Search
You have no alerts.

    DUKAN TAIKI

    Daga marubuciyar

    Ku yi mana adalci

    Aure A Yau

    Sandar dukan uwargida

    Miji goma

    Iya ruwa

    Wani auren

    Ranar kuka

    Da walakin

    Matar shige. Da sauransu

    08028966015

          PAGE 1

      Da farko zan fara da bayanin sunan labarin nan, karin magana ne wanda ake cewa (An bar jaki ana dukan Taiki) Taiki shi ne jaririn jaki mai rauni, to ya kamata a ƙyale jaki a daki Taiki? Ku biyo ni cikin labarin don ku ji ainahin ma’anar sunan labarin. Ina iyaye? Ina masu shirin zama iyaye? Har su ma yaran ba a bar su a baya ba. Duk wata uwa ya kamata ta duba wannan labarin in sha Allah za ta tsinci wani abu da zai taimaka wajen tarbiyyar yaranta.

        Farar safiya ce, misalin ƙarfe shida da rabi, gidan ya yi tsit, sai Hafsa dake tsaye a kitchen, cikin hanzari take yin aikin amma kana kallonta za ka san tana cikin damuwa, tana yin komai ne da ƙarfin gangar jiki, amma zuciyarta cike take fal da rauni da damuwa mai tarin yawa, hakan ya samo asali ne saboda mummunan labarin da ya same ta da asubar nan, na cewar an kama ɗanta ya yi sata kwanan shi uku a station an rasa wanda zai yi belin shi. Ta gama fere doya ta zuba a tukunya ta ɗora a gas, a maimakon ta rage wani aikin, sai ta nemi waje ta zauna a kitchen ɗin, hawaye suka fara silalo mata,  idan ta tuna rayuwarta ta baya, ta kuma kalle ta a yanzu sai ta tambayi kanta shin cigaba ta samu ko baya ta ci?

    Ta kammala aikin, tana shirin kwasar kayan ta kai dining, mijinta Usman ya shigo, sanye da jallabiya, murmushi ɗauke a fuskar shi ya furta “Beb, ba ki gama ba ne?”

    Ta juyo ta kalle shi, fuska babu walwala ta ce”Na gama”.

    Ya ce”Bari na taya ki ko?” Ya ɗauki wasu kayan, ta ɗauki sauran suka fita.

    Yaran gidan suna dining ɗin a zaune suna jiranta cikin shirin kayan makaranta, mace ce da namiji, namijin Sa’eed shekarunsa goma sha huɗu, macen kuma Humaira tana da shekara sha biyu, kallon arziƙi babu wanda ya yi mata a cikin yaran ballantana ya gaishe ta, sau ɗaya ta taɓa yi wa ubansu ƙorafi a kan rashin gaisuwar, ya nuna mata ba komai ba ne, ai yara ne, ita da su kowa rayuwarsa yake yi a cikin gidan, kamar ba matar mahaifinsu ba, wata rayuwa ake yi a gidan, kamar yan gidan haka, a bayyane suke nuna mata ba ita ce ta haife su ba, sannan ba su da wata alaƙa da su, mahaifinsu ne kawai nasu, lamarin yana ba ta mamaki kuma tana kyautata zaton wannan karatu ne aka biya musu ko ma ta ce ake biya musu, domin ta ga kishinta ƙarara a idanun dangin mahaifiyar yaran, don da alama suna takaicin rabuwarsu har yanzu. Ta zubawa kowa nashi abincin, sai dai ɗaki ta koma a maimakon ta zauna ita ma ta karya, Usman ya bi ta da kallo, kaɗan ya ci abincin ya bi ta ɗakin, ya same ta a banɗaki, bai jima da zama ba ta fito, ya ƙarasa ya rungume ta yana faɗin”Me yasa ba ki ci abinci ba? Ba na son rashin karyawarki da wuri fa”.

    Ta ce”Ba na jin yunwa ne”.

    A kunnenta ya raɗa mata”Ok na gane ni kike buƙata ko?”

     Ya fara wasa da jikinta, hawaye ya ƙwace mata, ta fizge cike da takaici ta ce”Don Allah ka rabu da ni, kamar ba ka san tashin hankalin da nake ciki ba?”

    Ya ƙanƙance ido da alama ranshi ya ɓaci ya ce”Tashin hankali na me?”

    Tana kuka ta ce”Ɗana ne fa a kulle ka sani, ta ya zan samu nutsuwa?”

    Ya yi guntun tsaki ya ce”Idan ɗanki yana kulle laifina ne? A kan me za ki huce a kaina? Rayuwarki da ɗanki da ban, rayuwarki da ni mijinki da ban, idan matsala ba ta shafe ni ba ki daina saka ni a ciki ta hanyar tauye min haƙƙina, don ko wannan rashin walwalar da kike yi ni fa cutata kike yi”.

    Takaici kamar ta rusa ihu, ta share hawayen, ta nufi gaban mudubi, za ta fara shafa mai ta ji ya murɗa key ɗin ɗakin, hakan ya tabbatar mata me yake shirin yi, tun kafin ya taɓa ta ƙuncin zuciyarta ya linka wanda take ji, tana yi masa kallon mamaki ta ce”Amma ka san sauri nake yi zan fita ko?”

    Ya ce”Fitar ta fi kula da mijinki? Idan har haka ne to ki tafi ɗin kawai, amma idan kin dawo ki tabbata gidan iyayenki za ki wuce ba gidana ba”.

    Kuka ya ƙwace mata, ta rasa wannan masifa, Usman yana taƙama da ganin yadda iyayenta suke son aurenta da shi, shi yasa yake amfani da wannan damar yana cutar da ita, yana taushe ta da nisanta ta a shiga lamarin yaranta, ta rasa da me za ta fassara lamarin, kishi ne ko mugunta?

     Ya juya zai bar ɗakin, ta bi shi ta riƙo shi, ba ta daina hawaye ba ta ce”Ka yi haƙuri”. Sai ya shiga share

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!