Dingishin Kwado book 2
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ya bugo mini waya ya ji ya jikina ma bai yi ba, watakila ma ya mance da ni. Duk yadda ya kyamaci Amrah ta dawo ita kadai. Na lura tunda ya fada soyayya da yarinyar nan haka yake bata umarnin ta dawo da kanta.
A kullum sai na tuna Abida sama da sau ashirin. Don kuwa kullum sai na ci karo da abin da yake na gaskiya a cikin hasashen da ta dinga yi akan Sahal. Zamanmu na nisa matsaloli na sake girmama.
Ya mike yana fadin “bari na yi wanka gabadaya na gaji.”
Bai jira abin da zance ba ya shige dakinsa da saurinsa domin kaucewa kallon da nake masa mai kaifi.
Tsawon lokaci ina zaune ina ta sake saken zuciya. Duk da ban taba yi masa magana akan kudaden da yake fitarwa ba, wannan kam ba zan iya yin shiru ba.
Kwanaki kadan da suka shude ya cire sama da 150 kuma shima store ne suka cire, tabbacin shopping suka je ya yi mata, yau ma ya cire kusan hakan duk a cikin sati guda bayan wanda ya fitar da ya je siyo mana kayan amfanin gida, yauma ya sake cirewa ban da kananun da yake cira yana yin alheri da su ga ahalinsa da duk wanda ya so.
A sanyaye na nufi dakina na watsa ruwa dan na samu na sake wartsakewa.
Na shafa lotion (coconut na oriflame).
Wanda na farare ne irina Aisha lame ta zaba mini, sosai nake jin dadin amfani da shi mussaman yadda ya sanya na yi tas fatar ta yi mulmul. Na gasgata products din da lame take sayarwa na kuma gamsu an mata baiwar sanin dukkan rabe raben skins, tare da sanin naui’in man da zai dace da kowa. Don kallon ka kawai zata yi ta gane irin man da zai dace da fatarka.
Tuntube ta a wannan layin dan samun kalar naki man da zai gyara miki fatarki ko da ta fara yamushewa saboda tsufa ko rashin samun kulawar da ta dace.
Lame Nig….07036662633.
Rol on kawai na saka na zura rigar barcina cotton wacce cikin siyayyar da na yi ne a wajen Umm Asalah +201121544627
+2349162662750 kamshin turarena ya kamata.
Na sanya dogon hijab din gunis na fita.
Na leka dakin Amrah na tarar da ita tana kallo a wayarta. Na mika mata hannu, ba ja in ja ta miko mini domin doka ce karfe goma zata kawo mini wayar ba dan makarantar da take zuwa sun màtsa kowanne dalibi sai an siya masa waya ba da ba zan amince ta rike waya ba sai ta kammala sakandire domin hadarin da yake cikin wayar a wajen yara masu shekaru irin nata yafi alkhairinsa yawa. Kana tarbiya kana ta boye musu abubuwan da basu kai su gane ba ashe su kam kallon fanko suke mana domin da wayar hannunsu babu iyashegen da basa ga ni ko ji.
Na tsani na ga ta bude tiktok din nan tana ganin yaran mata suna sakin maganganun rashin da’a da kunya hadi da shigar banza tamkar dai basa tuna watarana zasu koma ga ubangiji ga kuma doguwar kwanciyar kabari da take gabansu.
Na leka Farha da take kwance a kan gadonta da shine na farko.
Barci take yi cike da nutsuwa. A duk sadda take barci ko ta yi murmushi sai na ga tamkar Abida ce. Duk da ba kammaninta a tare da ita.
Na kalli Amrah na ce “kin sa ta yi addu’ar barci?”
Tana daf da shigewa bayi ta ce “Ta yi Mahmah, sai da safe”.
Ta shige bayin ni kuma na ja musu kofar na nufi dakinsa.
A kishingide na iske shi da waya a hannunsa. Na isa na zauna a gefen da nake kwanciya.
Kafin na yi magana ya kashe wayar ya ajiye a kan durowar gefen gadon.
Ya juyo ya kalle ni. Ya ce “Ya jikin dai?”
Na amsa da ce wa “Na ji sauki Alhamdulillah!
Muka kalli juna abin mamaki sai ban ji wannan dinbin soyayyar ta taso mini mai tsanani ba. Amma kuma duk haushinsa da nake ji bai saka na ji na tsane shi ba illa iyaka soyayyarsa ta fara samun tawaya.
Ya janye idanuwansa dan kauce wa kallon da nake binsa da shi wanda ya kunshi al’amura masu nauyi.
Ya numfasa ya ce “Wannan kallon fa? Tunda na dawo kike ta tsare ni da idanuwa, ya ya haka ne, gabadaya a kwanakin nan bana gane yadda kike mu’amala da ni fa!
Na sake zuba masa ido kirr ban tanka ba.
Ya kufulo ya ce “Oh yau ai Basma ta zo gidan. Komai kika yi babu laifi, sai dai na fada miki duk abin da kuke nufi nima na shirya masa.”
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Na hadiye takaicinsa na ce “Ai na ga alamun hakan tun dazu”.
Na gyara zama na ce “Da na ga sako daga H.M.H. store sun cire kudi daga asusun ajiyarmu na zaci ma kayan dubiya ka siyo mini, na adana yunwata ina dakon ka sai kuma na ganka hannu na dukan cinya”.
Ya kadu kwarai da gaske da furucina. Ya ce Bilkisu ke nan. Dama an sha fada mini zan fuskanci haka, sai ga shi kuwa na fara ga ni. Ki fito ki ce kin gamsu da hudubar da take yawan fada miki na ce wa ki daina hada aljihunki da nawa saboda naki mai nauyi ne.”
Karon farko da ya fadi hakan ban ji gabana ya fadi ba, ban kuma ji fargabar bai fahimce ni daidai ba. Na yi gajeran murmushi tare da ce wa “Ba dan nawa yafi nauyi ba ne. Watakila tana jiye mini tsoron faɗawa yanayin nan na k’ato da shan bugu kura da cinye wa.”
Ya zuba mini ido sosai cikin son ya fahimci azancina.
Nima din na zuba masa dukkan nawa idanuwan cikin rashin tsoro ko zullumim kada ya yi fishi.
Ya ce “Kina nufin ina shanye romon wahalar ki ne Bilki?”
Jin ya fadi Bilki nasan yana cikin rashin sukuni.
Dan haka kaitsaye na ce “Kusan hakane domin kuwa kana yiwa wadanda basu cancanta ba hidima da wahalata. A tunanina baka da son zuciyar da zaka yi haka, sai dai da yake kai din dan Adam ne kuma jinsin namiji ba abin mamaki bane idan ka yi fiye da hakan.”
Ya fusata ya mik’e ya dauko walet dinsa ya fito da ATM dina ya jefo mini. Ya ce “,Ga shi nan matukar ina shakar numfashi ba zan sake taba abin da yake na ki ba ne. Mafi munin kuskurena shine yadda da na yi imanin zan yi yadda nake so da abinki kaitsaye domin na dauka mun riga mun zama abu guda. A sadda nake da dama ba abin da ban miki ba mai asalin tsada ba garabiti irin wanda kike yi mini ba.”
Na kada kai na ce “Tafi nono fari domin kuwa ban yi lalacewar da zaka yiwa budurwa hidima da abin da yake nawane ba alhalin ni tuni ka y’anta kanka da ga yi mini hidima kowacce iri tun shekaru masu nauyi da suka shud’e.”
Ya fusata ya ce “Tabdi jam! Wato halittar mace da gori take da kuma manta alheri take!
Cikin nutsuwa na ce “Namiji kuma da son kai da zalunci yake ba.! Na fada a matukar zafafe.
Ganin na fara fusata sai ya sassauta fishin ya ce “Dan na yi aure a yanzu ai na yi miki adalci. Shekaru sha biyar zuwa sha shida dan zan k’ara aure sai ya zama zalunci?”
Na hadiye na ce ba zalunci bane. Amma a sanin da na yi maka baka da lafiyar da zaka iya gamsar da mace biyu. D’ayar ma ya ya ne? Sannan aljihunka ma bai cudi bayanka ba.”
Nan da nan ya muzanta ya ce “A da duk hasashe kike yi da tsananta bin diddigi a kaina. A yau kuma ina mai tabbatar miki ina neman aure, wanda zai tabbata a kusa kusa”.
Na kafe shi da kallo mai tsananin gaske murya babu amo na ce”Sai yanzu ne ya kamata na sani Sahal?”
Kaitsaye ya ce “Tunda ban bari sai bayan na yi auren kika ji ba, ai kuwa na mutuntata ki”
Gabana ya fadi sosai murya na rawa na ce “Tsakanin ka da Allah kana da lafiya da halin kara aure?”
Ya murmusa ya ce “Ba ki da hurumin wannan tambayar. Domin ba matsalar da ta shafe ki bace “
Murya babu amo na ce To ba zan lamince na cigaba da zama a gidana alhalin ka samu sukunin bani muhalli ban sani ba”.
Ya girgiza kai ya yi kwafa. Can ya numfasa ya ce “Kamar d’azu na na yi ta jaddada miki cewar duk abin da kuke nufi da ni na shirya masa. Kin sani Abida ma ta hak’ura ta bar ni da dukkan nak’asun da take jigina mini, bare kuma yar karere irin Basma!
Na hassala na ce “A da ba Sahal, a lokacin ina sonka, ina ganin adalcinka”.
Ya rausayar da kai ya ce “Shike nan lokaci zai fayyace komai.”
Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa cikin nutsuwa.

0 Comments