Duniya ta – Chapter Eight
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Ranar Asabar aka kaddamar da sababbin ‘yan kungiya. Hindatu, Lubabatu da Rokaiyatou. Aka kafa musu dokokin kungiya kuma duk suka yi mubaya’a.
Shugaba Hajiya Kububuwa wace irin ingarmar mace ce mai jarabar tsawo kamar daren wahala. Fuskarta baka ce kirin mai dauke da kalangu a kuncinta. Yanayin girman jikinta kadai ya isa ya yiwa dan adam kwarjini ya sa ma sa tsoro, ga ta da zafi kamar barkono. Sai dai mace ce mai haba haba a inda ta san za ta samu Naira.
Hajiya na da wasu irin “connections” a kasar Najeriya da ketare wanda idan ka ji sai ka sha mamaki. Mace mai tarin jama’a da dukiya. Duk wani wanda ya ci ya tada kai da Nera kuma shedan ya ma sa fitsari a ka ya san da Hajiya kububuwa kuma ta san da zamansa. Babu irin deal din da bata yi, ita ce safaran mata kano to jiddah, ita ce safarar mata da maza kasar italy su je su yo karuwanci su dawo ma ta da kudi tsababa. Ita ce safarar miyagun kwayoyi daga kasashen Afrika zuwa na ketare, habbaka madigo, luwadi. A halin da ake ciki ta kafa wata kungiya ta jajircewa da yakar gwamnati akan auren jinsi daya.
Babu wani hali na Allah ya tsine da Hajiya ba ta da hannu dumu dumu a ciki amma da yake su ke da kasar kuma tana da daurin gindi daga sama ko yatsa ba ka isa ka nuna ma ta ba. Sai ma al’amarin na ta ya ke dada bunkasa domin wadanda ya kamata su hana su ne maneman ta ko maneman yaranta.
Hajiya kubuwa ta cigaba da kallon sababbin ‘yan kungiyarta ta ce
” Ban tambaye ku labaran ku ba labaranku ba abun saurare ba ne don na san ba zai wuce na bakin ciki da takaicin duniya ba. Sanin labarin mutum ba shi da wani tasiri a rayuwar da zai yi gaba, ku dauka yau kawai aka haife ku, aka yaye ku , ku ka girma ku kayi hankali a ranar ku ka kuma zabi rayuwar da ta dace da ku. Rayuwar duniya zabi ce, sai ka so za ka sha wahala sai ka so zaka sha wuya. Da a ce na san dabarun duniya tun daga haihuwa to da tun farko na zana kaddarata da hannuna (astagfirulla) na tsallake wahalhalun banza a hannun wadanda ba su isa ba!
Ban taba ba wa kowa labarina ba, Da me za a anfanu da labarina, ba ni da sha’awar asan ko ni wacece. Ni kungiyata ba ta da takura bani kuma da katanga a aikata son rai. Wacce ta ga zata nemi maza ta nema, mai neman mace ‘yaruwarta ta nema. Kowa ku ka gani a nan da bazata yake rawa.
Kowa ya iya takunsa ni kuma zan rike ma sa ka maciji yayi wasa da jelar. Ban kuma ce ku ragawa da namiji ba, bariki sa kai ce duk inda ku ka samu faraga ku wawusa. Wanda aka ba ku da wanda ba a ba ku ba duk naku ne!Ni Kububuwa dan kungiyata ba shi da haramiya!
Wannan tafiya ce mai tsawo, mai cike da tarin nasarori da idan ku ka bi a hankali za ku ci moriya. Mu gagara gasa ne muna da hanyoyi dubu da daya na sarkafe da namiji. Muna yin kowani taro asabar din karshen wata. Haka kowani ciniki mace tayi muna da kamasho a ciki”
Da haka taro ya tashi , aka dauki sababbin ‘yan kungiya aka kai su gidan shugabar kungiya zuwa wani bangare da ta ware wa ire irinsu. Gidan Hajiya duniya ne fadar girma da fadinsa da kayan alatun da ke cikinsa ma bata baki ne. Hajiya tana da bangaren sabbin ‘yan kungiya da zasu iya zama kafin su ci gashin kan su, duk wacce ta girmama za ta iya barin gidan ta kama na ta. Aka zaunar da su a falo Hajiya ta ce zata turo ‘yar Modu ta karasa musu sauran bayani.
Da suka shiga falon mata uku ne a zaune jummai, Sima da Naima kowacce tana harkar gabanta. Hindatu , Lubabatu da Rokaiyatou suna daga zaune aka kawo musu abinci na alfarma suka ci suka yi kat! Ac na buso su. Wani irin farinciki ya ratsa zuciyar Luba ta ayyana dama tun dawowarta da ga Saudiyya ta hadu da Sadiya Indiyar Daji, ai da bata wahala ba! Dama akwai irin wannan rayuwar bata sani ba? Hajiya Kubuwa ta gama birgeta dama ita ce ta samu daula irin haka, ai da abun ba magana.
Kamar daga sama suka ji wata murya ita ba ta mace ba ba ta namiji ba an ce
” Yauwa ina bakin suke? Sako makoko daga Hajiya Kububuwa ta ce a shiga ayi wanka wacce ba zata iya ba in taimaka in cuccude ta a fidda dattin annakiya. Dattin talauci ai ba karamar dauda ba ce, shi ya baro mu daga kauyikan mu ya kawo birni domin mu ci miya da wasali”
Baki ne daga can sama suka zo zasu zaba su darje..ehe ..ba a bori da sanyin jiki” kawai ya kama hannun Luba zai tayar da ita daga zaune tayi sauri ta fizge hannunta tana yiwa wanda aka kira da ‘yar Modu kallon mamaki.
Ta ga namiji dan siriri fuskar nan ta sha bilicin yana da tsayi daidai misali. Ya sha kaftani amma sai ya dauki wani zani ya yafila da kallabi. Ta gama ganowa dai dan daudu ne. Yadda ta masa ya bashi haushi ya rike haba ya ce
” Haba ‘yanmata ‘yar Moduwaye ce fa mace yaruwarki, daga tabi? Ai a sa a baka ba tauna ba ce kuma tauna ba za ta taba zamo hadiya ba. Kin ji ko?…ehe!” Ya gatsina baki ya karya kugu.
Yanayin kwarkwasar sa da maganarsa ya bawa Rokaiyatou dariya ta kuwa dunga kyalkyatawa ya juyo gareta har da kashe ma ta ido ya ce
” Sukari..lallai yanmata ba ki yi farin banza ba, dalli kamar an haska tocila. Wannan irin murmushi haka haskensa kamar wata dan daren goma sha hudu. Ita waccan kawar ta ki ta zata na taba ta ne da wani dalili to ki gaya ma ta ni a wajena yadda ta san naman alade a wajen dan musulmi haka na dauketa. Billahillazi haramiya ta ce, to kin ji yadda aka yi. Ahayyeee!”
Luba ta daga kai ta galla ma sa harara da alama ba za suyi shiri ba shi kuwa ya ce
” Aa dakata ‘yanmata ai ban san kuna yi ba sai na ga idonki ya fado kasa yana birgima. Kar ki bari dai kwabarki tayi ruwa don duk hangenki da sama ba za ki yi tsallen alkafira ki hau ba, ni ce dai tsanin..kar ma ki ji da wai, na bar ki da wannan”
Jummai ita ce mai waya da wani maneminta a waya, Sima tana yiwa Naima kitso na karin gashin doki ta ce
” Kai haba ‘yar Modu wai kai ba za ka iya musu ko dan introduction ba ne a matsayinsu na sababbin zuwa”
“Ke Naima mai dattin hula da kika bari a gida kika fito yawan ta zubar shi ne kai ba ni ba, ka da ki sake ki kara sani a jinsin da ba nawa ba” cewarsa
Ta ce tana kama haba
” Ahh..daga shawara ‘yar Modu…wulakanci”
Ya ce
” Ba ki ga komai ba Alhaji Nafsin kira goma ya min duk don in nemo masa ke din in miki kafar baya na hada shi da wata sabuwar yankan raken ba wani sabon abu ba ne a gurina” Ta mika ma sa hannu suka tafa.
Ya juyo ga su Hindatu wacce tunda aka fara abun ta ke binsa da ido ya ce su biyo shi dakin suka bi shi a baya. Ya shiga bude wajen aje kayan sawa yana zaro su yana cewa
” To a tuttube a tuttube”
Ya juyo ya gan su kowacce a tsaye bata tube ba ya ce
“Yau ni ‘yar Modu na ga abinda ya isheni. Yo ina ruwana da tsarin halittar jikinku tunda duk abunda kuka mallaka ba bako na ba ne? Ni a duniya ba ni da abun kunya dayarku ta gwada shiga bayi yanzu na bi ta da soso da sabulu na cuccudeta kamar sabuwar jinjira wai menene a ido idan ban da ruwa?”
Haka dai suka yi wanka suka canja da kaya na alfarma. Duk cikinsu ba wacce ta taba saka irin kayan ko makamancinsa. Kowacce da kalar irin tata kwalliyar kayan ma mabanbanta kaloli ne. Shi da kan sa ya musu kwalliyar fuska ya kashe musu dauri. Ya gyaro gashin Rokaiyatou ya tazo shi har gadan bayanta. Sai ta ji ta kamar wata zinariya. Suka ji kan su yayi gingirin zukatansu sun yi fes. Kowacce tana ji kanta ita wata ce.
Yar Modu ya karewa halittar jikin Hindatu kallo ya ce
” Dankari! Wani kaya sai amale, wata babbar motar ai dole sai da babban direba. Wanda ya bar ki kika fito bariki ba karamin asara ya tapka ba. Mijin na ki barzahu ya sheka ko kuwa ma sauta ga wawa ce? Kai..Alqur’an daga gani ma sauta ga sakaran ce”
Sai suka yi dariya gabadaya. Daga gani sun soma sabawa da harkar kawali ‘yar Modu. Ya musu jagora zuwa babban falin Hajiya na kasa in da take mitin da wasu ciyamomi. Kafin su shiga ya ce
” wai me ma sunayenku ne? Suka fado ma sa ya kama baki ya ce
” Ya na ji kuna jero min su kamar sharuddan tuba? To daga yau kun koma Hindu, Luba da Rukky.
Daga ranar suka kulla wani kawance kawancen da sukai amanna ba zai taba tarwatsewa ba, wata amintaka ta ban mamaki! To sai dai me? Su ba masanan gaibu ba ne don da su masanan gaibu ne da sun roki Allah kar ya halicci wannan rana da ta za ta zame mu su mafari..mafarin gafalalliyar rayuwa mai cike da da na sani!
*****************************
“Shekarata hudu cur ina dadiro da Isyaku direban babbar mota a tapa, wani gari ne nan kusa da Habuja” cewar Ziza ” kwarankwatsa dubu ina ganin maza masu kishi ban taba ganin ya Isyaku ba. Zalamamme, mahandami ban isa ya ganni da manemi ba sai a nemi a bawa hanmata iska.
Fitowa ta yawon duniya kenen na hadu da shi ban waye ba ina farkon shigowata bariki tsumma gaba tsumma baya. Kar ki ce wani abu ne ya fito da ni da ya wuce auren dole.
Saurayina Audullahi tun na kuruciya muka yi alkawarin aure, toshi toshi kuwa na sa a karkashin gadon innata ba kya iya kirgawa ba. Ya kawo kudin na gani ina so, kudin gaisuwar uwa da uba da kayan sa rana har yake saura wata daya kacal aurenmu! Kwatsam ba sai ga wani Alhajin birni ba ya fito wai aure na yake so. Su Innata ba su duba tsawon shekaru da shakuwar da muka yi da Audullahi ba suka mayar da auren na wa kan Alhaji Akilu.
Irin halin da muka shiga ni da masoyina ba zai kwatantu ba. Abu ya ki ci ya ki cinyewa na gane idan na sake na zauna abunda zai hana a aura min Alhaji Akilu mutuwa. Daga ranar na tattara nawa ya nawa ban kare a ko’ina ba sai a garin Tapa. Dirata kenen Isyaku ya sauke lodi ya ce da wa Allah ya gama shi ba da ni ba.
Ban san kan dawar garin ba ni dai fatana na yi nesa da gida nayi nesa da auren dole sai ga shi na fado bariki tsundum! Isyaku ya zame min karfen kafa, qarma qarma.
Kar ki ce wata tsiyar yake tsinanamin, o’o o’o kudin hayar dakin da nake ne fa yake biya sai abinci da yake siyo min a wajen Tina, sai ‘yan sitturu da yake min idan an tashi ajo ajo, ko biki ko suna sai kuma kudin gudummuwa. Daga nan kar ki rage kar ki dada amma yadda kika san shi ya sai wa ubana ragon suna ya biya ‘yan fida idan gorinsa ya motsa.
Ta numfasa su kuma suka cigaba da zuba ma ta ido suna mata kallon talabijin
” Me akai akai dadiro? Dadiro ma da irinsu isyaku hoti ho. Sai ya zuba wata 6 cas! Bai ziyarci mai dakinsa ba, kwatsam rannan sai ba gata ba ta dira a dakinmu irin dirar nan ta mayaka.
Ashe duk kurin da isyaku ya kan yi duk ashe hotiho ne? Ashe hular ce kawai, a gida shi ke rike da muciyar. Ta tasa keyar shi ta tafi da shi ashe ashe ko kwayar shinkafa bai bar ma ta ba mu kuwa anan ba ma karin safe sai da ti da bredi har a soyo mana kwai a wajen Ilu mai shayi. Ai kuwa dana samu ya dawo sai da na rike shi wata takwas cas! Bai leka ko soron gidansa ba, anan na gwada ma ta sharrin tsohuwar karuwa”
Suka kwashe da dariya. Su hindu suka kura ma ta ido suna saurare kamar labaran karfe tara. Ziza ta ce
” Yanzun kuwa na daina wannan wahalar. Ai bari na gaya muku yanzu zamani ya canja ba a wani yayin ki kama gida a mararrraba, ko a gadar tamburawa ko a ibedi. Wannan na karamar karuwa ne me neman cikon canjin da za ta sa nama a miya ko ta dinke farfakken zani. Lo kilas karuwa kenen. Ke kuwa hai kilas abun yanzu duk ai gyara ne . Ya za a yi manemi ya zo wurinki ya gan ki a dan tsukakken dakin da bai ci albarkacin zanin gado ba ki ce zai biya ki da kyau.
Ai Yanzu matan da suka isa gidaje suke kamawa a manyan birane irinsu kano, kaduna , Abuja da legas. Gida na alfarma ga kayan alatu , ga situru na nunawa sa’a kin ga tun daga nan kin san meneminki ba zai wuce wani babban dan siyasa ba, ko gwamna ko dan majalisa ko babban manajan banki ko wani kasurgumin attajiri! Iya kalarki iya kalar sallamarki ‘yanmata.
Ni yanzu da kudi billahillazi bazan yi dadiro ba. Ka kankameni ka takureni akan ‘yan aninan da basu wuce na sha karan sigari ba. Yanzu ne zan yi waje rot da kai. Bazan dorawa kaina kwamfiyushan ba.Ai yanda kawai za ki fi gane lissafinki shi ne yau customer ya zo ya cake kudinsa gobe wani ya zo.
Luba ce ta ce to yanzu yaya za muyi mu fara fasowa gari? Kin ga dai daga zuwan mu wannan satin Hajiya ce ta hada mu da mutanenta ba ma mu fara fita yawo ba balle mu fara samo namu samarin.
Ziza ta murmusa ta ce
“Waye ya gaya miki ana zama haka sakaka? Duk karuwar da ta zauna ai sai dai ta zaunau. Ai idan kina da kyau kina karawa ne da wanka. Ku tashi mu tafi gidan malami na shi fa oya oya ne aikinsa kamar yankan wuka. Ai inda muka fi matansu na gida kenen , idan a tafe suke mu acan muka kwana!
Haka suka rankaya su ka shiga motar ziza, wata camry ce golden sai daukan ido take. Ziza farar mace ce ‘yar mitsil kamar kashin tsoro dauke da tsugunna- ka- ci doya daidai a fuskarta. Babu wanda ya san asalin sunanta ballantana daga inda ta fito. Ta fi shekara goma tana yawon duniya tana watangaririya har ta samu ta fado kungiyar Hajiya Kububuwa. Daga nan likkafar ta ta mike Ziza ba ta da tsoro ko na miskala zarratin. Wasu sukan yi gulmar wai ziza na bin kowane jinsi a neme nemanta amma har yanzu babu wanda ya adar da hakan.
Tana da wani tamfatsetsen gida a unguwar Garki da ke Abuja da wani tsohon maneminta ya mallaka ma ta, ya kuma dandasheta da sabuwar camry din da take hawa yanzu, duk da wannan bai hana an rabu baram baram ba. Haka suka rabu bai iya kwace ko asi ba , ‘yan shaida suka ce wai ziza ta shigar da sunayensa wajen ‘yan tsubbu sun rufe bakinsa ruf!
Ko ma dai ya batun yake ziza ba ta fasa harkokinta ba da wadakarta da naira. Yanzu ma taron Hajiya Kububuwa ne ya shigo da ita garin kano ta hadu da sababbin zuwa take karanto musu karatun karuwanci.
” Ban da so don Allah” cewar ziza a daidai lokacin da ta fara murza motarta akan titi ” babu wanda ya aike ki domin ko kin yi babu lada. Son karuwa ba ya wuce ta so abun hannun mutum ranar da ta raba shi da su sai kowa ya raba hanya. Abun duniya shi ake yi wa ranar kuwa da ya kare ai kowa watsewa zai yi. Kar ki sake ki ji tausayin namiji dan bariki shi ma ran da kika ci leda ( aids) tsakaninsa da ke kilometer dubu ce! Ba yace lalacewa yake so ayi ba? ai ke kina da gangar da za ki bugawa shedan kan sa kida kin ga kuwa idan kika bugawa mutum dole sai ya taka!
Daga nan suka iso gidan malamin. Ba wani boyayyen gida ba ne mai surkuki kamar yadda suka zata , gida ne na ginin zamani bulo da bulo. Suka shiga suka tarar da layi wajen mutum 7 suka zauna har aka zo kan su. Suka shiga sai su Hindatu suka yi mamakin ganin shi.
A tsammaninsu tsoho zasu gani tukuf zaune da kasa a gabansa amma sai suka sha mamaki. Saurayi ne mai jini a jika zaune a wani wadataccen falo. Ya sha farar shadda har da hula zanna bukar zaune a kan kujera mai cin mutum uku. Kafarsa a harde take ya rike wani dan littafi a hannunsa, fuskarsa kadaran kadahan. Suka gaishe shi a al’adance ya amsa ba yabo ba fallasa. Ziza ta ce
” Allah gafarta malam ga ni fa yau na dawo da wasu sabbin ‘yan kungiya. So nake a duba musu a ga ya tafiyar take? Ya za ta kaya (auzubillah) kamar dai yanda aka saba Allah gafarta malam. Sai kuma a yi musu shiri na makaman yaki”
Malam ya ce babu damuwa, ya tambayi sunayensu suka fada ma sa. Ya cewa kowaccensu ta zabi namba daga 1-20. Kowacce ta zaba. Sai Malam ya fara bude littafi.
Suka zuba ma sa ido kowacce da na ta tunanin har malam ya gama. Ya dago ya kalle su kamar koyaushe fuskarsa ba ta nuna alamun farin ciki ko bakin ciki ya ce
” Tafiyar guda daya ce, duk ta inda ku ka bi, ko ta yaya ku ka bi waje daya za ku isa, waje daya zaku kare. Akwai haske, akwai duhu akwai rasa rai!”
Daga nan bai kara cewa komai ba, sai kowa yake kallon kowa. Luba tayi caraf ta ce
” Allah gafarta Malam wanne ne farko?”
Ya ce
” Haske”
Sai tayi murmushi ta ce, komai yayi daidai.
Ziza ce ta karbi zancen da cewa
” To Allah gafarta malam sai kuma makaman yaki”
Ya dauko wani kwalli guda uku ya mika musu ya ce
” Wannan shi ne ” idonka idona”
Daga nan bai kara cewa komai ba. Ziza ta yi musu alamar su tashi, suka tashi bayan ta ajiye masa wani kulli. Suka tafi ba tare da kowa ya cewa danuwansa kanzil ba.
Har suka zo kwanciya ranar Rukky ta kasa cire maganar malamin nan a ranta
” Akwai haske, akwai duhu, akwai rasa rai!”
To wani ran za a rasa?????????
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
