You have no alerts.

    BAKAR TA’ADA

    BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

    1&2

    SHIMFI’DA

    Sunana Asiya Sani Toro. Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta. Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce. Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro ƙarami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana’ar a garin. Fiye da shekaru saba’in kenan, amma har yau ba’a juya wa sana’ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta.

    Gidanmu babban gida ne ƙwarai da gaske. Idan na ce babban gida ina nufin mai ɗauke da ahali daban daban masu yawa. Ko a ƙofar mahaifinmu Alh. Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne. Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai ƙifadi da kutunguila. Duk wani rikicin da yake ƙofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko wanne irin cigaban ɗan wata sai nata yaran kawai.

    Sannan komai cikin dabara da girma take yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin da take ƙullawa ba. Sai mu da muke rayuwa da ita kullu yaumin. Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfiɗa akan haka za’a tafi, sai dai ranar da ta samu baƙin rana Baba ya bijire mata. Ya’yanta biyar. Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa’a ta ta girme ni da wata uku.

    Sai Mahaifiyata Hajiya Asma’u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba, amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin haƙuri. Idan na ce haƙuri, ina nufin haƙuri gangariya, irin haƙurin nan da mai yinsa kan saka a al’ummar da suke kewaye da shi su halaka saboda hakkinsa da za su yi ta ɗauka. Yaranta takwas cif. Yaya Salisu, Yaya Rabi’u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima.

    Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a ɗakinta, kuma maza, ya sanya Mama ta tisa ta a gaba da masifa da tuggu. Kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba kowa ne yake mu’amala da ita ba. Duk gidan bakinsu ɗaya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta bata ta, take adawa da duk wanda za ta ga ya mu’amalanci mahaifiyata. Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma tana cikin gidan bangarenta daban.

    Sai Hajiya Sahura muna kiranta da Innah. Yaranta biyar. Na farkon ma mun dan girme masa kaɗan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba ɗaya Saliha. Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsakanina da Nazira ba. Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a ɗakinta ba a dalilin Nazira. Bare ita kuma da ɗakin Goggonmu take kwana.

    Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za’a yi Inna ta haɗa wa Goggo sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta dabarbarce ta, ta hana ta yin mu’amala da Goggo ta hanyar faɗa mata Goggo ce da gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din ‘yan kallo ne. Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya mallaka da har ake fatan ya mutu?

    A da kam ya yi arziki ƙwarai da gaske, domin duk girman gidanmu shi ya zaga ya gina shi, sannan mafi yawa na cikin zuriyarsu shine ya biya musu suka sauke farali. Amma tun shekarar da aka haife ni ya haɗu da ‘yan damfara suka yi masa sanadin karayar arziki. Har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfaɗo ba. Yan’uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi. Amma a hakan Mama take faɗin Goggonmu ce zata ja komai…BAK’AR TA’ADA

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!