Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE Hindatu ce ke zaune a gaban mudubi tana kwalliya, tayi da wani maneminta zasu hadu karfe hudu na yamma daidai. A wayarta ta saka wata wakar sa’adu bori da take so tana bi da baki

    Lale hadiza lale lale hadiza yar malummai ka ga hadiza ta birgeni

    Ina cikin yawona ka ga hadiza ta birgeni

    Yara suna kiranta amare manya suna kiranta amare

    Zama da kishiya tilas ne ba don uwargida na so ba!

    Kai! Duniya tana kaunar Saadou Bori Allah dai ya jikan sa. Anya idan ta tashi aure da Alhaji Awaisu ba za ta kira yaron saadou bori ya wake su ba? Irin arzikin Alhaji Awaisu ai sai da haka yanda za ta fantama a cikin kawayenta.

    Ita yanzu duk yanda za a yi bata iya auren wanda bai tara dukiya ba, wanda ba zai gina mata tamfatsetsen gida ba da motoci na alfarma suna harabar pakin. Ya bata ko da miliyan goma ne ta hado lefe na kece raini, Allah ta tuba ina tsiya tsiya ina miliyan goma a wajen Alhaji Awaisu! Ai wuce nan.

    A cikin akwatin ajiyarta ta banki ma jiya miliyan 2 ya sa mata duk da ta ji dan sa ya kira shi daga zaria inda yake makaranta kan cewa lokaci yayi na biyan kudi kuma yace baya da. A wayarsa uwargidansa ta dau nambarta ta kira tayi mata zagin uwa da uba. Har da cewa wai

    ” Halin da kika sani ni da ‘ya’yana da sannu sai kin fada! Inshallahu sai kin yi kuka da idanunki!”

    Ji wani mugun fata! Yo ita ta aike shi? Ita ta sa Alhaji Awaisu yawon ta zubar har da za a kafa mata kahon zuka? Tun kan a haifeta yake yawon bariki amma kawai kawai dan an rainata sai a aza mata jakar tsaba? Bai zai yiwu ba fa.

    Don haka ta dau aniyar auren Alhaji Awaisu ko don ta nuna wa uwargidansa ita ba komai ba ce. Da sannu zata gane wa ta zaga da sannu zata koya mata hankali.

    Da wannan tunanin ta kammala kwalliyarta. Wani jan leshi ta daura ta dau komai fari ta saka. Dama bata yafa mayafi don ba zata iya ba. Ta dau jakarta kenen wayarta tayi kara. Kallo daya ta yiwa wayar ta ja tsaki, safara ce kanwarta.

    Ta san ba zai wuce roke roke ba abunda ta tsana. Ko korafe korafe wanda ita ba zata iya saurare ba kar ta makara. Ita fa tunda ta dauke yaranta ba sosai take lekawa ba, ina za ta iya? Ka je ayi ta maka dogon wa’azi kamar kai ka yiwa shedan ungozoma.

    Sai ta ki dauka. Kara kiran da aka yi ne ta dauka a fusace tace

    ” Safara wai menene wannan irin kira haka kamar na dau kayan wani”

    A zafafe ita ma safara din ta ce

    ” Mai da wukar, Hajiyarmu tun jiya take kawance emergency na asibitin Nassarawa. Idan kin yi raayi za ki iya zuwa” kit! Ta kashe wayar tana mamakin irin mugayen halayen da Hindatu ta koyo.

    Sai taji gabanta ya fadi dam! Daga larurar idon nan Hajiyarsu bata cika ciwo ba. Sai taji jikinta yayi sanyi da ta tuna rabonta da ta leka gidan ma ta manta. Hidindimu sun mata yawa.

    Sai ta dau motarta kawai ta wuce asibitin. Ko da ta isa sauran kannenta ne akan hajiyar suka gaisheta sama sama ta amsa a banzace. Daga nan sai ta fara borin kunya

    ” wani irin abu ne haka? Saboda tsabar rashin hankali hajiyar ta kwanta tun jiya a rasa wanda zai kira ni a waye ya fada mun sai yanzu? Sai ka ce wata bare”

    Babu wanda ya tankata a cike suke da ita tam!Sai suka bar ta da halinta kawai dama su suka dage a kira ta, hajiyar cewa tayi a kale ta.

    Ta kara da cewa

    ” Bani takardar magungunan da ba a siya ba na je na siyo”

    Wannan maganar ce ta sa hajiyar ta dago kai a hankali ba don tana gani ba ta ce

    ” wanene zai siyo min magani?”

    Suka ce

    ” Hindatu ce”

    Sai a lokacin tayi kokarin zama ta kalli sashen da Hindatun ke tsaye kamar zinariya ta ce a cikin murya irinta rashin lafiya

    ” Hindatu! Ki taso tun kina karama yar marainiyar Allah, na ciyar da ke da halal, na shayar da ke da halal, na tufatar da ke da halal, da karfin kwanjina na ilmantar da ke da halal. Amma duk abin nan da nayi miki ba ki gode ba sai kika kalli gazawa ta akan ki na wani dan kankanin lokaci! A yau ke zaki nema min lafiya da haramun? Shin idan kika min haka kin min adalci? Ki rike kudinki Hindatu, watakila ni lokaci na ne yayi. Ina miki fatan shiriya, ina miki fatan ki gane kafin lokaci ya kure miki!”

    Wadanan maganganu na Hajiya Uwani sun yi mugun bakanta ran Hindu. A gaban kannenta da suka sa mata ido suke watsa jita jita akanta za a yarfa? Ai ita ce mai haramun din? Wai me yasa sau dayawa naka shi ke maka bakin ciki? Kana talauce baka huta ba kayi arziki baka huta ba.

    Amma ta san laifin safara ita ce ta zuga hajiyarsa da sannu zata koya mata hankali. Ta ce

    ” Hajiya wallahi ki daina sauraren maganganun batanci na mutane akaina. Suna bakin ciki da ni ne kawai. Na sha gaya miki babban aiki na samu daga nan kuma na hada jari nake biznes na tafiye tafiye zuwa kasashe ina saro kaya. Dalilin kenen da ban cika zama ba. Amma dai kiyi hakuri”

    Maimakon hajiyar ta amsa sai kawai ta kwanta abunta ta juya mata baya. Ai ita ba yarinya ba ce yaushe za a zaunar da ita ake tsara ta. Da Hindu ta ga kamar da ma an kira ta ne a wulakantata sai ta fice fuu cike da fushi. Daga nan ne ta kira karamar kanwarsu ta bata dubu goma. Ta ce duk abunda ake ciki ta gaya mata. Yarinyar ta ce tana jin yau za a sallame su ma. Ba ta bi takan hakan ba ma tayi gaba.

    A mota ma tana ta sake sake. Za ta je wajen malam a kama mata Alhaji Awaisu da kyau. Aure za tayi ko dan yan hassada su dauke ido akanta. Ga shi nan kiri kiri ana so a raba ta da mahaifiyar ta. Kai mutane ba su yi ba.

    Ta bar asibitin, har ta zo gadar lado sai taji karan wayarta. Gabanta ya fadi sosai don tunanin ko daga asibiti ne za a ce hajiya ta cika. Sai ta ga sabanin hakan. ‘Yar Modu ne . Ta yi sauri ta dauka ya ce

    ” Hindu kina ina?”

    Ta gaya masa. Ya ce

    ” Maza maza bamu da nisa karaso kan titin maiduguri road ki sha kallo. Kyaun karya ai hallara! Ahayye yau naga abunda ya isheni abun zama ya mutu ya bar zani! Za a yi yakin ojuku a karo na biyu. Mu dai ‘yan mu hada ne ba ‘yan mu raba ba! Duk wacce ta raba wannan fadan ni ‘yar modu na ce Allah ya tsine ma ta!”

    Ba tayi wata wata ba ta ce

    “gani nan!”

    Cikin minti biyu ta karasa inda ‘yar modu yake ya fado motarta ya na cewa

    ” mu tsaya cak anan, ki zuba ido kofar kemis din can ki sha kallo”

    Ta buga tsaki ta ce

    ” Ji wani sabon salon iskanci. Ni na zata ma wani abun ne. Zan tafi wani babban uzuri ka tsare ni”

    Ya kama haba ya ce

    ” Ke Hindu! Anya kuwa ba irinku ba ne ake bude kofar tuba gajen hakurinku ya sa har a rufe ba ku tuba ba! Minti nawa ne idan ma karya nayi za ki tsire ni? Uwar gajen hakuri! Ke idan gajen hakuri abun yi ne uwaki ta kawo ki duniya?! Ai da garin garaje ta barar da cikinki! Ahap!”

    Abu daya ne tal ya hana Hindu mayar masa da martani zagin tsintar waken da yake yi mata. Al mustapha ta ga ya fito daga wani babban wajen siyar da magani dauke da karamar leda, a gefensa Rukky ce hannayensu a sarkafe! Suka shige wata bakar mota mai bakeken gilasai suka shura gaba.

    Saboda tsabar mamaki sai Hindu ta ji kamar ruwa ya cinyeta. Ta juyo ta kalli ‘yar modu da ke mata kallon hadarin kaji ta ce

    ” Me nake gani haka? Yau ni Hindatu me zan gani! Yar modu ko ido na ne”

    Ya ce

    ” Ina fa idon ki..abun da yake akwai shi kika gani! Rukky ce take wasa da bakin bindiga! Duk inda harsashi ya subuce kin ga ai dole kan wani zai fada! Ahayye ana rikici a legas billahillazi har an kashe mutum dubu!”

    Mamakin Rukky da Almustapha ya kasa barin Hindatu. Ashe Rukky maciya amana ce. Ta san ita ta kwace Almustapha amma ta zauna cikinsu ake jaje? Abunda ya fi batawa Hindatu rai kenen.

    Don ranar a gabanta ta karbi wasu binne binne ta ce zata taya Luba da su. Ashe makirci ne!? Ashe basaja ne! Wasanta take gyarawa taka bata na luba. Lallai ta yarda karuwa bata da amana. Amma za su shayar da ita ruwan mamaki.

    Ta kalli yar modu da kyau ta ce

    ” Akwai matsala, Akwai babbar matsala!”

    *********************************

    A safiyar Ranar da Almustapha ya farka ne a matukar gajiya. Ya yini da tunane tunanen tunkarar Rukky ya ji wani abu a kanta. Sai kuma mutanen jam’iyyarsa suka kira sa kan akwai fa mitin yau da tsakar dare.

    Ba shi da wani zabi illa ya tafi can. Maganganu ne dai kan yarda abubuwa zuka dau zafi. Mafi yawan manyan manyan an yi musu kashedi da taka tsan tsan kan harkokinsu saboda abokanan gaba fa idonsu na kai. Neman dalili daya suke mutum ya tabka wani kuskure ko abun Allah wadai su yiwa mutum caa mutane su guje shi. Daga nan abu ya zo ya baci a rasa kuri’un dubban mutane. Abunda ba a fata.

    Daga wannan mitin bai kwanta ba sai bayan asuba. Ya tashi karfe 10 na safe a gajiye tilis. Shi ma ba wani abu ba ne ya tashe shi sai kiran waya daga mahaifiyarsa.

    Hankalinta kwance ta ce

    ” kwana biyu shiru kai baka leko ba idan an zo inda kake ma ba samunka ake ba. Abubuwan siyasa sun matso kuma ba a ganinku.”

    Anan ya gaisheta ya kawo mata dan uzurinsa. Ta karba ba tare da ta wani damu ba tayi masa maganar wasu kudade ya ce zai turo. Sai daga karshe har za suyi sallama ne ta ce da shi.

    ” Ka san mahaifinka kuwa an kawo shi yau kwana biyu daga Niamey jikinsa yayi tsanani ko maganar kirki baya iyawa? Da kyar dazu na sa masu aiki suka shiga suka dan goge masa jiki ko ya dan ji dadi. Amma fa bai iya daga komai”

    Wani irin abu ne ya tasowa Almustapha tun daga sassan jikinsa zuwa zuciyarsa ya tokare. Mahaifiyarsa ce kawai zata iya masa haka ya kale. Ubansa yana kwance irin haka sai yanzu zata gaya masa? Har take masa wasu zantattukan kudi? Wani wata irin zuciya ce da ita.

    Bai ma iya amsata ba kawai katse wayar yayi ya tashi ya shirya ya fice daga gidan. Gidansu ya wuce kamar yanda ya saba ya tardata a falo tana kallo. An kawo mata abun karin safe tana karyawa.

    Gaisheta yayi sama don kar ma ta tsare shi da wata hirar ya wuce sashen mahaifinsa. Abu daya ne ya sa ya tsaya cak! Wani irin wari ne yake busowa da ya rasa na menene. Ya tsaya yana ta dube dube a falon amma bai ga komai ba. Sa’annan falon ma ba kowa duk tarin abokanan Alhaji da ke zama a babban falo babu alamarsu. Bai ga wadanda ake ce suna kulawa da shi ba. Wai meke faruwa ne?

    Karasawa dakin mahaifinsa da yayi da tura kofar shi ya sa ya ji wani amai ya taso masa. Wani hamami ke fitowa ba kuma daga kowa ba sai daga Iliyasou Tillaberi.

    Da sauri ya karasa cikin mamaki yana taba baban nasa sai a lokacin ya lura kamar bacci ne ya fara daukan sa, an canja masa kaya zuwa jallabiya sai dai dakin idan ban da doyi ba abunda yake.

    A fusace ya fice ya tarar da Hajiya Hadiza ta dauki wani yankakken tufa ta kai bakinta. Idonsa ya rine yayi ja saboda bacin ran ganin halin ko in kular da aka bar mahaifinsa ya ce

    ” Mummy menene haka wai? Ashe haka jikin abbanmu ya tsananta shi ne ba a kira ni ba? Ga dakin duk wari ba a gyara ba amma ba shi abinci ya ci kuwa? Ina masu aikin ne wai..in dauke su aikin gida su tsaya suna min sakarci! To yau kowa zai bar aiki tunda ba gidan ubansa ba ne! “

    Ya fara kwala musu kira cikin bala’i. Ta kalle shi a lalace ta ce

    ” Duka na ka zo kayi kenen? Tun yaushe ake tsaye akansa? Ko kuwa don ba shi da lafiya sai kowa ba zai yi uzurinsa ba. Ita khulsomou da jiyyarsa ta isheta ta zo ta watsar shi anan wa yace tayi ba daidai ba? Tun da ya zo shekaran jiya ake hidima da shi, amma fa wari daki bazai daina ba don abun daga jikinsa ne. Wa zai jura?”

    Kawai sai ya rasa me zai ce mata. Mahaifinsa yana da tarin laifuffuka akansa amma ba zai taba barinsa a haka ba. Wucewa yayi ya koma dakin a fusace. Yana jin takunta a bayansa bai kula ba.

    Shirgin dakin ya fara watsowa waje. A lokacin ga lura mahaifin nasa ya tashi. Kokari yake yayi magana amma bakinsa kamar ya karkace. Abunda ya sa ya rude kenen. Yana masifa yana bala’i.

    ” mutum marar lafiya kamar wannan, a bar shi a gida. Sai ka ce marar gata!”

    Ya dunga sirfawa yan aikin nan balai suna kwashe kaya. Yana cewa duk yau zai kore su daga aiki. Mafi yawan fadan da mahifiyarsa yake amma kuma ba zai iya fitowa ga da ga ya fadi hakan ba.

    Ya kama laluben waya zai yi magana da mai kula masa da harkar shige da fice kasashen waje. So yake a gobe su bar kasar ya kai shi asibiti.

    Kwala kiran da uwar take masa ne ya katse shi. Kiri kiri ta kasa shigowa dakin wai wari ya isheta. Ya fito ta ce da shi

    ” Kai kar ka soma daukansa ka fita da shi. Acan ma haka khulsumou ta ce ya ki, shi ne ta kawo shi ta watsar anan. Wani malami aka kirawo ya ce kuma ciwonsa ba na asibiti ba ne. Sihiri ne ya dawo masa! An masa wanka ya fi sau bakwai. Amman wallahi ya ce ba zai daina wari ba!”

    Wani abu ne ya sa gabansa ya fadi dam! Jikinsa yai matukar sanyi. Ya ce

    ” To yanzu ya za a yi?”

    Ta ce

    ” Na sa a yiwa wani malami magana ya fara kawo masa rubutu ya sha. Amma fa yace babu wani abu da zai yi tasiri sai ya nemi yafiyar wadanda ya zalunta. To ka ji yanda ake ciki”

    Jikin Almustapha ya kara sanyi. Babbar magana ce aka baro kuma bai san ta inda zai liqe ta ba. Kawai sai ya koma dakin mahaifin nasa. Duk warin da jikin uban ke yi ya karasa ya kama hannunsa. Zafi ya ji rau! Ya ce da shi

    ” sannu Abba! Zan fita na siyo maka magani. Allah ya kara lafiya”

    Ya dago ya kalli Almustapha. Wani irin huci jikin sa ke yi kamar ana dana masa wuta. Ji yake kamar ana jan sa! So yake ya ce masa kada ya wahal da kan sa ya siyo magani amma ya gagara. So yake ya gaya masa irin tafasar da jikinsa ke masa da mafarkan da yake yi da Ahmadou a kullu yaumin! Ko dai ya fadawa Almustapha sirrinsa ko zai samu sassauci?

    Da Almustapha ya ga yayi bakam sai ya zata ko bacci yake so ya koma. Sai ya fita yana kiran wani abokinsa likita da ya rubuta masa wasu ‘yan pain reliever haka ya sai wa uban. Daga nan ya fice daga gidan.

    Fitarsa ke da wuya Rukky ta kira shi da ya biya ya dauke ta a wajen wani atm akan maiduguri road kan cewar bata fito da mota ba. Da ya dauketa ne ya tuna akwai wani wajen siyar da magani akan titin. Suka shiga ya siyo suka wuce. Anan ne yar modu da hindatu suka gan su.

    Ko daya bar gurin gida ya mayar da Rukky. Ta kalle shi cike da damuwa ta ce

    ” kamar dai wani abu na damunka ko?”

    A hankali ya nisa ya ce

    ” Wallahi mahaifina ne ba shi da lafiya”

    Yanayin fuskarsa ya nuna tarin damuwa abinda ya sa mata damuwa kenen. Wannan ne karo da farko da ta fara jin yayi magana akan wani nasa. Sai ta ji kamar ta ce za ta bi shi su duba shi. Amma ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne. Tayi masa fatan samun sauki ya amsa mata da cewar zai dawo komin dare akwai maganar da zasu tattauna.

    Da fitarsa ya koma gida ya tarda shi ya kara farkawa da alama dai baccin ba wani samuwa yake a gareshi ba. Ya ballo magunguna da ruwa a kofi ya tallafe shi zai ba shi amma sai ya ki.

    Illiyasou Tillaberi ya kurawa Almustapha ido yana ta kakarin magana. Shi ma Almustapha yayi tsai yana kallon bakinsa so yake ya gane me yake son cewa. Sai daga baya ya gane

    ” Ni…ni..ni…nik kashe Ahmadou!!”

    ********************************

    Luba ce tayi sakaka da baki tana kallon Hindu da ‘yar Modu da suke labarta mata wani labari mai kama da alamara. Bayan sun gama rantse rantsensu kawai sai ta fashe da dariya ta ce

    “Wai yau April ne? Har an fara april fool? Kawai dan ku samu abun fada akaina za ku ce Rukky ce ta kwace Almustapha? Ita Rukky in banda ranar da na kai ta wajensa ma yaushe ta san shi? Nawa Rukkyn take yarinyar da ki maganar arziki bata cika ba? Haba Hindatu idan yar modu yayi hakan dan ya ci kudina har da ke? Kin manta yanda muke da Rukky har za ki ci amanarta haka? Mu fa aminan juna ne!”

    Har cikin zuciyar Luba da gaske take domin kuwa tana kaunar Rukky da Hi ndu don a shekarun nan su kadai zata gani ta kira yanuwa. Tare suke fadi tashinsu a bariki kuma suke rufawa junansu asiri. Yanzu a zo daga sama a ce wai Rukky maciya amana ce ta yarda ai da sake. Sai ta ji Hindu ta fara fice mata a rai a ganinta kamar tana so ta yiwa Rukky cin dunduniya ne don wata manufa tata. Kai duniya ba gaskiya!

    Yar modu ne ya kama baki cike da mamaki sa’annan ya aunowa Luba dakuwa ya ce

    ” Ka ji ‘yar tselan uwa! Ana makadi ya fada ruwa kina ganga ta jiqe! Kanwar uwaki take Rukkyn? Allah ya sa kashin awaki kuke, kuna dirowa kawa rabewa za kuyi! Wannan da a mutanen farko kika zo billahillazi ba kya karbi shahada ba! Daga ganinki an ga su Abu jahal sarakan taurin kai! To ko ki yarda ko kada ki yarda sukari ita ce ta miki kwacen saurayi. Ta kwace Al mustapha. Ra’ayul aini muka gan su. Yadda na gan su Allah sa na ga annabi!”

    Luba ce ta kara kallonsa a sakarce ta ce

    ” ka ga annabi ko ka ga walakiri? Kayi abinda za ka ga annabin ne?”

    Ya ce

    ” Au au ka ga mutanen quraishi! Masu dangantakar jini da annabi! Ai abun rabo ne! To bari na labarta miki ko baquraishiya ce ke, idan ba ki shuka abun arziki ba, ke ba ki tuba ba, to ke da ganin annabi haihata haihata. Alquran sai dai ki ga gyatuminki! Ehe! Na dai gaya miki”

    Hindu ce ta kwantar da tarzomar ta ce

    ” look guys wannan fa ba abun musu ba ne. Ke luba tunda baki yarda ba sai ki shirya ki je gidan Rukky da dare. Jikina ya bani za ki same shi a gidan. Sai ki shiga ki ganewa idonki. Ai kyaun karya hallara!”

    Maganar Hindu ta sanya jikin luba sanyi. Sai ya zamana ta fara raba daya biyu. Ko dai? Don ta ga yanda suka hakikance to amma idan ta tuno fuskar Rukky sai ta ga kamar ba zata aikata ba.

    Anan dai aka bar zancen cewa da dare za ta je zuwan bazata. Luba ta cigaba da waswasi a ranta.

    *********************************

    Da daddare kamar yanda Al mustapha ya alkarwanta gidan Rukky ya wuce. Gabadaya ya kasa sukuni, maganganun mahaifinsa ne suke dawo masa. Ya san yayi zargin hakan amma gaskiya ya so a ce ba hakan ba ne.

    Wai ina zasu da hakki ne? Sai ya ji komai na kamfanin ya fara fice masa a kai. Tun ba a je koina ba mutane sun fara gudun mahaifinsa saboda wari hatta momynsa ya ga halayyar data fara nunawa.

    To yanzu menene abun yi? An ce sai ya nemi gafara to a ina zai nemi gafarar? Neman yarinya ya zama balai to amma yana ga lokaci yayi da zai fara sanarwa a gidajen radio. To amma ba hoto! Ba fasaltawar kamanni. Ga abubuwan siyasa da me zai ji ne wai??

    Maganar Rukky ce ta katse masa hankali ta ce

    ” Almustapha za ka iya taimakona ka kwatarmin ‘yancina?”

    Ya tsaya yana kallonta a tsanake so yake ya gane inda maganar ta dosa. Ya san ba mai son tambayoyi ba ce yana tambayarta zancen zai watse. Sai yayi kasaqe. Ta cigaba da cewa

    ” so nake kayi fito da fito da makiyana!Ga nunawa duniya kai masoyina ne! “

    Abu daya ne ya fado masa a rai..Luba! Sai yake gani kamar ya gane inda zancen Rukkyn ya dosa. Don haka sai yayi murmushi ya ce

    ” Baki da damuwa. Zan nunawa duniya ni masoyinki ne!”

    Ranta ta ji yayi fes! A take ya wurgo mata wata tambaya a karo na biyu

    ” Ya aka yi kika fada karuwanci?”

    Tsira masa ido tayi tana masa kallon tar. Tun bayan momodou bata taba jin wani a zuciyarta kamar Al mustapha ba wai me ya sa? Ta cigaba da gayawa zuciyarta cewa karuwa fa so ba nata ba ne amma ta kasa hana kan ta! Sai ta ji kamar tana so ta gaya masa ko ita wacece.

    ” Bam! Bam! Bam!”

    Karan bugun kofar da ya katse musu kallon juna kenen. Ya kalle ta a mamakince ya ce

    ” wani irin bugu ne haka? Ko maigadin dana aika ne?”

    Bata ba shi amsa ba ya karasa bakin kofar ya bude.

    Luba ce a tsaye sanye da wani wando tri kwata da riga marar hannu. Komai da ke jikinta baki ne kuma ya kama ta tsam! Da dare ne amma sai ta dauki wani bakin gilas ta kwama. Aka tsaya ana kallon kallo tsakaninta da Almustapha!

    Gilas din ta kwabe tana dubansa a tsanake idonta ya kada yayi jazir na alamar ta sha wani abu. Bata ce da shi kazil ba ta wuce ta karasa cikin falon inda Ruky ta ke a kishingide. Ta dago suka hada ido karaf! Gaban Rukky ya bada dam!

    To amma da yake ita ma ta goge a bariki maimakon ta nuna rudewa kawai sai ta koma ta kishingida tana raunar cingam kas kas. Sai dai ayi wacce za a yi! Almustapha ba ta ga mai raba ta da shi ba!

    Luba ta bi Rukky da kallo a tsanake cike da tsannanin mamakin da bata taba ji ba tunda uwarta ta kawo ta duniya! Ta sha cin amanar mutane amma ko da wasa ba a taba gwada cin amanarta irin haka ba sai yau! A yau din kuma wai Rukky! Yarinya karama da a gabanta ta shigo bariki! Lallai yau ake yin ta!

    Luba ta fara tafa hannayenta alamar jinjina ta ce

    ” lallai na baku award na manyan maciya amana na wannan zamani! Ashe batun da ake gayamin gaskiya ne? Almustapha ni ka yada ka dau aminiyata Rukky? Rukky ni kika yiwa zamba cikin aminci kika kwace Almustapha. Ku ka hada kai ku ka zambace ni!”

    Ya daka mata tsawa ya ce

    ” Who the hell do you think you are? Ai ni a rayuwata ke ba komai ba ce! Ni ina da zabi akan irin yarinyar da nake so kuma ke ba irinta ba ce! Ni Rukky ita raayina kuma ita na zaba. Dan haka get the hell out of this house!!”

    Luba ji tayi kanta na juyawa saboda tsabar yadda maganganunsa suka tarwatsa mata zuciya. Ita Luba da ta cika mace gaba da baya ita ake yabantawa kan wata aba Rukky? Wata irin tsana ce ta mamaye ta.

    Ta juya tana kallon Rukky wacce ke karkada kafa na nuna alamun ta ci gari. Ta yi murmushin takaici ranta na raya mata sun tafka kuskure ta ce

    ” Ba ku ji gabanku ya fadi ba! Ba ku ji shakku zama abokanan hamayyata ba! Rukky ba ki ji kamar kin shiga ukun ki ba? Da lokacin da kika fara son Almustapha kin gayawa zuciyarki ba a wasa abakin wuta. Domin idan aka fada mutuwa ake!!! Da sannu zan nuna muku wacece Lubabatu! Da sannu zan saku da na sani. Watarana idan kuka ga wani zai ci amanata da gudu zaku hana shi domin kuwa bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne!”

    “Get out!” Abunda ya ce da ita kenen yana nuna hanyar waje. Ita kuwa Rukky ta kasa cewa kanzil! Cikinta fargaba ne taf! Dan ta san waccece Luba.

    Luban ce ta kalle shi a tsanake. Ta mayar da gilas din ta ta nuna shi da danyatsa

    ” Ashe kai wawa ne! Ina ganinka kamar mai wayo ashe sakarai ne!! Wa ke fuskantar kura gaba da gaba? Da sannu za ka manta cewa kai ne! Ke kuma…!

    Ai ba tai wata wata ba ta daga hannu ta shararawa Rukky wani mahaukacin mari ji kake taaaaas!

    Ai bata ajiye hannu ba Rukkyn ta hankadata kan wani teburin glass na gefe ji ka ke tartatsaaaaa!

    Ya yanki Luba a hannu yana digar jini. Ta dauki bangare daya na gilashin ta wurgi Rukky da shi. Ya yanketa a kuncinta na dama ya daki bango ya tarwatse!

    Ganin idan ya kalle su za su iya hallaka junansu kawai sai ya hankada Luba waje ya kulle kofa. Tayi buge bugenta da zage zage da mugayen alkaba’i ta wuce.

    Ya dawo ya tarar da Rukky na sharar hawaye ya fara lallashinta da irin matakan da zai dauka akan lubar. Ta ce da shi

    ” Ba ka gane dalilin kuka na ba! Raba ni za tayi da kai! Luba ba zata iya jurar ganinka da wata ba”

    Nan ya gaya mata maganganun kwantar da hankali da cewar da safe zai sa yan sanda su mata gargadi, a yi musu tsakani. A haka aka kwana.

    Ko da ya tashi da safe nan ma gajiyar ce turum a kan sa. Kan sa ya dau caji ga shi ana jiransa a ofis game da wani mitin mai muhimmanci da za suyi. A haka ya bar Rukky da alkawarin zai dawo.

    Yana tsaye a ofis ne da misalin karfe biyun rana sun yi meeting sun fito. Ya sa sakatariyarsa ta hada masa shayi ta kawo masa. Rabonsa da cin abinci ya manta. Tunaninsa bai wuce ya gama da ofis ba ya garzaya ya ga jikin mahaifinsa ba.

    A lokacin ne wani daga cikin yan siyasarsu ya kira shi kan cewa ya kamata su fita kamfen wata karamar hukuma. Domin kuwa an yi ittifaki cewar su na da magoya baya dayawa a yankin.

    Sakatariyar ta sa ce ta leko da bayanin wai wata na son ganinsa. Ransa ya fara baci, ya san ba zai wuce luba ba. Wato haukarta har ta kai ta zo masa ofis ta ce za tayi masa tijara? Ta san ko shi wanene kuwa? Kamar dai ya kamata ya nuna mata madafan ikonsa! Ya cewa sakatariyar ya ce ta shigo zai ga iya gudun ruwanta.

    Ya juya bayansa yana waya so yake suyi sallama. Daga nan ya ji da wannan yarinyar , karamar kilaki! Ya ji shigowarta amma bai juya ba suka yi sallama a waya. Ya juyo fuskarsa a daure tam! So yake yayi mata gargadi na karshe! Babu ita babu Rukkyn sa. To amma me?

    Sai ya tsaya cak!!

    Idanunsa ya fara gano masa wata halitta daban.
    Doguwa ce sambal mai dauke da garun jiki. Tana sanye da wata bakar riga a jikinta da bata kara mata kyau ko rashin kyau ba. Fuskarta fayau ba alamun nuna kwalliya. Kitso ne irin na karin gashin doki a kanta siri siri ta daure.

    Suka tsirawa juna ido yana tuno abubuwa da dama! CACA!!

    Wani murmushi ta saki mai ma’anoni daban daban. Ta ce

    ” Hello Al Mustapha”

    Ya hadiye wani abu makwat! A makgwaronsa. Sai ya ji gabansa na faduwa, kawai ya san ba alheri ba ne.

    Ya ce

    ” Hello REBECCA…… “

    Sai ta tako a hankali har zuwa inda yake. Kawai sai ta saka hannu ta rungume shi. Ta zo daidai saitin kunnensa ta ce

    ” Our….. baby ……..is home!!!”

    Wasu sirrikan basu boyuwa

    Wasu sirrikan naso suke, suyi rassa su tarwatsa mai su!

    Irin haka ce ta faru da Almustapha Iliyasou Tillaberi

    Kun ji silar bala’in da ya janyo za a rasa rayuka…..

    Za a sake bankada sirri….

    Za a qarke a gidan yari….

    Haka yanayin tafiyar yake, wasu duk yanda aka so ba zasu taba kai labari ba!!!

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!