Search
You have no alerts.

    BACCIN SO

    Cike gidan yake makil da jama’a, kana ganin yanayin tsarin ginin gidan kasan irin gidan masu dan rufin asiri ne daidai gwargwado, babban compound ne mai dan madaidacin girma dakeda wata yar kodaddiyan milk gate dayake a bude sabida jama’a dake shiga da fita. Yammata ansha makeup ansha anko, sun zagaye wata yar budurwa dakana ganinta kasan itace Amaryan sabida yanayin tufafin jian gaban DJ dayake buga kida yana chanza wakoki anama Amarya liki yan 50, da yan 100naira….

    Duk wannan kidan da hayaniyan da ake bugawa bacci take acikin dakin dakeda dan duhu dan an sauke labulen window, kaman an tsikareta firgigita tabude idanunta tana kallon saman silin na dakin dawani irin sauri ta tashi zaune gashinta nawani irin zubowa bayanta mai tsawo baki kirin dayake a tsefe, sanye take da atampa wanda kana gani kasan sabuwa ce anko kuma dan tayi kama da na mutanen tsakar gidan yan biki, an manta dinkin doguwan riga dayamata wani irin bala’in kyau a jiki, very simple style mara nauyi kwata kwata, waige waige tashigayi kaman mai neman abu sai kawai tamike tsaye zumbur tana yarfe hannu karamin lips nata ya furta “Ammi” wanda muryanta baya fitowa, saita shiga tafiya ahankali ahankali still kalle kalle take tana shafa fuskanta da kanta tana sosa gashin data shiga hargitsawa yafara komawa wani iri kawai tabude kofan dakin, jama’a ne birjik afalon ana hayaniya, tana bude kofan kowa yadago kai yakalleta jikake falon tsit sai kuskus da aka fara, kanta tasauke kasa ahankali, saita cigaba da tafiya ahankali batare data hada ido da ko mutum daya na falon ba bakinta na furta. “Ammi, Ammi, Ammi” ba lallai ma kaji metake cewaba idan bakazo kusa da ita ba, sai gyaramata ake kowa na cire roban abincinsa daga kasa, kawai tawuce tayi kofa tafita jama’an dakin na kuskus. “Yarinya kyau iya kyau amman kan ba dadi sam, sam”. “Wai ahaka aka haifeta koko jinnu ne cus kyawawan yara haka daman ance yaran jinnu ne”? “A’a wannan fa haka aka haifota da tabin hankalin ba jinnu bane, yoh yarinyar da asibitin mahaukata ma ake kaita”………
    Jama’a ne cike a compound din ga rawa anayi tana fitowa kawai tafiya tashigayi har lokacin kuma kanta akasa tana magana ita kadai “Ammi, Ammi” tana tafiya tafiya irin wacce ba direction dinnan nan da nan jama’a suka fara kallonta.
    Amaryan dake filin rawane ta hangota taja tsaki takalli daya daga cikin yammatan wajen tace “je dan Allah ki kirawa mahaukaciyan chan mamanta kafin ta hargitsamin biki, dan wlh tabatamin biki sainaci ubanta kafin akaini gidan mijina” dasauri kawarta tace “toh bari naje” fita daga cikin filin rawan tayi tai bayan gida ta nufa inda mata ke girki dagudu tayi wajen mata mata tadan manyanta akalla zatai 46yrs haka tana sanye da same atampa da kowa yasaka tace “Ammi ga Amirah chan tsakar gida zata fara haukan” anatse Ammi tajuyo takalleta kafin tai magana matan dake kusa da Ammi tace “wai ku yaran yanzu maisa baku da tarbiya ne iyye haka ake magana Zainabu”? Turobaki tayi tace “to karya akayi? Danma nazo nafada mata ai danayi shiru abina kwashe nemanta anjima…..” Ammi bata tsaya jinsu ba wucewa tayi da dan sauri tazagayo cikin compound din tanabin ko’ina da kallo tana nemanta da idanu gabanta nadan faduwa ta tare wata yar yarinya tace “kinga mini Amirah Baby?” Baby tace “tana waje tana nemanki Ammi” dasauri Ammi tasaketa tai hanyar gate tana zuwa taganta awaje tafiya take still ba takalmi akafan dasauri Ammi tasa hannu takama hannunta tace “gani nan Amirah” Ammi tai maganan tana kai dayan hannunta kan kafadarta tajuyo da ita tanadan maida ijiyan zuciya sabida kalan saurin datayi, ahankali for the first time sai yarinyar tadago kanta Ya Rabbi! Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin daya hallicci kowani bil adama, dan yarinyar nada kyau, wani irin kyau da kafin kaga mace mai kyanta sai an tona, sak Amminta tundaga whi

    0 Comments

    Heads up! Your comment will be invisible to other guests and subscribers (except for replies), including you after a grace period.
    Note
    error: Content is protected !!