Duniya ta – Chapter Six
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Yawon duniya mafarki ne, idan an je za a dawo.
Saudi Arabia
A tsammanin Luba duk wanda aka ce ma ta ya tafi saudiyya to lallai kakar shi ta yanke saka domin arziki ne zai dangwala ya dawo gida yana gwalangwaso. Ga mamakinta sai ta ga ashe ba haka ba ne? Ashe rayuwar saudiyya rayuwace ta mai zaman kanta? Ashe gwagwarmaya ce kowa tashi ta fisshe shi?
Har a kullum a gudu ka ke kar a kama ka a maida ka inda ka fito. Kullum sai ka nema zaka ci , za ka sha ka kuma tufatar da kan ka. Duk wannan wahala bai sa Luba ta rusuna ba har yanzu zuciyar na nan cike da buri. So take ta bunkasa ta girma ta buwaya a cikin lamarinta. Rayuwa da babu kwabo rayuwace da ta gwammace mutuwarta da ta wanzu a cikinta. Ita dai kawai ta samu kudi tayi facaka ta more.
Ta cigaba da bin Hajiya ‘yar Sakkwato a sannu ba don ranta na so ba sai dan cewa bata da wanda ta sani sarai kamar hajiyan. To amma a tsarinta dama, za su raba gari da zarar ta samu mafita. Daga baya sai suka koma Madina kacokam inda Luba ta samu sanaar yin tuwon shinkafa, tuwon semo da miyar kuka.
Da ummara ko Hajji ba karamin ciniki suke ba saboda ‘yan Najeriya da basu waye da cimar can ba. A inda suke abinci akwai wata yarinya sa’ar Lubar sunanta samira ita kuma tana suyar dankali da kwai. A tun da can Luba bata son kawa a cewarta wai mata sun cika munafici da gulma. Amma ganin cewar samira tayi zaman shekara hudu a saudiyya ta fi ta wayewa sai tayi tunanin makale ma ta ko ta samu hanyar kubucewa Hajiya.
Samira wayayyiya ce asalinta yar cotonou ce yawonta ya kawo ta saudiyya. Da yake ita kuma luba duk inda mai wayo yake ta kai sai ta fara ma ta ladabin kare. Daga karshe sai suka kulla kawance inda samira ta yi ma ta hanya ta samu aikin wanke wanke a gidan wata balarabiya mai suna Ummu Rumana.
Aikin gidan larabawa wani irin aiki na mai tarin yawa. Ko ina so suke a gan shi fes fes, don Luba har tsani gareta na wanke bango. Ga wani irin wulakanci na nuna banbancin launin fata. Wannan abu ya isheta, ya ita da ta baro gida neman arziki za ta bige da wahala irin haka? Ba wuya kana aiki a gida maigidan ko yaron gidan ya neme ka. Ashe su ma lababawa mutane ne irin mu masu zuciyoyi da halaye irin namu?
A zaton ta idan aka ce balarabe ko wani iri ne to kankat kenen a kyawawan halaye. Ashe abin ba a haka ba ne a zuciya ne? Kes kes nawa ta gani na daga zuwa aiki maigida ko yaron gida ya bige da yiwa yarinya fyade? Wa ya isa ya bi ba’asi? To in dai haka ne mai ya sa suke kallonmu makaskanta? A ce wai har ta kai idan ka hada sawu da wani balaraben a masallaci don ayi sallah sai ya zame ya canja sawu wannan wace irin masifa ce?
Ta sha canje canjen gidan aiki har ta gaji don kan ta ta dawo gurin Hajiya. Hajiyar ta karkace baki ta dun ga sheka dariya har ta yi ma’ishi kana ta nuna Luba da sabbaba ta ce
” Dan uwarki Lubabatu an ka hwadi miki ni assh shegiya? To bari in gaye miki da uba an ka haihe ni ba ‘yar kwararo ta ba. Yawon duniya ni niz zabe shi a karon kaina don shi ne mahita din haka ban ga dan kazar uban da zai koyan ba!”
Ta cigaba da kura wa Luba mici micin idanunta ta karasa da
” Uwarki ma Tamadi na hi karhinta wallahi balle yarinya kankanuwa kamar ki!”
Kalmar uwarta da aka ambata ya mata ciwo amma sai ta danne tayi kus, ita fa nema take amma a kasan zuciyarta zagi kwando kwando take juyewa Hajiya. A fili kuwa sai ta ce
” Hakuri fa za kiyi Hajiya ki daure ki tallafeni yanda ki ka daukoni a gaban uwata ki ka kawo ni uwa duniya, kin ga ai bai kamata ki guje ni ba”
Hajiyar ta kalli luba tana mai mamakin ladabin harshenta ta ce
” Au ni na gguje ki? Ku ji ni da ‘yal tselan uwa!
Nan dai Luba tayi ta lallaba ta har dai ta amince zata taimake ta. Daga nan sai Hajiyar ta shigar da ita harkar goro shi ne suke zuwa jidda suke sarowa a hannun matafiya. Sana’ar kuwa ta karbe su Luba ta canza ta goge har larabci take ji. Sai dai kuma akwai wata a kasa, mazan da suke cinikayya da su ma fi akasari ‘yan Afrika Hajiya tana hada su da Luba suna nema. Fasikanci dama ba bakon Luba ba ne don haka za ni ce ta tarda mu je mu.
Bayan kamar shekara biyu da zaman Luba a Madina kwatsam rannan sai Hajiya ta shigo ta tarda ta a dakinsu da daddare tana hada kayan siyarwarta. Daga zaune a gefe akwai wata yarinyar Hajiya mai suna Halima. Halima yar Adamawa ce bafulatanar usul ta cikin maye belwa don a hausarta ma zaka gane. Ta fi shekara goma a saudiyya. Ba su cika shiri da Luba ba amma ko cacar baki bata taba hada su ba. Hajiya ta kalli Luba da rawar baki ta ce ba tare da ta lura da Halima da ke zaune ba
” Ji nan niya Lubabatu, ba ki jin ana hwadin za ayi rusau? Daga abunda shiyyi sharu mansur zuwa sharru sittin gabadaya gurin ga gwamnati za ta rusa. Wa ya sani ko abun ya taho ya game da mu a Madina? ga jidda muka komawa tunda dai garin ga ba na uwayenmu ba ne”
Wani takaici ya ka ma ta abu bai kai ya kawo ba ta dunga ambaton uwar mutum. Hajiyar ta ce su dan kebe suka kebe ta ce da ita
” Na yi miki sabon kamu”
Luba da son harkar kudi sai tayi kasake tana saurare.
” Shin kin taba ta’ammali da Larabawa na asalin saudiyya ba ‘yan haure ba? Ta girgiza kai ” kin san Allah tilo shi ke Luba? Sun hi son mata irinki. Matansu Laba Laba na, ba su ga kwarin kirki ga rashin gyara ina hwatan kin gane?”
Luba tayi shiru tana nazari cikin ranta kuwa tunani daya ne muddin ta makalewa larabawan jidda ai kuwa ta gama kudi. Jidda gari ne na kowa da kowa daga musulmai har kiristoci, gari na ‘yanci idan ka kwatantashi da Makkah da Madina. Mutane sun fi ganewa su bar Makkah su je suyi iskancinsu daga baya su dawo, wannan wata al’ada ce da suka fi kwanciyar hankali da ita.
Hajiyar kuwa ta ce
” Ai jidda ita ke ga kwanciyar hankali, ko banza kayi nesa nesa ga Allah (auzubillah) in kin dawo Makkah sai ki tai ki yo dawafi Allah shi wanke maki zunnubanki”
Ai Luba sai ta ji kamar ta rumgume Hajiyar don dadi lallai lokacin bunkasarta yayi. Idan kuwa har ta bunkasa to ba abunda za ta fara nema sai shaidar zaman kasa. Ai ita ta na ga ta ga wajen zama don ita da Nijeriya in ba sa’a ba sai ziyara. Hajiya ta daka ma ta duka ta ce
” Ke ji nan niya. Tahiyayyiya na sa an ka kawo muni magunguna na asalun mallaka daga sakkwato, jadidan wallahil azeem. Ki dibe ni nan sai nibba ki dabaru dubu! Da zaki kama namiji ga nan (ta kama wuyanta) ba ki ga Halima tana daddaga miki hanci ba? Matsayinki take bida. Tana miki bakin ciki yadda ta ga ina jawo ki ga jiki”
Kawai sai Luba ta rungume Hajiya suna kwasar dariya, wasa yayi kyau. Abinda Luba ba ta sani ba shi ne, wannan ne mafarin rushewar wasan na ta a kasar Saudiyya.
Bayan komawarsu Jidda sai hanya ta kara budewa. Hajiya ta san mutane yadda Luba ba ta zato don haka gama mata da maza mazauna can ya zame ma ta babbar harka.
Dama su larabawa masu mu’amala da bakaken fata su na bukatar sirri musamman idan suna da aure kuma hajiyar ta gwanance wajen tabbatar da hakan. Luba ta makance ta kurumce a son duniya, gani take wannan ya fiye ma ta komai. Larabawan mazan da ke cin amanar matayensu suka samu mafaka a gurinta ita kuma ta samu abunda take so a gurinsu. Ana cikin haka sai wata ta yi mata hanyar aiki a gidan Ummu khalifa.
Abu khalifa mutum ne mai tarin arziki sai kuma Allah ya hada shi fa mace mai mugun son mulki. Kasalalliyar mace mai saka aikin jaraba fiye da duk wani gida da Luba ta taba aiki. Babu inda Luba ba ta shiga a gidan ta gyara daga sashenta har na mijin. Mijin bai cika zama ba don haka a tsawon zamanta ba wai sun taba haduwa ba ne.
Watarana Luba ta dawo daga kasuwar Haraji (sooq kharaj) ta saro gumama ta shigo gidan ummu khalifa ta ga ana ta shirye shirye da girke girke. Sai mamaki ya kamata don sanin ummu khalifa ko tsinke bata dagawa. Daga zuwanta ta hau ta da fada kan cewar ba ta karasa gyaran sashen Abu Khalifa ba ga shi kuma yana kan hanya. Ta na ta maimaita
” Allahu yahdee ki, Allah yahdee ki”
(Allah ya shiryeki)
Nuni da ranta ya gama baci kenen.
A cikin ran Luba ta gama zaginta kwando kwando, mata gadon mijinta ma ba za ta iya gyarawa ba, malalaciya kawai. Can wata zuciyar ta ce ma ta ke idan ke ce da matsayinta za kiyi aikin wahala?
” Nan fa daya”
Ta bawa kanta amsa.
Ta na cikin aikin kwatsam sai ta ga an shigo sai ta dan diririce ashe mai dakin ne, sai ya sakar ma ta murmushi. Ta mayar ma sa don dama niqabinta a dage yake. Ya ce “Afwaan” yana mai ba ta hakuri ganin kamar ta rude. Ta gyada ma sa kai tana mai lura da satar kallonta da yake yi.
Abu khalifa ba zai gaza shekara arbain da biyar ba mutum ne mai mabanbanciyar halayya da matarsa. Yana da matukar kirki da tausayi, ya tara dukiya mai yawa ga shi da kyauta. Matsalarsa guda daya ce bata kai biyu ba, zina.. Mazinaci ne na bugawa a jarida shafin farko kuma ba irin kalar matan da baya kulawa. Ko da ya ga Luba a wannan ranar sai ran sa ya biya amma yayi mamaki don bai taba ganinta ba.
Ko da Luba ta kyalla ido ta ga kallon da Abu Khalifa ke jeho ma ta sai kudurcewa ranta kaya ya fadi a gindin kaba. Sai take tsirar gyaran sashensa a daidai lokacin da ta san yana nan har ma yayi sabo da ganinta. Rannan dai ya tambayeta
” Hal ta’arafina luggatul arabiyya?”
( shin kina jin harshen larabci?)
“Qalil..min arabiyya”
( ina ji kadan)
“Ma ismuk?”
( ya sunan ki?)
“Ismi Lubabatu”
(Sunana Lubabatu)
“Ah..mashallah..kaifa haluk ya lubabah?”
( ya ki ke ya lubabah?)
“Ana bi kyar, Alhamdulillah”
(Lafia nake,Alhamdulillah)
“Ana masrur bi muqabalataki”!
(Na ji dadin haduwa da ke)
Anan suka kulla alaqa wata irin alaqa da ta zamewa Luba sanadin wani babban al’amari!
Luba da Abu Khalifa dama zani ce ta tarda mu je mu kawai sai suka gimtse cif da cif kamar tif da taya. Dama shi halinsa kenen sai ya gamu da luba uwar cin nera kawai sai al’amarin ya musu armashi, bai yi wata wata ba ya fara mallakawa luba kaya na alfarma.
To dama ita gwanar girman kai ce da dagawa nan da nan sai ta fara izza a cikin yan dakinsu. Ita kan ta Hajiya ‘yar sakkwato sai ganin Lubar ya zame ma ta aiki, ta kwashe kayanta ta koma wani gida. Luba ba ta ga wuta ba ta ga aljanna Abu khalifa ya daure mata gindi sai yanda ta so. Sai dai duk abun nan da yake ma ta cikin sirri ne don yana tsoron matarsa ta sani. Duk wannan tashe da take yi ba ta taba tunanin waiwayar gida ba. Kusan shekaru hudu ba amo ba labarinta kawai sai bankadarta take zubawa. Ta jingine kowani maneminta tana mu’amala da Abu khalifa kadai saboda shi mai tsananin kishi ne.
Me zai faru? Luba tana cikin cin duniyarta da bakin allura sai ta fara zargin kamar yanayinta na canjawa. Ta dai share da fari saboda duk yawon duniyarta ba ta taba yin ciki ba don kwayar family planning kamar ruwan sha take a gurinta tun zamanin tana harka da su Olu. To sai dai a saudiyya ba wannan kwaya da zata je gaba gadi ta siya sai dai mutanenmu masu zuwa da suke sumogalin din ta suke sayar musu da tsada. Shi kan sa Abu Khalifa ba su taba wata muamala ba tare da yayi amfani da “condom” ba sai kan ta ya daure.
Ba ta yi sati ba zarginta ya tabbata tana dauke da jiki dan wata biyu cif a mahaifarta hankalinta yayi matukar tashin da bai taba yi ba! Ina za ta kai juna biyu? Wa ta isa ta nuna ta ce shi ne ubansa? Ta ma ina zata fara rainon ciki a garin da baka isa gaba gadi ka je mustashfa ba? Yaron da baka isa ka sa shi a madarasa ba? Duk wannan sai dai kayi kame kame a tsakaninku ku bakin haure.
Shawara dama guda daya ce ta zubar don dai ita ba ta ga wurin ajiye shege ba a duniyar nan. Ga shi ita ba wata kawa ba balle su kashe du rufe kowa sama sama take da shi.
Ita a karan kan ta ta san ciki na Abu Khaleefa ne don haka dole ta boye masa don bayyanawar mugun tashin hankali ne. Idan kuna nema da baki danuwanka don ka haifi shege ba wani abun a zo a gani bane amma balarabe? Idan ta bari ya sani kashinta ya bushe don tsaf zai iya sa. a batar da ita. Abu khaleefa babban mutum ne mai dukiya, iyali ga mu’amala ta arziki da mutane da wani bakin za ta gayawa duniya tana dauke da cikinsa? Daga zaman dadiro? Ba zata iya ba!
Luba fa ta rasa inda za ta sa kan ta ta ji dadi tayi ‘yan dubarunta amma kamar an shuka dusa, ciki girmansa kawai yake. Ba ta da wata mafita kawai sai ta dangana da Hajiya ‘yar sakkwato.
Ta kalli Luba kallon takaici ganin yadda tayi sabo da raina mata hankali ta ce
” wagga yarinya..wagga yarinya kin ci sunanki kaza ci ki goge baki. Sai yanzun ga kin ka ga damar zuwa dibo ni? Da ta kare miki? To ahir din ki hawainiyarki ta kiyayi rama ta”
Tayi ma ta tas! Luba ta sauke girman kai ta dunga rokon hajiya da bata hakuri tana ma ta bayani har dai ta huce. Can ta ce
” Yaro yaro ne. Kin san dai bamu iya zuwa asibiti ko? Don saudiyya ba a zubda ciki bari in dan yi miki hadi irin namu. Irin hadin ga nai yyiwa zulai ‘yar damagaran. Shekarun ga da sunka wuce ta dage sai tayi amre..nicce mata duk amre amrenki kar ki sake ki daura da basuddane..me akai akai dan sudan..sai kun tara yara goma ki wayi gari babu shi ya gudu ya barka, ina za ka tasamma nema nai?. Ita ma kahiya gareta kamar ki Luba, ta tai tayi anrenta sai ga ta cikin hwari ya gudu babu labari. Irin hadin ga nai mata ta rabu da kajaga!”
Ta yiwa Luba hade hadenta ita kuma ta karba jiki na rawa ta kwankwade. A daren ranar da kyar luba ta kai labari saboda yawan jinin da ta zubar ita kan ta Hajiyar ta zaci sai a a lahira.
Hajiya Yar Sokoto ta tsorata iya tsorata har tayi da ta sanin sanin luba a duniya kwata kwata ballantana har ta kawo ta garin jidda.
Tana zaman zamanta za ta je tayi sanadin rai a kama ta a daure ba ta ji ba ba ta gani ba. Sai ta ji ma Lubar ta fice ma ta a kai gwara kawai ta rabu da ita ta huta da kaya tun da dai ta samu na samu. Tun da dai ciki ya fice umma ta gaida assha. Luba kuwa tana warwarewa da ta ga jinin barin nan ya tsaya sai ta ci gaba da sabgoginta.
Ana murna bako ya tafi ashe bako na labe a bayan gari. Ba a yi cikakken wata uku ba Luba ta fara jin wani motsi motsi a kasan mararta sai abun ya daure ma ta kai ta garzaya wajen Hajiya. Hajiya na taba cikin Luba ta doka salati ta sanar da ubangiji ta ce
” Lubabatu wallahi cikin ga na nan!”
Luba ji tayi kamar an dauki bulo inci tara an maka ma ta. Kawai sai tayi zaman ‘yan bori. Ta ce cikin karaji
” Ina ce mun zubar?”
Hajiya ta ce
” Bai zubdu ba Al’quran. Na rantse da Allah Luba cikin ga so shi ke shi tona miki asiri don alamu sun nuna sai ya diro da kahwahunsa. Adashi ne kin ka zuba Luba, sai kin kwashe.”
Wani kuka ya subuce ma ta. Ta haifi shege sai ka ce a majigin mafarki? Yo ko a Kano ta haifi shege balle a saudiyya? Luba ta zauna anan ta rizgi kukanta Hajiya kuwa ta cigaba da dan hidindimunta ba ta kara bi ta kan ta ba.
Dama tun da Abu khalifa ya fara shagwabata da kudi ta raba muhalli da Hajiyar. Ita a lallai na gaba yayi gaba dama Hajiyar tana kule da hakan. Sai suka yi sallama da Hajiyar akan cewa za ta dawo washegari a san wacce ake ciki.
Washegari da Luba ta dawo sai aka ce ai Hajiya ta kwashe ‘yan kayanta ta bar gidan wani kullutu ya tsaya ma ta a makoshi. Ya Hajiya za tayi ma ta haka? Ta jawo ta ta kawo ta garin da ba uwa ba uba ga cikin shege kwance a mararta shi ne zata gudu ta bar ta? Nan ta fara sake sake amma ba ta ga mafita ba.
Garin saudiyya ya fara fice ma ta a kai gabadaya hankalinta sai yau yayi Najeriya. Ta tuno iya tamadi da bata waiwayeta ba a sama da shekaru hudu cas! Sai ta ja wani takaitaccen tsaki tana tunanin abun yi.
Munari yar Adamawa da suka yi zaman daki da Luba ita ta fado ma ta a rai. Ta je ta same ta ta gaya ma ta bukatarta ta kalli luba shekeke a sakarce ta ce
” Au ni ce ma zan nema miki inda za ki haihu a sirri? Gaskiya kina da rainin wayo a lamarinki. Menene kuma gamin kifi da kaska? Ta ina muka hadu da zan taimake ki? To ma wai ni ce na ce kiyi cikin ko kuwa ubana yayi miki?
Luba tayi murmushi irin na mai nema ta koro bayani
” Halima baki fahimceni ba. Ke kan ki kin san abun kunya ne a ce na haifi shege a bayyanar jama’a wanda suka sanni na san su. Haka kuma kin san uban cikina balarabe ne me iyali. Idan balli ya tashi ta ina zan like? Ni taimakon da nake so ki min shi ne, na san kin san mutane to ki samo min wajen da zan boye in haihu ba tare da wadanda na sani sun gani ba. So nake cikin nan ya zame min sirri.”
Munari tayi caraf ta ce
” Dama haihuwa na da sirri ne? Ai sai dai idan ba ki haife ba! Da can wani shegen ne ya ce kiyi cikin?”
Luba ta katse ta da
” Dakata munari zaki taimaka min ko ba za ki taimaka min ba?”
Munari ta mayar ma ta da
” Wai in taimake ki akan wani dalili? Kanwar uwa ta ce ke ko ta ubana?”
Luba ta ce
“Akan dalilin zan ba ki riyal dubu biyu”
Munari ta mika hannu ta ce
” In ji dumus”
Karantina unguwa ce da aka fi sani da “slum” a turance. Cike take da masu karamin karfi ma fi yawansu wadanda ba ‘yan kasa ba mararsa igama(shaidar zama). Yawa yawan ‘yan Afrika daga kasashe irinsu Niger, Nigeria, Ghana wadanda suka shiga saudiyya sama ta ka kuma zaune a jidda za ka same su a Karantina. Akwai kasuwarsu da take ci duk juma’a anan suke samu su siyarda kayan abinci, kayan shafa da sauransu. A cikin wannan tsukakkiyar unguwar ta Karantina
anan munari ta samowa Luba daki.
Banda Luba akwai wasu mata guda hudu wadanda shekarunsu suka dan tasa suka yi musu karyar cewa mijin luba ya fada hannun yan kame an mayar da shi Nijeriya. Ita Lubar tana kokarin tara kudi ne ta aika ma sa ya samu dawowa. Suka tausaya mata ganin tana dauke da juna biyu suka dan tattaimaka ma ta.
Watannin haihuwarta suka cika cikin gajeriyar nakuda da taimakon ‘yan dakin su da munari ta sallo kyakkyawar diyarta fara kal! Kallo daya zaka yi ma ta ka gane ruwa biyu ce. Luba ta kura mata ido gabanta yana dukan uku uku, yanayin yarinyar ya dauki hankalinta. Wani takaici da bakin ciki ya nanukota data tuna wai yau ita ce ta ajiye shege, sai ta ji gabadaya kamar ta hau kan ta ta murkushe kowa ya huta.
Yarinya na da kwana bakwai da duhun dare Luba ta sidade ta gudu. Don ma kar a yi cigiyarta sai ta gudu makkah daga nan ta fada madina tana ta canje canjen gurin zama. Kafin kwana bakwai ta hada ‘yan kudadenta ta yanki tikiti sai gida Najeriya!
*********************************
A lokacin da Luba ta dira a unguwar Birget babu wanda ya gane ta domin kuwa fuskarta rufe take da niqab. Ta iso kofar gidansu ta kare ma sa kallo babu abinda ya kara sai rakwarkwabewa. Ba tayi mamaki ba shekaru sama da hudu ba wasa ba.
Ta saka kai ta shiga ciki sai ta hangi Iya Tamadi a tsakar gida tana daka tunkwal tunkwal, ai ko ta kwararo sallama. Sau daya tak Iya Tamadi ta ji muryar Luba ta dago kai a firgice, ai luba na yaye niqabinta ta wurgar da tabaryar ba ko salati ta kwarma ihu mai hade da kuka ta ce
” Yau na ga ta kai na Luba ke ce ko kuwa fatalwarki?”
Iya Asabe da ke makewayi ta fito da sassarfa buta a hannu ta na ganin luba ta ajiye buta a kasa ta kama hanci ta rangada guda ta ce
” Yawon duniya mafarki ne, idan an je ma za a dawo!”
Iya tamadi ta share hawayenta da bayan hannu, Luba ta karaso ta rike ta ta ce
” Haba iyannan wai menene na kuka ba gani ba? Ga shi na dawo”
Iya Tamadi ta ce
” Haba Luba yanzu a ce shekara da shekaru ba amo ba labari. Babu wasika ko ‘yar wayar nan ta zamani da ta fito. Kin sa makiyana suna min dariya ubanki ko a jikinsa wai ai ni na tura ki. Wanna duniya da me tayi kama?”
Ta kare tana share hawayenta.
Luba ta buga wani uban tsaki ta ce
” Yo wai Iyannan ni daga dawowa ta daga wata uwa duniya ko ruwa ban saka a bakin salati na ba..ya salaam an taso ni da kirafe korafe.. Allahu yahdeek.Allahu yahdeek Duk mai zagina yayi a banza man kare. Arziki ne na yo shi..Alhamdulillah..na tako shi. Wallahil..azeem Kukan talauci sai dai wata shegiya ta yi ba mu ba!” Ta karashe tana hararar Iya Asabe.
Iya Asabe ta kwashe da dariyar mugunta tana mai karewa luba kallo ta ce
” Na yaushe kuma? Akwai wanda abun takaici ya baibaye irinki? Kin ki zaman aure sai yawon ta zubar, kano to jiddan ne bamu sani ba? ai muna da labarin komai! Ki je ki jiyo labarinsu hafsy sun yi zamansu dakin mazajensu har da albarkar ‘ya’ya ke kuwa sai yawon kawararo.”
Ta juyo ga iya tamadi da take mata kallon takaici ta ce
” Dama kin daina duba na kin kalli diyarki da kyau, daga gani jego take
Dubi kirjinta tantsan tantsan kwarankwatsa dubu idan aka tatsa za a ga ruwan nono! Eho!…an haifo shege ko an cire shege za a mana rufa rufa. Jama’ar gida ku fito..yau ga abun kunya..ahayye ayyururi!!”
Ihun da take yi ne ya janyo hankalin mutanen gida ciki har da amaryar baban yara Sabuwa. Ta fito tana yatsina irin na amarci ta ce
” Wai gidan nan gidan aure ne ko na masu zaman kai? Ku kullum kun girma amma ba ku san kun girma ba. Ba za ku bar mutum ya huta ba sai kun cika ma sa kunne da hayaniya..yo..ta yo shegen mana.. Asabe ubanki ne ya ma ta?”
Ta juya za ta shige daki Iya Asabe ta fizgo ta wai ta zageta aka fara damben alkafira. Har makota sai da suka shigo sannan aka raba su suna takaicin wannan gida mai kama da filin daga.
Sabuwa ta dauki zaninta da aka tumurmusa a kasa tana ta dure duren ashar ta ce wa Iya Asabe
” To ni ban kar zomon ba da zaki fizgoni ki daka. Ni nayi shegen ko kuwa uwata? Ki samu wacce tayi shege ki daka mana. Muguwar mace kawai danginsu fir’auna” tayi daki da sauri tana kullo kofa.
” Au matsoraciya ki tsaya ki ga yadda zan saba miki kamanni , wanda ya ajiyeki ma ba lallai ya gane ki ba” cewar Iya Asabe
Duk wannan badakalar da ake Iya Tamadi ba ta daina sharar hawaye ba tashin hankalinta shegen da aka ce Luba ta haifa. Ita ma da ta kare ma ta kallo sai ta ga kamar akwai alamun haihuwa a tare da ita.
Ita kuwa Luba ko a farcenta taunar cingam ma take tana yatsina tana kallon kowa daidai. Sabuwa da Iya Asabe dabbobi ta dauke su wadanda ba su san inda yake musu ciwo ba. Ta buga tsaki ta shige dakin uwar bayan ta ce musu
” Antuma….Majnutani!!”
( ku mahaukata ne)
Tana mai takaicin rashin canjawar rayuwar gidan.
Ta samu waje akan yaloluwar katifar uwar ta zauna. Iya tamadi da ta biyo bayanta ta ce
” Yanzu auta da gaske haihuwar kika yi? Za ki kara jawomin gori a sakani a waka cikin unguwa. Kina ganin guduwar da kika yi daga gidan Alhajin Kyalli dan kosan da nake yi sai hakura nayi saboda gore gore. Auta yaushe za ki bari raina ya huta ne?”
Luba ta galla ma ta harara ta ce
” Wai ke Iyannan yaushe za ki bar tsegumi da kananan maganganu? Daga dawowata an kafa min kahon zuka. A gabanki na haihu? Ko kuwa wani shegen ne yace muku ya ganni da goyo? Idan kina min irin haka yaya zan ji dadin nuna miki arzikin da na yo? Mutane suna so su raba mu kiri kiri amma ke kin kasa ganewa.”
Iya Tamadi tayi shiru taji batun arziki. Luba ta gama ‘yan fadace fadacenta kamar ita ce uwar kana ta zuge yar jakar da ta zo da ita da lalitarta ta fara ciro kudade. Riyal riyal ne da dalolin Amurka da Abu Khalifa ya sha wanketa da su. Iya sai zazzaro ido take tana washe baki
” Na shigangada ni Tamadi auta me zan gani haka?
Luba ta ce
” To ba na gaya miki ba ki ka tsaya mita. Yanzun haka wannan kin ga ba kudin kasarmu ba ne. Zuwa gobe idan nayi wanka na huta sai in je in canjo su zuwa naira na fitar miki da naki.”
Iya tamadi ta ce
” Allah auta? Yanzu duk kudin nan naki ne? Tabdijam lallai Saudiyya ta karbe ki..da gangan ma ake zaginki”
Luba ta ce
” Au dama ba na gaya miki ba. To bari ki ji har sarkar zinare zan siya miki”
Iya ta buga kirjinta da karfi ta ce
” sarkar zinari! Ni auta? Kamar wata matar gwamna?”
Luba tayi dariya ta ce
” tukunna ma iyannan idan na canzo kudin nan har jari zan ba ki ki sayi injin markade. Abinci sai wanda kika zaba. Na kai ki goron dutse ki zabi gado da kabet dan ubansu!”
Iya tamadi ta mike tsaye jiki na rawa don tsabar murna kawai sai ta karkace ta rangada guda. Ta ce
” yayi auta..duk cikin ‘ya’yana ba mai kaunata irinki. Allah dai ya karo arziki”
Suka cigaba da hirarsu.
Ita kuwa Luba ga shi dai tana murna ta rabu da kajaga amma zuciyarta cike take da tunanin jinjirarta. Idan ta rufe ido sai ta ga lokacin da diyar ta bude idonta masu tsoratarwa ta kura ma ta su. Sai ga ji gabanta na faduwa, ko yaya aka yi da jinjirar? Ta ma san ta mutu don ba yadda za a yi ta rayu ba ruwan nono. Da wannan ire iren tunanin ta yakice abun a ranta ta cigaba da harkokinta.
Bayan dawowarta da yan kudadenta sai ta zamo tamkar tauraruwa a gidan. Komai na ta daban ne ci , sha , suttura. Wataran ma kafin ta tashi daga bacci Iya Tamadi ta dafa ma ta ruwan wanka ta kai mata bandaki…wata irin rayuwa take yi tsadaddiya. Tuni ta karawa babanta jari har yake gani duk cikin ‘ya’yansa ba mai kaunarsa kamar ita.
Son zuciya irin na wasu iyayen kan zama abun mamaki. Daga baban yara har iya tamadi sai ya zamana ba wanda ke ganin laifin Luba. Ta girgije ta gyatse ta cigaba da harkokinta, iyayen suna kallo ba wanda ya isa ya ce da ita kanzil.
Har a wannan lokaci ba ta tunanin aure, sai ma take hangensa a matsayin wata hanyar tukurawa. Kullum hange ta ke akwai inda ya kamata ta kai wanda ba ta kai ba. Ta sawa ranta cewar in har za tayi aure to sai namijin da ya ci ya tada kai da nera.
Wata shida bayan dawowarta sai rayuwa ta soma yi mata matsi, ta kudurcewa ranta zama ba na ta ba ne.
A safiyar wata alhamis ta rangada kwalliyarta ta shiga wani tsadadden saloon domin a wanke mata kai. Kawai sai tayi kacibus da wata yarinya da suka yi sakandare tare mai suna Sadiya indiyar daji. Daga ita har luba dama can halinsu daya suka tafa Luba ta ce
” Sadiya kin buya kwana dayawa..khaifa haluk?”
Sadiya ta ce
” Shegiya Luba haka kika koma? Kwanakin baya an ce min kina saudiyya lallai ta karbeki”
Luba tayi galala tana kallon sadiya cike da tsananin mamaki. Ko da can ta san sadiya na tsalle tsalle amman kwata kwata baga goge irin haka ba. Yanzu Sadiga ta zama yar gayu komai na jikinta mai tsada ne. Wayar hannunta ma ba a gani sai a hannun wane da wane. Balle kuma uwa uba galleliyar motar da ta hawo ta zo saloon din da ita. Luba ta kama baki ta ce
” Aiwa..Sadiya haka duniya ta miki wankan albarka? Mashallah..mashallah. wa kika samu ya rike miki kan maciji ki ke wasa da jelar?”
Sadiya ta kyalkyace da dariya tana kada ‘yan mukullin mota ta ce
” Duniya ai ba gidan zama ba ce Luba sai ka tashi ka nemi sa’a tukunna.”
Luba ita ma dariyar tayi ta ce
” Aiwa..da gaskiyarki. Wallahil Azeem sadiya arziki ya karbeki. Nima ki min hanya mana in daina rabe rabe. Tun dawowata daga Saudiyya al’amura suka tsaya cak ba kamar da ba. Ga shi na tsani rayuwar babu wallahi.” Suka tafa.
Sadiya ta ce
” To in kina so sai in kai ki amma fa sai kin jajirce”
Luba tayi caraf ta ce
” Ku ji mu da Sadiyan nan ai ni duk inda kudi yake to ina nan. Ko ina ne ma kai ni..menene a cikin ido in ban da ruwa?”
Sadiya tayi dariya ta fara cewa
” Akwai wata kungiya…….”
Babu wani sashe na zuciyar Luba da ya taba tuna ma ta ranar nadama.
Kun ji masomin labarin Lubabatu.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
