Duniya ta – Chapter Twenty-one
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Wani irin ciwo kan sa ke yi kamar zai rabe biyu. Tun da yake a rayuwarsa bai taba shiga tashin hankali irin na yan kwanakin nan ba.
Ya wayi gari da wani mummunan al’amari mai ban alajabi da kusa sa kwakwalwarsa tarwatsewa. Wai an kashe Rebecca a cikin gidansa kuma wai Rukky ita ce da wannan aiki.
Tunaninsa ya kara daurewa ne ganin yadda suka rabu da Rebecca a cikin gidan lafiya lafiya kafin ya fita. To har yaushe Rukky ta shigo ta kasheta ta dauki gawarta ta saka a boot ta tafi? Wani irin rikitaccen al’amari ne wannan?
Ganin irin labaran da ke yawo a jaridu da gidajen talabijin na gari ya gane cewar akwai wata a kasa. Kamar wani shiri ne da aka yi shekara da shekaru da shiryawa aka tanada daidai wannan lokaci domin a tarwatsa shi.
Bai san ko waye ba amma yana tabbatarwa da kan sa akwai hada hannu da jamiyyar abokanan hamayya.
Almustapha ya san yana da makiya, makiya ba na wasa ba amma fa bai taba zaton kiyayyar ta kai haka ba. Sai yake ganin kamar an yi anfani da Rukky ne domin a cimma buri akansa.
Amma da gaske Rukky ta kashe Rebecca? Zancen da ya kasa kwanta ma sa a rai kenen.
To idan ba ita ta kashe ta ba ya aka yi gawarta ta zo boot din motar ta? Zai bincika sai ya gane inda laujen yake a cikin nadi.
Ya wayi gari yansanda sun tafi da shi kan cewar za suyi masa tambayoyi. Maganar da sa hannunsa a kisan Rebecca ya sa ‘yan gari babu abunda suke masa shi da Rukky sai tofin Allah tsine.
Babu wani labarin sirrinsa da bai gani yana zaga gari ba. A halin da ake ciki investors din su dayawa ne suke zare hannun jarinsu daga kamfanin I and A. Tsoronsu kar a maka shi a kurkuku dukiyarsu da suka dulmiya a kamfaninsa ya salwanta.
Hatta faifan video din da ke yawo na fadan Rebecca da Rukky ya sa kan sa kara daurewa. To wa ya dauka? Wannan alamarin ya sa ya zargi akwai wata manakisa.
Tambayoyi ake ta jero masa, ya kuma gaya musu iya gaskiyar abunda ya sani.
Ya bar gifan ne da dare misalin karfe bakwai na dare ya fita wani mitin. Kuma shi rabonsa da yayi magana da Rukky ma ya manta. Domin daga ranar da aka yi fadan nan ma bai kara contacting din ta ba.
Bai kara jin wani labari ba sai kiransa da aka yi daga police station na mummunan abunda ya faru.
To zarya dai aka cigaba da yi da cike ciken takardu amma ba su da wata hujja kwakkwara da za su daure shi da ita.
Zarge zargensa da ake yi a gari kuwa ya zaga ya karade koina. Yawa yawan masu zaginsa mutane ne da ya taimakawa mutane ne da yake lullube fuskarsa don su ga mutuncinsa. Amma a yanzu sai a sayi lokaci a gidan radio ma a zage shi tas! A tsine masa.
Babu abunda ya fi kona masa rai irin watsi da jamiyyarsu ta NPN ga masa. Jamiyyar da ya sa komai nasa da yake tunanin ita ce silar daukakarsa. Sai ga shi ba a je koina ba sun nuna ba sa yin sa. Saboda kar ya bata musu suna.
Ashe dama haka duniya take? Shi din da mutane ke haba haba da shi suna marmarin su kusance shi su rabe shi sai ga shi a kwanaki kalilan kowa ya guje shi?
Idan ya tuna Rukky na garkame a cell kafin ayi shirin zuwa kotu sai ya ji wani abu ya sari kan shi. Menene gaskiyar lamari? Ya kamata ya gan ta. Dole ne ma ya ji daga bakinta.
Da lauyansa wani barrister kabir tukur yayi magana. Ya kalle shi da alamar gargadi ya ce
” Almustapha ya kamata ka gane cewar yanzu duniya idonta akan ka yake. Ka ga maganar siyasarka ta riga ta rushe. Mutane dayawa na zargin da sa hannunka a kisan nan. Matarka ce Rebecca aka kashe, kai ne kuma ya kamata a tsaya tsakin daka ka bi ma ta hakkin jininta.
Yaya za a ji labarin kana neman haduwa da wacce ake zargi da kashe matarka? Ba ka tunanin za a kara tabbatar da cewar bakin ku daya?
Kar ka manta zance na yawo a gari cewa karuwarka ce ba ka tunani ya kamata ka musanta hakan? Abun da nake shawartarka shi ne lokaci yayi da za ka nuna baka san ta ba!”
Wani irin kallo ya dago ya qurawa barrister gabansa na lugude. Eh ya san cewa rayuwar da suka yi da Rukky ta haram ce shi yasa abubuwansu ba ko digon albarka a ciki. Amma ya ce bai san Rukky ba? Ya juya baya zai iya kuwa ? Anya?
Barrister ya cigaba da cewa
” kar ka manta wannan babban case na kisan rai, ka san kuwa ba adauki rai da wasa ba. Kar kuma ka manta wannan wacce aka kashe din mabiya addinin kirista ce. Kungiyar kare addinin kirista a yanzu kai take kallo kai kuma ta saka a gaba. Motsi kadan za ka yi su sako ka gaba. Kar a manta ana zarginka da sa a hannu a kashe Rebecca ne don ka boye sirrin dan ku da aurenku.
Da ni ne kai ita wannan yarinyar da ake zargi da kisan zan cinnawa karnuka. Ba karuwa ba ce? Ka game kai ma da hukuma ku yake ta.Yanzu fa ka san lauyan gwamnati ne akan lamarin, wannan yarinyar ce vs kano state. Ka san a kotu sai an kira ka ka bayar da bayani. Ka san fallasar da hakan zata jawo?
Hakan da za ka yi shi kadai zai sa ka tsira da kan ka. Ka nuna cewa ka tsaya tsayin daka wajen bi ma Rebecca jininta . Ka tabbatar Rukky tayi shekaru aru aru a gidan yari!”
Wani irin yarr ya ji jikinsa yayi wata irin zufa tana karyo ma sa. A hankali ya ce
” To idan ba ita tayi kisan ba fa? Sai a bar ta ta kare a gidan yari?”
” Toh ba karuwa ba ce!” Cewar barrister a fusace ” ko bata kare yanzu ba dole wataran zata kare. Dama iyakacin makomarta kenen. Ya kamata ka gane fa karuwa bata da daraja bata kuma da wata rawar takawa mai amfani a rayuwarka. Amfaninta daya ta zame maka abun nishadi a rayuwarka. Kuma ta ri ga ta zame maka. Abunda yayi saura kawai ka yar da kwallon mangoro ka huta da kuda”
Tayi ikirarin zata kashe Rebecca da fatar bakinta, ga shi video ya nuna sun yi fada. Ka ga akwai motive na kisan kenen.
Kar ka manta bincike akan gawar Rebecca ya nuna karfe 8 na dare zuwa karfe 9 aka kashe ta. An samu shaidu cewar Rukky ta shiga gidanka a tsakanin wadannan lokutan. Me ya kai ta?
A kama ta ra’ayul aini da gawar matar a boot din motar ta! An ce fa ganin za a bude boot ya sa ta zaro kudi za tayi bribing din su. Bayan an kamata da a kayan maye a tare da ita. Shin wata shaida ka ke bukata?
Shiru Almustapha yayi kan sa yana juyawa. Me yasa yake ji ba ita ba ce? Inaa..dole akwai wani abu. Ya ce
” Ya kamata ka gane barrister wannan alamarin yana cike da rudani. Akwai wasu behind this! Waye ya dauki wannan faifan videon? Kuma wanene yayi leaking video din? Wa ye behind watsa labarai na? Kana ga yadda kowane kamfanin jarida da tashar talabijin suke watsa labaran nan, a tunaninka yin kan su ne? Ko saka su aka yi?”
Barrister yayi shiru ya ce
” Alamari irin na kotu shi ne, duk lokacin da kake so ka dauke laifi akan wani to dole ka samu wani da za ka daurawa. Abun tambaya anan shi ne idan ba ita Rukky ba ce tayi kisan wanene yayi? Yanda za ka fara kafa hujjojinka akan wancan yadda alkali zai karba ya aminta da su”
Wani irin numfashi Almustapha ya saki kan sa ya gama daurewa. Ko ma dai menene ya zama dole yayi magana da Rukky. Ya ce
” Ina ga barrister ya zama dole nayi magana da yarinyar nan Rukky”
Wani irin kallo barrister ya watso ma sa cikin tuhuma ya ce
” Ka san me kake yiwa rayuwarka kuwa? Na ga kamar duk bayanan da nake maka basu gamsar da kai ba, ko baka gane don kai nake yi ba? Mu’amalarka da yarinyar nan Ruky dole ne ta tsaya. Dole ka ma ta matsaya.”
Wani irin huci Almustapha ke fitarwa daga bakinsa. Barrister ya tatttara ‘yan takardunsa zai fice. Ya juyo a hankali ya kalli Almustapha ya ce
” Ka da ka yarda da kowa, ka da kayi wata magana da ya danganci shariar nan da kowa. Babu wani abun yarda da. Mutane ne suke farautarka ya kama ta ka zama very careful”
Gyada masa kai kawai yayi suka rabu.
Tunani ne fal zuciyarsa Amma ya rasa yanda zai yi. Wai wanene masoyinsa na gaskia? So yake ya samu lauya a asirce ya tsaya akan case din Rukky..To amma hakan ba kuskure ba ne? Hakan ba cakawa kai wuka ba ne?
Har ya daga waya zai kira sadiq sai kuma ya ajiye. Maganar barrister ya tuna
” ka da ka yarda da kowa…”
Yanzu shikenen mafarkansa sun tafi? Yanzu shikenen siyasar sa ta kare? Mutuncinsa ya gama zubewa? Sirrikansa an watsa su a duniya. Wani irin ibtila’i ne?
A lokacin ya tuna da wani shahararren lauyan babansa. Barrister Kamal Dauda. Duk halin da babansa ya shiga bai saka kamal dauda mantawa da shi ba. Watakila a wajensa zai iya samun amsoshi. Watakila ya samu ya tsaya ma ta a kotu a sirrance ba tare da an gane da sa hannunsa ba.
Washegari suka hadu da shi. Bai boye masa komai ba ya gaya ma sa. Ya ce zai bincika komai akan case din ya sha kuruminsa zasu bari sai kafa ta dauke da daddare za su je wajenta. Yana da mutane a police station din da aka tsare ta zai san yadda zai yi.
Washegari da dare misalin karfe 10 ne suka bayyana a police station na hotoro.
Lokacin da ta fito kallo daya Almustapha ya yi ma ta ya dauke kai saboda tsananin tashin hankali. Me ya sa suka sa kan su a irin wannan rayuwar?
Ko da ta gan shi kuka take ta ce
” Almustapha dama za ka tuna da ni? Na dauka kai ma ka yarda da zargin da ake min…na shiga uku na. Ban san ya aka yi na samu kaina a cikin wannan rayuwar ba. Ina ma..ina ma na mutu tun da dadewa na hutasshe da kaina fadawa cikin wannan hali. Wallahi ba ni na kashe ta ba, sharri ne ake son kullamin”
Kallonta kawai yake. Ya kasa cewa komai. Kallon komai na ta yake, yanayinta ya canja kamar ba yar gayen nan Rukky ba.
Anan Barrister Kamal ya nemi ta ba shi bayani daki daki game da abu da ya faru. Ta kuma ba shi. Ya dubi ta ya ce
” ke a ran ki wa ki ke zargi da kulla wannan kullalliyar?”
” Luba”!! Ta ba shi amsa
” Dama na san wani abu dole zai biyo baya ganin yadda muka ci amanarta. Yanzu na gane ita ko wani da ke ma ta aiki ne suke turomin sakonnin nan. Musamman na in zo gidan Almustapha yana nema na.
Ya ce
” Da ki ka fito ba ki lura da canji ba a motarki na kamar an taba ta?”
Ta ce bata lura ba. Ya ce
“Da kika shiga gidan kin hadu da Rebecca”
Ta ce bata hadu da ita ba sai dai amma ta tambayi kuku ko tana nan.
Ya ce
” wannan hanyar da kika bi kin saba bin ta dama? Idan kin saba kin taba ganin check point na yansanda a wurin”
Ta ce
” Eh na saba bin ta amma ban taba ganin check point ba”
Ya sake tambaya
” Me ya sa kike zargin Luba?”
” saboda ita ce mu ke gaba da ita ta kuma ce zan ga abunda zai biyo baya.”
” Banda Luba wanene ki ke zargi?”
Ta ce
” Gaskiya a raina babu kowa”
Ya ce
” A report din da aka bani na post motem na gawar Rebecca ya nuna cewa lokacin da aka kasheta yayi daidai da lokacin da kike cikin gidan. Ba ki ji wani ihu ba? Ko sauti?”
Ta ce
” Ban ji ba gaskiya. Domin gidan fafadan gida ne mawuyaci ne aji hakan”
” Ban da Luba wanene ki ke zargi kuma?”
Ta ce babu
Ya ce
” A cikin binciken da na karba daga yansanda a gano cewar wukar da aka kashe rebecca da ita tana dauke da finger print na mutum biyu. Daya daga ciki wanda na ki ne!”
Wani irin abu ne ya dake ta ba da wasa ba. Ya dora da
” Malama Rukky shin kin san cewa yansanda sun kai bincikensu gidanki sun tarar irin wukar da aka kashe Rebecca da ita tana cikin set din wukake da kike da su a gidanki? Kamanin wukar da irin ta gidanki iri daya ne!”
Wani kuka ta fashe da ta ce
” wallahi ni ban san yanda aka yi ba. Ni ba ni na kashe ta ba. Amma…”
“Amma me?” Ya ce da ita
” Ina zargin ‘yar modu bakinsu daya da Luba”
“Me yasa kika ce haka?” Ya tambaya
Ta ce
” Shi ya zo gidana ya kawo labarin Almustapha. Kuma da ya zo na yanka mana lemo da kankana. To ina ga anan ya ya dauki wukar ta hanyar amfani da hankici ko abun rufe hannu.
Sannan shi ya ziga ni ya dun ga dirka min kayan maye akan na je na watsa taron nan. Ina zargin shi ya dauki faifan video din nan.”
A hankali bartister kamal dauda ya cigaba da gyada kai ya xe
” hakan ma zai taimaka. To amma kar ki manta fadanku da rebecca da ikirarin za ki kashe ta shi ne ya bata komai. Domin kuwa kin ga kenen akwai motive na kisa”
Wani shiru ne ya ziyarci wurin na ‘yan daqiqu kowa na wassafa abubuwa da yawa a zuciyarsa. Ya ce
” Ina ga zan dawo gobe , za.mu kara tattaunawa kafin a shiga kotu”
Da wannan suka yi sallama. Almustapha mamaki ya shallake masa tunani. Wai Luba!
Ko da yake ya san Luba na aiki ne tare da makiyansa. Domin sirrikansa da ke fita dole sai wanda ya san shi ciki da bai.
Wayarsa ce tayi kara message ne ya shigo. Wani abokinsa ne ya turo ma sa wata jarida ce ta hausa me suna “Gaskiya da Gaskiya”. An rubuta
” Shin ko kun san Almustapha Tillaberi cikakken dan caca ne?”
Sai wasu hotunansa a la mirage , kazaman hotuna.
Yayi sauri ya rufe gaban sa ke dakan goma goma. Ya san duniyarsa ta ruguje rugujewar da ba za ta kara dawo wa daidai ba!
Bai gama tunani ba aka kira shi a waya. Daga ofis ne. Ya dauka. Daraktansa ne me kula da harkokin shige da fice na kamfanin I and A group of companies.
” Yallabai ka kalli labarai kuwa?”
Bai kai ga ba shi amsa ba ya cigaba
” Yallabai muna cikin tashin hankali. Baban kanfanin nan na Amurka KNEELS wanda da karfinsa muke tsaya a kafafunmu ya zare hannun jarinsa saboda wai bai yarda da authenticity din mu ba. Suna ganin wataran za mu iya zuba dukiyarsu a caca ta salwanta. A halin da ake ciki sun janye shares din su hade da bada shawarwari tsaurara a kafafen yada labarai na duniya akan duk kamfanin da zai hada kai da mu! Yallabai wannan shi ne kamfani na 20 kuma ma fi girma da suka janye tallafinsu daga I and A. Yallabai we are about to go bankrupt!!”
Shiru Almustapha yayi. Wani irin shiru.
Shin ko wannan ita ce ranar da ake gudu? Shin ko wannan ita ce duhun? Shin ko ita ce ranar nadama??
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
