SANDAR DUKAN UWARGIDA
GIDAN ABDUL
Mace ce wacce a ƙiyasi za a iya ba ta shekara talatin da biyar, tana tsaye a falo tana kaiwa da kawowa, hannunta riƙe da wayarta, wacce a yau take jinta tamkar maƙiyiyarta saboda yau ɗin ta kasance ‘yar aiken da ta kwaso mata labarin da ta kira shi da baƙin labari, wayarta ƙawarta ce amma a yau dai ba haka abun yake ba, domin kuwa ta yi mummunan gani a cikinta. Hausawa sun ce labarin zuciya a tambayi fuska, fuskarta kawai za ka kalla ka san tana cikin yanayi mara daɗi na ƙunci, a cikin zuciyarta kuwa ji take tamkar ana gasa zuciyarta saboda zafin da ƙirjinta yake yi mata.
Ta sake kallon agogon wayar da ya nuna ƙarfe tara da rabi, sai ta ga kamar ma lokaci ba ya gudu saboda yadda ta matsu mijinta ya dawo gidan, kiran da ta yi masa babu adadi, tana shiga amma ba ya ɗagawa.
Ta sake dubo vedion da ya hargiza ƙwaƙwalwarta a wunin yau ɗin ta kunna, tabbas shi ne, mijinta Abdul’aziz wanda take jin idan babu shi ba za ta iya rayuwa ba, shi ne yake zaune kusa da wata mace ƴar ƙaramar yarinyar da ba ta fi sa’ar ƙanwarta ta huɗu ba, suna vedio a wajen cin abinci cike da nishaɗi, idan ta kalli yadda yarinyar ta kwanta a jikinsa sai ta ji kamar zuciyarta za ta fashe, amma kuma ta kasa daina kallo, daga lokacin da aka turo mata zuwa yanzu ta kalla har ba ta san adadi ba.
Ƙarfe goma da minti goma ta ji ƙarar motarsa, a ƙa’ida ita ce take zuwa ta buɗe masa ya shigo da ita, amma yau ta ji sam ba za ta iya yin hakan ba, ya ƙaraci horn ɗinsa ya gaji ya fito ya saka mukulli ya buɗe gidan ya shiga sannan ya buɗe get ɗin ya shigar da motar, ya mayar ya rufe a ransa yana kyautata zaton Hafsa bacci take yi.
Waƙa ɗauke a bakinsa ya shigo ɗakin yana faɗin”A bar wa rai abin da ya so, a bar wa zuciya abin da ta so…”.
Ganin Hafsa tsaye a falon ya katse shi, da mamaki ya ce”Maman Afna lafiya?”
Hafsa ta haɗiyi wani yawu ta kasa cewa komai.
Abdul ya ce”Hafsa lafiya? Ni fa na yi zaton bacci ne ya yi miki nisa ba ki zo kin buɗe mini ba, me kike yi a tsaye? Ina yaran?”
Nan ma dai ba ta kalle shi ba ballantana ta yi magana.
Ya ce”Ai shikenan!”
Ya cire hular kansa ya ajiye, ya cire babbar rigar, ya zauna yana cewa”Allah mai iko! Yau kuma da haka na samu gidan nawa, ni Hafsa ko dai taɓarya kika haɗiya ne?”
Ya ƙarasa maganar yana dariya, domin sarai ya san rigimarta tun suna da jajayen sahu idan ta birkice da ƙyar yake saita ta.
Ya ce”To ni dai na lura yau ruwa ma sai na samawa kaina a gidan nan, zan samu abinci ko na je na siyo? Kin ga sai na siyo tun kafin dare ya raba su tashi, ko kuma na tafi gidanmu na ci”.
Nan ma dai ba ta kula shi ba, sai ma hawaye da ta fara yi, wanda ya sa ya gane abun nata na gaske ne kuma mai dalili ne, sai ya kau da wasa a fuskarsa ya ce”Hafsa zauna mu yi magana”.
Ta ƙi zama sai ma juya kai da ta yi.
Ya ce”Ki zauna, kin ji ko?”
Ta zauna tana danne kukan da yake taho mata.
Jikinsa ya fara yin sanyi ya ce”Me ya faru? Mene ne ya saka ki kuka? Ko jikin ne?”
Ya ƙarasa maganar yana ɗora hannunsa a kan ƙaramin cikinta, ta ture hannunsa ta ce”Ni fa lafiyata ƙalau”.
Ya riƙe hannunta yana cewa”To mene ne? Ko wani abun kike so a siyo miki?”
Ta ce”Ka ga, ni ka daina yaudarata da wannan ƙaryar kulawar taka, ka je ka nunawa wacce ka damu da ita, wacce har kake jin darajarta ta kai har ba za ka iya jurewa ku kama hotel ko wani gidan ku raɓe ku biyawa juna buƙata ba, sai ka nuna zalamarka a titi har ma kana yi mata vedio cikin nishaɗi”.
Tun da ta fara magana ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, kunya da fargaba suka dirar masa, haɗe da mamakin ta inda ta samu labarin yau ya haɗu Farha.
Ta cigaba da cewa”Kai yanzu ko kunya ba ka ji ba? Da mutuncinka da ƙimarka da girmanka, amma duk ka take so ya zauna a titi kana rungumar ƴar ƙaramar yarinya wacce a haihuwar kaji ka haife ta? Ka manta kana da ƴaƴa matan nan ne? Ka manta kana da ƙannai?”
Ya ɗaga mata hannu ransa a ɓace ya ce”Ke ya isa haka, ban gane wannan shirmen da kike zayyanowa ba? Ni ɗin ne na je na rungumi wata? Ashe ba ki da hankali har yanzu Hafsa? Shikenan sai mace a gidanta ta ci ta ƙoshi ta tada kai da fulo ta kira ki a waya ta dinga tsara miki ƙarya saboda tana baƙincikin rayuwar aurenki, ke kuma ki hau kai ki zauna!”.
Ta ce”Babu wacce za ta yi maka ƙarya haka kawai, me aurenmu ya tsarewa wata da za ta so haɗa mu faɗa?”
Ba ta jira amsar shi ba ta kunna vedion ta miƙa masa, ya karɓa babu musu, yana kalla gabansa ya faɗi nan take ya fara tunanin yadda aka yi wani ya yi musu wannan vedion, amma sai ya daure bai nuna ba ya ja dogon tsaki yana miƙa mata wayarta ya ce”Hafsa! Yanzu shikenan kishin naki ɓa har ya kai ki kasa gane ni ko? Duk shejaraun da muka yi da ke ki ce har yanzu ba ki iya bambance kamannina da na Abdussalam ba?Saboda kishi ya rufe miki ido har za ki fara yi mini ƙazafin zina ko?”
Gabanta ya faɗi ta kuma shiga taraddadin shin da gaske ba shi ɗin ba ne?Tana kallon vedion, ta kasa cewa komai, mijinta ƴan biyu ne irin waɗanda suke matsananciyar kama da juna, bambancinsu kawai shi ne Abdussalam ya fi mijinta haske kaɗan, kuma ya fi shi fara’a, domin asalima shi Abdussalam mutum ne mai barkwanci, wannan fara’ar da ta ga na jikin hoton yana yi sai ya sa ta yarda ba shi ba ne har zuciyarta, har ta ji nadamar zargin shi da ta yi.
Ta ce”Ka yi haƙuri na yi zaton kai ne, kuma da na ga kalar kayan da ka fita da shi ne”. Ya ce

0 Comments