Duniya ta – Chapter Seven
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Mutuwa mai yankan kauna, bakin takobi mai raba soyayya!
Niamey, Niger Republic
A shekara 18 babu wani namiji da zai daga ido ya kalli Rokaiyatou ba tare da bukata daya ta mamaye ran sa ba, na ya mallaketa har abada. Amma a zuciyarta mutum guda ne kacal! Frère Momodou. Idan da shi a duniya to ba ta ki sauran maza duk a hada ayi jana’izarsu ba wannan ba matsalarta ba ce!
Sau da dama takan yi tunani a duniya akwai irin Frère kuwa? Dan adam guda daya tal da zai iya maye gurbin dangi guda ya zama kamar uba? A so da kauna, tausayi da jin kai babu ya Frère duk duniya a hasashen Rukaiyatou. Shin wai da babu shi wata irin rayuwa za ta yi ita da Momma. Shi ya tsaya tsayin daka cin su, shan su, karatunta tun daga Ècole Elementaire har Ècole Secondaire.
A halin da ake ciki yanzu Momodou yana kasar Faransa a wani gari mai suna Montpellier. Ya gama digirinsa na biyu da dadewa amma fafur mahaifinsa ya ki ya dawo gabadaya. Ya dora shi akan al’amuransa na kasuwanci ba shi Faransa, ba shi Nigeria ba shi Niger.
Da gaske mahaifinsa yake bai son ya dawo, tsakaninsa da Niamey sai dai idan ya zo ziyara. Ya gama gane cewa duk kan maganar Rokaiyatou ke ya sa yake ma sa walagigi da rayuwa na kusan shekara biyar. Ko son yayi maganar aure ba ya yi ga shi shekarun sa sun ja. Da wannan aniyar ya dawo gida wannan shekara. Rokaiyatou ta gama Ècole Secondaire aurenta a yanzu ba gudu babu ja da baya!
Da wata safiya ne Rukaiyatou na tsakar gida tana tankaden garin tuwo yayin da Momma ke dinkin hula akan tabarma. Ta dube ta cikin farin ciki ta ce
“Momma sakamakon gwajinmu ya hito kuma na kokarta na san Frere zai nema mun Universete ko amren namu za a yi?”
Momma ta buga tsaki ta nuna ta da dan yatsa ta ce
” ke ki fita idona, ni ki ke yiwa maganar aure?”
Rukaiyatou ta kwashe da dariya ta ce
” To gwada mini wa nake da shi baya ga ke?”
Momma tayi dariya suka cigaba da hirarrakinsu a ran Rokaiyatou fal tunanin Momodou
A lissafinsa satin da wuce ya kamata ya zo, to amma har yanzu shiru. Sai ta yini sukuku ko me ya rike shi ga Faransa? Ta kwaso kwanukansu ta kawo bakin rijiya don ta wanke, ta hado da wata tsohuwar rikodar momma ta kamo gidan radio. Ta fara wanke wanke ta ji sun sako wakar Sogha Niger, wayyo dadi zai kasheta don tana son wakar dankwali. Ta fara bin wasu baitikan tana aikinta kamar da ita aka rera
A can da dauri,
An ka je yin wasa
‘Yanmata su sanyo kwalli,
Sauran sai su sa janbaki,
Sai a taru hilin wasa
Samari sai suna wilgawa,
Ka ga wacce ranka yake so
Hitilla ce ka ke matsawa
Rawa da waka rannan sai sahe….
Duk sallamar da ake yi ba ta ji ba, sai kamar daga sama ta ji an ce
“Bonjour!”
( ina kwana/ ina yini)
Ta dago da sauri tana mai kashe rikodar jin muryar Momodou. Kawai sai ta sa dariya cikin wata murya ta ce
“Frère!”
(Danuwa)
Shi ma ya sa dariya. Ta dago ta kare ma sa kallo ya sa riga mai dogon hannu fara tas da bakin wando. Takalminsa ma baki ne sau ciki daga ganinsa fes fes. Jikinsa ya nuna alamar hutu, da wata karamar jaka a hannunsa daga alamu ko gidansu bai shiga ba dirowarsa kenen. Da ta kare ma sa kallo sai ta ji gabanta ya fadi sai take ganin kamar ya fi karfinta.
Murmushi ya sakar ma ta ganin kamar ta fada tunani ya ce
“Comment allez-vous”
( ya ki ke)
“Je vais bien. Merci”
(Ina nan lafia.nagode)
Daga nan ta wancakalar da kwanunkan tana kwallawa Momma kira cikin murna. Ta fito tana kokarin daura dankwali tana yiwa Rukaiyatou fafan kwada mata kira sai tayi ido biyu da Momodou. Duka sai suka kwashe da dariya. Ya tsugunna a gabanta yana gaisheta ta dafa kan shi cikin farin ciki ta ce
” Mon garçon, saukar yaushe?”
Ya ce
” yanzun wannan tsal na zo”
Ta kama baki ta ce
” Ba dai ko gida baka shiga ba?”
Murmushi kawai yayi.
Ta ce
” A’a Momodou ba a haka, maza je ka gida su gan ka su ji dadi kai da ka dade baka zo ba? Ma za je ka abunka idan ka huta sai ka dawo mu gaisa a tsanake. Ai maganganunmu dayawa ko?” Ta karashe tana dariya
Shi ma dariya yayi ya ce “To”
Juyawa yayi zai tafi ya zo daidai kunnen Rokaiyatou ya ce a hankali
” ki tsumayi zuwana anjima, Au revoir”
Sai ta ji kamar ta bi shi don farinciki!
Momodou ya dawo bai dawo ba har kwana biyu shiru sai kan ta ya daure. Ita ba ta isa ta je gidan nan neman shi ba, ba za ma ta fara ba, wacece ita? Da kwana uku tayi shiru kawai sai ta dauki sakamakon jarabawarta ta mayar karkashin akwatinta.
Sai a kwana na hudu tana shara ta jiyo sallamarsa sai kawai ta share. Momma ce kawai ta amsa ta ce ya karaso. Ya karaso yana satar kallon Rukaiyatou ta dauke kai ya isa wajen Momma ya durkusa ya ce
” Kuna lahiya”
Ta amsa ma sa. Daidai nan sharar da Rokaiyatou ke yi ta isko inda suke zaune kawai sai ta sa tsintsiya ta sharo kafafunsa. Momma ta daka ma ta tsawa ta ce
” Menene haka? Ji min rashin hankali fa ni Ramlatu”
Rukaiyatou ta tsaya tayi sororo. Momma ta cigaba da fada
“Momodou ki ke sharewa? Wai duk haushin bai zo ba ne? Ko zamanki yake? Ku ji ni da ‘ya”
Idonta ya cicciko da hawaye ta dalla ma sa harara wani murmushi ya kufce ma sa ta kara kulewa. Maimakon ya kula ta sai ma yayi wa Momma sallama ya fita yana dariya.
Wai mai ma yake neman maidata? Sakarya ko? Kawai sai ta jefar da tsintsiyar ta shige daki a guje tana kuka. Momma ta kama baki ta na cewa
” hauka kawai”
Sai da daddare bayan sallar isha Momodou din ya shigo, ya tarar da su a zaune Rokaiyatou na cin tuwo. Sai suka dan fara hirarrakin yaushe rabo da Momma yana tambayar makarantar Rokaiyatou, ita dai bata saka musu baki ba. Can Momma ta ankara ta ce
” Ni ke kadai za ki ci ne ba zaki zubowa Momodou ba? Wani kalar bakin hali ne haka kika koyo?”
Kawai sai ta turo baki. Momma ta dauki mahuci ta kwada ma ta kafin ta kara ta gudu daki. Momodou dariya ya kama yi ya ce
” Momma ki bar ta ta ci tayi jiki”
Ta yi tsaki ta ce
” yarinyar nan ban san me ke damunta ba kamar mai aljanu”
Ya ce
” kale ta Momma shagwaba ta ka ji”
Ta kama baki tace
” Hauka dai”
Budar bakinsa sai cewa yayi
” um..um Momma Rokaiyatou ai bata hauka”
Tayi dariya ta ce
” Au shigar ma ta zaka yi, kun fi kusa ko? Ku yanuwan juna”
Yana dariya dariya yayi hanyar waje yana cewa
” Hakuri za ki Momma, kuskure an ka yi”
Kawai sai Momma ta shige daki ta tarar da Rokaiyatou tana cika tana batsewa ta sakar mata rankwashi ta ce
” ki je na san yana jiranki a waje. Don rashin ta ido shi za ki wa rowar abinci? Don iyayenki wa ya kawo?”
Tayi rau rau da ido ta ce
” gori ne?”
Ta ce
” An miki gorin ke ai ba ki da dubara. Don bai shigo ba ki ke fushi? Kin ga yaron nan abinda zai hana shi shigowa sai Allah. Daga ganin idonsa akwai damuwa bana son takura shi ne ga fada. Amma ke dan rashin hankali kin dau fushi. Ba za ki tashi ki je ki jiyo ba ko sai na yo kan ki?”
Rukaiyatou ta fice tana dariya.
Dama soron na su akwai duhu, ta fara wucewa sadaf sadaf. Kawai sai ta ji an kurma wani irin ihu, ai fa nan ta zubar da takalmanta ta fice waje a guje ciki rudu. Tana isa waje ta ga Momodou a bakin kofar ya rike ciki yana dariya, nan ta gane shi ne sai tayi murmushi. Ta ce
” Wannan ai zalumci ne”
Ya nemi wani dan dakali ya share ya zauna yana karasa dariyarsa daga karshe ya ce
” pardonnee-moi!”
( ki yafe ni)
Ta samu waje ita ma akan dakalin ta ce
“Je pardonne”
(Na yafe)
Sai yayi shiru na wasu dakiku sannan ya ce
” Akwai damuwa Rukaiyatou, akwai damuwa”
Gabanta ya fadi ta tuna da maganar Momma ta ce
” Me shi faru Frère? Zucciyata bugu takai!”
Ya kama kan shi ya sake sannan yayi murmushin dole ya ce
” Dauko sakamakon gwajin naku tukunna in soma da wannan duk da dai na san abunda ke ciki akwai”
Da saurinta shiga ta dauko ta kawo ya duba cikin farin ciki. Ya ce da turanci
” Excellent! Thats my girl. Yanzu sai universete kenen ko?”
Ta yi rufe fuska tana dariya ta ce
” Ai Abdou Moumoni universete zan ke zawwa ko?”
Ya kalle ta sakaka ya ce
” Wa ya hwadi miki?”
Ta ce
” Ai ka shina dai ina sha’awal aikin jarida”
Yayi murmushi kawai yana nade takardun ya ce
” Ai ba a garin ga ma za ki yi ba Rukaiyatou”
Ta kura ma sa ido tana kokarin gane manufarsa. Ya ce
” Na samu wani aiki a Nairobi bar musu komai zan yi Rokaiyatou. Mu yi amre mu tai abinmu a can za ki karatu. Buri hwa gareni kan ki!”
Tayi sauri ta dube shi maganarsa na taba ranta jikinta yayi sanyi. Ta ce
” Haka ni kwanta ma cikin zucciya?”
Sai ta sunkuyar da kan ta. Me gareta cikin mata da Momodou ya ware ta ya daukaki rayuwarta haka? Allah Al Hakeem Allah Al Kareem.
Ya dawo da ita daga duniyar tunani ya ce
” Daga ke har Momma dauke ku zan na bal Niamey da ku. Momma zan maisheta gurin danuwanta, a shiryasu ina ga hakan zai fi. Shekarun dayawa, Na gaji da ganinku a wannan rayuwar. Ban san me Abba ke nuhi game da ku ba. Ashe dan danuwanka ba da yake gareka ba?Ashe haka amana take a zuciyal mutane? A ce ke kike yin kwana a wanga kangon gida mu kuma muna kwamci cikin kayataccen gida irin wanga? A ce ke ki kan yi cima irin wacce ki kayi mu muna cikin wadata sai wacce mun ka zabi? A ce yawo kika yi ba wanda zai nasa ki ga Lècole?”
Nisawa yayi muryar shi na rawa zuciyarsa na mamakin mahaifinsa. Momodou mutum ne mai tsantseni zuciyar shi mai kyau ce ba ya son duk wani abu na zalunci. Bai taba goyon bayan mahaifinsa ba kuma yana gaya ma sa gaskiya sai ya shure. Amma yanzu dai ya ri ga ya yanke hukunci game da rayuwarsa ,lokaci yayi.
Ya cigaba da cewa
” Na sha kai kararsa ga Baffaninsu na Tillaberi, sun yi sun yi ya ki ji. A tammanina yanzun ga idan ubanki ya hito kabari zai yahewa Abba? Dukiya ya danne wannan shi a amana? Tausayim shi nikke, ina ya ka zuwa da hakkinki?”
Gani tayi idonsa ya cika da kwalla sai ta ji kamar ta sa kuka. Ta ce
” Frère, yazunga ban yi butulci ga
Allah ba idan na hidi ban yahewa Abba ba bayan shi ya haihe ka? Babu wani mutum bayan uwata da ya darajantani kamal kai. Idan Allah bai nihe ni da yin uba ga Abba ba ga tammanina ai ya maishe mini da kai! Momodou rayuwar duniya hwa ba komi ba ce, watarana hwa sai labari!”
Ya mike tsaye a dake kamar ba shi ne idonsa ya kawo ruwa ba dazu. Ya ce
” Inaa..inaa Rukaiyatou wannan ba batu ba ne. Lamarin akwai zalumci ciki. Dole ne na sama miki mahita shi ya sanya kwana biyu ba ki ganni ba. Na riga na budewa iyayena zucciyata. Je suis amoreux! I’m in love! Yanzun ga rikici ne a gidanmu. Wai mi ne tattare da ke da anka hwadin bazan amre ki ba?”
Sunkuyar da kan ta kawai tayi. Wasu abubuwan duniya ba su da cikakken bayani. Suna nan ne kamar yadda suke, kamar yadda aka halicce su su zama!
Ya ce
” Ko da yake duk yanzun ba wannan ba ne. Amre kam sai an yi karshen satin ga. Nijeriya zamu wuce, mu kai Momma gida. Na yi wa Mustapha magana za a je ai maki fasfo a sanya visa da sauransu. Ta Najeriya zamu tahi shi zai kula da komai”
Ita ma tsaye ta mike cikin damuwa ta ce
” Ni dai bani so ka samu sabani da uwayenka”
Cikin zafi ya ce ma ta
” ke kin ga babu wanda ya ce ke zaki shiga. Kawai suna da akidojin da ni ban aminta da su ba. Abba na yana matukar kamnata ko ya yi hushi zai sabko!”
Ta jinjina kai. A ranta akwai tsantsar tsana ta Iliyasou Tillaberi amma sai ta share ko a fuska bata nuna ba. Sai tayi murmushi, kai a rayuwa tana kaunar Momodou ta ce
” Toh shikenen Frère yanzunga ta ina za a fara?”
Yayi dariya yana kallon cikin idonta sa’annan ya ce
” On se marie Rukaiyatou!!”
( Aure za mu yi Rukaiyatou!!)
Kamar wasa rigima ta balle a gidansu Momodou. Duka ‘yan gidan suka juya ma sa baya ba su son aurensa da Rukaiyatou. Hajiya Khulsomou ta dau zafi ta zage shi tas sannan ta ce za ta iya tsine ma sa idan bai yi hankali ba. Abba Iliyasou kuwa cewa yayi idan shi ne zai daura auren to kuwa har abada ba zai daura ba.
Abinda ke ran Iliyasou Tillaberi guda daya ne. Tun yanzu Momodou na ma shi fito na fito akan yarinyar ina ga idan ya aureta? Ya san babu dadewa yarinyar za ta hure ma sa kunne ya karbo ma ta dukiyarta. Momodou zai iya juya ma sa baya zai iya rusa ma sa ajandarsa na girma da fadadar dukiyarsa da bude kamfanunnuka da zasu girgiza duniya.
A halin da ake ciki yana kokarin bude hedkwatarsu a Najeriya. Muddin ya samu ya cimma burinsa to za a fara ambaton I.A and son’s a mujallu ma su kawo rahotani na masu kudin Afrika! Ba wuya zai fada nan. Yana bukatar ‘ya’yansa biyu su taimaka su talkafi burinsa. Idan aka zare gadon Rukaiyatou to ai ya koma baya shi da Ahmadou 50-50 suka yi amma wa ya sani idan banda shi? Idan yarinyar nan ta so ta fara bata ma sa burika to lallai zai iya sa a batar da ita!!
Kan momdou ya dau zafi yana ganin kamar ba ai ma sa adalci ba. A cikin satin ya shigo gidansu Rukaiyatou da shirin tafiya ta ce ma sa
” Frère ina ka ka zawwa?”
Ya ce
” Nijeriya “
Ta ce
” Ikon Allah ,wajen wa?”
Ya balla ma ta harara ya ce
” Ba ki min kara ko? Ina da uwa can da soba amma ba ki cewa na gaishe su. Ba ki neman ‘yanuwanki”
Dariya tayi ta ce
” Ni fa baki nake jin su, ban ga suna zawwa ba”
Ya ce
” Gaskiya ne. Kin san tsakanin uwata da uwal Mustapha akwai rikici tsakani. Da muna kankana kowa yana zawwa, sa’ilin kina kankanuwa sosai. Amma yanzun ga lamarin ya baci. Amma fa ni Hajja Hadiza bata nunamin kiyayya. Shi ya sa ma na kan je. Mustapha soba na ne, aminina duk ‘yan gidamu wa wanda nake kamna kamar sa. Da shi ni ke shirin komai. Sau biyu fa yana zawwa Montepillier ko iyayenmu basu so mu kuwa ma yi zumunci. Labarinki ba wanda bai sani ba. Yanzu zan je Nijeriya tare muka dawowa. Bari ma ki ji na kiraye shi a tarho”
Sai ya dauka waya a aljihunsa. Rukaiyatou ta bi shi da kallo tana mamaki. Tana dai ganinta hannun mutane ta baza gari amma bata taba magana a ciki ba, to ita a wa? Ita abun ma tsoro yake ba ta. Ta ji momodou ya ce
” Alo..ga kamnata ku yi magana”
Yana sa ma ta a kunne. Ta ji an ce
” Hello..Helloooo”
Ai kawai sai ta wurgar da wayar ta fyalla daki a guje! A irin labaran da suke ji wani an ce daga wayar nan aka zuke ma sa jini. Nan ya fadi matacce. Momodou yayi ta ma ta dariya yana cewa
” Wanga yarinya… an yi ‘yar kauye. Bari goben wannan tsal na sai miki tarho”
Kwanan Momodou uku a Nijeriya ya dawo, daga isowarsa gidansu ya shigo. Ta ji yana gaisawa da Momma sai ta fito da sauri daga daki ta ce
” Ina bakon namu shi ke?”
Momma ta ce
” ya tai koyo gaisuwa”
Suka sa dariya Rokaiyatou ta ji kunya ta koma daki. Ya fita waje sai ta bishi daga baya. Tana leke leke yayi dariya ya ce
” Za shi zo cikin sati. Mun yi wata shawara ne zan dawo gobe ni gaya miki.”
Ta ce
“To”
Suka yi sallama.
Shigarsa gidan ya tarar da iyayen na sa zaune a falo. Uwar ta cika ta cika tayi fam. Ta fara bala’i
” Ka tahi gurin uwal taka ko? Momodou kahiya gareka. Su wadannan din su sunka lashe kurwar kanin mahaihinka. Sai sun lashe min kai Momodou..Maita ke gare su!”
Cikin bacin rai ya soma cewa
” Habaa…”
Ta katse shi da salati
“Sun baka cikin ruwa ka sha ko? Oh ni Khulsomou na haihwa wa Ramlatu da, wani irin bala’i ne haka?”
Uban take kallo kamar ya samo mafita. Ya kurawa Momodou ido ya ra sa yanda zai yi da shi. Yaron ya cika taurin kai. Tabbas wadannan mutane suna da siddabaru kar su je su lahanta mishi da a banza, amma shi ya kasa ganewa.
Cikin wata irin murya ta isa ya daure fuskarsa tamau ya ce
“Momodou”
Ya amsa da
“Iye”
Ya ce
” Ban san ga ina ka sami kahiya ba. Da tammanina da fari kana zuwa gidan ne don kana tausaya musu. Ni ban taba tammanin wai amren yarinyar ga ka ke bida ba. Wace tsiya ke ga zuriyar Ahmadou? Hakkina ke wahal tasshi .Da zan gaya maka tsakanina da shi da sai ni gaya maka hakki na ne ya dauke shi. Mutum ne mai tulin zalumci. Ka ga wannan mata tasa da kake gani ai shedaniya ce danginsu dangin maita ne. Idan ba ka yi a hankula ba yarinyar ga sai ta zamo ajalinka! Kamal yadda tayi ajalin ubanta! Ka shiga hankalinka fa Momodou!”
Takaici ya cika shi amma sai ya hadiye cikin murya mai tausayi ya ce
” Abba ka dubi girman Allah ka dubi zumuntal da ke tsakaninku da mahaihinta ka yi hakuri. Jininmu ne su ko me suka mana mu yahe. Shi kan sa ubanta yau ina shi ke? Idan ba ma yahiya ya Allah zai dube mu ya yahe mana?”
Kawai Hajiya Khulsomou sai ta fashe da kuka ta mike tsaye ta ce da uban
” Wallahi Alhaji kar ka aminta da amren nan don wataran sai Momodou ya hi karhinka. Shikenen na shiga uku da dayan nawa namiji tilo za a salwantal mun da shi”
Ran Iliyasou Tillaberi yayi masifar baci. Zance daya ya ki ci ya ki cinyewa? Shi za a tsaya ana yiwa gardama? Fuskarsa a murtuke kamar hadari ya karashe zancen da cewa
“Kai tsaya ka ji ba lallashinka nake ba da zaka nuna min iyawa. Na rantse da kur’ani izifi sittin idan dai ni zan damra maka amre da wanga yarinya wallahi ba zaka amre ta ba. Daga kai har ita ai kalkashi na ku ke. Idan ta samu miji za a damra mata amre amma ba da kai ba. Lalataccen yaro kawai!”
Daga nan ya fice ran sa yana raya ma sa dole ya kora shi wata kasar su kuma ya dauki mataki akan su. Hajiya khulsumou ta kudurta a ranta abun nan ya zo karshe , dole ta yi musu gargadin karshe. Da haka aka bar Momodou cike da tunanin zuci.
Washegari kuwa Hajiya ta yiwa gidan na su dirar mikiya. Ba tayi sallama ba wasu kwanuka ta tarar a gefe tayi ball da su. Hakan ya fito da Maman da sauri sanin ba kowa ta aiki Rukaiyatou. Sai suka yi ido biyu.
Kowa na kallon kowa. Mamma na kallon irin shigar alfarmar da Hajiyar tayi ta nunawa sa’a. Tana tuno irin dadin da Ahmadou ya jiya ma ta amma yau saboda wadannan azzaluman ji ba yanda rayuwarta ta koma.
Hajiyar tayi ma ta kallo makaskanci ta ce
” Ramlatu kar ki min iya shegenku na Ingilishi gargadi kawai na zo in ma ki. Da ke da diyarki ku nisanci Momodou. Ko ya rasa mace kasar Niger ba zai amri wacce ta kashe ubanta ba!”
Hakurin Momma ya kare ta ce
” Yanzu ke Hajiya duk hakkinmu da kuka danne na shekara da shekaru ni ban je na ni ban je na tsare ki na ci mutuncinki ba sai ke za ki tako har gida ki zage ni?”
” To mi ne in an zage kin? Ke nan har wata abu ce muguwal mace kawai mai nacin tsiya. Da kina da zucciya da tuni kin koma kasal ku. Kurwar Momodou ba zata lasu ba, ‘yan kaniyal uwa!”
Har ta fita tana zage zage. Momma ta zauna kan tabarma tayi shiru tana tunanin wacce zata fissheta. Gorin da aka yi ma ta yau ya taba ta. Najeriya za ta koma!
Momodou da Rukaiyatou ne suka shigo suna dariya ganinta tana hawaye ya sa jikinsu yayi sanyi. Suna ta tambayarta me ya faru. Ta gaya musu abinda ya faru ga kara da
” Momodou ina so na gaya maka wata magana, ka hakura da Rokaiyatou. Iyayenka sun dage ba sa so, gwara duka mu hakura. Najeriya ma zamu koma, gwara na je duk abinda danuwana zai min ya min. Wannan rayuwar ta isa haka. Gorin da aka min yau ya sa na ji dole na kima kasata ko da ba za a karbeni ba son nan ne asalina.”
Ta share hawaye
” Kayi hakuri Mommodou wani lokacin ba mutuwa ce kadai take yankan kauna ba duniya ce take raba masoya. Ko babu mutuwa wataran sai ka ga an raba wajen zama!”
Rukaiyatou ta fashe da kuka ta rungume Momma. Shi kuma ya kura musu ido, zuciyar shi sai bugawa take. Ya daure ya ce
” Najeriya ko? Ita kike so? To ku tashi ku hada kayanku.” Ya ciro wasu kudade a aljihunsa ya ajiye ya ce ” ku sayi abinda kuke da bukata yanzun tsal zan je na dawo”
A guje ya fita Momma na kwalla ma sa kira bai waiwayo ba.
Rukaiyatou ce ta fita a guje ta bi shi daidai lokacin da yake kokarin jan motarsa ya dakata da ya ganta. Ta ce
” Frère ina za ka?”
Ya kalleta a tsanake kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce
” Amre za a damra mana”
Ta kura ma sa ido ta ce
” Aa ba za a yi haka ba. Momodou kar mu zo mu janyo abunda Abba zai yi hushi da kai. Idan mu ka dangana gaba idan Allah ya rubuta da amrenmu sai ka ga mun yi”
Wani duban takaici ya ma ta, ya fito daga motar a fusace ya ce
” Ashe ba ki hankali? Ni ne zan zauna jiran tammani akan amrenmu? Yanzu na hwahimce ki. Dama ba kamnata ki ke ba. Ni ne dai nake shiririta ta. Don mai kamnalka mai hwatan kuyi rayuwa tare ba zai ce ka tsimayi dogon lokaci ba kahin kuyi amre.”
Ya buga wani uban tsaki zai wuce ta kamo shi tana kuka ta ce
” Haba Momodou ya zaka min mummunal hwahimta irin haka. Wa nake da alaqa da shi kamal kai. Ina guje maka hushin iyaye ne wanda duk mai kamnal ka ba zai taba kamnal ka hwada halaka ba”.
Sai yayi dariya ya bubbuga kafadarta ta dama ya ce
” kwantar da hankalinki kamnata, babu abunda zai faru. Duk wata mishkila da zata faru bayan an damra amren nan ne. Yanzun tsal daga nan tillaberi zan shige. Ai ba su suka haihi kan su ba, baffaninsu na raye. Tunda ni da ke tushe daya ne, kin ga abun ya zo da sauki. Su zasu yi mana walittaka su damra mana aure. Wuyalta in dawo komi dare zamu bar garin ga Nijeriya zamu shige.”
Sai ta kura ma sa ido, sai ta ga kamar ya canja ma ta. Wani irin farinciki yake ciki marar misali. Wai kuwa a duniya akwai mai kaunarta kamar Momodou?
Ya katse ma ta tunani da ya daka wani uban tsalle ya ce
” Yau zan zama angonki Rukaiyatou!
Suka fashe da dariya
Sai ya fara ja da baya yana karkada ‘yan mukullayensa cikin farin ciki ya ce
” Tu es la femme de mes revès Rukaiyatou”
( ke ce macen rayuwata Rukaiyatou)
” Je ne peux vivre sans toi” ( bazan iya rayuwa babu ke ba)
Sai ta kama dariya ranta fari kal! Ta ce
” Nima, je ne peux vivre sans toi momodou! Kai ma ka sani”
Ya daga ma ta hannu ya shiga mota sauri sauri gudu gudu. Har ta juya za ta shige gida ya kwalla ma ta kira
” Rukaiyatou!!!”
Ta juyo da sauri. Sai ya fada ma ta wasu kalmomi da masoyan faransa kan fadi
” Je suis amoreux!”
(Ina cikin so/ im in love)
Rukaiyatou ta shiga gida da gudu cikin farin ciki ta tadda Momma har yanzu a zaune.
” Me yayi miki dadi haka?”
Ta tambaya ganinta cikin annashuwa. Sai ta labarta ma ta yanda suka yi da Momodou. Momma ba ta kasa cewa kkmai sai maimaitawa take
” Mommodou yaro ne, Mommodou yaro ne”
Jikin Rokaiyatou yayi sanyi ganin yadda Momma ta yi. Sai kawai Momman ta tashi ta soma tattare kayanta. Rokaiyatou ta kwashi takardunta na makaranta da yan kayanta kadan ta hada a waje guda. Suka zauna jiran Momodou. Wani jira mai tsawo irin na daren mutuwa!
An dauki tsawon lokaci tun Rokaiyatou na lissafin dawowar Momodou har ta bace wajen lissafi. Ina angonta ya shiga? Ta san i yanzu dai an daura. To ko a Tillaberin ne ba a yarda ba, gabanta ya bada dam!
Hankalinta gabadaya ya ki kwanciya ta fita leko waje ya fi a kirga. Dare ya fara yi Momodou shiru dukkaninsu sun yi cirko cirko. Suna zaune nan kan tabarma ta fara gyangyadi ta ji wata gigitacciyar hayaniya ta ban al’ajabi.
Dukkansu tsayuwa suka yi firgigit. Momma ta ce
” Ba lafiya ba, daga ji ba lafiya ba”
Ba ta rufe bakinta ba aka wurgo wani katon icce tsakar gidan yana cin wuta. Ai sai syka samu kan su suna falfalawa fa gudu waje irin na ceton rai.
Abinda ya gigita su ya kuma daure musu kai shi ne dandazon da suke jiyo hayaniyarsu ba fa a koina suke ba sai a kofar gidansu. Taron mutane ne wanda fadar adadinsu sai dai kayi karya. Kowanne rike da makami da itatuwa suna cin wuta.
Rukaiyatou ta kankame Momma da kokarin janyota su koma cikin gida sai din hakan ya gagara inda ba tayi aune ba ta ji an yi musu wata fincikar alkafira an wurgo su tsakiyar taron.
Ba su san yanda aka hau ba ballantana yadda za a sauka aka rufe su da wani irin duka ta ko’ina. Maganganun da mutanen suke fada Rukaiyatou ta kasa tantance su sai dai jimla daya
” galla mayu ne, ku kar musu”
Sai da aka yi musu ligi ligi don momma ma ta ri ga da ta sume. Rukaiyatou ta cigaba da ganin dishi dishi har ta gano surar Abba Iliyasou yana sharbar kuka a gabanta. Hajiya Khulsomou na birgima a kasa tana ihu da kuka tana tsinewa Rukaiyatou.
Iliyasou Tillaberi ya cakumota kamar zai balla ya kifa ma ta mari. Ya ce cikin kuka
” Ki ka kashe mun diyana ? Ki ka kashe min Momodou kamar yadda uwalki ta kashe Amadou. Allah shi tsine muku!”
Duk da Rukaiyatou ba wai ciki hayyacinta take ba ta gano maganganunsa. Abinda ya cigaba da daure ma ta kai bai wuce jin cewar wai ta kashe Momodou ba. Wani Momodou din wai? Na ta? Momodou mijin aurenta? Ba dazu suka rabu ba ya tafi a dauro musu aure? Shi ne za a ce ya mutu? Ba ta kara gane wa komai sai da taji muryar Abba Iliyasou yana gaya wa taron cikin kuka
” Mayyu ne! Su sunka kashemin danuwana. Ta dage sai ya amreta a hanyal bidar amren ya mutu”!
Sai a lokacin kwanyar Rukaiyatou ta dawo da doka da oda kawai sai jin ta tayi ta tashi ta ruga a guje ba don ta san dalilin yin hakan ba. Wani ne ya fincikota.
Wata hauka ce take ji a kanta ta wucin gadi. Sai ta ji tana so tayi kuka
tana kuma so tayi dariya. Wata gigita ce ta shige ta ta jin wai Momodou ya mutu. Kuma wai ita ake zargi saboda ana musu sharrin su mayu ne.
Bata san ko ita mayya ce ko ba ita ba ce amma fatan da take shi na ka da a sassauta ma ta. Ta dalilinta Momodou ya rasa ransa ko da ta lashe kurwarsa ko bata lashe ba don haka ya cancanta ta mutu. Wai me yasa ake gudun mutuwa? In dai a irin rayuwarta ne da babu Momodou to kuwa mutuwa abun ai wa lale marhabin ce! To ta zauna duniya tayi me?
Mutuwa mai tonin asiri, dama haka take? Haka dacinta yake? Ta ji wani abu yana yawo tsakanin makogwaronta da kirjnta ko makiyinta ba ta fatan ya ji. Ina ma daya daga cikin masu hayaniyar nan ya daga takobi ya caka ma ta. Ko ta je ta hadu da Momodou a wata duniyar!
Hayaniyar ta cigaba da juya ma ga kai. Can sai ta ji ta dauke wuta dif.!
Ta bude idonta a hankali bata gano inda take ba sai ta mayar ta rufe. Ko bata tambaya ba ta san nan ne lahirar da ake ambato. Ta kara bude au sai anan ga lura aahe ba ita kadai ba ce mutane biyu ne tsaye a kan ta. Daya yana sanye da kayan likitoci daya kuma irin na masu aikin hukuma.
Suka ma ta sannu ta amsa a hankali, likitan ya fita dayan ya ce
” ya jikin na ki?”
Ta kalle shi sosai amma ba ta gane shi ba. Amma ta gane ba dan kasar su ba ne saboda yanayin hausarsa. Ya ce
” Mamanki ma tana kwance ta samu bacci “
Aai a lokacin ta ji hankalinta ya kara kwanciya. Kamar ya san abinda take tunani ya ce
” Nan asibiti ne ni ne na dauko ku na kawo ku. Ki kwantar da hankalinki. Ta kasa cewa kanzil illa dai ta kura ma sa ido. To idan nan asibiti ne kenen ba ta mutu ba? Kenan ba zata je ta tarar da Momodou ba? Shikenen labarin ya kare an rufe littafin kaddar. Kawai sai ta soma kuka, kuka mai yawa da ba ta fatan ta sake irin shi a duniya.
Mutumin nan ya tsaye a kanta har ta kare kukanta ba tare da ya ce ma ta kanzil ba. Ya cigaba da latse latsen waya a hannunsa. Kwanansu biyu a asibitin ya zo ya dauke su ya kai su wani gida. Ya tara su ya ce
” Ni sunana Asp Mukhtar Badamasi. Ni mutumin kasar Nijeriya ne. Na san za kuyi mamakin ganina cikin lamuranku bayan ba ku sanni ba. Ina karkaahin wata kungiya ne ta kare hakkin dan adam sai bincike da sanin makamar aiki ya kawo mu kasar Niger.
Kwanana uku a garin nan aka kawo mana rahotan da aka yi don neman tozarta wasu abun har yana nema ya zarce da kisa. Allah ya taimaka muka iso duk da dai an kusa makara. Amma so nake mu san menene ainihin matsalar because saboda irinku irinku muka bude wannan kungiya. So nake na san gundarin al’amarin don mu san yanda za a shawo kan matsalar.
Momma ce ta kwashe labarin komai ta gaya masa tana kuka. Ta karasa da
” Na rasa tun farko abunda muka yiwa Iliyasou mai zafi..na rasa wannan kiyayya”
Wani mamaki da ban haushi ya mamaye zuciyar Asp Mukhtar a fusace ya ce
” In this era? A wannan zamanin a wannan lokacin da ilmi ya shigo a ce har akwai still masu duhun kai da canfe canfe da zasu tara mutane wai duk dalilin maita? This is absolute nonsense! Za mu neme shi yanzun zai ga sammaci sai an bi muku hakkinku.”
Momma ta girgiza kai tana murmushin takaici ta ce
” Ka san wanene Iliyasou Tillaberi kuwa? Kar ka soma dan ba zan iya yaki da shi ba. Yakin da ba shi da amfani mu zo muna wahalar da kan mu daga baya ya zo ya sa a daure mu ko kashe mu. Ka bar shi ma ya ji da mutuwar gudan jininsa..innalillahi wa in a ilaihirrajiun Momodou ka bar ni da miki!”
Tayi kuka tayi kuka har ta gaji sannan ta ce
“Ni yanzu taimako daya za ka min ka mayar mu gida Najeriya in roki danuwana gafara. Zaman Niger ba na mu ba ne!”
Rukaiyatou ba ta ce komai ba magana wahala take ba ta. Tunaninta daya ne
” Za ta dau fansa, ga mutumin da yayi wa rayuwarta kisan gilla, yayi mata kaca kaca saboda fin karfi. Ya handame ma ta dukiya ya bar ta tana watangaririya a duniya babu gata. Tana jiran wata rana ta daukar fansa akan Iliyasou Tillaberi.
Asp yayi iya yanda zai yi ya roke su su amince da shawararsa suka ki. Ya alkarwanta musu mota da zata kai su har cikin garin kano a haka aka kwana.
Washegari mota ta iso ya rako su har bakin motar. Ya ce a raka su tsohon gidansu su dauki abubuwansu masu muhimmanci wanda ba su kone ba. Har suka ce aa sai Rokaiyatou ta tuno takardunta na makaranta, ta ce a biya zata dauka. Duk abunda ake idonsa na kan Rokaiyatou. Sai yakan lalace a kallonta yana tunanin idan ta samu ingantacciyar rayuwa yanda za ta koma. Sai ya raya a ran sa cewa ina ma zasu yarda ya taimake au irin taimakon da yake niyyar ba su. Yana kallo suka kama ganya bayan ya taimaka musu da kudin guzuri.
Cikin ikon Allah suka biya ta tsohon gidansu takardunta da ta hada waje daya suna nan ba abunda ya taba su. Ta dauka tana mai fatan kar Allah ya kara dawo da ita garin Niamey.
**********************************
Kano, Nigeria.
Sai da suka kwana suka yini sannan suka shigo birnin kano. Jalla babbar Hausa, kano tumbin giwa yaro ko da mai ka zo an fi ka!
Momma ta kwatanta gidansu wanda ya zamo gadonta ita da yayanta a unguwar kawo. Har ta mutu ba za ta taba mantawa ba duk da sauye sauyen da aka samu.
Lokacin da suka iso kofar gidan sai jikin Momma ya kara sanyi tana fargabar shiga saboda abubuwa da dama. Na farko irin rabuwar baram baram da aka yi, na biyu gidan ta ga ya kara lalacewa. Tun da can yayan na ta a saninta ma’aikacin wani kamfanin inshora ne, ta san yana cikin rufin asiri. Amma shekaru sun ja komai kan iya faruwa.
Ta fito daga motar da kyar saboda ciwon da ke kafarta Rokaiyatou na bin ta a baya. Akwai wani shago a kodar gidan wasu na zazzaune akan benci tsayuwar motar ya sa hankulansu ya dawo kan su. Momma ta dingisa kafarta tana dosar gidan sai ta hango wani shi ma yana kokarin shiga sai aka yi cirko cirko kowa yana yiwa kowa kallon sani. Ya nuna ta da danyatsa cikin mamaki ya ce
” Wa nake gani kamar Ramlatu?”
Maimakon ta ba shi amsa sai ta fashe da kuka tana mai durkusawa daidai kafarsa ta ce
” Yaya ni ce..ni ce Ramlatu ..ka yafe min..innalillahi wa innailairrajiun!”
Tana kuka yana kuka ya mikar da ita ya ce
” Tashi mu shiga ciki yau ai ranar farinciki ce”
A tsakar gida matarsa Harira ce ke alwala a bakin famfo ta gama tana kokarin daura dankwalinta maigidan ya shigo yana sharbe. Gabanta ya yanke ya fadi ta dafe kirjinta ta ce
” Baban Ali lafiya?”
Ya share hawayensa ya ce
” Addu’ata ce ta karbu yau, Allah ya dawo da Ramlatu gida. Allah nagode maka”
Harira ta bi su da wani lalataccen kallo na kaskanci sannan ta ja wani matsiyacin tsaki ta ce
” Amma baban Ali ka dau alhaki na, ni na zata wani babban alamari ne ya faru nake kokarin jajanta ma ka. Sai ka ce fitsararriyar kanwarka da ta guje ka akan auren mai kudi, ta kare mata ta dawo gida. Ai mu tuni muka samu labarin miji ya mutu bai bar mata ko sisin kwabo ba. Shi ne yanzu ta dawo? Har da guzurin ‘ya? Gaskiya Ramlatu kin yi karkon kifi daga ruwa kin koma wuta!”
Wani abu marar dadi ya saukarwa Momma a rai. Harira ba bakuwarta ba ce ta san ta sarai, sai ta sunkuyar da kai. Ba ta ce komai ba.
Baban Ali ya dubi Harira cikin in ina ya ce
” kin..ji..kin.ji..ko Harira bana son diban albarka. Mutane sun diro yanzu sai ki sauke su da rashin mutunci. Haba Harira..Haba.”
Ya shigar da su wani falo jikinsu a sanyaye. Rukaiyatou sai rarraba ido take gani take matar nan za ta musu duka. Shi ya kawo musu ruwa ya sa aka siyo musu abinci don babu a gidan, Harira na tsakar gida tana habaice habaice.
Bayan sun nutsu ne aka yi hirar yaushe gamo. Suka yi labarin rabuwarsu aka yi kuka aka share hawaye aka yafe wa juna.
Yayanta na ta ya labarta ma ta shekarun baya aka kore shi daga aiko ba fansho ba garatuti. Yanzu ma gidan naau ya raba shi kashi uku ya bada hayar kashi biyu. Baya aikin komai sai buga buga Harira ce kashin baya gida don iga ke sanaar waina take kuma sayarda kayan masarufi. A haka har aka samu aka tura babban dan na sa Ali zaria yake karatu. A ranar dai a wannan falon suka kwana.
Dakin da ke tsakar gidan anan Harira ta zuba kajinta take kiwo. Baban Ali ya sa kafinta ya nemo tsohon silin ya raba daki biyu domin Harira ta ce ba ta ga uban da ya isa ya kwashe ma ga kajinta ba. A wannan rabin dakin anan Momma da Rokaiyatou suka koma zama.
Wata irin rayuwa suka fara marar kan gado. Sai Rukaiyatoh ta kasa ganewa shin acikin halittu akwai marar imani irin mutum dan adam? Ita dai Momodou kadai ta sani mai imani shi kadai ta sani mai taimako amma ragowar duk kyamatar talaka garesu. Wai shikenen idan baka da shi da kai da banza duk daya? Mutane suna tuna lahira kuwa? Inda za ka je kai daya sai dai halinka ya cece ka. To menene duniyar kai da zaka tafi ka bari?
A gidan Baban Ali a tsangwame suka abinci ma sai an damar ba su. Duk wata kyautatawa da za suyi a banza a wajen Harira. In ka gansu kamar almajirai babu kulawa. Babu abinda ke dagawa Rokaiyatou hankali irin ciwon uwar da ke kafarta har yanzu ya ki warkewa. Sun je asibiti amma abun har yanzu shiru.
Mutane biyu ke haya a gidan. Akwai wata mata da mijinta yan jihar Naija. Sai kuma wata baba yar tsohuwa da mai kula da ita a wani bangare. Amma duk tsakar gidan daya ce.
Wani abun al’ajabi shi ne duk tsangwamar nan da raahin gata da suke ciki sai ya zamo Rukaiyatou tana da matukar farin jini. Samarin unguwar kamar an sa musu ita gasa daga wannan ya yiwo sallama sai ka ji wani ma. Wannan abu yana konawa Harira rai ita me yanmata a gida. Gabadaya sai ka va annurin fuskarta ya canja don tsananin cin fuska sai ta cewa san aiken
” ka cewa abokin zinar tata tana can dakin kaji ya shigo ciki su tsadance”
Wannan magana tana bakantawa Rukaiyatou da Momma rai. Rokaiyatou ta kan yi kuka tana kallon mutuwa a matsayin babbar abar tona asiri. Oh rayuwa yau ina babanta? Yau ina Momodou?
Harira mai waina wata irin mace ce marar dadin zama. Ko mijjnta bai isheta kallo ba saboda yanzu ba shi da shi. Idan ta zauna suyar wainarta kuwa ko sallah ba ta tashi ta fi ganewa idan ta gama sai ta jero su.
Ranar wata asabar tana cikin suyarta sai aka doko sallama. Ta leko daga ‘yar langa langa da ta kewaye ta sai gayi ido biyu da Anti Saude. Ai kuwa tayi zumbur ta mike tana kwalawa diyarta bilki kira kamar zata fasa musu dodon kunne
” Dan ubanki fito ki taya ni suya, kin nannade a daki kamar macijiya wato ni wuta ta karasa ni ko? To don iyayenki idan na mutu zan ga uban da zai ciyar da ku tunda naki uban ya zama Allah zi wahidin”
Ta tafi da sauri ta je ta taro bakuwar da ba tata ba.
” Anti saude..Yau kike a gari in ji maki bako”
Anti saude jikar Baba yar taohuwa ce ta gidan. Yar gayu ce ta kin karawa za ta kai shekara talatin da biyar. Bata da aure ba kuma ta taba aure ba. Gogaggiyar yar duniya ce mai tashe da Naira son motar hawa ma biyu gareta.
Marainiyace gaba da baya don Baba yar tsohuwan nan ita ta haifi babanta kuma ita kadai ta rage ma ta. Babau wanda ya san takamaimai aikin me Anti saude take amma kudi ba sa yanke ma ta. Zama take a gidan kan ta sai dai takan zo wa kakarta ziyara akai akai har ta dan kwana biyu tana mai kawo mata abun bukata. Kudin hayar gidan ma ita ke biya. Tsohuwar nan tayi tayi ta dawo da ita hanya abun ga faskara sai kawai ta bi ta da addua.
Anti saude mutuniyar Harira mai waina ce saboda akwai sakin hannu kamar bata san ciwon kudi ba. Da yake kuma ita harira kaska ce rabi mai jini sai ta manne ma ta.
‘ Yar gajeruwa ce mai dan kauri ba dayawa ba, fuskarta kadaran kadahan. A ranar ta yi shigar wani leshi fari tas mai manyan huda huda kuma ba ta yi masa shafi ba don haka ana hangen ma fi akasarin halittar jikinta. Ba ta yafa mayafi ba dama haka take yawo.
Harira tayi sauri ta dauko kujera yar tsugunno. Ta aiki dan ta isyaku ya siyo mata lemon roba coca cola. Harira ta ce
” Lafiya kuwa Anti Saude. Nayi cigiyarki har na gaji.”
Fuskarta fal faraa ta ce
” wallahi Harira wata yar tafiga ce ta kama ni amma yanzu na dawo har sai kun gaji da ganina”
Harira ta ce
” Haba? Ko da na ji bari na dan debo miki wainar ki dan taba”
Sai a loakcin ta kura ashe bilkin bata kama ma ta suyar wainar ba har fa kan tandar ta soma konewa. Ta kwala ma ta kira, Bilkin ta fito tana yatsina ta ce
” Wai ke umanmu mutum na barcinsa ba za a bari ya huta ba?”
Harira ta aiko ma ta da tagwayen dakuwa da yatsunta goma ta ce
” Ubanki! Ubanki na ce. Idan baccin rana abun yi ne ni uwarki in zauna in yi mana amma idan nayi ke hanjin cikinki zai bari ki runtsa? Tunda ubanki bai san ya nemo ba kin ga ai ni dole na hana idon nawa bacci. Za ki karasa ki zubo ma ta ko sai na zo nan na maida ke abun kwatance?”
Bilkin ta karasa tana gunagunai. Ba a dade ba Rukaiyatou ta fito daga dakinsu fitsari ya matse ta za ta je bandaki. Sai ta dauki buta Harira ta daka mata tsawa ta ce
” Ke! tinkiya uwar tambele..ina za ki?”
Ta ce
” Sabani naka bida zan yi sayi”
Ta yi mata dakuwa ta ce
” Sahanin daga lahira ubanki ya aiko? Ajiyemin butata ‘yar Allah bani kawai!”
A sanyaye ta ajiye ranta a bace ta koma daki. Ba a taba yi ma ta irin wannan zagin ba a duniya.
Anti saude tana kallonsu ranta bai ma fa dadi ba. Ta share ta ce
” Ina kuma kuka samu ‘yan Nijar?”
Ta ce
” Wasu ‘yan alakakai ne talauci ya koro su suka zame mana karma karma. Tunda uwata ta halicceni ban taba ganin masu daudar talauci irin wadannan yan hauren ba”
Anti saude ta gyada kai ta ce
“Amman kuma yarinyar kyakkyawa da ita daga gani za a ci kasuwarta musamman a kano. Bakanon mutum da son farar mace..’
Ran Harira ya baci amma bata nuna ba ta tsani ta ga ana yabin kyawun yarinyar.
An yi wajen tsawon wata takwas suna zaune a gidan da dadi ba dadi.
Sai dai Momma bata cika lafiya ba, sai Rokaiyatou ta fito ma ta da tabarma tsakar gida ta sha iska. Harira a ranar ta gama suyar wainarta tana zaune a kofar falonta tana zukar madara peak sabida aikin gaban wuta. Ba ta ce musu ci kan ku ba illa ma ta ware rikodarta da ta sa kaset din waka na barmani coge. Sai abun kuma ya zama habaici ta fara bin wakar a shagubance
Kai ku kama sana’a mata ko don ku huce takaicin zamani…lale lale maraba da ke zinariya
Kai ku kama sana’a ayye..ai kuli kuli ko ai kosai, ai furar madu ko dan wake ko da dako aka samu ma ayi
(Amshi)
Ayye kida na sanaa mata macen da bata sanaa ta bani…
Banda sakarai bankaurar banza ,mata suna ta sana’ar nema, ta sai da gulma ta sai tabarma, kullum asin da asin sai ta ara…..
Su dai ba su ce komai ba. Ba ta kai ga ajiye gwangwani ba yara suka shigo suna oyoyo yaya Ali ya dawo. Harira ta biye musu cikin farin ciki, tana kaunar dan na ta Ali. Suka gaisa tana ta mai korafin bai kira a waya ba an shirya ma sa abun sauka, an kuma gyara ma sa daki.
Sai a lokacin ya lura da bakuwar fuska suka gaisa. Uwar ta masa bayanin su a wulakance ya kara gaida Momma ya ma ta sannu da kafa.
Washegari ya fito daga daki Rokaiyatoh na zaune kan turmi ta gaishe. Ya gaida Harira ta ba shi karin safe. Abinci yake ci amma kamannin yarinyar sun dauke ma sa hankali. Wannan da a makarantarsu take ABU Zaria da yanzu ya san an sa gasa a kanta. Ai ‘yan clique din su kadai sun isa suyi fada akanta. Da zai wuce ya ce ta zo ta gyara ma sa daki. Ta ce “to”
Dakin na sa ba wani babban daki ba ne, irin dai na samari masu son gayu. Fastoci ne a manne a bangi manya manya na ball na club din real madrid. Sai katifa sai kayan kallo.
Ta gyara koina fes fes. Wajen gyatan kayan kallon ne ta ci karo da fina fina batsa kala kala. Gabanta ya fadi ga shi mai kirki a fuska, tai sauri ta mayar. Ta bar dakin.
Wata irin yunwa harira ke barinsu da ita. Su rasa unda zasu sa kan su. Momma ta fi dagawa Rokaiyatou hankali saboda ita ba lafiya ba..kafar nan ta matsa ma ta. Momma kan yi kuka ta ce
“Rokaiyatou bango ya fadi, Momodou babu ko gawarsa ban sa a ido na ba”
Irin wannan maganganun kan sa su shiga tashin hankali.
Ranar da yunwa suka kwana. Da daddare Rokaiyatou ta kasa bacci tana ta murkususu. Sai ji an budw kyauren daki ta tashi zumbur! Ali ne.
Yayi ma ta magana rada rada
” ba kiyi barci ba kina jin yunwa ko? Ta gyada ma sa kai kamar kadangaruwa a tsorace. Ya ce ta biyo shi ta karba. Ta bi shi. Abincin ya ba ta ya ce
” Duk sanda kike jin yunwa kizo ki gayamin kin ji?”
Ta ce “toh” cikin murna
Ta kaiwa Momma suka ci suka koshi sukai kat! Tunda ta zo kano bata taba cin abinci ta koshi irin ranar ba. Wani irin dadi ya mamaye ta taji kaunar Ali a ranta. Har da nama!Dama a kano akwai mutane ma su kirki da za su bawa mutum abinci? Duk gidan ta daina ganin mutuncin kowa sama da Ali.
To sai halayyar lallabowa ya bawa Rukaiyatou abinci ya zamo wa Ali farilla. A lokuta da dama kuma sai yace ta zo ta gyara ma sa dakin sa. Ko kuma ya kira ta ya ce auyi hira. A lokuta da dama sai hakan kama hannunta ko ya ce zai taba nannadedden gashinta marar gyara sai yace ba ta son kulawa da shi. Ranar har sabulu ya siyo ma ta wai ta wanke, tayi ta murna. To ita bata saba da hakan ba sai takan nuna ma sa bata so ya taba ta. Sai yayi fushi ya ce bata dauke shi danuwanta ba.
Da yake ita ba wai tana da wayo ba ne ba ta dau hakan a matsayin gagarumar matsala ba. Ita dai tsoranta sau da dama kar ta je ta bata ma sa rai ya hana su abinci. Saboda irin gigitar da yunwa take jefa su ciki.
Momma bata kawo komai ba sabida yanzu ta lafiyarta ma take. A asibiti an dora ta akan magunguna ba su sa bacci da kasala. Komai yanzu Rokaiyatou ke ma ta.
Ali ya gama gajeran hutunsa a ciki yayi wa Rokaiyatou alkawurra da dama. A ciki har da yana son ta kuma ba zai dade ba zai dawo. Rokaiyatou ba wai son Ali take ba, a zuciyarta babu wani gurbi da ta bari na so. Ka wai dai Ali ahi kadai ha nuna musu kauna tun dawowarsu hakan ya sa ta ba shi matsayi daban.
Bayan tafiyar Ali da sati 4 ya dawo. Wannan dawowar ta Ali ita ta canza salon rayuwar Rokaiyatou. Dama an ce Hau ba ta wuce ranarta.
Harira ce ta jefi Rokaiyatou da kalmar ” karuwanci” Momma ta gaji ta tanka suka yi cacar baki. Cikin kuka Momma ta ce
” Ni ban san me nayi wa mutane suka tsane ni suka tsani ahalina ba. Wai Rukaiyatou ce karuwa??? Karuwa fa?
Don tsabar bakin ciki kawai sai tabyanke jiki ta fadi. Fadar irin tashin hankalin da ya biyo baya daga Rokaiyatou , Ali har baban Ali zuwa zaryar asibiti abu ne da bazai labartu ba. A asibiti aka gano tana dauke da cutar diabetes aka ba ta gado sai cacar kudi ya biyo baya.
Rokaiyatou bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba ga shi zaman asibiti yana neman gagararsu. Baban Ali da Ali suke buga buga. Kullum zarya tsakanin gida da asibitin. A lokacin ne Ali ya cimma burinsa akan Rokaiyatou.
Ya nuna mata cewar babu mai kaunarsu kamar shi kuma bata da danuwan da ya wuce shi. Shi ke ba ta kudin abincin da zata kai asibiti da kuma na mota. Da hilata da yaudara irin ta tashi ta dan boko sai da ya san yanda yayi ya ci galaba a kanta. Sai ya lallabata da tayi shiru kar ta gaya ma kowa, don idan ta fada ba zai kara bata kudin zuwa asibiti ba.
A wata rana aka rubutawa Momma allurar insulin da za a mata babu kudi babu dalilinsu. Haka ta garzayo gurin Ali yayi amfani da ita ya bata kudin a hannu N2500. Ranar ta ji kamar ta mutu don bakin ciki. Ji tayi ina ma ba a halicce ta.
Haka ta isa asibitin a galabaice. To amma abunda ya fi ruda ta shi ne Momma bata kan gadonta. Da ta tambaye na kusa da gadon ina mai gadon. Sai aka ce mata ai bayan fitarta kadan matar ta cika!
Wani abu ne kamar walkiya ya gifta ta idonta, daga nan ta ji dif! Wadanda suka yi zaman makoki su ne suka bada labarin cewa kwananta bakwai ba ta san inda kan ta yake ba.
Tana ta kirga kwanakin da zata mutu ba ta mutu ba. Sai take kallon mutane wai kuwa suna jin yanda take ji kuwa? Amma me? Ta san ba zata zauna a gidan nan ba dole ta samo mafita. Momma na da kwana 60 a kasa, sai ciki ya bullo ma ta.
Abin ya faro ne kamar abun al’mara. Tunda aka yi mutuwar nan bata fitowa. Ali ya dawo hutunsa ta kura ko harkarta ba ya shiga. Ba ta wani damu ba.
Baban Ali ne ya shigo bazar bazar a fusace ya tarda harira tana kullin sikari ya ce
” wai ke harira yaushe za ki saka ido kan ‘ya’yanki? Wannan yarinyar Bilki daga yau wannan ya zo sai wani. Tunda ba karatun za tayi ba ki ce na ce ta tsaida miji. Sau biyu tana rubuta jarabawar fita daga sakandare ta kasa tabuka abun kirki..ki gaya mata aure zan ma ta wallahi”
Abun ita ma yana damunta yau sai aka dace ta ce
” Wannan alamari na bilki akwai sa hannun makiya. Ji fa yaron nan kwanaki dan gidan Alhaji ya zo kanar gaske. Amma daga cewa ya fito ba amo ba labari”
Ya ce a fusace
” kin bar su suna yawon ta zubar ya kuwa zai aureta? Sai nayi magana ki ce ke kike ciyar da gida ni menene ban miki ba lokacin da ina da shi? Wallahi tallahi in dai haka arzikin mace yake to Allah wadaransa. Ki ce nace ta fidda miji..atoh”
Kafin ta ba shi amsa sai Anti saude ta fito dama ta zo jiya. Aka gaisa. Auna cikin gaisawar ne Rokaiyatou ta fito ta gaishe su ta shiga bandaki. Baban ali ga bi ga da kallon tausayi, yana kaunar yarinyar yana tausayawa maraicinta. Ya kudurce a ransa inahallahu sai inda karfinsa ya kare, zai kula da ita.
Anti Saude ta bi ta da kallo har ta bace. Cikin sauri ta ce da Harira
” wai me yasa ba ki da lura ne? Yarinyar nan ciki gareta”
Harira da ke zaune ta mike ta ce
” wani irin ciki kamar a wasan kwaikwayo?”
Baban Ali sai ya ji ya gagara tsayuwa gabansa yana faduwa. Ya kalli anti saude rai a bace ya ce
” Haba saude kamilar yarinya kamar wannan ko fita ba ta cika yi ba”
Ta katse shi da” cewar wallahi baban Ali yarinyar nan ciki gareta, amma bari ta fito.”
Kawai sai harira tavrangada guda ta ce
” Ahayye abun boye ya fito fili. Har aka dunga zagi na wai bakin cikina ya kashe Ramlatu don na ce da diyarta karuwa. To ai ga shi nan”
Baban Ali gabadaya jikinsa a sanyaye yake ba don komai ba sai don ya ga yarinyar suna mutunci da Ali. Ranar har ya ga ta fito daga dakinsa wai ta je gyara har ma ya tsawatar ma sa akan hakan. To tunda aka ce ciki sai zarginsa ya darsu kan Ali don yarinyar ba wani fita take ba. Amma dai ya zuba ido.
Rokaiyatou na fitowa harira ta rufe ta da duka. Ta ce
” uban waye yayi miki ciki?”
Baban Ali ya finciketa ya ce
” dalla malam ki bari a bincika mana, yanzu haka ma abun a gindinki ya ke”
A fusace ta ce
” Ban gane wannan bakin da ka ja ba fassara min. Yarinyabta yo ciki kwararo ka ce ba za a daketa ba. Na tabbatar da bilki ce da yau sai dai na dau ciki nayi goyonsa wata tara idan na haihu na sa ma ta bilki, domin kuwa ka kasheta!
A nan Baban Ali da Anti saude suka lallaba Rokaiyatou har ta fada musu cewa Ali ne.
Baban Ali ya jingina da bango hasashensa ya zamo gaskiya. Ya sa a kira ma sa Alin. Harira tana cewa
” ji munafukar yarinya algunguma abun a kaina zai kare? Dan nawa za ayi wa sharri”
Ali yan zuwa babansa bai wata wata ba ya kwaahe shi da mari guda biyu. Ali ya ce fafur ba shi ba ne. Ai fa gida ya rikice. Kan ka ce kwabo harira ta zari mayafinta akan igiya ta tafi kawo police starion ta taho da ‘yansanda mata biyu wai au kama Rokaiyatou ta laqa wa dan ta sharri.
Baban Ali ne don bakin ciki ya ce
” Harira wallahi idan kika yarda matar nan ta tafi da Rokaiyatou to ke ma ba zaki zauna mun a gida ba. Sakin ki zan yi. Aure da Rokaiyatou da Ali ba fashi!”
Kawai sai Harira tayi zaman ‘yan bori tana birgima a kasa tana kuka
” shegiyar yarinya ta zame min kadangaren bakin tulu, in kar ta in fasa tulu in barta ta bata min ruwa. Auren nawa na shekara aahirin da biyar za a min kandagarki da shi akan na sa a fitarwa da na hakkinsa?” A daren ranar ba wanda ya runtsa.
Da tsakar dare Rokaiyatou ta sadado ta fito daga daki, lokaci yayi ta gayawa kan ta. Za ta taba kofa kenen ta ji an ce
” ‘yar Nijar”
Ta waiwayo tayi ido biyu da Anti saude. Ta ce da ita kai tsaye
” ka da ki fita wahalar banza za ki sha ki zama karamar karuwa abunda zai raba ki da namiji bai fi kudin abinci ba.”
Rokaiyatou tayi shiru tana kallonta
Ta ce yar nijar ki yarda da ni. Rokaiyatou nan take ta yarda da ita, wa zai taimake ta in ba ita ba? Daga ranar ba ta kara kwana a gidan baban Ali ba!
Anti saude ita ta tsaya tsayin daka akan Rokaiyatou ta gudu da ita. Ta kai ta asibiti aka cire ma ta cikin jikinta. Sai da Rokaiyatou tayi tsawaon wata tara a gidan Anti saude idan ka gan ta ba zaka taba zaton ita ba ce. Ta bata cima mai kyau ta ba ta kulawa. Tayi bulbul ta zama wanke hannu ka taba. Ba abunda ba a koya ma ta ba, yanayin cin abinci, tafiya, magana uwa uba kwalliya!
Anti sauden kan ce da ita
” wannan hausar ta ki ki gyarata ki daure ki iya hausar kanawa. Ba a cika so farat daya a gane mace daga inda ta fito ba. Ki koyi canja harshenki, ki koyi wayo da hilata ta yanda zaki gwanance a yaudarar da namiji!”
Rokaiyatou ta kan yi murmushi . Ita kan ta ta san ta goge kuma ranta a kekashe yake. Kudi za ta nema don ba ta ga amfanin zama da babu ba!
Watarana da daddare Anti saude ta ce
” yar Nijar saurareni da kyau. Yanzu na miki iya panel beating din da ya dace kin fara zama irin macen da maza zasu gani su saka gasa akanki. Kar da ki sake ki manta jikinki shi ne jarin ki, shi maza za su dakawa wawaso. Ina so ki daukaka, ki fi haka…kina ji na ko?… akwai wata kungiya……”
Wani sashe na zuciyar Rokaiyatou yana hango ma ta Momodou ya na yi ma ta bye bye.
Kun ji masomin labarin Mai Tafiya
Mai Tafiya…wani guzuri ka tanada??????
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
