Duniya ta – Chapter Sixteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
” Ya ya aka yi ki ka fada karuwanci?”
Tambayar da Almustapha ya wullo wa Rukky kenen a bazata. Tana rike da wani donut a hannunta ta sa baki ta gatsa kenen sai ta ji tambayar, tayi sauri ta hadiye tana mai kallon inda ta gatsa. Ba ta ba shi amsa ba ta ce
” A ina ka sayi donut din nan? Dadin ba magana!”
Karasowa yayi yana daura agogon hannunsa ya zauna a daidai inda take zaune kan 2 sitter. Ya kai bakinsa inda ta gatsa ya ci ya ce
” A donutfairy “
Ta ce
” Me ke nan?”
Ya kalle ta cikin mamaki ya ce
” Ba ki san donut na donutfairy ba? Kuma kina kano? Ke kuwa wata irin ‘yar kauye ce? Ai duk wanda ke kano bai ci donut na donutfairy ba to kamar ya zo kano ne bai ga mota ba!”
Tayi ‘yar karamar dariya. Ya sa hannu a cikin kwalin ya dauko wani mai kamar an dura abu a ciki ya kai mata baki ta gutsura.
Ta lumshe idonta tana taunawa kana ta bude suka hada ido suka kwashe da dariya. Ta ce
” Wallahi sai na ji ni kamar ba anan duniyar nake ba don dadi”
Ya bude wayarsa ya nuna mata ya ce
“Kin ga shafinsu a instagram, order ake. Ki zama good girl sai a sake miki order. Ko ba haka ba?”
Ta gyada kai tana dariya dama can ba mai yawan magana ba ce. Ya kara maida hankalinsa yace
“Ina tambayarki baki bani amsa ba.”
Ta gane me yake nufi fara’ar fuskarta ta ragu ta ce
” Kaddara”
Ya ce
” Ba kya tunanin wataran ki daina”
Ta kalle shi da alama ranta ya fara baci ta ce
” Na daina na je ina?”
Da ya lura kamar ba ta so sai yayi shiru. Sun fi wata daya suna boyayyiyar soyayyarsu ba tare da kowa ya sani ba. Kuma a wannan lokacin ne ya ji kamar ba zai iya rabuwa da ita ba.
Wasu irin abubuwa yake ji game da yarinyar duk da dai ba zai iya fadawa kowa ba don a matsayinsa ba girmansa ba ne ya ce ya fada son karuwa.
To amma sai yayi tunanin kawai bari ya aje ta suyi zaman kai. Amma da sharadin ba zata kara kula wani manemi ba. Kuma ta amince.
Abu daya ke hada shi da ita wannan shaye shayen nata. Ranar da ya fara ganinta tana zukar wiwi ya tarar da wasu kwalaben syrup a gidan tsananin mamaki ne ya kama shi. Ashe duk yanda yake tunanin yarinyar ta wuce nan? Ashe yarinyar ba karamar lalacewa tayi ba. Ga ta nan a fuska kamar tagari a zuciya ko dafi ce!
Ya kalle ta ya ce
” Ke kuma me ke birge ki a shaye shaye? Duk wanda ya ba ki shawarar kiyi makiyinki ne”
Ta dube shi da kallon mamaki. Idan Al Mustapha na magana wani sai ya zaci shi mumini ne! Ga laifi akansa buhu guda ya take yana hangen na wani. Ta ce
” Kai me ya kai ka neman mata? Shi ma wannan halin arziki ne? Da ni da kai mun san muna aikata haram amma har yanzu mun daina?”
Ya kalle ta kamar maganar bata bata masa rai ba ya ce
” To ai dama a wannan kalar zunubin kadai kika tsaya shi ne har da tsallakawa shan kwaya! Ki lalace ki balbalce kenen”
Ta kalle shi kamar hankalinta baya jikinta ta ce
” Dama a lala..ce na nake! Idan na bal..balce wa zai yi cigiyata! Kar ka sake ka damu da ni ko ka ce zaka canjani, ra..yu..wata ba irin taka ba..ce! Ba..za ka gane ba!”
Kallonta kawai yake. Bai kamata ya damu ba, karuwar titi ce. Amma wani abun mamakin sai ya ji ya damu!
Duk wannan shagalin da ake yi Luba bata sani ba, ba ta kuma shinshino ba. Daga baya ma sai ya siya mata wani karamin gida. Da yake shedan ya gama yi masa fitsari a kai ya zuba mata komai na abubuwan more rayuwa ta bar zaman gidan Hajiya Kububuwa.
Duk sanda ta rayo masa sai ya kwashi jiki ya tafi gidan da daddare don ba ya so a gane ko shi waye. Wani lokacin kuma sai ya dauketa ya bar gari da ita kamar matarsa ta aure amma fa babu tunanin auren a ran sa.
Luba ganin kowa ya watse ita ma sai ta kama gidan kan ta. Sai ya zamana dai gidan Hajiyar shi ne wajen haduwa ai zaman hira ko warware matsala idan ta taso.
Luba tana nan tana fadi tashin yanda zata karkato hankalin Almustapha amma abu ya ci tura. Saboda tsabar munafunci wani abun da Rukky za ayi a gama amma ko da wasa bata taba nuna musu tana tare da Almustapha ba.
Rukky ta mato akan Almustapha har take ji zata iya fito na fito da duk wanda ya ke tunanin raba su. Da fari tana tsoron fitinar Luba kar balli ya tashi ta jawo musu masifa. Daga baya ma sai ta daina, a ganinta ai bariki ba zaman aure ba ne balle wani ya tada jijiyar wuya.
Ai Almustapha tamkar allura ne a cikin ruwa mai rabo ke da shi. Ba kuma don Luba kadai aka halicce shi ba! To don me yasa zata takura kan ta? Kawai sai ta mike kafa ba tare da tunanin me zai je ya dawo ba take soyayya da masoyinta.
A hankali ta gane ko shi waye da irin karfinsa a kasa. Sai ta kudurce a ranta za ta tayi amfani da hakan ta cimma wata manufa tata.
Me zai hana tayi amfani da wannan damar ta sa ya nemo mata Iliyasou Tillaberi , ta sa ya kwato mata dukiyarta. Ta ga ya girmama a kasa ta san karfinsa ya isa yayi fito na fito da makiyanta. Makiyan da suka jefa a wannan rayuwar.
Zata kara shiga jikinsa ta ayyana a ranta. Ta ga shi ma ta shiga ransa kamar yanda ya shiga ranta. Da sannu karshen wahalarta ta zo, da sannu zata cimma buri
Abinda Rukky bata sani ba shi ne
Burirrika kamar mayaka suke a fagen daga. Wasu su kan kai labari, wasu duk yanda aka so ba zasu taba kai labari ba!
*********************************
” Kwarankwatsa dubu na rantse da kabarin kishiyar uwata na ga saurayinki da kika mato akan nan nasa da wata a mota. Ban dai ga fuskarta ba amma Alquran ziza ce..daga gefe kamar barbarar yanyawa! Ni kuwa kin san ina dan ganin idonsa a la mirage dalilin kenen ma da na gane shi. To kin ji yadda aka yi”
Wani abu ya taso ya soki luba a zuci jin maganar ‘yar modu. Wai wannan wani irin hatsabibin mutum ne? Ana banka masa magani amma ko gezau. Ko wani malaminta da taje gurinsa sheran jiya cewa yayi nan da kwana biyu zai zo da kafafunsa. Sai ta ke kuma jin wannan bahagon labarin!
Wannan wata yarinya ce haka? Lallai kuwa ta tarowa kan ta aradu da ka! Ta kusanci Almustaphanta? Abunda ya fi komai soyuwa a ranta shin ita kuwa tana da makiyiya irin wannan yarinya. Ta ma san ita ta dauke masa hankali yanzu haka ma asiri ta masa. Malamin ziza ya sha gaya mata wai har yanzu duhun da ke kan sa bai yaye ba, wannan wata irin masifa ce!
Ga shi nan tana ji tana gani ta kasa kula kowa son sa ya zame ma ta bala’i.
Da sannu zata nemo ta tayi mata gargadi mai tsanani akan ta rabu da masoyinta. Ita ai tauraruwa ce mai wutsiya ganinta babu alheri!
Ta kalli ‘yar Modu ta ce
” wai a ina ka gan su ma? Ni fa bana son labarin kanzon kurege. Mutumin da aka ce duhu ya rufe. Ba macen ma
da zai iya tunkara”
” Yo Allah na tuba Luba duhun da ba duhun kabari ba! Yo ai duhun kabari ne ba zai yaye ba! In miki karya na ce na yi wa wa? Ko da yake je ki Allah zai hada ki da saddiqu sarkin gaskiya ya labarta miki yadda aka yi! Ni din nan dai ai turmin tsakar gida ce sha luguden mahassada! Haka nake ruwan jakara idan ba a sha ni a kauye ba a sha ni a birni!”
Ya mike ya dauki ‘yar posar sa zai wuce. Dama ziyara ya kawo mata don duk cikin matan nan uku babu wacce ke shiri da Yar modu irin Luba. Sai su kashe su rufe sauran ma ba su sani ba.
Ta tashi ta janyo shi tana cewa
” Haba tawan. Ke daga wasa. Duk garin nan da bazar wa nake rawa idan ba taki ba?”
Da haka yar modu ya dawo ya ce
” Ai ca nike iya shegen naku na karuwai zaki min. In cancareki in cashe!ehe! Na san halinku sarai kaza ci ki goge bakinki! Ai muku rana ku yiwa mutum duhun dare. Kin ganni nan, ta kwarankwatsa dubu iya shege na ko shedan ya shafamin lafiya.”
Nan dai ta rarrashe shi ta ba shi hakuri ya ce zai cigaba da bincika mata amma fa a yawan kudin da ya ji a tudun aljihunsa. Bai bar gidan ba sai da Luba ta ba shi zunzurutun kudi har nera dubu dari biyu.
Wannan kenen.
***********************************
Abubuwan siyasa suka cigaba da karatowa, Almustapha ba shi da lokacin kan shi. Sun tsayar da dan takara komai yana tafiya yanda ake so.
Masu take masa baya suka cigaba da nuna masa cewa yanzu ne fa ya kamata ya gina sunansa a duniya. Don Watan wataran shi za a tsayar.
Idan ya gama kuciba kucibarsa ba ya qarkewa a koina sai a gidan abokiyar shashancinsa Rukky. Kallo daya yake yi mata ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa. Ko zai ma kan sa karya ya san son yarinyar yake shi mamakin kan sa yake. Sai ya fara tunanin ko Allah ya fara jarabtarsa ne akan irin yanmatan da ya lalata a rayuwarsa?
A lokacin ne ya tashi haikan akan cigiyar Rokaiyatou. Wani abu da yake kwana da shi yake tashi. A wani yammaci sun fito yawon shakatawa shi da Rukky wayarsa tayi kara. Ya duba ya daga sabon detective din sa ne. Sai ya ba shi bayani akan an samu cigaba game da neman yarinyar nan domin an samu wani gida da ta zauna a unguwar kawo.
Abinda ya sa Almustapha paka motarsa kenen a gefen titi don sauraren wannan bayani. Suka yi zai dauke shi a hanya su wuce. Sai bayan ya ajiye wayar ya juyo ya kalli Rukky. Ya gaya mata yana da wani babban uzuri da zai gabatar. Ta ce ya ajiyeta gidan kawarta Hasina ya wuce. Hakan kuwa aka yi.
Almustapha da mutumin suka kama hanya basu tsaya a koina ba sai unguwar Kawo gidan Baban Ali. Ba su sha wata wahala ba don gidan ba boyayye ba ne sai kuma suka yi sa’ar taradda mai gidan zaune akan benci a kofar gida.
Suka yi masa sallama ba tare da bata lokaci ba Almustapha ya masa bayanin kan sa da kuma abinda ya kawo shi. Kafin kace me sai kuka ya kecewa baban Ali. Ya kuma gaya musu labarin abinda ya faru da cewar a halin da ake ciki an neme ta an rasa.
Ai kafin su yi aune Almustapha ya cakumo wuyan baban Ali ya shaqe shi. Shi dama matsalarsa kenen bai iya zuciya ba. Cewa yake
” Yar uwar tawa..kanwar tawa kowanta ya mutu shi ne a karkashin idonka dan ka ya dirka mata ciki? Mahaukaci ne kai ? Kuma daga karshe ka ce min wai baka san inda take ba. To sai ka nemo ta! Da kai da dan ka yau kwa kwana a cell! Wallahi tallahi sai nayi sharia da ku! Sai an daure dan naka ko labarinsa ba zaka kara ji ba!”
Abun da ya janyo hankalin mutanen unguwa kenen suka kwaci baban Ali da kyar! Sai a nan wani makocin su yake masa bayanin ai dan nasa ma ya fi shekara biyu a daure sun je wani gida sata a kama su. Har yau bai fito ba.
Tsananin bacin rai ya sa Almustapha barin gurin ya fada mota. Kawai sai ya ji wata kwalla ta tarar masa a ido. Yarinya kankanuwa, marainiya da ciki a jikinta ta bace kamar batan tattabara? Wai yana raye wadannan abubuwan suke faruwa?
Shi ba yayi cigiya a gidan radio ba yana tsoron mahaifinsa. To ma ya ma san kamanninta ne? Yarinyar da ba zai iya tantance ta ba a cikin mata biyar.
Wani abu ya ji yana masa yawo a zuciyarsa ya rasa inda zai saka tausayin yarinyar a ransa. Yana ganin kamar da sakacinsa ma. Cewa yake
“Momodou ka yafe min…na gaza amma da sannu zan cimma buri!”
Haka suka bar harabar gurin detective din na lallashinsa da cewar zai kara iya kokarinsa. Ya sauke shi a hanya.
Da kyar ya biya ya dauki Rukky fuskarsa kamar hadari. Tana kallonsa ta san akwai matsala. Bata taba ganin hakan a tare da shi ba. Ta so ta ji me ke damunsa ya ce ” its personal”.
Ya ajiyeta a gidanta kawai ya wuce. Ta bi shi da kallon mamaki. Hankalinsa yana kan Rokaiyatou , ina zai gan ta?
Ba ayi sati biyu da faruwar hakan ba yana zaune a ofis din sa aiyuka sun cabe masa. Yanzu Almustapha ya lura cewa yana da mahassada sai yayi taka tsantsan. Yan adawa sun fara sako shi a gaba.
Amma yana ji a jikinsa jamiyyarsu ta DSP ita ke da nasara. Don ya bi suk wasu hanyoyin samun daukaka da nasara ya bude. Yana da mutane manya manya a sama yana da mutane a kasashen ketare masu fada a ji.
Yana zaune a ofis din ne ya ji kiran detective din sa ya ce ya shigo ya same shi a ofis. Detective sammani ya karaso. Almustapha ya ce su dan fita ta harabar balcony su sha iska sai ya gaya masa a yanzu halin da ake ciki ko ana samun cigaba.
Suna tsaye a gurin ne Almustapha ya ce
” Yaya batun yarinyar nan? Ka san fa ya kamata ka zage da aiki tukuru domin kuwa zan iya kashe ko nawa ne akan wannan binciken.”
Detective Sammani yayi gyaran murya ya ce
” Ai yallabai aikin ne yana da matukar wahala domin kuwa babu hoton wacce ake nema. Dadin dadawa nema ne muke yi a cikin sirri ka ce babu damar mu sanar a kafafen yada labarai. Hope dina ya ta’allaqa ne a gidan da muka je sai aka yi rashin sa’a nan ma babu labarinta”
Almustapha ya nisa. Kan sa ya daure. To ko zai fara cigiyar a gidan radio ne? Komai ta fanjama fanjam. Maganar detective sammani ta katse shi da ya ce
” A cikin satin nan ne ma da dan ji wata jita jita. Wai kamar an taba ganinta a wani gari da ke hanyar zinder”
Almustapha ya zaburo gabansa na dukan uku uku ya ce
” wani gari ne haka?”
Ya ba shi amsa da
” Matamaye”
Almustapha ya hade girar sama da kasa alamun zancen bai zauna masa ba ya ce
” Har mai zai kai ta wannan kauyen? Me take yi? “
Babu wani kwana kwana ya ce
” yanzu haka ba zai wuce karuwanci ba”
Wata irin zabura Almustapha yayi har sai da detective din ya tsorata. Sai ya ji da ma bai fada ba saboda ganin irin shakar da yayiwa mutumin nan rannan.
Wani irin daci ya ji ya mamaye masa zuciyarsa har bai san lokacin da ya nunawa detective din danyatsa ido jawur ya ce
” Yar uwar tawa zaka danganta da wannan mummunar kalmar? Kan ka daya kuwa?”
Ganin yadda ransa ya baci matuka ya sa detective sammani cewa
” Yallabai ina ga fa ba ita din bace. Al’amarin zai iya zama jita jita.”
Daga nan Almustapha bai kara cewa komai ba ya buga tsaki ya koma cikin ofis din detective sammani yayi ficewarsa yana mamakin irin wannan zafin rai.
Ko da ya dawo cikin ofis din ma sai da ya nemi robar ruwa ta swan madaidaiciya ya kwankwade, mamaki ya kama shi wai Rokaiyatou ake dangantawa da karuwanci! Karuwanci fa! Me aka yi aka yi wannan sana’a. A ce jinin Ahmadou Tillaberi ta kare a haka? Inaa karya ne!
Yanzu da a ce Momodou zai dawo duniya ya ga ya bar Rokaiyatou na karuwanci ai sai ya kashe shi! Ashe ma bai kai a ba shi amana ba! Ashe ma shi ba danuwa nagari ba ne!
Mutuwar Momodou na tsaya masa a rai shin akwai wanda ya kai shi jin ta kuwa? Ji yake kamar wani bangare na shi a cire an yar har yau ya kasa daidaituwa.
Idan ya tuna maganganun da suka tattauna saura bai fi kamar kwanaki kadan ya rasu ba sai tausayi ya lullube shi. Ya kan ce masa
” Ina kamnar ta tun tana zanin goyo. Bata da wanda ya hi ni bani da wanda ya hi ta”!
Matar danuwansa!
Allah ya cika burin momodou an daura..Allah bai yi za a zauna ba!
Rokaiyatou ashe burin naku da Momodou ba mai nisan zango ba ne?!
Abu daya yake gani kamar ya zame mi shi wajibi. Ya nemo yarinyar nan ya mata gata. Mahaifinsu shi ne silar komai ya kamata shi ya gyara.
Ina ma za a gan ta , da sai yayi mata gata irin na uba! Shi zai aurar da ita, sai ya nemi mutum kamili wanda zai rike amanarta! Idan haihuwa ta yi zai kula da yaron! Wa ya jawo? Ai su ne!
A irin wannan tunanin ne ya ji zuciyarsa tayi baki kirin har ta kai shi ga janyo durowar teburinsa ya zaro kwalin taba. Abunda ya dade bai yi ba. Dama bai cika sha ba sai idan yana cikin bacin rai.
Ya kyastawa kara daya lighter zai zuka kenen sai ya tuno maganganunsu da Rukky. Yanda yake nuna mata ba ya son zuke zuke. Sai ya kashe ya yar. Bacin rai ne kawai ya taru ya masa yawa.
Abunda ya assasa lamarin bai wuce kiran da Hajiya khulsomou tayi masa ba na zagin kare dangi dazu. Wai dan ta ya mutu ya hau kan dukiya ya danne. Abu daya yasa bai tanka mata ba, Momodou.
Sannan ya wayi gari da son siyan wasu kanfanunnuka da suke so su hade da nasu. Dukiya bata son sanya, rassa ake mata domin ta cigaba da yado tayi mamaya yanda ‘ya’ya da jikoki zasu ci moriyarta.
Bai tashi daga ofis sai da ya tabbatar ya gama maganar siyan kanfanunnkan nan. Abu daya ne ya katse, shi shigowar sako wayar shi. Daga Rukky ne. Ya karanta
” Hi….je suis amorex!” ( im in love!)
Ya gane sakonta domin yana jin faransanci sai ya ji kashi tamanin din kuncin zuciyarsa ya tafi! Me yasa yake jin haka game da yarinyar?
Dama tana jin faransanci?
To wai ‘yar ina ce ma?
Kamar lokaci yayi da zai san wacece ita!
Rashin sani…shi ya fi dare duhu
Ina ma ya san waccece
Ina ma ya sani …kafin lokaci ya kure
Ina ma ya sani…kafin lokaci yayi halinsa
Lokaci sakarai ne…yakan tafi da abinda ka ke so!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
