Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Sai gyada Hajiya, sai gyada ci ko tsaraba..”
    Wata yarinya dake ɗauke da bokitin tallan gyadanta ta faɗa tsaye daga bakin wata hayis dake dauke da fasonjoji wanda mafi akasarinsu mata ne dsuke da yara da kuma wasu a goye, banda hayaniyar cikin tashar akwai ta cikin motar ma da baka jin komai sai sautin muryoyin matan kawai dake ta kacaniya suna kuma ciye-ciyensu kala-kala.
    Wani dattijo ya taso ya tsaya daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da littafi zai fara karɓar kuɗin mota da kuma rubuta sunaye, wata mata dake ɗurawa yaronta wani farin kunu a leda tace.
    “Motar fa bata cika ba…”
    Ya gyada kansa.
    “Na sani ai Hajiya ba saura mutum ɗaya ba, kowa ya fito da kuɗin motarsa… Ke ya sunanki?”
    Ya faɗa yana ƙoƙarin rubuta sunan mace ta farko dake bakin ƙofar yayin da kowa a motar ya shiga ƙoƙarin binciko kuɗi daga jakarsa, mutumin ya gama rubuta sunan ya dago da kansa daidai lokacin da idonsa ya sauka akan wata yarinya da ta karaso jikin motar sanye da wani farin hijabi dogo.
    “Ƴan mata ina zaki je? Jaji ko kuma Kawo?”
    “Sameru zanje…” Muryarta ta faɗa kusan a shake sautin na fitowa a hankali, sai ya girgiza kansa.
    “Ga motocin Sameru can a wancan layin… Kudinki dari takwas ne, amma zan miki ragi, kawo dari bakwai a rubuta sunanki tun daga nan kafin mu isa.”
    Zainab dake tsaye tana kallonsa ta haɗiye a wani abu a makogwaronta kafin ta girgiza kanta a hankali.
    “Bani da kudi malam, dan Allah…”
    “Baki da kudi?”
    Ya tambaya sautin muryarsa na juyewa zuwa wani abu kamar izgili.
    “To rawa zaki yi su kai ki Samerun ko kuma ya za’ayi?”
    “Haba bawan Allah, kace mata babu mota kawai mana, sai ka bi ta da bakar magana.”
    Wannan matar ta faɗa daga cikin motar, vai saurari daya daga cikinsu ba ya juya kawai ya cigaba da neman sunayen mutanen dake cikin motar.
    Wani abu ya sake wucewa ta makogwaron Zainab a lokaci guda da ta shiga murza yatsun hannunta daga cikin hijabin, ƙwalla ta sake cika idanunta a lokaci guda, kafafunta sun gaji, tayi tafiya mai nisa kafin ta kawo tashar, tayi tafiya tun daga cikin kauyensu inda ta fito ta baya har zuwa wannan ƙauyen dake gabansu inda anan babbar tashar da ake samun mota zuwa ƙauyuka daban -daban a wannan hanyar take.
    Kuma bayan isowarta kai tsaye aka nuna mata wajen da ake hawa motocin inda take son zuwa, Sameru… Ƙauyen da ƴan uwan mahaifiyarta suke… Wajen da ta san cewa duk duniya bata da inda yafi shi a yanzu, babu wani waje ko kuma wani masaukin da wani zai bata da matsayinsa a idanun al’umma dama nata gabaɗaya zai kai can.
    Hadiza, wata yarinya da tayi kusan sa’arta a cikin gidan mijin nahaifiyarta da ta baro ita ke shaida mata dukkan abinda ya faru a lokacin rasuwar mahaifiyar tata, yadda yan uwansu kowa da kowa ya hallara a gidan da kuma tarin rigimar da aka sha da mijin mahsifiyar tata skan aikin da tmya tura ta.
    Wani abu da lokacin da tana Abuja babu abinda take tunawa kamar hakan, yadda yanuwan mahaifiyar tata suka yi iya kokarinsu wajen ganin ta basu ita sun rike a lokacin da zata yi aure, amma ta ƙi haksn,tace ta san zsi tike ta da amana kamar mahaifinta tunda amininsa ne, sannan ta kafa hujjar cewa duk duniya ita kadai take da ita a matsayin ƴa kuma bata tunanin sake samun wata haihuwar a yanzu duba da shekarunta, don haka babu yadda suka iya suka bar ta a wajenta.
    Kuna tun daga farko zaman gidan baiyi dadi ba sam! Sun sha wahalar da duk da karancin tunaninta tasha lissafa musu mafita ta hanyar mahaifiyar tata ta rabu dashi, amma bata yi hakan ba har karayar arziki tazo ta same shi inda babu bata lokaci ya shiga tura ƴaƴan sa aikatau, wanda daga baya ya hada har da ita da tarin hujjojin da mahaifiyar tata bata iya ƙarewa ba.
    Tana tuna ranar da ta tafi, ranar da ta tafi ta barta, tana tsaye daga kofar dakinta tans share hawaye da bakin zaninta, kwana suka yi tana bata hakuri da kuma shawarwarin da zata kare kanta yayin da itama ta shafe daren tana saƙe-saƙe cike da tunanin haƙuri irin na mahaifiyar tata da kuma taraddadin inda zata je da abinda zata tarar.
    Ashe dukkan tarin abinda zata tarar din bai kai wanda zata dawo kuma ta iske ba, ƙofar dakin mahaifiyarta a ƙulle da wani ƙaton jwado a daidai lokacin da ta taka kafarta cikin tsakar gidan, da kuma idanun mutanen gidan da yadda suke kallonta da mamaki da kuma wani abu da bata iya fassara shi ba sai a lokacin da mutumin nan yake gaya mata cewa babu mahaifiyarta…
    Ta rasu, babu ita a duniyar nan, ta rasu sati biyu da suka wuce… Ta rasu babu wanda ya gaya mata, babu wanda yabi ta inda aka tura ta ya gaya mata. Mahaifiyarta ita kadai take da ita a duniya, guda daya ce babu wata… Amma ta rasa ta babu wanda ya iya zuwa ya gaya mata sai da ƙaddara ta dawo da ita da ƙafafunta sannan ta samu labari, fuskar Jawad ta haska cikin idanunta a sannan, lokacin da ya riko hannunta kafin ta kai ga fita daga motar ya gaya mata cewa yana jiranta, zai jira ta a wajen har ta gama abinda zata yi ta dawo…
    _”Ba zan iya tafiya babu ke ba, amma nayi alkawarin zan dawo dake insha Allah Zainab…_
    Haka ya faɗa da sautin muryarsa da duk da ba ta shi take yi a lokacin ba sai da ya ratsa har cikin zuciyarta, bata san me suka fito nema a lokacin ba, bata san me ya kawo shi har cikin garinsu ba, amma zata kiyasta cewa yana cikin kwatankwacin matsalarta ne a lokacin, ko ma wadda tafi tata.
    Kuma ta tabbata abinda ke gabansa shi yasa shi barinta a lokacin, idan ba haka ba ta sani,ta san Jawad ta fahimci galinsa a dan kankanin lokacin da ta sanshi, baya fadin abu sai idan har da gaske yake kuma ya tabbatar dashi har cikin zuciyarsa don idan ya fada ɗin, to babu wani kuma a duniya da ya isa ya canja ra’ayinsa, ko a bakin Hajiya Mardiyya tasha jin tana bawa kannensa hakuri akan su hakura da wani abu, tace ko ita tsoro sa take yi idan ransa ya baci.
    “Malama idan baki da kudi gwara ki koma gida, alkur’anin Allah babu wanda zai dauke ki har Sameru kyauta a wannan tashar…”
    Wannan mutumin ya sske fada a lokacin da ya gama rubuta sunaye ya shiga haɗa kan yan canjin da aka tattara masa, a lokacin kuma wani mutumi ya ƙaraso ya biya nasa kudin aka gama cika mitar,direban ya zagayo ya karbi kudinsa ya cire kamashon tasha sannan ya shiga ya tada motar.
    Sai kafafunta suka matsa daga wajen ta koma gefe, gefe kusa da wasu kanti da kuma rumfuna ta tsaya, tana kallo motar ta juya ta fita ta nufi hanyar fita, idonta ya koma kan jerin motocin da akace mata sune ke nufar garin da take son zuwa, mutane na ta hada-hada a wajen ana lodi da kuma jera kaya yayin da masu karbar kudi ke yi.
    Bata da ko sisi, bata ma san inda zata same su ba, amma alƙawari ne ta yiwa kanta cewa ba zata sake komawa cikin Yakura a yanzu ba, watakila watarana zata dawo ko don ziyartar kabarin mahaifiyarta, amma a yanzu ta yarda cewa babu abinda zao sake maida kafafuwanta wannan gidan.
    Tunanin Jawad ya sake haskawa a cikin kanta,ta san zai dawo zai neme ta, amma rashin samun nata da zaiyi bai dame tasosai akan tunanin samawa kanta ƴanci da take son yi ba.
    _”Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, I just want to feel you close to me… So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari’a zan iya yi da kowa idan akace za’a hana ni aurenki…”_
    Abinda ya fada mata kenan da yabayin fuskarsa dake tabbatar mata da kowacce kalma da yake fada a lokacin, don haka ta yarda idan har da gske yana son ta, zai nemo ta a duk ind take tunda ta san va zata yi nisan da hakan zai gagare shi ba.
    Tana yawan son korewa kanta nauyi a kodayaushe, ta yarda babu wani ingantaccen abu da rauni ke samawa mutum a duniyar nan, don haka ba zata bari rauninta ya rinjaye ta wajen zama jiran Jawd ba, idan har ta mike da kafafunta, ta tafi wajen da zai tabbatar da darajarta tun kafin yazo da ma bayan yazo din, abubuwa zasu canja daga kalar yadda suke tafiya a baya, shi kansa zai san cewa bai same ta ne a wani hali na rashin gata da madafa ba.
    “Har yanzu kina nan?”
    Mutumin nan ya fada bayan ya dawo zai wuce, hannunsa babu littafin nan a yanzu. Ya ja ya tsaya a gabanta sannan ya gyada kai.
    “Lallai da gaske kike, hala mutuwa akayi muku a can din ko?”
    Kalmar mutuwa ta sake dawo mata da zagayen halin da take ciki, sai kawai idanunta suka ciko da kwalla sannan t ja hancinta kadan kafin ta gyada kanta. Sai shima ya girgiza nasa kan.
    “Allah ya jikan musulmi, ai kuwa kya so tafiya… Kuma zan taimake ki tunda haka ne.”
    Ba shiri ta dago ta kalle shi da idanunta da har a lokacin suke rine da kuka, ya sake gyada masa kana alamun ya tabvatar da hakan.
    “Akwai shugabanmu anan wajen, wallahi ba wani abu zai yi miki ba, kawai dai taimakon juna zaku yi ki sami abinda kike so, ke fiye da hakan ma zai baki a yau din nan, babu wanda zai sani kuma babu wanda zai ganki.”
    Wani abu ya doka a kirjinta da jin hakam,don tsaf ta fahimci inda zancen nasa ya dosa, ta zare idanunsa akanta tana kallonsa cike da tashin hankalin da shi bai fahimta ba ya cigaba da cewa.
    “Kuma walkahi ma ni a duk wadanda nake kai masa babu irinki, duk yan kauyen nan ne dake kawo tallan kaya cikin tashar nan, to suma baki fa abinda suke samu ba balle kuma ke… Ai ina gaya miki sa’ar da zaki raka yau…”
    “Kayi hakuri Malam, amma ba zsn iya abinda kake nufi ba.”
    Muryarta ta fito a hankali tana katsse shi, kuma dukda hayaniyar cikin tashar yaji abinda ta fada da yake hankalinsa na kanta.
    Zainab ta juya zuwa batanta inda wajen yake da rumfa daga gefen wani shagon container ta cire takalmanta ta zauna tana jin yadda hakoran bakinta suka kasa tsayawa waje guda sakamakon kukan da yake shirin kubce mata tana danne shi, mutumin ya kalle ta daga inda yake tsaye, takaicin asarar kudin da yake hangen zai samu a wajen shugaban nasa na bi ta kan zuciyarsa.
    Har zai juya yaji ba zai iya dannewa ba, don ba karya yayi mata ba, shi dai ta hanyarsa ya sani cewa bai taba kaiwa Alhajin wata mace kamar ta ba, fatarta kadai wata kala ce dake tsakanin fari da kuma ruwan ƙasa, wata kala mai ɗauke da kuma daukar hankali, bata da shahararren kyan da a lokaci guda zaka gane shi, amma ƙirar jikinta kaɗai da yake gani tun daga cikin hijabin, ya sani ba kowacce mace take haka ba.
    Don haka a lokaci guda ya canja shawara, shawarar daya san tunaninta ba zai iya kufce masa ba.
    Bai sake cewa komsi ba ya juya ya tafi kuma sai a lokacin ƙwallar dake tare a idanun Zainab ta ganganro kan kumatunta, bata taba yiwa kanta wannan fatan ba, bata taba fatan za’ayi ranar da zata zubar da mutuncinta don biyan wata bukatar ba… Zata gwammace ta koma inda ta fito da tayi wani abu makamancin hakan, a hankali ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta biyu tana kokarin goge hawayen.
    Banda Jawad babu namijin da ya taba rike ta a duniya, kuma shi nasa daban ne, baya kallonta da niyyar komai, yawanci fushinsa ne ma ke sawa ya rike ta, fushinsa da take mutukar jin tsoro a lokacin, amma a kwanakin nan musamman tahowar da suka yi, idan ta kalle shi a wannan yanayin, sai taji kamar ta rungume fuskar sa a jikinta tsawon lokacin da ba zai kara ganin komai ba bayan ita…
    _”…zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni.”_
    Wani abu tsaya a makogwaronta a lokacin da ta tuno hakan, Jawad bai sani bane amma halayen rayuwa sun sa tun a yanzu ta fara koya…
    “Baiwar Allah…”
    Muryar wata mace dattijuwa ta sa ta dago da kanta bayan wucewar wani lokaci, fara ce, farin da bata sani ba idan na gaske ne ko kuma wanda ta samawa kanta, fuskarta dauke da fara’ar da ta sa a lokaci guda tasa bayan hannunts ta goge hawayen dake kan fuskarta.
    “Ance min taimakon kudin mota kike nema ko?”
    Ta sake tambaya da wani murmushin, kuma kafin ta bata amsa ta cigaba.
    “Gidan abinci ne dani anan baya, kuma almajiran dake min wanke wanke bai zo ba yau, idan zaki yi in biya ki kinga sai ki samu kuɗin motar ko?”
    Babu shawara ta biyu tunanin Zainab ya amince da hakan, bata ga aibun hakan ba, bata ga komai ba… Don hausawa sun ce wanda yake ruwa aka miƙa masa takobi kamawa zai yi, ƙafafunta suka mike a daidai lokacin da nasa suka ƙaraso wajen.
    *
    “Kace ta san sunan garin ko?”
    Jawad ya tambaya a cikin gudun da motar ke yi, gudun da suke yi daga gefen titi wajen da babu komai sai kasar dake tashi a baya da zarar sun wuce.
    Nura dake zaune a gefe ya gyada kansa.
    “Ta sani, haka Baban ya gaya min cewa ai tun da daɗewa ta san sunan garin.
    “Kuma ka tabbata babu wata tasha da ake zuwa garin sai wannan da zamu je?”
    Ya sake tambaya yana zura hannunsa a cikin gashin kansa.
    Nura ya sake gyada kansa.
    “Ita kadai ce a kusa yallabai, ita kadai ce wadda zata iya zuwa, kuma gashi ma Isa ya tabbatar mana da cewar ya ganta akan hanya…”
    Jawad ya cije lebbensa na kasa, hannunsa ya sake danne sitiyarin motar da babu shiri suka kara figa da gudu, Abdallah ɗan wan Hajiya Salamatu wanda bata yarda da tafiyar Jawad ba sai da ta turo shi ya biyo shi yayi magana daga inda yake zaune a bayan motar.
    “Easy mana bro,zamu isa yanzu ai Insha Allah.”
    Jawad ya girgiza kansa.
    “A kowanne lokaci mota tashi take yi a tasha zamu iya sabanin ko kuma minti daya ne Abdallah. Tun yaushe ta fita, tun safe fa yace badu ganta ba.”
    Nura ya gyada kansa.
    “Amma ai da tazarar tafiya,ta dauki lokaci kafin ta isa na san sannan kuma bata da kudi a hannunta, sai da kowa ya caje kudinsa a gidan yau duka bata dauki ko sisi ba, kaga kafin tayi abinda zata samu kudin mota shima wani lokacin ne don haka za…”
    “Me zata yi ta samu kudi?!”
    Ba shiri Jawad ya katse shi yana daga muryarsa, kafin ya juyo da fuskarsa yana kallonsa.
    “Me zata yi ta samu kudi a cikin tasha Nura? “
    Kafin Nuran ya amsa, wayar Abdallah tayi ƙara a hannunsa ya dauka ya kara a kunnensa da sallamar da Jawad ya riga ya san ko wacece, Hajiya Salamatu… Don tun daga lokacin da suka sauka daga jirgi a Kaduna suka je gidan abokinsa suka ɗauko motarsa da ya bari a can, ta kira shi da kuma Abdallah fiye da sau goma, sai da ta fahimci shi yake tuƙin motar sannan ta koma kira Abdallahn.
    Zai rantse da Allah a lokacin da ya gaya mata cewa zai taho Kaduna a yau, kalar tashin hankalin da ya sauka a idanunta iri ɗaya ne da wanda ya gani a idanun Hajiya Mardiyya kafin tahowarsa… Tsoro ne karara da kuma taraddadin rasa shi, wani abu da ya kara bashi tabbaci na cewar da gaske ita mahaifiyarsa ce Uwa wadda babu makamanciyarta a duniya, tunda a kwana daya rak da ta san shi har zata iya tarayya da halin da wadda ta raine shi tsawon shekaru ta shiga wajen tunanin rasa shi.
    Har hannunta ya riƙe ya gaya mata cewa zai dawo su tafi can Abujan tare kamar yadda ta tsara har ma da wasu ƴanuwanta, tana gaya masa cewa akwai tarin wasu yanuwan nata da zaau zo wajensa a yau daga Gombe shima yana gaya mata cewa baya fatan abinda zai kaishi ya ɗauke shi tsawon wani lokaci.
    Bai gaya mata ba, bai gaya mata abinda zaizo yi ba kamar yadda shima Abdallahn bai gaya masa komai ba, kawai ya tsinci labarin ne bayan sun dauko Nura a cikin irin maganganun da suke yi na zuwa nemanta.
    “Bamu karasa ba har yanzu Aunty muna hanyar…”
    Abdallah ya faɗa a cikin wayar yana dawo da hankalin Jawad kan halin da suke ci kuma a sannan ne suka fara hango tashar, daga can saman wani waje da ya danyi tudu alamar tsanuni ne a wajen tunda hayar tana da hawa da sauka da yawa.
    Ya cije lebbensa na kasa hannunsa ya sake danne kan motar a lokacin da Abdallah ke cewa.
    “Insha Allah Aunty, insha Allah za’a ganta…”
    Ya sauke wayar sannan ya shiga sake tambayar Nura sunan wajen da kuma tazararsa da cikin garin Kaduna, sai dai Jawad baya ko jinsu idanunsa dama duk wani abu mai motsi a jikinsa sun tafi ne ga bakin tashar nan, baya ko damuwa da gudun da yake yi ganin ya fara shigowa cikin mutane.
    Tayoyin motar suka tsaya tun kafin ya ƙarasa kofar tashar, kuma ya fito a lokaci guda da motar ta tsaya yana rufe kofar motar, su Nura suka biyo bayansa suka nufi ciki gabadaya, tarin mutane da kuma hayaniyar dake faruwa a ciki ta cika kunnen Jawad kota wanne bangare, wata yarinya ya fara hangowa dauke da kaya, kammaninta suka koma ba Zainab sak a idanunsa.
    Har ya fara tafiya sai ya hangi wata irinta itama daga wani gefen, ya ga wata da goyo sannan ya ga fuskoki da yawa daga cikin wata mota duk irin nata, sai kawai ya ja ya tsaya, ya tsaya daidai lokacin da Nura ke tambayar wani inda ake samun motocin Sameru.
    “Wallahi maigida nima matafiyi ne ban sani ba, sai dai ko ku gwada tambayar wancan na ganshi da rigar ƴan union.”
    Yana faɗa yana nuna wani ma’aikaci dake aiki daga can gefe, kuma Nuran ne kadai ya tafi yana ganin kwatancen da mutumin yayi masa tun daga can, kuma tun daga can ɗin ya gane, don haka kafin ma Nuran ya dawo ya riga yayi cikin tashar Abdallah na binsa a baya.
    Mutum biyu suka samu akan wata mota dake kan layi kuma duk irin tambayar da suka yi musu kai tsaye suka nuna cewa basu ga yarinya mai makamancin kwatancen da suke yi ba.
    “Amma bari a kira Sani, sune a wajen da safe, watakila bakuwar taku da safe tazo.”
    Dayan ya fada yana yin gaba zuwa wani gini daga gefe. Dayan ya kalli Jawad sosai yace.
    “Yallaɓai wallahi kar ku saka rai, tashar nan sai mutum dari su zo a kasa da minti goma,wani ko fuskarsa ba zaka kalla ba zaka karbi kudinsa ka tambayi sunansa… Da ka rubuta shikenan kai dashi har abada, to ta yaya za’a iya gane wata yarinya?….”
    Bai ƙarasa maganarsa ba sai ga daya ya dawo tare da mutumin da aka kira da Sanin, yana tsayawa tun kafin ma Jawad ko Nuran su ce wani abu ya tambaya.
    “Yallabai farin hijabi ne a jikinta…”
    Jawad ya daga kansa da sauri yace.
    “Ofcourse bata da tsawo sosai…”
    Sanin ya daga kansa shima.
    “Ai bata je ko’ina ba, bata hau mota ba, tazo inaga kamar bata da kudi ne saai kuna ta tafi. To bayan hakan kuma sai na ganta a zaune a wajen shagon Ashiru, amma wallahi tun ɗazu ne, ban sani ba yanzu ko za’a same ta…”
    “Ina ne wajen? Nuna mana wajen kawai…”
    Cewar Nura.
    Mutumin ya shige gaba, dukkaninsu suka bi shi a baya zuwa daya bangaren tashar wajen da ake lodin motocin dake karasawa cikin Kadunan, Jaji zuwa Kawo.
    Kuma Ashirun da Sanin ya ambata shi suka fara gani a wajen yana ɗaukan sunayen wasu mutane a cikin mota. Basu san me Sanin yace dashi ba, don shi ya fara ƙarasawa kafin su, idon Jawad na kan Ashirun a lokacin da yake gyada kansa yana nuna wata hanya da ke gefe don haka bai ko ƙarasa wajensu ba ya yi hanyar.
    Ya isa daidai jikin wani shago lokacin da idonsa ya hango masa ita a lokaci gudataa mikewa da aamun zata bi wata farar mata dake tsaye a gabanta tana yi mata murmushi.
    Ta juya bayanta tana fuskantar matar, bata ga tahowarsa ba balle ta ganshi, don haka bai jira komai ba ya ƙarasa da taku biyu ya riko hannunta, yatsunsa suka lankwasa a tsakanin nata tun kafin ta juyo a lokaci guda da ta kalle shi, ta kalle shi da idanunta a zare da tsananin tsoron da cikin sakanni biyu kawai ya juye zuwa mamaki.
    “Jawad…??”
    Bakinta ya furta a hankali yayin da zuciyarta ta buga sau ɗaya, ta buga da wani sauti da ta tabbatar da cewar dukkan sauran mutanen dake zagayensu sun ji shi. Ba shiri idanunta suka cika da shekin kwallar da bata san ta ina ta fito ba, mamaki take idan shi din ne ko kuma mafarki take yi… Don tunaninta ya kasa bata cewa zai iya zuwa ya same ta a wannan wajen kuma a wannan lokacin.
    Sai dai babu wani bata lokaci, yayi abinda ya tabbatar mata da cewar da gaske shi din ne ba wani ba, da gaske Jawad din da ta sani ne…
    Hannayensa duka biyu suka zagaye jikinta, ya rungume ta a cikinsu, ya rungume ta a kirjinsa, ya rungume ta a gaban tarin mutanen dake wajen ba tare da tunanin komai ko kuma abinda za’ace ba..
    Sai kawai ƙwallar da ta cika idanunta ta zubo kan fuskarta, ta riga ta sani komai ya zo ƙarshe, wahalar da take tunani ta yanke tun kafin ma ta fara, shikenan tayi sallama wa dukkanin wahalarta!
    ***
    *03:15 am.*
    Tana tsaye daga jikin tagar dakin, hannayenta duka biyu dafe da gilashin da aka rufe yagar wanda ta manna fuskarsa a jiki yayin da idanunta ke tsaye ƙyam! Akan wanda ke kwance a akan gadon dakin, ance mata Ma’aruf ne, kowa yace mata shine, amma fiye da minti goma da take tsaye a wajen babu wani abu a kwakwalar ta da yatuna mata cewar Ma’aruf din da ta san shi take kallo.
    Fuskarsa a kumbure take idan ka dauke katuwar robar zukar numfashin da aka manna a fuskarsa da kuma gashin kansa da aka aske, wannan sumar… Wannan sumar ta Ma’aruf da kullum take tare da hannaensa, yanayin yadda yake cusa su a ciki kadai Kala-kala ne ta yadda ta kan fahmci wani abun da yake nufi idan yayi tun ma kafin ya furta.
    Don haka gabaɗaya kamanninsa sun canja ta yadda ko ba’ayi wa mutum bayanin rashin lafiyar dake damunsa ba shi da kansa zai kintata tun daga harafan dake rubuce ɓaro-ɓaro akan gilasan wajen da launin ja… ICU.
    Wani abu ya wuce ta makogwaronta lokacin da ta tuna da san da ta farka ta riski labarin komai… fuskar Amma ta fara gani kafin komai, tana zaune daga kujerar dake gefen gadon da take kwance, hannunta rike da wani carbin ta kalar yalo, wani carbi da a cikin su gabaɗaya babu wanda zai iya fadar adadin shekarun da suka san shi a hannunta, dashi take lazimi kulum, a kowacce safiya da kuma yammar Allah.
    Ta rufe idanunta a hankali sannan ta sake bude shi tana kara kallon Ammar da kanta ke sunkuye tana addu’o’in ta, yanayin sai ya koma mata iri ɗaya sak da wani lokaci a can baya, lokacin da Maryam bata da lafiya, lokacin da suke zaman jinyarta a asibiti, haka Amma ke zama a gaban gadonta da wannan carbin tana lazimi.
    Fahimtar cewa yau itace ba Maryam din ba ya dawo mata da zagayen halin da take ciki, ya tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta da ma irin tashin hankalin da ta shiga…
    Ko kuma tashin hankalin da har a yanzu ta farka a cikinsa, tunda bata san me ya faru ba har a lokacin, bata san ina Ma’aruf yake ba sannan bata san a wane hali yake ciki ba, tun a lokacin aga yanayin fuskokin su Munayan da suka shigo wajenta tunaninta ya gaya mata cewa abinda ya faru ba labari ne mai daɗi ba, sannan a lokacin ta ƙara tabbatar da cewar da gaske tunaninta hakan ne tunda bata ganshi ba.
    Ta sake bude idonta a hankali, lokaci ya nuna mata ƙarfe goma sha biyu na safiya wanda hakan ya tabbatar mata cewar har a yanzu tana cikin wannan ranar ne tunda da sassafe ne lokacin da su Munaya suka zo suka same ta.
    Ƙofar ɗakin ta buɗe a sannan, Aunty Ma’u ta shigo bayanta goye da ƴar ƙaramar ƴar ta, hannunta da rike da wani a kwandon kwanukan abinci.
    Amma ta amsa sallamarta tana juyawa.
    “Bata farka ba dai ko?”
    Ta tambaya tun kafin ta karaso.
    “A’a har yanzu, amma Nurse din da ta fita tace ba zata dade ba zata farka.”
    Aunty Ma’u ta ajiye kwandon abincin sannan ta sauko hoyon yar tata dake bacci Amma ta karbe ta.
    “Su Tanti suna hanya, tace akan kwana suka hadu da Safiyya yanzu zasu taho.”
    Kuma sai da ta zauna daga gefen gadon sannan tace.
    “Ya muka ji da wadannan abubuwa da suka faru Amma? Labari haka rana tsaka babu daɗin ji…”
    Amma ta gyara kan yarinyar dake cinyarta tace.
    “Wallahi Ma’u muma haka muka tashi da kira wai an kawo ta asibiti ta suma, yanzu su Maryam suka koma su ma tare da yariyar dake wajenta Hamida, don likitan yace da ta farka zamu iya tafiya, rashin kwarin jikinta ne yasa suman ya same ta a lokaci guda.”
    Aunty Ma’u ta gyada kanta tana sake kallon Aminan dake kallonta ta tsakanin gashin idonta.
    “Inalillahi wainna ilaihir raji’un… Ɓari fa akace ta kusa yi Amma, wannan wane irin labari suka gaya mata?”
    “Su waɗanda muka tarar anan sun ce ai tun kafin ma su san wannnan al’amarin aka kawo ta asibitin. Komai ya rikice ne kawai Ma’u don ita kanta Tantin da muka yi waya ban iya gaya mata wani abu ba tunda har yanzu su ma babu wanda ya gama sanin abinda ake ciki, Munayan tace min sun san dai an tafi da ita Kilshin wajen ƴansanda daga asibitin nan, shi kuma an kwantar dashi.”
    Aunty Ma’u ta gyada kanta.
    “Irin wannan sai an kwana biyu dama za’a san me ake ciki tunda su kansu yanzu hankalinsu ba’a jikinsu yake ba.”
    Amma tace.
    “Duk sun taho ma, har da ƴarta daya Sameerah, suran ne suke can gida tare da wasu yanuwansu don Mama Rabin da na hadu da ita tace gidan ya zama kamar na makoki daga safiya zuwa yau…”
    “Allah ya kyauta, ni wallahi banyi mamaki ba Amma, a wannan zamanin jama’ar da suke da fuska biyu wajen cutar al’umma suna da yawa, kuma ba ma wai sai a wani babban abu ba, wani ko ba zai samu komai ba idan ya nuna baya kaunar ka a bayan idonka zai ji daɗi, kawai dai ita nata yayi yawa ne, cuta da kuma zaluntar ciki tafi karfin tunanin mutane ire-irenta da yawa..”
    Amma ta yi shiru kafin tace.
    “Zancen babu daɗin ji Ma’u, iya wanda ya fito a yanzu kaɗai balle kuma abinda zai fito daga baya, ƴan uwanta ma wasu basu yarda ba, abin ne kamar mafarki, kamar labari… Sai dai addu’a kawai.”
    “Allah ya kyauta, Allah ya basu hakurin ɗaukar hakan ya bi musu hakkinsu, sai a godewa Allah don watakila da lokaci ya ja, zata iya aikata fiye da wanda tayi ma a baya.”
    “Wannan haka yake, don al’amarin yafi karfin tunaninki, Allah ya bata fikira da kuma dabarar da ta bari shaidan ya karbi linzaminsu.”
    Ƙwalla ta cika idanun Amina a lokacin tana hana mata ganinsu bakiɗaya sannan tunaninta ya cilla kan maganganunsu tan son fahimtar da kanta abinda bata gane ba… su waye suka yi hatsari? Wanda take nufi an kawo asibitin Ma’aruf ne? Abinda su Munaya zasu gaya mata kenan? Abinda ta kasa tsayawa ta ji kenan? An kama wani? Hajiya Kilishi ce? To ta yaya hatsarin ya faru? Komai yazo ƙarshe kenan? A wane hali su Samirah ke ciki? Baffa… Sauran mutanen gidan…. Ma’aruf ma…
    Wadannan tambayoyin su suka yi ta haskawa a cikin kanta har lokacin da taji Amman tace.
    “Bari na sake lekawa can inda aka kwantar dashi naga me ake ciki dama jiran ƙarasowar ku nake kar a bar ta ita kaɗai.”
    Ta faɗi hakan sannan ta miƙe tsaye ta juya kan wata kujera daga can jikin bango ta ajiye yarinyar.
    Amina bata ga sanda ta fita ba ta dai ji ƙarar rufewar ƙofar da kuma muryar Aunty Ma’un bayan nan tana kwatance wa su Tantin da suka kira ta a waya, don haka bata bude idanunta ba sai a daidai lokacin da ta kai ƙarshe a wayar wanda hakan yasa tana bude idon ta kula da ita
    “Alhamdlilah, Amina kin tashi? Sannu…”
    Ta faɗa kai tsaye tana ƙarasowa gaban gadon.
    “Sannu Amina, sannu….”
    Ta sake faɗa tana rike hannunta wanda ba’a saka masa allurar drip ɗin da take ji a jikinta ba, sai tayi kokarin miƙewa a hankali tana kama hannun Auntyn Ma’un sosai.
    “Sannu…”
    Ta ƙara faɗa tana riƙe ta.
    Bakinta a rabe yake kaɗan amma bata ce komai ba… Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta tana ƙoƙarin gyara zamanta.
    “Bari in zubo miki abinci ki iara jin kargin jikinki..”
    Aunty Ma’u ta sake faɗa tana ƙoƙarin juyawa, sai tayi saurin kamo hannunta da sauri tana kallon ta.
    “Aunty me ya faru? Su waye suka yi hatsari?”
    Muryarta ta fito a bushe kamar yadda lebbenta yake. Aunty Ma’u ta girgiza kanta.
    “Bari ki fara cin wani abu Amina…”
    “Aunty dan Allah…”
    Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa. Tana jin yadda wani abu kamar kwalla na kokarin cika idanunta yayin da bugun zuciyarta ke dokawa ta yadda bata tunanin ko yawu zai iya wucewa ta makogwaron nata.
    Sai kawai Aunty Ma’un ta dawo ta zauna a gefen gadon ba tare da ta saki hannunta ba sannan tana kalonta sosai tace.
    “Ma’aruf ne yayi hatsari tare da Hajiya Kilishi Amina, amma ba wani abu ne ya same shi ba, jikin nasa da sauki, kar ki daga hankalinki sun ce babu abinda ya same shi… Ki samu ki ci wani abu yanzu, Amma tace za’a iya sallamar ki a yau, sai mu je ki ganshi….”
    Abinda ta fada mata kenan, abinda ta rude ta dashi har ta kwantar da hankalinta ta iya cin wani abu a abincin da ta kawo ba tare da ta san cewa babu zance ɗaya daga da yake gaskiya ba a duk abinda ta fada.
    Don bayan Amma ta dawo har kuma an kira likita ya sallame ta, tun daga hanyar zuwa wajen ta fahimci cewar al’amarin yafi karfin yadda ta lissafa shi… Babu kowa a wajen lokacin da suka isa, su Hajiya Maimuna da duk dimbin jama’ar da suka taru a wajen lokacin da aka kawo shi duk sun koma gida, can gidan da a yanzu ya koma kamar gidan zaman makoki saboda ƙarancin tashin hankalin da ya wanzu a cikinsa.
    Don haka ita kadai aka bari ta shiga wajen yayin da su Amma suka tsaya daga waje… Kuma Amma ce ma ta danyi mata bayanin abinda ya same da taji daga wajen su Hajiya Maimuna lokacin da tazo ta same su… Likitocin sun ce bugun zuciyarsa baya tafiya daidai, sannan ya farka sau biyu amma duka ba’a haiyacinsa yake ba… Sannan bayan haka numfashinsa ma baya iya fita daidai (Respiratory insufficiency).
    Bata san tsawon mintunan da ta shafe tsaye a wajen ba,ta san dai kawai lokaci mai tsawo ya tafi zuciyarta na ta sake-sake da tunanin ayyana halin da Ma’aruf ko kuma sauran ahalin gidn ke ciki kafin wata Nurse ta gaya mata cewa su Amman dake waje suna jiranta.
    Ƙafafunta suka dauke ta zuwa waje, dogon koridon asibitin inda t barsu a zaune, dogon hijabi ne a jikinta na Maryam wanda Baba ya dawo daga baya ya kawo mata, ta fita daidai lokacin da su Amman ke gisawa da Ishaq da kuma Abdurrahim wanda suka ƙaraso a lokacin, kuma kallon Ishaq din kawai tayi taji kwalla ta cika idanunta don haka kanta a sunkuye ta karaso gabansu sanda suka shiga gaishe ta da jiki shi da Abdurrahim ɗin da kawai ɗago mata hannu yayi.
    Ta share hawayenta da bayan hannu sanda Amma ke gaya musu cewa ta kira su Hajiya Maimuna babu wanda ya ɗaga idan yaje yace musu zasu tafi da ita gida zuwa jibi don ta kara jin daɗin jikinta tunda Hamida ma na can tare dasu Maryam, Ishaq ɗin ya amsa amma ko daga muryarsa kaɗai Amina ta san cewar har yanzu ba’a haiyacinsa yake sosai ba, tashin hankalin da shi da kuma zagayen al’ummar dake gefensa ke ciki ya isa ya sa shi a kowanne irin hali.
    Kowanne irin halin da mutum guda daya yayi sandinsa ga tarin mutnen da a yanzu ita kanta bata san adadinsu ba….
    Kilishi….!
    ****
    Tana zaune akan kujerar da teburi ya raba ta da wadda ɗansandan dake kallonta ke zaune.
    “Hajiya gwara ki buɗe baki kiyi bayani kawai, komai yazo karshe, mun kama duk wani wanda kike mu’amala dashi a harkar ki, hatta sabon yaron ki Sadik Awwalu yayi mana kwatance munjeun taho dashi, sannan mun kama likitan da kika hada baki dashi a asibiti ma da cewar kin makance, so ki bude baki ki yarda da laifinki, Shari’a sabanin hankali ce da za’a iya yi miki rangwame, baki da kowa kuma baki da komai a yanzu, don bana tunanin koa cikin iyalanki ko kuma yanuwanki akwai mai bin goyon bayan ki a yanzu…. Zai fi kyau ki sallama ki saukaka mana aiki Hajiya…”
    Dan sandan yayi dukkan wannan bayanin yana kallon Hajiya Kilishi, yana kallon fuskarta da take manne da baneji a wajaje da yawa da kuma karyayyen hannunta wanda aka sakale shi ta wuya bayan anyi mata gyara, idanunta a tsaye suke cak!
    A tsaye tana kallonsa, tsawon sakan ɗaya biyu, uku… Kafin ya mayar da kansa kan file din dake bude a gabansa wanda akan farar takardar dake kai, jerin laifukan da ake zarginta dasu ne wanda tun farkon suka rubuta bayan an tabbatar da kama ta da kwayoyin nan da kuma wanda a yanzu suka ƙara samu daga bakin yanuwanta bayan hatsarin da ta samu na biyu.
    Baki da kowa kuma baki da komai…!
    Sune kalaman dake maimaitawa a cikin kwakwalar Kilishi, suk sae dawowa suna komawa baya a lokacin… Tun bayan lokacin da Ma’aruf ya fitar da ita daga asibitin nan, tun daga lokacin tunaninta ya tsaya, komai ya faru ne a idanunta kamar tatsuniya, kamar wani mummunan labarin dake faruwa a cikin mafarkin yaro, bata gama warware zaren daya kulle ta a cikin al’amarin cewa yansanda na jire da ita suna nemanta ba, batagama lissafa hanyar mafitar ta da ta fara budewa ba,bata yi komai ba,tana cikin zagaye guda daya nesa kuma ga abinda zata ya kira da tashin hankalin duniya da kuma lahira ya riske ta.
    Jiya rana ce da bata taɓa tunanin tunanin Allah zai haiccce ta ba a duniyar nan, a dukkan tsare-tsare da kuma lissafin da a tsawon rayuwarta bata taɓa hangen irin abinda ta gani ba a jiya, tana tsara komai kuma komai din yana tafiya daidai, kawarta Salamatu ce ma kawai kan tuna mata da cewar a duniya take ba’a aljanna ba cewar wani abun zai iya zuwa mata a karkace, amma ko yazo din, tana daga kwance take sa hannun guda ta gyara shi.
    Alah ya bata tarin nasarori a rayuwar nan, bata jin akwai abinda ta taba zanawa zuciyarta da bai faru ba, bata jin ta taba ko da hasashen manufarta ne kuma hakan bai kasance ba, to dan me yasa sai a yanzu da rana tsaka kawa komai zai gargitse mata kuma ta yarda?
    Ta yarda ta rasa Ma’aruf, ta rasa shi ta rasa kulawa da kuma ƙaunarsa. Babu kalamansa ko a cikin kanta, ta ji su a lokacin da ya fade su kuma ta barsu a wajen, babu abinda ta dauko sai ciwo da kuma takaicin rasa shi da tayi ta wannan hanyar a raywarta, ta shirya dama, ta shirya barinsa don haka ta dade tana ywa zuciyar tata tanadi na wasu abubuwa da zasu dauke hankalinta bayan ta bar cikin rayuwarsu, amma da hakan ya faru a lokacin da bata shirya ba sai ya dake ta da tsananin tashin hankalin da bata ƙara ganin wani abu da ya tsorata ta ba bayan hakan ba.
    Ko sanda ya danna kan motar suka tafi suka daki bishyar nan, bata ji tana tsoron mutuwa kamar tashin hankalin cewa an riga bude ainihin kammaninta a idanunsa ba.
    Da kuma sanda ta kalli idanun su Baffa, Baba Usman, Ishaq, abokin Ma’ruf mai suna Faruq da kuma Abdurrahim… Ta kalli idanunsu ne tana jin zuciyar fayau yayin da tunaninta yake wasai, don tunda zuciyarta ta karɓi tashin hankalin wajen Ma’aruf bata tunanin kuma akwai wani abu a duniyar nan da zuciyar tata zata sake rusunna masa, hatta Baffan kuwa, hatta shi din da ya zame mata tsani kuma hanya wajen aikata dukkan abinda ta wanzar a rayuwarta.
    Tana kallon kowa ne kawai tana kuma jin abinda suke cewa, amma yadda bata furtawa Ma’aruf ko da kalma guda ba, haka babu abinda tace har wayewar garin yau, abu daya kawai take so ta yarda dashi shine cewar ba zata yi biyu babu ba, ba zata rasa Ma’aruf ta kunyata a idon duniya a rana guda ba sannan kuma ta rasa burin rayuwarta ba, ba zata taɓa iyawa ba, ba zata yarda an zo gaɓar da zata je ƙasa ba kamar yadda ta shar’antawa kanta a baya ba, har yanzu tana da yardar cewar damarta bata ƙare ba, dole ne ta fidda kanta kamar yadda ta sa ba.
    Dan sandan yace bata da kowa a yanzu,ta yarda, ta yarda da hakan… Don tun da ta rasa yardar Ma’aruf ta sani cewa ko yardar ƴaƴan ta ba zata samu a yanzu ba, don haka ta yarda zata barsu, zata bar kowa nata sannan zata bar kowa da ta sani, abinda bata yarda ba shine da yace bata da komai, wannan ne zuciyarta bata amsa masa ba don ita ta san tana da abinda zata kare kanta ko a gaban wane alkali ne a duniyar nan.
    Amma ba za’a kai nan ba ma, ba zata je gaban kowanne alkalin ba, zata yi nisane da kowa, zata yi nisa zuwa wani waje da zata kafa sabuwar rayuwarta, sabuwar rayuwar da ta san a cikin lokacin da zai ja mata… Dole ne yayanta zasu dawo gare ta, dole ne watarana zasu juyo su waiwaye ta, don meye yake raba ya’ya da uwarsu a duniyar nan?!
    Sai kawai ta mika hannunta mai lafiyar ta janyo file din dake gaban ɗan sanda, ya dago ya bita da kallo fuskarsa na shaida mamaki da kuma tunanin abinda take shirin yi, ta ajiye file din sannan ta sake mika hannunta alamun ya bata biron da yake rike dashi, sakan daya, biyu… Kamar ba zai bata ba sai kuma kawai ya mika ma tan, bayan ta karba yana kallon yadda yatsunta dama rubutun da take yi ke rawa, rawar dake shaida rikicewar da yanayinta ke ɓoyewa.
    Lambobi ne, lambobi ta rubuta guda goma wanda ba sai ya tambaya ba ya san lambar asusun banki ne (account number), ta ajiye biron akan file din sannan ta sake turo masa shi gabansa.
    Idonsa ya kalli lambobin sannan ya dago ya sake kallonta, a lokacin ne kuma tayi magana ta faɗi abinda ba ga ɗansandan ba kadai, har ga ita kanta ya tabbatar mata da cewar har yanzu tana nan a matsayin Kilishinta…. Tanan bata canja ba!
    “Akwai kudi sama da miliyan dari huɗu a cikin account din nan, ka taimake ni in fita daga wannan wajen, ka taimake ni inyi nisa daga dukkan wadannan matsalolin dake rubuce a cikin file dinka, ni kuma nayi alkawarin zan baka rabin kudin da nake dashi, zan gyara rayuwarka ta yadda har ka koma ga ubangijinka ba zaka taba sanin ɗacin Babu ba!”
    Ta kai karshe a lokacin da idanun ɗan sandan ke kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassara a lokaci guda!
    ***
    A cikin ɗakin asibitin ba ka jin komai sai ƙarar kaɗawar iskar Acn da ya kaure ko’ina.
    Hajiya Mardiyya ta girgiza kanta riƙe da wayar dake kare a kunnenta kafin tace.
    “Kar ku damu Khadija, ki bawa su Innan ma hakuri, tahowarmu ba zata wuce gobe zuwa jibi ba insha Allah, ni ban san haka wannan asibitin yake ba da muka dauko ta wancan na gwamnatin muka kawo ta nan, su bamu refferal kawai abu na neman gagara… Ashraf dai yace yayi magana da likitan dazu, ni ko bai yarda ba zan dauko ta ne kawai mu dawo ba zan jira ba.”
    Ta gyada kanta sannan ta sake cewa.
    “Eh, Ahmad ne ya taho yau, da asuba ya kira ni yace Babansu yace yazo ya kawo min saƙo… Amma shi kadai ya taho banda sauran.”
    Wadda suke wayar a ciki ta amsa kafin ta ta lashe wayar tana ajiye ta a gefen bedside drawer dake kusa da gadon, kusa da gadon da Rukayya ke kwance idanunta a rufe.
    Kusan awa guda kenan da ta samu bacci, awa guda bayan ta farka da tarin surutan da a ciki basa iya gane komai sai sunan Hamida ƴarta da kuma Hajiyan Sudan da take ambata, Ashraf yace zai iya yiwuwa shine abu na ƙarshe da ta dinga fada lokacin da hatsarin ya faru, ta ga Hajiyan Sudan din a wancan asibitin na farko da suka je dauko Rukyya, ita bata ganta ba kuma bata bari ta ganta din ba, babu kowa a wajenta kafafunta na karye duka biyun an nade su da bandeji an kuma dage su zuwa sama.
    Tana ji wata Nurse na faɗan cewar har yanzu ba’a sami wani danuwanta da zai zo ya biya kudin treatment da akayi mata ba… Bata ce komai ba suka biya kudin Rukayyan kawai suka karbi sallama suka juyo.
    Don abu na karshe da zata yi a rashin hankalinta shine ta nuna wata mu’amala tsakaninta da Hajiyan Sudan ɗin a gaban Ashraf, ta sani kashinta ne zai bushe idan har mijinta ya san da hakan… Ya san abinda ta tura Rukayyan yi a Niger kuma tare da ƙawarta. Don haka bata ce komai ba har suka bar asibitin suka kawo ta wannan.
    To a yanzu Ashraf din ya dame ta da tambayar wacece Hajiyan Sudan din da Rukayyan ke kira, ta gaya masa cewa itama bata san ta ba amma kallon da yayi mata bayan ta gaya masa hakan ta san ba na yarda bane.
    Ta sake kallon Rukayyan, ciwonta da sauki ba kamar yadda suka zata a farko ba, mild stroke ne mutuwar barin jiki wanda likitoci suka tabbatar masu da cewar ba zai dauki lokaci ba zata warke ta koma daidai idan har za’a bi dokin da da kuma kaidojin da suka dace… Ita ta sani dama, ta san Allah ba zai jarraba su ta wannan hanyar ba, kyawun yarta haɗe kuma kyawun jikinta wani abu ne da ba zai nakasa ba.
    Don haka hankalinta ya dan kwanta ta yadda bata hango komai sai komawarsu Nigeria don su cigaba da jinyarta acan ba tare da asirinta ya tonu ba.
    Lokaci ya nuna karfe biyu daidai yana tuna mata da sallar azahar din da bata yi ba, don haka ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala sannan ta shimfida slaya a gefen gadon ta tayar, zuciyarta cike da fatan kafin idarwar tata, Ashraf ya dawo tare da Ahmad din da yaje daukowa daga airpot.
    Ai kuwa sai fatan nata ya karbu don a sallamar raka’a ta karshe su ma suka yi sallama suka shigo dakin.
    Ta amsamusu a lokaci guda da ta fahimci rashin fara’ar dake kwance akan fuskarsu… Ahmad din ne ke gaishe ta yayin da Ashraf ya samu kujera ya zauna fuskarsa na numa tsananin bacin ran da ta dade rabon da ta ganshi a fuskarsa.
    “Me ya faru? Wani abu ne ya faru kuma?”
    Ta tambaya tana kallon dukkanninsu… Kuma Ahmad din dake gabanta bai ce komai ba sai kawai yasa hannu ya ciro wata takarda daga aljihunsa ya dora akan sallayar da take kai.
    “Sakon da Daddy yace in kawo miki ne.”
    A lokaci guda zuciyarta ta buga a kirjinta, bata san meye a cikn takardar ba, bama tayi tunanin menene din ba, amma daga yanayin fuskokin yayan nata kadai ta san ba abu ne wanda zata so shi ba, dn hak ta yankewa kanta nisan taraddadin, ta mika hannunta a hankali wanda ke rawa ta dauki takardar, kuma tun kafin ta kai ga buɗe ta, taji kwalla ta na neman cika idanunta yayin da kwakwalar ke gaya mata cewa ita ta riga ta karbi sakon tun kafin ma ya iso.
    A rubuce a ciki, Hajiya Nafisa ta tadda kalaman da sune abu na karshe da kunnen kowacce mace zai so yaji su daga sautin mutumin da take raba rayuwarta tare dashi!
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!