Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Sau dayawa a rayuwar dan adam mutane kan aikata laifuffuka da suke gani ba a bakin komai ba. Zamani ya zo mana da wasu halaye da suka zama ruwan dare. Zinace zinace, shaye shaye, tsubbu da sauransu.

    Ka dauka cewa a rayuwarka kai matafiyi ne duk tsawon tafiyarka akwai inda zaka kare. Za kuma a tambayeka abubuwan da ka aikata a hanyarka ta zuwa wannan guri. Wani tanadi ka yi? Ka tabbata lokacin da aka nuna maka tafiyarka cikin majigi za kayi alfahari da kan ka?

    Ga duk wanda bai san Almustapha Iliyasou Tillaberi ba to a anan ya gama cutarsa. Yana da fuskar kamala da za kayi zaton mutum ne mai tsantseni wajan aikata zunubi. To sai dai me? Sau dayawa mutane na sanyawa jikinsu wata riga mai badda kama. Akuya da fatar kura!

    Da ne ga Hajiya Hadiza da iliyasou Tillaberi. Ya taso cikin gata da tsananin soyayyar uwa da take ganinsa da daya tilo.

    Almustapha da Momodou ‘yanuwan juna ne kuma aminan juna. Sun yi zumunci ba tare da iyayensu sun damu da suyi hakan ba. Momodou ba shi da wani abokin shawara sai Almustapha musamman akan soyayyar shi da Rokaiyatou. Almustapha ya ba shi goyon baya dari bisa dari abinda ya rasa a duk cikin yanuwansa.

    Almustapha yayi wa Rokaiyatou ne sani tun tana zanin goyo don haka har yau ba zai iya tantance ta ba a cikin mutane. Momodou ya sha masa mitar ya zo su gana abinda ya sa ya ce zai zo Niamey kenen. Zuwan da aiki ya rike shi suka yi da momodou zai taho shi kuma momodou din ya wuce Tillaberi a daura musu aure sai su hadu a Niamey. Daga nan zasu taho da shi, momodou, Rokaiyatou da Momma. Yana taya danuwansa murna yana taya sa samun abinda yake so. Sai a lokacin shi ma ya fara tunanin aure.

    Momodou da Almustapha sun riga sun gane halin mahaifinsu sun kuma rantse ba za su goya masa baya ba. Suka yi ajandar cewa amarya da angon zasu karasa shiri a Nigeria su wuce nairobi inda momodou ya samu aiki. Shi kuma Almustapha ya cigaba da kula da harkokin biznes din su da zasu bude babbar hedkwata a kano.

    A wannan shirin na shi na zuwa Niamey ne ya ji wayarsa tayi kara. Yana duba ya ga momodou ne dariya ta subuce masa ya san ba zai wuce zancen aure ba, inshallahu su ke da nasara. Daga jin alama Momodou din akan hanya yake don yana jin karar iskar mota. Ya ce

    ” Hello..Frere”

    Network ke yanke maganar sai ya ji baya jin sa. Ya kara cewa

    ” Heloooo…”

    Muryar momodou kawai ya ji yana cewa

    ” An damra..Mustapha an damra…. amrena da Rokaiyatou” sai ya ji wayar ta dauke.

    Dariya ya kama yi, ya ji abunda yace sai yake ta kara kokarin kira. Wayar ta ki shiga. Sai ya hakura ya fara shirye shiryen wucewarsa Niamey. Ya san dole ya je don wannan fadan da suka tarko da mahaifinsu ba mai karewa ba ne. Shi dai yana bayan danuwansa ko ana ha maza ha mata bai ga dalilin da zai sa a hana masa abunda yake so ba!

    Abu daya ne ya sa bai je da wuri ba, daga Abuja ya hau jirgi za shi Niamey sai yayi missing flight. Har a lokacin yana gwada nambar momodou bai samu ba. Sai ya fara wani tunani kar ya tafi niamey shi kuma momodou da Rokaiyatou sun taho nigeria a samu sabani. Sai yayi tunanin bari ya kwana in ya so washegari sai suyi waya su tsara yadda abun zai kasance. Ya riga ya kira wani abokinsa a immigration ofgice da zai yiwa Rokaiyatou fasfo a kwana 2 daga nan sai ya shigar musu da biza. Da wannan ya kwana a rai.

    A wannan daren ne gabanni asubahi mahaifinsa ya kira shi yana rusa wani irin kuka. Ya ba shi labarin da ya girgiza duniyarsa wai momodou ya samu hadari a hanyar dawowarsa daga tillaberi, Allah ya masa rasuwa. Jirgin farko ya bi zuwa niamey cikin tashin hankali. Ya kira mahaifiyarsa hajiya hadiza da cewar su hadu a can.

    Irin rudanin da wadannan iyali suka shiga ba cewa komai. Duk irin rashin jituwar mutapha da hajiya khulsumou kawai sai ya rukunkumeta yana kuka. Mutuwar ta dake shi ba da wasa ba. Sai yake ji a zuciyarsa ya kullaci mahaifinsu a ganinsa da ya bar Rokaiyatou da momodou sun yi aure tun farko to da hakan bata faru ba.

    Sai a lokacin yake jin wani labarin kanzon kurege. Wai mahaifinsu na zargin wannan yarinya da uwarta da kashe momodou. Wai har ma an so kashe su an kona musu gida an kore su. Yanzu haka ba a san ma inda suka yi ba.

    Wani irin kallon tashin hankaki Al mustapha ke wa uban. Ya kan kasa gane me mahaifinsu ya mayar da duniya. Ai alkawarin Allah baya tashi, duk yanda yaki auren ai sai da aka daura. Sai yakan tuna maganganun momodou

    ” kamnata amanarmu ce ni da kai.. marainiyar Allah marar gata..ba ta da wanda ya hi mu duk duniya.!”

    Ya yarda ya amince har ya ji yana kaunarta kauna ta zumunci. Zai nemo ta zai kuma inganta mata rayuwa kamar yadda momodou ya so. Zai yi hakan ko mahifinsu yana so ko baya so. Ya san nemanta ba zai masa wuya ba watakila ba za su wuce can niamey ba, watakila sun samu wani gida sun boye..watakila..watakila…Neman da ya shayar da Almustapha mamaki.

    Mahaifiyarsa Hajiya Hadiza wata irin mutum ce da ba abunda ta sa a gaba sai duniya. Ita in dai tana cikin daula to bata damu ba da kowa ba sai dan ta tilo. To yanzu da yake ma shi kadai ya rage momodou Allah ya masa rasuwa to ai danta yanzu shi zai zama akan komai. Momma kawarta ce tun ta yarinta amma bata damu da ta bincika akanta ba. Ita dai tun da duniya ta samu shikenen. Ko da Almustapha ya nuna mata nemo su sai ta nuna ba ruwanta ta kuma yi masa gargadi da kar ya sake ya shata layin gaba da ubansa don abun ba zai masa kyau ba.

    Duk cikin halayensa ya san shi ba azzalumi ba ne shi din kuma mai tausayi ne. Sai yake jin wani nauyi a ransa da bai sauke ba muddin bai nemo yarinyar nan ya sa ma mata ‘yanci ba. Neman da ya wuce tunaninsa saboda ko hotonta ba shi da shi. Sai wani hoton momma da ita tana jaririya da ya samu a binciken da yayi a dakin mahaifiyarsa.

    Bayan mutuwar momodou ne mahaifiyarsa tayi masa auren hadi da wata yar kawarta, auren gata. Auren da bai dade ba ya kare saboda wani mugun hali na Almustapha..CACA. Daga baya duk yanda aka so ya ki kara aure ya tsunduma harkar bariki.

    Shekarun da suka gabata sun zo da canje canje dayawa mafi yawansu ta habbakar I and A group of companies. Hakan na da nasaba da Almustapha da ya jefa dukkanin rayuwarsa akan tabbatar da hakan. Mahaifinsu tun lokacin da mutuwar momodou ta dake shi sai abun ya zame masa kamar ciwo yau da lafiya gobe babu. Sai ya zaman komai yana hannun Almustapha.

    Komai ya bunkasa fiye da zaton mai karatu. A karancin shekarunsa ya zama babban mutum mai madafan iko. Ba shi da wani abu da yasa a gaba sai I and A group of companies.

    Daga baya ne ya fara hiring detectives da za su cigito masa Rokaiyatou da Momma sai ya bada hoton Momma a matsayin shaida. Yayi yayi da mahifiyarsa ta nuna masa asalin gidansu momma watakila ko zai samu labarinsu amma ta ki. Tsoronta daya mahaifinsa ya ji tana da hannu a almarain yayi watsi da ita. Taurin kai irin na Almustapha ya ki saduda. Yakan ce

    ” Sai na nemo ta, sai na inganta mata rayuwa. Zan yi abunda danuwana zai yi farin ciki, zan cika masa buri!”

    Abinda Al mustapha bai sani ba shi ne, wasu abubuwan suka faru ne a kurarren lokaci. Wasu abubuwan mafarkai ne. Lokaci sakarai ne..yakan tafi da burirrika…yakan tafi da imani!

    *********************************
    La mirage wani waje na da Al mustapha ya mayar da shi wajen nishadi. Ba wai don ya dauki hakan a matsayin wani babban laifi ba sai a matsayin wata hanyar nishadi. Sukan nemi matansu suyi wasan karta na caca a gurin kuma bai dauki hakan a bakin komai ba.

    Ba ma’abocin shaye shayen wiwi da sauran kayan maye ba ne ya kan dauki masu yin hakan wawaye. Idan ya fara shaye shaye ya je ya haukace a banza wa zai kular masa da dunkiya? Ai shaye shaye na marar dubara ne wanda bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba kuma ba shi da wata madogara a gaba.

    Amma idan yayi nishadi suna cacarsu a la mirage akan kawo musu kofunan whisky suna zuka a hankali. Ya kan sha kofi daya ya wadace shi ya tunda dai ba shiga halin maye ba a ganinsa hakan ba laifi ba ne.

    To wataran daga nan ne zasu kwashi yanmatansu da suka yi daidai da raayinsu. Almustapha ba wai mayen mata ba ne amma zama cikin abokanai masu irin halin ( dan Allah mu kiyayi abokai da kawaye bata gari) ya sanya suka fara nuna masa a bin mata ba komai ba ne. Kamar wani abu ne ma da zai yiwa rayuwarsa ado da shi. Tun da ga shi mai kudi mai madafan iko ai kowacce mace ya ga dama zai zara.

    Da irin wadannan hudubobin ya zama yana neman mata jefi jefi. A cikin matan ma dan ra’ayi ne sai wacce ya ga ta masa ga zabin masifa. Tun da yayi aure suka rabu da matar ya mayar da gidansa inda yake shigo da mata. Iyayensa sun san wasu abubuwan da yake yi amma sun kasa daukar mataki akai. Son sa da kaunarsa ya rufe musu ido daga baya ma sai Hajiya Hadiza ta fara shiga malamai na cewar makiya sun yi masa asiri ya ki aure ya balbace. Ya zama bata ga gidan boka bata ga gidan malam.

    Jin dadin duniya wani abu ne da Almustapha ya ganewa saboda bai rasa komai na rayuwar duniya ba. Ya girma ya gawurta a karancin shekaru irin na sa ya na zama da manyan da suka isa su juya duniya. Tun yana tunanin ya kara aure har abun ma ya fice a ransa tun da kadangarun bariki suka daura masa laya. Aure takura ne a wajensa yakan hana bawa ya wataya ya ji dadin duniya.

    Iyayensa sun yi sun yi akan ya kara aure amma abun ya gagara. Yanzu mahaifinsa ba shi da wani karfin jiki da mulki komai Almustapha ke juyawa idan ya tasamma masa zai masa fada sai ya nuna zai ajiye komai na kamfani ya nemi na yi. Abunda ke tayarwa mahaifin hankali kenen, baya so a ce guminsa na shekara da shekaru ya tashi a banza.

    Akwai wani abu da Almustapha ke ji a ransa game da ubansa da ya kasa yafewa. Gani yake shi ne silar rasa momodou kuma ba zai taba yafe ma sa ba. Yakan kalli mahaifinsa a matsayin azzalumi mai danniya. Anya ba shi yayi sanadin mutuwar Ahmadou Tillaberi ba? Almustapha ne kadai ya san iya adadin dukiyar Ahmadou Tillaberi da mahaifinsa ya hade da tasa. Sai mahaifinsa kan ba shi tsoro, ina za shi da hakki. Irin wadannan tunani kan sa ya ji yana neman wannan yarinya ko banza a mallaka mata dukiyarta.

    A halin da ake ciki ya hadu da manyan kasa sun kafa wata jamiyya ta siyasa ta DSP. Ba takara yake so ba ba kuma mulki yake shaawa ba. Sai dai a rayuwarsa shi capitalist ne. Duk wani abu da zai kawo habakar dukiyarsa to ya san ta. Ya gane cewa gama kai da manyan gari manyan kasa shi zai dada karo bunkasarsa da kuma kanfanunukan sa.

    Haka rayuwar take, ka daga ni na daga ka. Hakan ba karamin taimaka masa yayi ba wajen shige da fice da kayan masarufi na kamfaninsa. Ana wannan halin ne suka tsayar da dan takarar gwamna. A kuma lokacin ya tafka wani kuskure da ya zame ma sa abun bibiya.

    *********************************

    Zaune yake a ofishinsa a wata ranar litinin aiyuka sun cabe masa. Suna da kaddamar da wani kamfanin man gyada da karfe biyu na rana ga shi har karfe daya ta gota amma yana zaune a ofis.

    Ya tuno abunda ya faru yau da safe da ya biya wajen mahaifiyarsa har ya sa shi ya dan makara.

    Tana zaune a wani tangamemen falo mai dauke da kayan alatu sanyin ac yana buso ta.

    A hannunta remot ne tana caza tasho shi a tv ya gaisheta ta dube ta ce

    ” ka ga text dina jiya da daddare, ba ka ji ina maka neman gaggawa ba? Tun da yanzu idan an kira ba a isa ka dauka ba”

    Sai ya iso har inda take ya kama kafafunta ya rukunkume ya ce

    ” Mummy kenen ai na san zancen guda daya ne shi yasa na ki zuwa. Wai kin gaji da ganina hakan ne da kike so na kara jajibowa kaina wani auren?”

    Ta shafa kan sa tana kallonsa cikin kauna irin ta uwa. Tana so ta gaya masa abubuwa dayawa da zai gyara a rayuwarsa amma sai ta ji kamar ta kasa. Yaron yana mata kwarjini sannan bata so yayi fushi ( karshen duniya baiwa ta haifi uwargijiyarta).kuma ma ai da kuruciya a jikinsa wataran zai daina. Maimakon ta yi masa fada kan kwashe kwashen yanmatan da yake yana kaiwa gidansa sai cewa tayi

    ” Ni na fi so ka nutsu waje guda kayi aurenka ai ya fi mutunci. Ba ka so na ga ‘yan jikokina?”

    Dariya yayi. Ya saba da irin zancenta. Ya ce

    ” To ai matsalar yanzu za ki ce sai zabinki. Ba haka aka yi da Fadila ba abun ya zo bai yi dadi ba”

    Tayi sauri ta ce

    ” Aa, wannan karin dai ka zabo wacce tayi maka. Amma kar ka manta ka zabo yar babban gida yanda ka ke dan babban gida. Ka san ni mutum ce mai shiga kawaye bana son abunda zai jawo min raini ko a ga gazawata”

    Kallonta kawai yake. Zancen dai kenen. Ita dai ta shiga ko’ina ta kece raini. Da haka ya amsa da to kawai ya shigar da zancen da ke ransa don ya ga yau tana nishadi. Ya ce

    ” To ya maganarmu? Yanzu mummy ya kamata a ce a neman nan na kawarki da diyarta ki kasa sa hannu?”

    Nan da nan ta gintse fuska. Ta nuna masa danyatsa ta ce

    ” wai mustapha wannan zancen bai kare ba? An gaya maka su suna so a gan su ne? Da suna so ai da kan su zadu bayyanar da kan su. Ka ga alamun rashin gaskiya kenen.A irin wannan turbar danuwanka ya rasa ransa shi ne kake nema ka salwantar mun da kan ka?”

    Tsayawa kawai yayi yana kallonta. Idan da sabo ya saba da halinta na ko in kula in dai ba akan hamshakan kawayenta ba ne. Yanzu duniya ta koma sai da mai shi ake yi. Ya san idan ya tsaya ma bata lokacinsa zai yi.

    Ya mike yana gyara kot din sa ya rasa me ke damun iyayensa. Ya ce

    ” To Allah ya bayyanar da su”

    Cikin kosawa ta ce

    ” Amin”

    Ya mike yayi mata sallama. Har ya zo bakin kofa ta ce

    ” kun yi magana da mahaifinka kuwa? Daga zuwansa Niamey jikinsa ya motsa ba zai samu damar dawowa yau ba. To Allah na tuba zama da wannan matar tasa ma kadai ai ya isa ya tayar masa da hawan jini. Khulsumou..khulsomou ai matsala ce”

    Wani abu ne yazo ya tokare masa a makogoro. Dama duk zancen da take masa dazu babansa ba shi da lafiya ta kasa gaya masa.Ya share korafinta akan Hajiya Khulsomou yayi sauri ya fara laluben wayarsa yana cewa

    ” Bari na kira na ji..idan jikin ya matsanta kawai Indiya zamu koma. Na kasa gane wannan wani irin ciwo ne”

    Da haka ya fita bayan ya kira baban yace masa da sauki a satin ma zai shigo kano. A haka ya zo ofis aiki ya sha masa kai. Ya katse aikin suka tafi wajen kaddamar da kamfaninsu na man gyada. Ko lokacin da ya gama aikin ranar ya gaji likis. Wani sashe na ran sa ya ce ya wuce la mirage ya barje gajiyarsa ta yau.

    Da misalin karfe 10 ne na dare harabar gurin a cike take da mutane manya da kanana. Tebur din su Almustapha na sashen Vip suna zaune da shi da waau abokansa 4 suna tattauna al’amuran siyasa.

    A kan teburin akwai kwalayen taba da wasu gajerun kwalabe na giya masu tsada. Da tambulan a hanunsa yana kurbar abinda ke ciki a hankali.

    Tun daga nesa ta kura masa ido ta fi sati daya tana bibiyarsa. Komai yayi sha’awa yake bata ta rasa wani irin abu take ji game da shi. A hankali ta taka har teburin da suke.

    Sanye take da wata riga irin gown dina mai masifar tsada fara kal. Ta kwanto gashinta da ta yiwa kari zuwa kafadunta. Babu abunda take yi sai kamshin turare. Kowa a gurin ita yake bi da kallo saboda kyaun da tayi. Ta zauna a wata kujera kusa da shi ta rangwada kai ta ce

    ” Ranka shi dade…kar ka ce dani baka gane ni ba”

    Kallo ya kare mata a hankali so yake ya tuna inda ya san fuskar. Ya ce

    ” A mafarkai kike zuwa ko?”

    ” Mafarkan ido biyu ko?” Tace da shi

    Ya bude ido alamar mamaki ya ce

    “Su kuma wadanne ne hakan?”

    ” Irin mafarkan nan da mutum ba zai so ya farka ba” ta bashi amsa

    Kallonta kawai yake akwai wani abu na kyaunta da ke fizgarsa, ya rasa menene.

    Ta dauki kofin da ke gabansa ta kurbi abunda yake ciki ta kalle shi cikin idonsa ta ce

    ” Ana ahabak ktheer…ktheer habiibi”

    (Ina son ka sosai da sosai masoyina)

    Kun ji haduwar da ta zama silar bankadar sirri. Sirrikan Almustapha.

    Wasu sirrikan ba su boyuwa wasu sirrikan bibiya suke yi, su yi naso suyi rassa su tarwatsa mamallakinsu! Irin hakan ce ta faru ga Almustapha Iliyasou Tillaberi!!
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!