Search
You have no alerts.

    OXYLITTLETHING **
    OXYLITTLETHING **
    OXYLITTLETHING **
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Shekaru dayawa sun ja dauke da abubuwa daban daban.

    Tsaye suke a gaban sasshen SS wali na Asibitin AKTH inda ya danganci kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki.

    Abba ne da mahaifiyarsa Hindatu, hannusa rike da ledar magunguna. Shi ne ya kawo ta kamar yadda ya saba, suka doshi wata jaramar mota kirar starlet. Fuskarsu kadaran kadahan suka shige suka fice daga asibitin.

    Abban ne ke cewa

    ” Ai mama, idan na samu na ajiyeki. Yanzu yanzun lodi zan yi na je Dutse na dawo kafin la’asar. Sai ki ga wasu ‘yan kwabbai sun shigo hannuna.”

    Wani irin kallo Hindatu ke masa tana son yin dariya tana kunshewa. Cikin mamaki ta ce tana mai nuna masa dan yatsa

    ” Anya Abba! Anya kuwa nan kurkusa akwai mai son jarabar neman kudi irinka? A kofar gida ka kafa tireda, kana kanikanci, kana koyarwa a islamiyya, yanzu juma ka tsiri lodi zuwa jigawa. Dazu dazu aka kira ka wai interview din da kuka yi ka ci, an dauke ku aiki. Wannan neman kudi da me yayi kama?”

    Wata irin dariya ya kwashe da ita har da buga sitiyari ya ce

    ” Ka ji mama! Na san babu wani abu da ya fi ba ki haushi irin tiredar nan. Mama kin raina tiredar nan. To jiya jiyan nan da aka siyo miki zabuwa kika sashe baki da kudin tireda ne!”

    Dariya take, ta kama baki ta ce

    ” tiredar?!

    Ya ce

    ” Ahaf mama! Ai ku ne kuka raina sanaa. Mutane sun fi so su jira aikin gwamnati to ina aikin gwamnati yake? Yanzu wannan tiredar da kudin bautar kasata na kafata. Da a ce mutane za su dauki hanyar rashin dogaro ga aikin gwamnati su kafa kan su da kansu ba tare da sun sa girman kai ba, to da an yaki talauci. Yanzu da kudin wannan tiredar sai ki ga an dallo miki suruka!”

    Ware hannayenta tayi guda biyu ta masa dakuwa ta na cewa

    ” uwaka! Ka ga marar kunya, ni kake wa maganar suruka. Ka mai da ni kakar ka ko”

    Suka kwashe da dariya

    Ran Hindatu wani farin ciki ne jin ya ambaci aure. Tana fatan ta ga auren Abbanta. Ko za ta kai?

    Ya ce

    ” Ba ga shi ba yanzu aikin ya samu daga Allah. Kafin ya samu fa ai da sai mu zauna mu nade hannu muyi maula? Allah ya ce tashi in taimake ka. Babu maraya sai rago mama!”

    Shiru tayi tana nutsar da maganganun Abba. Ya lura zata fada tunani ya ce

    ” Ehem..ehem”

    Ta ce” ya dai?”

    Ya fara shafa keyarsa yana cewa

    ” Yau ma fa na ga mutumin naki a kofar gida kafin mu taho. Allah Mama yana wahala”

    Take annurin fuskarta ya gushe, ta san maganar mahaifinsa yake. Mutumin da ba shi da wajen ziyara sai kofar gidansu idan ya bushi iska, duk wai don ta yafe masa.

    Ya lura da daurewar fuskarta ya ce

    “Mamah…”

    Ta dakatar da shi da sauri idanunta fal kwalla

    ” Abdulhakeem!….ka da ka ce Allah ya ce na yafewa mahaifinka! Dan Allah kar ka ce!”

    Ya ga yadda hankalinta yake neman tashi ya dafa kafadarta ya ce

    ” To shikenen. Ka da ki damu. Yafiya abun so ce amma ba tilas ba ce. Allah ya ce ayi koyi da hakan amma ba dole ba ne. Ita wata aba ce da kan zo daga zuciya. Idan har bata zo miki zuciya ba sai a hakura.”

    Motar tayi shiru, a lokacin ya zo wani shatalele. Ya kalle ta fuska a sake yace

    ” Ai kuwa kamar kin dan dade ba ki je kofar wambai ba, ya kamata ki dan yini acan yau ku sha hira. Alabashi idan na dawo daga dutse sai na biyo na dauke ki.”

    Bai jira amsarta ba ya karya kwana ya dau hanyar gidan kakarsa. Murmushi tayi. Abba ya dage sai ta shirya da yanuwanta. Haka ya tara su yayi musu nasiha akan zumunci. An samu abun ya dan daidaita.

    “Uhum Mama”

    Me ne kuma! ” ta fadi ta san abba ba zai bar zancen ubansa ba sai ya bibiyeta da waazi

    ” Mama kin ga ita duniya mafi yawanta jarabawa ce. Shin za ki iya tuna tarin laifukan da kike ganin kin yiwa Allah? Amma kika iya ki roke shi gafara? Shin ya kai tarin laifin da babana ya miki?

    Mama da a ce mu fa mutanen duniya mun san irin abunda za mu fuskanta ranar gobe kiyama da mun daina wahal da kanmu akan duniya ba.

    Shin kin san suratul “zalzalah” da Allah yayi wa laqabi da “girgizar kasa” wato ranar karshe. Allah ya ce a ranar kasa za ta fitar da duk wani abu da ke cikinta mai kyau da marar kyau saboda shi zai umarceta tayi hakan. A ranar mu halittu za mu tarwatse mu rikice muna rokon a nuna mana ayyukanmu. Sai Allah ya ce

    Faman yaAAamal mithqala tharratinkhayran yarah

    Duk wani wanda ya aikata wani abu mai kyau ( alkahairi) ko da kwayar zarra ne, to zai gan shi

    Waman yaAAmal mithqala tharratinsharran yarah

    Haka duk wani wanda ya aikata abu marar kyau (sharri) ko da kwayar zarra ne, to zai gan shi.

    Mama so nake ki wayi gari a ranar alkhairinki ya fi duk wani sharrinki yawa!”

    Kwalla ta cika mata ido amma murmushi take. A daidai lokacin sun iso lungun gidan. Ta goge idonta ta ce

    ” To na ji, na yafe”

    Dariya yayi ya ce

    ” To a ce ya zo kenen, a daura”

    Da sauri ta karo sako masa dakuwa ta ce

    ” Abba ka ci kaniyarka”!

    Dariya yake kyalkyata ma ta ya ce

    ” Au ba za ki yi auren ba kenen? Ko za ki aure shin?”

    Fita tayi daga motar cikin sauri ganin Abba na neman maidata kakarsa. Irin wannan wasanni ya fi jan ta da su don sanin tana cikin damuwa game da ciwonta.

    Bayan ta fita ne ta nuna masa danyatsanta alamun gargadi ta ce

    ” Banda gudu, ka ji na gaya maka.”

    ” Inshallah” ya fada.

    Yayi ribas alamun zai tafi. Ya leko ta window ya ce

    ” Mama zancen nan fa da gaske nake. Na surukar nan”

    Ta ce

    ” Ho dan nema! Allah ya nuna mana”!

    Yana dariya ya ce

    ” Amin!”

    Sai ta ji ranta fes! Tana mai son ganin wannan rana da za a kawo mata suruka.

    Motar ya ja yana daga maga hannu, ita ma tana daga masa.

    Ba ta bar wajen ba har ya kule. Ba ta gajiya da kallon gudan jininta mai tarin ilmi da hangen nesa.

    Ta san tana cikin kwanciyar hankali, amma ciwonta na bata tsoro. Shekaru na ja wasa wasa cin jikinta yake.

    Ta san ko ta mutu Abba zai mata addua. Abba ba zai daina roka mata rahama ba.

    Shin ko za ta ga auren Abbanta?

    Ta ce

    ” K’….Allah masani”

    *******************************
    Cape town

    Tsaye yake yana daura agogo a hannunsa na hagu wani abu da ya zame masa halayya. Hankalinsa ya rabu kashi biyu.

    Wasan kallon kafa yake kallo, saannan hankalinsa na matattakalar bene inda yake jiran Rokaiyatou.

    Zuciyarsa ta wani bangaren tana tunanin ko zai fara neman wata hanyar samun kudi ne? Ba wai dogara da aiki kawai ba. Ya fara shawarar kai ” spare parts” na motoci kasarmu ta najeriya.

    Hakan yana da nasaba da cewar kwanan nan ya ji asusun bankinsa yayi kasa saboda hidindimu.

    A halin da ake ciki ya biyawa mahaifiyarsa da Almustapha junior su kawo musu ziyara. Shirin da yake na zuwa tarbo su ne. Amma kuma ga shi Rokaiyatou ba ta sauko ba.

    Ya gama daura agogon, saannan ya kara kallon bene, lokacin ya ga tana saukowa.

    Shigar hausawa tayi na wata koriyar atamfa mai ratsin fari da aka yiwa dinkin siket da riga. Har ta karaso ta zauna bai dauke idonsa akanta ba.

    ” Frere yi hakuri kana ta jira na ko?”

    Almustapha ya dago ya kalleta ba tare da ya bata amsar tambayarta ba ya ce

    ” Kin sha maganin ki”?

    Har yanzu tana gwagwarmaya da cutar da ta shafi kwakwalwa. Har yanzu tana kan magunguna ne. Tana fuskantar matsaloli irin na masu lalurar, sai dai magungunan da take sha suna matukar taimakawa. Shi ya san ba lallai Rokaiyatou ta dawo daidai ba amma wanda aka samu ma an gode Allah.

    Murmushi tayi tana mai jinjina damuwarsa akan harkokinta ta ce

    ” Na sha”

    Ya ce

    “Abinci fa?”

    Ta ce

    ” Na ci”

    Hannunsa ya dauko guda biyu ya ritsa kugunta daidai tunbinta. Ta zame tana dariya ta ce

    ” lafiyarka kuwa?”

    Ya ce shi ma yana dariya

    ” so nake na auna ko kin ci din kin kara kiba”

    Bai bari ta amsa shi ba ya ce

    ” wato ke a dole bahaushiya ko? Kin dauki hausar kanawa karfi da yaji kin dorawa kan ki. Hausar Niger ma yanzu kin manta”

    Kama baki tayi ta ce

    ” Ni mmanta mi? Ya za ai mutum shi manta tushe nai! Ai niger ba ta gushemin cikin zucciya!”

    Dariya suka yi. Ya ce

    “Ah! Kwarai ke ‘yar gado ce. Ni ma Niger ita attushe na. Mutumin arziki ba shi manta tushe nai. Allah shi hobbaka Niger da Nijeriya gabaki daya”

    Tana murmushi ta ce “Amin”

    Ya ce da ita yana dube dube

    ” Ina Momodou ne?”

    Ta daga kai a hankali ta kalli benen kana ta ce

    ” Bacci yake…sai nace bari lokacin tafiya yayi sai na dauko shi”

    “Dauko shi” haka kawai yace da ita yana duba agogon hannunsa.

    Ta tashi a hankali ta hau benen ta dauko dan jinjirin a farin shawul. Ya karbe shi yana tsaye ya fara jijjiga shi ba don yana kuka ba. Yaron da bai fi wata uku ba ya bude idonsa tar uban ya ce

    ” wakie..wakue” ya juyo yana kallonta ya ce

    ” Allah yaron nan da ni yake kama”

    Ta ce ” wannan zance ai na haddace”

    Ya cigaba da kallonsa yana tuno irin adadin gwagwarmayar da aka sha kafin ya zo duniya.

    Samun yaron da sai da yayi sanadiyyar da aka cirewa uwarsa mahaifa. Ta sha magunguna na hana daukan ciki har suka yi mata lahani. Allah ne kawai ya kadarta yaron zai zo duniya. Kallo daya yayi masa ranar farko ya san ya dace da sunansa.

    ” Momodou”

    Kaunar yaron na shiga ransa yana kara godewa Allah.

    Ya mayar da shi dan wani gado a falon.

    Ya dauko wani zane yana nuna ma ta. Ya ce an kawo fa

    Cikin tsananin doki ta karba. Zanen Momma ne. Wani tsohon hoton ta ne ya bayar aka yi zane da shi.

    Tana ta kallon hoton kwalla ta cika mata ido. A shekaru da dama tayi kewar momma. Momma ta tafi a lokacin da ya kamata ta ji dadi. Shin ko za ta yafe mata? Ta kan ji wannan nauyin na damun kirjinta , kamar ta ci amanarta.

    Ya karbi hoton ya sakala a wani bangon falon. Ya dawo yana cewa

    ” Mu anan gidan ba a kuka…huh..mutum daya aka yarjewa yayi kuka. His royal highness Momodou!”

    Dariya take yi sosai ta ce

    ” wannan dole ne ai! Kuka har da na gyara akwai shi. Ai kai ya biyo, kana yaro kai ma an ce ba dama!”

    Ya zaro ido da mamaki ya ce

    ” waye ? Ni? Ni da ina jinjiri aka ce min damo sarkin hakuri. Ai sai na kwana na yini ba a ji kuka na ba” ya kashe idonsa guda daya

    Ta ce

    ” Au haba? To tunda mummy yanzu zata iso sai a tambayeta labarin damon nan….”

    Ya nuna mata danyatsa da sauri yana cewa

    ” ke..! Ke! Wallahi ki kiyayeni”

    Dariya suke. Ya maida idonsa kan hoton momma ya ce

    ” iyayenmu, da yanuwanmu da suka riga mu gidan gaskiya Allah ya jikansu ya musu rahama ya yafe musu”

    A sanyaye ta ce ” Amin”

    Wannan karin agogon bango ya kalla ya ce

    ” Ina ga lokaci yayi, ya kamata mu tafi. Kar suyi ta jira. Da fatan kin tanadi cakulet din da aka ce miki na mutuminki”

    Ta kama baki ta ce

    ” Ni na isa na manta? Abinda aka fi sati biyu ana jaddamin”

    Ya ce ” Ah lallai kam” yana dauko jinjirin daga kwandon da aka kwantar da shi. Ya cigaba da cewa

    ” Ai kin gama siye yaron nan da abun duniya, baya ji da kowa sai ke”

    Ta ce

    ” Frere kamar kana kishi”!

    Ya ce

    ” Nahh..ni.ma ni da danuwana za muyi building team guda agaisnt you two!”

    Sai kuma ta ga ya dan canja fuska ya ce

    ” Idan suka gama hutunsu tare zamu koma gida Najeriya. Da ni da ke za mu je gidan Baban Ali. Bai kamata a yada shi ba”

    Tayi shiru kamar wutar nepa ta dauke. Tana tuno irin balain da ta shiga a wannan gida, da irin silar da ya janyo ma ta. Ya kamo hannunta ya ce

    ” You have to be strong, duniya ba ta ragwage ba ce”

    Ta gyada masa kai, sai kuma hawaye ya cigaba da zuba daga idonta. Babu wani abu da zata iya ce masa ya riga ya gama ma ta komai.

    Dama ta hadu da shi da wuri, dama abubuwan da suka faru ba su faru ba. Ta tuno labarin da ya zo musu na mutuwar Luba, sai jikinta ya kara yin sanyi. Ya ce

    “Yaya dai?..huh?

    Ta ce a sanyaye

    ” Kana ga zan warke watarana? Kana ga zan zamo mai hankali kamar kowa ba tare da na sha magani ba?”

    “Ina ga za ki rayu ki fi haka wataran Rokaiyatou!”

    Ina ga wataran komai zai zamo labari,

    Ina ga wataran za ki zama malama ki bawa wadansu labarin rayuwarki,

    Ina so wataran ya zamana wata ta shiryu ta dalilinki,

    Watarana labarinmu zai zame wa wasu izina!

    Kuka take ta rukunkume shi ta ce

    ” Ni baza…n zam….o ni ba idan ba..bu kai, shin baka gane haka…n ba!”

    Bubbuga bayanta yayi ya ce

    “Shhhiit!..shin ban gaya miki mutum daya aka yarjewa a gidan nan yayi kuka ba? Ran shi ya dade…”

    Ta zame tana dariya ta ce “ohhhhh!”

    Ta sa hannu ta dauki jakarta, Ya dauki dan mukullin mota. Tana dariya ta bi shi a baya.

    Tsaye suke a harabar airport din , wajen karbar wadanda suka iso. Can suka hango Mummy da Almustapha junior. Da gudu ya saki hannun kakarsa ya taho gun Rokaiyatou yana cewa

    ” Mammah”!

    Ta rungume shi tana cewa

    ” Mon garcon..!”

    Almustapha ne ya janye shi yana cewa

    ” Kai, sakar min matata”

    Dariya suka ta mishi

    Mummy ta ce

    ” Allah ya shirye ka”

    Suka gaggaisa cikin annashuwa da farin ciki ana ta hayaniyar yaushe rabo. Mummy tana dungure kan momodou wai bai biyo dan ta mai sunansa a kyau ba.

    Mummy ta karbi babyn suka fara fita daga harabar gurin. Almustapha yace suyi gaba ta ba shi passport din su a dauki kayansu. Rokaiyatou zata bi su ya fincikota

    ” ke malama waye dan dakon ki?”

    Dariya tayi, hakan ta kan yi don bata fiye yawon magana ba.

    Shirgin kaya mummy ta jibgo, ya san bai wuce ta yo musu kayan abincin Najeriya ba.

    Kafin ya ankara ta tsinci yan kananan kayan ta dora a keken tura wa tayi gaba. Sai a lokacin ya lura manyan jakankunan ne a gabansa.

    Ya dago da sauri ya ga tayi gaba tana dariya. Ya kwala mata kira yana ma ta alamu da hannu na kama kunne da shauda bulala.

    Sai ma ta tabe baki alamar oho masa

    Dariya suke a yana cewa ” zan kama ki ne”

    Ya loda kayan yana murmushi ya ce

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!