Duniya ta – Chapter Fifteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Rukky ta cigaba da bin Iliya bakanike da kallo. Ya mike ya zura hannunsa a cikin aljifansa na biri da wando shudaye. Fuskarsa kadaran kadahan.
Sai take jin kamar ta je ta ce ma sa
” Ka san irin abunda nake ji kuwa? Ka san kalar damuwar da ke zuciyata? Idan ban sha ba, ya zan yi na manta da damuwa ta?”
To amma sai jikinta yake bata Iliya bakanike ba zai bata gaskiya ba. Watakila ma ya bita da zagi ganin hakan kamar dabi’arsa ce.
To amma bata iya ce masa komai ba. Ta gabanta ya zo ya wuce yana mai daga mata hannu da cewar
” Hajiya barka da yamma”
Ya wuce abunsa. Ta bi shi da kallo. Lokaci daya a rayuwarta tayi tunanin dama ita ce Iliya bakanike, daga ganin shi ba shi da matsala irin tata. Dama wasu abubuwa ba su faru ba. Ta na jin kewar wani nata tana so a ce ga wani na ta ko za ta ji ita ma mutum ce kamar kowa.
Zuciyarta ta ji tana mata wani irin ciwo, sai ta mike. Lokacin kuka ya wuce, yanzu lokacin fuskantar rayuwa ne a yadda ta zo.
An gama service din motar ta karba ta hau kan titi. Ta danna wata wakar mutanen ethiopia tana bi tana gyada kai. A hankali damuwa na barin jikinta.
Wayarta ce tayi kara, ta rage volume din wakar ta dauka tana dariya ta ce
” Bashari..shegen sama! Ta samu kenen!”
Ya ce ya na dariya
” Ta samu Hajiya..ai ina gaya miki babban kifi ne ya samu”
**********************************
Luba ta ci gaba da danna wayarta a karo na barkatai amma ba ansa. Ta buga tsaki ta dubi Rukky da ke shafa Mai ta ce
” Kin san har yanzu baya daga wayata. Na je ofis din sa sakatariyar shi ta ce wai baya nan. Har fa gidan shi na je security din sa suka ce wai yayi tafiya. Mutumin da tabbas na san yana gari. Sukari wai a tunaninki menene dalilin wadannan abubuwa? Ana mushush!( na shiga rudu/ im confused)
Sai da Rukky ta ji gabanta ya fadi. Tun da suka je ofis din mutumin nan ta gagara daina tunaninsa. Abinda ya cigaba da sa ta a cikin damuwa wannan satin kenen. Ita bata ga dalilin da zai sa ta rike shi a rai ba. To wai dan me?
Sai dai ta kasa cire shi. Yana yi mata kamar wani wanda ta sani. Yana mata yanayi da wani amma ta kasa gane waye. Watakil cikin tarkacen samarinta ne amma wa? Da idonsu ya hadu sai ta gane ta ma san shi dole a wani guri watakil ko ya taba nemanta a baya. Ita fa ba za ma ta iya tuna samari nawa ta yi ba.
Amma bata gayawa Luba wannan tunani nata ba don ta san halinta. Yanzu cibi zai zama kari musamman akan wannan mutumin mai tauraro a goshi.
Rukky ta dauki jan bakinta tana shafawa ta ce
” Luba kin kira gayen nan kusan sau hamsin kenen..dalla rabu da gara. Ke me farin jini ma wuyarta yau ki baza turare ki fita Allah kadai ya san wanda zaki samo”
Wata muguwar harara ta dallawa Rukky ta ce
” Sukari yanzu na tabbatar baki da hankali. A tunaninki a duniya akwai kamar Al Mustapha? To a ina yake ina zan same shi? Wallahil azeem ko makwafinsa babu! Ki ga mutum kamar shi ya tsarawa kan sa rayuwa. Shi yasa nake so na mallake shi ni kadai..Almustapha nawa ne ni kadai. Kin san iya adadin kudin da nake kashewa akansa a jawo hankalin shi? Amma kina ga kamar ma ana ziga shi!”
Rukky tayi sakaka tana kallon Luba da mamaki. A hankali ta ce
” Luba wannan son zai haifa miki da mai ido kuwa? Mutum irin wannan ko baya bariki ai zai yi yanmata dayawa ballantana. Ki hutasshe da kan ki fa!”
Kafin Luba ta ansa Hindu ta shigo yawonta ya biyo da ita. Suka gaisa aka mayar mata da yadda aka yi. Tsaki tayi bayan ta dauko ruwa a fridge ta tsiyaya a kofi ta kurba ta ce
” Wai kawata yaushe kika koyi bakin naci ne? Gaskiya kin bari gayen nan ya shiga ran ki. Karuwa fa bata da hurumin so. Ki share kawai tunda kin kwashi abunda zaki kwasa”
Luba tayi narai narai da ido , kwalla ta taru tana neman zubo ma ta ta ce
” Hindu kin san kallar son da nake ma sa kuwa?”
Jikin Hindu yayi sanyi ganin halin da kawarta take ciki ta nisa ta ce
” To mu je wajen malamin nan mana. Wanda ziza ta kai mu farkon zuwanmu gidan nan”
Tuni Ruky ta zabura ta ce
” Gaskiya Hindu ba za mu je ba. Mutumin da ya ce za a rasa rai! Ni tun daga ranar nake tsoransa”
Wata dariya suka kwashe da ita. Suna cewa ta cika tsoro. Wai ai ko an je wajensa ko ba a je ba, mutuwa ai dole ce.
Kawai sai suka tashi suka fara shiri Rukky bata da yadda za tayi kar Luba ta ce bata damu da halin da take ciki ba. Don ta san ita ma ko ita ce Luban zata mata kamar haka.
A motar Hindu suka fita ta ce ita ce zata gane hanyan. Anan take musu korafin dan ta, ta ce zata gayawa malam ya rufe masa baki ya daina shiga al’amuranta.
Luba tayi tsaki ta ce
” Wannan dan dan yaron shi ne har zai firgita ki har sai kin sa an yi masa aiki hindu! Dan cikin naki!”
Nisawa Hindu tayi ta ce
” Kawata ba zaki gane ba”
Daga nan har suka isa gidan malamin. Kamar koyaushe akwai dogon layi haka suka jira har aka zo kan su. Suka shiga.
Wannan karin ma yana zaune akan kujerar da yake zama sanye da wani shudin yadi ya masa dinkin malum malum. Ya sakar musu murmushi da alama ya gane su. Aka gaisa irin na al’ada sannan Luba ta rattabo masa bayani.
Ya ce ta gaya masa sunan saurayin sannan ta gaya masa cikakken sunanta. Duk ta fada masa. Ya ce ta zabi lamba daga daya zuwa ashirin ta zaba. Malam ya fara bude littafi.
Sai da ya gama ya ce
” Kiranye a yanzu ba zai yiwu ba , al’amarin babu sa’a. Al’amarin akwai rikici. Al’amarin akwai rasa rai!”
Innalillahi wa inna ilairrajiun
Abinda Rukky ke fada kenen cikinta ya bada kululu. Sai da tace kar su zo yau ma ga shi ya ambaci rasa rai. Ji tayi gabadaya hankalinta ya tashi. Luba za ta jawo musu masifa.
Ita ma Luban hankalinta a tashe yake . Ta ce
” Malam me ya sa al’amarin ba sa’a? Dan Allah ranka ya dade ka taimakeni ka duba min zan iya kashe ko nawa ne. Ina son karin bayani. Dan zuciyata ta mato akan mutumin nan”
Malam yayi shiru. Ya bata wani carbi ya ce ta kama waje daya ta kama ya karbi carbin. Ya fara bude littafi
Sa’annan malam ya dago ya ce da ita
” Na ga mata guda biyu banda ke. Zuciyar shi tana ga guda daya. Daga nesa ta ke amma tana daf da ke!!”
Daga wannan malam bai kara cewa komai ba. Luba hankalinta ya kara tashi tana rokon taimakon malam. Ya ce da ita
” Ki dawo nan da sati daya watakila kafin nan zuciyarsa ta sassauto. Za muyi aiki akansa kar ki damu.”
Sai a nan hankalinta ya kwanta. Hindatu ta fadi bukatar ta. Suka aje masa makudan kudi suka tafi. A mota dai zancen ake ta jujjuyawa. Suna ta yiwa Rukky dariya wai ta tsorata bata karbi taimako ba. Ita dai bata ce komai ba.
Da suka koma gidan ma hirar ce dai har bashari ya kira Rukky wai ta shirya bakon nan na hanya. Sai ta ji kamar ta ce masa ta fasa bata jin dadin jikinta. Amma sai Hindu ta nuna mata ba a haka, ina lefin mai nemanka da arziki.
Da wannan Hindu ta taimaka mata ta shirya jikin wasu jajayen kaya. Ta gyara mata dogon gashinta. Ta kalleta a tsanake ta ce
” Lallai kin ci sunanki sukari…ba kiyi farin banza ba! Cancadi!”
Luba ita ma kwalliyar ts burgeta ta ce
” Wallahi sukari ba ki da wayo. Zuwanmu wajen malam ai da kin sani kin ce ya kama miki wannan sabon kamun tunda kuwa Bashari ya ce babban kifi ne! Ai da zafi zafi akan daki karfe!”
Ita ma Rukky anan ta ga rashin azancinta ta ce
” wallahi kuwa. Ai tsorata nayi shi yasa duk na rude”
Suka kwashe mata da dariya suna kiranta ” farar kura”. Wayarta ce tayi kara, bashari ne. Ta dauka ya ce mata mutumin yana bakin gate sannan kuma ta turo masa na shi kamashon. Suka yi dariya suka yi sallama. Ta fita kawayen nata suna ta mata fatan sa’a wai Allah sa ya dalle ta da mota.
A tsanake ta fita a bakin gate ta ga wata bakar mota ta san shi ne.Gilasan cikin motar masu duhuwa ne ba a ganin wanda ke ciki. A hankali ta bude ta shiga. Waya yake yana kallon gefen taga. Ta zauna har ya karasa kana ya juyo ya kalleta.
Sai a lokacin ta gane ko wanene. Tayi sauri ta zabura zata bude kofa tana cewa
” Yi hakuri kuskure ne. Luban tana ciki bari na kira maka ita. Na zata bako na ne ya zo”
Kafin ta bude ya sa central lock ya figi motar kamar zai tashi sama. Ita kuma ta fara bin sa da kallon mamaki.
Har suka yi tafiya mai nisa bai ce mata kala ba ita kuma ta zira masa ido tana tunanin adadin rashin hankalinsa.
Ita bakuwa ce a iskanci? Ta gane kanta ya dawo kenen. Ta tuno halin da ta bar kawarta a gida akan son sa, shi ne shi kuma ya zagayo nan. Namiji kenen kanin ajali! Idan bai kashe ka ba ya sa ka jinya! Zai kare yawonsa ya dawo da ita. Inaa..ba zata sabu ba bindiga a ruwa!
Sai a lokacin ta lura hanyar fita kano yake bi kuma ya kasa ce mata komai. Ta ce
” Ka ga malam. Ba da ni za a yi wannan cin amanar ba. Ka Karaci gudun ka ka nemi guri ka ajiyeni”
Wannan karin ma banza yayi mata sai ma ya danna wani selection din wakoki da ya nacewa na Oumou sangare. Yana son Oumou sangare. Sautin wakarta Ah Ndiya ya fara fita daga manyan sifikun motar.
Abinda ya sa jikin Rukky yayi sanyi kenen. Ta san Oumou sangare yar mutanen Mali. Lokacin da take Niamey wakoki biyu take ji na sogha Niger da Oumou. Dan har tana jin yaren ‘yan Mali sama sama. Tana son ta saboda irin maganganun da take fada a wakokinta na ban tausayi. Don har Momodou na yawan ce mata idan Oumou za tayi show watarana dai zai kai ta kowa ya huta. Sai ta ji kamar ya tono mata miki!
Tayi shiru ta runtse idanunta. Wani abu na mata ciwo ta rasa ko menene. Maganar Almustapha ce ta katse mata tunani
” Ke ma kina son Oumou Sangere ko?”
Ta bude idonta amma bata ansa shi ba. Wani kullutu take ji na bacin ran sa. Zai jawo mata masifa da Luba. Ita ta san kowacece kawarta.
Ya cigaba ba tare da ya kula da shirunta ba
” Na kan ce a Africa babu mawakiya kamar Oumou. Tun tana shekara 5 take waka. Wahalhalun da ta sha a rayuwarta masu yawa ne. Ita kan ta a wakokinta tana wa kanta take da sangare kono a cikin yaren mali. Wato kamar wata tsuntsuwa kenen mai waka”
Rukky ta cigaba da kallon mutumin. Kamar yana mata kwarjini. A halinta na rashin mutunci ta kasa dura masa zagi. Yana yi mata yanayi da kamar ta san shi. A hankali ta ce
“Kono wassoulou, tsuntsuwa mai waka ta wassoulou!”
Dariya yayi. Ya ce
” Haba ni na san abu ne mawuyaci mutum ya kasa sanin oumou”!
Murmushi tayi. Abinda ita kan ta ya bata mamaki. Ita da take tunanin yanda zata masa rashin mutunci sai ga shi ta bige da masa murmushi! Yau rana daya sai ta ji ta kamar ba karuwa ba! Farin cikin daga zuciyarta ne!
Ya ga murmushin ya mayar mata. Sai yake ji kamar ba yadda ya tsara ba, daga zuciyarsa ne. A lokacin Oumou ta fara wata waka djorelen. Ya kalle ta a tsanake ya ce
“Djorolen kônô mi kan toula…
Tsuntsuwa mai waka, mai cike da damuwa tana kuka a daji..kin sa da wa take? Da kan ta take! Kina jin yaren mutanen mali?”
Bata ansa shi ba don tana tsoron ansar da zata ba shi. Ba ta so ta ce tana ji ya zamana ta bada wata kofa da za a san ko ita wacece. Sai tayi shiru kamar mai tunani
Ya yi dariya ya ce
” kwantar da hankalinki na san ke ba ‘yar Mali ba ce..ba kiyi kamanceceniya da su ba!”
Murmushi ne ya kuma subuce mata . Komai mutumin yayi birgeta yake. Abinda ya sa gabanta ya buga dam! Ta san tana wasa da wuta. To amma me yasa ta kasa hana kanta bayan ta san wutar akwai zafi?
A daidai wani lokaci sun iso wani tafkeken guri yana mata kama da gidan gona. Wajewajen gari ne bata taba zuwa irin gurin ba. Sai a lokacin ya juya ya kara kallonta ya ce
” Shall we?”
Ta ce da shi
” ka san abunda muke yi kuwa? Ka san wacece Luba kuwa? Bari na baka shawara idan za ka nemi abokin gaba ka guji Luba domin bata da shamaki. Kuma kai ma ka san tana son ka. Ya za ta ji idan ta ji mun ci amanarta?”
Dariya ma abun ya ba shi. Dama karuwa na da amana ne? Ka ji ta kamar mutuniyar kirki. Ba kudi suka fito nema ba? To ta tara ta samu!
Ya sa hannu akan sarkarta mai alamar harafin “R” ya dan juya ta ya kalle ta a cikin ido ya ce
” Tauraruwa….ai abun sirri ne!”
Zuciyarta na raya mata kada ta fara amma ta kasa controlling din ta. Yayi wa Zuciyarsa alkawari na sati daya kacal ya daukar mata daga nan sai ajiyeta kamar yanda yake ajiye sauran tarkacen ‘yanmatansa. Amma yanzu zai mata shigo shigo ba zurfi. Alkawari da ya shayar da shi mamaki.
A satin suka dinke da wani haramtaccen al’amari. Soyayyar ban mamaki da Rukky ke tunanin ta wuce wajen saboda ta yiwa kan ta katanga.
Haduwar da ta zama silar bankadar sirri, silar tashin hankula har daya daga cikinsu ya qarke a gidan yari!!!!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
