the way suka zagayeshi ana gaidashi kaman wani celebrity yazo sai abin yakara batamai rai dan har yanzu abinda Mom tamai da Haleema na batamai rai, the way suka wani fito suna gaidashi abin kular dashi ma yayi wucewa kawai yayi batare daya kula ko mutum daya cikinsu ba yana tafiya a kasaitacce Munir shine ya tsaya amsasu daidai takai gate zata fita taji wani iska ya kadata kamshi mai dadi gaske wanda bata taba jin irin shi aduniya ba yadaki hancinta da saida ta lumshe idanu sabida dadin kamshin daidai an budemai kofa shima ya tsaya sabida sanyin dayaji yakai 10secs ahaka kafin yadaga kafa yashiga cikin lobby su dan security sun budemai glass door din, ya shiga ciki yana bin koâina da kallo sai kawai yawuce wajen elevator manager tafito dasaurin ta daga office dinta tana murmushi tace âwelcome Sirâ Gyadamata kai yayi yadauke kai yadaga hannunshi yana kallon agogon hannunshi daidai kofan na rufewa 5th floor yawuce direct office nashi yaje hannu yasa a aljihunshi yaciro wayanshi kawai ya manna a kofan kofan yabude yashiga ciki an kunna AC wajen sanyi, tsayawa yayi chak yana kallon frame na artwork dake bango dudda manager ta turama Munir hotunansu ta email shikuma ya nunamai but yanzu daya gansu in reality sai sukamai mugun kyau. Daga kafanshi yayi yataka zuwa wajen yasa hannunshi yasauko dashi yana kallo sai kawai yayi murmushi for the first time today yaji abu yasashi farin ciki. Zama yayi akan kujera tareda lumshe idanu yadaura hannunshi aka yayi shiruu he donât like the way Mom kesashi yin abubuwan dabayaso yayi, she made him king dudda bayaso, she made him marry dudda bayaso, yanzu kuma sheâs telling him how to handle family shi, bude kofan office din akayi aka shigo hakan yasa yabude ido kadan Munir ne yamaida kofan yarufe yashigo yaja kujera ya zauna kai tsaye tace âwaikai meke damunka ehâ? Kallonshi Riyad yayi saikuma yayi shiru tareda fuzar da iska, tashi Munir yayi yasan bazai gayamai ba yawuce wajen kofan bathroom haryasa hannu a kofan yajuyo yakalleshi yace âRiyad I hate seeing the slightest damuwa akan fuskan ka, banda youâre my brother, you are also my best friend, kowani yanayi kake ciki affects me, life can be colorful idan you let it be that to you, be the Man of your life karka bari kowa yagaya maka ga yanda zakayi, you are loved, jamaâa harda wayanda basu sanka ba na yabonka, kana adalci asarautan dakake yi kadena bari anything na damunka kajiâ? Dan kallonshi Riyad yayi for the second time yayi murmushi yace âokayâ bude kofan bathroom din Munir yayi harzai shiga ahankali Riyad yace âthanksâ kallonshi Munir yayi sai kawai yayi murmushi yawuce yashiga bayin maganan Munir yasa yaji sanyi aranshi he will take things easy on kanshi and everyday he will try and do wat makes him happy he will live his life, daga yanzu kullum saiya fita zai chanza schedule nashi daga 4:00 har dare ya warema kanshi da safiya kuma fada, he will leave 2 separate life dinshi privately and peacefully, tashi yayi ahankali shima yawuto yabude kofan dakin yashiga bathroom yawuce direct yadauro alwala yafito abu yataka dayaji ya chaki kafanshi dasauri ya tsaya yadaga kafar ya kalli kasan carpet din yaga karamin dankunne ne baki ya shiga kafanshi dudda bai shiga sosai ba, ahankali yakai hannunshi yacire daga kafanshi yakalli earring din murya chan kasa yace âwho dropped this here?â Yayi shiru yanabin dan kunnen da kallo daidai Munir yace âkana alwala ne koka fito? Muje mosqueâ dasauri ya zura dan kunnen a aljihunshi absentmindedly gudun kar wani yataka, yataho yabude kofan yadauki glasses nashi da waya Munir yace âba nan kasa zamuje salla mudawo muyi aikin baâ wucewa yayi yace âI thought kaikace i should always be happy, zanje na buga golf yau, tunda Mom tasamin aikin sarki ban buga golf baâ murmushi Munir yayi sai kawai yabiyoshi suka wuce suka fita.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ1ïžâŁ
Salla sukayi a mosque nan ma anata gaidashi still few ya amsa dazasu wuce yasa Munir ya basu bandir na kudi dake pocket nashi, sannan yawuce mota ya shiga mazaunin direba Munir yana zuwa yazaro ido yace âmehaka rabon dakai driving da kanka about 1year kai tunda kazama sarkiâ murmushi yayi yamikamai hannu ya karbi key baice komi ba yatada mota suka wuce wani private waje dayake buga golf chanza kaya sukayi ga maâaikatan shi yafara buga golf din yanayi yana murmushi, sosai Munir yaji dadi ganin heâs very happy today kullum ganinshi zakayi so moody. Anan sukai Ishaâi sai wajajen 11 na dare sannan yagama yatafi office nashi na wajen yayi wanka ya maida kayanshi yana kallon yanda wayanshi ke ringing yakalli screen yaga Haleema a rubuce kaman bazai dauki wayan ba saikuma ya dauka yakai kunnenshi yayi shiru daga ta dayan bangaren tace âina kajene yau Mai Martaba? 11 nadare yanzu faâ lumshe idanu kadan yayi bayabo ba fallasa yace âyanzu zan fara dawowa, make tea for me before i comeâ yana maganan yacire wayan daga kunnenshi ya katse ya ijiye ya karasa saka boturan riganshi shima Munir yashigo yace âmutafiâ wucewa sukayi wannan karan Munir yayi tukin har gida, ta private gate dinshi as usual suka shigo parking sukayi yafito yana tafiya a natse har flat nashi, heâs very hungry but tea yakeso dan is late, waya yadaga yayi dailing number Haleema tana dagawa kafin tai magana yace âina teaâ? Dasauri tace âbari natashi na daura tunda kadawoâ jiyayi ranshi yabaci but baiso ranshi yayta baci sabida ita hakan yasa yace âkibarshi bansoâ ya katse wayan yajuya yafito daga flat nashi, shi kawai bai iyajin yunwa ba ne, wajen kofan dazai sadashi da cikin gida yayi yabude fadawa na ganinshi suka zube zasu faramai kirarin rai abace yace âkuje kuyi bacci na sallamekuâ sauke kansu duka sukayi kasa yawuce fuuu direct flat din Ammi yawuce yana adduâa Allah sa Munir daya shiga bai rufe kofa ba kai tsaye yabude kofan, babu kowa a falo sai TV dake aiki tashar CNN, dinning ya kalla ganin kuloli akai ga flask na shayi yasa yawuce wajen sadaf sadaf kaman barawo yashiga bude warmers din sinasir yagani dake tururi kaman yanzu akayi abunka da kula mai kyau da miyan taushe dayasha cow tail dudda ba abinci yaso yaci ba dan dare yayi sosai saiyaji abun yabiyamai rai zama yayi ahankali yadauki plate ya ijiye yasa sinasir guda 3 da Miya yasa nama dayawa yadauki spoon yafara ci ahankali he loves abincin Ammi har ranshi, tafiya yaji a stairs hakan yasa yadago kanshi dasauri ganin Ammi tana sanye da lullubi ga carbi a hannunta yasa yasauke kanshi kasa da sauri murya chan kasa yace âina yini Ammiâ batace kala ba cigaba da saukowa tayi daga stairs din shikuma yakasa ci gaba da cin abinci sai ahankali ya yunkura zai tashi strictly tace âina zaka?â Kanshi akasa still yace âuhmm dama nagama ci zan tafi neâ âsit downâ tafadi babu wasa a muryanta, baiyi musu ba zama yakoma yayi har dinning din tazo tsayuwa tayi kusada shi rabon dayaji Ammi tsaye kusadashi haka harya manta he canât even remember when, hannu tasa ahankali tadauki flask da cup mai kyau ta tsiyayamai ruwan shayi tadauki spoon da bottle na honey ta digamai aciki ta tura agabanshi kafin ahankali tace âidan kanaso katafi finish abincin daka faraci, nobody waste abincina in this houseâ kanshi na kasa har lokacin yakasa dago kanshi ya kalleta, juyawa tayi tawuce takoma falo tazauna tadauki remote ta chanza channel din zuwa Aljazeera ta maida idanunta wajen, adan hankali ya wiago ya kalleta sannan yajuyo da kanshi yacigaba da cin abincin kadan kadan tass ya cinye ya kora da ruwan shayin saiyaji hankalinshi ya kwanta, yanada cin abinci shi but only yasamu abinda yakeso, tashi yayi ahankali yajuyo yadan kalleta hada ido sukayi da sauri ya sauke kanshi kasa cikeda ladabi yace âgood night Ammiâ âAllah tashemu lafiya Riyadâ tana maganan yawuce da sauri yabude kofa yafice tareda maido kofan yarufe ahankali karyayi kara, ahankali ta sauke ijiyan zuciya sannan ta lumshe ido kaman irin sheâs hurt ko akwai wani abu azuciyanta, kafin ta tashi tawuce inda yatashi zama tayi wajen ta dauki cup din dayasha tea ta kalla tai shiru kaman wacce ke tunanin wani abu sai chan tadaga flask din ta tsiyaya tea dazun nan ta dafa shayin tawuce taje tai wankan dare, itama bata iya bacci idan batasha shayi da daddare ba, daukan cup din tayi takai bakinta ta kurba sannan ta taso tadawo falo ta zauna tana shan shayin.
Yana shiga side nashi yaga Haleema azaune ga tray shayin tasa wasu arnayen kayan bacci da sauri ta taso tace âina kaje nakawo maka shayin baka nan babu masu gadinka ka koresu neâ? Rigan jikinshi yahau cirewa yace âyes, kidau shayin kitafi dashi I donât wantâ Shiru tayi tana kallonshi tana bin jikinshi da kallo wucewa bayi kawai yayi bayan ya rataye rigan a hanger dake dakin mai kyau ijiyan zuciya tasauke tace âwash Allah na mutum kaman shi yayi kanshiâ wucewa tayi ta dauke tray takai falo ta ijiye sannan tadawo dakin tai kwanciyarta akan gadonshi tana jiranshi yafito, yadan jima a bathroom din sannan yafito daure da towel a waist daya a hannunshi yana tsane kai, kallo daya yamata yadauke kai yashiga shafe shafenshi yana fesa turare kafin yawuce walk in closet room nashi yasaka wani dark blue pajamas sannan yafito ko kallon inda take baiyiba iPad nashi yadauka yawuce ya zauna kan sofa ya makala EarPod yayi playing video ranan da akaso kasheshi wanda yarinyar nan ta ceceshi ke ciki, ya kalli video nan yafi sau dubu he is just looking for the girl number datasa a file nata baya shiga, yatura anje address datasa a file nata baâa ganta ba, yaje da kanshi shima bai ganta ba ance babu wata kamanta ma a layin heâs just greatful yarinyar saved his life, video always give him peace he donât even know why he donât care ko sata take koma wacece ita he just wants to reward her yabata better job for saving his life, and huge money to startup business or anything datakeso, gama kallon yayi sai ya zare EarPod din ya rufe iPad din ya ijiye yadan kalli gadon hada ido yayi da Haleema ba yabo ba fallasa yace âwatâ? Dan murmushi tayi tace âletâs try having Baby, nakosa naga ina dauke da cikinka na haifo maka magajiâ dan yatsine fuska yayi da ita da Mom baisan mesa duk suka damu da cikiba kaman auren yayi 10yrs this is just a year, Allah ke bada haihuwa not him, kaman bazai tashiba saikuma yatashi ya kashe wuta yawuce yahau gadon ya kwanta tareda juya mata baya da sauri ta mirgino ta kankameshi ta baya kaman zata fashe da kuka tace âletâs make Baby kaji My loveâ shiru yayi shi baisan kodan baida feelings for her kawai an auramai itane koko shine baida lafiyane amman kwata kwata bayajin shaâawan Haleematu ko zata tsaya gabanshi tsirara, everything heâs doing yanayi ne sabida matarshi ce dole ya kyautata mata yakuma sauke hakkin ta daga kanshi, before ya ankara hawa jikinshi tayi tana kokarin mai kiss yadauke kanshi haryau bai taba hada bakinshi da nata ba, jefar da ita gefenshi, hannunshi yakai yaja wandon pajamas dinshi kasa dasauri tashiga daga riganta sama itama, ahankali yakai hannunshi kan boobs nata ya shiga squeezing nasu sannan yayi adduâa yayi sliding in, nishinta ke tashi kawai daga dakin kaman zata shide, dakin yayi tsit, if thereâs one thing she kind of understood about him yanada son wasa da boobs, anytime zaiyi abu da ita sunashan squeezing a hannunshi saisa bayan aurensu boobs nata suka kara girma sosai dudda baya sha but ya iya wasu dasu abin namata mugun dadi almost hour and half yayi duk tagama ficewa hayyacinta sannan ya rirriketa tasan heâs cumming cus thatâs only time din dayake rirriketa and just be in her body itakuma she uses that opportunity to cuddle him, alokacin zai fara nishi da karfi kaman zai fashe mata da kuka like a baby, kankameta yayi sosai kanshi nakan kirjinta yafara nishi da karfi he just wants to cum yahuta baida kawowa dawuri, idan yakawo once idan heâs going for 2nd round zai iyakai 4hrs bai kawowa, rirrikeshi Haleema tayi tana shafamai kai kalan nishin dayake mata a kunne da fuska na kara tafiya da imaninta yana hitting wajen da kyau chan yayi karaaaa mai sauti wanda haka yake yajuye mata komi ciki, yakai almost 2min ahaka baitashiba yagama tsiyayewa ciki kotayi cikin shima yahuta da jaraban Mom sannan yasauka daga jikinta tareda maida wandonshi yajuya mata baya yana sauke ijiyan zuciya, dasauri tabiyoshi ta hugging nashi ta side, ko 1min baiyi da gamawa ba sai bacci jikinta yamata dadi, yakai kusan 1hr a kwance sannan yajanye jikinshi yatashi yawuce bayi yasake wanka ya chanza kaya yafito sai kawai yawuce dayan sakin yaje ya kwanta awajen.
*
Wuraren 6 takai gida da kafa takoma tana shiga taga Mama tareda Uwargida Baba Liman, Baba Liman shi kadai ke mutunci dasu a unguwan, yana tursasa matanshi suzo su duba Mama once in a while hakkin makotaka, anytime yayi noma ko wasu yan kudade suka shigomai he always send something to Mama dudda Rashida bataso dan shima bukatan taimakon yake, but tana girmamashi kodan mutunci da suke da Mama da yanda Mama ta daukeshi itama. Uwargidan tana shigowa once in a while tazo gaida Mama dudda ko ruwa batasha aka bata kujera ma saita share da dankwalinta take zama akai kaman irin idan ta zauna ko ta taba wani abu nasu zata kamu da HIV itama, Rashida bata sonta sabida Mama ne ma take gaidata dan da wannan zuwa tana kyama tana kaffa kaffa gwara tayi zamanta agidansu ai babu wanda yace dole saitazo, tana ganinta ta kirne rai ganin ta shimfida dan kwalinta saman kan tabarman da aka bata a tsakar gida ta zauna kai tsaye bayan tai sallama ta wuce wajen Mama dake zaune kan dakalin bakin kofansu ta rungumeta tace âMama nadawoâ murmushi Mama tayi tace âsannu da zuwa ga Indo baki gaidatabaâ kallon Matan tayi dake kallonta tana washe baki, mugun kallon da Rashida tama matan yasa da sauri Indo tamike tsaye tana dauke dankwalinta tace âbari naje Maryam Allah Kara saukiâ Mama tace ânagode Indo saida safe a gaida yaraâ takalli Rashida tace âwaike mesa fitinanniya ceâ? Tashi tayi tace âMama tunda ba dole akamata tadinga zuwa gidanmu ba ai sai tadena wannan kyama kyaman bazan dauka baâ shiru Mama tayi ta buga tagumi tana kallonta hakanma saiyasa tayi dariya tace âMama mehaka kikai tagumi kina kallona kaman kinga hotoâ? Cikeda damuwa Mama tace âtunani nake wakika biyo da temper nan naki Rashida? Kap dangina babu mai fada masifa, fushi, taurin kai da kafiya irin naki, to maybe sai dangin mahaifinki dan bangama saninasu ba abinki da yan Sarauta sunada yawaâ tamau Rashida ta daure fuska sai kawai ta tashi tace âMama inaga harda kallan son da mutumin nan yaga kinmai saisa ya wulakantaki, baki magana baki kawoshi ba after how many years Mama you still remember mutanen da mutumin that hurt and destroyed life dinkiâ kallonta Mama tayi tace âbabanki yamin kirki abaya dudda ya wulakantanin amman hakan bazaisa na manta kirkinshi baâ ayanda fuskan Rashida yayi da ace zata iya dukan Mama datayi akufule tace âAllah karya dauramin son wani haka Mama cus inaaa! Mama you have no idea yanda na tsani mutumin nan and duk randa na sami opportunity wlh I will hurt him sama da yanda yayi hurting naki, bari nagama makaranta nazama wani abu saizan ya wulakantamini uwa!â Mama zata kara magana Rashida ta tashi da sauri kawai tashige ciki Mama tai murmushi kawai tareda sauke ijiyan zuciya.
*
Around 7 na safe yadawo daga masallaci wanda haka yakeyi daman before yayi bacci yatashi 10 ya shirya yaje fada by 11. Bacci yakoma adakin daya kwana ya kwanta, harya fara bacci yaji hayaniya sama sama da alamun kuka, dan bude idanunshi kadan yayi trying yaji da gaske anan side yaji kuka, knocking kofar dakin dayake ciki akayi saikuma yaji muryan Mom afadace tace âopen this door Riyad nasan kana jinaâ tashi yayi ahankali ya kunna wutan dakin yana mamakin meya faru, yadauki jallabiya ya zura dan dagashi sai short yayi wajen kofan ahankali yabude kofan Mami yagani ranta abace saikuma ya hango Haleema duke tsakiyan corridor tana kuka sosai kaman an mata mutu har yanzu rigan baccin jiya ne ajikinta, yadai daure yace âgood morning MomâŠâ hannu Mom tadagamai ranta amasifan bace tace âhold greeting naka I donât want it Riyadâ confusingly yake kallon Mom saikuma yakalli Haleema dake kuka sosai trying to ask meya sameta kawai yaga Mom ta mikamai hannunta da karamin dankunne ke kai tace âa ina kasamo wannan Riyadâ? Kallon dan kunnen yayi harga Allah baigane dan kunnen bama hakan yasa yace âMom wat is thisâ? Cikin fushi sosai Mom tarufeshi da fada tace ânikake tambaya wat is this? Matanka ta tsinci dan kunnen mace a aljihun rigan kayan dakasa jiya kadawo very late kusan to 12 nadareâ sai alokacin yama gane dan kunnen nan dayatake ne akasa a office nashi dasauri yawani ma Haleema dake kuka kallo kai tsaye yace âkayana kika duba kika bincika is that abinda kikeyi anytime kikazo this side?â Mami tace âlook at me here nine nazo nike magana dakai not Haleemaâ authoritatively tace âtell me, me dan kunnen mata keyi a aljihun ka wanda bana matarka ba, mata kake bi yanzu Riyad? Me ka nema wajen Haleematu karasa? Dan kunnen waye tell me nowâ? Tunda yake baitaba jin Mom ta batamai rai irin na yau ba kanshi ya nuna yanama Mom wani irin kallo yace âMom Iâm your Son, kin sanni sama da kowa a duniyan nan, Mom yanzu akazo aka cemiki ina neman mata bazaki iya shedana ba? Do I look like ina neman Mata? Ni?â Harga Allah tun Riyad na yaro bai taso dason Mata ba, ko kallonsu bayayi hasalima kunya suke bashi amman dai cikeda kafiya dason nunama Haleema she own her Son tace âhow do you want me to trust me bayan matarka taga dan kunne akayan dakasa jiya and kadawo very late eh? Look at the way the poor thing is cryingâ tanuna Haleematu dake wani irin mummunan kuka tace âko kadan banso kayi hurting yarinyar nan cus sheâs a good gurl, tadaukeni mahaifiyarta, Babanta yataka rawan gani sosai wajen zamanka sarki, heâs the one blocking all kulle kulle da akeyi yanzu daka zama sarkiâ âdid I ask him to do anything for me?â Riyad yayi maganan da karfi da saida Mom tabude idanunta cikeda mamaki ta kalleshi, yau Riyad ya daga mata murya haka? Agaban matarshi, cikeda mamaki tace âNikake dayama Murya Riyad?â Cikin fushi sosai yace âMom abinda kikemin is totally wrong, sabida Haleema tace inabin mata saikizo ki yarda da maganan ta kinamin fada agabanta baki san danki ba? Youâre not allowing me to be the man in my marriage, nagaji I canât continue with this marriage because of Babanta kikasa ya nemamin sarki dagayauâŠâŠ.â da sauri Haleematu ta taso tana kuka sosai afirgice kawai ta zube agabanshi tarike kafanshi tace âdan Allah kayakuri wlh nasan bakabin mata bansan menakeyi ba danaga dan kunnen saisa nakira Momâ fizge kafanshi yayi yakalli Mom yace âdagayau tell her bata babu this side I forbid her from coming to my side, duk sanda nake bukatanta zan nemeta!â Rushewa da kuka sosai Haleematou tayi takama kafan Mom tace âMom do something, dan Allah kimai magana ya yakuri, bazan karabaâ
Yakalli yanda Haleema ke rokon Mom ya cije baki ya kalli Mom din dake kallonshi mamaki yagama kasheta yace âand for your question Momâ sai kawai yadaga mata kafanshi yanuna mata tafin kafan inda dan kunnen ya shiga yace ânataka dan kunnen nan akasa ya shigan min kafa, na cire zan yarda ganin ina cikin premises kar wani yaje yataka yasa nasa a pocket with the hope nafito i will trash it but I forgotâ ya maida kafanshi ya ijiye yace âI donât want the sarauta ki nemo wani kibashi, I need a breakâ yana maganan yabi ta gefensu yawuce dagashi sai jallabiyan jikinshi yanda ranshi yabaci ko waya bai daukaba Mom tajuya tabiyoshi dasauri ganin ahaka zai fita tace âRiyad, Riyadâ hannu yasa yabude kofa azuciye yafito key motar compound nashi na wajen Munir hakan yasa yayi gate yafice fadawa zasumai kirari ya buga musu tsawa âleave me alone!â Kawai yawuce fuuuuuuuu shi kadai yana tafiya a balaâin zuciye kawai yawuce side din su Munir bude kofa yayi azuciye key daya hango akan table yawuce kaman zaki yadauka daidai Ammi na lekowa daga kitchen ganin shi yadau key dinta ranshi abace yasa tai shiru daidai yabude kofa yafice parking space nasu yaje yana danna key wani jeep yayi kara motar Ammi ce direct yawuce yabude ya shiga yanda ya danna horn zakasan ba lafiya aka budemai key yawuce yafita.
Kusan yaune rana na farko da Mom take ganin serious fushin Riyad haka, and for him to provoke like this that means abinda yafadi gaskiya ne babu matan dayake nema, hankalinta yatashi sosai, wayanta dake hannunta ta daga zata kirashi saitaga wayanshi akan gado kawai cike da takaici takalli Haleema dake kuka tace âyou are not sure of something akan wani dalili da rashin hankali zaki tafka shirmen nan eh Halimatu? Jibi abinda kika jawo yanzu? Bakisan idan mai hakuri yayi fushi yafi zama worst ba? Jibi yanda yafita ko wanka baiyiba bai dauki wayanshi ba tsabagen bacinrai, sabida kinga dan kunne in this pocket mesa zaki assuming mata yakebiâ? Cikin kuka Halimatu tace âMami kishi ne yarufeni I canât share mijina with anybody wlh, kiyakuri Mom kiyafemin dan Allahâ dan tsukin takaici Mom tayi tace ânaji is not your fault nima daban biyemiki ba nasan waye Riyad, yana tashen samartaka ma beyi neman mata ba sai yanzu, tashi kitafi side naki zansa azo agyara dakinshi lemme handle the situationâ Kama hannun Mom Haleema tayi tace âMom kinsan baya tsallake maganan ki, please kice yayi hakuri karyayi fushi dani koya chanzamin fuskaâ ânaji tafiâ Alkyabban tadauko tasaka tawuce tafita daga side din, Mom itama tafito ta tafi sauro da idanu takira babban bafaden gate din yataho da sauri ya zube yace âan gaida Mai Babban daki matan da darajanta yakaiâŠ..â Mom bata bari ya karasa maganan ba cikin whispering yace âinada aiki for you Sarki baida lafiya bazai iya fitowa ba shine abinda zaka sanar kaida yaranka bansan kowa yasan Sarki bayanan, zakaga babban sakon tukuici kai hakaâ Gyadamata Kai yayi yace âangama me Babban dakiâ juyawa Mom tayi takoma ciki takira Dr su kaman da gaske, kazo gida by 10 duba Riyadâ.
**
1 dot tagama da hospital wanda a outpatient department group nasu yake tareda wani consultant na pediatrics, sheâs happy sosai yanda itada Bilal da crew dinsa na yanmata basa group daya, salla tawuce tafarayi a masallaci sannan ta linke lab coat nata tasa a bagpack tawuce tafito daga mosque din tagoya jakan abaya tasa takalmi tafito Keke napep ta tare zuwa hotel, sauka tayi tabiyashi ta shiga ciki ko kallon receptionist wajen batayiba as usual changing room tawuce tashiga cire kayan jikinta tayi ta saka dark blue dogon wandon da light blue shirt mai botur tundaga kasan rigan har sama wajajen wuya, farin fatan jikinta ya haska kayan sosai kaman dan ita akai uniform din, clean baby hijab nata farı ta dauka ta saka wanda yarufe mata kirji sannan tasa takalminta, fitowa tayi zuwa office din Madam tai knocking akace mata ta shigo, shiga tayi tace âgood afternoonâ âAfternoon Rashida oya ga card din jeki goge office din maza maza, ki dauko kayan gyaran office din a storeâ karban katin tayi tace âokayâ fitowa tayi tawuce store tahada duka abubuwan dazatai amfani dashi sannan tawuce elevator zuwa 5th floor tayi corridor office din, manna katin tayi kofan yayi kara sannan ta tura kofan ahankali hakanan kawai taji gabanta yafadi ga office din yayi mahaukacin sanyi kaman kankara AC a kunne, ahankali ta shiga tareda maida kofan tarufe cikin yar muryanta tace âwayyoo sanyiâ dasauri tawuce wajen kashe AC ta kashe tanabin office din da kallo alamun an shigo dama jiya ance Oga yazo lokacin da zata tafi saisa ya shigo office dinshi kenan, a aljihunta tasa hannu ta zaro yar wayanta ta makala earpiece din a kunnenta ta danna wakan Araina Grande mai suna Into You, sannan takoma wajen kofa tadauko kayan ayyukanta tawuce bayi ta tara ruwa tafara bin wakan tafito tadauki handglove black na aiki tazura a hannu tadauki brush din share kura tafara aikinta tana wakaâŠâŠ
Ko manager shi batasan yana nan ba babu wanda yasani sabida yanda yazo da jallabiya he looks like normal guest yawuce direct elevator, tunda yazo yake kwance dazun nan ne ma ya iya tashi yayi zuhur yakoma ya kwanta though ba bacci yakeba but ya lumshe idanu kawai having moment of peace, tunda aka bude kofan office din aka shigo yaji, sai chan kuma yaji murya mai balaâin zaki tace wayyoo sanyi, saikuma ga same muryan tafara waka tana aikace aikace dake making sound, shi kadai yace âis she some sort of DJ ko wata Artist?â Cus muryanta dadi bata missing ko harafi daya, kaman tana performing a stage, chan kuma kawai saiya tashi zaune sabida ta kunna vacuum cleaner bayajin muryan nata da kyau kaman da, karan vacuum cleaner yafi muryanta kara, ahankali yataso yataka zuwa wajen kofan hannunshi yakai ahankali zai kama handle na kofan yabude kofan sai kawai yaji yafasa cus baimason aganshi amman kuma saiya tsaya chak awajen yanajin the way sheâs singing din cus takashe machine din yanzu tana bin wakan Into your arms na Witty Lowry, God! Her voice is captivating kawai yaji yakasa matsawa.
Daukan bucket na mop din tayi a hannu tarike vacuum cleaner shima a dayan hannun ta tako zuwa gaban dakin sabida tagama da office sai uwardakan before wanke bayuka, juyar da fusknata tayi tana ijiye vacuum cleaner akasa still holding on to the bucket na mop takai free hand din tabude kofan ahankali fuskanta na kallon side din tana rera waka tadawo da hannun tana kokarin daukan vacuum cleaner back danta shigo tunda tabude kofanâŠ
Tunda tabude kofan yayi setting eyes nashi chak akanta yana kallonta tundaga kan pink crocs din dake kafanta dayay finding nasu so funny, dogon dark blue wandonta dabai kamata ba at all kusan ma yaso yamata yawa ya kalla, zuwa navy blue rigan dashi ma bai kamata ba zuwa farin hijab din jikinta that looks extremely neat da side na face nata da he could see sajenta da dan gashinta baki sidik daya leko, daidai tadaga vacuum cleaner ta juyo da kanta kawai taga dogon farin mutum da farin jallabiya ajikinshi ya tsaya chak kaman gunki yazuba hannu a aljihun jallabiyan yana kallonta batada tsoro but saida ta tsorata tayi baya da sauri ganin namiji hakan yasa cord (wayan) vacuum cleaner ya kwasheta jikake timmm tafadi akasa ruwa mopping din hannunta ya kware mata daga ciki zuwa wando, zaro ido tayi atsorace tace âwayyoo Allah naâ tai maza maza ta tashi tama rasa mezatayi arude tace âI am sorryâ ganin kaman ba ghost bane maybe shine me hotel din takai hannu tana kakkabe jikinta da cinyanta da sauri chan ta lura da aljihuta ajike dasauri tace âInnalillahi wayanaâ hannu tasa a aljihun taciro wayanta ta cisge earpiece din tashiga tattaba wayan baya haske tace âinnalillahi Innalillahiâ bude wayan tayi da sauri taciro battery ta huhure wayan sannan tawuce table dagudu ta ijiye wayan awajen danya bushe sannan tajuyo tama kasa kallonshi taduka tana daukan mop tace âsorry i will clean everything yanzuâ chak yake kallonta dan yana ganin full fuskanta ya ganeta the girl from the airport! The feisty gurl! Yarinyar daya dade yana nema to reward her for saving his lifeâŠ.
GOGAN NAMU BATA GANESHI BA? KODAI IDONANEđđ€š
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ2ïžâŁ
Bucket na moping din tadauka da gudu tawuce bathroom na office din ta tara wani ruwa ta taho da sauri jikinta duk rawa yake zata fara mopping ruwan kunfan kasan jikinta duk yana tsiyaya kaman daga sama taji sassanyar muryanshi yace âstop!â Dasauri tadago manyan fararen idanunta ta kalleshi, hada ido tasakeyi dashi for the second time da sauri ta dauke kai aranta tace âsai shegen kallon mata mtswwâ fitowa daga dakin yayi ahankali, cikeda tsantsan kulawa yace âstep asideâ dasauri ta matsa gefe ga mamakinta sai kawai taga ya tsugunna yadauki bucket na mop din ya matsar gefe da vacuum cleaner, yashiga nannade carpet din na tsakiyan office din yadaga yadauka yawuce wajen kofa yabude yafitar dashi ya ijiye bakin kofan nan yashigo yasameta tana kokari fara mopping wajen cikin kwantacciyan murya yace âgo and changeâ dan kallon daga kasan riganta har zuwa crocs na kafanta tayi dake tsiyaya tace âkarka damu I can do it banda wani uniform, zai bushe aiâ yanda take kallon jikinta tana maganan yake kallo with her voice dake piercing kunnuwa sabida dadinsu, calmly yace âgo take them off kisa kayan gidaâ kawai dan tasan office din mai hotel dinnan ne, sannan shita gani cikin offive din so dole tai assuming shine mai hotel din banda haka data gayamai me ruwanshi da yanda zatai aikinta yabarta tayi abinta tagama mana haâa, sai gwadamata yanda zatayi yake, sai kawai tawuce kofa batare datace komiba tana zare handglove din, tabude kofa tafita yabita da kallo kafin kawai yazaga yazauna kan kujeranshi na office yayi shiru.
Changing room dinsu tawuce ta chanza kayan tasaka doguwan rigan atampanta brown ne da milk just straight gown babu wani ado ajiki, dan kwalin kayan ta daura aka sannan ta zari gyalenta brown ta yafa daya kara haskata hasken fatanta yayi bau aciki, ta kwashi kayan bayinsu na staff ta shiga ta dauraye kayan ta wanke cinyanta da kafanta da takalmin tama wanke fuskanta kawai gaba daya hakan yasa tai wani haske mai kyau dinnan na bayan ka wanke fuska, tawuce baya ta shanya kayan sannan tafito tana tafiya da sauri sauri sabida tasamu tai sauran ayyukanta tabar office dinshi, tashiga elevator zuwa 5th floor tawuce office din kofan office din ta bude ahankali tashigo tunda ta bude office din ya kafamata ido, the first time daya ganta uniform ne jikinta, yauma haka yanzu ne yafara ganinta da kayan gida, kasa dauke idanunshi yayi akanta, ta taho direct cikin office din batare data kalli wajen dayake bama, zubamata idanu yayi yana kara tantancewa itace dai wannan mara kunyan ta airport, bai cika manta face ba idan yasan mutum, hade fuska tayi batacemai komiba dan jikinta yabata kallonta ake, tadauki moping stick din tafara moping wajen ahankali tana gamawa tadan juyo ta kalleshi karaf suka dake hada ido dauke kai tayi tace âzan iya shiga dakin na gyaraâ? âYesâ ya amsa calmly hakan yasa kwai ta shiga ta sharo tai arranging bed din dataga baâa gyare ba, ta wanke bathroom din, kusan 5min tayi sannan tafito tawuce bayin nan office ta gyara shi in 3min sannan tafito tai arranging abubuwan datai amfani dasu tafita dasu waje sannan tadawo tazo gaban table dinshi tasa hannunta tana kwasan wayanta na wajen yanabin white long fingers dinta da kallo that looks so feminine, ahankali yace âwat is your name?â Batare data kalleshi ba tace âRashida Almustaphaâ tana maganan tajuya dasauri zata wuce kaman daga sama yace âis your back hurting you naga kin fadi tabayaâ? âNo itâs notâ tabashi amsa atakaice tacigaba da tafiya da sauri bataso yayi wani maganan kuma, hartakai kofa tasa hannu zata bude yace âRasheedahhh!â Wlh batasan meya faru ba hakanan gabanta yafadi chak ta tsaya takasa motsi sabida yanda yakira sunanta, kawai she felt something strange in her dayasa dasauri tajuyo ta kalleshi sake hada ido tayi dashi saikuma ta dauke kai tace ânaâamâ kusan 30secs yayi shiru saichan ahankali yace âThank Youâ Da sauri ta kalleshi zatace thank you for wat saikuma ta tuna maybe na gyaran ne hakan yasa ta gyadamai kai kawai tama kasa magana sabida yanda heart nata yafara racing tajuya tafito dasauri ta kwashi komi tawuce kasa ta maida komi store tawuce taje dakunan dazata chanza duvet nasu takai washing machine takai sannan tahau gyara Allah yasota bata hadu da Madam ba balle ta tambayeta ya akayi tasa kayan gida ba.
Wuraren 6 tafito daga hotel din sai fama take da wayanta dayaki kunnuwa sai cire battery tana maidawa take sabida ya kunnu yaki kunnuwa, ga jakanta goye abayanta. âHi Rashyâ Aisha receptionist dake night zuwanta kenan tai waving nata tana murmushi awkwardly tadaga hannunta saikuma ta maida ta gyada mata kai kawai tawuce tafito waje tana hure huren waya, Munir da Riyad na tsaye awaje wannan karan ya chanza kaya zuwa jumper na milk yadi suna magan kaman daga sama ya hangota tafito tana hura wayanta, yanda hankalinshi da attention nashi yatafi wajenta saida Munir yajuya dasauri dan yaga meyake kallo haka ganin wacce yake kallo wacce kallo daya yamata she looks like worker nasu not guest yasa yace âwho is she?â Batare daya dauke kanshi daga kallonta ba yace âmy saviorâ dasauri Munir yadauke kanshi daga kallonta ya kalleshi dasauri yace âkaman ya your savior?â Yana kallonta yace âthe girl that saved me from those goons a airportâ dasauri Munir yajuya ya kalleta yace âwow the clearner damuka dade muna nema wat a small world ashe anan hotel namu take aiki, but did you tell herâ? Girgixamai kai yayi daidai tasha kwanan layin yadauke kanshi yace âNo bangayamataâ Munir yace âwhy?â mota yashiga yace âbata ganeni baâ tada motan Munir yayi yace âai da saika gayamata, How will you reward her yanzu?â Kai tsaye yace âI will ask her kome takeso arayuwa i will grant her any wish take da shi sheâs part of the reason Iâm alive todayâ murmushi Munir yayi yace âwat got you so angry today?â Yatsine fuska yayi yace âI donât wanna talk about itâ ahankali Munir yace âto mutafi gida? Mom tasa an sanar bakada lafiya just to manage situation din harda kiran Dr, tace na tabbatar mun dawo gida tareâ hannunshi yasa yasauke glass na window ya lumshe idanu bai sake cewa komi ba, ganin baison magana yasa yace âazumi saura 7days fa bakai approving fund na kayan abincin dazaâa rabama al umma da maâaikatan ka baâ dan ijiyan zuciya yayi yace âi forgot bani file din da pen lemme signâ ahankali Munir yace âbari mukai i will give u yana file dake back seat.
JOIN GROUP DANAKE POSTING
SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ3ïžâŁ
Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan.
Tana idarwa cikeda damuwa tace âMama ruwa yashiga wayana taki aiki wlhâ tai maganan tana jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace âgarin yaya meya sameta?â Cikin damuwa tana kara huhhure wayan tace âfaduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har wayanâ dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace âbari mugani kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bakoâ? Gyadama Mama kai tayi tace âbanji ciwo baâ Mama tace âto ai mun gode Allah tashi kiyo wanka kici abinciâ dasauri tace âMama girki kikayiâ? Gyadamata kai tayi tace âeh nayi shinkafa da wake da mai sa yajiâ murmushi tayi tace âMama banace ki dena girki baâ ture mata hanci Mama tayi tace âto banji maganan ki ba Anty Rashidaâ kwashewa da dariya tayi hakan bakaramin dadi yama Mama ba ganinta duk cikin damuwa sabida wayan tasan lissafi take ta yanda zata taba kudin saving dinsu tasai waya dashi kafin takara samin wani kudin fa, rashin lafiyan Mama fa, abinci fa, kudin wuta fa, tasan duk abinda take tunani kenan ganin tayi dariya yasa hankali ta ya kwanta, cikin shagwaba tace âkai Mama nine Anty Rashidaâ Mama ta kama haba tace âyooo ai hakane, Mama karki kaza, karki kaza, kullum command kike bani yarnan kinga ai kinzama Anty Rashidanâ sake bushewa da dariya tayi kawai saita kwanto jikin Mama tace âMama stoppp wlh ni ba Anty Rashida bane, Mama ina hanaki ne fa sabida karki fadi, kinga kinada yawan ganin jiri, kınada migraine kuma, Mama I have to take care of you gwara namiki komi ko ruwan dazakisha na ijiye kusa dake sabida karki wahala wajen daukowaâ tabe baki Mama tayi tadagata daga jikinta tace âjeki wanka kizo kici abinciâ tashi tayi ba musu ta rage kayan jikinta tadaura zani ta kwashe kayan da lab coat da kayan Mama data cire yau dasafe tafito saida ta fara wankesu tsaf ta shanya sannan tawuce bayi tai wanka tadawo Mama tabata abincin ci tayi bawani sosai ba batawani cin abinci abin yabi jikinta sannan takai kwanon waje ta kuskure baki ta dawo tahau salla kusa da Mama tana idarwa ta kwanta awajen ko 2min baâayiba tafara minshari Mama tai shiru tana kallonta sai kawai tasa hannu tadauki feet dinta ta daura kan cinyanta dudda uban tafiya akasa datakeyi bata da kaushi kafanta still looks very fine ga nails dinta farare kal masu kyau, ahankali take massaging kafafun ayanda ta gyara kwanciya kasan tanajin dadin tausan Mama is just looking at her babu salloli biyar dazatayi arana da zatakai goshinta kasa dabazatama Rashida adduâa ba, banda kiyamun Layli datakeyi kullum, kullum adduâan ta shine Allah yakawo ma diyarta karshen wahalan nan Rashida ita ke ciyar da ita, itace cinta shanta suturanta magungunanta da komi na rayuwan su Rashida ke nema, babu yanda zatayi ne dan batama da karfin aikin ne da itace zata fita ta nemawa diyarta abinci da komi ba diyarta tayi ba, kullum adduâan ta is Allah ya tsare yarinyar ya tsare imaninta kar wata rana tagaji da aikin wahalan nan tace zata shiga duniya tabi maza dan shine hanya mafi sauki da akebi asami kudi, adduâanta koda yaushe shine Allah yabata ikon kammala wannan karatun likitan, kowani shekara da hayya hayya take tara kudin school fees nata na last year bai musu wani wahala ba sabida tasami aikin hotel din nan ana biyan ta dubu 50k duk wata a nan ta tattara tabiya, fatanta shine Allah sa wannan shekaran na biyar kar kudin makarantan yayi yawa dubada yanda aka kakkara kudin makarantu, hawaye ta share ahankali daya zubo mata bata taba sanin dan Uwanta na jini zai iya juya mata bayaba sabida wannan cutan dudda da ranshi da lafiyanshi, bata da kowa sai Rashida, yau shekaru ashirin da uku kenan tana wannan wahalan tun Rashida na cikinta, ta haifo yarinya cikin wahala ta tashi cikin wahala sannan itama tana rayuwan wahala, batabama yarta komiba sai wahala, babu wanda ya yarda ya auri Rashida, ga yanda yar karaman yarinya ke aiki kaman namiji wata kalan uwace ita, hawaye ne suka kara zubo mata sai kawai ta jinginar da kanyon a bango takalli sama murya chan kasa that is very weak tace âYa Allah idan mutuwata shine mafi alkhairi agareni dakuma yâata, idan mutuwata zai cireta daga cikin wahalan nan datake ciki Allah ka kasheni, ka aurar da Rashida gidan dazata huta, karufama Rashida asiri, ka lullubeta cikin nimarka Ya Allah.
Tadade ahaka yawanci tana boyema Rashida damuwanta da dama sabida kar yarinyar takasa karatu idan kanaso kaga Rashida ta birkice tarasa sukuni to Mama tace kaza namata ciwo tuni yarinyar zata rude, damuwa, tunani ga constant ciwon kai koda yaushe shiyafi damunta, saisa kullum tane asibiti BP ta is high, magungunan BP nema ke cinye musu kudi cus maganin HIV free ake bata a clinic dinsu.
Ganin yanda bacci ya shigeta yasa bata tadataba tabarta tai baccin anan kan dadduma.
Wuraren 5 Mama ta tadata da kyar ta tashi wanda hakan daman is daily battle nasu, gyaran gidan tayı tasa takai Mama tai wanka tai salla tazo ta dumama shinkafa da waken sannan tama Mama tuwo sunada miya daman kafin ta shirya cikin bakin abaya da stones nashi yagama fita tass but dudda haka ya mugun mata kyau abunka da fara tazo taje wajen wayanta taciro daga shinkafan tasa battery ta kunna amman still yaki kawowa Mama tace âbai kawo ba?â Gyadama Mama Kai tayi ahankali, dasauri Mama tazo karban wayan tayi tace âkodai ba chaji neâ tawuce wajen chazanta dake bango ta makala kusan 3min bai dauka ba, ahankali Mama ta tashi tace âbari nabaki dubu talatin din nan saiki sayo wata wayan kawaiâ dasauri tace âaâa Mama ki adana talatin din nan, bari zan kaita wajen yan waya a gyaramin zasu iya gyaraminâ badan Mama taso ba dan wayan tariga tagama tsufa dukta farfashe tace âto shikenan bari na baki kudin gyaranâ sip tabude taciro wani leda ta kirgo 5k tabata karba tayi sannan tayafa gyalenta tace âbye Mamaâ har zaure Mama tarakota tace âadawo lpyâ dayake 9 ake fara clinic dinsu hakan yasa taje shagon Maman kuwa tayi aiki ta karbi 2k dinta sannan tawuce shan wajen gyara takai wayan ganin zai dauki lokaci tace âzata dawo da yammaâ tashiga keke sai hospital nasu.
sheâs not really doing much a consulting room take zama attached to consultant din da aka assigning nata to him yana duba yara marasa lafiya yana tambayanta me aganinta take tunanin is diagnosis din tafadi, kokuma yace wani investigation yakamata ayima yaron tafado sunayen series of test da zaâayi ganin how brilliant d girl is tsohon likitan yace âi will comfortably leave the office for you tommorowâ gyadamai kai tayi dan she hardly smile outside, haka dai tagama by 1 tawuce mosque tai salla ta linke labcoat tasa a bag sannan tafito tashiga keke sai hotel.
Yau tadanyi latti sabida traffic sai around 2:30 tashigo hotel din ko kallon mutanen dake reception da lobby gabaki daya batayi ba da sauri sauri tawuce changing room nasu kofa tabude ahankali, maâaikatan su tagani gudu uku a lobby suna chanza kaya da kallo suka bita batace musu kala ba tawuce locker dinta tasa password dinta tabude, daya daga cikinsu ne taja tsaki tace âmutum sai fadin dai, nagadai da mutum dan wani ne dabaizo hotel neman aikin shara da wanke bayi ba, tundadai duk ansan juna menene na jijji dakai kaman diyar wasuâ ? Sauran biyun ne suka kwashe da dariya daya tace âdadine dake Hussy baki hadiye abu acikiâ parking gashinta tashiga yi da ribbon tace âeh mana kullum fuskan mutum amurtuke ana fadin rai ana daga shoulder kaman yar shugaban kasa amman shine akazo aikin wanke bayi a hotelâ wani irin buga marfin locker Rashida tayi saida yayi kara pammm!Tajuyo tai facing Hussy direct cikin zafin rai tace âdani kike maganganun nan?â Wani banzan shakiyin kallo Hussy tamata dan tadade tanajin haushin Rashida wai ace maâaikata nawa a hotel din nan yarinya bata kula kowa, kuma kai kasauke kanka ka kulata taki kulaka back, bama wannan yafi bata mata rai ba yanda take nuna bamatasan anyi hallita irinsu a wajen ba ko ka kulata ita bazata kulakaba sai bakin taurin kai, jibidai yanzu datazo tasamesu ko Hi bazata iya gayamusu ba? Amman basu isheta kallo ba, cikeda tsana tace ânaga dai ban kira suna ba, amman duk wanda ya tsargu dashi nakeâ wani irin kallo Rashida tamata kaman taci ubanta saikuma ta tuna nan wajen aikin tane, da kudin aikin wajen nan zata biya school fees and other things bari kawai ta barta today is her lucky day, sai kawai tajuya tasa hannu zata dauki uniform nata batare data kara magana ba, cikeda neman fada Hussy tai wani shewa tace âjakan ta tsorataâ juyowa Rashida tayi da mugun zafin rai batai wata wata ba ta fizgo gaban rigan Hussy ta kifa mata mari a fuska ihu jikake tasss! Hussy tayi ihu ta chakume gaban rigan Rashida tace ni kika maraâ? Sai dambe, dukanta Rashida take bana wasaba har gyalenta na fadi kasa bakin gashinta datai parking donut mai balaâin kyau ya bayyana, sauran yammatan biyu na kallo sunajin dadi ganin suna dakan juna dudda Rashida nacin uban Hussy amman kallon fada da dadi yake sukaki rabasu, ganin jini Rashida tafasa bakin Hussy yasa daya cikinsu ta tsorata tace âbaruwana kar ayi kisan kai agabanaâ dasauri tabude kofa tafita da gudu dayan ma tabiyota hango Madam sukayi a lobby tana magana da receptionist kafin sukai wajen ma sukai ihu. âMadam ana fadaâ daidai lokacin Munir da Riyad na shigowa yana shaye da brown jumper yasa brown shade a idanunshi na CK dayamai kyau sosai, arude dayan tace âMa come oo harda blood everywhere!â ganin Riyad yasa Madam tace âSir welcome wai ana fada I donât even know with who lemme handle itâ tawuce jin yasa Munir yace âletâs interveneâ Munir yayi gaba Riyad yabiyosu abaya yana tafiya one one a kasaitance, da gudu Madam ta shiga dakin tai ihu âwhat is thisâ? Ganin blood har wuyan Hussy, Rashida bama tasan an shigo bama Munir yashigo dakin daidai Riyad na isowa chak ya tsaya wajen kofan batare daya shigo ciki ba yana kallon su, jan Rashida Madam ta shigayi da karfi gaske ganin yanda take dukan Hussy, sauran yan aikin suna banbare hannunta daga jikin Hussy sunajan Hussy da bakinta yayi jina jina da jini harda hanci baya suka kwasheta da kyar daga hannun Rashida, Madam data rike Rashida cikin tsananin bacin rai tace âfighting awajen aiki are you too Mad? Rashida wat is this why did you beat her up like this?â Itafa idan tana fushi bata gane kowa, kabar da hannun Madam tayi daga jikinta a haukace kaman ba Rashida ba cus ranta yabaci tace âdalla sakeni kekuma Malamaâ tajuya zata closet nata cikeda taurin kai duka maâaikatan har Munir saida yakalli Rashida yasake kara kallonta jin abinda ta gayama Madam, Hussy dake haki an riketa tace âMa kinga halinta ko saisa all worker ke cemata psycho, kolomental ce wlh, mahaukaciya ce very weird girl, shegiya yar shaye shaye, an gayamiki bamusan asalinki bane, uwarta nada HIV!â Chak Rashida dake tafiya ta tsaya kaman kankara, ihu Hussy tayi ganin ta tsaya chak da tafiyan datakeyi that means maganan ya shigeta tace âai duk munsan sirrin ta Ma, harnan akazo tundaga layinsu aka gayamana we should be careful with her tanada HIV Mamanta ma nadashi, bamu gayamiki ba Madam sabida karki koreta cus munsan she needs this job for her virus drugs da Mamanta, amman shine zata kama dukana ba ban mata komiba bayan tanada wacce tafi chanchanta adaka islamically agida, diyar fasika kawai!â Wani irin juyowa da Rashida tayi zaka dauka zakanya ce ta taho da gudu tareta Madam tayi tace âwhere do you think youâre goingâ wani irin hankada Madam Rashida tayi saida Munir yatare Madan da sauri dan inda tafadi wlh saita karye, Hussy na ganin haka ta wuce da gudu tabi gefen Riyad ta gudu tafice da gudu Rashida ta taho itama tsabagen fushi ko ganin gabanta batayi ahankali Riyad yadaga kafanshi yashigo ya tare kofan yayi blocking nata, hakan yasa ta dago jajayen idanunta takalleshi adake cikin tsananin fushi da zuciya tace âka tashin mini daga hanyaâ Madam da Munir ya daga kyar tace âit seems da gaske yarinyar nan is mad, call security namu and call the policeâ yana kallonta ta glass batare daya dauke idanunshi daga kallonta ba yace âdonât call anybodyâ cikin kumfan zuciya kaman zata fashe tai wani irin ihu tace ânace ka tashinmini daga hanyaâ strictly yace âyouâre not going anywhere!â Wlh ayanda zuciya ke daukanta kaman ta dagashi ta yar takeji kawai tasan batada karfin ne, yanda hannayenta ke rawa da jikinta yasa kawai ta juya fuuuu tawuce dan bence din dake wajen ta zauna tai folding hands dinta akirji duk yan dakin kallonta suke sheâs shaking, sai alokacin yakalli Munir yace âget first aid box go and attend to that girl, yakalli Madam da sauran yar aikin dake kallon Rashida da mamaki kaman yau suka fara ganinta yace âku wuce kutafiâ cikeda mamaki Madam tana kallonta tace âthis is your last day hereâ duk wucewa sukayi suka fita yarage Riyad kadai dake tsaye awajen kofan dan kwalinta dake kasan dakin ya kalla ahankali ya shigo ya duka gently yadauka dusting nashi yayi sannan yataho inda take zaune kanta akasa tayi folding hands a kirji ahankali ya yafa gyalen akanta.
Dago kanta tayi tazubamai jajayen rinannun idanunta yanda yara masu taurin kan nan sukeyi tace âina ruwanka dani? Wayace katabamin gyale na? Wat is your business with me? Nabar aikin naku dagayau nima, bazan kara aiki inda wata ta kira MamanaâŠâŠ.â Saita kasa karasa maganan sabida yanda abin ya tsayamata awuya saikawai tajuya mai baya da sauri takai hannunta ta sharce hawayen daya soma zubomata, data sharce da wani yasake zubowa sunki tsayawa yakai almost 1min yana kallonta sannan yajuya ahankali yafice tareda maida kofan yarufe kaman jira take fashewa tayi da kuka haryafara tafiya yajuyo sautin kukanta chak ya tsaya har shesheka takeyi yakai kusan 1min ahaka sannan yabar wajen, kusan 5min tayi tana kuka sannan ta goge fuskanta tass ta tashi tawuce drawer ta ta shiga kwashe yan small small tarakacen datake dashi awajen uniform nasu tabar musu sannan ta goya jakan abaya ta tsaya takara goge fuskanta tass bazaka gane tai kuka ba unless u look into her eyes tafito sai kallonta ake a reception amman ko kallonsu batayiba ta wuce tafita ta tafiyanta gida.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ4ïžâŁ
Wuraren 3 Mama na zaune tsakar gida tana gyaran shinkafa ta kunna radio ta ijiye gefenta saman tabarma tana sauraro taji an turo kofa an shigo hakan yasa ta kafa ido taga wazai shigo bakuwa tayine saitaga Rashida sosai gabanta yafadi ganinta cus bata taba ganin Rashida ta shigo gida around this time ba, kallo daya ta mata tagane tai kuka dawuya ne Rashida tama wani abu tai kuka, ita kadai ke iyasa yarta kuka dasauri ta ijiye tray shinkafan tace âlafiya menene kika dawo dawuri haka?â Murmushi ta kakalo tace âMama kaina ke ciwo sosai saisa nadawoâ tai maganan tana zama kusada Mama kanta Mama ta taba tace âbari na kawo miki vitamin C kisha tashi ki cire jallabiyan kisha iskaâ tashi tayi tawuce ciki Mama tabi jakanta dayay strange girma da kallo sai kawai ta jawo tabude ganin karikitan ta ne ciki yasa da sauri ta tashi tabita daki tana tsugunne gaban ganamasgo tana neman kaya Mama tace âan koreki wajen aiki neâ? Dago kanta tayi ta kalli Mama zatai magana Mama tace âkarki kuskura kimin karya an koreki daga wajen aiki ne?â Ahankali tace âMadam dina tace yau ne last day na aiki na a hotel dinsuâ waje Mama tasamu dasauri ta zauna jin jiri zai dibeta tace âMeya faru tell me everythingâ Mama tariga ta ganota hakan yasa tafadima Mama komi ba karya, ba karamin baci ran Mama yayi ba tace âsau nawa zan gayamiki ki dinga hakuri arayuwa Rashida eh? Zagi na kari ne? Koko zagi na nunawa ajiki ne? Dan an zageni sai meneâ dasauri Rashida ta kalli Mama, Mama tace âyes dan wata ta zageni and so wat dazaki hau fada awajen aikin ki kina hankade Madam dinki har sau biyu mai hotel din gabaki dayama shima kinmai rashin kunyaâ ahankali takai hannu ta goge hawaye tace âMama bazan iya daurewa azageki agabana ba ko ace wani abu mara kyau wlhâ saikuma tarushe da kuka tace ânarasa me nayima yan layin nan duk inda nake aiki sai sunsan yanda sukayi sukaje suka batani su fallasani, wlh kowaye meyi ban yafemai baâ tabama Mama tausayi amman kawai saita wuce tabude drawer tadauko hijabinta har kasa ta saka da sauri Rashida ta mike tace âMama ina zaki?â Cikin dan masifa tace âina zani? Ina kuwa zani inba wajen aikin naki ba naje nabada hakuri itama yarinyar a nunamin gidansu naje nabada hakuri, idan babu aikin nan tayaya zaki gama makarantan ki eh? Me zamuci? Dame zaki sami kudin siyan tufafi? Ga wayanki ta lalace baki dawo da itabama that means bata gyaruba duk ina zamu samu kudin nan kafin kisami aikin nan kin manta kalan wahalan dakikayi eh? To zuwa zanyi nabada hakuriâ dasauri ta taho takama bakin hijabinta tace âMama dan Allah dan Allah karkije kinji Mamaâ fizge hijabinta Mama tayi tace âinda bakiso kisani naje nabada hakuri ai da bakiyi abinda zai tursasani inje ba, yau ko basu karbeki ba dolena naje na bada hakurin abinda kikayi kinma mutanen dake gaba dake reni sannan kin fasama yar mutane hanci da bakiâ baki Rashida tabude zatai magana Mama ta nunata da hannu tace âkimin shiru ananâ ta fiziÄe hijabinta tajuya tafita fuu Rashida nada zuciya so tasan yarinyar didnât even realize how important this work is to them most especially towards karatun ta she will do everything ta tabbatar Rashida tagama karatun ta lafiya.
Kafa Mama tasa ahanya tana tafiya ahankali kanta na sarawa amman ta daure cus she knows what school din Rasheeda means to her, she will not allow her to sabotage mean na school fees payment nata ba, she just hopes darajanta zaisa sumata afuwa.
Tanakai junction ta tare keke da taso taje da kafa ne, amman taji jiri na dibanta bazata iyaba, har hotel din aka kaita ta sauko tabiya kudin tajuya ta kalli tamkeken hotel din almost duka inda Rashida take aiki ta sani musamman take binta dan tasan inda diyarta ke aiki incase wani abu yafaru she knows inda zataje neman diyarta amman bata taba shiga wajajen aikinta ba, ijiyan zuciya ta sauke jin yanda heart nata ke beating saita dan natsu kafin ta shiga building din motoci cike anyi parking, hotel din yahadu bana wasaba, karasawa tayi zuwa entrance door din zata shiga from yanda take looking security guard dake gadon kofan shiga reception din yace âHajiya wakike nema? Idan zancen taimakone Oga yace jibi ranan jumaâa zaâayi rabon abincin azumi you can come by 10AMâ ahankali Mama tanuna kanta tace ânine Maman Rashida sannunku da aiki, Rashida na aiki anan maybe kasanta, to tayi laifi ne shine nace bari nazo nabawa Oganta hakuri dan Allah akomar da ita sannan nabama yarinyar hakuriâ kallon Mama sukayi sannan suka kalli juna kafin daya ya nuna mata kujera dake chan gefe wani plastic chair yace âguest da maâaikata kadai ke shiga ciki jeki zauna achan Oga nada baki amman zai fito anjima kadan sai a gayamaiâ Mama batai musu ba tace âtohâ wucewa tayi zuwa kujeran dasuka nuna mata ta zauna tabuga tagumi tai shiru burinta kawai karsu kori Rashida adduâanta kenan, gabanta sai faduwa yake cikeda fargaba.
Tunda yaje office nashi yayi shiru bakin dasukayi ma yawanci Munir ke kulasu, agogon hannunshi kiran Rolex ya kalla 5 tayi na yamma kaman an tsikaresh ya mike duk kallonshi sukayi âexcuse meâ yafadi tareda wucewa wajen kofa yafice Munir yabishi da kallo kafin yacigaba da abinda yake samin kanshi yayida shiga elevator ya sauka kasa, he doesnât even know why heâs doing this but samun kanshi yayi da zuwa hanyar changing room din ganin kofan wangale abude yasa yadan leka ciki babu kowa wajen fuzar da iska yayi yajuyo yafito daidai Madam zata shigo hanyar chak ta tsaya ganinshi surprisingly tace âYallabai wani abu kake bukataâ? Kaman bazaiyi magana ba saikuma yace âwhere is sheâ? Kallon hanyan Madam tayi tace âwa she? Oh mahaukaciyan nanâ? Dan lumshe idanu kadan yayi hakanan yaji kalman azuciyanshi yadai daure bai nuna wani abuba ya kalleta, dasauri tace âta tatare kayanta ta kwashe komi na locker ta tatafi tabar aikin da kanta kafin mu mata official koraâ yanda taga yahade fuska yasa dasauri tace âsorrâŠ.â Ahankali yace âsack the other gurl HusâŠ.â Cikeda Mamaki Madam tace âHussyn Yallabaiâ? Babu wasa akan fuskarshi yace âI donât want her working for my company, just compensate for the injury, give the other gurl a call tadawo aikiâ yana maganan yawuce baki Madam yakasa kulluwa tana kallonshi, yarinyar data barar da ita yake cewa akirata back, wacce aka jibga yayi sacking, dan ijiyan zuciya tasauke aranta tace âhis company his rule!â Tawuce ta tafi office nata.
Wucewa kawai yayi yabar wajen yafito, security daya budema wani guest kofa dazai shigo ne ya hango yallabai hakan yasa yashigo ciki da gudu daidai zai shiga elevator yace âYallabai barka da hutawa dama wata mata ke nemanka awajeâ wani kallo Riyad yamai irin wata wa? Shi kuwa? Dasauri security yace âtace wai itace Maman yarinyar da aka kora tazo tabada hakuri tana waje, sheâs Rashidaâs Mom Sirâ hakanan Riyad kawai yaji gabanshi yafadi but yadaure yace âwhy is she sitting outside?â Dan sauke kanshi kasa Security yayi yace âuhmm Yallabai cewa akayi cutan kanjâŠâŠâ fuuu Riyad yawuce zuwa entrance door din kafinma abudemai kofan dayake glass door ne yana iya hangota yanda tazauna kan kujera tayi tagumi tana kallon waje daya cikeda tsananin damuwa and kana kallon matan kasan sheâs really sick she looks so skinny and pale jiyayi zuciyanshi yamai ba dadi sosai yanda security sukai trashing nata awaje haka, dasauri yafice bayan an budemai kofan yayi wajenta direct yana zuwa kawai saiya duka cus bemasan mezaiyi ba, sheâs the mother of the girl that save his life kome yayi bai biyataba, cikeda girmamawa yace âMamaâ firgigit Mama tadawo daga dogon tunani datake tajuyo ta kalleshi, dasauri tace âNaam Bawan Allah kaina mai wajen nan nazo nabada hakâŠ..â kafin takarasa maganan dasauri yace âMamaâ hakanan Mama taji yanda yakirata yataba zuciyanta, yanda yakira sunnan just touched so many things a zuciyanta kawai sai hawaye, life and sickness nata have made her so emotional, muryanta na rawa tace âdan Allah dan Allah kuya kuri nasan Rashida da zafin zuciya ga fada ga taurin kai, kome akace tama yarnyar nan nasan tayi dan Allah kuyakuri kurufamin asiri kada ku koreta daga aikin nan dan Allah ku taimakeniâ tai maganan tana jan kujeran baya zata duka dasauri Riyad yakama knees nata ahankali yace âMama dan Allah karki rokeni, ban koreta ba zata iya cigaba da zuwa aikiâ da sauri Mama ta kalli fuskanshi tace âda gaske?â Gyadamata kai yayi yace âehâ ijiyan zuciya Mama ta sauke tace âto inane gidansu yarinyar naje na bada hakuriâ ahankali yana sakin knees nata yace âbasai kin bada ba lafiyanta kalau Mama, is just normal misunderstanding da kananun maganan yara yajawo fadan kada ki damu kinjiâ gyadamai kai tayi tace âAllah maka albarkaâ murmushi yamata kadan baice komiba, Mama tace âbari natafi gida to Alhamdulillah nagode nagode nagode kajiâ daga yanda take maganan kasan hankalinta ya kwanta gyadamata kai yayi, Mama tace âto sai an jimaâ âsaida safe Mamaâ yafadi ahankali, Mama ta wuce cike da farin ciki tafara tafiya kadan kadan sabida yanda kanta ke sarawa, tayi tafiya daya biyu uku ana hudu kawai ta yanke jiki tafadi, Riyad na tsaye yanama security magana sukaji karan fadin abu juyowa sukayi ganin Mama yasa dawani irin gudu Riyad yayi wajenta suma security din haka dago kanta yayi yana tapping hannunta yana kiranta. âMama Mama Mamaâ amman shiru dasauri yace âhelp meâ daukanta sukayi yabude bayan motanshi yasata yakoma yashiga gaba yatada motar sai wani babban private hospital dayake zuwa anytime yake Kano yana zuwa aka karbi Mama sai emergency yawuce office na Dr dinshi ya shiga Dr ya sallami patient dayake tareda shi yace âRanka shi dade mai Martabaâ dan yatsine fuska yayi yace âdonât call me that I have a patient tana Emergency I want you to be on her case fastâ tashi Dr yayi suka fito tare ya shiga emergency din, shi ya tsaya agaban wajen yarasa yanda zaiyi sai kuma yakoma office na Dr ya zauna, yana nan zaune yana jiranshi har aka kira magrib saiya tashi yafito yawuce mosque yana gani Munir na kiranshi yaki dauka salla yayi yafito yawuce ciki yakoma office na Dr yazauna sai gashi Dr yashigo dasauri Riyad yatashi yace âhow is she ta farfado?â Gyadamai kai Dr yayi yace âda kyar muka samu ta farfado amman tana bacciâ saikuma ya zauna ya kalli Riyad yace âkasan wacce ka kawo? Who is she to you?â Batare daya amsashi ba yace âdoes that matter? Meke damunta? How can I help?â Gyara zama Dr yayi yace âsheâs HIV patient!â Yayi maganan yana kallon fuskan Riyad dayaga bai chanza ba saima yace âme da me take bukata yanzuâ? Ahankali Dr yace âis like sheâs on medication so bahsine abinda ke damunta ba bashine kuma dalilin yankewan jikinta tafadi ba, abinda yafi komi damunta is BP, BP ta yayi raising sama sosai I donât think zan sallameta yau ko gobe ko jibi ma sef, sai ya sauko sannan zan sallameta, just get wanda zai zauna da ita and then drugsâ yashiga rubuce rubuce duk Riyad na kallonshi saida yagama komi sannan yanunamai takardan, tashi Riyad yayi yazaro wallet dinshi ya ijiye akan table din cikeda izza yace âtake any amount kake bukata for drugs, bills, pin is 6648â yana maganan yawuce yafita akasaitance yasauka kasa dakin dayaga an shiga da ita yawuce shiga yayi ahankali ya tsaya bakin gadon an cire hijabinta daga ita sai riga da zani da hulan dake kanta an samata drip, shiru yayi yana kallonta sannan yajuya yafice daga dakin yawuce yaje motanshi yashiga yadau wayanshi yana shirin kiran Munir wayanshi yashiga ringing Munir dinne yana dagawa kafin yayi magana yace âMunir open file na employees dina a desktop get info na Rashida I need address nata ASAPâ kafin yayi magana ya katse wayan yayi shiru chan saiga Munir din yakira yace âsuna Ranji, wajen tudun Murtalaâ baimasan inane wajen ba but haka ya katse wayan ya kunna google map yashiga drivingâŠ.
Tunda tai magrib ta zauna tai shiru tana mamakin ina mama taje harta dau hijabi kota bita hotel dinne ko wani case dinne akeyi achan but karta kara bata ran Mama taje wajen hakan yasa ta daure ta hakura, kuma zai iya yuwa tadawo takai karanta wajen Baba liman ne dantana haka wani zubin hakan yasa ta zauna adaki zugum kaman wata marainiya idan aka kira ishaâi bata dawo ba zatasa Hijabi taje ta nemetaâŠ.
Shigowa layin yayi ga majalissar maza gaban shaguna ana zance rage wutan motan yayi karya haskosu yana karasowa yakashe motan kawai ya bude ya sauko yazo wajen yamika musu hannu yace âAssalamu Alaykumâ atare duk suka amsashi suna karban hannunshi ganin arniyan motan dayake ja, yace âdan Allah tambaya nakeâ dasauri sukace âAllah sa mun saniâ anatse yace âgidansu Rashida nake nemaâ tsit wajen sukayi kaman ba su ba saikuma daya daga cikin samarin yatashi yace âbismillah yallabai zomu kebe manaâ binshi Riyad yayi sujkaje wajen mota kaman mutumin arziki yace ânasan ba laifinka bane Rashida kam nada kyau Masha Allah yarinya kaman Balarabiya amma dai kyan dan maciji ne, yanda muke gayamaka dinnan haka muke gayama duk wani saurayi dazaice zaizo nemanta hakkinmu ne na yan unguwa, hakkin makotaka tunda su basu fadin gaskiyaâ tunda yafara magana Riyad yaji ranshi na baci amman ya daure dan he wants the address, mutumin yace âkagadai uwar yarinyar nan fasika ce garin kwashe kasheta ta kwaso kanjamau Rashidan ma muna kyautata zato tanada shi tun acikinta tasamâŠ.â âZaka fadamin adreshin ko bazaka fadi baâ? Riyad tafadi sounding bitter and angry baki mutumin yabude zaiyi magana Adamu mai chemist da tun zuwan Riyad ya hangoshi daga chemist yace âkaje chan kasan layi zakaga gida mai jan kofa nan ne gidansu Rashidaâ kallonshi Riyad yayi yace âthank youâ yawuce yakoma mota yatada mota yabar wajen, gaban gida mai red door yayi parking ya sauka ya tsaya gaban kofan yakai hannu yayi knocking, Rashida na zaune kan dadduma taji ana knocking hakan yasa ta tashi dasauri batare data cire pink hijab dinta ba tafito silipas ta zura gabanta sai faduwa yake ta taho zaure tana mamaki Mama ta kulle kofan ne dazu dan idan aka rufe yana shiga jam, ganin kofan abude ga wani arnen black car parked agaban gidansu wani mutumi a tsaye yajuyama kofan baya so bata ganin fuskanshi yasa ta fito kai tsaye cikin muryanta mai balaâin dadi tace tace âkaine kai knocking wa kake nema?â Har cikin zuciyanshi yaji sanyin muryanta hakanan, cikeda wani irin kwarjini yajuyo yana zuba hannun cikin aljihun rigan dake jikinshi, hada ido sukayi ta kalleshi ido cikin ido dan akwai wuta a kofar gidansu mamaki da tunani yacika kanta, ba mutumin nan bane mai hotel dinda take aiki ba? Ko idanunta gizo yake mata? How is he agidan su? Ganin ya tsaya yana kallonta bayako kyafta ido yasa tadan dauke kai tattare bakin hijabinta tashigayi tana tabawa saikuma takai hijabin bakinta, saichan tacire, saikuma chan ciki ciki kaman an sata dole ahankali tace âina yiniâ heâs looking at her mostly sabida baisan mezai fada mata ba, chan yace âMama wants to see youâ hakanan gabanta yayi balaâin fadi dasauri ta kalleshi baki tabude zatai magana saita kasa sabida yanda kirjinta ke bugawa da gudu da sauri sai kawai ta tsugunna, wani irin tausayi yaji tabashi yakasa cemata komi, da kyar kusan 30sec sannna ta mike jin tadawo daidai cikeda karfin hali tace âina Mama wat happened to her? Nace mata kartazo tabada hakuri but taki jina, normal Mama da tuni tadawo, tana ina yanzu? Just tell me wat happened to my mother mekuka mata? Me kuka gaya mata? My Mom is very sick, tell me tana ina yanzu?â Tai maganan hawaye na cika idanunta harwani kyalli suke adake still kallonta yake yace âsheâs fine now but tana hospitalâ hannuwanta biyu ta daura a fuska saikuma ta juya takai hijabinta ta goge fuskanta tass tajuyo ta kalleshi da jajayen idanun hijabinta daya jike da kuka ya kalla sannan yakalleta, cikeda dauriya da karfin hali tace âinane asibitin bani address din natafiâ batare dayay magana ba yajuya yace âget few things da Mama zata bukata lock the house I will take you there is late bazakije da kanki baâ yayi maganan authoritatively yawuce yabude motan ya shiga gaba, kallonshi tayi sai hawaye sai kawai tajuya takoma cikin gida, drawer tabude takwaso simple t-shirt tasa ajaka tadaga kayansu ta dauko ledan duka kudin dasuke ijiya 139k, tadauki dadduma da zanin gado wankakke tasa ajakan bayanta takashe wuta tafito sai goge hawayenta take tarufo kofan waje tasa key sannan tajuyo ta kalli motan, bata taba shiga mota babba haka ba, ahankali yakawo hannunshi yabude kofan ganin yanda take kallon motan kaman matsoraciya, daurewa tayi ta matso ta shigo ta zauna agaban ta maida kofan tarufe wani sanyi da kamshi na dukanta ta rungume jakan a hannunta gam.
Tada motan yayi ahankali sannan yafara tafiya bini bini tajuyar da kanta takalli gefen window tana goge fuska, sunyi tafiya na kusan 30min sannan sukakai asibitin da saida ta firgita ganin kyanshi dan tasan zaiyi tsada tayaya zata biya kudin?
Parking motan yayi yafito, kokarin bude kofanta tashigayi tafito takasa, cus ba irin normal kofan mota data saba dashi bane, abinma yana nema yakarasata kuka ta daure ganinshi ya zagayo ta inda take yana kallonta ta glass dan wannan motan ba tinted bane, bude mata kofan tayi da sauri ta sauko batare data kalleshi ba ta tsaya gefenshi dan nesa dashi maida kofan yayi yarufe sannan yafara tafiya tabiyoshi abaya da saurinta suka shigo cikin hospital din har zuwa dakin da Mama take kwance kafinma yasa hannu yabude kofan da sauri tasha gabanshi ta rigashi tura kofan tashiga ta tsaya chak tana kallon Mama dake bacci an samata ruwa an makala mata wasu abubuwa a hannu yarda jakan dake hannunta tayi awajen tawuce dakin da gudu taje inda Mama take kawai ta kwanta jikin Mama ta manna fuskanta akan wuyanta tana kuka sosai wanda babu kara idanba ka kalli kakkarwan da jikinta keyiba bazaka gane kuka takeyiba, ahankali yaduka yadauki jakanta yashigo dakin yakawo gefen gadon ya ijiye saikuma ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallonsu, takai 3min ahaka sannan ta taso da sauri ta dauki Dr note dake saman table na gadon ta shiga karance karance magungunan da alluran dake wajen ta shiga duddubawa tana karantawa har drip din da aka samata sannan ta sauke ijiyan zuciya tasake zama bakin gadon takama hannun Mama tarike gam tana kallonta, kawai kana ganin Rashida kasan yanda takeson Mamanta, ta dade ahaka tana kankame da hannun Mama sannan tasaki hannun takai hannayenta ta share fuskanta tajuyo tareda tashi tsaye ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta dauke kai cikin muryanta dahar ya chanza sauti sabida kuka tace ânawa ka kashe nabiyaka inaso akira Dr ya sallameta na nemo keke napep nakaita chan asibitin datake amfani dashiâ yana kallonta right in the eye yace âwhich hospitalâ? Ahankali tace âteaching hospitalâ kai tsaye cikeda izza da iko kaman Mamarsa yace âkibarta ananâ da sauri ta kalleshi sake hada ido sukayi cikin konewan idanu Rashida tace âwannan kuma nice next of kin nata i decide and make decision for my Mom not you, nawa nidai ka kasheâ yadade yana kallonta baitaba ganin feisty mara kunyan yarinya irin this girl ba, yana kallonta yace âidan Dr yazo ki tambayeshiâ yajuya zai wuce tace âeh zan tambaya and i will pay you back cus banson any favor ko taimako from anybody zan kawoma kudinkaâ dan jimm yayi sai kawai yabude kofan yafita, mota yawuce yashiga yatada yayi dialing number Dr yana dagawa yace âDr on no condition zakai releasing that patient without letting me know, donât let the Daughter take her to another hospital, sign them up for abinciâ cikeda girmamawa yace âto Ranka shi dadeâ dan yatsine fuska yayi ahankali yace âand about that!â Yadanyi shiru chan yace âdonât disclose my identity to anyone nor address me ahaka in front of anybodyâ Dr yace âshikenan RiyâŠ.â Harya katse wayan ya balaâin gaji hotel yakoma ya kashe mota ya sauke ya shiga ciki ana gaidashi ko amsasu baiyiba yawuce office nashi straight yana budewa ya shige ganin desktop a kunne yasan Munir na ciki, hakan yasa yawuce ciki Munir na kwance yana buga game a tv dagashi sai singlet da 3quater ganinshi yasa ya ijiye remote yataso yace âance Maman yarinyar tazo and she fainted kasata a mota hospital ka kaitaâ yana cire riga yace âehâ tsayawa Munir yayi yana kallonshi yace âI know the girl itace wacce saved you but are you sure zaka barta tacigaba da aiki kai the girl have quiet a temperâ batare daya amsashi ba kawai yawuce yafada bayi wanka yayo yafito daure da towel a waist turaruka ya tsaya ya fesa sannan yazo yazauna, Munir tace âMom takirani yafi sau goma nace mata we are not together tace she will call back in the next 5mins idan ban hadata dakai ba zata kai karana wajen Ammiâ Shiru yasakeyi hakan yasa Munir yadafa kafadanshi yace âcommon mana fushin ya isa haka before kasa karyan vakada lafiya da Mami tayi azo asani please go back homeâ yatsine fuska yayi yace âIâm hungry Muneer, please kaje gida ka kawomin abincin Ammiâ tashi Muneer yayi yace âokayâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ6ïžâŁ
Rashida tadade awajen tsaye ranta na kunan wulakancin daya mata sannan takoma ciki Mama tace âina kikajeâ? Kudinsu ta nunama Mama tace ânaje rage kudin daya kashe mana ne amman yaki kulaniâ yanda take maganan kasan ranta abace yake Mama bata cemata komiba idan sabone tasaba da halin Rashidan nan na batason ataimakesu, itafa kawai bataso ne sabida gori da wani abu dazaije yadawo.
Har dare duba Mama ake akai akai ana zuwa auna BP da sai sauka yake ahankali ahankali, kawai Mama is at stage da batason damuwa da wani abu dazai tsoratata ko tadamata da hankali ko kadan, tare suka sauko sukai ishaâi suna idarwa tazare hijabinta ta ijiye nan kan dadduman yanda kanta kemata nauyi sabida jiya batai bacci ba jiya batasan lokacin data wuce tahau kan gadon ta shige cikin chan bango danta barma Mama dake azkar space nata, taja bargo ta rufa ko 1min bata karaba sai bacci tafara jan munshari juyowa Mama tayi dagakan dadduma ta kalleta sai kawai ta cigaba da jan charbinta tana zikiri, knocking akayi tareda budo kofan Mama tace âbismillahâ ahankali ya shigo rikeda basket na kayan abinci wannan karan yana sanye da jean da riga dasukamai kyau, dasauri Mama tace âRiyad kaine sannu da zuwaâ zata yunkura dasauri yace âNo Mama karki tashiâ yataho inda take ya duka basket din ya ijiye yace âabinci nakawo miki Mama na gida, nasan abincin asibiti ba dadiâ murmushi Mama tayi tace âsannu da dawainiya Riyad, sannu Allah saka da alkhairi, ni bandama bakin maka godiya againâ dan satan kallon Rashida yayi daya hango a gado tarufa da bargon gadon sabida AC amman kana ganin fuskanta karaf a kan idon Mama dauke kai yayi dasauri daga kallonta yamike tsaye yace âMama bari najeâ dasauri Mama tace ânagode Riyad saida safe ayi tuki ahankaliâ âToh Mamaâ yafadi yajuya hakanan yasami kanshi da sake kallonta yana tafiya harsaida ya bude kofa sannan yajuyar da kanshi ya kalli kofan yafice Mama tadanyi murmushi kadan tareda bude kulan, she just feel wani irin strong trust for Riyad connection that she feels towards the boy yawuce misali, bude kulan tayi taga tuwo da miyan kuka ga man shanu da yaji a gefe da namomi sai kuma 3rd kulan pepper soup ne, shiru tayi tana kallon abincin tana tuna rayuwan datayi abaya ire iren abincin nan sune cimarta dan abincin da Baban Rashida yafici kenan, he always complements abincinta especially pepper soup yace baitabacin pepper soup mai dadin nataba, spoon tadauka ta debo naman takai baki wato duk kalan dadin rayuwa da mulkin dakake ciki idan Allah yaso kwacewa it takes seconds yayi hakan, alokacin bata taba sanin zatai rayuwan da abinci zai gagaresu ba! Ijiyan zuciya ta sauke sai kawai ta ture tunanin kafin kanta yafara ciwo.
Mota Riyad yawuce da Munir keciki yana jiranshi yabude gaba yashiga Munir yatada mota yace âhope sheâs feeling better tunda you donât want me to go with youâ yatsine fuska yayi yace âthanks for the food daka karbomin daga wajen Ammiâbaicemai komiba suka wuce gida, ta side nashi suka shiga as usual, parking Munir yayi yawuce yafita dan yaje side nasu shikuma yawuce flat dinshi, zaune yaga Mom afalo tana ganinshi ta taso da saurinta tazo wajen kawai ta rungumeshi saikuma ta dago tahau taba fuskanshi tace âyou have not been eating Son, look at you, duk ka rameâ ahankali yace âIâm fine Momâ waje yasamu ya zauna Mom ma tazauna tace âkayakuri kayafema Haleematu is not her fault banson kayi fushi da ita over petty mistake, sheâs just 25 yanzu so kagani sheâs still a small girl, kishi take batason ka kula mata which nayi supporting hakanâ kaman bazaiyi magana ha saikuma yace âMom she needs to learn to respect my privacy, tadena bincikamin kaya and tadenaâŠ..â yadanyi shiru Mom tace âtadena me?â Baki yabude saikuma yayi shiru sai chan kuma yace âtadena sharing my private affairs with my Momâ dakuwa Mom tamai tace âshe shared private affairs naka dani da duniya tai sharing? Zanje nagayama duniya baka iya kwanciya da matanka kullum neâ? Lumshe idanu yayi sai kawai ya kalli gefe duk Mom na kallonshi sai kawai ta mike tsaye tace âif you donât want that then kaima do the needful, kama yarinyar nan ciki kagani, I just need heir to the king, gabaki dayan masarautan nan jira ake aga matarka ta haihu so kake ace ita juya ce? Yanzu gashi kayi fushi kabar gida 2 nema ko 3days yanzu bakuyiba, I will tell her to come now kuma wlh kamata maganan fadan nan saina sabamaka umarni na baka, tarayya nace kuyi kui bacci good nightâ tai maganan tawuce tana fita daga daki yabita da kallo wondering wat happened? Mom bata damunshi ada tana duk abinda yaga dama yanzu ko she dictate everything. Tashi yayi ahankali kawai yafada bayi yashiga wanka fitowa yayi ya shirya cikin pajamas yadan gaji so he just wanna sleep kwanciya yayi yana kashe wuta yana ji akai iso Sarauniya zata shigo ta telecom ana neman izininshi dan barinta danna boturin yayi alamun a barta, da saurinta Haleematu ta shigo taci gayu tasaka gold alkyabba wucewa ciki tayi da sallama ta shiga bedroom nashi dayayi sanyi sosai ga duhu hannu tamika zata kunna wutan strictly yace âkarki kunnamin wutaâ da sauri ta tsaya saikuma ahankali tashiga cire Alkyabban wasu arnan kayan bacci tasaka tataho ahankali ta hayo gadon kawai ta rungumeshi tana manna boobs dinta awuyanshi tace âIâm sorry Ranka shi dadi bazan kara maimaita kallan laifin dana maka ba dan Allah ka gafarce ni kajiâ.
Kasa magana yayi yay shiru dago kanta tayi takai hannunta kan gefen fuskanshi ta shafa tace âamin afuwa akulaniâ tashiga shafa fuskanshi ahankali zuwa kirjinshi zuwa kasa daidai zata kai hannun wandonshi kawai ya jefata gadon yabita yanajan wandonshi kasa he donât know so many things na zuciyanshi harda mara kunyan yarinyar nan he just needs natsuwa kawai ya shigeta tareda sakin ijiyan zuciya sannan yafara ita kanta takasa gane yanason sex ne bayaso ne oho shifa yafi karfin ya nemeki saidai ke kizo, kuma kikazo ya rikeki kaman mayunwaci wani zubin, saida tafara kabar da hannayenshi akan boobs dinta sabida yanda suke mata shegen zafi yau dan heâs handling her very rough but yaki yau yabata wahala saida tafara tureshi amman cinta yake chan ya kankameta yafara numfashi da karfin gaske ahhhh! Uhmmmmm! Assshhhh! Ya feso ciki sannan yasaketa dasauri yatashi yawuce yafada bayi wanka yayo kawai yafito feeling calm ya kwanta sai bacci.
Wuraren 7 Mama ta tursasata dole taje gida ta shirya ta sanar da Baba Liman batada lafiya sannan ta tafi school karta kara latti bataso tabar Mama ita kadaiba amman tawuce ta tafi, yau in patient pediatric ward tayi aiki the kids loves her, sheâs so gently and sweet with them har sauran yan group dinta ma were jealous hakadai tai aiki har 1 tai salla ta tafi tadawo hospital har dare Riyad baizo ba suna zaune kan dadduma Mama tace âyau Riyad shiruâ tabe baki Rashida tayi tace âsai kace daman kin sanshi daga wani waje ne ni wlh bakiga yanda nakejin haushin sa ba na tsanesâŠâŠâ wani kallo da Mama tamata yasa ta hadiye maganan kawai ta tashi tawuce ta zauna akan kujera tahau duba log book nata tana yan karance karance, tadauki book tana karatun everything datayi takuma koya tunda bata samu taje library ba sabida Mama, anan kan kujeran tai bacci.
Yau dadi takeji zaâa sallamesu Mama tace âwai bazaki school baneâ dasauri tace âMama Dr yazo ya sallame mu zan kaiki gida saina tafi ai nadauki permission a hospitalâ Shiru Mama tamata wajajen 9 Dr yazo yakalli Mama dayaga har hijabi da kaya ta chanza sun gama arranging komi yace âMama yanzu kin gaji damu zaki tafi ki barniâ? Dan dariya Mama tayi tace âai asibiti ba abun so bane likita dan haka zan tafi in barka faâ dariya yayi sosai yaduduba Mama duk Rashida na kallon abinda yake da manyan idanunta kaman zaâa Mamanta wani mugunta yace âAlhamdulillah Mama BP ki yasauko Mama, dan Allah ki rage tunani kinjiâ yajuyo ya kalli Rashida yace âmakesure baki barin Maman ki na yawan tunani, da shiga damuwa da stress da tashin hankali none of abinda na lissafo is good for her, she needs to be happy all the time, Mama take your drugs akai akai kinji Mamaâ gyadamai kai tayi sannan yabama Rashida takardan sallama yaced âyou can go now, mun sallameta everything has been cleared by Riyad, ga magungunan ta nan bari namiki bayanin yanda zatashaâ yashiga yima Rashida bayani gyadamai kai tayi tace âthank youâ murmushi yayi yace âMama yarki kaman Balarabiya akwai wani akasa ne idan babu kowa ina kamâŠ..â kasa karasa maganan yayi sabida turo kofan da akayi babu ko knocking duk suka juyo Riyad ne, yasaka wani ash color shadda mai haske yana wani irin kamshi mai dadi dake banbanta shi da mutane da dama, dasauri Rashida tadauke kai daga kallonshi mugun haushinsa takeji, takalli Mama tace âMama tunda na hada komi bari naje na nemo mana keke napepâ kafin Mama tabata amsa ma tajuya ko kallon Riyad batayiba tabi ta gefenshi tafice, Dr yace âahh Riyad kaine barka da zuwaâ adikile yace âyauwaâ dan kallonshi Mama tayi bata tabajin irin muryan nan tattare dashi ba, kin kallon Dr yayi yawuce wajen Mama yace âMama ina kwana nazo nakaiki gidaâ yakalli kayan dasuka hahhada yaduka ya kwasa duka da kulolin yafice Dr yabishi da kallon Mamaki, aranshi yace âwho are this people to Riyad cus this is just more than help akwai wani abu akasa, look at the way heâs serving themâ saikuma yakalli Mama yace âMama Allah kiyaye hanyaâ yawuce yafita shima, shiru Mama tayi kaman mai tunanin wani abu sai chan tai murmusa kawai, shigowa yayi yazo har wajen gadon yace âMama can you walk? Ko in dauko kujeraâ? Dan murmushi tayi tace âhaba zan iya tafiya Riyadâ saukowa tayi daga gadon ahankali tafara tafiya yana kaffa kaffa da ita dudda bawai riketa yayi ba Mama ta rame sosai kaman iska zai kadata tafadi sunyi tafiya sun fito cikeda kulawa yace âzaki huta Mama?â Wlh har cikin zuciyanta tajejin Riyad yanzu, heâs caring and just too protective da sauri tace âaâa bangajiba da karfina fa muje kaganiâ murmushi yayi suka fito har wajen mota baya yabude mata dayake jeep ne sai alokacin ya taimaka mata ta shiga ta hanyar dan dukawa ya nuna mata shoulder shi yace âdafani ki shigaâ kallon shaddan jikinshi kalkal Mama tayi saikuma ta kalli hannunta dudda bawai datti bane a hannunta amman saitace âkai haba karna bata maka kayaâ ahankali yakai hannunshi yakama nata yadaura akan shouldershi yana rage tsayi yace âMama kibata duk albarkanki neâ ahankali Mama tai murmushi kafin ta dafashi da kyau ta daga kafanta ta taka step din ta shiga motar yana kallonta yace âare you comfortable Mamaâ gyadamai kai tayi tace âyes Riyad thank youâ daidai lokacin Rashida na shigowa hospital din tana cikin wani empty keke napep ta hangosu, azuciye ta sauko ta taho wajen daidai yajuyo, chak ya tsaya yayi folding hannunshi a kirji tundaga kan kafafunta yake kallo dake cikin wani bakin flat shoe daya gama mutuwa but dudda haka kafanta ya haska flat shoe din, zuwa skirt dake jikinta na atampa da pink hijabin data saka mai hula ya tasya mata a guiwa, tana zuwa ta tsaya agabanshi cikeda masifa tace âbakai zaka kaimu gida ba nariga na kira kekeâ wani banzan kallon raini yamata yace âthen saikije ki sallameshiâ yanda yamata maganan kaman ta kurma ihu mutumin nan dan balaâin rainin wayo ne sabida yaga yanada kudi da hotel shine zai dinga ma mutane magana yanda yaga dama, wai ina ruwanshi dasu? Cikin fushi tace ânace maka kafito mini da Mamana daga motan ka, wayasani ma ko dan yankan kaine kai tunda sai shegemana kakeâ wani kallo yamata sai kawai yawuce yabude mazaunin direba ya shiga ya zauna itakuma ta shiga kiciniyan bude kofan back sit, da hannu Riyad yakira mai keken da sauri ya sauko yazo wajen yace âgani yallabaiâ kudi dayawa yazaro daga aljihu ya mikamai yace âgashi kajeâ karba yayi yahau godiya Mama tai murmushi ciki ciki dan duk tana kallon draman tai kaman batasan sunayi ba making sick and tired face, danna glass na window tayi takalli Rashida dake tsaye tana kallon Riyad kaman zata iya fada dashi akace tayi, Mama tace âshigo muje kina batama Riyad lokaci zaije aiki fa Rashidaâ kallon Mama tayi har idanunta sunyi ja akufule tace âkuje ni bazan shiga motan baâ Mama na kallonta tace âzan saba miki fa wlh, zoki shiga mota muwuceâ kallon Mama tayi bataso ta batama Mama rai yasa ta danne zuciyanta da kyar ta zagayo harta bude kofan baya Mama tace âtunda ga direba kin samu ko dole ki shigo bayaâ wani sweet smile Riyad yasaki ya gyara fuskanshi da sauri yana kallon waje kaman baisan anayi ba, kaman tayi ihu Rashida ta maida kofan tarufe takoma gaba tabude kofan ahankali tadan kalleshi ganin waje yake kallo abinshi yasa da kyar tashiga ta zauna ta jawo kofan tarufe tana harare harare, murmushi yayi yatada yajuyo yadan kallo Mama da tausassan murya yace âMama are you comfortable? Natada motanâ wani irin murmushin dadi Mama tasaki tace âIâm comfortable dâana mujeâ wani irin zafi Rashida taji aranta yanda Mama takira Riyad danta kawai saita ciro wayanta ta manna earpiece tasa a kunne, tada motan Riyad yayi suka tafi baya wani gudu sosai, Mama sai hira takemai kaman tasanshi hakan yakara tunzura Rashida dudda batajin mesuke fadi but tana ganin bakin Mama na motsi, har anguwansu hira suke sai kallon motan ake a kofar gidansu yayi parking ya bude kofa ya sauko yabude baya Mama ta sauko ahankali yabude booth ya kwaso bags nasu Mama tace âkey na bakin jakanâ takai hannu tasa blavk jakan aljihun taciromai tabashi yana sane yasan bata iya bude kofan motanshi ba ya shareta shiga da Mama ciki yayi sai kallon gidansu yake koina a gyare tsaf zaunawa Mama tayi yace âbari naje Mama Allah kara saukiâ Mama tace ânagode nagode Allah maka Albarka, wai ina Rashida ne hala ta wuce wani wajeâ baice komiba yawuce Mama tabishi dagodiya dayake motan tinted ne baya iya ganota but yaga yanda motan ke motsin ana bubbugata yayi kaman bai saniba yawuce yabude kofa yashiga ya zauna batare daya kalleta ba yace âwat are you still doing in my carâ? Akufule tace âinba dole ba mema zai kawoni cikin your so called carâ? Still yaki kallonta yace âget out!â Kaman yana magana dawata dabba kirjinta tafarfasa yake tace âka budemin kaga idan nakara wani numfashi a motan nakaâ dan kallonta yayi strictly yace âwho are you to make Riyad work for youâ? Mamaki ne yakashe Rashida irin what exactly guy din nan thinks of himself ne, tadai daure ta danne zuciyanta da kyar tace âto ai ban iya bude kofan bane niâ dan juyowa yayi yayi facing nata yace âthen learn to soften muryanki and ask for help politely missâ ido cikin ido take kallonshi ya zubamata mayun idanunshi dayasa kawai taji jikinta namata wani iri, duk yanda taso ta daure tacigaba da kallonshi itama saita kasa tadauke idanunta dan kasa jure kwayar idanunshi tayi, ta hadiye wani abu da kyar dataji yaa tsayamata a wuya tadan runtse idanu kai kasan sheâs about to say komene zatace ne out of compulsion tace âkadan budemin kofan motan nafitaâ sosai yake kallonta sabida yanda kawai yaji muryanta pierce his heart, this is the first time tunda ya santa takemai magana softly but da gangan dan ya kureta yakaita bango yace âsoften your voice more and add please cus no one command Riyad!â Da sauri ta kalleshi wani kallo yamata na idan baki fadi ba zanja motata nayi gaba abuna, kaman tayi ihu takeji shine namiji na farko so far so good tunda ta girman nan ya iya tankwarata yakuma juyata haka, batasan mesa ba batakaimai duka ko kokawa ba the normal ita datuni takaimai duka suyi dambe but shi takasa, agogon hannunshi yakala kirar TAG Heuer yace âyou have 5secs left ko i will go wherever zani u will be here is none of my businessâ yayi maganan yana kunna motan ma abinshi, wani ijiyan zuciya ta sauke ta sauke muryanta kasa kaman ba ita ba sounding like a Baby tace âkadan budemin kofan motanâ dan juyo da kanshi yayi ya kalleta muryanta is the best muryan mace daya tabaji in his entire life, yanda yake mata wani irin kallon yasa ahankali kaman ba itaba lips nata na rawa rawa tace âpâŠâŠ..pâŠ.leaseâŠ..please!â sannan ta dauke kai da sauri kaman tai abin kunya din nan, sabida son yakaita bango gabaki daya shikuma annoyingly and authoritatively yace âgood gurl!â kaman wata damusa ta kalleshi for the first time Riyad yasakin mata wani kalan murmushi dayasa taji zuciyabta yabuga rasss! Yana beating dum! Dum! Dum!! Da sauri ta dauke kai trying to control yanda zuciyanta ke beating takasa, dan tasowa yayi daga sit din dayake ta gefen ido taga ya nufota da sauri ta juyo da kanta ta kalleshi dan kaman zai hugging nata, hada ido sukayi gashi yaki daina kallonta kaman akwai wani abu dayake son gani game da ita sai kawai lips dinta yahau rawa tawani koma baya da sauri ta manne jikin kujeran kaman zata nitse ciki har hannunta rawa yake barin yanda kamshin turarenshi ke shiga hancinta jinshi dab da ita infact yadin kayan jikinshi ke tabata ta she was scared, lost, shaking, it was just a freaking reaction jikinta keyi dabatasan na me ba, he could feel heartbeat dinta, he could clearly see kwayan idanunta, this whole fadan nata is just an act! A mask! Hannunshi yakai ahankali kaman baiso yabude kofan still looking at her ya bude kofan tareda komawa seat nashi ya zauna bude idanunta tayi da sauri he was expecting tamai rashin kunya but saiyaga duk ta dimauce ta sauka da sauri kawai ta maida kofan tawuce ta shiga gidansu da sauri sai kawai ya girgiza kai yatada motan yawuce yabar anguwan.
SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ7ïžâŁ
Tana shiga gıda Mamag tace âke kuma an ina kika tsaya?â Ahankali tace âwajeâ kawai tashiga ciki zata kwaso kayan abinci dan daura girki Mama tace âkibar girki inada abincin da Riyad yakawomin har yanzu da zafinsu a kula shi zanci, kizo kije school daganan ki wuce aiki, Riyad yace kidawoâ dasauri tafito daga dakin ta kalli Mama tace âMama nifa yau na dauki permission bazanje school baâ saikuma ta taho ta zauna wajen Mama tace âMama wai kinsan mutumin chan neâ? Mama na kallon kwayar idanunta tace âwani mutuminâ? Cikeda mugun hali tace âshi wannan mutumin daya kawomu naga kunatayi kaman daman kunsan juna ne tun chanâ dan murmushi kadan Mama tayi tace âaâa amman kawai zuciyata ya natsu dashi kaman na sanshi daga wani wuri, kema kinsan dawuya nake natsuwa da mutane amman shi kawai yayi fuce araina, mutumin arziki ne mutunci da dattaku, yanada halaye da dama nagari, bantaba gani a idanunshi yamin kallon mai wata cuta ba, gakuma yanda yabiya kudin asibiti akamin komi, wanda yamaka Akhairi kasoshiâ ranta adan bace tace âMama ni na tsaneshiâ baki Mama tasaki tana kallonta ganin da gaske take, yunkurawa tayi tace âkuma konawa ya kashe miki a asibiti saina biyashi alkawari ne ko zanyi shekara dari ina neman kudinâ dan dariya Mama tayi tace âzo ki juye abinciccikan ki wanke kulolin nidai fitinaâuâ wucewa tayi ta kwasa batai musu ba haka dai tai aikin komi Baba Liman ma yashigo gaida Mama wuraren 1 ta shirya ta tafi aikin sabida yanda Mama tace âsaitajeâ ga mamakinta ko kallon banza Madam bata mata ba hakama sauran maâaikatan dudda bataga Hussy ba, kin zuwa office na Riyad tayi tadaiyi duka ayyukanta idan tana gaban desk aka kira ana neman cleaner a so so room ta taje, harta tashi by 6 bata ganshi ba bakaramin dadi tajiba ta tafi gida.
Washegari da sassafe ta tafi hospital nasu yau pediatric surgery departmant zasu to watch not to do itada team dinta zasu, direct tawuce inda suke ijiye bags nasu ta ijiye aka dan musu lectures kadan sannan tawuce tashiga shirye shiryen shiga surgery tsayawa tayi tana wanke hannunta wata tazo itama ta tsaya kusada ita tai murmushi tace âHiâ saikuma ta kalli Labcoat nata tace âRashida Iâm Maimuna but Maimoon ake cemin, tun ranan monday nake noticing naki, can we be friends plsâ? Dan tsayawa Rashida tayi tana kallonta like a weirdo dasauri Maimoon tace âpleaseâ dan lumshe ido Rashida tayi yarinyar seems very cool and calm ahankali tace âI donât know yanda ake friendship gaskiyaâ murmushi sosai Maimoon tamata tace âI know and I will teach you, letâs goâ shiga cikin operation room din sukayi duk hannayensu a sama aka sassaka musu handglove ga yaron da zaâama operation din da baifi shekara biyar ba anyi sedating nashi shigowa surgeon din yayi wanda Babba ne bawai yaro ba aka samai nashi handglove din yawuce surgical table din student Doctors din dasuke su bakwai duk suka tsaya a gefe, Dr yace âyaron nan dake kan table din nan nada hydrocele wazai gayamin procedure da zanbi in this surgery, and ya sunan surgery dinâ? Maimoon ce tafara daga hannu tabata amsa yace âwrongâ almost dukansu saida suka bada amsa yace âwrongâ yakalli Rashida dabatai magana ba dan ita bata show off ko a aji, yace âmake attempt missâ dan ijiyan zuciya ta sauke Rashida confidently cikin turencinta that is good muryanta kuma makes it sweet a kunne tace âzamuyi Hydrocelectomy surgery to remove the hydrocele daga scrotum din, zamuyi making incision ananâŠ..â tafara bayanin procedure din da sai kawai Dr ya tsaya yana kallonta exactly abinda zaiyi tafadi kaman ta tabayi, hannu yamikama head nurse yace âscalpelâ samai wuka akayi a hannu yarike yadauki marker yamikama Rashida yace âcome closeâ ahankali ta matso kusada surgeon din gabanta nadan faduwa yabata marker yace âdraw the lineâ karba tayi ahankali taja, to her biggest shock yace âmake the cutâ dasauri ta kalleshi, confidently yace âIâm here you wonât make a mistake so go aheadâ dan tsayawa tayi Dr yace âwe all start ahaka, go for it, Iâm right here ina kallonkiâ bismillah tayi ahankali ta karba tana kokarin kallon fuskan yaron yace âdonât look at his faceâ ijiyan zuciya ta sauke tareda rufe ido what is her biggest motivation da inspiration na son zama likita? Ahankali tace âMama! I want to become the best Doctor for Mama! I want to make research nagano yanda ake curing HIV for Mama! I want to make Mama better, I want to be the best Dr in Nigeria da kewaye da al umma zasuyi alfahari dasun samuâ daidainan tabude idanunta kawai tashiga cutting Dr na tsaye kusa da ita yace âsuctionâ aka kwashe jinin, wasa wasa da shi da Rashida sukai surgery din nan tass yasake barinta tai stitching yaron up, her stitching style kadai saida ya kalleta almost 10yrs yana aiki in this surgery student Doctors daban daban interns but baitaba ganin skilled yar baiwan Dr like this girl ba ita kanta for now bama tasan wacece itaba imagine abinda take iyayi in year5, sallaman su yayi yakalli Rashida yace âmakesure you become a surgeon Doctor Râ dan sunnar da kanta tayi batare datai murnushi ba cus she hardly smile outside tawuce tafita Maimoon tabiyota tace âwowwww you are amazing Rash kai! I can never do thatâ ahankali tace âthanksâ dasauri Maimoon tace âletâs go grab some drinksâ wayanta Rash taciro daga jaka taga 2:30 tace âohh no I have to go to workâ taciro log book dinta da sauri tawuce taje aka mata signing tajuyo takalli Maimoon tace âgobeâ bata jira amsanta ba tajuya dasauri Maimoon ta tsaya awajen tai shiru tana kallonta, tace âsheâs unique, Bilal you loose a rare gemâ. Wajajen 3 takai hotel din dan saida ta tsaya tai salla tana shiga tawuce changing room tafito kenan saiga Madam tace âyanzu ne lokacin zuwa aiki i will deduct 5k from salary nakiâ sauke kanta tayi kasa tawuce tashiga aiki thank God yau Friday gobe ba aikin, tass tagama aikace aikacen ta wuraren 5 Madam ta kirasu hall duk suka wuce, abinci tagani an kakkasa buhun shinkafa, jarkan mai, indomie, madara da milo sugar sai gero da taliya tace âkowa ya tafi da abincin azuminshi gida courtesy of Ogaâ sai murna ake, tunda tafara aiki dasu da Ramadan ana basu abinci last year an bata is not new thing amman saitakeji yanzu kaman karta dauka sabida Riyad but kuma idan bata dauka ba zaâayita surutu daman ance tanada girman kai, Madam tace âzansa security su taya kowa fita da nashi sai kuje ku kira keke, Happy Ramadan to everyoneâ ihu duk sukayi ana shouting thank you Ma sannan ta sallamesu wucewa tayi ta chanza kaya ta goya jakanta tafito taje ta taho da keke tana zuwa security suka tayata lodawa abayan keken ta tafi.
Yau sunday tana so taje kasuwa tadan yo musu yan kananun cefenen azumi tunda batada aiki yau, atampa tasaka green shima ya kwana biyu tadau wani black hijabi ta daura asama mai hula ya tsaya mata a knee aiko yamata kyau tafito falo inda Mama ke zaune tana kirga kudinsu, zuwa tayi kusada Mama ta zauna Mama tace âyauwa kin shiryaâ? Gyadama Mama kai tayi, kudin da Mama takasa agabanta kashi biyu ta dauki me yawan tabata tace âga wannan kudin dubu talatin ne nakine kisai dan atampa da takalmi da yan kayan kwalliya da turare kema kiyi kyau da salla kuka dawo sai akai dinki koâ dasauri ta maidama Mama kudin tace âMama bana bukatan kayan salla, kayan danake dasu zan iya sawa da salla, Mama we have important things to do, drugs dinki, abinci, school fees dina dakuma kudin da mutumin chan ya kashe na asibiti ni sai na biyashiâ kallonta Mama take tace âshiyace miki kibiyashi â? Girgizama Mama kai tayi tace âMama youâre my responsibility ni kadai donât others, banson wani ya taimakeni wajen kula da mahaifiyata, inda bekaiki asibitin masu kudin nan nasu ba dana iya biya amman yakama kaman an sashi ya kaiki asibitin kudiâ tai maganan tana batarai tsayawa kawai Mama tayi tana kallonta tun Rashida na yarinya tanada wani irin kishi dasai ka san halinta ne zakasan kishine itafa batason kowa na raban Maman ta, yana daga cikin abinda yasa takejin haushin Riyad dakuma so tabiyashi kudinshi sabida yanda taga yana nan nan da ita bataso taga Mama na kula wasu with a smile, maida kudin kawai Mama tayi hannunta ta danne tace âlisten to me umarni nabaki kisai kayan salla inaso nima naga yarinyana tayi kyau takuma fito da salla kinjiâ shiru tayi tana kallon Mama taki magana hade fuska Mama tayi tace âbazaki amsaba?â Ahankali tace ânaji tohâ dan murmushi tayi tabata 20k tace âwannan sai kiyo su cefene su maggi da nama da kayan miya tunda mun sami kayan abinciâ gyadama Mama kai tayi ahankali ta tashi Mama tace âadawo lpy ki duba titi kafin ki tsallaka kinjiâ toh ta amsa tawuce tasa takalminta tafita abinta Mama tai murmushi.
Kusan 3hrs tabata a kasuwa, tasayo atampa mai kyau da gyale da takalmi tadansai bra da pant guda biyu sai pad dan tanaji cikinta na ciwo sannan tayo cefene tashigo keke tabar kasuwan.
Abakin titi aka saukesu hakan yasa ta dandaro cikin anguwansu da kafa, tun kafin takai gidansu ta hango wata arniyan karaman mota baka pake a kofar gidansu motan waye wannan? Hakan yasa ta kara sauri tana zuwa tabude kofar gidansu da sauri ta shiga saura kadan tayi karo da Riyad azaure yadan koma baya kadan tsayawa itama tayi gabanta kawai yafadi ta zubamai ido, yana sanye da wani milk soft yard dake kyalli yabi jikinshi kaman magic, kafanshi kafanshi sanye da Jordaan leather loafers brown, hannunshi daure da agogon Audemars Piguet, dayan hannunshi rike da waya samsung galaxy fold, ba hula gashin kanshi ya kwanta yana sheki sai kamshi yake zubawa, dauke kai tayi da sauri daga kallonshi dan heâs so clean wlh ko datti ko stain ko tabo guda daya babu ajikin kayanshi, haka kayan a goge babu squeezing ko daya, shima tundaga kan kafafunta dake sanye dawani black takalmi flat da duk an dinke ya kalla dudda fararen kafanta are shinning ga long fararen nails na kafanta da babu lalli ko daya akai zuwa ataman dake jikinta da hijabin da ledoji biyun dake hannunta bakake data rike sannan yazubama fuskanta idanu she looks tired, sheâs even sweating a goshi dan duk gashi ya kwanta a goshin nata, ga lips dinta sun bushe kaman sheâs a bit sick. âKallon faâ? Tai maganan cikeda rashin kunya dayasa ya daidaita kwayar idanunshi cikin nata dasauri ta janye idanunta hakanan taji takasa kallonshi but tsabagen karfin hali tace âkadena zuwa gidanmu bansoâ cikeda isa kaman anyi forcing nashi yayi maganan awulakance yace âare you angry ba wajenki nake zuwa baâ? Wani dum! Taji saukan maganan da sauri ta kalleshi tsaf shima yake kallonta mene mutumin nan yace? Mema ya dauketa? Taji haushi dan ba wajenta yake zuwa ba on wat ground? Kokarin hado martanin dazata bashi take dan she was a bit speechless but yarigata wani kallon raini yamata calmly yace âbakida matsayin dazan zo nemankiâ yana maganan yabi ta gefenta yafice wlh takai 1 good minute fassara maganan shi take akanta taji ranta na kumfa dasauri tajuyo tafito kofar gida daidai yaja motanshi tabishi da kallo yana wani saka bakin glass a idanunshi ko inda take bai kallo ba yawuce abinshi kaman zata hadiye zuciya tamutu tace ânima ka isa kazo wajena ne aka gayamaka? Sai ji dakai kaman wani dan shugaban kasa sabida yana takama da dan hotel din dayake dashi I will leave your company soon zan nemi wani hotel din wlh kuwaâ tana maganan tajuya tana saisaita bacin ranta takoma cikin gidan kaya tagani cikin gidansu harda su indomie da kwalin kwai kudan 5 crete gasu manta manyan roban madara Milo oat, wlh shopping data gani zube a compound yakai na 300k ga bandir na kudi kuma ijiye kasa na yan 1k guda biyu dasauri ta shiga ta tsaya gaban kayan ranta abace tace âMama waya kawo mana abubuwan nanâ?
Ahankali Mama tace âRiyad yakawoâ kaman zata fashe sabida bacin rai tace âMama shine zaki karba?â Kallonta Mama tayi tace âbabu yanda banyi dashi ba amman yaki yarda wai ni mahaifiyar sa ce kodan darajan azumi na amsa, kinga uban kudin daya ijiye dane naki amsa da kyar na zari yasake daura daya, haka ya ijiye komi anan dan ni naki karbaâ cikeda bakin ciki harda abinda yamata a zaure tace âMama shine baki kira yara kinsa sun maidamai da kayan mota baâ? Kaman wacce aka daka kawai saita fashe da kuka sosai ta ijiye kayan data shigo dasu daga kasuwa nan kasa ta tsallaka tashiga daki kawai tahau kuka idanunta sunyi jajir tashi Mama tayi tabiyota ciki cikeda damuwa tace âRashida mekuma haka da kuka? Duk mai imani yadaga ido yaga rayuwanmu dole yaji tausayinmu, na karba badan komi ba saidai naga yaron kirki ne hakanan zuciyana ya natsu dashi kuma bawai saurayi bane ya gayamin yanada mata so mutum ne mai hankali ba yaro ba, saikuma dalili nabiyu shine karbansu zai saukaka miki kema at least daganan zuwa 2month zamu manta da siyan Kayan abinci albashin dazaki samu saimu hada da wayan nan kudin ki biya kudin school fees ragowan mu rike na asibiti, you think Iâm happy da rayuwan wahalan dakikeyi? Understand me itâs Ramadan kyaututuka haka is normal ko na yan anguwan man sabida baki karba ne da yanzu an kawo mana, itâs okay ya isa stop cryingâ Mama tajawota cikeda lallashi rabon datai kuka haka tun ranan da aka kwantar da ita a asibiti cikin kuka tace âMama stop collecting abu daga hannun kowa, Iâm enough for you, Mama bazan taba bari ki kwana da yunwa ba, I will neverâ hawaye taji yaciko idanunta saikuma tai murmushi ta danne takai hannunta ta share mata fuska tace âI know yâata will never allow me to go hungry, natuba to bazan kara karban komi daga hannun kowa ba, Rashida na is enough for me, the best daughter aduk duniyan nan, come hereâ Mama kawai ta rungumeta tana murmushi sheâs lucky Allah ya azurtata da yâa dake sonta haka, sun dade ahaka sannan Mama ta dagota takai hannu ta yaye hijabin jikinta ta tana taba wuyanta tace âjikinki da zafi baki da lafiya neâ? Ahankali tace âcikina ke ciwo kadan gobe naje asibiti zan karbi maganiâ cikeda so Mama tace âsannu kinji, zauna kihuta ni zan miki girkiâ dasauri tace âzanyi Mamaâ tashi zatayi Mama takama hannunta bawasa kan fuskanta tace âzauna kihutaâ zama tayi Mama ta tashi atampanta tafara dubawa ta yaba sannan tashiga daura musu abinci itakuma anan bacci yayi awon gaba da ita.
Da kyar Mama ta tadata around 4 na asuba sabida suyi sahur, tariga tasan bata azumi wucewa tayi tama Mama abincin sahur sannan tawuce bayi yau da hot water tai wanka dan zazzabi takeji da ciwon mara but she feels she can manage dan is not that serious tana dawowa takaima Mama itama nata ruwan zafin tashigo daki tace âmuje Mamaâ idanunta Mama ta kalla tace âdan Allah kina zuwa clinic kisha magana kar zazzabin nan yarufeki da kyau kinjiâ gyadamata kai tayi Mama tace âbarshi zan iya zuwa bayin da kaina jeki kimtsaâ batai musu ba ciki tawuce tashiga kimtsawa tasa black abaya tahada jakanta na baya saikuma ta kara kwanciya yawanci a rashin karfi ne kafi gane Rashida is sick dan baka ganewa a baki da fuska sabida masifa da fada, shigowa Mama tayi ganinta a kwance yasa Mama tace ânamiki shayiâ? Girgizama Mama kai tace âidan naje school zanci abinci Mama karki damuâ da dan damuwa Mama tadauko mai tana shafawa hartai salla tana kwance wajen saima lumshe ido data farayi sai kawai Mama ta barta zuwa 7 ta tabata tace âtashi kitafi schoolâ tashi tayi ganin Mama tafara damuwa yasa tace âlaaaa Mama kinga najini garau maybe dama baccin danake ji yakara karamin zazzabiâ 200k na jiya Mama takawo da 100k nasu tasa asama tabata tace âgashi ki biya kudin makaranta kisai yan littafan da bazaâa rasa baâ kallon kudin tayi zatai magana Mama tace âni Maman ki aka bama kudin nan, nikuma nabaki, kaman yanda Hajiyan nan taraba mana 20k a clinic naje na siyamiki crocs consider wannan kudin haka, go and pay school fees naki and buy textbooks dakike bukataâ ayanda fuskanta kadai yayi kasan bataso ba but ganin yanda Mama tayi yasa tasa hannu ta karba kawai tasa kudin ajaka ta goya, taja black gyale tashiga rolling tai kyau kaman balarabiya dudda bakomi akan fuskanta sannan tace âMama natafiâ 5k takara cirowa cikin kudinsu dabaifi 50k ba Mama tabata tace âdan Allah kihau keke yau, kici abinci mai kyau a school kinjiâ gyadama Mama kai tayi tace ânatafi Mama thank youâ âadawo lpy Allah bada saâaâ fita tayi tana kaiwa junction ta shiga cafe tai printing ramita, sannan tafito tashiga keke sai bank taje tafara biyan school fees nata sannan tafito tashiga keke again sai asibitin su, sauka tayi wuraren 9:30 taga student nasu Maimoon na hangota ta taho wajenta dagudu tace âanyi releasing namu yau, kaman zaâayi manyan baki ne dai ance mu student mutafi wlhâ ahankali tace âreally, bari na karbi magani to natafiâ dasauri Maimoon tace âmeke damunkiâ? Dan yatsine fuska tayi tana tafiya tace âI think Iâm coming down with Maleria saikuma crampsâ Maimoon tace âoh no sorryâ office nasu tashiga tabude locker ana ijiye musu magani haka tadauki na Maleria da cramps suka fito yawance Maimoon ke hiran, ahankali tace âI want to buy food da water dazansha magani dashiâ dasauri Maimoon tace âmuje cafeteriaâ Jellof rice tasaya da beef 800, tasai ruwa daya ganin tana bude jaka yasa Maimoon tace âmu zauna anan kici manaâ girgiza kai tayi tace âkema kawai na gayamiki ne only Mama na ke sani idan bana azumi I donât want people knowing kunya yake saniâ dan murmushi Maimoon tayi tana kallonta yanda take arranging abincin ajaka tana maganan she looks so cute and adorable maida jakan bayanta tayi ta goya tace âbari naje to sai gobeâ Gyadamata Kai Maimoon tayi suka fito tana kaiwa titi tashiga keke, is just around 10 yanzu gwara ta tafi hotel tamusu aiki saita sami free evening har gaban hotel din aka kaita ta sauka tabiya kudi tashiga ciki, direct changing room nasu taje, saida tafara chanza kaya sannan tadan fito ganin kowa na aikinshi yan morning sun riga sunzo tun dazu so kafin wani yadawo dakin nan cikinsu kuma probably sai idan yan afternoon sunzo kuma, hakan yasa tadawo ta maida kofan tarufe batare data saka sakata ba takoma ta zauna taciro rice daga bag da water dakuma maganinta ta ijiye kan long bench dake wajen itama ta sauna ahankali sannan ta dauki abincin tabude tasa spoon tafara ci ahankali bayamata dadi ma abincin sabida zazzabi.
Ahankali yake tafiya da shi da Munir dawasu maâaikata guda biyu dake biyedashi abaya, akwai some changes dayakeso ayi abinda ma yakawo shi hotel din kenan this morning, duk ya gama nuna musu saura changing room na maâaikatan shi corridor suka shigo suna biyeda shi yasa hannu yabude kofan yasakai ciki yana magana yace âthe lockers nakesâŠâŠ.â Shiru yayi ganin yanda Rashida tawani yarda takeaway jellof rice din da ruwan yashiga tittila akasa ta tashi tsaye da sauri daidai su Munir zasu biyoshi su shigo ciki yace âwait!â Duk kallonshi sukayi suna tsaye bakin kofan batare da sun shigo ba strictly yace âkuje lobbyâ yanayinshi kawai yasa Munir yace âokayâ yajuya maâaikatan ma suka bishi yajuyo yazuba mata ido tana kallonshi cikeda fada baki tabude zatai magana dan akwai abinci abakinta sai kawai tai wani wawan kwarewa sai tari, maida kofan yayi yarufe ya kalleta ganin yanda take tari kaman zata mutu yasa gently yaduka yadauki bottle water nata daya fadi yadan zube yamike tsaye yasake kallonta tsabagen tarin datakeyi tama kasa tsayuwa ta tsugunna idanunta sunyi jajir ga rice guda daya fito daga hancinta alamun ba karamin kwarewa tayi ba, dasauri yataka zuwa inda take ahankali ya tsugunna yamika mata bottle water batare dayayi magana ba yana kallon fuskanta, tsabagen azaba sabida ga yaji a abinci ga kearewa mai kyau batasan lokacin data daura duka hannayenta biyu saman kan nashi ba takama both hannunshi da goran takai bakinta hakanan jiyayi jinin jikinshi ya tsaya chak jin saukan hannayenta biyu kan nashi, ahankali yadaura idanunshi kan hannunta dake saman nashi sannan yakai idanunshi kan fuskanta da yanda takeshan ruwan kaman yaki, tass ta shanye ruwan sannan tacire bakinta daga goran har lokacin tana rikeda hannunshi dabatasan tayiba tana sauke ijiyan zuciya kaman wacce tagudo daga hanyan mutuwa idanunta sunyi jaa, kusan 1min tayi tana sauke ijiyan zuciya sannan ahankali kaman mara gaskiya tadan dago kanta tadaura idanunta akan nashi yanda yake duke dab da ita kamshin turarenshi ya bade wajen da sauri ta maida idanunta kasa still bata sakeshi ba, yana kallon fuskanta baya ko kyafta ido yace âcan you let go off my hand nowâ? Dawani irin sauri ta kalleshi saikuma ta kalli goran ruwan data rike ganin yanda ta kama hannunshi da duka hannuwanta biyu saida taji kaman ta kurma ihu sabida kunya dawani irin sauri tasakeshi hakan yasa ya mike tsaye ya kalli magungunan ta dake kan bench na wajen sannan yawuce kofa haryasa hannu yabude kofan ya tsaya batare daya juyoba yace âkifito amaidaki gida, kafin ki mutu in my buildingâ dasauri ta kalleshi kaman wata damusa dan juyo da kanshi yayi but bai kalleta ba yace âtake days off when you feel better you can resumeâ yasa kafa yafita saikuma ya tsaya yace âsomeone will clean the place you donât have to, kifito akaiki gida!â Yana maganan yawuce yafita takai almost 2min aduke a inda yabarta saikuma ta daga hannuwanta ta kalla yanda tarikeshi saikawai taji kunya da haushin kanta sai abin yasa taji mugun zazzabi ya rufeta tanama jin sanyi, ahankali ta lallaba ta mike tadauki jakanta ta goya abaya batare data chanza uniform nata ta maida abayanta ba kafin wani ya sake shigowa yaganta tana chanza kaya she will not take the risk, tadauki magungunanta tarike a hannu tafito tana tafiya ahankali hakanan kawai sanyi taji tanaji barinma a hannuwanta dasuke abude dan uniform nasu short hands ne, gashi small farin baby hijab ne jikinta that covers her chest only, ahankali take tafiya is as if every step datai taking yana kara mata zazzabi harta fito lobby kadan kadan take tafita tana jin sanyi kaman akwai kankara awajen, hakan yasa bakinta yahau kakkarwa irin na me jin sanyi din nan kaman an sata a cold room, idanunta na rawa rawa suna kukkullewa kadan kadan take bude idanunta tasan ta hango mutane zazzaune da suit a lobby daganan kuma batasan meya sake faruwa ba dipp kaman an dauke wuta ta zube awajen.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ8ïžâŁ
Ahankali take bude idanunta dataji sun mata nauyi sosai kafin tagama budesu da kyar tazubasu asaman dakin sake lumshe idanun tayi tabudesu taga drip na ruwa hakan yasa tabi dakin da kallo da kyau, idanunta ne suka sauka kan Riyad dake zaune kan wata kujera mai kyau one seater, wannan karan babu jacket na suit ajikinshi just white shirt da trouser hannunshi rike da wani file yabude yana karantawa ga pen a hannunshi, faduwa gabanta yafarayi kadan kadan hannunta daya ta daga taga anyi fixing drip hakan yasa ta daga dayan hannun takai saman fuskanta sabida iska dataji yana shiganta da kyau jitayi babu hijabinta kan fusnanta babu dan kwali asaman kanta, hannunta takai saman wuyanta zuwa saman riganta taji an bude boturan saman riganta har zuwa wajen bra Allah yasa tasaka singlet sauke hannun tayi kasa tacikin bargo taji an daga riganta da vex din sama cikinta abude ga hook na wandonta an bude ahaukace ta tashi zaune tawani fincike drip din da aka samata taja bargon sama tana kare kirjinta tai wani irin ihuuu tace âmekaminiâ? Sauke file din dayake rikedashi yana karantawa yayi kan coffee table dake gabanshi yakalleta tareda sauke soft boyayyen ijiyan zuciya, yazuba mata mayun idanunshi daidai lokacin tufkin gashinta ya warware black silky hair nata yawani irin zubo half ta face nata ragowan ta baya abun just grip his attention dayasa yawani zuba mata idanu kaman tsohon maye kaman akwai wani abu dayake kallo ajikinta, ihu Rashida tayi sosai taja bargon tarufe har wuyanta tace âyou pervert Allah ya isa ban yafemaka ba wlh mugu azzalumi kaci amanata ta, wat have you done to me? Dame kai drugging dina? Wani substance kasa aruwan daka bani, sabida kaga kanada kudi idan kasaba yima yan mata haka ana kyaleka wlh akaina youâve messed with the wrong person bazan taba kyale wanda ya batamin rayuwana baâ gashi takasa tashi sabida yanda aka kwance hook na wandonta daidai lokacin taji an bude kofa dasauri tajuyo idanunta sunyi jazur wata mata tagani very elderly zatakai 45 tafito daga bathroom na dakin rikeda bowl a hannunta tace âyoung Lady calm downâ ta taho wajen da sauri tana ijiye bowl din da Rashida tabi da kallo taga ruwa ne da karamin towel aciki tace âcalm down no one did anything youâre sick, your fainted and Mr Riyad called, my name is Dr Amara Kennedy, Iâm this hotelâs Doctor, incase of any emergency or anything ni ake kiraâ tadan sauke ijiyan zuciya tazauna bakin gadon tace âcalm down, I came in immediately an kirani, you were running serious temperature dayasa kikai passing out kina convulsing this is the result of your blood testâ tai maganan tana mika hannu ta dauki wata paper dake saman drawer gadon hakan yasa itama Rashida da gabanta ke faduwa sosai ta kalli wajen, taga allurai da magunguna daukan takardan tayi tamika mata tace âtake a lookâ matse bargon tayi da wuyanta tasa hannunta dake rawa har lokacin ta karbi takardan tashiga dubawa Dr tace âkinada high typhoid da Maleria, namiki allurai so I got water ina shafa miki ajiki just to get temperature nata to cool down and for Mr Riyad dakika gani he just came in not less than a minute ago yadubaki saina tashi nima after I cover you up naje bathroom dan na zubar da ruwan and get another oneâ ji tayi hankalinta ya wani irin kwanta saikuma taji kunyan abubuwan data gama fadi, gashi ta gama zage zage kasa kallon wajen dayake tayi ta kalli Dr ahankali tace âI want to go homeâ Dr tace âI think Mr Riyad arrange driver that will take you home, but I think you need to change sabidaâ tanuna mata kafanta da idanu tashi Riyad yayi yajuya yafita daga dakin yace âku sameni awajeâ lumshe idanu tayi jin muryanshi tana kara mugun jin kunyan wat she just did.
Da taimakon Dr ta tashi bayi ta kaita bayan ta dauki gown nata dake jaka she change, kayan kuma ta kulla a Leda tasa ajaka takai gida ta wanke she is feeling better yanzu tareda Dr suka fito waje yana tsaye jikin mota shida Munir suna magana yayi shiru hangosu dayayi har saida Munir yajuyo dan ganin meyake kallo kin karasawa wajen motan tayi tace âI will take kekeâ kafin Dr tayi magana tayi gate da saurinta tafice duk yana tsaye awajen yana kallonta ta tare keke ta shiga sai kawai yabude bayan motan ya shiga ya zauna Munir kuma yadanyi magana da Dr ya sallameta sannan yadawo ya shiga yaja motan sundanyi nisa kadan Munir yace âin tambayeka mana Riyad?â Dago kanshi Riyad yayi ya kalleshi batare daya bashi amsaba alamun yana jinshi, Munir yace âwhy do you give that girl special attention?â Shiru yayi yadauke kanshi ya maida kofa yana kallo sai chan yace âdo i?â Munir yace âyes on different occasionâ wayanshi yaciro daga aljihun gaban riganshi ya shiga dannawa yace âI had no ideaâ shiru Munir yayi yace âbefore you hardly come to the hotel cus I always handle it, office kafi zuwa but tun randa ka ganta anan hotel yazama shine latest head office namu, look at dazu when she fainted you took off jacket naka ka rufamata and just picked her up ka kaita sama kahau kiran Dr without assigning me to do that, not to mention dat day datama yarinya duka normal you dakayi sacking nata but bakayiba, saikai sacking wacce akama duka, are you perhaps interested in her? Cus this is beyond she saved my lifeâ Chak ya tsayan da danna wayan dayakeyi ya tsare screen din da ido kawai that moment na dazu na gashinta na zubowa nadawo mishi rabon dayaga breath taking view haka harya manta sai yau, dan fuzar da iska yayi yasa hannu yasauke glass na motan kasa ahankali yace âIâm not interested in her I just find the girl fascinating! Sheâs a topic!â dan murmushi kadan Munir yasaki yace âokay oo, but wat do you mean by sheâs a topicâ? Wannan karan shiru Riyad yayi yafi nada chan yace âsheâs a topic in my heart that I just feel obligated to studyâ Riyad ma dan rainin wayone Munir yafadi a zuciya jin yanda yake using english yana sugarcoating the word affection dayake developing for the girl but woo idan tai tsami zaâaji ai hakan yasa yace âuhmm topic indeed!â.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 1ïžâŁ9ïžâŁ
Har kofar gidansu me keke yasauketa tasauka tabiya kudi ta shiga gida, anriga anyi magrib Mama na ganinta tabar kunun datakesha ta taso dasauri tace âyaya jikin ne?â Kin fadama Mama ta suma tayi sabida karta tsorata tace âMama naji sauki wlh har allura an mini, kinsha ruwa lpyâ zaunar da ita Mama tayi tasamata kunu karba tayi tashiga sha still bata da karfi Mama bata wani bari tai aiki ba wanka kawai tabarta tayi tana shiga daki ta kwanta ko kaya bata saka ba sai bacci washe garin ranan ma ko school bata iya taje ba, bini bini taita tuna abinda tayi tanajin kunya.
Sai jibi ta tashi garau taje school tadawo dayake tagayama Mama a bata off a aiki bataje ba.
Azumi biyar tasha arana na 6 ranan day 7 taje hotel din sai adduâa take karsu hadu cikin ikon Allah bata ganshi ba har azumi yayi nisa basu kara haduwa ba taji sosai dataji wasu maâaikatansu na cewa Oga umara yaje saisa tunda aka fara azumi baya zuwa itadai ko ajikinta.
Yau saturday morning taje aiki around 2 ta tashi ta shirya ta goya jakanta abaya yau daman hijabi tasaka tunda aka fara ramadan hijabi take sawa hakanan kawai taji kirjinta nata bugawa tana tuna Mama hakan yasa tana shiga keke taciro yar vivo nata ajaka tai dailing number Mama amman harta katse bata dagaba that is so unlike Mama, sake kira tayi shima shiru hakan yasa ta shiga damuwa ko zazzabin Mama yatashi ne?
Abakin junction ta sauka tashigo layin su da kafa tun kafin takai gida ta hango manya manyan motoci guda biyu agaban gidan saikuma taga yaran layi an taru a kofar gidansu some nata fitowa da biscuit da taliya guda guda a hannunsu yanda taji zuciyanta na tafarfasa har sarkakewa numfashinta yake da sauri ta kutsa cikin yaran ta shiga cikin gidan wata babban mace ce tsaye tsakar gidan taci uban lace da duwatsun lace din har kashe ido suke tarike wani arnen jaka a hannunta akalla zatai 45-48yrs gawasu mata haka wanda kana gani maâaikatan ta ne sun rike kwalin taliya a hannu datake rabama yara ga wani buhun local rice akasan tsakar gidan an yatsar da karamin man gyada a jarka, Mama takalla dake zaune kan tabarma sanye da hijabi abinta duk yanayinta yayi wani irin alamun sheâs not happy ganin Rashida yasa tai maza ta gyara fuskanta tace âkin dawo yarinya naâ? Daidai lokacin matan ta dago kanta ta zubama Rashida wani kallo, da sauri Rashida tai wajen Mamanta cikeda tsananin so takai hannunta ta taba fuskan Mama tace âMama did you cry? Sun miki wani abune? Mesa baki kirani baâ? Tai maganan tana daga hijabin Mama tana duba jikinta da hannayenta cikeda so.
Matar dake tsaye tana kallonsu, tawani bushe da dariya tace âakanme zan daki me kanjamau banda yarinta irin nakiâ? Dasauri Rashida tajuyo da kanta ta kalli matar zatai magana Mama tajuyo da ita yace âtashi mushiga ciki tunda kindawo abincin zakka takawo mana nace mata karta damu mun gode, muje ciki idan tagama rabo saita tafiâ Rashida zatai magana matan tace âke har kinyi darajan korana daga gidanki wulakantacciya irinki me bin maza da aurenta nasunnaâ zabura Rashida tayi ta tashi Mama ta taso dasauri takama hannunta tace âke zonan muje dakiâ wani irin dariya matan tayi tace ânaga alama baki bata tarbiya ba saki hannunta dan Allah zan bata tarbiya niâ kama Rashida Mama tayi takomar da ita bayanta tahade hannayenta tace âHajiya Jummai na rokeki da girman Allah kifitan mini daga gidana stop provoking my daughter, banson hayaniya dan girman Allah kitafiâ kallon idanun Rashida tayi yanda take kallonta kaman zata kasheta da idanu to be honest sabida Rashida tazo, Mama batada karfin balaâi kuma banda haka tasan babu abinda Zainab keso aduniya irin yarta Rashida saiso yanzu burinta shine ta nakasa diyar tata itama ta lalata mata rayuwa, da gangan matan ta kalli yaran dasuka cika gidan tace âku nuna matar nan kuce ke tsohuwar banza me HIVâ aiko yaran suka kalli Mama sukace âke tsohuwar banâŠâŠ.â Wani fincike kanta da Rashida tayi daga hannun Mama ta taho wlh watsewa yaran nan sukayi dan ansan halinta suka fice daga gidan dagudu, kaman zakanya tawani tsaya agaban matan tanuna mata hanyar zaure tace âke Jummai fita daga gidan nan tunda bana mijinki bane before I loose my temperâ dasauri Mama tazo takama hannun Rashida tace âke mujeâ cikeda masifa Rashida tace âMama ki banni lemme put this useless woman in her place babban banza kawai yar wahalaâ fizgota ama tayi cikin fushi tace âstop insulting eldersâ itama Rashida cikin fushi tace âMama sheâs not an elder, waye ita dazata shigo gidanmu ta zageki enough! Yanzu ba da bane, I will protect you Mama, Madam ki fita daga gidan nan and take this trash dakika kawo away we have morethan enoughâ tafarfasa zuciyan Jummai yake kaman ta chakamata wuka takeji ta nuna kanta tace âni kika zagaâ? Rashida tace âakwai wata kalanki anan ne?â Kallon yan matan dake tare da ita tayi tace âkuma ita da uwarta dukaâ kambu! Rashida jitayi jikinta yakama da wuta rike ta Mama tayi tasan halinta tace âmuje ciki mu rufe kofa Rashida donât fight themâ ganin yan matan biyu sunyo kansu yasa tawani kama Mama ta maida bayanda daidai sunzo suka kakkawo mata duka dunkule hannu tayi ta zubamusu nushi aciki duk sukai ihu kafin tafara dambe dasu sai kawai Mama ta shiga kuka ganin yanda su biyu suka tarunma yarta dudda Rashida nacin ubansu cikin kuka Mama tai gaban Hajiya Jummai tahada hannunta tace âHajiya Jummai na rokeki da Allah kiyakuri kifita daga rayuwan mu shekaru ashrin da uku munyi zaman kishiyoyi narabu da mijinki tun kafin na haiho Rashida, narabu ashi ko amafarki kinsan bazai kara aurena ba takuran nan ne menene eh?â Daidai lokacin jikake kum kum kum Rashida ta barar dasu duk sun daki bango sun zuzxube kasa a sume goshinsu na jini daga Mama har Hajiya Jumai ihu sukayi Mama tace âInnalillahi wa innailaihi rajiâun Rashida me kikeyiâ?Mama tai wajen da gudu hankalinta atashe tana tattabasu itakuma Haj Jumai tashiga ciro waya daga jaka tace âshikenan ta kashemin bayi, yarki is a killer sheâs a murderer wayyooo jamaâa ku taimakeni sun kashemi yan aiki daga mun kawo musu abincin taimakoâ Jumai tafice waje da gudu tana ihu tana making call before you know it yara da manya an shigo gidansu maza sukai kan matan ana dagosu amman ko motsi basuyi Jumai tashiga nuna Rashida dake tsaye a gefe tace âwlh yau idan Police basu rabamu ba sai nasa kema an kasheki kokuma nakashe uwarkiâ takama Mama zata kai mari wani irin damke hannunta da Rashida tayi ta murda saida tahau ihuuu bana wasaba mazan duk sun kasa tabata sabida tsoron Rashida itakuma tana ihu Mama najan Rashida amman bataji zuciya yakaimata wuya idanunta sunyi jaaa tace âyou keep hurting my Mom tun kafin a haifeni Iâm ready to kill you today to die Mama na tahutaâ kawai takai hannunta dayan takama wuyanta ta matse gam daidai lokacin saita yar sanda macen dake tare da yan sandan tawani rapkama Rashida kulki a baya hakan yasa tasaketa Mama tafashe da kuka ganin yanda aka rafkama yarta kulku itakuma Jumai da gangan tazube tana haki tace âofficer sheâs a murderer daga zuwa basu abinci munga mabukata ne shikenan, macen police din tashiga sama hannun Rashidan ankwa tace âyouâre under arrest for attempt murder na Hajiya Jummaiâ sauran yan sandan suka shiga duba sauran sukace sunada rai but they need hospital, kutafi da me laifinâ fashewa da kuka sosai Mama tayi tai kneeling tace âdan Allah kuyakuri laifinane niku tafi dani not my daughter sheâs a small girl ko aure batayiba dan Allah karku kullemini diya dan Allahâ cikin zuciya Rashida tace âMama stop begging kowa babu Allah cikinsu kitashi Mama, babu wanda ya isa yamin wani abu anan Mama kitashiâ macen police din tace âau haka kikace? Kinyi laifi still kina rashin kunya kina taurin kaiâ? Cikeda dakewa Rashida tace âlaifin me nayi kin tambayeni mesukayi min su? Ko nima bakiga jikina da ciwo ba ne it was self defense, kuma garau suke sabida Ogan su tace karsu farfado ne sukai kaman suma Iâm a doctor I know idan mutum is unconscious, dukanku are corrupt officers working for this evil woman!â Tassss!! Yar sandan ta dauke Rashida da mari da saida tai tangal tangal zata fadi Mama ta tashi da gudu tai ihuuuu tana tare Rashida, Jumai tai wani murmushi kaman an mata busharan aljanna, tarota da Mama tayi yasa bata fadi ba ta kalli yar sandan da idanunta dasukai jazur kaman zata daketa babu ko alamun hawaye, yar sandan tace âke me taurin kaiko? Zan gyaramiki zama muje police station wlh saikinyi dana sanin abinda kikayi dahar yasa na kaiki police stationâ kallon Rank dinta Rashida tayi tace âyar wahala saisa har yau bakikai any matakiba, corrupt evil womanâ zata kara kaimata mari dayan dan sandan yace âstop letâs go to police station tarubuta statement, letâs goâ wani irin finciketa yar sandan tayi daga hannun Mama sukai gaba da ita Mama tabisu da gudu, yanda suka wurgata bayan motan kaman wacce aka kama da bomb suka ja motan Mama na gudu tana binsu harsaida ta fadi akasa duk Rashida na kallo idanunta sunyi kamar jini ganin yanda mahaifiyarta ke wahala all because of this family gidan Sarautan nan, she hates that house da kowa naciki, duk randa tazama wani abu she will ruin them, they will pay for abinda sukama mahaifiyarta, this woman tazo har gidansu ta wulakanta mata mahaifiya duk all because of kishin jakin mijinta Alhaji Mujitapa Baba Ali! Give Rashida few years! I will come for dukanku! I will ruin all of you and gabaki dayan gidan sarautan saina tarwatsashi!!!.
SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ0ïžâŁ
Mama na duke a tsakiyan anguwa tana kuka sosai ana kallonta an taru Hajiya Jummai tazo inda take tsugunnawa tayi takai bakinta saitin kunnen Mama tace âmission accomplished! Now watch how I will ruin rayuwar yarki this is just the 1st step, watch and see how zanyi feeding yarki to those hungry police officers, I will make sure sunyi kacha kacha da duk wani abu daya maidata diya mace, barima kiji Amarya na aikamusu yau akwai bikiâ tawani kwashe da dariya, juyo da kanta Mama tayi ta kalleta irin kallon nan na bakomi akwai Allah sannan tace ânabaki raina ki dauka Jummai, yau kidauki wuka ki sakamin aciki na mutu na yarda, kome kikeso kiyi dani kiyi amman spare yarinya na, sheâs a small girl, meta miki? Mijinki dama tun tana ciki yace ba tasa bace haryau ko fuskanta baitaba ganiba to meta miki? Sheâs not a threat, sheâs a small child kulleta a police station will ruin her life, Hajiya Jummai banda kowa sai ita, kiyafema Rashida ni kisa a kulleniâ murmushi tayi tace âkinga I hate you with every blood na jikina saisa I want to end you using abinda kikafi komi so, wlh wlh ko kudina zasu kare yau saina tabbatar an yaga yarki a cell, wlh sainasa sun maidata nama, saina tabbatar sun halakar da rayuwanta tass, maybe then na hakura nasa afito da ita kokuma na aikata prison she need to be taught a lesson, ke I will cook her up bazata fito daga cell anytime soon ba, this is for auren Mijina dakikayi!â Tana maganan ta tashi tawuce wajen mota ahankali Mama tajuyo da rinannun idanunta ta kalleta ga mamakin Mama saitaga yan matan sun taso fess da kafansu sun fito sun shiga mota direba sun yatada motan sun tafi, Ahankali Mama ta tashi wani kalan bubbugawa zuciyanta keyi dabai taba mata arayuwanta ba, yan layin sai kallonta suke mata an lalleko daga gida tanaji ana kananun magana ana dama maraji makomarsa kenan anzo baku abinci mu makota mun shaida but yarki tazo tana dukan mutanen arziki ai gashinan tahadu da daidai da ita, gida Mama ta shiga ta tattaro duka kudin dasuke dashi tasan belin mutum da kudi akeyi sunada 80k agida a account din Rashida kuma akwai 100k da aka mata salary na hotel just jiya 50k ake biyanta but sallan nan sai aka basu 100k, sakawa tayi a lalita tasa takalmi tafito ta kulle gidan ta shiga tafiya bama tasan wani police station aka kaita ba, tafiya take a anguwa wasu nacemata Allah kiyaye gaba wasu na Binta da kallo Adamu me chemist ne yafito hangota dayayi dan shi yana mutunci dasu yace âMama Allah kiyaye gaba ina zaki yanzuâ? Bama ta iya magana sai hawaye bakin hijabinta tasa tace âbansani ba duk police station dana gani zan shigaâ dasauri yace âina ganin kije head quarter dan naga babban police car suka zo dashi sabida local street police post baâa ijiye musu manyan motoci haka, Allah kiyaye gabaâ gyadamai kai tayi ta wuce ta tare keke ta shiga 500 aka kaita headquarters.
Sauka tayi tashiga ciki ta tafi chan gaban kanta yan sanda dake wajen sukace âlafiya Hajiyaâ baki Mama tabude zatai magana sai kuka matar tace âHajiya dan Allah kifita ki gama kukan saiki dawoâ dasauri dayan dan sandan yace âmehaka Grace? Mama lafiya calm down meya faru fadamanaâ? Da kyar ta tsagaita kukan tace âyâata wasu yan sanda suka kama kusan minti talatin kenan bansan inda aka kaitaba yan anguwan mu since nazo nan headquarterâ mutumin yace âya sunan diyar takiâ? Ahankali tace âRashida Almustaphaâ log book dake gabansu yaduba yaga sunanta kafin yayi magana Grace tace âbanan aka kawota ba kije wani police station dinâ kallon Matan Mama tayi saikuma ta kalli wanda ke attending to her ahankali yace âMama je waje ki zauna ina zuwaâ fita waje Mama tayi tasami waje ta zauna, kirjinta bugawa yake like never before ga azumi abakinta wlh kusan 2hrs tai spending awajen dan har 5 tayi sannan yafito yazo wajenta yace âzo gefe Mamaâ Dasauri Mama tabishi ahankali yace âMama bansanki ba amman kin bani tausayi wlh tuntuni sai bin office daban daban nake ama barki kiga diyarki sunki, wai yaran data daka suna ICU, sannan she attacked officer mu wata and abuse herâ cikeda tashin hankali Mama tace âwlh wlh karyane sherine agabana yaran suna shiga mota da kafansu basa ICU, kuma wlh Rashida bata taba police dinbaâ ahankali yace âto yanzu dai bani dubu goma zan taimakeki da kyau koda yarki zata kwana zansa ido akanta kar acutar da itaâ fashewa da kuka Mama tayi tana tura hannu alalita ta kirgo 10k tabashi ya karba yace âbari kiji Mama the truth is powerful mutane sukasa aka kulle miki yarinya dan haka yanzu dai idan kinada wani babba haka kije kitaho dashi ko zaâa miki alfarma abaki belinta inba hakaba wlh bazama kisan yarki na nan ba ninedai nafada mikiâ yanda Mama ke kuka sai yataba zuciyanka tace âwanake dashi? Banda kowa sai Allah niâ dan sandan yace ânidai nayi miki iya nawa kije ko waye kisamo, suna ganin kalan kudi ajikinsa zasu badata, bari nakoma ciki kada anemeniâ wucewa yayi yakoma ciki yabar Mama wajen tsaye shiru Mama tayi saikuma ta daga idanunta takalli sama irin kallon Ya Allah kana ganin komeke faruwa sannan tasa bakin hijabinta tashiga tafiya tawuce gate kafanta yayi butu butu da hijabinta ma sabida zaman kasa datayi sai tunani take ina zata shagon Mama miwa tane tunda tanada kudi but tace baruwanta da police station bata zuwa, Rashida tafada mata tace taji ance Riyad na Umara saisa batai tunaninsa ba.
Bari taje ta gwada yima manager magana kozata taimaketa gashi Baba Liman yaje kauyensu shima duba gona, adaidaita tasake shiga ta tafi hotel din hanyar shiga taje yauma wasu security daban ne dana ranan suna ganinta sukace âina zakiâ? Arude Mama tace âmanager zan ganiâ wani kallo suka mata daga sama har kasa sannan sukace jira anan daya yashiga ciki yama manager magana tafito daga office nata hango Mama tayi daga glass door tace âI donât know her, please send her away yau banda lokacin all this beggars Iâm very busyâ takoma office security yafita yaje inda Mama take tsaye yace âbatananâ tsayawa Mama tayi tana kallonshi yanda taji kaman jiri na neman dibanta batasan sanda ta duka ba saitahau kiran sunan Allah. âAllahumma ajirni fi musibatiâŠâŠInnalillahi wa innailaihi rajiâun, Ya Allah kadubi yarinyana dake cikin cell kar awani abu yasameta please karsu cimma burinsuâ tashi tayi tana taba bango kawai kaman kanta ya kwance takeji cus batada hope kuma yanzu sai magana take ita kadai. âRashida na is scared, yarinyana bata taba zuwa police station bama, yanzu tanachan locked up a cell an ciremata slippers, an karbe komi nata, hala ana azabtar da itama, idan suka batama mata rayuwa fa, wat if they rape her? My poor baby must be so scared yanzu, yarinyana batada kowa aduniya sai ni, wat are they doing to my child right nowâŠâŠâŠ.â Diiiiiiiiiiiiii! Taji karan ana daddanna mata car horn dayasa kawai ta birkice hannunuwanta tadaura saman kunne ta kulle idanunta kawai tahau juwajuwa akan titi go slow kawai yahadu bama tasan meke faruwa ba, âMamaa!â Taji an kira sunanta da karfi dasauri tabude idanunta dasukai jazur, Riyad tagani tsaye agabanta yana sanye da farin shadda datasha aiki kanshi da kula ganinshi kawai saita fashe da kuka sosai ahankali yasa hannunshi yasauke hannayenta daga saman kunne ganin sheâs not herself yakama hannuwanta duka biyun sukabar tsakiyan titi zuwa motanshi yabude baya yasata shima yashiga bayan wani bodyguard dake tukanshi yaja motan suka gangara gefen hanya yayi parking, Riyad dake kallonta yace âMama menene? Why are you in the middle of roadâ? Bakinta rawa yake ta birkice kawai tace âRiyadâŠâŠ.RiyadâŠâŠ.Riyadâ hannunta yakama ahankali yace âget me waterâ fita direban yayi anatse Riyad yace âMama calm down Iâm here now, calm down everything will be fine, calm down Mama kinjiâ bakinta is still calling name nashi, ahankali yace kice âInnalillahi Wa Innailaihi Rajiâunâ ahankali Mama tace âInnalillahi wa innailaihi rajiâunâ dan natsuwa tasamu kadan daidai lokacin an kawo ruwan budewa yayi yabata tasha kadan sannan yace âwat happen Mamaâ? Fashewa da kuka tayi tace âtasa an kamamin yarinya an kulle a police stationâ anatse yace âwaceâ? âKishiyata wacce mukai zaman aure tare kafin mijinmu ya koreniâ? âWat happened Mamaâ? Labari Mama tabashi tundaga time datazo gidan da time da Rashida ta shigo, da all abinda yafaru da duka abinda tagayama Mama na zatai feeding Rashida to yan sandaâ jiyayi ranshi yayi tsananin baci, âdriveâ yafadi ahankali yama Munir text dan daga gidansu zuwa head quarter is even closer than daga nan hotel zuwa wajen.
Wajajen magrib sukakai police headquarter ya kalli Mama yace âMama ki zauna anan zan fito da ita kinjiâ gyadamai kai Mama tayi ya kalli security yace âmake sure she stays in the car sheâs not feeling wellâ âyes sirâ ya amsa yana fita yaga Munir yafito daga tashi motar ga sauran bodyguard nashi yayi gaba kawai Munir da guards nashi na binshi abaya, all eyes yadawo on them ko kallon yan sandan wajen baiyiba yawuce sama direct zuwa office na inspector cus yasanshi sosai yana kawo gaisuwa fada dudda bai sanshi babu rawani ba, kai tsaye yabude kofan ba knocking babu komi Inspector na zaune yana dube duba, da zafi sosai an anger kan muryan Riyad yace âI will sue you and I will sue the entire police headquarters for rashin adalci for tauye hakkin talaka, for rashin yin investigation, I will make sure anyi sacking all of you anyi replacing naku with better and eloquent officers dasuka shirya yin aikinsu yanda yakamataâ from yanda yake magana kadai yasa gaban Inspector yashiga faduwa yama kasa magana, Munir yace âyou must be confuse kana magana da Mai Martaba SARKI RIYAD! Sarki mai adalci, sarkin talakawaâ wani kalan tashi inspector yace âan gaida Mai Martaba Allah huci zuciya ka, tubâŠâŠâ hannu Riyad yadagamai yace ârelease Miss Rashida Almustapha, and nabaka 24hrs kuyi realeasing evidence cewa yaran data daka suna ICU with Doctors report and everything, and again inaso kuyi proving cewa sheâs really a killer, banda haka I want to know wat right that officer takedashi to slap and hit Miss Rashida, and again wanda aka bishi har gida shine akaje neman tsokana, prove all this ba set up bane inba hakabaâ Munir yace âzaku hadu da bacin ran Mai Martabaâ baki Inspector yabude zaiyi magana Riyad yadagamai hannu for the second time yadakamai tsawa sabida yanda ranshi yake abace yace ârelease her now!!!!â Shi kanshi Munir saida ya kalli Riyad rabon dayaga dan uwanshi yayi fushi haka harya manta, da wuya Riyad yayi fushi, jikinshi har rawa Inspector yake yafita dasauri shi baimasan case din ba duk suka bishi yawuce kasa Riyad na biyedashi yadauki key na kofan da ake budewa a shiga bangaren cell nasu yabude kofan da sauri ya shiga saikuma ya juyo yace âAllah taimaki ranka shi dade ban santa ba ita yarinyarâ wuceshi Riyad yayi kawai yashiga ciki mutumin ya bishi abaya cell cell ne daban daban, na mata daban na maza daban but duka ajere suke, ga mutane kukkule amman baiga Rashida ba in any of cell na mata dasuka wuce ba, zagawa dashi Inspector yayi zuwa cell masu kama dana kaji ana kiran dakunan NO SS CELL wato no sitting no standing cell, wanda shi na punishment ne bazaka iya tsayuwa ba bazaka iya zama ba kana duke kawai idan anaso a azabtar dakai ake kaika wajen, hangota Riyad yayi ita kadai an rufeta a cell dayakenan kaman cell din dan buri alalo alalo gwanin ban tausayi she looks very very miserable and terrible ko kadan bata kallo inda suke ba danta dauka matarce tadawo, ahankali Inspector da gabanshi ke faduwa ganin ita kadai ce abarayin NO SS yace âitace naga kana kallontaâ? Juyo da kanta Rasheeda tayi jin datayi anyi magana tunda ta shigo wajen sai yanzu taga haske hasken Riyad dake tsaye yana kallonta idanunshi sun chanza launi kallo yake mata dabazaka iya tantance na menene ba, ahankali yake kallonta even though sheâs not crying but kasan sheâs very very scared, sheâs terrified, sheâs lonely, sheâs afraid, dauke kanta tayi daga kallonshi da sauri tashiga wasa da fingers nata, bude kofan Inspector yayi yace âfitoâ kokarin motsi tayi da kafa amman takasa sabida yanda kafafunta suka sankare suka rike sai kawai Riyad yaji zuciyanshi ta tsinke awani irin hankali yafara tafiya dudda bata kallonshi but every step nashi tana jinshi har a bangon zuciyanta, ahankali azo gaban cell din ya tsaya chak still taki dago da kanta, yakai wajen 10secs yana kallonta kafin awani irin hankali yaciro hannunshi daga aljihu yamika mata cikin wani irin murya mai masifan taushi yace âRasheedah!â Har kasan zuciyanta taji yanda yakirata hakan yasa tadago kanta takalleshi sannan takalli hannunshi dayake mika mata batare data karbi hannunba, ahankali yace âcome Mama is waitingâ dasauri ta kalli fuskanshi kafin awani irin hankali takai hannunta tadaura gently kaman mai tsoro cikin nashi, atare dukansu sukaji shock amman yadaure yakamata sannan ya fizgota tashi daya tafado kirjinshi making deep sound mara kara sosai dazai nuna how hurt sheâs, kafafun na mata ciwo sosai amman sabida dauriya da taurin rai taki nunawa but takasa motsi tana kirjinshi, dan sauke kai Inspector yayi aranshi yace âbudurwan mai martaba muka kulle dama? Suwaye keson sani a balaâiâ takai one minute a kirjinshi batare daya taba bayanta ba banda hannunta daya rike but ita takasa motsa kafan tafita daga kirjinshi, in a very caring tone dabama tasan yanada shi ba yace âcan you walk nowâ? Duk yanda taso karta kalleshi kasawa tayi tana kirjinshi tadaga fuskanta takalleshi hada idanu sukayi cikeda tsananin kulawa yace âcan you walk yanzu?â Very soft itama ta gyadamai kai tana yunkurin fita daga kirjinshi, saitai baya zata fadi dasauri yakai hannunshi daya yakama waist nata sai kawai adake yakama hannunta daya yakai ta bayan kanshi ya ijiye yayi supporting nata dakyau kafin yace âletâs goâ sheâs scared internally, sheâs shaking bamata da karfin wani abu so she just followed him tana dan dingishi suka fito ahaka.
Hannu yasa yabude kofa mutanen data gani awajan da yawa gasu police gawasu kaman bodyguard ga Munir datake gani a hotel nasu ga yan sanda maza biyu na dazu bataga macen ba yasa tadan yunkura cikeda karfin hali zata fita daga jikinshi kaman daga sama taji saukan hannunshi akan waist nata yamaidata side nashi da kyau dawani irin sauri tadan juyo da kanta ta kalleshi but fuskanshi is looking straight bayako kallonta yacigaba da tafiya da ita hakan yasa ahankali ta maida kanta kasa daidai sunzo kofan fita saiga yar sandan dazu tana shigowa itama suka hada ido wani abu Rashida taji yazo mata wuya ya tsaya duk kalan ciwon da kafanta ke mata amman saida taji tasami karfin daga kafan kawai takai ta kwasheta within a blink of an eye jikake tippptipp! Officer tai wani mummunan faduwa danko ita bata lura da kafan da Rashida tasamata ba dan fuskan Rashidan take kallo dana Riyad datagani tareda ita, da all the people dake wajen, yan sandan sukai kanta ganin kalan faduwan datayi ana âlafiya kika fadi haka sannu me kike kallo hakaâ dan babu wanda ya lura da abinda Rashida tayi dagowa officer tayi hancinta na jini ta kallo kofan hada ido tayi da Rashida dake mata kallon munyi settling score dake, tsayawa shima Riyad yayi yana kallon Rashidan cus he saw wat she did saikuma kawai yacigaba da tafiya da ita suka fice har wajen motan shi su Munir suka biyosu baya yabude baya Mama idanunta harsun kumbura na zaune taganshi da Rashida dataga har yar rama tayi, sai kawai Mama tafashe da kuka jikin Rashida yayi mugun sanyi da taimakonshi ta shiga bayan motan sai kawai ta rungume Mama dan jim yayi yana kallonsu kafin ya maida kofan bayan yarufe yajuyo yadan taka zuwa wajensu Munir dake kallonshi kallon what is going on, anatse yace âI will see you at home bari na kaisu gidaâ bai jira amsan Munir ba yajuya yawuce saiya shiga gaba direban yatada motan yaja har lokacin Mama kuka take wlh takasa magana ma, hakuri take ta bama Mama amman yana shigowa tayi shiru kawai dai ta rungumeta agaban wani pharmacy yasa aka tsaya yafita yashiga yakai kusan 10min aciki yafito rikeda leda yadawo ciki ya zauna aka tada motan har zuwa anguwan su parking yayi yabude gaban motan yafito yabude bangaren Mama ahankali Rashida tasaketa goge fuskanta tayi ta sauko sannan ta mikama Rashidan hannu tace âtaho mujeâ cike da karfin hali ganin yana wajen yasa tace âni zan iya fita dakainaâ tsayawa Mama tayi tana kallonta irin kallon wani irin taurin kai da karfin hali Rashida kedashi ne, shima Riyad folding hannunshi yayi a kirji ya tsaya kawai suna kallonta jan jiki tayi har tazo bakin kofan ahankali ta daga kafa daya tafito hakama dayan sannan ta yunkura ta tashi dudda sheâs not showing the pain a fuskanta but wlh kasan da kyar take komi takawa tashigayi ahankali sai kawai tawuce tai zaure da dafa bango ta shige cikin gida, Mama tabiyota abaya tana shiga rabin buhun shinkafar taci karo dashi a tsakar gidan nasu jitayi zuciyanta kawai yarikice ranta yabaci tama manta tanada ciwo kawai tai wajen shinkafan azuciye ta daga shinkafan zata mike kafanta yayi wani irin kara da duk dauriyanta saida tai ihu daidai lokacin Riyad ya shigo gidan azuciye yayi wajen yasa hannu ya fizge buhun shinkafan yayi ihu yace âwhat is your problem?â Kallonshi tayi ido cikin ido tace âmezamuyi da shinkafarsu? Zubarwa zanyâŠâŠ.â âQuiet!â Riyad ya daka mata tsawa da saida taji jikinta yayi rawa, cikin tsananin fushi ya nuna Mama datake rabe a bangon zaure kawai ta tsaya chak tana kallon yarinyar tata gwanin ban tausayi, irin kallon yaya zanyi da wannan yarinyar ya Allah, yace âcan you give your Mom just a minute of peace?â Kallon Mama tayi saikuma ta kalleshi zata bude baki authoritatively Riyad yace âI said quiet!â Cikin kwayar idanunshi ta kalla the anger datake gani da fushi kawai saitaji takasa magana wani bai taba shutting nata up in her life ba sai yau, cikeda tsananin bacin rai yace âkina tunanin komi arayuwan nan you settle it da fada da duka you think is by fighting?â Yasake shiru saikuma ya lumshe idanu tareda fuzar da iska yasake kallonta yace âevery action have consequences do you for once sit down kiyi tunanin waye ke suffering consequences na action naki?â Yadan mata ihu kadan still kallonshi take da manyan idanun nan nata, saiya sake nuna Mama dake tsaye looking at them tana goge hawaye da bayan hijabi yace âdo you have slight idea of abinda Mamanki went through today? Did you even know an ina naganta?â Yasakeyin shiru saikuma a sanyaye yet da tsaurin harshe yace âdo you even love your mother?â Wani kallo datamai har saida idanunta sukahau sparking sabida anger kaman zata rufeshi da duka, cikin fushi tace âkai waye dazaka tambayeni ko inason mahaifiyata, waye kaiâ? Cikin tsatsauran murya Mama tace âtamaka rashin kunya ka yanka mata mari Riyad!â.
RASHIDA IS STUBBORN CUS WATTđ„
SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ1ïžâŁ
Kallon Mama Rashida tayi zuciyanta yafara tsinkewa ganin shi Mama take supporting tabude baki zatai magana saitaji kuka na son subuce mata hakan yasa tarike maganan da kyar ta danne kukan tace âto sai in tsaya ina kallo ana zagin Mamanaâ? Rai abace Riyad yasa hannu a lips nashi yace âshushâ abu taji yazo mata wuya wayeshi dahar zai dinga mata fada agidansu kuma Mama na supporting nashi sai kace wani Yayanta, dauke kai tayi daga kallonshi tana huci kaman damusa yace âzagi baya kari, zagi baya chanza fatan mutum, you are a very selfish girl that care about feelings nata not her motherâ wannan karan juyo da kanta tayi ta kalleshi idanunta sun ciko da hawaye amman tahanasu zubowa shima yana kallonta kyar yace âduk yaron daya gwammace yabi zuciyanshi dayabi maganan Mamanshi is selfish! Your mother is sick! Anything daya shafeki affects her greatly, akanme bazakiyi hakuri ba just for her safety and wellbeing huhh? And kince kinason Maman ki? Your are just a terrible selfish daughter wacce ta damu da ego nata not her motherâ shima yayi maganan idanunsa na ja Mama kawai kallonsu take bata tabajin tanason Riyad kaman yanda taji tana sonshi ba yau, cikin fushi yace âyour Mom nada BP very high BP, kwanciyan hankali takeso but kullum cikin tashin hankali take sabida ke! Kullum fitinan ta kike da fitinu daban daban do you want to kill her?â Daidainan hawaye ya zubo sharr daga idanunta da sauri ta dauke kanta tasa bayan hannu ta share, cikeda fada yace âI saw your Mom at the middle of titi bamatasan metakeyi ba she was panicking calling your name, yarinyana! Yâata, da kinfito daga police station kinga ta mutu fa?â Takawa yayi zuwa inda take facing ya tsaya chak agabanta adake hakan yasa ta kalleshi da rinannun idanunta ya nuna mata yatsu cikeda wulakanci đđ» yace âtake this as your last and final warning, idan kika kara troubling Mama zanzo I will take her away from you na kaita inda zaâayi cherishing nata forever, sannan abata peace of mind data rasa daga wajenki, I dare you ki kara trying wani nonsense hali dazai tadama Maman ki hankali saina sabamiki you selfish egotistic girl!!â Yana maganan yajuya zuwa inda Mama take a zaure cikeda so yace âmuje Mamaâ juyo da kanta tayi ta kallesu abunda taji tuntuni yana wuyanta kawai taji yazo mata baki da sauri tajuya tashiga daki tawuce uwardaka sai kuka taji kawai ta tsani Riyad, kishi yakamata yanda Mama kaman tafisonshi sama da ita, heâs making her look like a bad daughter.
Zaunar da Mama yayi akan tabarma sai ya zauna a gefenta yace âMama kidena damuwa kinji sheâs fine babu abinda yasameta, itakuma Matan zansa anemota she will pay for abinda ta mukuâ dasauri Mama ta girgizamai kai tace âRiyad tunda ka karbomin Rashida kabar mutanen nan da halinsu duk inda kake tunani sun wuce haka I donât want to involve you a matsalanmu this people are terrible and very powerful banso sumaka wani abu, kamin alkawari bazakasa anemota ba, kabarta da halinta, karma ka koma police station din, bawai koda yaushe take damunmu ba, rabonta da gidan nan kusan 5yrs ago sai yau datazo maybe sai nan da another 5yrs kuma zata kara zuwa, banson wani tashin hankalin banson damuwa, banda ma karfin zuwa police station bada statement, haka kuma banso Rashida taje police station wazai aureta? It will ruin her life? Cell din nan kadai yanzu ma yayi ruining life nata yan anguwan nan babu inda bazasukai labarin ba, Iâm tired of all this, I keep causing pain arayuwanta, nice darkness na rayuwanta, nasan Rashida bataji sheâs stubborn but she became like this sabida ni, no body wants to be friends da ita, no body wants to marry her, koyaya wani yazo nemanta Sheri da gaskiya sai yan layin nan sun tara sun fada akanta yanzu kuma dataje cell we are ruin gabaki dayaâ Mama ta share kwallan daya zubomata saikuma tadaga kai ta kalli Riyad da fuskanshi yayi kaman zaiyi kuka tace âRiyad kamin komi arayuwan nan wanda har dan uwana na jini bemin ba, thank you for everything, thank you for saving my daughterâs life, nagode Riyad kaji, but donât involve kanka in our personal family issues is not worth it, babu amfanin shiga 23yrs of matsala kana shiga zata dawo sabuwa I hope you understandâ? Shiru yayi sai chan ya gyadama Mama kai yace âI understand Mama nabar case din but duk randa tasake zuwa I wonât spare herâ murmushi Mama tamai tace âtashi kaje gida kaima ka huta gobe salla, kasha ruwa Allah maka Albarkaâ wlh har cikin ranshi heâs feeling very attached to Mama kaman karya barta ahaka amman yadaure ledan Pharmacy dake aljihunshi yaciro yabata yace âgashi Mama na kafanta neâ yayi maganan yana tashi yace âsaida safe Mamaâ kallonshi kawai Mama take cikeda kauna tace âsaida safe Riyad ayi salla lafiyaâ sannan takalli ledan pharmacy din tana tuna yanda yama Rashida fada yanzun nan saikuma tai murmushi.
Gyara zama Mama tayi tai shiru ita kadai awajen Allah kadai yasan tunani tunanin metake bini bini tasa hannu ta share hawayenta dayake zubomata, ruwan dabatasha kenan ba, har wajen 12 na dare ita kadai, sannan ta tashi da kyar tawuce tayo alwala kanta kaman zai cire tashiga daki tadauki pure water tasha sannan tahau dadduma azaune tai sallan tana idarwa tashiga uwardaka akasa taga Rashida na bacci ko hijabi bata cireba tsabagen fitina, zama tayi wajen ta yaye skirt na jikinta tadauki ledan ta ciro man shafawan daya siyo Mama tai shiru tana kallo saikuma ta kalli fuskan Rashidan ahankali tace âstop this madness and see Riyad Rashida, is because youâre hurt abin yakara batamai rai yake miki fada not just sabida ni kadaiâ dan murmushi kadan Mama tayi tace âheâs romanticâ saikuma takai hannunta saman bakinta kaman mainin kunya tace âke Zainabuâ budewa tayi ta lakato ta shafa mata maganin a kafafunta sannan ta ijiye maganin saikuma tai tagumi tana kallonta adduâa kawai take Allah yarage mata zafin zuciya da yawan fushi din nan kar watarana fushi yasa tai kisan kai yanda ta watsar da matan nan biyu dazu ga jini a goshinsu Mama ta girgiza ainun batasan Rashida tayi nisa hakaba.
Har asuba tayi Mama bata kulle idanu da sunan bacci ba.
Ahankali tabude idanunta jin an tabata ganin Mama sanye da hijabi tai alwala yasa ta tashi zaune da sauri ahankali tace âMamaâ kallonta Mama tayi saitai shiru bata amsaba kaman irin da abin ta kwana hakan yasa tafashe da kuka mai karfi tace âMama dan Allah kiyakuri ki yafemin bazan kara miki rashin ji ba, kome kikace nayi zanyi, Mama everything is my fault, danaji maganan ki dakikace nabari nabarsu munshiga dakin da duk haka bai faru ba, Mama da mota ya kadeki dame zan gayama Allahâ? Yanda take kuka wlh saita baka tausayi Mama taso yau ta shareta Amman saitaji bazata iyaba saita zauna tace âkimin shiruâ tsagaita kukan tayi tana kallon Mama da rinannun idanunta, ahankali Mama tace âyawan fushi nasa kai abu da dama dazakai nadama Doctorâ cikin raunin murya tace âMama u hate that woman, I hate mijinta, I hate entire family nasu, those people made you suffer all your life har yanzu kuma basu barkıbaâ Mama na kallonta tace âidan zaki bimin hakki na ne then kiyi focusing a school, ki gama school ki zama wani abu, ki nuna musu cewa Mamanki dasuka wulakanta ta haifoki diya me albarka me goshi, ki zama Dr tukunna and cure me kinji kidena fada da mutane akaina focus on goal naki nan gaba na warke no body can troll me rightâ? Gyadama Mama kai tayi Mama tace âbansan ko zamuyi rayuwa tare har karshe ba babu wanda yasan gobe ke babu wanda yasan anjima ma, idan bana raye kikai wani abu who will protect you and stand by you? Ayau dudda banda wani abu but at least I use strength dina na shiga gari ina neman wanda zai taimakeni ya tsayama diyata but randa bananan fa? Who will fight for you and stand by you? Lokaci yayi dazaki bar halin nan, ke kadai gareni kene komi nawa if something happens to you I die, jiya I was so scaredâŠ..â saikuma tafashe da kuka dayasa Rashida ta rungume Mamanta da gudu tace âMama itâs okay bazan kara ba kinji, Iâm here now Iâm fine kinga kafan ma naji ya warke tassâ ta shilla kafan sama Mama tace âmaganin da Riyad ya siyamiki neâ haderai tayi da sauri tace âMama wlh na tsaneshi baida kirki niyake gayama zai rabaki dani yana kirana selfish daughterâ ahankali Mama tace âhe did the right thing, kuma kika dameni zan bishi dagaske, Allah yamai albarka daya miki fada, naji dadi da akwai wanda zai iya miki fada haka kiyi shiru dan gani kike kaman kinfi karfin kowaâ tashi tayi sabida bataso tace wani abu tasake batama Mama rai kawai tawuce tafita.
Alwala tayo sai yanzu ma ta Tuna ki ruwa batasha ba jiya to waka yasha? Har Mama ma batasha ba Tana salla tafita tea tahada musu sukasha sannan takaima Mama ruwan wanka tadawo tadawo ta gyara gidan ciki da waje tsaf Mama tace âzoki wanka karmu rasa sallan idi idan muka dawo mayi girkiâ.
Wanka awuce tayo tadawo atampanta na salla data karbo fara wajen dinki ta warware skirt da riga ne blue pink atampa ne tasaka da sabon bra da pant tayi kyau sosai dudda batai lalle ba daman jiya sukace zasuyi but Allah bai nufa ba, ta daura dan kwali Mama tace âzauna kisa kwalli ki shafa jan baki kodan darajan yau sallaâ batai musu ba tazauna tajawo basket na kayan kwalliya tadauki kwalli tasaka tadau wani pink tsohon jan bakinta ta shafa ta gyara gashinta wanda shi ta wanke abayi yanzu da safen nan ta shafa mai ta taje tai parking sannan ta daura dan kwali ta fesa turare ta tashi sai Mama dake kokarin sa hijabi tabita da kallo batasan lokacin datace âtubarkallah Allah ubangiji ya nunamin aurenki haka kici gayu kısa kayan amareâ turo baki tayi taki amsawa tadauki pink hijabin data dinko na salla tasaka ta dauki dadduman su da yar wayanta suka fito rufe gidan sukayi da kafa sukaje masallacin ana salla ana kaiwa sujud Mama tashiga rokon Allah yabama Rashida mijin dazai sota ya tsaya mata yakuma kula da ita, sallamewa akayi suka wuce kasuwa kaji guda biyu suka sayo da kayan Miya da fulawa dasu butter sannan suka shigo keke suka tafi gida suna dawowa ta shiga kiciniyar hada gawayi dan daura abinci ganin gawayinsu saura kadan gashi tasa abinci a wuta yasa tarike kudi a hannu tawuce zaure dan neman yaro ta aika makotansu yakawo mata gawayi, tana sakai awaje karaf suka hada ido da Riyad daya bude kofa yafito daga cikin mota yana sanye da manyan kaya da babban riga da hula bugawa kirjinta yayi sabida yanda yayi kyau na balaâi, sai kawai ta tsaya chak ita takasa komawa ciki ita takasa motsi ita takasa daina kallonshi, har saida shi yadauke kanshi daga kallonta akufule yace âkifito yan duniya suga kwalliyan sallan da kyau!â Runtse idanu yayi dan baisan ya akayi maganan tafito daga bakinshi ba, saikuma yahade giran sama da kasa yajuyo yamata wani irin kallon da kawai taji tajuya da sauri takoma cikin gida kirjinta na bugawa dim dim dim chan sai ga sallaman yaro yashigo da kwalin kaji yace âgashi wai inji Riyad aba Mamaâ afadace Rashida tace âKai maidamai kace batananâ yaron yace âai yashiga mota yatafiâ ranta taji yabaci daga daki Mama tace âijiye zo ga tukuiciâ dasauri yaron ya nuna new 1k note dake hannunshi yace âai yabani dubu dayaâ yajuya yafita abinshi, hijabi Rashida ta dauka tasaka tafita ganin bayanan yasa ta shiga makota tasayo gawayi tana dawowa taga Mama tacire just 3 acikin kajin da an gyara but baâa yayyanka ba tace âdauka sauran kikai gidan Baba Liman kice kawo mana akayi karsuki karbaâ batai musu ba ta dauka tawuce takai a zaure tahadu da Liman yace âjiya naje kauye saida nadawo naji abinda yafaru Allah kiyaye gaba ki gayama Mamanki zan shigo anjima da yammaâ gyadamai kai tayi tawuce ta koma gida lafiyayyen girki tayi tai dambun naman kaza ta soya some tai pepper chicken da some, tai jellof rice tai cincin around 4 tagama komi ta shiga daki ganin Mama duk bata wani cicciba yasa tace âMama baki cibaâ ahankali Mama tace âkaina kedan ciwo anjima ya sauka zan shaâ kallon Mama tayi saikuma ta zauna kusada ita tace âMama kedai sabida ina chan ina aiki ne yasa bakiciba, bude bakinki kigaâ ta deba rice din takai bakinta dan murmushi Mama tayi tabude ta karba just to make her smile ta yarda taci amman ko taste bataji na abincin ba.
Har ishaâi hira sukeyi around 9 tai bacci awajen Mama tabita da kallo sannan ta lallaba ta mike tana dafa bango kujera ta dauka da buta tawuce chan bakin makwarara amai ta kwara sai ijiyan zuciya takeyi ta wanke fuska tadawo daki kafafunta ta kalla da tun dazu da rana sai zugi suke mata gashi ta lura sunata kumbura, yanzu ma sun karu sai kawai ta zauna tai tagumi tana kallon Rashida damuwa da fargabanta data shigane yasa kawai taji jikinta yanaso ya rikice haryakai ga abinci ma bataso, tunani take, takasa manta maganan Jummai, dudda tahana Riyad karyay involving kansa a case din tasan yanda aka ciro Rasheedan nan that woman will find a way ta cutar da Rashida Alkawari ne wannan! Sheâs just scared for yarta, idan tafita school aka dauketa fa? Idan aka halakata fa? Idan tasa akama Rashida wani abu fa? Wat if she set Rashida up yanzu ta yanda zata tura mata yarinya prison inda ko Riyad bazai iya cirota ba, abinda ke kara firgitata is zuciyan Rashida just like yanda tazo jiya ta takali Rashida and she fell for it still haka zata karayi Rashida kuma ba hakuri taje tai wani abu shikenan akamata akai prison with concrete evidence. Yaya zatai protecting Rashida? Kodai su saida gidan su koma kauyensu dudda Kawu ya koreta ada dasuka je? But makarantan Rashida fa, itafa asibiti fa, auren Rashida fa? Riyad fa? Batama Rashida kwadayi tai auren kauye, tanaso diyarta tazama wata babba aduniya, but idan matan nan ta turo maza suka dauke Rashida sukai amfani da itafa suka lalata mata rayuwa tunda dai burinta na police station bai yuwuba, tayaya zata kare yarta? Dudda Rashida akwai karfi akwai zuciya but maza maza ne! Idan akai kidanapping Rashida yanzu yaya zatayi? Tunani daban daban take sai kawai jikinta yasake rikicewa har aka kira asuba yau takasa tashi tana wajen zaune tana kallon yarta,har Rashida ta farka da kanta tabude ido taga Mama murmushi tayi tai mika ta tashi tace âMama baki tadani ba sabida ba aiki koâ gari yawaye Mama banyi salla baâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ2ïžâŁ
Dasauri ta tashi tafice alwala tayo tashigo agurguje tasa hijabi ta tada salla tana sallamewa daganan kan daduman ta hango kafan Mama yanda suka kumbura suntum dawani irin sauri ta taso tazo wajen tace âinnalillahiâ dan yatsa tasa ya nitse akafan yanda jikin Rashida yahau rawa saida ta tsorata tace âMaâŠ..mâ tama kasa magana tsabagen yanda zuciyanta ke bugawa saikuma ta juya a haukace zata fita daga dakin hijabin dake jikinta Mama takama hakan yasa da sauri tajuyo saikuma ta duka, ahankali Mama da bakinta baya motsi sosai tace âkaini nai fitsari nai alwala nai sallaâ gyadamata kai Rashida tayi da sauri tace âto Mamaâ tawuce tafita takai ruwa bayinsu sannan tadawo daukan Mama tayi ta dagata Mama ta tashi kafan natama nitsewa yake dasauri Rashida ta zaunar da ita tace âMama tsaya nakawo po kiyi fitsarin adaki namiki alwalaâ ta zaunar da ita tacire hijabin ta ijiye tafice taje chan hanyan bayi ta dauko po ta wanke tadawo dakin da taimakonta Mama tayi tai tsarki tadauko tafito tadawo ta goge wajen tass sannan tamata alwala ta daura ta kan dadduma dantai salla hannunta Mama takama tamata murmushi tace ârelax babu abinda zai sameni daga hannunki inajin yanda zuciyanki ke bugawaâ kallonta Rashida tayi idanunta sun cika da hawaye baki tabude zatai magana saita kasa tafashe da kuka tace âMama wlh ina sonki Mama, Mama kene rayuwana gabaki daya Mama kiyakuri kiji sauki I know damuwana yasa BP ki yatashi bare naje nakira Musa yaron Baba Liman ya kaimu asibiti, Mama kiyafemin wlh wlh wlh bazan kara saki magana ba, Mama kina cewa nabari nabari kinji Mama wlh na rantse da Allahâ dayan hannunta Mama takai saman fuskanta ta goge hawayen dasuka zubo ahankali Mama tace âcomeâ matso da fuskanta tayi kiss Mama tamata a goshi muryanta chan kasa tace âI love you Rashida remember this always konai fushi dake bahar zuciyata bane kinji, stop crying I will be fine muje asibitin jeki kira Musaâ tai maganan tana kara goge mata fuskan tass tashi Rashida tayi tadauki hijabinta tafice daga gidan, gidan Baba Liman tawuce a kofar gidama taganshi ganinta yasa kafin tamayi magana yace âlafiya?â Ahankali tace âMusa nazo kira yakaimu asibiti jikin Mama yatashiâ ahankali Baba Liman yace âSubhanallahi Allah yabata lpy jeki kimtsa zan biyoshi muzoâ juyawa tayi takoma gidan Mama nakan dadduma kallonta tayi da kafafun dasuke amike kaman kara kumbura suke every minute, wata yar jakarsu ta dauka ta shiga debama Mama su t-shirt da zani sheâs a student doctor she know case din Mama is not something dazaâa sallamesu gobe, tadau zanin gado wankakke da hijabi itama tasa yan kayanta dan daga wajen zata dinga zuwa department dinsu ta kwaso duka kudin dasuke dashi tashiga kirgawa gashi sun kashe kudi akasuwa ranan salla, Mama sai kallonta take yanda jikinta ke rawa kaman tamata kuka tadai daure bataso ma tanuna mata kalan azaban datakeji saisa take daurewa sunayen Allah akwai take kira abakinta, 85k sukedashi tadauki wayanta tanada about 51k a account, jakan makarantan da da komi keciki tagoya ta gungura jakan takawo tsakar gida daidai lokacin an buga gate dasauri ta gungura box din waje su kasa a keke ahankali tace âMusa zoka tayani mu dauketa bazata iya tafiya baâ daga Musa har Baba Liman biyota sukai ciki, Baba yakalli Mama da idanunta ke a kulle sabida tsananin ciwo yace âsannu da jikin Maman Rashida sannuâ gyadamai kai tayi batare data bude idanubta ba, Baba Liman yace âkawomin ruwa Rashida namata adduâaâ dan yana ganin Mama yasan ita kadai tasan metakeji, kawomai ruwa tayi da sauri karba yayi yayi adduâoâi ciki yabata yace âbata tasha ki shafa mata sauran akafaâ karba tayi cike da tsantsan so tace âMama sha Baba Liman yamiki adduâaâ ahankali Mama tabude idanunta dasukai jazur tadaurasu kan Rashida tadan bude bakinta kadan samata ruwan Rashida tayi tasha kadan sannan ta tsiyaya a hannunta ta shafa mata a kafafun sannan ta ijiye a gefe tace âMusa zoka tayaniâ zuwa yayi atare suka daga Mama tsaye sannan suka dauketa chak suka fita da ita a keke suka sata dawowa ciki tayi tadan gyara koâina agurguje sannan tadauko key tafito ta kulle gidan da kofansu tazo tashiga keke tazauna Musa yatada keken Baba Liman yace âduk yanda ake ciki kinkirani, Allah baki lpy Maman Rashidaâ Ameen Rashida ta amsa Musa yaja keken itakuma tashiga kiran HOD nata wacce suke kira da Mrs Bugaje wacce take Doctor Mama, kusan a kira nabiyu ta daga sabida girkin salla yau yawon salla, tana dagawa tace âRashida how are you sorry ina kitchen ne I missed call naki is everything fineâ? Ahankali tace âMa jikin Mama ne kafafunta sun kumbura sosai sheâs in pain muna hanyan tafiya hospitalâ Dasauri Dr Bugaje tace âtake her to A & E, she must be treated as emergency, bari I will call Dr Usama yau ina off but I will come once na gama girki for my family, donât worry okay Maman ki will be fineâ gyadamata kai Rashida tayi tana sharce hawayen dakeson zubomata daga idanu sannan ta katse wayan, suna kaiwa asibiti A & E tawuce baâasa sun jira anything ba sabida Rashida is a Dr aka sa Mama agado akai ciki da ita Dr Usaman yazo Rashida takasa komi, all ciwon Mama tadamata da hankali yake but hakanan sheâs getting a special vibe daga wannan kaman zaifi kowannne worst duba da kafafunta tana tsaye inda yagama dubata, sannan yajuyo yakalli Rashida Dr Usama yazo yace âfollow meâ binshi tayi ahankali har zuwa office nashi saikuma yajuyo ya kalleta dan murmushi kadan yamata cikeda hikima na manya yace âcalm down Dr Rashida sitâ tana tsaye tace âtell me meke damun Mamana Drâ Dr Bugaje warned him about telling her anything yabari saitazo hakan yasa yace âis just blood pressure ta yatashiâ tana kallon kwayan idanunshi tace âtell me I can handle anything I know People living with HIV (PLHIV) dakuma HBP (High blood pressure) Hypertension sunada significantly high risk of cardiovascular events abubuwan daya danganci matsalan ciwon zuciya da mutuwa, which is thought to be due to a complex interplay of various factors including immune dysfunction, endothelial dysfunction, and inflammatory changes, nasan Mama na is at risk of coming down da stroke, heart attack, heart failure, kumburin jijiyoyin daukan jini na jikinta, taushewan vessels dake daukan jini daga zuciya zuwa jiki, kidney issues, high cholesterol, dakuma matsalolin iya numfashiâ hijabinta takama tadaura daura kan fuskanta tana matse idanunta sosai dakeson suyi kuka tace âjust tell me wanne daga ciki ke damun Mamana?â Wlh ayanda yaga Rashida shi kanshi saiyaji bazai iya gayamata ba gwara Mrs Bugaje tazo tagaya mata, dan murmushi yace âI actually called you nagaya miki yanayinki din nan zai saka Maman ki cikin tashin hankali, calm down Mrs Bugaje is coming wuce kitafiâ wani irin kallo tama Dr saikuma ta tashi tawuce takoma A&E din tazauna kan kujeran dake gaban gadanso takalli Mama da idanunta ke kulle sai bakinta daketa motsi na laâilaha illallah tanashan azaba takai hannunta takama tarike gam, kawai sheâs just looking at Mamanta feeling pains she wish itane akan gadon kwance ta dauke ciwon instead of Mamanta, tana zaune awajen wayan jakanta yashiga kara na Mama cirowa tayi taga Liman dauka tayi takai kunne yace âYaya jikin nata me akace Rashida?â Ahankali tace âDr Bugaje nake jira tazo gatanan a hanyaâ anatse yace âkome ake ciki ki kirani Allah bata lpyâ ahankali tace âAmeen ta katse wayanâ ta ijiye.
Around 12 Mrs Bugaje tashigo office nata tafara zuwa ta ijiye bag nata da komi ta sanya lab coat tafito Babban mace ce dazata kai 50yrs haka office na Dr Usama taje tadan jima kafin sutaho ward din tare Rashida na zaune rikeda hannun Mama taji muryan Mrs Bugaje cikeda wasa irin na professional Doctors din nan tace âMama yaya mukayi ni da ke?
Wat was our agreement? Dasauri Rashida ta juyo ta kalleta, handglove tashiga sawa tana murmushi tana kallon Mama kaman irin nothing serious din nan sannan tataho gaban gadon tace âopen your eyes for me Mama kar Rashida tafashemin da kuka anan dukta damuâ ahankali Mama tashiga bude idanunta da kyar tabude kadan sunyi jazur takalli Rashida dake tsaye gefen Mrs Bugaje tai zuru zuru bakaramin dadin hakan Mrs Bugaje tajiba tace âgood job Mama, tell me meke damunki? Meya tadamiki da hankali haka dahar kika bata agreement namu na bazaki dinga tunani be?â Mrs Bugaje tai maganan tana duba kafafun Mama tana dubawa kumhurin yanzu ya wuce guiwowinta ma, cikin wani irin murya da baya fita Mama tace âJummai, Jummai zata halakamin rayuwan yarinyana, Jummai nason halakamin yarinyaâ dasauri Rashida tai wajen takama hannunta da sauri tace âMama dama abinda kiketa tunani kenan babu wacce zata iyamin komi I can defend myself kinji kidena tunaninâ girgizakai Mama tayi hankalinta nawani irin tashi takalli Dr tace âMrs Bugaje hideâŠâŠ.hide my daughterâŠ..banson ta cutarmini da yarinya, nasan Jummai nasan bazata kyaleta ba, Jummai Jummai, yarinyana, RashiâŠâŠRashiâŠ.RashâŠ.â Kawai sai Mama tafara yunkurowa tana wani irin nishi kaman zata mutu numfashi kaman yana gagaranta ma, Mrs Bugaje tai maza takama kafadarta tana maidata gado tace âMama calm down calm down Mama I will hide Rashida babu abinda zaâa ma yarinyarkiâ inaaa kaman ma Mama batasan inda kanta yakeba wani irin gasping breath Mama keyi dayasa Rashida kawai tadaura hannunwanta kan baki tana wani irin kuka tana kallon Mama dataga Mrs Bugaje da Dr Usama are trying to save at all cost Mama tasha ciwo but not irin wannan bata tabajinta this scared arayuwanta ba Mama is her biggest strength for the first time arayuwanta taji karfinta jarumtarta ma gaxawa she donât even know ina kanta yake tadaiji an jijigata ance âRashida!â Firgigit tadawo daidai Mrs Bugaje ne tace âcome with meâ dasauri takalli Mama dataga an sama oxygen a hanci wasu maâaikata na gungurata zuwa wani wajen dabama tasani ba har office na Mrs Bugaje taje zaunar da ita Mrs Bugaje tayi akan kujera itama tazauna ganin yanda take kuma saita kara tashi tabude fridge na office din taciro cold water tamika mata tace âshaâ ahankali Rashida tabude tadan kurbi kadan daidai lokacin Dr Usama na shigowa dawasu papers kusan guda 5, Mrs Bugaje ta karba tace âthank you Drâ gyadamata kai yayi yace âbari nakomaâ yajuya yafice papers din Mrs Bugaje tasaka glass tana dubawa kusan 20min sannan ta ijiye tareda sauke glasses din takalli Rashida daketa kallonta she doesnât even know what this small girl will do, ahankali tace âRashida tun kina 100 level nasan how strong you are, bantaba ganin strong resilient student arayuwana like you ba wacce at a very young age shoulder responsibilities Mamanta da school da komi na rayuwansu, I supported you all through pull some strings na tabbatar kina gamawa da clinic dinki by 1PM wanda baâa taba dagama student kafa haka ba, but I made it happen sabida I see you I see rayuwan dakikeyi a daughter like you deserve standing ovation, dan haka banson ki karaya this time fight this also kaman yanda you fought komi na baya kuka cigaba da rayuwa kinji Rashidaâ gyadamata kai Rashida tayi tana kallonta tana rike duka abubuwan datakeji azuciyanta, Dr Bugaje tace âBP Mama yakai level din da ko makiyina bazanmai fatan yakaiba, legs nata are starting to have stroke sabida blood vassel nata na zuwa wato Artherties nata are blocked jini baya fita da kyau, now dole mu mata procedure callâŠâŠâ ahankali Rashida tace âarherectomy!â Ijiyan zuciya Mrs Bugaje tasauke tace âyes, minimal invasive procedure ne dazamuyi dan muyi flushing buildup din daya cika vessel din sabida jini yasamu yawuce wajen freely, that is oneâ tadan sauke ijiyan zuciya tadauki paper gabanta tamika mata tace âga result na express ECG da Dr Usama yasa aka mata can you read ECG da kyau?â Gyadamata kai Rashida tayi da sauri takarba tana karanta rhythm din, cikin wata kalan sassanyar murya Mrs Bugaje tace âI think zuciyan Mamanki is failing!â Wannan karan ijiye paper Rashida tayi agabanta tadaura hannunta saman idanunta ta matse hawaye still yana diddiga from side, wlh kawai dan ita Dr ne but she wants to cry for the girl, ahankali tace âmatsalan HIV is yanacin kwayoyin garkuwan jiki, dazaran cuta tashigeka HIV yana cinye wayan nan garkuwan na jikinka da naturally suke fighting cuta kowace iri, itâs a long shot but banso kiyi loosing hope we can still save your Momâ har lokacin Rashida batasaki idanunta ba hancinta kawai yake motsi tip na hancin yayi jazur wani tsinkakkiyar majina na lekowa daga hancin, ahankali Mrs Bugaje tace âRashidaâ dago kanta tayi tana sakin idanunta cikin muryanta dahar yakoma kaman na me mura tace ânaamâ wani paper again Mrs Bugaje tabata tace âidan kinaso muyi treatment nata ayi procedure sannan ai connecting Mama da machine dazai taimaki heart dinta dake failing sannan ayi tackling BP da stroke din, to this is just a rough estimate na kudin dakike bugata rough estimate dan zaifi haka anything heart magungunan shi da treatment nashi is expensive, plus oxygen da yanzu muka sata akai dazai dinga tayata breathing you need about 2.5M!â Kallon list din take kawai, ta ina zata sami kalan kudin nan? Wani aiki zatayi tasami kudin nan just today sabida afarama Mama treatment sai alokacin kawai taji kuka yazomata kawai tafashe da kuka da karfin gaske tawani zube kasa daga jikin kujera ta dunkule paper a hannunta tana kuka sosai tashi Mrs Bugaje tayi ta zagayo ta duka ahankali agabanta idanunta sunyi jaaa tadafata tace âI know bakida this kind of money bakida hanyan samunsu Rashida itâs okay ya isa kukan we will not let Mama dieâ wani irin kallon Mrs Bugaje take tana kuka, Mrs Bugaje tace âRashida Iâm a family woman kwanan nan nama yarana dake UK registration na school wlh banda kudi but I will give you 200k sauran kudin kuma akwai this student loan da student ke iya applying idan kafara internship duk albashinka zaâa dinga karba as payment for the loan, but matsalan shine CMD kadai ke signing and approving but baya gari dole mujira yadawo which bamuda lokacin the next option is student doctors and other peopleâs help seek for donation for Maman ki yawanci an sanki ansan situation na Mamanki they will help you hopefully zamu iya tashi da something, in the meantime kudin nan dazan baki dayan chanjin dake hannunki jeki sayi necessary magani dasu drip da ake bukata sabida afara ma Mama treatment kinji and pay for oxygen also dan na this hour kawai zasu bata idan baku biyaba bazasu bata again ba, Stop crying, remember na gayamiki you have to be strong ke kadai Mamanki keda shi, kene kadai zaki iya kula da ita, stand up dagata Mrs Bugaje tayi tace âAllah baya hada bawa da abinda yafi karfinshi kinjiâ gyadamata kai Rashida tayi takama hijabinta ta goge fuskanta tass, jakanta Mrs Bugaje tadauka ta bude taciro bandır na 100k guda biyu wanda sabida ita ta taho dashi tabata tasan basu dashi cus tun awaya Dr Usama yagaya mata komi tace âtakeâ tsayawa tayi tana kallon kudin Allahu Akbar tunda tafara girma tafara aiki bata taba accepting wani kudi dazaâa bata sabida Mama ba saidai Mama ta amsa yau gashi ita ake bama kudin taimako zata karba hannunta tamika dahar rawa suke ta amsa tama kasa godiya sabida shock Mrs Bugaje ta dauki precribtion sheet dawasu papers tabata tace âjeki sayo magungunan sannan kibiya kudin ECG da aka mata ki kowamin a ICUâ gyadama Mrs Bugaje kai tayi tafito tafiya kawai take taje ta bibbiya kudin ECG tasayo magunguna dasu drip tabiya kudin oxygen na kwana uku dan per hour ake biya shi, da kudin da Mrs bugaje taba tada kudin account dinta da na hannunta duka sun kare sai naira dari biyar daya rage mata this is duka kudinta gaba da baya, dawowa tayi ta tsaya gaban ICU mrs bugaje tafito ta amsa tace ânow go round ask for help from this Doctors kinjiâ gyadamata kai tayi tajuya batamasan taya zata faraba stufent Dr dinsu duk sunje hutun salla public holiday wayanta ta dauka tasami waje ta zauna tai shiru yau ne rana na farko datai realizing good human relation ma wani abu ne arayuwa muâamala me kyau yanada ranan sa, duk yanda kakaiga you donât need anybody las las you still need everybody saidai in Allah bai jarabceka dawani abu ba, yanzu kotai magana a group ma yan class dinsu zasu taimaketa? Yawanci tayi fada dasu, yawanci bata kulasu kosun kulata, daurewa tayi tashiga typing komi na neman taimako Mamanta na critical condition tana neman 2.5M ta tura group din da acct details nata bini bini tana duba info kusun gani taga duk sun gani Layla ma fitowa tayi tafara hira a group din babu ko Allah sawake few friends nata suka shigo suka biyemata suna hira suna turo emojis na dariya.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ3ïžâŁ
Kawai saita fito daga watsapp din da sauri tama kashe data ta ijiye wayan tasakeyin shiruu batada kowa Baffa yakori Mama takirashi? Yadena daukan number Mama banda haka ta tsani duk wanda ya wulakanta mahaifiyarta tashi tayi tana numfashi ahankali tashigo A&E ward din ta tsaya tana kallon yanda Doctors ke aiki trying to save lives duka duka nawane salary su babu wanda baida matsala tayaya zata fara binsu one by one tana neman taimako? Da kyar taja kafanta tawuce wajen wata Macen Dr datake tsaye gaban nursing station tana magana dasu ahankali Rashida tace âsannuâ dasauri likitan tajuyo ta kalleta tace âyauwa sannuâ kasa magana Rashida tayi batasan ta yanda zata fara rokon ba Dr tace âlafiya?â Ahankali Rashida tace âtaimako nake nema, uhmmmâ tahadiye abu awuyanta tace âMama na needs 2.5Mâ kallonta Dr tayi saikuma chan tace âsorry about your Mom but kinsan this is the 2nd month da government basu biyamu ba? Metron fadamataâ Dasauri katuwar Metron na wajen tace âwlh da na iya roko nima Iâm bold enough like you danabi kowa na nema tsabagen rashin kudi this Tinubu Tenure no good for us kawai, baâa biyamuba everyone is brokeâ gyadamusu kai Rashida tayi tawuce kawai taje wani lungu ta duka tana maida numfashi tana ahaka wayanta yahau ringing fitoda wayan tayi ganin Mrs Bugaje yasa ta tashi tama kasa daga wayan ta taho da gudu danta dauka wani abu yasami Mama agaban ICU taga Mrs Bugaje, tana kallon Dr Usama dake kokarin helping Mama machine din da aka samata sai kuka yake arude tace âDr what is happening to Mamaâ? Dasauri Dr tace âshe needs atherectomy now vessels dinta sun kara blocking, you need to pay I think 800k ne or so kudin amata before we loose your Mom goâ Mrs Bugaje na maganan ta juya takoma ciki Rashida tajuya itama bamatasan mezatayi ba Baba Liman tashiga kira tana tafiya kaman mahaukaciya ahanya tace âBaba Liman wazaisai gidanmu Mama na bukatan 2.5M yanzu kuma ana neman 800k ayi flushing zuciyantaâ Baba Liman yace âSubhanallahi ta ina zamu samo wanda zaisai gidanku yanzu yanzu Rashida ai kusan is impossible amman bari natara jamaâa najiâ ya katse wayan batasan ma ina xatasa kanta ba Riyad! Kawai taji zuciyanta ya ambato, Riyad ne yafado mata arai, he helped them before, and yana shiri da Mama taje ta nemi rance ne kafin a saida gidansu? Tunanin yasa tashiga keke tawuce hotel last 500 naira tabiya keke dashi, ta sauka saikuma ta tsaya tai shiru tayaya zatai facing nashi? Mutumin dabata tabamai godiyan abubuwan dayama Mama ba saima rashin kunya datakemai accusing him of lalata mata? Yau Allah yana nunamata abubuwa da dama datayi abaya that were wrong gashi yanzu she needs his help desperately dudda tagama mai rashin kunya da kurin cewa she alone can take care of Mamanta bata taba sanin a day like this will come ba, takai kusan 5min tsaye take awaje cikin rana tana lissafin yanda zatai confronting Riyad kafin tadai daure tadaga kafa tashigo building din tawuce ciki direct elevator ta tafi tana adduâa Allah yasa yana nan, har office nashi taje ta tsaya gaban kofan tana kallo kafin ahankali tadaga hannunta tai knocking, jin shiru yasa takara knocking, harta fara tunanin kobezo bane dan yau ranan yawon salla ne nabiyu sai chan taji daga ciki ance âcome inâ cikeda isa, ahankali ta murza kofan ta shige yana zaune gaban desk nashi yana sanye dawani milk yadi shidai yanason kaya masu haske, rubuce rubuce yake da pen da sauri he seems busy batare daya dagokai ba yace âyesâ ijiyan zuciya tadan sauke saikuma maganan ya makale a wuyanta batasan ta yanda zata fara maganan ba, chan dai tadaure cikin muryanta me rauni tace âaron kudi nake nema 2.5million kafin asaida gidanmu nadawo maka da kudinâ tunda tafara maganan chak ya dena rubutun dayake batare daya dago kanshi ba saida takai karshen maganan sannan yadago kanshi ya kalleta tundaga kafafunta dayaga slippers tasaka dawani maroon hijabi har kasa da koâina dabbare dabbaren ruwan hawaye, kanta akasa takasa dago idanunta ta kalleshi but tip din dogon nose dinta dayagani that looks reddish and runny nose yagane she cried, ahankali yataso yazagayo ya tsaya agabanta yana kallonta but taki dago kanta awani irin hankali akuma taushashe yace âwat happened to Mama?â Kaman yatabo mata wani gyambon ciwo a kirji dago fuskanta tayi tazubamai jajayen idanunta shima kallonta yake baki tabude zatai magana sai kawai tafashe da kuka jikinta and everything is just shaking, tunda ya santa today is the first day yake ganin hawayen ta eye to eye, today is the first time yake ganinta this weak, wani irin sheshekan kuka kawai take agabanshi dayasa yakai hannunshi cikin aljihu yazaro handky yabata cikin wani irin soft tone yace ânothing will happen to Mama kinjiâ gyadamai kai tayi kaman baby tasa hannu ta karbi handkerchief din takai fuskanta tana gogewa still wasu hawayen na zubowa shikuma yajuya yadauke car key nashi da wayanshi yakalleta yace âstop crying letâs goâtsayar da kukan tayi da kyar sannan tabishi yayi gaba fitowa sukayi atare suka shiga elevator tana gefenshi suka sauka kasa yan reception dake lobby sai kallonsu suka dasuka fito but koâajikinshi hanyar mota yayi da kanshi yaje wajen yabude mata kofa yana kallonta ahankali tazo ta shiga ta zauna ya maida kofan yarufe yazaga ya shiga dayan yatada motan suna tafiya sai kiranshi ake yaki dauka daga Mama takira sai Munir yakira yau hawa ana bukatanshi da sassafe yafito because of wani important work nashi da US sunce yatura musu wani abu abun yake tashigo yabarshi yanzu ma.
Dayake yasan kwanaki sunce general hospital suke using hakan yasa hanyar ya dauka motan yayi tsit sai ijiyan zuciyan datake saukewa na wayanda sukasha kuka, suna shiga asibitin yace âina zamuâ cikin muryanta da baya fita sosai tace âA&Eâ nan sukayi yasami waje yayi parking yafito praying babu wanda zaiyi recognizing nashi yadauki black glass nashi yasaka yafito yazagayo yabude mata, ahankali tasauko suka jera ciki har zuwa ICU daidai lokacin Dr Bugaje natahowa wajen ganin Rashida tareda wani hadadden guy yasa glass yasa takarasa shima ya zare glass nashi, yana zuwa yabama Dr Usama hannu yace âsannunkuâ yakalli ciki ICU dayaga Mama da oxygen unconscious yace âme ake bukata yanzuâ? Anatse Dr bugaje da dudda batasan wayeshi ba but he looks responsible tace âfollow meâ office dinta suka bishi Dr Bugaje da Usama explained everything to him yana fahimtan komi with so much care and affection yace âidan akayi Atherectomy din zaiyi aiki bazai koma ya taushe ba or do you think nafita da ita UK within the weekâ? Ahankali Rashida tadago kanta takalli Riyad dayayi maganan da hankalinshi nakan su Dr sunamai bayanai, Dr Bugaje tace âkozaka kaita UK dole muyi flushing na pipe din nan inba hakaba she wonât make itâ gyadamusu kai yayi yace âokay a ina zan biya kudin komiâ? Dr Usama yace âaccount building yana nan opposite MOPD idan kafita daga this buildingâ gyadamusu kai yayi yace âthank youâ yatashi rikeda takardun biyan kudin itama Rashida ta tashi tabiyoshi ahankali yajuyo yakalleta hada ido sukayi saikuma yadauke kai yacigaba da tafiya tana biyeda shi har saida sukazo wajen ICU din da kujeru ke gaban wajen, da hannu yanuna mata kujeran gently yace âsitâ kallonshi tayi da rinannun idanunta saikuma ta gyadamai kai like an obedient girl ta zauna ahankali shikuma yawuce yatafi, almost 20minutes shiru hakan yasa ta tashi tun kafin takai account building din taganshi tsaye a layin biyan kudi jitayi zuciyanta yamata wani iri game dashi, no one tunda ta taso has ever done something like this for them, saikuma tajuyo tadawo tazauna wajen tana kallon Mama ta glass almost 15minutes sai gashi yadawo ga papers a hannunshi gawata yar leda a hannunshi, yana zuwa daidai inda take zaune saiya tsaya agabanta ya bude ledan yaciro wani iced coffee yakalleta yana mikamata yace âhave thisâ ahankali take kallonshi yanda yazuba mata ido yasa gently tasa hannu ta karba hawaye na kara cikowa a idanunta, sai kawai taji sheâs feeling bad sai kuma taji tabama kanta tausayi sai kawai tafashe da kuka kaman an daketa tarike cup din gam a hannunta gwanin ban tausayi, softly yace âitâs okay, stop crying kinjiâ yanda yayi maganan sai taji zuciyanta yamata wani irin sanyi ta gyadamaikai tareda kai cup din bakinta saida yaga ta kurba kadan sannan yawuce.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ4ïžâŁ
Yadan jima acikin office din Dr Bugaje kafin su fito dukansu atare daidai lokacin kuma Baba Liman da danshi Musa na zuwa asibitin sun shigo cikin A&E din hango Rashida yasa suka taho wajen suma su Dr nazuwa wajen tareda su Riyad Baba Liman yace âya jikin nata mai siyan gidaje wai baya gari saiya dawo ga abinda nahado dai daga masallaciâ yaciro wasu kudi dabasukai 30k ba zai bata Riyad yace âkabarshi an sami kudin Babaâ Dasauri Baba ya kalleshi daidai lokacin kuma an fito da Mama zaâa wuce da ita operation room Rashida ta tashi dasauri zata kama hannun Mama that is unconscious Dr Bugaje ta hanata tace âwait here nan da 1hr zamu gama, sit and rest okayâ komawa tayi tazauna tasake daura hannayenta kan idanunta Baba Liman yace âsai hakuri Allah yabama Zainabu lpy, Allah yabata lafiya, Allah yabata lpyâ duk zama sukayi banda Riyad dake tsaye awajen, kusan 20min Baba Liman yayi sannan yatashi yace âbari naje Rashida, lokacin salla na gabatowaâ ko dago kanta batayiba anatse Riyad yace âmungodeâ hannu Baba yabashi suka gaisa yawuce Musa biyedashi suka tafi ahankali Riyad ya zauna kan kujeran gefenta ya kalleta zaiyi magana kuma saiyayi shiru tabashi tausayi, itâs just she and her Mom. âYour Mom is going to be fine stop crying kaman this is the endâ dago jajayen idanunta tayi ta kalleshi, ahankali yace âokayâ? Gyadamai kai tayi.
After 2hrs aka fito da Mama but baâa barsu sunje wajenta ma aka sake shigar da ita ICU aka connecting nata da machine again.
Har dare Riyad na hospital din nan, Rashida looks so miserable, mutane ma rahama ne, batada kowa, sheâs just alone, kawai yaji he canât leave her, koda bazai dinga mata wani magana ba but at least presence nashi is something, gashi batada karfi to handle anything, wasa wasa har 4 na asuba suna zaune wajen nan ita Rashidan ma bacci yadan kwasheta shiko idanunshi biyu, yana zaune awajen yana kallon yanda take bacci azaune idanunta sun kumbura suntum, heâs feeling just too many things towards her acikin zuciyansa.
Ahankali Mama ke bude idanunta, glass ne dakin ICU, na waje can see naciki, and naciki can see waje, ahankali idanunta suka sauka kan Riyad dake zaune kan kujeran dake facing room nata na zaman wayanda keda patient a ICU, kallon Rashida dake bacci awahale kawai yake, kallo ne da duka abinda Mama tagani a idanunshi is so much care, love, tausayi, concern da affection daidai lokacin Dr Mumina tashigo, ganin Mama idanunta biyu yasa tace âhow are you feeling Maâ? Oxygen din Mama tai yunkurin cirewa tana kokarin magana dasauri Dr Mumina tace âmekikeso tell me?â Waje Mama tanuna cikin muryan dabata fita sosai tace âI want to talk to My sonâ juyawa Dr tayi takalli Riyad da Mama ke nunama ta ta gyadamata kai tajuyo tafito hakan yasa Riyad yajuyo jin an bude kofa, da hannu tamai alamu yazo tashi yayi dasauri yana kallon ciki ganin Mama ta farka finally, scrub Dr Munina abashi yasaka da takalmi da hula da handglove sannan yabi Dr ciki Dr taduba komi kafin tadan zarema Mama oxygen mask din tace âkimai magana ahankali, donât stress too much, I will be back to put it for you nan bada jimawa baâ tajuya tafita zama Riyad yayi kan kujeran gaban gadon cikeda so dakuma tausayi yakalli Mama da ko idanunta bata iya budewa da kyau yace âMama ya jikinkiâ? Hannunta Mama ta mikamai alamun yabata nashi, bata hannunshi yayi da sauri Mama takama tarike gam tasake shiru tana numfashi ahankali kaman magana wahala yake mata, cikin muryan tsananin rashin lafiya dake fita da kyar tace âRiyadâ ahankali Riyad yace ânaâam Mama please stop talking, Mama it looks painful Iâm here bazanje koâinaba kinjiâ
Ahankali Mama takara cewa Riyad, kankame hannunta Riyad yayi sosai heâs just feeling Mamaâs pain yace âMama dan Allah stop talkingâ girgixamai kai tayi tace âRiyad lokacina yayi aduniya lokutan da Allah yadeba miniâ Dasauri Riyad yace âMama kidena magana haka zaki sami lafiya bagashi yanzu kin farfado ba eh Mamaâ? Dan murmushi tayi ta kankame hannunshi tana numfashi wani kala wani kala, chan tace âRiyad duk duniya dakai kadai na yarda! Kanada hankali, kanada amana ga taimako kaiba yaro bane sannan kanada iyali, ka taimakeni so da dama, thanks to you Rashida bata kwana a police cell baâ tayi shiru kuma tana sake kankame hannunshi tace âbanso na rasu ban damkawa kowa amanar yâata ba banda wanda zan bamawa, Riyad Yayana na jini ya koreni! Mijina ya koreni! Baba Liman matanshi basa sona, tsorona da tsoron ciwona kowa yake! Kaine mutum na farko daya shigo rayuwanmu baka kyamace muba baka tsorata damu baâ tasake shiru saikuma tace âkishiyata data kulle yarinyana a police station ka fito da ita nasan saita bata ma Rashida rayuwa, nasan saitayi wani abun, yanzu haka rayuwan Rashida nacikin hadari zata cutarmin da diyaâ hawaye ne suka gangaro daga gefen idanun Mama saikuma tafashe da kuka sosai tana kankame hannun Riyad tace âRiyad dan Allah dan Allah na rokeka da girman Allah ka auri Rashida! Sabida na samu na mutu in peace nasan na damka maka ita, wlh Rashida batada HIV kaman ni batada wani cuta ajikinta, Riyad ka taimaki yarinyana, kayi jahadi akanta, ka aureta kahadata da matarka su zauna lafiya, inaso na mutu bayan nadan tana under care naka da kukanwanka amatsayin matarka zaka karemin itaâ Kai! Yanda Mama ke kuka sai yasa Riyad yaji kaman zaiyi kuka, Mama na son Rashida beyond words, sheâs on sick bed but still damuwan Rasheeda ne aranta, ahankali yakai hannunshi dayan that is free ya sharemata fuska muryanshi sounding so weak yace âstop begging me! And kidena damuwa, stop worrying Mama, Mama zan auri Rashida! And namiki alkawari zan kula da ita amana! Bazan taba cutar da ita ba! Zan tsayamata! I will be her shield! I will be her shade! Mama I will stand by her and with her, and zan so yarki and stay her husband till my last breathâ wani irin murmushin kuka Mama tayi tace âbayan narasu nasan she will be shattered be there for her Riyad and make sure tayi completing karatunta na zama kwararriyan likita!â Gyadamata kai yayi yakasa magana, Mama tace âRashida is a good sweet person wata rana you will see her other side, rayuwa ya maidata me taurin kan nan but my daughter is an Angel!â Gyadamata kai Riyad yayi yace âMama stop talking ya isaâ girgixamai kai Mama tayi tace âkaje kazo da yan uwanka zan kira Baba Liman inaso na aurar da Rashida dakaina anan kafin na rasu! Inaso naga yarinyana tai aureâ âMama bazaki rasu baâ Riyad yafadi da karfi jijiyan kanshi na fitowa daidai Dr na zuwa ganin Mama na kuka yasa tace âohh noo, BP ta will shoot again, she needs to stay happyâ ahankali Riyad yajuya yafita.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ5ïžâŁ
Yana fitowa tsayawa yayi yakalli Rashida dake bacci kafin yawuce yafita yatafi parking space ya shiga motanshi yatada gida yawuce yana zuwa remote dake motanshi ya dauka ya danna gate yabudu ya shigo yayi parking motan ya sauko yana tafiya ahankali yawuce ciki yana bude kofa yaga Mom zaune kan kujera saida gabanshi yafadi ganinta tashi tayi tace âdaga ina kake?â Rasa abinda zai fadi yayi cus ya tsani karya and ya tsani yinta da bakinshi Mom tace âdid you know how important yesterday was for Royal Family kuwa? Kasan mekayi Riyad? An nemeka an rasa, Baffan ka Mai babban daki, su Kabeeru duk ansan baka gida narasa mezance? Wani dalili yasa mukaje Umara da wuri dan mudawo kayi salla da mutanenka ayi hawan salla dakai right? Kasan kalan tijaran da abin kunyan daka jamin kuwaâ? Runtse idanu yayi yama rasa mezaice ahankali yace âI will handle it Mom wani important work ne yatasomin, I can create another event at my leasure time kiyakuri, its workâ âimportant work da ake fita da sassafe adawo by 5 na asuba are you out of your mind Riyad!â Mom takirashi azafafe dayasa yasauke kanshi kasa tace âbanso na zargeka the first time da matan ka tai accusing naka fushin dakayi yasa ban yarda ba but bari kaji idanma wata kake nema wlh wlh dukda kana sarki baka isa ka karomin aure ba!â Ahankali Riyad ya kalleta Mom tace âyes! Haleema is the only daughter Inlaw dana yarda da ita cus yarinyar nan worship me sama da uwarta data kawoni duniya, ban yarda da karo aure ba azo arabani da dâana ba! Aurenka is just a year now na auramaka yarinya datake da komi kyawun sura, good tsatso, oxford graduate, full package ce Haleema har yau ka kasa mata ciki ragon banza ragon hofi kaman ba jinin Baba Ali ba, nagaya maka idan baka dena all this abubuwan ba wlh zan mugun saba maka, yau Haleema na period still ka kasa mata ciki this month again yawo kake a duniya donât allow me to face you fa Riyad nafara bin lamarinka ina binciken ka, look at me nakasa bacci all because of you gadin dawowanka nake eh why are you doing this Riyad yaushe kadawo mara jin maganataâ? Wani iri dayaji yasa ahankali yace âMom kiyakuriâ mugun kallo ta watsamai tawuce tafice daga flat din, shikuma ahankali yawuce bedroom dinshi wanka yayi yayi salla sannan yadan kwanta bawani bacci yayi ba around 8 yatashi yadauki wayanshi yakira Munir sannan yashiga wanka yafito yaji Munir a falo yana waya shiryawa yayi cikin wani mahaukacin farin gizna yasa hula ya Allah hula yamai kyau, yasaka wani bakin takalmin Berluti, ya daura agogon Vacheron Constantin a writs nashi, ya manna wani Carrera black glasses a idanunshi Ya Allah kaga Riyad saika kara kallonshi saukowa yashigayi Munir ya tsare shi da ido yace âwannan gayun ina zamu haka!?â
Kin magana Riyad yayi yana karasa zuwa falon ya jefamai car keys Munir ya chabe yana mikewa tsaye suka fito tare mota sukayi suka shiga Munir yatada motan yace âina zamuâ? Ahankali Riyad ya sauke ijiyan zuciya heâs just torn between Mom dinshi and Mama, yana tausayin Mama and he feels obligated to help them, Rashida batada kowa, and he promised kanshi kafinma ya gano Rashida cewa he will helped the girl, heâs doing this for the girl that saved life nashi, murya chan kasa yace âIâm sorry Momâ kallonshi Munir yayi jin abinda yafadi hakan yasa ahankali yace âwajen Baba Buba zamuâ dasauri Munir ya kalleshi yace âBaba Buba? You mean Baban Ammiâ? Dauke kai Riyad yayi ahankali yace âyes Kakana!â Tada motan Munir yashigayi mamaki yagama kasheshi yace âRiyad as far as I know I canât even remember the last time kaje ka gaidashi, ni banmasan kasan yana existing baâ wani iri fuskanshi yayi saikuma ahankali yace âi will change from nowâ fita sukayi saikuma chan Munir yace âmezai maka? Youâre sounding kaman you need something from him?â Shiru Riyad yayi na kusan 5minutes chan yace âaure nakeso ya karbanmin! I want to Marry Rashida!â Wani burki da Munir yaci kan titi saida yakusan creating hatsari yaja motan da gudu yana gangara wa gefe yakalli Riyad daya ciro wayanshi yana dubawa jin karan text message daya shigo wanda yaga na Haleema ne.
âBaby marana na ciwo? A ina ka kwana jiya?â.
Ahankali Munir yace âRiyad looked at me! Zaka auri Rasheeda? Waya sani agida? Mom tasani? Gwaggo tasani? Baffan mu yasani? Waya sani?â Batare daya kalleshi ba yace âno one knows! Will tell when I feel like itâ yasake shiru chan yadanna mata âKisha magani, Allah kara saukiâ ya maida wayan aljihu sannan yadago ya kalleshi yace âI feel obligated to help them Munir, the girl is young, sheâs a child, the Mom is very sick a ICU lets goâ tada motan Munir yayi harsukakai wani kauye nan Outskirts na Kano bai kara magana ba gaban wani babban gida sukai parking ga rumfa da dalibai suka cika gawani tsoho kan kujera dake da haske kaman Riyad yaci manyan kaya na sauraransu yana hangosu ya tsare Riyad da idanu wanda ya manta rabon daya ganshi saikuma ya dauke kai sannan ya sallami yaran yama Munir alamu da hannu dasuzo.
Shiga rumfar sukayi suka zauna atare suka gaidashi ya amsa sannan yakalli Riyad da kansa ke kasa yace âyau katuna dani? Meya kawoka gidanaâ? Wani iri Riyad yaji amman ya daure yace âkayakuri Bubaâ ijiyan zuciya Buba yayi yakalli Munir yace ânasan wani abu yakawoku so tell meâ kallon Riyad Munir yayi sannan yace âBuba Riyad keso ka bishi ka karbamai aureâ kallon Riyad yayi yace âmesa baka nemi yan uwan mahaifinka ba kazo nan? Ko yan uwan wacce itace mahaifiyar ka yanzu?â Munir zai bude baki Buba yace âkamin shiruâ yakalli Riyad yace âkamin magana koka tashi ka bar nan wajenâ murya chan kasa Riyad yace âbazasu barni na aureta bane na gaya musu Buba sabida ciwon Mahaifiyartaâ Buba na kallonshi yace âwani irin ciwoâ? Ahankali Riyad yace âHIVâ shiru Buba yayi chan yace âkanason yarinyar tsakaninka da Allah?â Shiru yayi chan yace âinaso na aureta, banso ta auri wani karya wulakantataâ saikuma ahankali yace âita ce ta ceci rayuwana lokacin da zaâa kasheniâ Buba yadan jima yana kallonshi sai chan yace âkutashi mujeâ Dasauri Riyad yadago kanshi ya kalli Buban yana dan murmushi daya karamai kyau Buba yace âsaina chanza raâayina tunda ka tsaya kana kallona kaman yauka fara ganina a doron kasaâ tashi da sauri Riyad yayi yana murmushi yawuce Munir ya bishi Buba yabisu da kallo Allah yasani yanason jikanshi sama da duk yanda zai kwatanta abin aduniya, tunda har yatuna dashi a lokacin dayakeda serious bukata haka he will support jikanshi, Babban Aminunshi yakira suka shiga bayan motan Munir da Riyad suka shiga gaba suka wuce.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ6ïžâŁ
As usual wajajen 6 Rashida tabude idanunta da kyar sabida tsabagen gajiya da kuka, kaman ba itane tuntuni ake hayaniyan asibiti ana shiga da fice ba ko bude idanu batayi ba sabida nauyin baccinta, dasauri tamike tsaye ta tafi wajen glass door din ta jingina kanta tana leka Mama trying to see ko tana numfashi, taganta tana bacci and tana breathing, dan ijiyan zuciya tasauke takalli inda ta tashi tasan har tai bacci Riyad na nan koda yaushe yatafi oho wucewa tayi bayi tayo alwala bayan taciro brush ajakanta tayi ta tafi masallaci tai salla tama Mama adduâa sosai tadauki Qurâani yau ta karanta tasake ma Mama adduâa bayan tagama, tana dawowa Dr Mumina tace âYour Mom wants to see youâ jikinta har rawa yake ta gyada matakai abubuwa aka bata tasaka sannan tashiga dakin idanun Mama abude kadan take kallonta dasauri taje gaban gadon ta duka takai fuskanta saitin na Mama tace âMama ya jiki? Are you fine Mama? Kinji sauki? Sannu Mama na, sannu kinji Mama, Mama ina sonki kinji, mezakiciâ? Girgiza mata kai tayi bakinta nadan motsi hakan yasa dasauri takai kunnenta saitin bakin Mama, murya chan kasa Mama tace âinaso namiki aure yau!â Dasauri Rashida tajuyo takalli fuskan Mama kodai bata hayyacinta ne kodai sheâs hellucinating ne? Ganin bakin Mama yacigaba da motsi yasa tasake kai kunnenta saitin bakinta ahankali Mama tace âI want someone that will take care of you koda zan mutu I want to die in peace, I told Riyad ya aureki!â Dawani irin sauri ta kalli Mama gabanta nawani irin faduwa naban tsoro murya chan kasa Mama tace âI trust Riyad! Yanada hankali zai hadaku ku biyu yarike amana! Rashida I need to hand you over to wani tun yanzu da raina kafin na rasu!â Hawaye ne yazubo daga idanun Rashida cikeda damuwa tace âMama nace bazaki rasuba! Mama nothing will happen to you In sha Allah, Mama yaya zanyi idan kika tafi kika barniâ? Kallonta Mama take saikuma tai yunkurin dago hannuwanta biyu dasauri Rashida takama hannuwanta takai fuskanta, hawaye na gangarowa daga idanunta cikin muryan Mama da baya fita da kyau tace âRashida ina sonki, inasonki sosai my little Rauda, ina matukar kaunarki My Doctor my Rish Rish, my only baby, yarinya na kyakkyawa I love youâ wani irin kama hannuwan Mama Rashida tayi saita fasheda kuka sosai, Mama itama hawaye gangarowa yayı daga gefen idanunta tace âIâm scared na mutu banyi handing naki over to anybody ba, Riyad is the only mutum da xuciyana ya yardashi aduniya! Riyad zabina ne Rashida! Riyad is my choice! Riyad is the only man dana kalla namiki shaâawansa as miji will you marry Riyad for me? For my sake? For my happinessâ? Kankame hannun Mama Rashida tayi sosai tana kallon kwayan idanun Mama tana kuka itama Mama kuka take, cikin wani kalan murya Mama tace âwat if na mutum? Wakike dashi? I want to hand you over to Riyad kinji, zaki aureshi sabida inasoâ? Gyadamata kai Rashida tayi at this point the only burin datake dashi aduniya is taga magaifiyarta ta warke jin kanta take idan Mama tacemata tai kisan kai zata iyayi tsabagen yanda takeso ta faranta mata rai and make her happy, cikin kuka tace âMama I will marry Riyad sabida kince nayi! Nariga namiki alkawari bazan kara saki a damuwa ba, kome kikeso Mama shixan dingayi I will always keep you happy, Mama dan Allah karki mutu kinji, kinji Mama karki mutu ki banni kinji Mama? Kin tuna namiki alkawari zan zama likita and develop a cure for you? Mama you have to stay alive and wait for me! Mama kinga inaso kixama hope for mutanen dakeda HIV dudda already youâre, kinyi rayuwa da HIV for 23yrs, you fought Mama ba dare ba rana, kika haifeni, you protected me Mama look at me yau na girma but banda shi, Mama karki banni kitafi kinji help me fulfill this legacy nawa after all this battle yarki likita Dr Rashida found a cure and Mama is HIV FREE!!! Kimin alkawari you will live for me and zaki jirani har lokacin Mamaâ? Murmushi sosai Mama tayi kawai tajawo kan Rashida tadaura akan fuskanta ta kankameta sosai tama kasa magana, sun dade ahaka sannan Mama tace âstop crying babu inda zani, I will stay for you, ranan graduation naki na saka exclusive super wax na kafa gwargwaro akai harda glassâ dan murmushin kuka Rashida tayi tama kasa magana Mama tace âkiramin Baba Limanâ gyadamata kai tayi tadauki wayan takirashi, yace âgashinan zuwaâ around 8 Dr Bugaje tashigo duba Mama ahankali Mama tace âinaso nama diyata aureâ shiru Mrs Bugaje tayi tana kallon Mama wanda somehow she understand Mama, she knows daga inda decision na Mama is coming from, gyadama Mama kai tayi tace âshine mutumin nanâ? Gyadamata kai Mama tayi, Dr Bugaje tace âbaâa bari mutane su shigo ICU sukazo zansa akawoki office dina sai ayi awajenâ gyadamata kai Mama tayi Mrs Bugaje zata tashi Mama tace âMrs Bugajeâ dasauri tajuyo takalli Mama, ahankali Mama tace âkina ganin zan warke?â Tambayan yazoma Mrs Bugaje wani iri amman ta daure tai murmushi tadawo tasake zama tace âMama mutane na mutuwa amusu wanka akusan binnesu ma su farfado balle ciwo, the point is shi cuta da mutuwa duka suna hannun Allah Mama kuma Allah sai warkar dake in sha Allah kinjiâ daidai lokacin ta hango Riyad ya shigo tareda wani tsoho dakuma wani matashi, Mrs Bugaje tace âIna Rashidaâ? Ahankali Mama tace âtaje siyomin abinci dudda na ce mata banson cin komiâ dasauri Mrs Bugaje tace âyou need to eat Mama, bari na musu maganaâ fitowa tayi cikeda faraâa ta gaisa dasu tace âbismillahan ku a office dina zaâayi komiâ ahankali Riyad yakalli Munir da Buba yace âkuje ina zuwa i need to get something in the carâ yayi maganan yana juyawa sukuma sukabi Dr Bugaje.
Samin kanshi yayi da fitowa waje yana kalle kalle just to look for her lura da yayi batanan.
Daga cafeteria take, swallow tasai ma Mama da miyan kubewa sai bottle water ahankali take tafiya dukta rame batada karfi kawai gatanan ne, idanunta har yanzu basu washe ba sunyi ja sun kumbura, gashin idanunta sun tattare, tip na nose dinta is still looking very reddish sabida kuka, lips nata sun kara yin pinkish sosai sabida kuka, sheâs is looking tiredly beautiful, daidai tazo ta wajajen A&E din taji an kwala mata kira. âRashyâ dasauri tajuyo Bilal ta hango yafito daga parking space yana tahowa wajen da dan gudu gudu sauri sauri yana sanye da riga da wando na jean da riga yazo daidai gabanta ya tsaya cikeda damuwa yace âtun jiya bana online ina jirgi coming back from Dubai ina dawowa kuma nahau baccin gajiya da asuban nan naga message dinki a group ya jikin Mamaâ? Yayi maganan cikeda so dakuma damuwa soyayyanta nawani dawomai fresh arai, ahankali dan batada karfin hayaniya yanzu ko fada tace âAlhamdulillah da saukiâ dasauri yashiga tura hannu a aljihunshi yaciro wraps na kudi yan 500 guda biyu thatâs 100k yana mata wani irin kallon soyayya smiling and feeling kanshi yamika mata yace ânazo nabaki this and to assure you cewa youâre not alone Iâm here for you, Dad na UK but he will send his accountant to take care of all the bills kinji Rashy ko miliyan hundred ne Daddy will pay I got yoâŠâŠ.â Kasa karasa maganan yayi ganin wani hadadden guy yazo wajen ya tsaya dab da Rashida ga bakin shade a idanunshi yazuba hannu a aljihu kaman military, ko kadan Rashida bataji alamun tafiyanshi ba kawai taji tsayuwan mutum kusada ita dakuma kamshin turarenshi daya cika mata hanci hakan yasa ta dago kanta ahankali ta kalleshi daidai shima yana kallonta batare daya kalli Bilal ba, cikin warm yet controlling voice yace âdaga ina kike?â Ya Allah! Wani irin kyau Riyad yamata dayasa takasa daina kallonshi like a little girl innocently tace âabinci naje siyoma Mamaâ yana kallonta still batare daya dauke idanu daga kanta ba yace âand who is this?â asanyaye tace âdan ajinmu neâ bayabo ba fallasa Riyad yace âletâs goâ ko musu batayiba tajuya tafara tafiya yama Bilal wani banzan kallo da hannunshi har yanzu yake position na bada komi sannan shima yajuya.
SEE YOU ALL ON MONDAY
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ7ïžâŁ
Albishir! Albishir! Albishirrrr!!!
Dawani irin full confidence Bilal yazo wajen ta yau but ganin wani lafiyayyen guy me kirarran jiki tareda ita and from the way heâs doing kaman saurayinta ne yasa yaji zuciyanshi na kumfa, daman Rashy nada saurayi ne? Who is he? Waye atare da ita? Waye dan wulakancin nan? Well yasan koma waye da wuya idan yakaishi kudi he will wait she will come begging for the money yana gama tunanin yajuya azuciye yayi motanshi ya shiga yabar hospital din.
Tare suka shigo ward din daidai lokacin shima Baba Liman na zuwa da ladanin masallaci su biyu, gaisawa suka tsaya yi da Riyad ita kuma Rashida ta wuce, shiga cikin ICU Nurse din da Mrs Bugaje ta turo tayi akasa Mama akan wani wheelchair aka gungurota har zuwa office din Mrs Bugaje Rashida na biyeda ita saikuma su Riyad da Baba liman da Ladanin is duk suka shiga ciki.
Already Mrs Bugaje tasa an saka kujeru duk aka zazzauna gawasu sababbin syringe agabanta guda biyu, anatse tace âwelcome to my officeâ sannan tace âbefore muyi proceeding muyi asalin abinda yakawomu nan office din, as a medical Doctor i want do something for both Riyad and Rashidaâ ta taso dagakan kujeranta da kanta tazo gaban desk ta kalli Riyad ahankali tace âbani hannunkaâ bata hannunshi yayi ta kulle igiyan tajajininsa tasa a specimen box tarubuta suna sannan tama Rashida ma haka, sannan tabama wani Nurse dake wajen data kira musamman tace âAbbakar take it to the Lab I need Asap results on this two sample kan genotype blood group HIV, hepatitis da sauransu important blood test na aureâ gyadamata kai yayi yace âYes Maâ yawuce yafita takoma tazauna takalli Riyad tace âinaso kasan wakake aure ba kokanto ba zargi a zuciyanka ko na yan uwanka dake nan wajenâ Baba Liman yace âkwaraiâ Rashida dai na wajen Mama kanta akasa takasa kallon kowa na dakin, almost 20min akayi aka kawo result din Mrs Bugaje ta karba tarike na Riyad a hannunta tamikama Riyad na Rashida tace âtake open itâ karba yayi ya warware takardan ahankali, Mrs Bugaje tace âread it kowa yajiâ dan shiru Riyad yayi chan yace âgenotyp AA, blood group O+, HIV negative, HEP B Negative, HEP C Negative komima negativeâ yayi maganan ahankali, Mrs Bugaje ta bude na Riyad tana saka glass na idanunta like a professional tace âGenoyype na Riyad is AS Rashida is AA so you guys are compactable zaku iya aure, Blood group O+ shima, HIV, HepB and HepC da sauran komi negative, Masha Allahâ tai maganan tana bama Baba Liman wanda kaman shine zai tsayama Rashida as uba, sannan tace âAlhamdulillah nayi part dina sai daura aure yanzuâ faduwa gaban Rashida ya shigayi sosai, cikeda hikima na manya Buba yace âAlhamdulillah Masha Allah, muna adduâa muna kuma rokon Allah daya bawa mahaifiyarki lafiya Rashida Ameen Ameen, Mahaifin jikana ya rasu nine zan tsaya mishi a matsayin uba, sannan sunna ne atambayi yarinya nawa takeso amatsayin sadakinta, dan haka Riyad tambayi your wife to be nawa takeso a matsayin sadakiâ. Dan murmushi Mama dake cikin ciwo tayi ahankali Riyad yakalli Rashida da kanta ke kasa ki fuskanta baka iya gani da kyau sabida yanda kan nata ke kasa cikin murya mai taushi yace ânawa kikeso na biyaki sadaki?â Kasa magana tayi kai ko motsi bata iyayi itama Mama batace komiba, Mrs Bugaje tai murmushi itama tai shiru, Baba Liman yace âtunda nine zan tsaya amatsayin waliyin Amarya bari na ari bakinsuâ yakalli Rashida yana murmushi yace âyarmu me kyau ce! Ga ilimi boko da islamiyya ga hazaka gakuma son iyaye dan haka bazanmuma Riyad karamin kudi ba ko Zainabuâ? Duk ciwon Mama saida tai murmushi sosai hakan ba karamin dadi yama kowa na dakin ba, Baba Liman yasake murmushi yace âdubu dari biyu mukeso akudin sadakiâ harga Allah yafadi haka sabida yasan basuda kudi kuma dole amata Kayan daki dazaran Mama taji sauki an sallameta saisa yasa kudi haka, hannu Buba yasa acikin babban rigan dake jikinsa yaciro wrapper na 1k guda biyu yasa akan jikin Riyad yace âtashi kaje kabata sadakintaâ kallon Buba yayi cikeda so sannan yatashi ahankali har zuwa inda Rashida ke zaune yamika mata kudin cikin wani kalan murya mai taushi yace âga sadakin kiâ hannu dasauri takai ta kulle fuskanta tana rike kukan datakeji gawani irin kunya Mrs Bugaje tace âayiriri Amarya na kunya ijiye akan cinyantaâ ijiyewa Riyad yayi yajuya yakoma ya zauna sannan aka fara daura aure agaban Buba da Aminin sa, Liman da Ladani, Munir da Riyad, Dr Bugaje da Dr Usama, Mama dakuma Rashida, agaban su aka daura aure tsakanin Riyad Baba Ali da Rashida Almustapha akan sadaki naira dubu dari biyu!.
Mama na ganin an shafe Fatihan daura aure sai kawai tajawo Rashida ta rungumeta tana wani irin emotional kuka bata taba sanin Allah zai nuna mata auren yarta Rashida haka ba, itama Rashida kuka take she canât believe ita aka daurama aure just now, wai yanzu tazama matar Riyad? Dreaming takeyi ne, tasowa Buba yayi yazo wajen su yace âkidena kuka shi ciwo na Allah ne, hakama waraka ta Allah ce, komi yayi zafi maganinsa Allah, Allah zai baki lpy kinjiâ gyadamai kai tayi ahankali Mama tana sakin Rashida tace âRiyadâ zuwa wajen yayi yadan saci kallon yanda Rashida ke sharce hawaye Mama tace ânagode Riyad!â lumshe idanu yayi, Buba ya juyo ya kalli Rashida dake kuka sosai sai kawai yaduka agabanta hannunshi yakai yakama kuncinta hakan yasa Rashida takalleshi da jajayen idanunta, cikeda wani irin tausayin yarinyar da kaunarta dayaji Allah yasamai hakanan yace âdena kuka Allah zai bawa Mahaifiyarki lafiya kinjiâ gyadamai kai tayi ahankali cikeda kunya ganin tsoho dashi ya duka agabanta, murmushi yayi mata yasa yadauki byro daya gani akan table na Dr Bugaje yace âdan tsammini takarda Doctaâ paper Dr Bugaje tabashi rubuta number shi yayi yabama Rashida yace âduk randa Riyad yamiki wani laifi, koya bata miki rai, call me zanzo har gidanku na sabamishi, saina ciwa mijin naki mutunciâ akunyace ta sunnar dakai Mama tai murmushi sosai Buba yace âkarbaâ ahankali Rashida tasa hannu ta amsa sannan yatashi yakalli Munir yace âmuje ka maidamu gidaâ dasauri Riyad yace âzan maidaku Bubaâ kallonshi Buba yayi yace âstay da iyalanka kabar Munir ya kainiâ wani iri Rashida taji jin ance iyalanka shikuma Riyad saiya gyadamai kai suka wuce suka fita nurses sukazo suka wuce da Mama aka fita da ita, ganin Riyad har lokacin tsaye a office din itakuma Rashida takasa mikewa sai hawaye take gogewa yasa Dr Bugaje ta tashi itama tace âbari na bisuâ gyadamata kai yayi tawuce tafice ganin haka yasa itama Rashida ta tashi da sauri tazo zata fice kawai taji yakama hannunta, mugun faduwa gabanta yayi da saida ya lura dasauri ta kalleshi hada idanu sukayi yamata wani irin kallo kaman baimasan yarike hannunta ba gently yace âwho is that guyâ? Yanda yamata maganan yana kallon kwayan idanunta dasuke ajike yasa takasa jure kallonshi takasa magana, dan jawota yayi sabida yanda take so light this days kawai ta taho dab dashi gabanta nafaduwa sosai mehaka yake mata, cikin whispering voice yace âme tsakaninkuâ? Heart dinta na racing sosai tace âbakomi classmate dina neâ âmesa yakawo miki kudi?â Dan kallonshi tayi yanda yau yake kallonta saitaga kaman ya banbanta da yanda yasaba kallonta ada, sake sauke kanta kasa tayi tace ânayi seeking help a group namu for Mamaâ hannunshi dake free ya mikamata yace âyour phoneâ dan kallonshi tayi saikuma ba musu tasamai wayanta a hannunshi ya karba a aljihu taga yasaka wayan nata ahankali yace âthe next time he approaches you tell him someone owns you now! And that person is Me!â dago kanta Rashida tayi da sauri ta kalleshi yanda yake maganan kaman yaci wani competition saikuma ta gyadamai kai yace âzanje and get you food and clothes you need to shower and changeâ sake gyadamai kai tayi takosa yasaki hannunta dataji yana mata kaman shock, ahankali yasaki hannun yace âletâs goâ tare suka fito har zuwa ICU Mama da Mrs Bugaje dake tare duk suka kallesu murmushi Mama tayi Dr Bugaje tace âcongratulations Mama, Allah ya sanya albarka, Mama yanzu saiki kwantar da hankalinki ayanda nake ganin yaron nan Riyad he will protect Rashida no matter what so dan Allah kiji sauki BP ki ya saukoâ gyadamata kai Mama tayi tanajin wani karfi da lafiya na shiganta.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ8ïžâŁ
Gyadamata kai Mama tayi cikeda farin ciki dudda maganan ta baya fitowa da kyau tace âAlhamdulillah Mrs Bugaje wlh ina cikin wani irin farin ciki da bazan iya misalta miki shi baâ murmushi tayi.
Wucewa Riyad yayi yatafi yabar Rasheeda awajen, fitowa Mrs Bugaje tayi takalli Rasheeda tace âscrub in kije wajen Mamankiâ da sauri ta taso tayi cikin ICU din bayan tasaka abubuwan Mama na ganinta cikeda karfin hali tasa hannunta asaman hanci tace âayiriâŠ..â saikuma tahau tari da sauri Rashida tazo wajen tace âMama stopppâ ijiyan zuciya ta sauke tace âRashida kinsan yanda nake murna kuwa naga aurenki Alhamdulillah kinga na warke tass kalli kafafuna harsun soma sakewaâ kafafun Rashida takalla saikuma takalli Mama yanda taketa murmushi is not like tanason auren nan, infact ita bamata taso da burin tai aure ba sannan one single feeling batada shi for Riyad kawai dai daga jiya saita fara kallonshi ta fuska daban compare to before data tsaneshi, jiya ta gane Riyad shi mai sonsu ne ba kyamatan su ba, yana kula da Mama, shine the first person that genuinely know them kuma yasosu ahaka sannan ya tsaya musu, kallonta Mama tayi tace âme mijin naki yace? Ina yajeâ? Dasauri ta kalli Mama jin kalman mijin yamata wani banbaran, murya chan kasa tace âwai zaije yakawomin kaya da abinci nai wankaâ wani irin blushing da Mama keyi saida Rashida kawai ta maida Mama tv tana kallo is this aure of a thing yakesa Mama farin ciki haka ko wani abun ne dabata sani ba to wani abuma? Is just auren nan, sai murna Mama keyi. Wajajen 4 Riyad yadawo tareda Munir dake rike da basket na abinci shikuma yana rikeda wani paper bag dan babba Mrs Bugaje ta kallesu tace âyauwa I was waiting for you to come inaso na maida Mama wani daki kodan this big occasion she seems very happy, her biggest fear and worry is yartane yanzu data damka maka ita kaman 90% of matsalanta sun tafiâ anatse Riyad yace âI prefer private single roomâ gyadamai kai Dr Bugaje tayi tasa Nurse ta gunguro Mama daga dakin tana fadamusu dakin da zaâa kaita, dan satan kallon Rashida Riyad yayi dayaga idanunta sundan soma sabewa, first floor aka kaisu wani single room mai kyau da komi ciki akai connecting Mama da machine na zuciyan still sannan Nurses din suka fita ijiye abincin Munir yayi shikuma Riyad ya kalli Rashida tareda bata bag din, dan kallonshi tayi saikuma tasa hannu asanyaye ta karba murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasuji maganan yace âshower before I come back, zanje mosqueâ gyadamai kai tayi suka wuce mosque Mama tawani yunkuro ta tashi kaman maison gulma tace âzonan mugani meya kawo miki? Imaza jeki wankan ke to karya dawo ya ganki daka dakaâ kallon Mama kawai Rashida take with a huge suprise kaman ba Mama ba, farin cikinta yaki boyuwa, bag din tamikama Mama, Mama ta zazzage tana fito da abin ciki tana washe baki sosai abaya ne kala uku acikin jakan duka black black amman sun hadu duba tsayinsu tayi taga 58 wlh tsayin yarta, sai cream dakuma wasu lafiyayyun turare guda biyu, daya cikin abayan Mama tazaba tadauka tabata tace âungo wannan zakisa jeki wankan, ki chanza breziya da wando kuma, akara wanke baki ba kyau miji yaji wariâ sokoko Rashida ke kallon Mama wai ba Mama ce mara lafiya ba take maganan wani miji? Ita Mama tadauka ta Riyad take sheâs just after her taji sauki kawai shine burinta, just to make her happy ta karbi wanda ta zaba mata tawuce, akwatinsu tabude tadauki bra da pant tashiga bayin dakin that is very neat tai wanka ta shirya tai alwala tabude turarukan ta fesa wow saida ta lumshe idanu sunada wani irin feminine scent mai dadi, yafa gyalen tayi akai tafito Mama ta bita da kallo sabida yanda yarinyarta takoma tsaf kalan yar masu kudi tai murmushi itakuma ta shimfida dadduma tai salla Mama tace âzoki zubamin abincin bikin kiâ dasauri ta juyo ta kalli Mama dake murmushi sai kawai ta tashi tawuce tadauki plate tana bude warners din ta debama Mama tuwo tazauna gaban gadon tana feeding Mama ahankali tace âMama ai kin warke ko?â Gyadamata kai Mama tayi tace âna warke tass bakiga inacin abinci baâ murmushi tayi tace âthank you Mama dakika warkeâ tana cikin bata abincin suka shigo dakin duk yanda Riyad yaso ya daure karya kalleta kasawa yayi baitaba ganin abaya yama wata kyau kaman yanda yaga wannan yama Rashida kyau ba, dudda Mama bata cinye tuwon ba but taci rabi, sai satan kallon yanda Riyad ke kallon yarta take kaman tace yadauketa su tafi kawai dai dan rashin lafiya ne, Mama tace âdeba kici kemaâ girgizama Mama kai tayi alamun bazata ci ba, Mama tace âRiyad kaga yarinyar nan batason cin abinci fa wlh sai kayi da gaskeâ murmushi Munir yayi duk suka zazzauna tareda Mama har magrib sannan suna tafi.
Yau kwanan Mama 3 a hospital sheâs recovering like magic tun jiya sukai resuming amman kiri kiri taki zuwa taki maganan ma sabida kar Mama tace ta wuce tatafi, tana zaune tareda Mama around 8 na safe Mrs Bugaje tashigo dakin ganinta tareda Mama yasa tace âba some of yan class naku naga a A&E ana wardround dasu ba? Wani department kike this week?â Ahankali Rashida tace âGynaeâ hararanta Mrs Bugaje tayi tace âmy friend stand up and goâ Mama tace âwai dama sun koma?â Mrs Bugaje tace âtun jiya ma taki zuwaâ dakanta Mama tayi abaya bada zafi sosai ba tace âwuce kafin na saba mikiâ tashi tayi tawuce wajen drawer daki tadauki jakanta taciro gogaggen lab coat dinta, daya daga cikin abayan da Riyad yasaimata ne ajikinta hakan yasa ta warware gyalen tai rolling aka sannan ta warware lab coat din tasaka tadauki stethoscope nata pink ta makala a wuya tadauki pink crocs nata tasa sannan ta dauki turaren ta fesa, tunda tana asibiti yasa bazata dauki jaka ba, pen ta dauka ta makala a pocket nata sannan tadau wani dan jotter tasa a aljihu, earpiece nata ta dauka zatasa a pocket ta tuna haryau Riyad bai bata wayanta ba kuma takasamai magana ahankali ta maida ear piece din jaka ta rufe, ta rufe wardrobe din sannan tajuyo takalli Mama da Dr Bugaje ke dubawa tace ânatafiâ âadawo lafiya Amaryaâ dan turo baki tayi tana kallon Mama sannan tabude kofan tafito tafara tafiya tawuce staircase daidai ta sauka kasa Riyad na zuwa wajen hada ido sukayi yana sanye da wani jumper dark brown daya haska fatanshi yasa bakin glasses a ido, ranan nan Mama tagayamai tanaso ya tsaya akanta tagama karatunta na likita hakan yasa yasan yes sheâs doing medicine but today is the first time yake ganinta cikin kayan dake nuna ita likita ce, ahankali yakai hannunshi ya zare glasses daga idanunshi yazuba mata mayun idanunshi, da sauri tasauke kanta kasa gabanta na faduwa azuciyanta tace bantaba ganin wanda baya kunyan kallon mace irinsa ba, murya chan kasa tace âina kwanaâ batare daya amsaba koya dauke ido akanta ba yace âina zaki?â Ahankali tace âdepartment namu munyi resumingâ yana kallonta still yace âwhich departmentâ da dan kankanuwan murya kaman ba Rashida ba tace âthis week ina outpatient department a gynaeâ gyadamata kai yayi yace âletâs goâ dasauri ta kalleshi but haryayi gaba hakan yasa tabishi suka jera har ward dinsu yabita sannan ya tsaya yace âgoâ agabanshi tawuce tashiga consulting room 2 yadan jima tsaye saikuma yajuyo.
Mama na zaune ita kadai tai shiru tana tunani though good tunani yau take akai knocking kofan tareda sallama daga ciki tai murmushi jin Riyad ne tashigo âshigo dâanaâ bude kofa yayi yashiga yana murmushi yawuce wajen gadon yaja kujera yana zama yace âyou look good Mama, ya karfin jikin?â Murmushi tamai tace âAlhamdulillah ya iyalinka?â Ahankali yace âAlhamdulillah Mamaâ murmushi tamai tace âka kwatanta adalci kaji, mata munada kishi dan haka ka lallashi matarka da kyau kaji Riyadâ gyadamata kai yayi yace âtoh Mamaâ cikin farin ciki tace âkaga nasoma samin sauki sosai ana sallamana muka koma gida sai afara shirye shiryen bikinku ko sabida Rashida ta tare gidan kaâ gyadamata kai yayi feeling happy ganin how excited sheâs with the whole wedding yace âMama kome kikeso haka zaâayiâ wani irin murmushi tayi harda dan kyalkyala dariya kadan tace âinaso ama Rashida lalle a hannu amata kwalliya saikuyi hoto kubani amaidashi frame nasaka a falona ina kallonku kullumâ dan murmushi Riyad yayi yace âto Mama haka zaâayiâ murmushi tayi sosai saikuma tace âtayani daga gadon na zaunaâ tashi yayi ya taba botur din dake dago gado gadon yataso Mama tai kwanciyan zama ya gyara mata bargo sannan yakoma ya zauna ganin tai shiru tana tunani yasa yace âtunanin me kike kuma Mama?â Ahankali tajuyo takalleshi cikin dan damuwa kadan tace âkana gani nakira mahaifinta na sanarda shi an daurama yarshi aure?â Shiru Riyad yayi, dan murmushi Mama tayi ganin baice komiba tace âI put you in a tight spot ko? Kona kirashi ma bazan sameshi ba yayi blocking dina tun lokacin amman nakan turamishi sakon waya duk ranan birthday Rashida na gayamai yarshi ta shiga shekara kaza kaza dakuma lokacin dataci jamb taci UTME aka bata admission medicine na aikamai sako amman haryau bansan ko yana ganin sakona ba ko baya gani baâ ijiyan zuciya ta sauke takalli Riyad tace âbari nabaka labari na yau Riyadâ.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 2ïžâŁ9ïžâŁ
Ahankali Mama tace âni yar jigawa ce, anan kauyenmu yake ance kakan kakana daga Morocco yake wai saisa mukeda haske, iyayenmu dani da Yayana Samaâila suka haifa, iyayena nada gonaki da dama a kauyen mu, Babana is a very very big farmer har su CNN sunyimai interview, banda nashi gonakin yanama mutane managing gonaki kaman gonakin sarkin kano nan marigayi Baba Ali naji yarasu, Allah ya jikanshi da rahamaâ Ahankali Riyad yace âAmeenâ yana kallon Mama jin she just mentioned Babanshi, Mama tace âdudda a kauye muke Babana yasani makaranta yace yanaso na zama yar jarida nima namai interview wata rana, yayana Samaâila shi baiyi boko ba tare suke komi na gona da Babana, kauyenmu ba school wani next village yakesa yayana Samaila na kaini makaranta kullum a machine dinsa saina dawo da dakainaâ tai shiru tace âina JSS 3 akwai wata rana nazo gida naga wasu maza guda biyu sunzo gidanmu na gaidasu natafi dakin Mamana, so daga bayane Baba kecemin ai sarkin kano ne da kaninsa Al Mustapha sunzo wajen Baba, nace Baba ina doki bangansu da kayan sarakuna ba, to alokacin nasan ashe sarakuna na private outing suyi normal shiga kaman kowa, gasu basu wani girma sosai ba Babana ya girmesu duka dan yadan manyanta, bayan kwana biyu Baba yacemin Kanin sarki na sonaâ Mama tadanyi murmushi tana kallon wani zoben dake hannunta tace âkafin kace me haka akamana aure anan kauye aka tafi dani gidan Sarautan Kanoâ.
Wani irin kallon Mama Riyad keyi to be honest besan Mama ba, dudda yasan labarin lokacin auren anata cewa Baffa yakaro aure daga kauye and Baba supported him shiyamai auren, shida baison shiga mutane, banda hakama yawancin idan zakaga matayensu da Alkyabba zaka gansu unless youâre very close to them ko kana zuwa bangarensu you hardly knows fuskansu, ko first wife na Baffan su is because tana zuwa wajen Mom akai akai yasa yasan ta daba hakaba dabai santa ba. Ahankali Mama tace âRiyad even though Mujitappa Baban Rashida yayi hurting dina deeply bazan taba iya ignoring the fact cewa that Man loves me and care for me kaman ba gobe ba, bai bar kowa ya hantareni ba, dakanshi yake koyamin etiquette na gidan Sarauta da sauransu, yasa aka cigaba da koyamin karatu a gıda, ya kuladani Riyad bai bar kowa yayi hurting dina ba hatta Jummai kishiyataâ tadanyi murmushi tace âance tana kishi dani alokacin sabida bata haihuba then nikuma bayan bayan 1yr da aurenmu saiga ciki watan cikin daya ajikina nafara ciwo sosai da saida aka kaini asibiti lokacin anmin all test but banda HIV banda komi nadawo gida yacigaba da kuladani yana nan nan dani itama Jummai surprisingly tana kula dani, tadena min kallon kishiya, she was so happy then zan haifa musu Babyâ Mama tadanyi shiru kafin ahankali tace âina around 5month Baba na da Mama na sukai hatsari a motan dazai kawosu Kano dubani, kawai abin yakara birkita jikina ina shiga 6month nai landing hospital ciwona was serious dahar ICU aka sani cus banajin magani, banci bansha na rame kaman tsinke, akamin test dayawa the next thing was inada HIV!â Mama tai shiru tareda fuzar da iska idanunta yayi ja tace âimagine ina around 1-2 months da ciki anmin all test baâaga HIV ba ina 6 months da ciki ace inada shi dole Muji ya yarda maza nakebi da cikina da aka fadamai inada HIV, an sashi yazo yayi test din shima da matarshi Jummai sukayi su negative abinda yasa yasake yarda da zargin inada HIV sabida laulayin ciki yasa babu abinda ya shiga tsakanina dashi tundaga watan farko harna 6 din nan cus bana iya komi Riyad mugun laulayi nayiâ Mama tai shiru tace âhaka nadanji sauki aka sallameni yatafi dani gida naje na samu an kira yayana Samaâila an tara jamaâa a fada dan Muji bai iya fushi baâ ta share fuskanta chan tace âkoran cin mutunci, koran toxarci, koran tijara akamin agaban kowa ana nunani ana shiga barayina bayi na watso kayana waje wai sabida cikin nema baâamin duka ba aka korani no one! No one Riyad, Babu wanda a masarautan nan ya tsayamin ba mai Martaba Baba Ali ba! Ba mai Babban daki ba! Ba sauran matan sarki ba! Babu ne kawai aka koramu ni da Samaâila ana tunkudaniâ runtse idanu Riyad yayi Mama tace âmunafita daga fada Samaâila yahau zubamin Allah ya isa bai yafemin ba wannan tijaran dana jamai da cikina ina fasikanci karna sake na bishi, Riyad haka yatafi ya barni dan uwana na jini biyar babu a hannuna ni da aka sallameni daga asibiti da safen ranan, nahau tafiya a hanya yunwa menene menene naje wani gidan abinci na wanke kwanuka na kusan kwana goma sannan natara kudi natafi kauyenmu nan ma Samaila yace ban isa na zauna ba, bashi bani nace to araba gado abani yace yaji haka yaraba yabani miliyan biyu nadawo nazo ina neman gida ahaka na sami gidanmu dakake gani nasaya akan miliyan daya agine ahaka nasai yar katifa nadan natsu nafara tunanin rayuwan to me yafaru? HIV Taya zan samu? Banda Mujitapa babu namijin daya taba rikemin hannu aduniya sai Babana da Yayana.
Nai tunani nai tunani narasa tayaya nasamu, nama kaina fada natashi natafi general asibiti, na hadu da Mrs Bugaje tun tana matsayin resident Doctor ta taimakeni da shawarwari da abubuwa da dama, dakuma ilimi kan yanda ake rayuwa da HIV, duk yanda zanbi nabi dan na samu Muji ya saurareni yaki bansan ya akayiba ko bibiyata Jummai take haka ta gano gidan nan ita tazo ta fallasama kowa na anguwan mu inada HIV nice Matar kanin sarki aka koroni menene menene, dabadan nina sayi gidan ba da sun koreni tuni, ahaka cikin wahala na haifo Rashida duniya ta CS, ban bata nono ba gudun karna bata cutan, duka kudadena na gado suka kare a siyamata madara da sauransu hakan yasa na dage nafara aikatau still ina zuwa asibiti ina karban maganin HIV da ake bamu free sabida yâata banso na mutu inaso nataso da ita inaso na rayu nayi accepting ni mutum me HiV ce, nacigaba da renonta harna soma gazawa ta karba aiki awajena tun tana primary school sabida Rashida nada kwazoâ hannu Mama tasa ta share fuskanta tace âGidan Sarauta wani irin gidane da bada kowa ya dace ba kaman ni yanzu Iâm one, haryau bansan yanda na sami ciwon nan ba but nasan itâs connected to gidan, banason wani alaka da gidan nan har abada!â.
đ« SANYI DA ZAFI đ«
âđ»M SHAKUR
EPISODE 3ïžâŁ0ïžâŁ
Faduwa gaban Riyad yayi sosai jin abinda Mama tace, ahankali Mama tace âgidan nan gave my life tabo dabazai taba goguwa ba, gidan nan yasa yâata is like this, ranan nan i told you karka shiga maganan nan sabida Jummai can hurt you Riyad basu da imani, look at yanda suka maida rayuwana yau, look at how far theyâre willing to go tana kulle innocent yarinya a police cellâ Mama tafashe da kuka tace âjibeni kaman tsinke nida keda kiba and Riyad nobody stood for me yayi defending dina, tsoro ne, menene oho but kowa stood there and watch me being humiliated, Riyad those people hurt me! An min sheri anmin kazafi, na wahala sannan poor child dina ta wahala look at Rashida, all her life washing plate da washing bayuka daban daban in different organizations takeyi just to feed me and sponsor school nataâ Mama tai maganan tana fashewa da kuka dayasa Riyad yatashi daga kan kujera soyake yama cema Mama sorry yakasa saikawai yajuya yafita da sauri ya shiga sauka kasa yana karasa sauka beben yana cin karo da Munir dake kokarin hayowa rikeda Basket na abinci da sauri yakama hannun Munir yashiga tafiya da sauri da sauri Munir yabishi hankali tashe yace âRiyad what happened youâre scaring me, Meya faru?â Saida sukaje jikin mota Riyad ya tsaya tareda dafa kanshi Munir dasauri yace âRiyad menene waiâ? Fuzar da iska Riyad yayi ahankali saikuma yakalli Munir yace âRashida is our cousin! Yarinyar Baffa ce!â Dawani irin sauri Munir yace âwait wait, watâ? Ya ijiye basket na hannunshi yana kokarin connecting dot din yace âMama ce daman matar Baffa daya kora me ciki?â Gyadamai kai Riyad yayi dasauri Munir yace âbut ai ni nataba ganinta sau daya tazo gaida Ammi tanada kiba could it be sabida pregnancy ko maybe lokacin ban wani yin wayau nayi ba sosai ba I think ina around 10yrs lokacin saisa ban gane ta ba?â Lumshe idanu Riyad yayi yadafa mota yana sauke ijiyan zuciya sannan yadago yakalli Munir yace âMunir Mama donât want anything to do with our family and Iâm here na auri Rashida without knowing su waye su? I want to tell Mama wayeni!â Da sauri Munir yace âidan tace ka saki Rashida fa?â Dasauri yakalli Munir saikuma yakasa magana yadan duka ahankali awajen yayi shiru even though wani bangare na cemai karya fadama Mama yanzu yabari a sallameta but another part na zuciyanshi na cemai gwara yafada mata here and now she deserves to know waye ke auren yarta, tashi yayi yakalli Munir dake kallonshi yace âletâs goâ Munir baicemai komiba yabi bayanshi suka tafi ahankali yabude dakin ya shiga yaga Mama na bacci peacefully.
Ijiye abincin Munir yayi yace âsheâs sleeping zomuje muyi sallaâ fita sukai salla by 2:00PM Rashida ta dawo ganin Mama na bacci yasa ta duddubata tai murmushi tazauna tana kallon kulan abincin tadauki plate tabude kulan jellof rice tadeba kadan cikinta harya saba bata iyacin abinci sheâs really missing her phone hakan yasa ta faraci tana cikin ci aka bude kofan Riyad ne hada ido sukayi da sauri ta dauke kanta ya kalli abincin dake plate din datakeci saikuma yakaraso ya ijiye wani waya wanda ga dukkan alamu sabo ne but bai bata kwalin ba ya ijiye gefen gadon ahankali yace âbe using this ur sim is insideâ kallon wayan tayi iPhone ne dudda batasan iPhone nawa bane dan bata saba dasu ba bataso ta karba but kuma batasan yanda zatai rejecting wayan ba, abu tahadiye a wuyanta murya chan kasa tace âthank youâ juyawa yayi haryakai kofa yace âbari naje if anything comes up call me my number is insideâ gyadamai kai tayi ahankali sannan yabude kofa yafice itakuma ta tsaya tana kallon wayan kafin chan tasa hannu tadauka tana taba screen din yabude gallery tafara shiga taga all pictures nata na yar vivo nata na wajen wanda yawanci hotunan pages na textbooks datake karatu dasu a library ne sai few pictures nata da lab coat da picture nata da Mama saikuma tashiga wajen waka taga songs dinta duka akwai murmushi tasakeyi sai kawai ta ijiye plate na abincin da duka baifi 3spoons tayiba ta kwanta jikin Mama tana kallon hotuna ahaka har akai magrib Mama tadan tashi taci abinci saikuma tasake komawa bacci magungunan ta da alluran dama suna sata bacci sabida abun ka da mai BP.
Zaune suke cikin mota wuraren 8 nadare gaban A&E, bude bayan motan akayi aka shigo Jummai dataci lafiyayyen shadda tadago kai takalli officer data shigo tana murmushi tace âthanks for coming Graceâ Grace tace âyouâre welcome Hajiya but wat is so urgent dakika kirani asibitiâ bandage dake saman hancin Grace Jummai ta kalla tace âI want to end this mutanen da yarsu tamiki this but I want to confirm something are you sure Sarkin Kano ne yazo yayi bailing yarinyar Grace?â Dasauri Garce tace â100%, Oga yafadi mana haka fa kinga yanda jikinshi ke rawa ne daya budetaâ mamaki yakara kashe Hajiya Jummai tace âhow did Riyad know Zainab? Lokaci da aka kori Zainab Riyad was maybe around 13 yrs, yanzu duka dukanshi heâs 36, Riyad da baya zama gida how ya sansu haryake maâamala dasu?â Saikuma ta kalli Grace tace âyasa kayan sarki dayazo?â Dasauri tace âno Ma, nothing shows heâs a king banda bodyguard dake binshiâ shiru Hajiya Jummai takarayi saikuma tadauki wayanta cus takasa yarda Riyad ne taciro hoton Riyad ta nunama Grace tace âshine?â Shiru Grace tayi bata wani kalli fuskanshi ba lokacin dazata shiga Rashida take kallo but kaman shi hakan yasa tace âeh kaman shi but Iâm not sure kinsan da daddare yazo and bana officer dasuke fitowa ne nikuma nake shigaâ gyadakai tayi tace âokayâ sannan tadauki wata bakar ViVa leather tabata tace âuse this hold body I will look for you soon when itâs time to cook the girl upâ murmushi Grace tayi tana hango how thick ledan looks da kudi ta karba tace âHajiya I will remain loyal forever and ever thank you Ma saida safeâ tabude motan tafice ta maida ta rufe Hajiya Jummai takalli wata mata dake gaban motan bakakirin da ita fuskanta sai uban muni ga kujera tace âkin shirya aikin ki Yar Mussa?â Da sauri matan tace âkwarai Hajiya! Rayuwata taki ceâ Hajiya Jummai tai murmushi tana kada kafa tace âsauka kije ki tabbatar kin zuba ko a abinsha ko a abin ci, saikinzo gidaâ Dasauri tace âtohâ sauka tayi anan parking space tawuce tana gyara hijabin jikinta sannan tawuce ta shiga cikin A&E tana sunnar da kai kasa, dakin cleaners tawuce dinsu tawuce anan ta dauki roban mop ta cire hijabi tasaka wani green riga da wando uniform sannan tafito ward tashiga gogewa tass kafin tawuce sama first floor lokacin 9:00 knocking gaban kofan 211 tayi but shiru hakan yasa tabude tashiga ciki Mama na bacci ga drip ga komi na aiki, Rashida itama tana zaune kan kujera but ta kifa kanta kan gadon takama hannun Mama tana bacci tana minshari kadan kadan dan bata gaji sosai yau ba, maida kofan Yar Mussa tayi tarufe tace âlaaa nazo goge goge suna bacciâ ta tsaya takalli dakin tass babu CCtV, bude idanu Mama tayi kadan dan ta dade tana bacci da sauri Yar Mussa ta juya taciro mop tashiga goge gogenta, dan tari Mama tayi jin wuyanta ya bushe sosai murya chan kasa tana kallon mai moping tace âdan taimakamin da ruwaâ ijiye mop din Yar Mussa tayi ta juyo da sauri ta taho tace âtoâ dukawa tayi tadauki bottle water guda daya daga jakan bottle water dake wajen tanajin dadi azuciyanta tace âperfect opportunityâ tabude goran tana tura hannu a aljihunta da sauri taciro wani syringe dake dauke dawani substance ta matsa da sauri aruwan tana jijjigawa, ahankali Mama dataji shiru tace âbakiga ruwan bane ko Rashida ta chanza musu wuri ne? Bude fridge kika dan Allahâ Da sauri ta taso tana murmushi tace âaâa naganiâ tamikama Mama goran tana ijiye marfin goran saman gadon sannan tajuya tacigaba da moping din da sauri da sauri, sosai Mama tasha ruwan thirsty kusan rabin goran tasha sannan tadauki marfin ta rufe, Yar Mussa tagama moping tazo gaban gadon takalli ruwan da Mama tarage tace âdan Allah dan bani Insha nima kishin nakejiâ Mama tace âkidauka karkisha ragowanaâ dasauri matan tasa hannu ta fizge ruwan har saida gaban Mama yafadi hakanan hakan Yar Mussa tace ânadau sabo bazan shanye ba wannan ya isa karmuyi asara bari naje kiyi bacci abinkiâ tana maganan tayi kofa bayan tadauki mop da bucket tabude kofan tafita tashiga next room tacigaba da aikacenta.
Mama tabita da kallo saikuma tace âhala batasan inada HiV baâ saikuma takalli Rashida da yau bata minshari sosai sabida batai aikin wahala sosai ba tashafa kanta tana murmushi tace âAmaryan Riyadâ knocking akayi aka shigo office din Dr Bugaje ce sanye da scrub tana kallon Mama tace âkinga sai yanzu nafito daga surgery nan dana gayamiki wlh nace nadubaki kafin natafi, akwai wani abu dake miki ciwo?â Tayi maganan tana makala stethoscope dan duba heartbeat na Mama, Mama tace âlafiyana kalau wlh kaman ki sallame ni gobe ma naje nafara shirye shiryen bikin Rashidaâ dan dariya Mrs Bugaje tayi tace âmother Inlaw of the year Mamaâ kafafun Mama ta kalla da sun sabe kusan rabi tace âAlhamdulillah Mama kin sami lafiya sosai Welldone Mama, youâre a superwoman, wannan hartai bacciâ tanuna Rashida, Mama tace âai Rashida gatada nauyin bacci kamanmeâ Mrs Bugaje tace âtom bari naje Mama saida safe, banda tunani kinji koâ murmushi Mama tayi tace âto nagode, a gaida yaraâ juyawa Mrs Bugaje tayi hartakai kofa Mama tace âDoctorâ juyowa Mrs Bugaje tayi Mama tace âina alfahari na sanki, nasan ko bani Rashida nada wata uwa da mentor, thank you for everythingâ dan blushing tayi tace âMama stop thanking me ki warke sabida ki koma gida nan da jibi ko gataâ Mama tace âshikenan a kiyi tuki ahankali dare yayiâ âtohâ tafadi tana fita Mama kuma tashiga shafa fuskan Rashida har bacci yasoma kwasheta kafin chan bacci yayi nasaran dauketa.
Jijjiga da bed keyi up and down yasa cikin nauyayyen bacci Rashida tadan bude idanunta sabida yanda motsin ke mugun damun kanta, kafin chan motsin yayi yawa tabude idanun gabaki daya tana tashi zaune, Mama tagani tana wani bankarewa tana kama cikinta tana. âHasbunaallahu wa niâimal wakeel, Lailaha illallah wayyooo cikina wayyooo cikinaâ dawani irin sauri Rashida tai ihu. âMamaâ daidai Mama tawani irin mirgino zata fado daga gado Rashida ta tareta takamata ajikinta tama rasa mezatayi, bata taba ganin Mama in this pain and agony ba cus tanada dauriya na ban mamaki, kankame Mama tayi datake abu kaman zata tashi ga kafafunta basa motsi tsabagen azaba tace âRashida cikina wayyooo Rashida cikina, Rashida cikinaâ âsomebody help me Doctorsssss!â Rashida tai wani irin ihu daya dauka akoâina daidai lokacin kawai hancin Mama yafara fitowa da jini dayasa tasake buga wani uban ihu. âDoctorsâ daidai nan Dr Mumina dawasu nurses suka shigo ganin Rashida da Mama akasa yasa tace âmeya sametaâ? Jikin Rashida kawai rawa take bamata iya magana ba, kankame Mama tayi a hannunta Dr Mumina tashiga saka handglove hakama Nurses din wasu Drs ma na shigowa aka daga Mama daga jikinta aka daura akan gado Rashida na wani irin kuka tace âwat happened to her? Why is she bleeding daga hanciâ Dr Mumina tama Nurse alamu tafita da Rashida wayanta Rashida ta dauka Nurse tafita da ita, rawa jikinta yake tana tsaye awajen Doctors sai zuwa suke ana shiga dakin da Mama ke, tanajin wayyyoo Allah cikina, cikina abinda Mama ke fadi kenan, tunda ta taso bata taba ganin Mama tai ihu tana kururuwa for ciwo ba sai yau, chan Rashida taji ana call Professor call him fast, taga nurses sun fito da gudun gaske sai kawai taji kafafunta na lankwashewa ta zube akasan wajen flat hannunta ya shiga rawa tabude wayan nata tashiga contact taga Riyad hakan yasa tai dialing number.
Yau sabida damuwa yamai yawa koda yagama abinda zaiyi da Haleema anan kan gadon ya kwanta bayan yayo wanka, wayanshi yahau kara hakan yasa yabude ido is so odd akirashi da night wayan yatashi yadauka Rashida tafito jikin screen din dayasa kawai yaji gabanshi yafadi fita yayi daga dakin yasauko kasa daidai wayan na katsewa yayi dialing number back yana ringing ya daga. Anatse yace âmeke faruwa?âNunfashinta kawai yakeji bata iya magana da kyar tace âzanâŠ..zan mutuâ katse wayan kawai yayi yakoma sama yashiga saka kaya Haleema na tashi dan tun ringing na wayan ta tashi tace âina zaka Babyâ? Ahankali yace âsleep fita zanyiâ zatai magana yadauki car key yafita da sauri yashiga motanshi yana danna remote gate yabudu yaja motan aguje dayake dare ne wlh cikin 5 good minutes ya iso asibitin sama yahayo aguje, tana zaune a inda take akasa ta hangoshi yana tahowa yana kallonta she felt as if her strength is coming towards her, dawani irin gudu cikin kuka ta tashi tai wajenshi batai wata wata ba tawani irin fada cikin kirjinshi ta kankameshi gamgam kaman wani zai rabata dashi tana wani irin kuka tama kasa magana, ahankali yasa hannunshi on her back yariketa yama kasa magana sai breathing fast, suna ahaka saiga Mrs Bugaje da hijabi tana gudu sosai tawuce su tai dakin kawai his mind tell him something hakan yasa yayi hugging nata so tight tareda manna mata peck a wuya, cikin wani irin murya na lallashi yace âstop crying Jewel, comeâ yadagota hannu yasa ya sharemata fuska yace âIâm here now Mama will be fine kinjiâ? Gyadamai kai tayi yakama hannunta saiya sauka kasa da ita yayi wajajen wasu kujeru ya zaunar da ita yaduka agabanta yace âstay here bari naje sama naga meke faruwaâ gyadamai kai tayi yatashi yajuya yakoma sama gabanshi faduwa kawai yake non stop, direct yabude kofan dakin daidai lokacin da babban professor kecewa ke daga hannunshi yana kallon wristwatch dinsa yace âTime of death 4:57AMâ chak Riyad ya tsaya kanshi na wani irin making bell sound yashigabin kowa na dakin da kallo tundaga kan Mrs Bugaje datai mutuwan tsaye tanama Mama wani irin kallo da idanunta ke kallon sama ga jini a hancinta da bakinta na gangara har lokacin, kafin ahankali Professor yakai hannunshi dake sanye da glove ya rufemata idanu sannan yaja farin zanin gadon yarufeta.
SANYI DA ZAFI
EPISODE 32
Cikin minutes Buba yayiarranging canopy ganin ranayasoma fitowa ga jama’a atsaye, aka kawo taburmaitundaga makarantan sa akashimfida awaje, Munir daRiyad suka kawo likafani dahandglove da turare dasuaudugu Matan anguwa dukababu wacce tai attempting yimaMama wanka da Mrs Bugaje ketambaya duk sunki karsu samiHIV, wai tsoro, hakan yasa MrsBugaje ta karbi komi tashiga kairuwa ciki ita zatayi.
Ahankali Rashida ke budeidanunta takalli Mrs Bugajedake kanta anatse tace”Rashida!” Tashi tayi zaune dagudu tana kallon matan layinsuda hijabai da suka cika falonwasu na kuka suna kallontawasu na mata kallon tausayisai kawai ta tashi kamanwacce bata hayyacinta tayiuwardaka tana daga labule MrsBugaje taje wajen tace “zanmaMamanki wanka Rashida come”
sannan tawuce ciki Rashidatabita tazauna tana kallonMama kuri, handglove MrsBugaje tasaka sannan tafaraRashida sai kallon Mama take,zata kuskurema Mama bakitaga bakin Mama yayi greenda abin saida yasa tabudebakin Mama da kyau har throatdin Mama was green dasauritakalli Rashida but from the wayyarinyar ke kallon Mama kasanbata hayyacinta saita fasamaganan takarasa yima Mamawan
Wuraren 8:10 wani dan dattijonmutum dake kama da Mamayasauka daga machine danBaba Liman yamai kwatance,hannunshi rikeda da yar jaka,fuskanshi ba yabo ba fallasayashiga yima jama’a sallamaBaba Liman na ganinshi yace”Sama’ila ya hakuri”? Ahankaliyace “hakuri sai ma’aiki” butaaka bashi yazauna yafara alwalaRiyad sai kallonshi yake irinhope you’re happy yanzu tamutu? Yana gamawa da Riyadda Munir da Baba Liman daBuba dashi Samailan sukaicikin gida har zuwa uwardakanda makara Rashida na zaunetana kallon Mama da anriga anshiryata tsaff tagansu Riyad saikallonta yake yanda take kallonMama ganin zasu dauketa yasatarushe da kuka tahau kabar da
mutu? Yana gamawa da Riyadda Munir da Baba Liman daBuba dashi Samailan sukaicikin gida har zuwa uwardakanda makara Rashida na zaunetana kallon Mama da anriga anshiryata tsaff tagansu Riyad saikallonta yake yanda take kallonMama ganin zasu dauketa yasatarushe da kuka tahau kabar dahannunsu tace “wallahi Mamana da rai wlh kubarmin ita, zatatashi” zata kama makaran Riyadyariketa kuka take da haki ganinan dauketa ansa aciki an dagamakaran saita kara sumewaajikinshi karbanta Mrs Bugajetayi yatashi suka fice aka sallaciMama aka kaita makwancintaRashida bata tashi ba.
Wuraren 1 suka dawo dagamakabarta akai sallan zuhursannan aka kawo abinci wandaRiyad yasa Munir yakira hotelkitchen nashi aka dafa akakawo abinci a big big kulaakakai cikin gida bangarenmata sauran kulan waje,abunka da anguwan yaku bayi
mata sauran Kuan waje,abunka da anguwan yaku bayisai jama’a suka fara tururuwakaman gidan biki ana zuwa cinabinci anama Mama addu’a.
Riyad dinma gashi nan ne kawaitunanin Rashida yake kuma bahalin ya shiga cikin gidan danmata sun cika gidan, yaki kulauncle din Rashida Sama’ila,yadaiga Baba Liman namaiexplaining komi chan yakiraRiyad din yace “bismillah Riyad”bayabo ba fallasa yazo wajenyabashi hannu Sama’ila yakarba yace “Allah sanya alheri,Allah baku zaman Ipy” AmeenRiyad ya amsa ahankali sannanyatashi daga wajen.
Wuraren 2 Rashida tabudeidanunta dake mata nauyikaman duwatsu Mrs Bugajedake kusada ita ta kalleta dasauri tace “kin tashi” fuskanMrs Bugaje take kallo chankuma cikin yar muryanta dabata fita sosai bakinta nawaniirin rawa tace “da gaske Mamana tarasu”? Yanayin sigan dayanayin da maganan yafito
yanayin da maganan yafitodaga bakin Rashida sai kawaiyasa hawaye ya sauko dagafuskanta ta gyadamata kai kafinahankali tace “yes RashidaMama tarasu har an kaita, prayfor Mamanki, yar aljanna ceMama in sha Allah wani irinnumfashi Rashida keyi kamanzuciyanta zai bare yarabebiyu sai kuma ahankali tanadaga kwance awajen kawaitajuyama Mrs Bugaje baya tamanna fuskanta a bango tanawani irin kankame jikinta isas if ma batasan metakeyi ba,ahankali Mrs Bugaje tadaurahannu kan jikinta ta dagotatana kallon fuskanta yanda yayijajir gabaki daya tace “Rashidacry Mama tarasu” sarawakanta yayi takulle idanuntatace “Mama na, Mama?” MrsBugaje tace “eh Maman ki” tanama Mrs Bugaje kallon asalinwacce bata hayyacinta tace”to menene amfanin rayuwanayanzu? Banda kowa Mama tatafi, Rashida batada kowa!”Fashewa da kuka sosai MrsBugaje tayi sabida tausayinRashida dayasa matan falon
Rashida dayasa matan talonsuka taso suna shigowauwardakan jin sautin kuka sosaikawai Mrs Bugaje ta kankameRashida gangan ajikinta tace”Rashidaaaaaa l’m so sorryabout your Mom, wayyoooAllah kirjina Rashida yau kinbani tausayi kaico! Naso aceAllah yana barin wani dan wanidanasan definitely zai barmikiMama, Rashida kiyakuri karkicebakida kowa wlh kinada mu,gani ga mijinki Riyad ga BabaLiman, Rashida you are notalone” duka yan dakin kallonRashida suke da aka rungumeidanunta sunyi jajir da fuskantaamman bata kuka idanuntama kaman sun juyane batasanmetakeyi ba gata nan ne kawai.
Mrs Bugaje saida tai kuka tagodema Allah sannan tasakiRashidan tace “muje kiyi salla”kallonta Rashida tayi tace”salla an kirako bari nafara kaiMama tai alwala saini nayi”tafita daga jikin Mrs Bugajeda sauri tana mikewa tsayetayi falo da sauri, Mrs Bugaje
tama banamataaIai Motn
tayi falo da sauri, Mrs Bugajetama kasa motsawa sai MatanBaba Liman ne ta tashi da sauritabita tace “Rashida’ tsayawatayi tajuyo takalleta tace “laaaanatuna kayan Mama nazodauka” tawuce uwardaka dasauri tabude sip tadauki wanikaramin jaka tashiga sakarigunan Mama awajen tace”bari nai sauri” tamaida sipdin tarufe tajuyo kowa yakasacemata komi tayi falo kotakalmi bata sakaba tarike jakangam tana tafiya Matar Limantabiyota da gudu tanajan wanihijabi data gani kan igiya tana”Rashida Rashida” ganin batajitafiya kawai take yasa tafarakwalama mijinta kira. “MalamMalam” amman har Rashidatafito tayi gaba Riyad na zauneyaga fitowanta dasauri yatashidaidai Matan Liman na fitowaitama tace “Malam Rashidatahada kaya wai zata kaimaMamanta a asibiti” tareta Riyadyayi takalleshi da sauri tananunamai jakan tace “Mamazan kaima kaya jirana take”kallonta yayi daga sama harkasa ba takalmi akafanta da
Ronta yayi daga sama harkasa ba takalmi akafanta dagaita sai abayan daya siyamata dadankwali daure akanta fuskantais looking reddish.
I WANT TO GIVE YOU ONEMORE EPISODE FROM UPDATENA GOBE YA ZAMTO GOBEJUST ONE EPISODE ZAN BAKU
SANYI DA ZAFI
EPISODE 33
Hannunshi daya yasa yarike mata hannu yamikamamatan Liman dayan hannunshi alamun tabashihijabinta bashi tayi yajuyo yakalleta ya warwarehijabin yana kokarin samata ahankali yace “to sakahijabi kafin kitafi” yayi maganan yana samata hijabiya kalli jakan data rike gangan yace “babu safaajakan Mama tace ki kawo mata safa muje ciki kidauka saimuje” wani irin murmushi ta sakinmai dayabayyana fararen hakoranta tajuya da sauri tai cikingidan batare data kalli su Buba dasuka tattashisuna kallonta ba anatse Liman yayi sallama cikingidan mata suka amsa Buba ma yabishi ciki yanamaSama’ila magana yace “muna bukatan ka muje”tashi yayi yabisu sai Riyad shima yabisu falon sukashiga Matan Liman tace “tana ciki tana zazzago dakayan durowas su” ciki suka shiga hakan yasasauran matan dake dakin suka fito banda MrsBugaje dahar lokacin take inda take, jikin kofanuwardakan Riyad ya tsaya yana kallonta dawani irintausayi aka zazzauna Baba Liman yaje gabandrawer ahankali yace “Rashida” batare data kalleshiba tace “sauri nake safa nake nemawa Mama”hannunta yarike chak dayasa tajuyo takalleshi cikinihu yace “Rashida! Ki natsu! Maman ki tarasu!”Tarasu! Tarasu!! Tarasu!! Haka kalman ke singing abrain nata dayasa tai wani irin ihu tana taushekunnenta tawani zube awajen tace “nooo” ahankaliBuba yace “yanadaga cikin shikashikan musuluncishine imani da kaddara mai kyau da mara kyau,Allah yama Mama cikawa, ga dan uwan Mamankiyazo daga kauyensu” yanuna Sama’ila dake kallontayace “mutuwa ba dadi Rashida amman kiyakuri, kidaure, ki cije ki hadiye, kima Mamanki addu’a,agabank12:08
Maman RashidaâŠniâŠniâŠ.Mama na ni, nawa MyMama achan”? Kai! Wani irin fadowa hawaye sukayidaga idanun Riyad yanda kalaman ke fita dagabakinta adaburce, akuma hargitse, ya gyadamatakai gently yace “Mama ta rasâŠâŠ” “Noooo000o!”Rashida tai wani irin ihu tafashe da wani irin kukada majina yafeso daga hancinta har zuwa baki tanawani irin babbaka kuka tana dukan kirjin Riyad dababu karfi a hannunwanta, daidai Munir ya isoshima yaci birki ya tsaya yana kallon yanda Rashidake kuka beating Riyad chest, kuka Rashida takedake tsumarai daidai nan shima Buba ya iso damanyan abokanenshi mota guda sukayo dawatamota doguwa cikeda hikima da dabara yace “Munirkayi procedures kabiya komi abamu gawanta mutafidashi” yakalli Riyad yace “Riyad take her to the carkujiramu tunda bamusan gidansu ba” ahankali MrsBugaje tace “I will go with you Riyad nima bansangidan ba” daga Rashida dake kuka yayi kawai tasheme a suma daukan ta yayi chak yawuce mota yaijiyeta abaya.
Within 1Omin Munir yagama komi aka basu Mamasuka sata abayan luxurious hadaden bus dasukazodashi akaja motocin lokacin 6 yawuce na safe akatafi Riyad na gaba har anguwan su da alreadymutane sun taru a layi da masallaci, parking akayi,aka fasa key dake kofar gidansu sannan aka shigagidan da Mama Matan anguwa suka faffara zuwaana shiga cikin gidan, Riyad yadauki Rashida daharlokacin take a sume itama yayi ciki da ita MrsBugaje ta karbeta Baba Liman ya sanar za’ai sallaby 9 danuwanta zai iso anything 8:00dagakauyensu.
SANYI DA ZAFI
EPISODE 34
Shiru Riyad yayi saikuma yace “just ka kawominkayan sawa gobe, I can’t leave her alone like this,she has no one, babu anybody a anguwan dayayimaking attempt yama kwana da ita” gyadamai kaiMunir yayi yawuce yatafi shikuma yakoma cikingidan batare daya kalli Sama’ila dake zaune a kofargidan ba, falo yashiga yawuce uwardakan tanakwance inda ya barta tana bacci lips nata yagasuna motsi ahankali yaduka awajen yakai hannunshisaman goshinta yaji jikinta kaman wuta wayanshiyasake cirowa yayi dialing number Mrs Bugaje dayakarba ringing daya tadaga ahankali yace “she’srunning temperature Ma” ijiyan zuciya Mrs Bugajetasauke tace “she must! Ko ruwa batasha ba tunsafe, if you can get her to eat something kafin nankabata paracetamol idan temperature yaki kwanciyaget water and towel kadan goga mata ajiki” ahankaliyace “okay” katse wayan yayi yatashi yafitacompound kulolin abincin da aka kawo daga hotelnashi yaje yaduba babu komi ciki an cinye tass,makota ma sun wanke a ijiye wucewa yayi wajeganin yanda Sama’ila ke kallonshi yasa yace “barina sayo mata magani bata da lafiya” gyadamai kaiyayi yace “toh Allah sawake” mota yashiga yabarwajen, shikuma Sama’ilan yashigo ciki uwardakanyaje yakalli Rashida dake sambatu cikin baccinzazzabin Mama kawai take kira, girgiza kai yayikawai yatashi yafito tsakar gida ya shimfida tabarmaya ijiye pilow daya dauko a uwardakan su damanyariga yasa gidan akasuwa yana saidawa yabamayar gadonta Alhamdulilah ta aurar da ita batabarmai kaya akaiba yaji bala’in dadın hakan mijintava tattarata sutaur can kauyan su agayara kwanciya
SANYI DA ZAFI
EPISODE 35
Zufa yaji yana keto mata sai nishi take, ahankaliyadagota yakalli jikinta dasauri yadauke kai whitesinglet ne acikin dogon rigan da white inner skirtperky huge boobs nata daya gani yasa yadauke kaidasauri dan da abayan zai ciremata saiyaji yakasasai kawai ya rungumeta yana shafa bayanta itakumatafara lumlimshe idanu ahaka yana shafa matabayan genuine bacci yadauketa ajikinshi shimaahaka yayi baccin rikeda ita thank god yasawayanshi a silent dan kiran Mom dana Halima saidaya kashemai batir.
Yadanyi nisa kadan a bacci yaji tana rawa dakafafunta cikin bacci bude idanunshi yayi yakalletafrom the way she’s doing yasan fitsari takeji baijintayi fitsari jiya all through ba dasauri yatashi yanadagata bude idanu tayi kadan takalleshi hannunshiyasa yakamata suka fice Sama’ila na tsakar gidankan tabarma yanajan minshari hanyar daya ganiyake kyautata nan ne bayinsu yayi da ita kafin sukaifitsarin yazubo mata tsayawa tayi chak ta kalli kasahakan yasa shima ya kalli kasan sai kawai tafashedawani irin kuka mara sauti dayasa ta bashi tausayiahankali yace “shiga bayi lemme get you water andanother clothes” Wajen wasu robobi daya gani yajega karamin basket na sponge da soap kawaiyadauka yadawo inda ya barta ganin bata motsaba,hannunta yakama sannan yabude bayin that is veryclean yasamata bucket din da basket na soso yace”shiga bathroom” hannu tasa tagoge fuskantatadaga kafanta da kyar ta shiga bayin, shikumayakoma daki yabude wardrobe nasu but almostduka kayan wajen na Mama ne daga yanayinsu waniganamasgo daya gani yaje wajen yabude kayan tane duka agage very neat Dogowar riga daya fara
duka kayan wajen na Mama ne daga yanayınsu wanlganamasgo daya gani yaje wajen yabude kayan tane duka agoge very neat dogon rigan daya faragani a sama na atampa ya dauka yaga pant yagabra dudda sun tsufa but they look neat daukansuyayi yakoma hanyan bayin yace “here are theclothes nasa miki akan rope” yawuce yadawocompound ya tsaya andan jima chan sai gata tafitobutansu tadauka ta tsugunna tana alwala sai kukamara sauti take sannan ta tashi takoma ciki yabi tada kallo yakalli kayanta dayaga ta shanya ma tawanke abayi dawowa yayi dakin yaganta kandadduma tana salla tana kuka zama yayi yanakallonta ta rama sallolinta na jiya sannan ta kwantatana kallon gefe daya yanajin sheshekan kukantahar aka kira asuba yatashi yatafi mosque.
Bayan yayi sallan asuba hotel nashi yakoma yayiwanka ya chanza kaya dan nan Munir yakaimaikayan, wajajen 7 yadawo gidan with breakfast natabut luckily yaga tana bacci Mrs Bugaje itamahartazo tanaso tamai magana but tanaso tagamainvestigation.
Yau 3days da rasuwan Mama, Riyad shi kadai yakekwana da ita ganin yanda babu wanda zaiyi hakan,he noticed batada friends, wayanta has been withhim but babu wani wanda yakirata banda some fewplaces datake aiki dasuka kira suna nemanta yaamsa da tadena aiki. Bata magana da kowa, theonly thing dayasan yana bata ta amsa is that coffeeko abinci bataci, dudda kawunta Sama’ila try talkingto her amman ko kallo bai isheta ba haryau takidaga fuska ta kalleshi.
Wuraren 8 Riyad yayi parking akofar gidan yagaSama’ila akofar gidan dawani mutumi kalakalan sadan kauye da Baba Liman, kashe motan yayi daidai lokacin yane salIama da mutane yana kurban ledan
more, Rashida have to start a new life away fromthis hausa da Mama ta raineta ta girma ta tasoaciki, death is painful! Rashida yakalla yaje indatake hannunshi yasa yadagota tadan bude idanuntakadan dasuka kumbura ahankali yace “let’s gohome” hijabi yadauka yasamata sannan yadagatayajata dan kaman bata gane komi harzuwa waje,bayan mota yabude mata yasata aciki ya kwantarda ita sannan yarufe kofan yakarasa zuwa wajenmasallaci yasami Baba yace “Baba zamu tafikayansu na dakin za’a iya rabarwa idan da masu so,ko akai gidan marayu, sai watarana Baba” yabamaBaba hannu, Baba Liman ya amsa yace “karikeRashida amana marainiya ce ba uwa ba uba kawukuma kaga kalansa, duk randa ta zama likita kugayyace mu zamuzo Allah maka albarka Riyadyanda mahaifiyarta ta yarda dakai haka nima nayarda dakai dari bisa dari, nasan bazaka cutar daRashida ba dan haka Allah baku zaman lafiya, Allahya albarkaci aurenku” ahankali yace “Ameen” harmota Baba Liman yarakoshi ko kallon Sama’ilaRiyad baiyiba ya shiga yadauko kudi yabama yarananguwa, sannan yakara dauko bandır na 1k gudabiyar yabama wani babban matashi yace yakaimaBaba Liman yasan yabashi bazai amsaba, sannanyaja motan yabar anguwan feeling emotional,rayuwa kenan! Kowa fa saiya mutu is just time!.
SANYI DA ZAFI
EPISODE 36
Bini bini yake tuki yana lekata ta mirror na motaidanunta a lumshe suke fuskanta is swollen isreddish, tun ranan datai wanka haryau bata karaba,wayanshi yadaga yakara a kunne yana driving dahannu daya chan yace “idan akwai any bayi a sidenaku or ma’aikata send them away, and stay wajengate idan nazo i will call you to open it for me”katse wayan yayi ya ijiye yasake kallonta kusan20min tafiya sukayi dan akwai holdup a hanyasannan yakai zagaye yayi again sabida ta indayakeson ya shiga yana sake kiran Munir sannan yaijiye wayan yana kaiwa gate din Munir yagani tsayeyabude gate shiga da motan yayi Munir ya maidagate din yarufe sannan yajuyo da sauri yatahoshima Riyad na saukowa daga mota Munir yatahowajenshi da sauri cikin whispering yace “tarekuke?” Gyadamai kai Riyad yayi Munir yace”mezamu gayama Ammi cus kasan Buba baigayamata ba, wat are we going to say?” Dan ijiyanzuciya yasauke ahankali yace “I don’t know” shimaMunir shiru yayi Riyad yajuya yabude bayan motanjakan goyonta yafara dauka yajuyo yabama Munir yakarba sannan yakalleta ahankali yanda idanunta kearufe kafin yasa hannunshi gently yadagota kamanbabu jini ajikinta tasowa tayi tana bude idanuntakadan hawaye na zubomata shiru yayi yana kallontakaman yazare kowani irin pain takeshi shi ya karba,saikuma ahankali yasa hannunshi yakai kanfuskanta ya share fuskan nata murya chan kasayace “we are home let’s go” hannunta yakamayafito da ita da kyar take tafiya haka sukai cikiMunir biyedasu abaya ahankali yasa hannunshiyabude kofar flat din Ammy da callama yar gajera
Munir biyedasu abaya ahankali yasa hannunshiyabude kofar flat din Ammi da sallama yar gajeraabakinshi Ammi na zaune a falo kan kujera ta ijiyeMacBook akan cinyanta tasaka glasses tana aiki,sallaman dataji yar kadan yasa tajuyo da kanta hadaido tayi da Riyad dake kallonta dasauri yasaukekanshi kasa tabishi da kallo da yar matashiyandataga yarikema hannu kanta na jikinshi ta jinginadashi idanunta a lumshe saikuma Munir dataganiyarike bagpack yayi tsuru kawai ranta yabata waniabu amman tadaure tace “kushigo” shigowadukansu ukun sukayi suka sake tsayawa duk sunkasa magana sun kuma kasa wani abu, itama Ammisaita tsaya kallonsu batace komiba da kyar Riyadyadago kanshi yakalli Ammi hada ido sukayi dasauri yasake maida kanshi kasa saikuma chan dakyar yace “can I take her up Ammi?” Yarinyar looksick hakan yasa tace “okay” juyawa sukayi Muniryayi gaba Riyad biyedashi ganin bata iya daga kafatahau bene yasa Riyad ya dauketa ahankali sukaisama duk Ammi na kallonsu.
Dakin dake next to na Ammi Munir yabude dakinyahadu is very simple daki yarinyar Sister Ammi kezama aciki duk idan tai hutun school tazo gidaawajen Ammi take zama, har gado Riyad ya kaita yakwantar da ita, ijiye jakanta Munir yayi yafice,ahankali Riyad yasa hannu yacire mata hijabin dakejikinta ya ijiye gefe yana kallon atampan dake jikintatun na ranan nan yasauke ijiyan zuciya sannanyasake kwantar da ita ahankali yadanja duveeyarufe mata kafafu saikuma yaduko saitin fuskantaya matso da bakinshi ya manna mata kiss a goshikafin yatashi ahankali yafita daga dakin yawucekasa tundaga kan staircase ya hango Munir tsaye afalon Ammi na kallonsa saikuma yakarasa saukowaahankali yana satan kallon Ammi dake kallonshianatse yasauke kanshi kasa yasami kujera yazaunada sauri Munir ya zauna gefensa Ammi tabisu dakallo kafin amatse cikin muryanta da baya nuna
anatse yasauke kanshi kasa yasami kujera yazaunada sauri Munir ya zauna gefensa Ammi tabisu dakallo kafin anatse cikin muryanta da baya nunafushi ko ihu kokuma wasa tace “wa kuka kawomingida?” Dan dago kai Riyad yayi yakalli Ammisaikuma yasauke kanshi kasa yakasa maganaahankali Munir yace “matar Riyad ce Ammi” DasauriRiyad yadago kanshi yakalli Munir dashima kekallonshi saikuma yadan juyo kanshi akasa ahankaliyace “Ammi I married her 6days ago” sosai Ammike kallonshi cus bataji any labari a gidan nan ansanda sarki zai kara aure ba, koko anmasan inda sarkiyake tadaiji anata cewa wai yayi tafiya, urgenttafiya, anatse tace “Riyad” gently yadago kanshi yakalli Ammi ahankali tace “wayansan kayi aure bandaMunir? Mai babban daki tasani?” Girgixa mata kaiyayi, ahankali tace “Baffan ka yasani?” Nan magirgiza mata kai yayi alamun a’a chan kuma tace”Mom dinka tasani?” Sake girgiza mata kai yayistrictly Ammi tace “who knows about thewedding?” Ahankali yace “Buba” da sauri ta gyarazama jin Babanta yasan about the wedding saikumatace “how did Buba yasan about this wedding”?Ahankali Munir yace “shine ya karbamai auren”sosai Ammi ke kallonsu baki tabude zatai maganaahankali Riyad yace “she’s our cousin Ammiyarinyar Baffa ne” dawani irin sauri Ammi takalleRiyad kafin ahankali tace “wat do you mean yarinyarBaffa? Is that Maryam?” Shiru Riyad yayi Munir yace”Ammi we are talking about biological yar Baffanmu not su Maryam” Munir yahau bama Ammilabarin komi daga A zuwa Z da rasuwan Mama dakomi ba karamin girgixa Ammi maganan yayi ba taishiru tana kallonsu daga ta kalli Riyad saita kalliMunir, Riyad dinma har ya rame kana ganinshikasan he has not been eating and resting properlysabida damuwa, ahankali tace “katashi kaje kaiwanka kaci abinci and rest I will take care ofRashida in the mean time dole na sanar da maiBabban dak da II Kkoma meka fa’uwa da
yarinyar Baffa ne” dawani irin sauri Ammi takalleRiyad kafin ahankali tace “wat do you mean yarinyarBaffa? Is that Maryam?” Shiru Riyad yayi Munir yace”Ammi we are talking about biological yar Baffanmu not su Maryam” Munir yahau bama Ammilabarin komi daga A zuwa Z da rasuwan Mama dakomi ba karamin girgixa Ammi maganan yayi ba taishiru tana kallonsu daga ta kalli Riyad saita kalliMunir, Riyad dinma har ya rame kana ganinshikasan he has not been eating and resting properlysabida damuwa, ahankali tace “katashi kaje kaiwanka kaci abinci and rest I will take care ofRashida in the mean time dole na sanar da maiBabban daki da Baffan ku koma meka faruwa theyneed to know wa kuka kawo gidan yasan yarshi kaauro accepting nata or not as yarshi is totally up tohim, kaidai ka aureta matarka ce so dama ba zamanshi zatayiba, so I will tell them” dan dagokai Riyadyayi yakalli Ammi adan shagwabe mugun kalloAmmi ta zubamai tace “me kake kallona?” Ahankaliyasauke kanshi kasa murya chan kasa yace “Ammiplease don’t tell them now at least tadan warketasami kanta for now let’s keep her wajenki secret”kallonshi Ammi tayi saikuma tace “tashi kaje kaciabinci” tashi yayi ahankali babu musu yatafi dinningMunir yabishi sosai yaci abinci rabon dayaci abincihaka harya manta itakuma Ammi tawuce ta tafisama yadan saci kallonta saida yaci yakoshi sannanya tashi sanin Ammi na sama yasa yawuce yafita.
Tnx
Pls Continuation
Part 3&4
Pls part 5
Thanks, please part 5
Page 62