Duniya ta – Chapter Twelve
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Ayye mama ayye mama, mama ye iye
Ayye mama labo labo, mama ye iye
Da aure ya kan raba aure, mama ye iye
Da na biki mun tafi tare, mama ye iye
Kandala ta cigaba da rera wakarta tana jefa danwake. Dirkekiyar mace ce da ta doshi shekara 50 a duniya. Fuskarta na dauke da fashin goshi, yanayin fatar jikinta tayi haske irin na bilicin da kuma dabbare dabbare na tabubbukan da bilicin din ya bar ma ta. Lebanta sun yi baki sidik saboda shan taba.
Jikinta sanye da wata atamfa code vore da aka yiwa dinkin zurmemiyar riga mai aljifai na saka kudi. Fuskarta ba yabo ba fallasa tana jefa danwakenta na siyarwa da yayi suna. Daga wajaje daban daban ake zuwa saya a wani kango data kama. Tana da kananan ma’aikata masu zubawa mutane da mika musu.
Kandala wata tsohuwar karuwa ce da duniya ta yi mata atishawar tsaki daga karshe ta qarke da sana’ar danwake. Ba wai ta daina kananan iskance iskance ba ne, kawai dai yanzu duniya bata ta tata.
Daga gefenta kadan Rukky ce kwance akan wata tabarma tana ta bushe bushenta na iska. Sanye take da wani wando tiri kwata da ya kame ta tsam, ta sa wata riga marar hannu. Duk wanda ya shigo kangon nan yakan zuba mata ido cike da mamakin rashin kunyarta amma ko a jikinta.
‘Yan iska kuma zauna gari banza su ke jifanta da fito ko yabo amma babu wanda ta kula.
Sai ma ta kara mikewa ta dago kafarta tana karkadata a hankali. Duk na mujiyar mutanen nan ma su siyan danwake su fice bai dada ta da kasa ba.
Wajen danwaken kandala wani waje ne da Rukky ta mayar wajen nishadi. Anan ta kan zauna idan bata son magana da mutane tana so ta kadaice tayi tunane tunanenta na duniya. Haduwar jininsu da Kandala ya sa ta mayar da gurin wajen zuwanta ko banza ta mata hirar duniya.
Tana wannan kwanciyar ta lissafa yawan wakokin da kandala ta rera a zamanta na kasa da awa biyu. Ta rera sama da 20..tana kan ta ashirin da daya. Shin wannan matar na da matsala kuwa? Ta dauke tunaninta daga kan wakokin kandala ta koma tunanin abunda ya shafe ta.
Burinta a duniya bai wuce ta kai wa makiyanta farmaki ba..to amma ta yaya. Ta zata i yanzu ta gawurta ta kai matsayin da za tayi fito na fito da su to amma abun ya gagara. Ga shi ba ma ta da wani takamaiman labari a kan su. Idonta idon Iliyasou Tillaberi ko wani da ya dangance shi, to kashinsu ya bushe.
Muryar Kandala tana aiken wani yaro shi ya tsayar ma ta da tunaninta.Ta ji ta ce
” kai ajiye kwanonka a nan in aike ka”
Ta zira hannu a daya daga cikin aljifan rigarta ta zaro N20 ta baiwa yaron ta kara cewa
” maza maza je ka shagon Namadi ka siyo min taba rotmans..idan ka siyomin benson sai na ci uwarka…”
Ta karasa tana nuna masa danyatsanta sabbaba alamar gargadi. Sai daga baya ma ta karewa yaron kallo ta washe hakora ta ce
” Au…au..ashe ma isuhulle ne na wajen tabawa….ai ga idon nan irin na uwarka..maza je ka kafin ka dawo an zuba maka”
Yaron ya fyalla a guje. A wannan lokaci ta gama jefa danwaken ta dauraye hannunta ta goge a jikin atamfarta. Masu saya sun fara raguwa dan isuhulle ya kawo mata tabar ya dauki kwanon danwakensa ya tafi.
Mutane suka watse saboda danwake ya kare sai masu taimaka mata da ke wanke wanke. Zaune take aka kujera ‘yar tsugunno ta kunna wannan tabar ta fara zuka a hankali. Sai ta karkato da jikinta gaba daya tana kallon Rukky ta ce da ita
” Yarinya ki bar zuke zuken nan..kar ki je ki haukata kan ki a banza a wofi!”
A hankali Rukky ta taso daga kwanciyar da take ta kurawa mata ido da lumsassun idanunta. Kallo ne take mata na ‘ke me kike yi’. Kandala tayi murmushi ta ce
” Kin ga waccan mahaukaciyar tabargazuzu ta bakin rawul din can? Billahillazi a gabana ta zo garin nan shekarun baya. Babu irin tashen da bata yi ba. Idan kika ga yadda maza ke rububinta za ki sha mamaki! Har ‘yan bani na iya kan ce wai ta dalilinta ne wani gwamnan lokacin ya shimfida mana wannan titin da ya shigo unguwarmu.
Ita ma ta kafa wannan bushe bushen da shan kwaya..to kin dai ga karshenta nan. Tun tana haukarta a cikin gida har ta fara yawo.Ni abunda ya sa kenen daga taba ban dara ba, ita ma dan ta zame min jiki ne”
Rukky tayi wani murmushin takaici ta ce
” To ita taba kin san illar da take yi? Dagargaza huhu take. Ba ki ga ko jikin kwalin ba..masu yin ta ma sun aibatata da cewar mashayanta za ta iya kawo musu mutuwa a kananan shekaru. Taba ita ma ai balai ce!”
Maimakon Kandala ta kula ta sai ma ta cigaba da zukar tabarta tana fitarwa ta hanci ta baki. Suka yi shiru na dan mintuna har suka daina jin kwaramniyar masu wanke kwanuka. Su ma sun gama kandala ta sallame su. Ya rage daga ita sai Rukky a wannan waje.
Ta murje tabar a kasa ta kurawa Rukky ido ta ce
” Ke ‘yar wani gari ce?”
Rukky tay caraf ta ce
” Ni asalina ‘yar kazaure ce..acan jihar jigawa babana dan wani kauye ne mai suna karkarna. Bahaushiya ce ta usul!”
Kandala ta buga tsaki ta yi mata kallon uku saura kwata ta nuna ta da danyatsa ta ce
” Ke yarinya kallo daya na miki na san ke jinin zabarmawa ce! Ba ki wuce maradi ba ki wuce zinder da kewaye! Ni kuwa kin ganni nan uban da ya haifi uwata ma cikakken dan damagaram ne!”
Rukky bata kula ba ,kandala ta gyara zamanta ta ce
” kin ganni nan bana shekarata 30 cif a bariki! Ba wani abu ya fito dani ba sai sanadin fyade. Na taso ina marainiyata a hannun wata gwaggo na to mijinta shi ya fara lalatani!
Tun da uwata ta kawo ni duniya ban taba ganin azzalumi irin Alhaji Isa ba. Ina kankanuwata ban fi shekara goma sha biyar ba ya fara min fyade a cikin gidansa! Ga shi lokacin akwai karancin shekaru da karancin wayewa a lamarina. Sai ya shigo da zarmemiyar wuka ya ce idan na fadi ma gwaggo na sai ya yanka ni!
A lokacin babu wani abu da nake tsoro sama da shi haka kuruciya ta sa na ja bakina nayi gum, amma kamar an tarwatsa zuciyata. Dana gaji ranar na samu gwaggo na na gaya mata ko da zata cece ni daga wannan rayuwar kin san me ta ce?”
Rukky ta girgiza kai tana tuno abubuwa da dama. Idanunta suka fara hasko mata Ali. Kandala ta ce
” Sai cewa tayi ina yi wa mijinta sharri. Ta kafa duka na da kyar makota suka cece ni. Ba irin tsinuwar da bata mun ba a ranar. Har da ce da ni butulu na zama kaza ci ko goge bakin ki.
Ba a fi kwana biyu ba ta kuwa kama shi da idonta yana kokarin haike min. Amma kin san saboda tsabar son zuciya sai kira na tayi daki ta ce wai nayi shiru kar na fadawa kowa saboda Alhaji Isa babban mutum ne. Idan na tona mishi asiri kamar na tonawa kai na ne saboda uban ‘ya’yanta ne. Amma za ta dauke ni ta kai ni aikatau birni.
Da kin san tarkon da fyade ke jefa zuciyar wanda aka yiwa to da ba kiyi fatan ya faru ko da ga makiyinki ba Rukky. A irin wannan bakin cikin na fara rayawa rai na na kashe Alhaji Isa! Barin irinsa a doron kasa ai ba karamin fitina ba ne!
Kandala ta daga kai tana kallon sararin samaniya na wasu ‘yan daqiqu sannan ta mayar da idonta kasa ta ce
” Ina ma za a ji labarina iyaye su hankalta! Ina ma za a ji labarina a ke bi wa ‘ya’ya hakki! An jefa rayuwata a cikin haula saboda maraicina, tun daga lokacin na kudurta a raina sai na gurgunta rayuwar duk wanda ya kusance ni.
Tun da ta kai ni aikatau ba ta kara bi ta kai na ba ni kuma ba marmari nake ta ce na zo na koma gida ba. Na riga na kudurta ni da gidanta har abada! Don haka daga gidan aikatau gaba kawai na kara ina ‘yar kankanuwata na tsinci kai na a karuwanci!
Ba so nayi ba , ba kuma so nayi na balbalce ba amma rayuwa ta fi karfina ba ni da yanda zan yi ba ni kuma da inda zan je.
Kin ganni nan?A yanzu na fi shekara guda cur dauke da cutar kanjamau! Amma fa shan maganina nake akai akai ba tare da kowa ya sani ba. Kuma har yau ban fasa tu’ammali da maza ba. Yanda na kwasa kowa ma ya kwasa! Ai kowa ya kwana lafiya shi ya so dan uwatar!”
Rukky ta kurawa Kandala ido ta rasa matakin da zata dora ta a zuciyarta. Maganar fyaden nan ta tsaya mata a rai.
Fyade…ina ma wadanda aka yiwa fyade na da murya…ina ma..ina ma…..
*********************************
Irin soyayyar da ake bugawa tsakanin Idi Maina da Luba dan kallo sai ya rike baki. Luba ta makalkale shi ta yi masa dabaibayi a cikin salo, hilata da yaudara irin tata. Har ya zamana bai iya zuwa koina sai ya ratayo luba a jikin sa ta masa rakiya. Sosai shedan ya shiga al’amarin nasu yayi rawa yayi juyi har ya zamana ba sa komai sai diban albarka.
Idi maina mai samu ne don kuwa duniya na yayinsa a lokacin akwai yan kwabbai a aljihunsa. Sai da Luba ta tabbatar tana tatuke shi fiye da zatonsa. Shi kuma ya makance a a jarabar karuwa ya watsar da matansa na gida. Da yake duk abun bautar shedan ne sai suka gamtse suka zama tif da taya.
Har ‘yar Moduwaye kan ce
” Ki tatuke shi ki masa kat! Ai duk wanda yace bariki zai..ai ba uwarsa ta turo shi ba!..kar ki tausaya masa ko na miskala zarratin! Kowa ya ci dubu ai sai ceto! Kowa ya tuba don wuya ba lada! A dade ana yi sai uban da ya sa kan sa..tun da yace zai hadiyi gatari to sai a sakar ma sa kota! Duk shegen da ya fasa baya kaunar uwatar!”
Wannan nema na su da Idi ya sa Luba ta kara wayewa don Ya san ta kan duniya. Kacokam ma sai ya dauke ta ya kai ta Abuja suke sheke ayarsu. Yawa yawan lokuta sai ya kashe wayarsa kar matansa su dame shi da kira. Yayi nisa kadangarun bariki sun daura masa laya.
A abuja irin mahaukatan kudin da yake kashewa Luba ba a magana. Ba su joint joint ba su club club.Daga baya ma har ya dalle ta da mota sabuwa fil ‘yar yayi. Ranar da suka dawo ta taho da motarta gidan Hajiya Kubuwa su yar modu aka siyo lemon fanta aka fara mata wanka suna shewa! Cewa yake
” Da kyau Luba shegiyar wutsiya..kowa ya hango ki ya taya to dama uwarsa ta ce da shi je ka ka gani..tsinanne ne! Ahayye…yau ina ganin abun da ya ishe ni..abun zama ya mutu ya bar zani!”
A ranar wata alhamis Idi Maina ya dauki Luba a mota suna yawan ta zubar. Yau ma wani wajen cin abinci suka je suka cika tumbinsu. Suna kan hanyar dawowa ta ce ya biya da ita wani shagon sayar da kayan kwalliya sun dauki hanyar kenen sai wayar shi tayi kara.
Bai cika son ansa kiran waya ba idan yana tare da Luba musamman ma da ya san ba zai wuce matansa ba. Don haka sai yayi kamar ya share sai kuma ya duba sunan. Cikin sauri ya rage karan sautin redio da ke tashin wata wakar p square ya dubi Luba ya gaya ma ta ogansa ne ke kira.
A hankali ya daga wayar da
” Hello Sir”
Ba ta ji mai ake cewa ba ta dai gane kamar fada ake masa. Bayan ya ajiye wayar ne ya kalleta rai a bace ya ce
” Oga na ne yake nemana a ofis yanzu yanzu..kuma ya zama dole na ansa kiransa na gaggawa. Don gaskiya shi in dai akan aiki ne ba ya wasa”
Luba ta tabe baki irin na shagwababbun ‘ya’yan tabara ta ce
” To baby ni yanzu ya zaka yi da ni..ka san fa gobe ina da bikin kawata hannatu kuma da kayan zan yi amfani..gaskiya ni..gaskiya..” Sai ta fara buge buge da kafafunta
Ya dan fara rikicewa..a rayuwarsa ya tsani fushin Luba. Yana kaunar yarinyar kamar ba gobe. Ransa ya fara raya masa abubuwa dayawa game da ita. Shin ko dai ya aureta ne ya ajiyeta a Abuja? Idan ya so ragowar karabitin matansa ya bar su acan garin da suke sai yake leka su loto loto.
Da irin wannan tunanin ya shafa fuskarta a hankali ya ce
” Haba gimbiyata, kin san fa in ba don dole ba ba zan je kiran nan ba. To amma maganar aiki ce ogana kuma baya wasa da aiki. Ni fa so nake ki zamo tawa ni kadai! Ki kwantar da hankalinki i’m all urs”
Cikin shagwaba ta fara cewa
” To yanzu yaya za a yi..sai dai mu je na raka ka daga nan sai mu wuce”
Ba zai iya musu ba ya ce mata to..suka wuce ma’aikatarsu. Da suka isa yayi pakin ya ce ta jira zai je ya dawo ta ce zata bi shi . Suka fito gabadaya.
Ba dai hakan ya so ba amma ba yadda ya iya. Tunanin ogansa yake ko yau kuma da wacce ya zo ya ga sai zazzaga masa masifa yake. Sa’annan baya so ya shiga da Luba ofis din sa amma ya san ba zata amince ba.
Ya san ogan nasu dan hannu ne don ko da can ya san wani kawali da ke kawo masa mata jefi jefi. Bai tsumduma a harkar ba amma dai ya san yana tabawa.
Ba ma wannan ba shekarun baya wanene ya kai ogansu tashe a La mirage? Hadadden wajen cacan nan da yayi karin suna. A dan shekarun nan ne ma ya ga ya bace bat! Baya ganinsa kwata kwata ko me ya sa? Oho
Yanzu da suka doshi ofis din da Luba sai ya ji zuciyarsa ta cika da waswasi. Ba wai don zubewar mutuncinsa ba sai don kar fa ogan nasa ya gani ya kyasa. Ko da yake shi fa ogansa mai taste ne mai dan banzan ra’ayi. Sai a kawo masa mata 10 ya ce ba su masa ba..ba lallai ma Luba ta birge shi ba. Da wannan tunanin suka doshi ofis din.
Tun da Luba ta shiga katafaren ma’aikatar jikinta yayi sanyi. Dama anan Idi Maina ke aiki lallai ashe arzikinsa ya kai haka? Ashe ma bata tatsi komai ba! Da sauranta dole ne ta san yadda za tayi ta raba shi da komai. Daga karshe ta kora dan banza! Amfaninsa ya kare.
Sakatariya ce tai musu iso suka shiga. A jikin kofar ta ga an rubuta ” The Chairman, A. I. T”. Shigar Luba wannan Ofis sai ta ji kamar ta suma. Tun da take shige shigenta ofisoshi yawon ta zubar bata taba shiga wanda ya kai wannan haduwa ba. Komai na cikinsa ruwan toka ne. A wani bala’in sanyi da ke busawa ka ji ka kamar ba a kasar ka ke ba. Lallai wannan ogan ba karamin tsoho ba ne da ya tara kudi tsababa!
Idi Maina yayi mata mazauni a wasu kujeru da ke ofis din shi kuma ya karasa tebur din gaba suka fara tattauna abunda ya shafe su.
Ogan ta ji yana cewa
” You have to be careful, very careful”
Dago kan da Luba za tayi idonsu yayi caraf ya hade. Wani irin shock ne ya ziyarce ta wanda saura kiris ta fadi daga zaune. Ya dauke idonsa suka ci gaba da maganarsu ita kuma ta zuba masa na mujiya.
Menene haka? A zatonta zata ga tsoho tukuf kawai sai ta ga matashi mai jini a jika da ba zai haura shekara 35 ba!. Baki ne daga gani dogo ne ya ajiye wani gemu da ake wa laqabi da na kwata miliyan a fuskarsa.
Yana sanye da wata bakar kot da takalmansa sau ciki kallo daya za kai mu su ya fallasa tsadarsu. Jikinsa ya nuna alamar hutu da jin dadi..kai daga ganinsa young miloniya ne!
Kan ta ta ji yana juyawa da ta kare masa kallo da wassafa tunaninsa. Tun da take a duniya take haduwa da maza kala kala bata taba ganin wanda ya kai haduwar ogan idi maina ba! Komansa sha’awa yake ba ta, ta rikice ta dimauce a cikin wani TARKO! Tarko irin na so!
Ashe dama haka so yake? Ashe da mutane suke cewa “so” ashe da gaske su ke? Ashe akwai shi? Haka yake dama? A yau ta tabbatar so gaskiya ne domin ya dana mata tarko kuma ta kamu har iya wuya!
Tun da take shanawarta bata taba tunanin yin aure ba. To amma yau da idonta ta ga miji. Ta ga miji na nunawa sa’a. Ko ana ha maza ha mata sai ta mallake shi. Sai ya so ta kamar yanda take son sa. A yau ta ga abun so abun kauna! A dalilin son wannan gayen da son aurensa har suka bar wannan ofis da tunani daya ranta!
” Zan mallake ka, ko da abunda na mallaka a duniya zai kare! Ko da duk mutanen duniya suna so ko da basa so!”
Ko bayan sun fita daga ofis din ,Luba na waiwayensa a sace da tunanin zata masa zuwan bazata. Daga nan ta yi masa kamun kazar kuku.
Shi kuma ya cigaba da aiyukansa dama gwanin aiki ne. Wayarsa tayi kara ya daga da sauri ganin mai kiran. Wani private detective din sa ne. Ya ce
” Yaya ake ciki? Any progress?”
Daga jin amsar da ya bashi ba ta masa dadi ba ya ce
” Har yanzu? Ba wani information? Idan nan da sati biyu ban ji wata cikakkiyar magana ba mai amfani i’ll fire u!”
Kit ya kashe wayar yana huci dama zafin rai ne da shi. Wani irin damuwa ya ji tana taso ma sa ,ran sa ya gama baci. Tunani ya masa yawa ya zai yi da ransa ne? Yana jin kan sa a matsayin wani wanda ya gaza! A rayuwa ya tsani ya gaza, gazawa ai ta raggon maza ce! Shi juwa ai jajirtacce ne!
Wasu irin maganganu ne suka cigaba da kuwwa a kunnuwan ALMUSTAPHA ILIYASOU TILLABERI…
An damra………Mustapha ……..an damra amrena da Rokaiyatou!
Daga nan ya ji dif! Komai ya tsaya cak!!!
A hankali ya ce
“Ina ki ke?… Ina ki ke???????”
Me zaka ce game da wannan babin? Menene zai faru? Menene raayinka game da wannan labarin? Idan kuna jin dadinsa danna tauraro in kuma ga comment din ku rututu!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
