Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Harabar kotun a cike take makil! Babu wanda bai halarci wannan sharia ba mai daukan hankali.

    A gefe daya Luba ce zaune da yar modu tana karkade kafa. Daga gefe can hindatu ce a cikin matsanancin tashin hankali. Abubuwan da suka faru ba abubuwa ne masu dadi ba, ganin Rukky a cikin halin da take ciki ya sa jikinta yayi mugun sanyi. Tsoro take ita ma kar karshenta ya kare a haka. Sai sharar hawaye take.

    Bata da wata masaniya akan shirin Luba ko wata manakisa na ta. Ita dai kawai tana tausayawa Rukky.

    Almutapha na wani gefe daban shi da mahaifiyarsa. Ta ji labarin komai a bakinsa sai a lokacin take Allah wadai da irin rayuwar da ta bar dan ta yana yi saboda son duniya. To amma yanzu wa gari ya waya?

    Lokacin da aka fito da Rukky a cikin sarka sai da wata kwalla ta tarar masa, yayi sauri ya dauke kai. Gabadaya komai na duniya ya sire masa a zuciya.

    Rukky kallon kowa take daidai. Yanzu ga shi an hallara duk akan dalilinta. Ga shi an tara mutane ana zarginta da kisan kai. Shin ashe haka duniya take bata da tabbas? Ashe abubuwan cikin duniya yaudararrun abubuwa ne? Ashe ma jin dadin duniya kalilan ne,?

    Ta yarda duk wanda ya bar Allah to ya bar komai. Yanzu ga inda rayuwa ta kai ta, ga shi ta baro ta. Lallai ba ta da makiyi a duniya irin zuciya!

    Lauyoyi suka gabatar da kan su. Lauyanta kamal dauda yayi ma ta tambayoyi shigen irin wanda yayi mata a police station ta kuma ba shi amsa daidai da yanda aka yi. Ya ce

    ” Ina fatan mai sharia zai duba cewar yanayin da abubuwan suka faru a tsare ya nuna akwai sa hannu a ciki. Daga lokacin da aka dauki faifan video na fadan rukky da rebecca ya nuna cewar akwai wani shiri da ake yi akan hakan. Ana so a lakaya mata wannan kazafin ne don wata manufa.

    Ga waya waya da take nuna irin tasa tasan da aka aiko ma ta da sunan Almustapha. Har wanda aka ce ta zo gidansa da misalin wannan lokaci na kisan”

    Ya mika wayar a matsayin shaida

    Alkali ya ce

    ” Kana da shaidu da ka ke bukatar gabatarwa da kotu?”

    Ya ce

    ” Ina da su My lord”
    Ya ce

    ” To ka gabatar da su”

    Almustapha ya fara kira. Ya kuma tambaye sa tsakaninsa da wacce ake kara ya fada ba wani boye boye. Abinda ya kawo cece ku ce a kotun kenen. Ya tambaye shi game da batun tura sakonni ya ce shi ba shi ba ne. Ya kara da cewa rabonsa da yayi wani contact da Rukky tun kafin aurensu da Rebecca.

    Daga wannan aka kira maigadin gidan Almustapha. Ya tambaye shi abunda ya faru a ranar ya labarta shigar Rukky gidan da fitarta. Ya tamabaya

    ” shin ko ka ga alamu da ke nuna ta fita da wani abu daga gidan”

    Ya ce

    ” Ni dai ban gani ba”

    Ya sake tambaya

    ” Ka ga lokacin da take komawa mota ko ta saka wani abu “

    Ya ce

    ” Gaskiya ni ban gani ba..ita kadai na ga ta shigo kuma ita kadai ta fita sai dai abinda ke boye , wannan kuma Allah shi ne masani”

    Barrister ya ce

    ” to kana ganin kamar dai wani ya taba motar kafin ta fito ba tare da ta sani ba..”

    “Objection my Lord” cewar lauyan Gwamnati. Bartister yana leading witness din. Yana saka maganganu a bakinsa”

    “Objection Sustained. Ka kiyaye” cewar Alkali.

    Daga nan aka kira kuku. Shi ma ya fadi abinda ya wakana. Barrister ya ce

    ” ka ga fitar ta lokacin da bata samu oganta ba?”

    Ya ce

    ” kwarai na gani”

    “Shin ka ga wani makami a tare da ita? “

    Ya ce

    ” A’a”

    Daga nan ya kare tambayoyi ya dubi Alkali ya ce

    ” Ina so mai sharia ya gane wacce aka kara Rukky ta taka sawun barawo ne kawai. Amma ganin yanayinta da karfin ta na diya mace ba zai iya yiwuwa har ta kashe mutum ta dauki gawarsa ta saka a boot din mota ba. Ya kamata kotu mai adalci ta zurfafa bincike ta gano gaskiyar lamarin. Nagode”

    Ya koma ya zauna. Barrista yunus ya fito ya fara yiwa Rukky tambayoyi kamar haka

    ” Malama Rukky mecece sanaarki? Kuma wata alaqa ke tsakaninki da Almustapha?”

    Ta yi jim kadan can ta ce

    ” Karuwa ce ni! Kuma muna dadiro da shi”

    Wata irin hayaniya ta cika kotu. Baka jin komai sai tsine tsine. Ya ce

    ” ba ki da wace sanaa da ta wuce wannan”?

    Ta ce ba ta da ita

    Ya ce

    ” Irinku ne ku ke raba mutum da iyalansa? Dalilin kenen da ki ka yanke hukuncin kashe Rebecca”

    ” objection my lord. Ba muna sharia a yau ba ne akan tuhumar da ake wa wacce ake zargi da laifin karuwanci. Akan wani abu ne daban.Barrister yana kokarin laqabawa wacce ake tuhuma kisan kai ba bayan ba a tabbatar ba zargi kawai ake” cewa Barrister Kamal.

    “Objection sustained. Korafi ya karbu. Ya kamata barrister Yunus ya kiyaye”

    Ya gyada kai

    Ya ce

    ” Faifan video din da ke yawo na ke da Rebecca kuna fada. Ya nuna inda kika yi ikirarin kashe ta. Shin wannan wani shiri ne kika dauka akanta?”

    “Objection my lord”! Ya kamata Barrister ya daidaita tambayarsa” cewar Barrister kamal dauda

    Alkali ya masa gargadi.

    Ya cigaba da yi mata tsauraran tambayoyi. Daga nan aka kira mai gadi. Ya ce

    ” Shin ko ka lura da yanayin ita Rukky lokacin da ta zo ficewa daga gidan?”

    Ya ce

    ” eh to, gaskiya na dan lura kamar akwai bacin rai a fuskarta don ina kokarin yi mata sallama ta figi mota ta fice”

    Ya ce

    ” To kana ganin akwai wani yanayi da ke nuna sauri a tare da ita?”

    Kafin ya amsa Barrister kamal ya ce

    ” objection my lord, yana leading witness”

    ” objection overrulled. Korafi bai karbu ba. Barrister yunus yana kan sharafinsa ne”

    Ya kira kuku ya cigaba da yi masa tambayoyi. Ya ce

    ” Da ta leko wajenka me ta tambayeka?”

    Ya gaya masa. Ya kara da cewar

    ” sai ta ce min ina madam..na ce tana side din ta”

    Barrister Yunus ya dubi Alkali ya ce

    ” Hakan yana nuna cewar tana da wani shiri akanta tun da ga shi ta tambayeta don ta san inda ta ke”

    Daga baya ya kira shaidu 3 abokanan Almustapha ne da suka halarci cin abincin nan. Suka bada shaidar fadan da kuma gaskiyar magana cewar Rukky tayi ikirarin zata kashe Rebecca.

    Ya dubi Alkali ya ce

    ” Daga jin wadannan bayanai za a gane cewar Rukky da shirinta ta zo gidan Almustapha. Domin kuwa akwai jin haushin Rebecca a zuciyarta na ta raba ta da masoyinta. Duba da yanayi da cewar bincike ya nuna ko lokacin da aka kamata da gawar tana dauke ne da kayan maye da ke nuna ba cikin hayyacinta yake ba. Hakan ya na nuna za ta iya aikata kisan.”

    “Objection my lord. Ya kamata barrister ya gane har yanzu zargi ake wa wacce ake tuhuma. Maganganunsa hasashe ne kawai.” Cewar barrister Kamal.

    Korafi ya karbu. Barrister Yunus kotu na yi maka gargadi.

    Da haka aka tashi daga kotu bayan an daga kara zuwa 10 ga watan gobe. Alkali ya yanke hukunci da cewar a mayar da wacce ake tuhuma gidan yari na kofar mata a dauketa daga police station na hotoro.

    *****************************

    An yi zaman kotu kamar sau uku kafin ayi wannan zaman. A tsawon lokacin nan ya zamana ko masallaci a bi jam’i Almustapha bai isa ya shiga ba ba tare da an zunde shi ba.

    Yawan yawan mutane hankalinsu ya fi raja’a akan Almustapha da Rukky su ke da alhakin kashe Rebecca. Da ba su ga yanda za ayi mutum ya bada shaida don taimakawa wacce ta kashe matarsa ba.

    Sun fi gane cewar da sa hannunsa dumu dumu. Sai dai duniya yanzu da mai hannu da shuni ake yi, ya cika jamian tsaro da kuma alkali da kudi domin a wanke sa. Don haka ba su da wani abun da suke masa sai tofin Allah tsine.

    A yau ma kowa ya hallara a kotu. A wannan lokaci Barrister kamal ya sare domin babu wasu kwararen hujjoji a kasa. Wacce su a rans u suke zargi luba ce, kuma babu wata dama da za su nuna hakan. Domin kuwa bata bar wata shaida ba da za a iya amfani da ita a ramfota.

    Yar modu da yake tunanin da hannunsa idan ya dora shi akan stand kwabarsa zai sa tayi ruwa. Da farko ba zai fadi gaskiya ba. Illa ma ya bi ‘yan shaidar fadan da ya wakana. Kan sa ya kulle qam haka na Almustapha. Don shi numfashi ma da kyar yake fitarwa. Ya rame ya lalace sabida tsananin tashin hankali.

    Wanan karin da fari yansanda aka kira, aka musu tambayoyi suka bada bayanin abunda ya faru. Barriater yunus ya ce

    ” Ka na nufin ga bude jakarta ta miko kudi a matsayin cin hanci?”

    Ya ce hakane

    Ya dubi alkali ya ce

    ” Shin wannan bai ishemu shaida ba, cewar akwai abunda take boyewa?”

    Objection my lord. Ba ana zarginta ba ne akan bada rashawa da cin hanci” cewar barrister kamal

    “Objection overulled!Korafi bai karbu ba. Ka kiyaye barrister kamal” cewar Alkali.

    Yansanda suka bada shaidar cewa akwai shaidar yan yatsun hannun Ruky akan wukar da aka yi kisan.

    Sa’annan Rukky ba ta da Alibi wato wajen da take a lokacin da kisan ya auku. Wajen da take bai wuce cikin gidan da kisan ya auku ba!

    Barrister Kamal shi ma ya tashi ya bada hujjojinsa da cewar. Wukar da aka yi kisan da ita akwai shatin yan yatsu na wani da ba a sani ba. Dole kenen akwai wata manakisa.

    Da wannan kowa ya samu waje ya zauna alkali zai yanke hukunci. Ya yanke hukunci kamar haka

    ” Duba da irin hujjojin da aka gabatar a kotu, kotu ta kama wacce ake tuhuma mai suna Rukky da laifin kisan Rebecca! Kotu ta yanke ma ta hukuncin daurin rai da rai a gidan yari! Wanda hakan yayi daidai na sashe na 3** na pinal code. Wacce ake zargi tana da damar daukaka kara zuwa nan da 27 na watan gobe. Kooot!”

    Wani kara Rukky ta saka mai gigita hankalin mai saurare. Numfashin almustpha yake neman daukewa saboda tsananin rudani har sai da ya dafa bangon kotun. Cewa yake

    ” innalillahi wa inna ilairrajiun.. Allah idan saba maka da muka yi wannan ne hukuncinmu ya Allah mun tuba. Ya Allah ka yafe mana. Ko a yanzu mun gane kai madaukaki ne mai buwaye ne, ba daidai ka ke da mutum danadam ba. Ka fi karfin kowa kai mai iko ne akan kowa! Astagfirulla ya Allah! Astagfirulla!

    Ya dago kai yana kallon Rukky ana janta za a tafi da ita wani irin kuka ta ke. Ta kwalla kara

    ” Almustapha!! Ka taimake ni!”

    Kawai sai ya ji hawaye ya subuce masa. A hankali ya ce

    ” Allah ne zai cece mu! Zan kuma taimake ki da karfin kwanjina! Zan taimake ki da kwandalar da zata kare a aljihu na”!

    Ficewa yayi daga cikin kotun zuwa harabar waje. Yana cewa

    ” Zan daukaka kara daga nan har sai na ga abunda ya turewa buzu nadi! Wasu abubuwan na duniya ba sa zuwa da sanyi. Wasu abubuwan sai an dage kafin a cimma buri!”

    Cin karo yayi da Luba da ‘yar Modu a tsaye suna kwasar dariya. Ta dubi shi ta ce

    ” Shin a tunaninka ka dauka shata layin gaba da Luba abun wasa ne? To bari na gaya maka, tamkar ka daga hannu ka zagi uwarka ne! Za ka daidai?

    Na so ka fiye da yanda na taba son duk wani namiji na duniya amma ka juyo ka watsamin kasa a ido. To abun son naka na salwantar! Kai kuma na bata maka suna, dukiya ba dai ka ji ana lissafinka a masu mallakinta ba.Sai naga yadda za kayi.!Wanna shi ne daidai hukuncin da ya dace da maciya amana!

    A tunaninka zan kale ku? To mu muka shirya komai! Wanda na sa ya kai Rebecca barzahu ko ka neme shi ba zaka same shi ba! Shin ko ka san ya fi kwana 3 da kai a cikin gidanka yana kwana da matarka Rebecca baka sani ba? Hahahahha

    Kwarton matarka shi na saya na kuma saka ya sheka ta barzahu! Shin ka dauka kana da masoya Almustapha? Su waye su?”

    Daga bayanta sadiq ya bullo yana kallon Almustapha yana murmushi. Ita ma dariya take ta ce

    ” Awww…kan ka ya daure ko? To ina muka san sirrikanka idan ba ta hanyar makusantanka ba? Bar zargin yan adawa Almustapha, mutanen jamiyyarka ashe makiyanka ne ai da su na hade baki aka watsaka a duniya akai maka daidai! Da su aka taimaka wajen kai rahoton cacarka dan a tarwatsa ka a hannun investors din ka! Kai da Rukky Almustapha sai dai ku hadu a jahannama! Don ita ce makomarku!!”

    Rintse ido yayi ya bude wani irin tiriri ke fitowa daga bakinsa. Kallonsu yake, musaman sadik ya zai ci amanarsa irin haka? Me duniya ta zama ne wai?

    Amma yayi wa kan sa alkawari daga yanzu ya zama jajirtacce. Zai iya fada da kowa kuma ya ci shi da yaki. Ya kalle ta a tsaurare ya ce

    ” Ki jiraye ni! Ki jira ranar da zan waiwayeki ko da kuwa shekara dari biyu ne masu zuwa!. In dai ina raye sai kin gane ba a taka ni a wuce. Ki cigaba da harkokinki amman a kasan ran ki ki raya cewa wani kasurgumin makiyinki yana take miki baya.

    Lokacin da zan bayyana gabanki, Allah ya sa kin gama cika burirrikanki domin kamar mutuwar bazata haka zan datse miki cikar buri!! Zamu hadu a ranar da ba zamu sake haduwa ba!!!!!

    Ya bar su a gurin ya hau motarsa ya figa a guje zuciyarsa na tafarfasa. Ya rasa ina za shi. Wata zuciyar ta ce masa ya kamata ya gano wacece yarinyar nan Rukky. Ko dan ya waiwayi iyayenta su san halin da diyarsu ke ciki. Kawai sai ya dauke kan motarsa ya wuce gidanta.

    Budewa kawai yayi ya shiga yana da fan mukulli. Gidan yana nan yadda ta bar shi. Dakin kwananta ha shiga ya fara hargitsa komai.

    Suk iya bincikensa bai ga komai ba. Ya bude drawer ya fara wurgo kayanta . Ya duba koina da koina. Har zai rufe ya hango wata karamar akwati ya janyo ta.

    Tarkace ne a ciki, wasu abubuwan kamar sun dade. A fara binciko su bai gane komai ba.

    Har zai rufe acan kasa ya ga wata envelop sai ya zazzage ta. ID card ne a ciki sai wasu takardu kamar na makaranta haka. Sai hoton wata mata da shekarunta ya ja haka.

    Da ya kura mata ido sai ya ga kamar ya san ta, kamar kuma ya san hoton sai ya mayar kawai. ID card din ne da takardun makaranta suka dan dauki hankalinsa. Suna ne iri daya a jiki baro baro

    ROKAIYATOU AHMADOU TILLABERI

    E.S.A L’ ECOLE SEKANDARE DE NIAMEY

    Rubutun sunan iri daya ne da na jikin sakamakon jarabawar. Sai ya rufe zai mayar. Sai kuma yayi sauri ya bude yana kurawa id card din ido yana kara karantawa cikin rudani.

    ROKAIYATOU AHMADOU TILLABERI

    Gabansa ya ji ya bada dam!!!

    Cikin azama yayi sauri ya zaro hoton nan sai a lokacin ya gane wacece. Hoton mahaifiyar Rokaiyatou ne sak irin wanda ya sata a dakin mummyn sa lokacin cigiyar nan!

    Saboda tsabar tashin hankali wani amai ne ya taso masa, kawai sai ya ru ga bandaki ya dunga kwara amai ba da wasa ba.

    Da kyar ya fito ya fadi akan kafet na dakin yana birgima!! Birgima yake yana malelekuwa cewa ya ke

    ” wayyo Allah na..wayyo Allah. Allah na tuba ka yafe ni! Allah na tuba bazan kara ba! Da kanwata nake zina!! Rokaiyatou! Matar danuwana! Innalillahi! Innalillahi”

    Kuka yake, kuka kashirban na ban mamaki. A rayuwarsa bai taba kuka irin haka ba. Jikinsa karkarwa yake zazxabi ya rufe shi. Da kyar ya dauki I d card din da takardun ya tafi mota ya ja ta a guje.

    Wani abokinsa mai aiki a prison din kofar mata ya kira. Ya ce ya masa hanya zai ga wata yanzu yanzu aka kawo ta. Ya taimake shi ko nawa ne zai iya biyansa. Ya ce ya karaso.

    Haka ya karasa, ba a jima ba aka sada shi da inda zai gan ta.

    Ta fito sanye da shudin yinifom idonta luhu luhu bata ko gani sosai. Jiki na karkarwa ya watsa takardun nan akan tebur ya ce

    ” Ki yi wa ubangijin da ya halicce ki ki gaya min ko ke wacece. Ke ce mamallakiyar wannan takardun? Shin kece mai wannnan sunan?”

    A hankali ta gyada masa kai. Bai yi wata wata ba bai san lokacin da ya sharara mata mari ba saboda tsananin tashin hakali.

    Ta rike kuncinta cikin mamaki take kallonsa. Kuka ta ga yana yi kashirban. Ya ce

    “Me yasa tun da wuri ba ki gaya min wacece ke ba? Me yasa kika boye? Kin ga abunda hakan ya janyo ko?

    Kin san wanene ni? Ni ne Almustapha! Almustapha danuwanki jininki! Ni ne danuwan momodou masoyinki! Ni na dan babban makiyinki! Ni ne masoyin da ba ki da tamkarsa a yau duk duniya! Da ni da ke muka yi zaman haram! Zaman haram din da ya kai ki gidan yari!Ni ne Almustapha”

    Durkushewa tayi a gurin. Kuka take amma ba ya fitowa. Yanzu ta gane me ke faruwa. Yanzu ta gane dalilin da take jin Almustapha a ran ta. Ashe jininta ne? Shi ya sa kaunar tayi yawa?

    Ina ma ina ma..ina ma. Ina ma ana dawo da hannun agogo baya. Yau ta tsinewa karuwanci! Yau tayi Allah wadai da rayuwar bariki. Allah ta tuba, a yau tana cikin da na sani marar amfani.

    Kawai bai san lokacin da ya daga ta ya rungume ba. Dukkansu kuka suke

    ” Tsakanina da ke ashe ‘yanuwantaka ne? Tsakanina da ke ashe kauna ce? Kauna irin ta jini! Ya za ki yi min haka Rokaiyatou? Yaya za ki yi min haka? Ki zo a sa’ilin da lokaci ya kure?

    Ashe zina da na sani ce? Ashe haka ciwon yake idan kayi da diyar wani? Ina ma ban yi ba! Ina ma na tuba kafin na hadu da ke!

    Ina ma ..ina ma ina ma.akwai rabo, da an rubuta ke tawa ce! Da mun gyara kura kuren mu. Ina ma bamu tarwatsa rayuwarmu ba! Ina ma bamu sabi Allah ba. Zai karbi tubanmu kuwa? Kamar lokaci ya kure.”

    A hankali ya fara ja da baya. Ya san dole ya tafi.

    Tsakanina da ke dangantaka ce…

    Tsakanina da ke soyayya ce…

    Da sannu da sannu yanzu tafiyar ta sauya

    Tafiyar tana da tsauri

    Yaushe zamu cimma buri?

    #maitafiya
    #donutfairy

    What can you say about this novel? What can you say about the writer? Rate the novel!

    20. Uwa da da

    Shin ko ka san irin son da ke tsakanin uwa da d’a? Shin da gaske za ka iya komai saboda wannan abu da ake kira d’a?

    Bayan shekara goma

    Ajiya..ina bekin cikin senar miki, kina doke da cutan kanjamau! But ya kamata ki gane cuta wannan ba mutuwa ba ne, mutane dayawa dayawa suna doke da ita but suna shan megani, ba a seni ba. so, if kana shan magani ake ake..babu damuwa..babu mesala..

    Zaune take akan kujera ta zuba ido tana kallon bayeraben likitan yana idar mata da sako a cikin gurbatacciyar hausar sa. Wani irin abu ne ta ji yana mamaye mata zuciya na tsananin fargaba da bakin ciki.

    Mace ce da ta haura shekara arbain. Baka ce mai jiki, wanda yake nuna alamun jindadi a tare da ita. Tana sanye da wani farin leshi qal mai manyan huda huda da aka yiwa ado da ja. ‘Yanyatsunta akwai zabban zinare guda biyu, fuskarta babu kwalliya sai dai kayan jikinta sun bayyana tsadarsu ta nuna cewa ita mai arziki ce.

    Dankwali ta daura akanta amma bata yafa mayafi ba, rabi rabin jikinta a waje ya ke. Komai kuma na jikinta abun shaawa ne, abun kallo ne. Tayi kama da wacce zata halarci wannan babban taro, to amma ga ta a gaban likita yana labarta mata mummunan labari.

    Hindu ta hadiye yawu maqwat, zufa na tsatssafo ma ta ce

    “Ban gane bayaninka ba likita. Ni din ce naje dauke da kanjamau? Anya kuwa ka duba da kyau? Ni fa idan banda dan zazzabi zazzabi babu abunda nake ji. Sakamakona ne kuwa?”

    Ya gane a rude take. Ya kara kallon takardar ya karanta sunan jiki ya kuma tabbatar mata da cewar ita ce. Ya ce

    ” Ajiya, wannen fa ba abu tashin henkali ba ne. Me cutan nan ba shi da bebenci da kowa. Yenzu megani yayi yawa wanda za kana sha..cikenen! Dats ol. Kuma megani is free! Kawai za kana zuwa asibiti ake ake kana karba. Za muyi guiding na ka.”

    Ta cigaba da zuba masa ido kirjinta na lugude. Rayuwarta ce ta bayyana a idanuwanta. Kokari take ta danne firgicinta da bakin cikin da take ji amma ta kasa. Kawai sai ta fashe da kuka, wani irin kuka mai cin rai.

    Tun likitan yana ba ta hakuri har ya gaji ya daina. Ta fito daga ofishinsa ta wuce wata bakar hadaddiyar motarta kirar camry. Motar da idan ta kalle ta ko wanke ta ake sai taji wani nishadi ya lullube ta.

    Sai take jin kan ta cewar ta kai inda ta kai, ta isa domin kuwa motar lokacin da aka siye ta ba ta fi wata shida da fitowa ba. Alhaji Awaisu ya siyo mata, ya dalle ta da ita a matsayin kyautar ban girma a lokacin da akai wani shagali na cikarta shekara 40 cif a duniya.

    Amma me sai taji bakin motar a rine a idanunta, sai taji bata son ko ganinta. Ba ta ma son wani ya mata maganar Alhaji Awaisu ballantana dalleliyar motar da ta dangance shi.

    Babu makawa Alhaji shi ya sanya ma ta kanjamau! Dama yana da ita bai gaya mata ba? Ita a iya saninta a ‘yan shekarun nan shi kadai take kulawa domin da shi suka kulla dadiro.

    Sama da shekara goma kenen Alhaji Awaisu na ma ta alkawarin aure, yau gobe , jibi ,gata amma shiru. Ta raba shi da matarsa da ‘ya’yansa duk don wai ta samu da shiga ta bararraje da nata ‘ya’yen amma batun aure shiru maqatau bulaguran lahira.

    Sai alkawurra na iska. Yau ya kai ta dubai, gobe tana ingila ta zame masa jaka duk inda za shi da ita zai je. Ya bude mata bakin aljihu wanda bata taba sanin ana budewa mace ba take wawasa iya wawasa.

    Shagunanta biyu na sayarda lesissika da kayan kitchen akan titin zoo road, business take yi ba na wasa ba. Alhaji Awaisu ne kuma ya tsaya tsayin daka.Duk da a boye dai ta kan dan kula manemanta amma jikinta ya fi ba ta cewar Alhaji Awaisun ne ya shafa mata wannan qajagar.

    Ta bude motar a hankali ta fada ciki, ta dafa kanta akan sitiyari kuka take rusawa babu ji ba gani. Ba ta da mai lallashinta. Sai a ranar a lokacin ta ji kewar wani na ta, shin wa zata labartawa wannan bakin labarin?

    Uwarta mahaifiya har yau tana nan da rai, amma rabonda ta taka ta je ta manta. Haka kannenta ba ta zuwa inda suke suma ba sa zuwa. Ba wai dan komai ba sai dan kalar tata rayuwar da suke ganin ba ta mu su ba.

    Babarta mahaifiya tayi fadan tayi fadan amma ko gezau, hindu ta yi nisa. Har ta kai bata son zuwa gidan don ta san karshen zancen fada ne. Da wayo da wayo ta fara janyewa, tunda dai yaranta ai ba sa gidan. Daga baya sai suka ji dif harkar gabanta kawai take.

    To yanzu da haka ta same ta wa zata je wa ya jajanta ma ta? Wannan zance ne ma na abun fada? To amma idan ta durkushe wa zai yi jiyyarta? Ta tuno ‘yan yaranta da suka girma yanzu, ba ta so su sani ba ta son duk wani abu da zai jagula ma su lissafi.

    Rayuwarta ta fara dawo ma ta a idonta kamar majigi. Wata irin nadama tana hudo ma ta jiki. Da gaske tayi kuskure? Da gaske ne? Shin kuskurenta ne ya sa ta fada a wannan halakar ko kaddararta ce?

    Tsawon shekara sama da goma sha biyar kenen tana wannan rayuwa ta zaman kai, amma bata taba samun abunda ya dake ta irin na yau ba. Yanzu ya za tayi?

    Da kan ta ta lallashi kan ta tayi shiru ba don ta so ba, ta kunna motar ta dau kan titi. Wata irin nadama ce take dirar ma ta, sai take ganin bai fi nan da sati 1 zata rasu ba to wai me za ta ce wa Allah?

    Ta fada zurfin tunani tana tuno abubuwan da ta aikata a wannan doguwar tafiya ta shekara 15 sai ta ga gabadaya babu abun tsinta a ciki. To ita yanzu idan ta mutu ta cewa Allah me? Har me ta tanada da zata nuna?

    Har ta hau kan titi kuka take. Da niyyarta daga nan zata wuce shagunanta ta duba halin da ake ciki to amma ba zata iya ba.

    Luba ce ta fado ma ta a rai. Tayi tunanin bari ta je wajenta ta labarta mata halin da take ciki. Suka dade ba su hadu ba saboda cewar Lubar yanzu ta kama kasa.

    A shekaru goman nan abubuwa dayawa sun faru, a ciki har da auren Luba da mashahurin attajirin nan kuma tsohon sanata Alhaji Hamza Dala. Wani aure da ya zo a lokacin da Luba ke bukatarsa, auren da ya zame ma ta tsani na taka haye.

    A halin da ake ciki yanzu takara take yi ta dan majalisar tarayya, matakin da Alhaji Hamza Mai Dala ya dafe ma ta. Burirrikanta suna neman ida cika, babu wani abu da take yiwa kallon nasara fiye da wannan kujera.

    Luba na son mulki tana kaunar ace yau ga ta a matsayin da ta isa ta taka uban kowa. Yau ga ta a asusun gwamnati tana yaftar abunda yayi daidai da raayinta, yau ga ta a duniya tana juyata a tafin hannu.

    Kiranta tayi ta gaya ma ta zuwanta, ba tayi wata wata ba tayi hanyar gidan. Kerarran gida ne , tamfatsetse na zamani. Tun daga gate aka bata izinin shigowa don dalilin cewa matar gida ta sanar.

    A falo ta tarar da ita tana waya sanye da wata doguwar riga irinta larabawa. Akwai jaka akan karamin teburin da ke gabanta da alama bata dade da dawowa ba. Kafin ka ce me an cika gaban Hindu da kayan makulashe. Amma Hindu ba ta iya taba ko daya ba. Ta dube ta ta ce

    ” Hindu lafiya kuwa? Ni ko a waya sai naji muryarki wata iri..kamar ma kin sha kuka. Kamar dai kina cikin damuwa, da fatan dai ba ta kudi ba ce?”

    Wani abu ya tokarewa Hindu a wuya kawai sai ta fashe da kuka. Ina ma damuwar ta kudi ce! Yau ga damuwar da bata bukatar kudi, wayyo Allahnta!Ina ma kudi zai iya gyara mata rayuwarta.

    Da can tana hangen kudi kare magana, yanzu kuma sai ta ga gashi tana cikin kudin amma matsala bata kare ma ta ba. Ashe dama haka duniya take. Ta ce

    ” Asibiti na je, aka ce wai ina dauke da cutar kanjamau”

    Wani shiru ne ya gifta. Kawai sai ta ji Luba ta fashe da dariya. Wata irin mahaukaciyar dariya har da faduwa kasa.

    Hindu ta zuba mata ido tana mata kallon mahaukaciya don tunanin da take ko shaye shaye ya taba ma ta kai. To amma sai ta ga ta dube ta ce

    ” Yanzu ke Hindu don cutar kanjamau shi ne kika zauna kina rusa kuka kamar an ce kudin hannunki sun kare? To mene a kanjamau idan dai ba an san cewa kana dauke da ita ba. Kin ganni nan na fi shekara uku dauke da cutar kanjamau, to amma me kika ga ya canja a rayuwata”

    Cikin tsananin mamaki Hindu ke kallonta, jikinta har karkarwa yake ta nuna ta da danyatsa ta ce

    ” Kina dauke da cutar kanjamau fa kika ce! Kuma shi ne har kika yi aure?”

    Dariya Luba ta cigaba da yi tana yiwa Hindu kallin sakarci ta ce

    ” To Hindu sai kar nayi aure bayan ina bukatar amfanin da auren zai min? To a goshi na aka rubuta cutar? Ya kamata fa ki gane Hindu, ke ce za ki tafiyar da rayuwarki fa yanda kika so. Ai cuta ba mutuwa ba ce, a wannan zamani da magani ya yawaita ai kawai cigaba za kiyi da harkarki.”

    Hindu ta ce a tsorace

    ” kuma ba kya tsoron wataran ya gane kina da cutar. Shin Luba kina da labarin ko mijinki waye kuwa? Wanenne bai san shi ba akan harkar aiwatar da ta’addanci ga duk wanda ya sake ya shiga huruminsa”

    Luba tayi galala da baki ta ce

    ” To sai dai in ke za ki gaya ma sa!.shi Allahn musuru ne da zai sani? Ba a shafa kanjamau ni aka shafa min? Shi mata nawa yake bi da zasu iya shafa ma sa? Ya za a yi ya san ni ce?”

    Ta rage murya a hankali ta ce

    ” Kuma ba ma shi kadai na shafawa ba, muna nema da kaninsa Alhaji Bilya Dala”

    Wata irin zabura Hindu tayi. Ta kankance idanuwanta ta ce

    ” Shin ko kin san Luba kina wasa da wuta? Shin kin ko san yanzu siyasa kike ciki dumu dumu ba ta kuma bukatar abun fada?”

    Luba ta ce

    ” Hindu ke kadai ce aminiyata ta tale tale, muna tare sama da shekaru 15. Ke kuma kadai na gayawa, idan magana ta fita ke ce. Ai ni ban taba kaunar Alhaji Hamza ba, dama can bilya ne manemi na..shi Alhaji Hamza ai tsani ne. Sai da shi zan samu cikar burina. Dalilin kenen da muka yi da Bilya din na auri yayan na sa, kin ga baya zabe kawai sai mu hadu mu salwantar da dan banza mu ci duniyarmu da bakin allura.”

    Jikin hindu har karkarwa yake, duk iya barikinta Luba ta shafa mata lafiya.

    Ta fara yi mata hirar fita wani kampen na siyasa da za suyi da irin yadda take so ta cimma burirrikanta sai Hindu ta mike. Ji take komai na duniya ya gundureta.

    Sallama suka yi Hindu ta wuce mota da cewar bayan kwana biyu zata dawo su tattauna.

    Daga nan gida ta wuce. A zuciyarta tana tunanin zata hadu da Alhaji Awaisu. Da tayi niyyar ta yi masa cin mutunci na fitar hankali, amma yanzu ta canja tunani.

    Lallaba shi za tayi ya aureta ba zata nuna masa maganar cutar nan ba ko a ido. Ta san dai shi ya sa ma ta, za ta nuna kamar bata gane ba ta samu dai ayi auren ko ta tsira da wani abun.

    Tana shiga farfajiyar gidan tayi hamdala ganin dalleliyar motarsa a fake a gurin. Wato ya zo kenen, faduwa ta zo daidai da zama. Ta fito jikinta ba laka ta shige bangarenta na gidan.

    A falo ta tsaya dube dube bata gan shi, ta san watakila bandaki ya shiga. Sai ta zauna zaman jiransa. Amma me? Sai take jin wani irin kara haka kamar ihu. Me ke faruwa ne?

    Abunda ya sa ta tashi zumbur kenen ta shiga daya bangaren zata tuntubi iya mai kula ma ta da gida ko lafiya.

    Sai a lokacin ta ji ihun sosai daga bangaren. Da ta tsaya tsai sai ta gane kamar ihun budurwar diyarta asiya mai kimanin shekara 19 zuwa 20.

    Sai a lokacin ta tuna ta ga motar ta da ta siya mata kwana 7 da suka wuce ta ke zuwa makaranta, Kano poly. Guda biyu ta siyo amma babu yanda bata yi da Abba ya karba ba ya ki, ta rasa kalar taurin kan da ke damun yaron.

    Kawai banka dakin ta yi a gigice, a daidai lokacin ta ji ihun ya dauke. Numfashinta ne ya tsaya cak saboda abunda idanunta ya gane ma ta.

    Alhaji Awaisu ne ya daure diyarta gudan jininta Asiya yayi ma ta fyade!

    Da alamu ma kamar a buge yake.

    Shigarta yarinyar ta sume, ga jini nan male male a tile din dakin.

    Tun da take a rayuwar duniyarta bata taba ganin mugun gani irin na wannan ranar ba!

    Wani irin ihu ta kwalla

    ” Ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh”!

    ******************************

    Wani saurayi ne fari dogo sanye da fararen kaya tazarce zaune a gaban ajin na makarantar islamiyya ta ” Riyadul Quran”

    Ba shi da wasu tarin shekaru amma sai zurfin ilmi. Malami ne a makarantar kuma shi ke daukan ‘yan babban aji saboda mahaddacin Alqurani ne. Ya sauke manya manyan littafan addini.

    Dalibi ne a makaranta Bayero da ke kano, yana karatun injiniya. Da yamma yana koyarwa ne a wannan islamiyya ta “riyadul Quran”. Ranar asabar da lahadi da safe yana koyarda yan tahfeez.

    Alashinsa duk wata bai taka kara ya karya ba amma ya gwammace wa hakan. Mutum ne mai kokarin neman na kai domin a lokuta da dama yakan je wani garejin mota yana taya su aiki nan ma yana samun kudin kashewa.

    Abdulhakeem wanda aka fi sani da Abba mutum ne mai zuciya da sanin ya kamata. Zama daya za kayi da shi ya shiga ranka farat daya saboda hankalinsa. Yawa yawan yanmatan islamiyyar na yawan rubuto masa wasika na wai suna son sa saboda yanayin kyaunsa da hali irin na sa amma sai ya share. Shi ba wannan ne a gabansa ba.

    A yanzu ma sun kammala ajin, aji ne na mata da maza. A lokacin ne ya dago kai yana murmushi, ma’abocin murmushi ne Abba ya kalli ‘ yan ajin ya ce

    ” shin ko akwai wani mai tambaya kafin mu rufe da addua?”

    Anan wata zaqaqura Hafsa ta mike, kallo daya ya ma ta ya dauke kai. Ta aiko ma sa wasika ya fi shurin masaki akan irin kaunar da take ma sa, ya share. Sai daga baya ya gane kamar wata gaba take yi da shi, wannan ma bai dame shi ba. Ta ce

    ” Malam ina da tambaya”

    Ya ce

    ” bismilla malama hafsa”

    Ta yi yatsina ta ce

    ” Allah gafarta Malam menene matsayin dan karuwa a musulunci?”

    Wani irin shiru ne ya ziyarci ajin. Wani abu ya tattaro daga zuciyar Abba ya zo ma sa maqoshi. Yayi sauri ya danne bacin ran sa, ya mamaye fuskarsa da murmushi ya ce

    ” Malama hafsa shin akwai wani banbanci tsakanin dan karuwa da ragowar ‘ya’yan duniya?”

    Ya nisa ya ce yana mai duban ajin

    ” Abunda ya kamata ku gane shi ne shi Allah yana duba ne i zuwa aiyukanmu ba aiyukan iyayenmu ko ‘ya’yayenmu ba.

    Da a ce sakamakon aiyukanmu na zuwa ne dangane da na iyayenmu ashe da Allah bai bawa Annabi ibrahim annabta ba! Domin kuwa ai mahaifinsa kasurgumin mai bautar gumaka ne. Da Allah bai alkarwantawa Asiya matar firauna aljanna ba domin kuwa mijinta kasurgumin kafiri ne! Shin ko kin san dan annabi Nuhu kan’ana bai yarda da shi ba? Shin kin san cewa da annabi Nuhu ya gayyace shi shiga jirgin ruwa bai shiga ba..domin bai bada gaskiya da shi ba?

    Shin Allah ya hukunta wadannan bayin Allah don dalilin makusantansu?

    Shin kin san cewa Allah ” Azza wa jalla ne? Madaukaki ne shi? Shi kin san Al Hakeem ne shi mai hikimar fidda baki daga fari, ya fidda fari daga baki?

    To ko zina aka yi aka haifi mutum hakan ba yana nuna cewa shi batacce ba ne a musulunci, ba zai samu da Rahamar Allah ba. Laifin iyayensa daban na sa daban.

    Allah yana cewa

    Duk wanda ya zabi ya bi hanya madaidaiciya, to yayi ne domin kan sa. Haka duk wanda ya zabi ya baude hanya , shi ma yayi ne domin kan sa. Babu wani wanda zai dauki nauyin zunubin wani. Suratul Israa (17:15)

    ” Allahu Akbar” yan aji suka yi kabbara.

    Ya sunkuyar da kan sa a hankali ya dago ya zuba wa hafsa ido ya ce

    ” Malama hafsa da fatan na amsa miki tambayarki?”

    Ta gyada kai a sanyaye yan ajin suna watso mata harara.

    Adduar rufewa yayi aka tashi. Allah Allah yake ya bar makarantar saboda tsananin bacin ran da yake ciki.

    Ya rasa yanda zai yi da rayuwarsa, yayi kuka ya gayawa Allah amma har yanzu bai samu sauki ba.

    Kowa ya san babarsa karuwa ce wani abu da yake kwana yake tashi da shi a rai. Wani abu da ya zame masa abun tsayawa a rai tun yana karami.

    Ya taso da wani irin kyankyami na halayyar mahaifiyarsa alamarin da ya sanya ko kusa da ita bai cika son zuwa ba. Yana rayuwar shi ne shi daya kuma yayi alkawarin sai ya inganta ta.

    Zai zama jarumi jajirtacce mai tsantseni na addini. Talauci ba hauka ba ne da zai je ya sayar da imaninsa domin sa. Ko yaushe mahaifiyarsa zata gane? Sai yaushe?

    Haka ya taka a hankali ya soma fita daga harabar makarantar. Babu tazara sosai da gidan mahaifiyarsa inda bacci ke kai shi ya soma takawa.

    A hanya ya hadu da wannan mutumin da ya zame ma sa sabo su gaisa. A wani benci yake zama kamar yana bara kamar baya yi. Kayan jikinsa babu na zaba, haka yake diki diki.

    Yau ma da ya zo wucewa mutumin ya ce

    ” Ah yaro an fito, Allah ya albarkaci karatu”

    Abba ya tsaya suka yi musabaha. Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro dari biyu ya ba shi, dama haka yake yi. Ba su dade da karbar albashinsu na wata ba, shi kuma dama can mai yawan sadaka ne.

    Mutumin ya karba yana ta zuba godiya kamar yadda ya saba har ya kara da cewar

    ” Yaro Allah ya maka albarka! Allah ya kiyaye ka ya kare ka. Biiznillahi sai ka zame wa musulunci jakada. Sai ka zame wa iyayenka abun ceto!”

    Tsayawa yayi cak!

    Ya waiwayo a hankali ya cigaba da karewa mutumin kallo a tsanake wani irin farin ciki na fatattakar bacin ran zuciyarsa. Ba a taba adduar da ta zauna ma sa a rai irin ta yau ba.

    Har akwai abun da ya fi ya zama jakadan musulunci, ya ceci iyayensa. Duk da cewa uwa gare shi yanzu kawai, mahaifinsa ya rasu a kullum dukkaninsu yana musu addua.

    Dawowa yayi ya kara wa dattijon mutumin nan kudi ya juya yana murmushi. Zuciyarsa fes, watakila yau mahaifiyar ta sa ta samu tukuicin fara’a darajar wannan addua.

    Haka ya shiga gida, ya ga motar kanwarsa Asiya abunda ya dada kara masa farin ciki kenen. Wato ta dawo daga makaranta, yana kaunar kanwar ta sa kamar ran sa. Allah Allah yake ya gama makaranta ko dan aiki ne ya kara samu, aure zai yi ya dauke kanwar tasa. Ba ya so ta taso a irin wannan rayuwar gidan na su. Ko da yake ita ma kanwar ta sa ai ta girma, Allah ya bata miji nagari da zai aureta yayi nesa da ita daga mahaifiyarsu.

    Da wannan tunanin ya shiga gida. Wani abu ne ya sa ya tsaya cak. Karan ihun da mahaifiyarsa ta ke yi.

    Abun ya ba shi mamaki don ita ba maabociyar shiga sashensu ba ce. Da sauri ya fada dakin Asiya ganin daga nan ihun ke fitowa.

    Shigarsa kenen, abubuwa guda biyu suka sa numfashinsa yayi tafiyar wucen gadi.

    Ganin kasurgumin makiyinsa kuma dadiron mahaifiyarsa Alhaji Awaisu cukwikwiye a hannunta kamar ba zata dake shi ba tana zabga kuka. Ya tsani ganin mutumin a rayuwarsa duk kuma duk yanda ya so ya danne kiyayyarsa ya kasa domin ko gaisuwa bata iya hada su.

    Alhajin da kan sa ya ce zai biya masa karatu zuwa ingila, a ranar mahaifiyarsa da ta isar da sakon ba karamin haukarsa ta gani ba. Ya tsane shi tsanar da bazai iya kwatantawa ba domin ya taimaka kwarai wajen kara dulmiyar da mahaifiyarsa.

    Na biyu sai ga Asiyan shi a yashe an yaga kayan jikinta kwance male male cikin jini, da alamar zubar jini har daga goshinta da ke nuna an doka ta da wani abu.

    A cikin kankanin lokaci ya gane mummunan abun da ke faruwa. Bai yi wata wata ba ya daga hannunsa a dunqule ya dirkawa Alhaji Awaisu naushi ya kifa jini ta baki ta hanci. Ya hau kan ruwan cikinsa ya dunga kirbarsa kamar Allah ya aiko shi.

    Gani tayi zai kashe shi ta fara jan sa kawai sai ya wancakalar da ita. Kamar baya cikin hankalinsa ya dube ta idanunsa sun yi jazir ya ce

    ” Kar ki sake ki kara taba ni”!

    Duk halin da take ciki sai da taji gabanta ya fadi. Kamar ba dan cikinta ba, kamar wani sabon mutum da bata sani ba.

    Kinkimar Asiya yayi, ya nemi wani zani ya rufa ma ta yana kuka. Ya dauketa kamar bebin roba, da mukullin motarta, a lokacin Alhaji Awaisu ya samu kan sa ya fice a guje.

    Hindu ta yo kan Abba tana kuka da nufin za ta taimaka masa da rike Asiya ya fincike. Cikin kuka ya ce ma ta

    ” Ita ma kar ki taba ta! Ya za ki haifa diya a cikinki ki tarwatsa mata rayuwa irin haka! Duk abinda ya same ta ke da shi kuyi kuka da kan ku! You have to pay for this!”

    Fita yayi da gudu ya bar Hindu kamar zata mutu da kuka. Ya dauki motar Asiyan ya wuce da ita asibitin da suke zuwa. Anan ma aka tsaya bata lokaci akan report na yansanda da sakaci irin na asibitin kasarmu.

    Likitan da ke kan ta mamaki zai kashe shi. Ya dade a rayuwarsa bai ga mummuna case irin haka ba, dalilin ma kenen da ya dage sai an taho da yansanda. Jinin da ke zuba a jikinta ya ki tsayawa. Hakannan ta fara aman jini da ke nuna an dake ta sosai a ciki.

    Abba ke ta zarya a coridor har Hindu ta iso, da kyar take tafiya saboda bakin ciki. Tun da take a rayuwarta bata taba da na sani ba iri na yau.

    Ashe Alhaji Awaisu azzalumi ne irin haka ta sa hannu ta gayyato shi rayuwarta ga shi ya tarwatsa ma ta ita. Da me za ta ji? Yau tayi Allah wadai da rayuwar karuwanci da ta fada domin kuwa bata kare ta da komai ba sai da na sani.

    Bayan awa kamar 2 likitan ya fito ya ce za su iya zuwa su gan ta, amma fa ba ai mata aiki ba domin yana jiran babban likita ya zo wanda yake kan hanya.

    A sassarfa suka shiga su duba halin da take ciki, gabadaya kamanninta sun canja. Da sauri Hindu ta nufe ta zata kama hannunta yarinyar ta janye.

    Ta tsirawa uwar ido da wani irin kallo a cikin wata irin siga ta ce a hankali

    ” Ki…n ..kash..eni mamah!way…yo mama..wa..yyo Alla..h.na”

    Hindu bata san lokacin da ta fada kan Asiya ba. Bata manta da cewar Alhaji Awaisu da yayi wa Asiya fyade na dauke da kanjamau ba! Da me za ta ji”

    Kuka take ta ce

    ” Asiya kar ki min haka. Kar ki zargeni ba ni da hannu! Asiya ki yafe min..ki yafe min na zame miki sanadi”

    Wani irin amai yarinyar ta fara yi na jini, likitan ya kora su waje. Abba baya iya cewa komai sai hadiyar zuciya yake. Rokon Allah yake ya sa a ce mafarki ne ina ma ba da gaske ba ne.

    Ita kuwa Hindu jikinta gabadaya ba laka, don yadda ta ga Asiya ta san sai wani ikon Allah!

    Likitan ne ya fito, cikin sharbar hawaye Hindu ta ce

    ” Yaya ake ciki likita?”

    A sanyaye ya ce

    ” Ta zubar da jini dayawa…i am sorry..i am so so sorry Hajiya…we lost her!”

    Ta gane me yake nufi, ta san kawai Asiya babu!

    Ji tayi kamar zata zube ta jingina da bangon gurin. Rayuwar ta ce take dawo mata a idonta kamar a mafarki. Ta tuna irin ranar da mutuwa ta warce nata jinjirinta muhammadu sabode tsananin talauci.

    A yau ga ta a babban asibiti da kudi fal jakarta amma ba ta fi karfin mutuwa ta sure ma ta Asiya ba! Asiyar da ta zamo sanadiyyar da mutuwa ziyarce ta. Ashe sanadin da Alhaji Awaisu zai zame mata kenen?

    Ina ma ina ma, ina ma ta zauna a talaucinta da ya fiye mata wannan rana da dadironta ya haikewa diyar cikinta ta sheka har lahira! Wannan wani irin labari ne, labari mafi muni da bata taba jin ko makamancinsa ba a kafafen yada labarai ba.

    Ashe haka Allah yake hukuncinsa? Ashe kai bawa ba komai ba ne? Ashe baka isa da komai ba? Da me za ta ji? Ina zata je? Asiya kuwa zata taba yafe ma ta.

    Waji irin naushi Abba ya kai wa bangon da ta ke jingine da, karfin naushin ya sa ta gane tabbas ya targada daya daga cikin yan yatsunsa. Ta san ji yake kamar ya kashe ta.

    Ta dube shi tana makyarkyata a idanuwansa ta hango wata matsananciyar tsana da bata taba zaton da yana iya yiwa uwarsa shi ba. Hawaye ne yake zubar masa kamar da bakin fanfo, yana so yayi magana ya kasa.

    A hankali ta ji ya ce

    ” Ba zan yafe ba, tunda ku ka raba ni da Asiya”

    “Ba zan taba yafewa ba!”

    Shin ko ka san irin son da ke tsakanin uwa da da?

    Shin da gaske za a iya sadaukar da komai saboda da?

    Shin da zai iya yafewa uwa komai dumbin laifukanta?

    Wasu abubuwan su kan zo mana a sigar da na sani domin mu hankalta

    Wasu abubuwan izina ne!

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!