HAYATEEM 1&2
BismillahirRahmanirRaheem.
Fadi da tsawon nisan da dajin yake dashi ya zubawa manyan idanuwansa yana kallan shuka da ganyen hakukuwan da suka cike gurin Wanda babu hanyar wuce a gurin idan ma kace wucewa zakai to sedai Kabi hanyar da adda ko wuqar ringa sare ganye dan Ka ringa ganin gabanka Wanda su hakan ba komai bane a garesu sbd sun saba haka suke rayuwa a cikin ganye da shukoki hakama yawo da wuqa me tsananin kaifi da dafi a jikinsu kaman dole ne kokuma ace al’ada ce me karfin gaske sbd yanayin karni da ake ciki na safarar mutane Ana saidawa a matsayin bayi,
Rayuwa ce ta koina zaka iya haduwa Wanda sukafi Ka karfi su raunana rayuwarka suyi safararka zuwa inda zasu siyar a matsayin bawa,
Ba iya dan Adam daya ko biyu ko uku koma da yawa ake nuna karfin hakan ba hadda gari sukutum masu safarar basu Bari ba suna cinye gari da karfi su tattara suyi safararsu.
ANJOM GHAZ
Garin ANJOM GHAZ gari ne dayake zagaye da ruwa masu ya wan gaske gabas dinsa yamma,kudu da arewansa kafin manyan hakukuwa da bishiyoyi masu tsayi da hadarin gaske da suka rufesa a zagaye duk kuwa girmansa,
Idan Ka shigo daji ne me girma da nisan gaske dayake dauke da macizai masu yawa wanda hakan ya samu ne sbd tamkar suna kiwonsu ne sbd yanda suke baza abincinsu da abubuwan da sukasan macizai na so dan zama a guri,
Daga inda dajin ya qare kafi ne da tsaro suka kafa masu tsananin karfin da babu Wanda zai iya karyasu sai jinin shugaban garin wanda shine yayi kafin sbd zaman lafiya da tsaron jamaar garinsa dan haka wannan kafin baya barin Miciji ko daya shigo wa garin iyaka cinsu dajin Wanda duk baqon Daba gayyatarsa akai ba shigo wa garin kokuma Wanda bai saniba ya nufo garin baya kaiwa yake haduwa da ajalinsa sbd tsananin hadarin dayake garin,
A duk girma da tsananin yawan garin ANJOM babu Wanda baida yanci da kwanciyan hankali a garin,
Babu Wanda babu tsari a jikinsa na al’adarsu,
Allah ya rufa musu asiri sosai a garin sbd arzikin qasa da Allah ya bas,
Basu da talauci sbd kusan kowa nada tarin arziki kalan nasa,
Babu bare kusan kowa dan uwan kowane sbd samun jajirtaccen shugaba Wanda babu kamarsa a jajircewa,Zarrah da karfi tareda rashin tsoro,
Asalin sunan garin ANJOM GHAZ ya samo asaline ne daga asalin kakannin shugabansu na yanzu wato GHAZ ALI Wanda asalin sunan na ahalinsu ne wato ANJOM kakansu na farko kuma ANJOM Wanda shine ya kafa garin Shiyasa garin yake da sunansa.
A yanzu GHAZ ALI shine shugabansu Wanda yake na uku a tarihin shugabancin ANJOM kuma Wanda shine ya dauko kakansa ANJOM da karfi da Zarrah tareda taurin zuciya da rashin tsoro ba kaman mahaifinsa ba daya zama me sanyi sosai.
Lokaci ya tafi sosai kusan duka kakakkani da iyaye sun rasu a yanzu daga ghaz Ali sai iyalansa da suke rayuwa cikin mulki da kwanciyan hankali da Shaquwa tareda aminci.
Matarsa daya Amma sai ‘ya’ya Hudu mace uku namiji daya,
Namijin ne qaraminsu gaba daya ‘yayan,
Shine namiji kuma shine me rauni da tsananin tausayi,
AYANAH itace babba Wadda tayi gadon Mahaifinta a gurin tsananin so da kaunar Yan uwanta fiyeda kanta da komai,
Bata hada kaunar kannenta data kowa,
Bata iya karban abinda basu samu ba,
A ko Yaushe sune a gabanta ba buqatarta ba Wanda hakan duka koyarwa ce da raayin hakan da mahaifinta ya saka a ranta tin tana Qarama sosai sbd kasancewanta babba dan duk ranar da babu shi itace a dolen dole zatai shugabancin garin sbd shine gadonta na farko da garin zasu Bari ta fara hawa sai idan bata da lafiya ko rashin hankali kokuma idan tanada ‘dan data Haifa Wanda ze hau a maimakonta shi kuma idan ya sauka a lokacin ne shugabancin ze dawo hannun Wanda ke Binta a kannenta.
NURAT itace me bin AYANAH itama kaunar iyaye da Yan uwanta a jininta yake sedai ita tanada fada,
sai ZUHRAH wadda mahaifiyarsu take tsananin Ji da ita dan haka ita gata yasa lalaci yai mata yawa amma itama tana tsananin son Yan uwanta Wanda duka a jinin su abin yake,
ABAAS GHAZ Wanda asalin sunansa ABBAAS shine qaraminsu Wanda yakeda tsananin rauni fiyeda Yan uwansa da suke mata hakan ya saka ya kasance Wanda ake tsananin tausayi a cikinsu,
Tsananin tausayi da kaunarsa suke fiyeda kowa,
Rauninsa da yayi yasa baya iya ko shiga mutane baya sakewa a koina bare iya shiga koina saida Yan uwansa musamman Ayanah da itace tamkar kariya da kuzarinsa sai kuma mahaifinsa.
Magani da kowane irin kokari anyi na kawar masa da hakan amma Sam babu nasara dan haka suka hakura suka barshi Akan lokaci kila zai iya sauyasa wata ran zuwa jarumin namijin da suke fata.
Ghaz Ali ya bawa yayansa gata da dukkanin tar biyan da suke buqata tareda shaquwa me tsanani da sakewa a tsakaninsu,
Dashi da yayansa babu boyo sai sakewa da kauna me karfin gaske,
A duka fadin ANJOM GHAZ babu inda zasu gifta baa basu girma me tsanani ba,
Girmamasu ake yi tamkar mahaifinsu ghaz Ali wasu guraren ma idan anje tamkar zaa bauta musu ake yi kasancewan zamani ne da musulmai da masu addini daban daban suke zaune kalau cikin aminci da kwanciyan hankali tamkar Yan uwa.
Rayuwa a ANJOM GHAZ rayuwa ce da kowane dan Adam ya samu zaiwa Allah godia da samunta,
Rayuwa ce da mutane daga duniya daban daban suke fatan samu sedai tayi musu nisan da baza su samu ba,
Rayuwa ce ta kwanciyan hankali da nutsuwan da manyan Masarautu da dama basu samu ba sbd babu fitina babu tashin hankali,
Gari ne da wasu garuruwan da dama suke kiransa da gidan kwanciyan hankali,
Gari ne da basa karban bakon da basu San komai akansa ba bare Yan gudun hijira ko yan ci rani hakama gari ne da baya Aminta da kowane irin gari ko Masarauta ko wace iri sbd ikonsu suma dasuke Jin sunada shi.
Gyara tsayuwa Ghaz Ali yayi yana sake zubawa fadin dajin dabai iyaka idanuwansa yayi zuciyarsa na sosuwa da tsananin radadin masifar datafi kowace fara fadowa garinsa da zai iya bada rayuwansa dan basa kariya sbd garin anjom ghaz shine gata da rayuwar ‘yayansa da duk Ranar da suka tsallaka wajen garin suka barsa zuwa wata duniyar daga ranar kaddararsu zata sauyane zuwa wadda baisan ya rayuwa zatai dasu ba,
‘Yayansa sune rayuwarsa dayake tsaye cak akansu,
Yayansa sune ginshikin rayuwan daya tsayu ya ginawa anjom ghaz,
Yayansa sune bazai taba iya barin wannan masifar ta fadawa ba sai idan babu ransa a duniya,
Mutuwansa fitar ransa a kirjinsa itace kadai zata Bari yayansa su fuskanci wannan masifar dayake Jin tamkar kirjinsa zai qone sbd Zafin baqin cikin dayake cikinsa,
A taurin zuciya da Zafinta da Allah ya basa yasa ya zabi akawo masa gawar ‘yayansa kaf a jere a gabansa cewan sun mutu yafi masa Akan Ayi farautarsu zuwa a siyar a bayin wata qasar suyi qasqantacciyar rayuwar Bautar bayin da har kwanciya sarakuna ko yayan sarakuna zasu riqa yi dasu.
Wannan zazzafan kakkarfan raayin na GHAZ Ali yasa duk Wanda yake ANJOM hakan ya kafu a ransa sun zabi mutuwa Akan a kamasu a tafi dasu bauta qasar da kaddararsu zata sauya har mutuwa.
Matansu ma kusan hakan suka zaba mutuwa Akan barin a tafi dasu a maidasu dabbobin kwanciya da biyan buqata.
Numfashi me zafi Ghaz ya sauke yana rintse idanuwansa kafin ya juyo ya kalli tarin mutanen da suka zo farkon garin dan gane wa ido da kuma tsoro daya fara shigar kowa na abinda yake tinkarosu sbd kaf a tarihi an sani duk garin da KUSRA( masu karfin safarar bayi da ikon siyar dasu qasashe qasashe na sarauta me karfin gaske) suka sakawa lamba to tabbas komai karfinsu to sai sun tashi garin sun tabbatarda duk wani me Sauran rai da numfashi a garin sun mallakesa sun tafi dashi sbd siyar da bayi ga manyan Masarautu.
Mutanen ANJOM tinda suka fara samun Alaman Kusra garinsu suke hari take kwanciyan hankali ya fara qauracewa a anjom duk da shugaban gari bai nuna hakan ba amma sunsan wannan masifaffiyar kaddara ce da baza su iya kaucewaba idan ba ikon Allah ba hakama a garin baa tafiya gudun hijira idan ba shugabansu ne ya bada damar yin hakan ba.
Abinda yake dan kwantar musu da hankali shine sanin baa iya shiga garin Kai tsaye sbd karfin nasu tsari da kafin da sukai duk da sunsan kusra nada karfin gaske suma amma kuma sanin su ne baa iya karya kafin saida jinin ahalin GHAZ dan haka tsananin karfin tsaron ahalin GHAZ ya tsananta baa Barinsu fita koina saida tsaron askarawa masu karfin gaske shi kuma Abaas kwata kwata ya Dena fita koina sbd ko wuqar jikinsa baa iya amfani da ita dan bama Kansa kariya.
****Gawar mutane sama da ashirin ne na mutanen ANJOM din da kusra suka kashe a Daren jiyan a wajen dajin Darin jere a qasa gaban ghaz Wanda yake sake kallan girman dajin yana tunanin yanda kusra suka samu damar isowa har gap da shigowa dajin garin Wanda sai an tsallako ruwa me karfi da yawan gaske duk da su kusra daman a ruwa suke rabin rayuwansu dan sunfi zuwa qasashe a jirginsu na ruwa me kamar gari dasuke tsallakawa da bayi Wanda yake dauke da dakunansu na bacci da komai na buqatan gudanar da rayuwansu dan bayinsu na kansu masu musu bauta da girke girke duk a ciki suke da nasa dakunan daban daban suna rayuwa hakama a inda suke zuba bayin da zasu siyar wa yana iya daukan sama da bayi daruruwa dan haka su babu Wanda ya taba sanin inda suke saidai idan Ka gansu kawai dan haka babu mai ikon daya taba kamasu sbd rashin sanin duniyoyin dasuke.
Basu taba sanin akwai gari a tsallaken ruwan dasuke bi su wuce ba saida tsautsayi yasa suka bi wasu bayi da zasu Kama ba suka gudu har cikin dogayen itatuwan da suka rufe dajin hanyar garin daga Bakin ruwa dan haka Mutum ashirin da suka bi bayin suna ganin sun ratsa itatuwan binsu sukai suka ratsa ciki Wanda suna shiga tin anan mamakinsu ya fara dan haka suka bazu a dajin suka bisu.
MAMUH
SLAVERY
BEST MALE CHARACTER
LION OF BOYEM
BEST LOVE STORY
ROYALTY
BRAVERY
HISTORICAL
LOVE/HATE STORY
HAYATEEM
Mamuhgee
2
Shugaban kusra subawa hanyar da sukabi idanuwa yayi sosai yana kalla yana Jin wani iri a jikinsa sbd duk inda aka samu hanya akabi to tabbas idan an kuwa ankai karshe komai nisa bazaa rasa inda zaaje ba a gurin.
Gudun cetan rai bayin sukeyi sosai suna Waiwaye sbd mashin da ake harbo musu masu tsananin kaifi da dafin da take zai karya duka garkuwan jikinsu matiqar ya tabasu ko kadan ne.
Basusan ina suke jefa kafafunsu ba bare inda suka dosa gudu kawai sukeyi na tashin hankali da tsananin tsoron da zuciya bazata iya dauka ba.
Nisa suke Qarama suna kusantar hanyar ANJOM wadda take cike da hadari batareda sun sani ba.
Cikin tsananin rashin Imani da babu ko Kadan a ran wainda suke biye dasu Wanda yake kaman shugaban Sauran ya bude baki yana tsaya wa daga gudun dayake ya Fiddo harshensa dayake da duhu sosai ya lashi fatar bakinsa dayake baqi qirin ya daga Kai sama yayi wani irin Ihu me karfi kafin ya sake dariya kaman me ciwon aljanu ya bude murya sosai yace
‘Dayan zuciyarsa nakeso a hannuna kafin ta Dena bugawa daga fitowa kirjinsa,
Dayan kuma idanuwansa nakeso zanyi wa dass sarka dasu a wuya’
Sauran na Jin hakan suka qara gudu suna sake Harba musu arrows masu tsananin tsini.
Na farko ganin ya kusa fita bishiyoyin zuwa filin dajin dayake hango hanyar da yasan zai iya samun gurin tsira da sauri ya sake tsananta gudu kafafunsa na fidda wani irin Jini na fashewan kafafunsa da tarin qayar da suke cike da tafi harma da saman kafarsa.
Na bayansa kasawa ya fara yi sbd zuciyarsa dake kasa dauka fara rage gudu yayi kafafunsa na jinin dayafi na gabansa hancinsa ma jini ne yake fita dan haka hannunsa ya daga ahankali ya Zare jakar fatar jikinsa Qarama ta kudin da suke tare dasu ya daga zai jefawa dan uwansa ya bude baki daqyar zai Ambaci sunansa wani irin jini me karfi ya feso ta kirjinsa,.
Cak ya tsaya hannuwansa na dawo wa qasa ahankali idanuwansa na yin jajir kaman zasu fidda hawayen jini sbd tsananin azabar dasuke bayyanarwa,
Ahankali ya saukar da Kansa zuwa kirjinsa ya kalli tsinin mashin daya shigo ta bayansa ya bullo ta kirjinsa.
Sarewa kafafunsa sukai cikin tsananin azabar da bata da Kama a lokacin.
Kafin ya qarasa kaiwa qasa wani mashin ya sake ratsa wuyansa ya bullo ta gaba take wani jinin me yawan gaske ya feso ta bakinsa da wuyan yake ya zube a gurin ba rai a jikinsa.
Suna isowa gurin Sauran basu tsaya ba tsananta gudu sukai dan cimma daya sbd a tarihin kusra basa rasa duk Wanda suke bi.
Mutum biyu ne suka tsaya Akansa ba wata wata suka fidda wata kakkaifar wuqar da ko ice zaa yanka da ita bazaiyi Kyan gani ba take suka fara huda kirjinsa dan cika umarnin shugabansu.
Jemo daya waiwayo yaga dan uwansa rayuwarsa ta riga ta fita take yaji zuciyarsa da jikinsa na sarewa wani irin Ihun kuka ya fasa yana cigaba da gudun da yasan ba tsira zaiyiba
Kuka yake yi sosai sbd dan uwansa jininsa dashi kadai yake dashi a duniya baisan yaya zai yi rayuwa babu dan uwansa
Juyowa ya sakeyi koina na jikinsa na wata irin rawa gudunsa na tsananta
Juyowansa da shigar mashi a goshinsa lokaci dayan hakan ta faru take ya tsaya cak yana zubewa gefe ahankali jini ya gangarowa zuwa idanuwansa take ransa shima ya fita a gurin.
Cikin rashin imanin fa basuda shi suka qaraso suna durqusawa gabansa Sauran kuma hanyar da suke hange suka zubawa ido wadda ganyen Shuke shuke suka rufe amma sunada tabbacin indai akwai shuke shuke a gurin to tabbas akwai mutane kokuma gari sbd shuke shuke ne da qaramin gari sosai bazai iya ba sai garin daya tara mutane da dama hakama kuma indai har akwai gari a cikin gurin to tabbas irin hakan suke so garin dayake a boye Wanda har zasu Kai hari su gama su tafi baa sani ba.
Mutum hudu ne a cikinsu suka tinkari hanyar zuwa shuke shuken da suke hankowa daga nesa sosai suna dake zubawa hanyar ido sosai daga nesa suna kasa yadda da akwai gari a cikin wannan Jejin me tsananin hadari.
Tafiya suke suna sake Sauri sbd wannan abune na farin cikinsu,
Cak suka ga na gabansu ya tsaya tareda kallan qasansa da sauri sakamakon abinda yaji sai kuwa ga maciji baqi qirin yana wani irin qyalli cikin rana.
Wuqar hannunsa ya saka ya fizgo macijin da ita ya rabasa biyu ya jefar suna cigaba da tafiya cikin zalamar son kaiwa inda suke son,
Taku goma suka qara dafin macijin ya fara aiki a jikinsa duk da ya yanka gurin daya cijesa da wuqa dafin ya biyo jini yana fita.
Wani irin zufa da zafi jikinsa ya fara dauka take bugun zuciyarsa ya fara sauyawa ya tsaya cak tareda durqusawa ya sake yanka fatar jikinsa da wuqa yana turo jini waje da hannunsa.
Daga bayansa wani macijin yaji ya kuma sararsa take ya juyo yana kokarin Kai masa hannu ya kashe wani ma ya sake sararsa take ya fara kokarin mine wa amma ba damar hakan sbd sankarewa da jijiyoyin jikinsa suka fara suna Dena aika jini koina.
Ganin hakan Sauran yan uwan nasa basu tsayaba suka cigaba da tafiya sedai ko ina basu kaiba dukkaninsu suka zube a gurin kowannesu kumfar tsananin dafi na fita jikinsu na dafin macizai.

0 Comments