Search
You have no alerts.

    QURUCIYAR JUMMAI

    BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

    GARGADI
    wanan littafi ban yishi dan cin zarafin wata ko wani ba,suna ye,da wurare da ke cikin duk ansa ne domin ya kayatar da masu karatu

    TUNASARWA

    a guji juya littafin ko ta wane irin tsiga ne,domin malakin marubuciya ne

    SADAUKARWA

    na sadaukar da wanan littafi gare Ku iyaye na a bisa namijin kokarin da kukayi wurin tarbiyarta dani,bani illimi both western and Islamic educationa,ina alfahari daku a duk inda Nike,without u am nothing confia to who I am today.jazakallahu fil jannah

    JINJINA
    GARE KU

    MEMBERS NA AMEENCI WRITERS

    AMEENCI FANS 3

    WRITERS ONLY

    WATA RAYUWAR FANS GROUP

    COMMENT NOVEL’S

    MY NOVEL GROUP

    SURBAJO 4 LYFE

    R&A KITCHEN

    MACE KYAUTAR ALLAH GROUP

    CHIEF’S CORNER

    YAN MATAN HUTU NOVEL GROUP

    ABOVE ALL ADMINS NA WATA RAYUWAR FANS;MOPOL,RUKKY,MEELAT AND LEEMA JAZAKALLAHU FIL JANNAH

    DA SAURAN GROUP DIN DA BAN SAMU RUBUTA SUNA YENSU BA

    ALLAH BAR ZUMUNCI AMIN

    1-2

    Dan dazo yara ne akkala sun kai su goma,suna biye da wata yarinya wadda bara ta wuce shekaru goma ba,sai waka suke rere wa,kamar haka;

    Wata ke fadin;jummai, jummai,jummala,,,,,,,

    Sauran yaran na amshi,kamar haka;mai jagwalin ido ba karfi sai tonan fada.

    Jummai ce ta juyo ta murguda masu baki,tana cewa dana tona,na tone June.

    Wata yarinya ta amshe,jummai mai kan kwakwa,cibike mai katon cibi

    Sauran suce eyeeerr mai katon cibi.

    Haka suka yita mata waka har suka rakota kofar gida.

    Ita ko sai shan majina take, hanunta guda na baki yana tsutsar babban yatsarta,guda na kanta tana faman Susan dumbujin sumar kanta wanda yayi jajawur saboda tsabar dirty da kasa da yara suka tula mata a wurin wasa, domin duk yadda a ka daura mata dan kwali sai ta yar dashi,haka takalmi.

    Umman suce ta leqo data Ji hayaniyar yara.

    Ta riqe kunen JUMMAI.
    Tace me kuma kika barkato yau?

    Wata bakar yarinya,gajeruwa Wanda ta fisu kiba,tace umma jan MU tayi gidan sale mai lesson, wai muje leken shi ta ramin get din gidan shi yana wanka.

    Shine aka kama mu, yasamu kama kune, bayan yace mu wuce ta fara zagin shi cikin waqa.
    Sale sale salele

    Bakin kwarto
    Salele

    Amalala
    Salele

    Kullum sai ya shanya katifar shi
    Salele

    Mai gadin gidan alhaji ammany
    Salele

    Barawo kaji
    Salele

    Axxalumi
    Salele…….

    Shine yasa aka kamo ta ya zane ta,yasa rabe ya mata ature da kasa,muko yace mu rakata da waqa har gida.

    Umma tace ya mata kyau ai, jubeta kamar mahaukaciya.
    Kuje gida Alawiyyah.
    Ke kuma wuce ciki kiyi wanka.

    Daga murya tayi tace allawiya mu hadu gurin mai masara bakin titi….

    Umma tayi mata wanka, ta wanke kan nan sosai da gaban ta Wanda yake cike da qasa.

    Vaseline umma ta shafe ta dashi ta Saka mata purple riga yar kanti, sai black hulla.

    Tace ci abinci kije ki tsare ma yayar ki masara ta dawo tayi sallah.

    Da yake bai fi taku goma ba daga gidansu zuwa bakin titin.
    Tana zuwa daga gefe ta tsaya.

    Aysha ko kallon ta bata yiba tana ta aikin gasa masaran ta.

    Wani yazo yace nawa nawa masarar?
    Aysha tace qarami naira talatin
    Babba naira hamsin.

    Jummai tai caraf, karya take Mallam.
    Karami naira goma
    Babba Naira ashirin.

    Yace ya akayi haka.
    Jummai tace gidan mu daya, haka nan aka kasa mata,ita ke qara kudi Dan tsabar keta da bakin ciki,kada ya qare da wuri, ta koma tayi aikin gida…

    Mutumin yace tunda haka ne bai saya.

    Aysha da mamaki take kallo jummai.

    Haka mutane suka yita zuwa sayan masara jummai na korar su, wasu su saya, wasu su wuce.

    Aysha ido cike da hawaye tace,haba jummai menene dalilin ki nayin haka,masarar nan fa kwanar sa uku a gida ba a sai da ba,yanzu idan umma taji labari kin San bara taji dadi ba.
    Tace oh yanzu ma zanyi kashin kasuwar da tushe,tunda cutar mutanee ake yi,masarar kwana uku ake sayar wa a matsayin na yau.

    Tace wai me ma ya kawo ki ne?
    Tace sallah akace kizo kiyi

    Aysha tace shine bakyi fada min ba tun dazu?

    Jummai tace yanzu ai kin sani ko?””tana zarey mata idanu.

    Tashi tayi tace gashi nan sai na dawo.

    Zama tayi ta budea lema ta rufe fuskar ta””wai kada a ganta tana gashin masara””
    (Oh ni halima,da magrib ake shiga lema,ba ruwan sama, ba rana)

    Wuta taba masarar sosai ya babake,yadda ba wanda zai saya, sai data gasa da yawa, ta kashe wutan duka.

    Sai tsaki take tana duban hanya har yanzu aysha bata dawo ba

    Gashi su Alawiyyah sunki fita wasa.

    Can sai ga dan dazo yan wasa maza da mata, ai da gudu tabar kujerar masara ,tayi wurin su.

    Tace rabe samo kwali mai karfi,salama SAMo bakar leather.

    Bayan sun samo ta yayanka,ta shirya cikin ledan, yayi kamar damin kudi, sanan ta nade shi,tace alawiwi aje gefen titi.

    Gefe suka koma,suna jira suga wanda zai dauka.

    Aka ci sa’a kuwa sai ga sale mai lesson, yasha wanka, sai kumbo yake””as fa babban yaro””….

    Wai wai gawa yayi,yaga ba mai kallon shi,ya dauka cikin style…
    Jummai tace yau zaka ci ubanka a hannu na………

    L££MA💞
    [07/01, 14:41] ‪+234 812 140 7930‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    🌷🌷🌷🌷🌷🌷
    QURUCIYAR JUMMAI
    🌷🌷🌷🌷🌷🌷
    🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    HALIMATU SADIYA MUHAMMAD
    L££MA💞

    @AM££NCI WRITER’S ASSOCIATION📚

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!