Farar Huta 2 – Chapter Twenty-four
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“Anan wajen ya mutu Mami…”
Ma’aruf ya faɗa da sautin muryar dashi kansa ya sani baiyi kama da nasa ba, a zaune yake a cikin motar idanunsa a manne da wata katuwar bishiyar dake gabansu, daga bayan motar, kujerar baya Hajiya Kilishi ce zaune kanta a sunkuye yayin da idanunta suka yi jawur da tsananin tashin hankalin da baya mata kama da zahirin da mutane ke rayuwa.
Tashin hankalin da ya canja kamanninta, ya mayar da lissafin kammanin ta wani irin da da wuya ne ka gane ta a lokaci guda, don hatta jikinta ya canja a cikin kwanaki biyu kaɗai! Ta rame ta sirrance sannan tsufa da kuma shekaru ta da a kullum kwalliya da murmushin ta ke ɓoye su sun baiyana tar!
“Anan wajen ya mutu bayan ya gaya min kar na kashe… Shine abu na karshe da ya gaya min Mami bamu sake magana bayan hakan ba, yana amsa waya lokacin da kaddarar da kika halitta mana ta faru… I was driving safely, na sani cewa tun a wancan lokacin banyi wani abu ba daidai ba.
Kawai naji sitiyarin ya ƙwace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi a wannan lokacin Mami, sannan ina ganin hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta taho cikin dajin nan, daga ni har shi babu wanda yaga wannan bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda wani reshenta yake a karye sannan daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa reshen ya faso ta cikin gilashin ya soke shi a ko’ina na kirjinsa….”
Muryarsa tayi ƙoƙarin shaƙewa amma ya cigaba.
“… Ya rasu yana kallona Mami, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama’a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, kuma ba’a iya fito dashi ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa…. Har akayi masa wanka aka kaishi kabarinsa da itacen bishiyar nan a jikin sa Mami.
Kina tare dani a asibiti a lokacin, kin san wannan ranar itace sanadiyar samun ciwo na, ciwon da ya tauye tarin abubuwa da yawa a rayuwarta, kin san dukkan wahalar da na sha Mami, kusan haukacewa nayi kin sani, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar kadai ke maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru…
Na dade inabincike Mami, na daɗe ina bincike fara bincike akan al’amarin, sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutum biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tuƙin nan, na gane cewa da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ƙara sai kawai ta fashewar tayar.
Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin amma har aka zo gaɓar da hankalina ya karkata ga aikin kamfani da kuma binciken wata ɓarakar da kike haifarwa acan ban sami komai ba Mami, duk hanyar da na bi bata ɓullewa kamar yadda a binciken kamfanin ma bana samun komai, kawai ina ƙarewa ne da tarin bacin ran dake sawa ciwona ya tashi, komai ya sake tsayawa a rayuwata ta yadda bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal, in kuna kawo ƙarshen komai, wanda hakan shi ke kara baki dukkan wata dama da kike kassaramu da ita….”
Wani abu ya wuce a makogwaronsa da bai san meye ba, yayin da yake jin tasirin kowacce kalma da ya furta da kuma yanayin tare da tashin hankalin dake zagaye dasu na haddasa wani abu a ƙirjinsa da bai san meye ba, kuma a lokacin ne ya juyo ya kslle ta, har yanzu bashi take kallo ba, kanta a juye ysketana kallon waje, idanunta auna tafiya zuwa wani nisan da bashi da karshe, idanunta da har yanzu basa nuna masa kamanin Mamin da ya sani, baya ganinta a tare da matar dake gabansa kwata-kwata.
Har yanzu a gaban bishiyar motar take, bishiyar da ta shiga cikin wani ɓari na rayuwarsa, ɓarin da ya riga ya zama tambarin da a kodayaushe a kowanne waiwaye shi zai fara kalla a rayuwarsa.
Ƙarfe shida na safiya, ƴan mintuna kaɗan bayan sallar asubahi lokacin da suka ƙaraso wajen, yana tafiya ne da karfin gudun da tun daga nesa wani magidanci dake tahowa akan keke daga hanyar shiga kauyensu ya hango ta, hasken fitilun gaba ya fara gani kafin kurar dake bin ta a baya ta cika idanunsa.
Ba shiri ya dawo da idanunsa kan gonakin dake gaba, gonaki kusan biyar dake dauke da sabbin shukoki da suka fara fitowa, kuma kafin ya gama lissafin abinda ke shirin faruwa, motar ta karaso ta zarce ta cikinsu da tsananin gudun da tayoyinta har dagawa suke saboda tudun kunya-kunya dake gurin, tana wucewa tayoyinta na murje shukokin da matukin cikinta baya ko ganinsu balle yaji alamunsu daga ciki.
Hannunsa akan sitiyarin suke kawai yana danne shi wajen kara nausawa ciki, dogwayen bishiyun da idanunsa ke gani kadai yake iya kaucewa bayan haka baya ganin komai, baya jin komai sai tarin maganganun dake tarewa a cikin kansa suna sake dawowa.
Maganganun dake sa wa tun yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, yana jin huci da kuma dumin wani abu na ratsa kirjinsa zuwa cikin idanunsa, har ya daina…. Ya zama baya jin komai… Baya jin komai sai sautin muryarta dake fitowa daga cikin wadannan CD’s din a lokacin da yake tsugunne a gaban computer Abdurrahim.
Yana tuna kowacce kalma da ta shiga kunnensa yana tuna su bi da bi saman kwakwalwarsa na tsara masa su daki-daki a yadda al’amarin ya faru a yadda komai ya kasance… Sannan bayan haka daga can ƙarshen kansa muryar Awwalu ce ke amsawa, dukkan bayanan da zai iya tunawa yaji lokacin da yake shaidawa su Baffa tarin abubuwan da suka daɗe suna binne su a cikinsa.
Ya sani cewa zuwan Awwalun da kansa a wannan lokacin da kuma abubuwan da yake fada abu ne mai mutukar mamaki duba da tsawon lokacin da suka shafe suna nemansa, amma mamakin sautin muryar Mamin da kuma tarin abubuwan da dake fitowa daga muryar tata ya shallake dukkan wani abu a cikin kansa bayan hakan duk da cewar bayanan Awwalun wani abu ne da ya ƙara basu dukkan tabbacin da zasu nema, don Allah ya sani zai iya ƙaryatawa.
A wannan lokacin zai ce ba haka bane, zai ce dukkan abinda yaji karya ne… Zai yarda da dukkan wata hujja da zata gaya masa cewa impersonation ɗin Maminsa aka yi, Mamin da ya sani mai ƙaunarsu ce, zuciyarta a buɗe take ga kowa, ba zata taba ko iya hada hanya da wanda zai cuce su ba balle ta saka hannu, balle kuma ace itace ja gaba wajen faruwar munanan abubuwa da yawa a rayuwarsu….
Sai dai me? Bai ma yi wannan fatan ba, baiyi ma yi wannan tunanin ba aka tafi har zuwa gaɓar da komai ya tabbata, komai ya tabbata ta sigar da basu da wata kafa ko kuma hujjar ƙalubalantar abinda suka ji.
Kuma ba ga shi kaɗai ba, ya sani dukkansu a yanzu dalili zasu so sani, dalilin da yasa tayi hakan, ta aikata tarin abubuwan da baya jin ko akan fatar bakinsa zai iya furta su, dalilin da yasa ta shigo rayuwarsu tun farko ma, dalilin da yasa basu taba ganin komai ba sai tarin murmushi da kuma dimbin kaunar dake nunawa akan fuskarta mai kaifi, kaifin da take amfani dashi tana huda zuciyoyinsu a tarun lokutan da ko sau daya wsni a cikinsu bai taɓa waigawa yaga makamin da hannayenta ke rike dasu ba.
Wani? Akwai wanin da ya dace ne bayan shi? Akwai wanin da ya kamata ace a cikin ɗinbin shekarun da ya rayu tare da ita ace ko sau ɗaya idanunsa ko kuma tunaninsa basu taɓa haska masa wani abu da ya kamata ya ɗorawa ayar tambaya akanta ba?
Hannunsa ɗaya ya shiga cikin gashin kansa a lokacin da ɗayan ke kara danne kan sitiyarin suna ƙara nausawa cikin dajin, a cikin hannunsa ya shake likitan da aks ce ya jagoranci ƴar karamar tiyatar da akace anyi mata an tabbatar da makantar idanunta, kuna ba’aje koina ba a cikin hannun nasa likitan ya gaya masa cewa ita ta nemi da yayi mata hakan ya fadawa kowa cewa ta makance bayan tayi masa alkawarin tarin wasu kuɗaɗen da ba zai iya ƙin tayin ba.
Kuma daga idanunsa kaɗai ya san ta sani, ta san ya san komai, tun kafin ma ya faɗa shi yasa bata ce komai ba har yanzu, har suka ƙaraso wajen da bai manta hanyar ba, don ba zai taɓa manta ta ba, yazo fiye da sau goma kuma a zuwan farko ne kaɗai yayi bilinbituwar da ta ɗauke shi awanni kafin ya iya gane ba wajen, bayan haka baya jin ko a mafarkinsa ya taɓa kauce hanya.
A lokacin da suka ƙaraso, idanunsa sun tsaya akan bishiyar da kuma gudun da motar ke yi a cikin hannunsa, yaji wani abu na yawo a cikin kansa kamar wancan lokacin, shekaru goma da suka wuce, lokacin da hannayensa dama duk wani abu mai tsini a cikin kansa suka kasa tsayar da motar dake nufar bishiyar da yake kallo a yanzu, da sanda suka tafi suka dake ta, suka dake ta a yanayin ba zai taɓa fita daga kansa ba…
Sai kawai ya danna birkin motar a yanzu da ƙarfi, da ƙarfin da ya fitar da sauti mai ƙara daga waje, ƙarar ta karaɗe cikin dajin zuwa nisan da ba zai iya kintata ba, kuma duk da karfin birkin, motar bata tsaya ba sai da taje dab da bishiyar, dab da ita sosai ta yadda bai fi tazarar taku biyu kawai ba a abinda ya rage
Tayoyin na tsayawa ya buɗe ƙofar ya fito, ya fito ya buɗe ta baya idanunsa na kaiwa kan Hajiya Kilishin da har yanzu bata kallonsa, kanta na juye daga gefe tana hangen wani wajen daban, da tafiyar da suke yi da ma karfin birkin da ya faru a yanzu babu daya da ya canja ta daga mazauninta, idonsa ya tsaya akan fuskarta, awanni kadan da suka wuce, awanni da basu fi kirgen yatsunsa ba, duniyarsa a tsaye take game da rashin lafiyarta, yana jin komai ya birkice masa yana jin rayuwar ba daidai take tafiya ba tun kafin ma ya san sakamakon abinda ya same ta.
Amma a yanzu gashi tsaye a gabanta sai dai a yanzu bashi ɗin bane, ba Ma’aruf ɗin da yake a jiya bane, ba Ma’aruf ɗin da yake a shekarun baya bane… Baya jin kansa a matsayin kowa da kuma komai, jin sa yake a wani sabon mutum daban, sabon mutum ɗin da babu komai a zuciyarsa illa tarin abubuwan da yaji ya kuma sani daga daren jiya.
A karo na farko, yaji wani abu kamar kwalla na shirin ziyartar idanunsa, sai kawai ya juya ya koma mazaunin direban ya juya ya buɗe booth ɗin baya na motar… idanunsa suka tsaya akan rediyon motar yayin da yake jin zuciyarsa na girgizawa tamkar yadda yatsun hannayensa ke yi, sai kawai ya danna ya play buttun a jiki kuma a take sautin dake fitowa ya karaɗe kowacce speaker dake cikin motar.
_”Ka yi masa magana kawai Awwalu, na yarda zan bashi hakan, babu abinda ba zan bayar ba saboda wannan aikin… Ya kamata ka sani tun da har na kashe Jamal babu abinda ba zan iya ba akan cikar burina…”_
Tashin hankalin da ya daki tsakiyar kan Hajiya Kilishi a lokacin ba abu ne da zata iya misaltawa ba, tun daga lokacin da ta farka a daren jiya, lokacin da ta gama jin hirar dukkanin abinda ya same ta, ta daɗe kwance a wajen tana tsara hanyar mafitar da zuciyarta ke saƙa mata, ta da yadda zata wanke kanta a idon kowa ta kuma fita daga ƙullin ƴansandan nan… Kuma tsarin nata ta tafi daidai a cikin kanta, ta ƙirga komai ta fitar da dukkan hanyoyinta kamar yadda ta saba, hatta kuɗin da zata kashe ta lissafa da kuma yadda bayan hakan tsarinta zai cigaba da tafiya daga inda ta tsaya.
Ta sami wani likita da ta farar-ɗaya ya amince da buƙatar ta jin makudan kuɗin da a take tayi masa alkawari. Tana tuna murmushin da tayi bayan fitarsa, murmushin jin dadi da kuma jinjina wa kanta na yadda a kodayaushe mafita ke zywar mata, sai dai me? Ashe bata sani ba wannan murmushin shine na karshe da zata yi a wannan karnin watakila har ma da me zuwa a gaba… Don wadannan lokutan na jiya ta sani cewa har abada su zata lissafa a matsayin lokuta na ƙarshe da suke daidai a rayuwarta.
Tana iya tuna maganganun da suka yi da Baffa kafin nan, sun shigo wajenta shi da Baba Usman, kuma dukkan maganganun da zasu kwantar da hankalinta su suka zanta, suna tabbatar mata da halin da kowa a can gida yake game da ciwonta da kuma cewar ta kwantar da hankalinta abubuwa zasu daidaita, wasu maganganu da suka ƙara saita hankalinta waje guda bayan tabbatarwar da tayi cewa abubuwa suna nan a yadda ta san su har a lokacin.
Sai dai tun daga lokacin da tayi ido hudu da Ma’aruf bayan ya shigo ya fizge bandejin da aka rufe fuskarta dashi, da kuma mutanen da ta gani a ƙasa a kofar ɗakin a lokacin ta fara fahimtar cewa tabbas abubuwa sun fara karewa mata, rayuwarta ta birkice a daidai ƙarshen da bata taɓa hangensa ba, kuma abinda Ma’aruf ya fada kai tsaye na cewar ta biyo shi yana kallon cikin idanun nata da zuwa wannan lokacin ta tabbatar da cewar an kai musu sakon makancewarta shine mataki na farko da ya fara tabbatar mata da cewar, rayuwa tana ɗauke da mabanbantan kaloli kuma ba a kodayaushe ne abubuwa ke tafiya kamar yadda ɗan adam yake tsarawa a rayuwarsa ba.
“Babu kowa a duniyar nan, mu kaɗai ne Mami… Babu kowa mu kaɗai ne a wajen nan… Kuma na kawo ki ne don ki bani wata hujja kwakwara Mami, Me muka kasa baki a rayuwar nan? Me tasa zaki kashe Jamal? Me Hajiya tayi miki kika gurgunta kafafunta? Me Abdurrahim yayi kika dauke muryarsa? Me yasa kike kwashe dukiyar Baffa?
Me zaki yi da ita Mami? Ina zaki je ina zaki kai ta? Ƴaƴanki da su kansu kike rufe su da halaiyarki kike tarawa? Me zasu yi da ita Mami? Me suke nema a duniyar nan da basu samu yanzu ba? Me zasu nema ban gaba da ni ko Baffa zamu kasa Mami? Me yasa kike hukunta ni da soyayyar karya Mami? Me yasa kika sa na baki matsayi da kuma girman UWA a zuciyata? Me yasa kika kassara rayuwarmu kotawanne fanni Mami?….”
Muryarsa ta jero tambayoyin da dukkanin dauriyar da yake jin zai iya wajen saita kansa yayin da idanunsa ke kallon fuskarta, har yanzu bata kallonsa kuma bata ce komai ba, baiyi tunanin zata yi magana ba dama don baya zaton idan za’a tara kalmomin duniyar na kaf zata sami wadanda zata iya kare kanta dasu, sai kawai ya juyar da kansa yana sake kallon bishiyar dake gabansu, a lokacin hawayen da yake dannewa suka sulala kan fuskarsa.
Yana jinsa ne fanko, kamar wani ya zazzage dukkanin abubuwan da ya sani da kuma abinda yayi mu’amala dashi a rayuwarsa, kamar wani ya shafe dukkan tarihinsa komai ya zame masa sabo, yana jin kamar bai san ina ya nufa ba bayan nan, kamar bashi da wani takamaiman wani abu da zai sake yi a rayuwarsu, sai kawai ƙwallar dake danne a idanunsa ta fito tana gangarowa kan fuskarsa.
Kuma a lokacin ne dukkaninsu suka jiyo jiniyar motocin ƴan sanda dake tahowa daga bayansu, motocin guda biyu ne yana hango su tun daga can nesa ta gilashin motar suna tahowa, daga gefensu motar Faruk ce ke tahowa, sai kawai ya sake juyo da fuskarsa ya kalli Hajiya Kilishin da har a lokacin take zaune bata motsa ba…. Kuma sai a sannan ne idonsa ya gane masa hawayen dake gangarowa kan fuskarta…
Wani abu da ya saka shi murmushi a lokaci guda kafin ya sake juyawa, dogwayen yatsun hannunsa suka rufo kofar motar yayin da dayan ya murda mukullin mitar yana kunna ta.
“A tunanina, nan wajen shine mafari Mami, shine mafarin dukkan wani abu da kika dade kina ƙulls mana, daga kan Jamsl kuka fara, don haka daga kansa zsmu tsaya.”
Yana faɗin haka bai jira komai ba ya ƙarasa tayar da motar sannan ya danne kanta, a lokaci guda ta figa da tsananin ƙarfi kai tsaye tana nufar Bishiyar nan….
Kuma ta cikin gilashin dake gaba idanun Ma’aruf na kan fuskar Mamin da ta ɗago tana kallonsa fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye sanda motar ta karasa ta daki bishiyar da wani irin ƙarfin da karasa ta karade ko’ina!
Ƙarar da ta sanya Faruk taka nasa birkin motar sannan ba tare da jiran komai ba ya buɗe kofar motar ya tafi da gudu zuwa wajen, sauran ƴan sandan dake bayan motoci biyu suka diro da nasu saurin suka rufa masa baya!
***
*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*
“Basu kira ba har yanzu?”
Hajiya Nafisa ta tambaya da idanunta da suke a zare tana kallon ɗan ta Ashraf wanda ke rike da waya a hannunsa, a cikin falon da suke akwai Ahmad ma, yana zaune daga cikin kujerun falon yana hannayen sa duka biyu dafe akansa yayin da yake sauraren Ashraf ɗin dake riƙe da waya yana amsa kiran mutane daban-daban ɗin da suke fatan su isa ga abinda suke nema… Rukayya.
A yanzu bincike da kuma dukkan hasashensu ya kai ga abinda suke nema, an basu tabbaci na cewar Hoton da suka gani Rukkayya ce kuma a cikin gawarwakin da aka fito dasu daga wata mota dake nufar wani kauye a can kasar Niger.
Idon Ahmad ya koma kan mahaifiyarsu, Hajiya Nafisan dake ta zarya a cikin falon idanunta shabe-shabe da hawayen dake fitowa wani na bin wani akan fuskarta.
Ashraf ya girgiza kansa sannan yace.
“Bai kira ba Maamah, kiran da nayi masa kusan na biyar kenan ya ce suna hanya, bana don inyi ta kara kiransa…”
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
“Ka kira shi Aahraf… Ka sake kiransa, ya san al’amari irin wannan ai, ya san ba zamu iya jira ba, dole ne hankali ya tashi….”
Ahmad dake zaune ya girgiza kansa.
“Maamah ki jira yanzu zasu isa kar muyi abinda…”
“Kar muyi abinda me? Kar muyi abinda zamu tashi hankalinsu? Saboda kai naka bai tashi ba? Ƴaruwarka tana can a halin da babu wanda ya sani amma kai kana zaune babu abinda ya shafe ka?”
“Babu abinda ya shafe ni? Babu ya shafe ni zaki ganni anan Maamah? Ni na tura ta Niger din ko kuma idan Allah ya ga damar ɗaukar ta zan iya wani abun da zai hana ne…?”
“Ahmad…”
Ashraf ya katse shi yana juyowa kansa. Sai kawai ya mike tsaye.
“Me nayi? Nayi laifi ko? Ni kullum mai laifi ne a gidan nan, Ruƙayya ce ta tafi yawon barbadancinta har Niger amma ni da nake zaune anan nine mai laifi?”
Ashraf ya girgiza kansa fuskar sa ɗauke da tsananin ɓacin rai muryarsa a sama yace.
“You are crazy! Baka da hankali Ahmad me yasa kai a kullum kan ka kawai kake gani? Me yasa baka taba considering mutane a kowanne hali da ake ciki?…”
Sai kawai Ahmad ɗin ya miƙe, shima cikin daga murya yace.
“Saboda nima babu wanda yake considering dina a gidan nan….!”
“Inalillahi wainna ilaihir raji’un!”
Hajiya Nafisa ta faɗa tana komawa da baya ta zauna akan kujerar dake bayanta.
“Da wanne zan ji Ashraf?? Da wannan halin da muke ciki ko kuma da fadan da zaku fara? Inalillahi wainna ilaihir raji’un!…”
Ta rufe bakinta daidai lokacin da kiran waya ya shigo cikin wayar Ashraf din, hannunsa na rawa ya ɗauka ya kara a kunnensa, Hajiya Nafisa ta taso da sauri ta tsaya a gabansa yayin da Ahmad ya koma ya zauna yana kallon fuskar Ashraf din.
“Eh, eh ita ce..”
Ya fada yana gyada kansa, yayin da hannayen Hajiya Nafisa ke rawa akan fuskarta tana sauraren sa. Ashraf ya sake cewa.
“Eh ita ce Yallabai…”
Sai kuma ya gyada kansa yace.
“Alhmdlilah… Okay toh… Mun gode sir, mun gode mun gode….”
“Me ya faru? An ganta? Sun ganta? Tana da rai Ashraf?”
Tun kafin ya sauke wayar Hajiya Nafisa ke jero waɗannan tambayoyin, kuma ga mamakin kowannensu sai kawai ya gyaɗa kansa sannan yace.
“Sun ganta, tana da rai Maamah, tana asibitin a kwance…”
“Alhmdlilah… Alhmdlilah.”
Dukkaninsu su biyun suka faɗa a lokaci guda yayin da Ashraf din ya shiga girgiza musu kansa amma babu wanda ya lura dashi a cikinsu, sai kawai ya kira sunan mahaifiyar tasa kai tsaye.
“Maamah…”
Ta juyo ta kalle shi da sauri, idanunta a zare dauke da wani sabon fatan da a yanzu ya sani cewa maganarsa zata rusa shi ne har garinsa.
“Maamah sun ce ta samu paralysis (mutuwar ɓarin jiki)!”
***
*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*
“Wallahi Sister Maryam muna gidan har yanzu, abu ne kamar wasa, shekaru kusan talatin da wani abu sai yau Allah ya baiyana shi.. “
Cewar wata dattijuwa da take ƴaruwar Hajiya Salamatu wadda suke kira da Aunty Bilki. Zuwansu gidan kenan a safiyar yau da suka tashi da labari mai daɗi mai kuma cike da dimbin al’ajabi na cewar ƴaruwar tasu ta samu danta bayan tsawon wasu shekaru, ɗan da duniya da ma kowa a cikinsu ya riga ya bada tabbacin cewa ya koma ga mahaliccinsa tun a ranar da yazo duniya.
Sai a gashi a cikin ƙanƙanin lokaci kawai, a cikin wasu kwanaki da hannu zai lissafa su labarin ya canja, ɗan da yake natan na asali ya baiyana a raye tare da kammanin da ko bashi da hujjar labarin da ya bayar wanda yayi daidai da na Hajiya Salamatun, kowa a cikinsu zai shaida ya kuma gasgata cewa shi ɗin da gaske ɗanta ne na asali, don kamarsa ɗaya da mahaifinsa sak! Mijin da ta fara aura Ibrahim Shanawa, komai nasu iri ɗaya ne ta yadda babu wanda ya isa ya musa hakan.
Su kusan biyar ne ƴan uwanta suka zo a yanzu, harda guda biyu da suke a Abuja, tun a daren jiya da ta gaya masu suka yi booking jirgi a safiyar suka taho… Kuma a cikinsu babu wanda ya ƙaryata hakan saboda sun zo ne sun iske tarin hijjojin da ita Salamatun da kuma yaron dake kiran kansa da Jawad suka tanadar ta kowanne bangare, musamman babban al’amarin da ya ƙara girgiza kowa na cewar Jawad ɗin ya tashi ne a gidan Alhaji Bashir wanda yake ƙanin mahaifinsa.
Komai ya faru ne kamar almara, kamar mafarki ko kuma wani labari da ba zai zama gaskiya ba, shi yasa a cikin lokaci kadan zancen ke ta tawo kusufa-kusufa a cikin danginsu har ma da waje, wadanda ke zaune a garin Kanon ma har sun fara zuwa don ganewa idanunsu, don Salamatu kiran kowa take yi, kowa ya kira ta zata ce yazo gidan saboda murnar dake cike fala ranta.
Ko ta zancen ƙawar tata Kilishin da kuma matakin da ya kamata su dauka akanta na irin wannan zaluncin da ta haifar bata yi, sai yayyensu maza uku da suka gama shawara tare da Nasir ne sannan suka yanke shawarar ɗaukan yansanda a tafi har inda Kilishin take, don wanda yake Babba a cikinsu ya ɗauki zafi da yawa ta yadda ya rantse da Allah babu abinda zai hana su zama akan shari’ar.
Wayar da Aunty Bilkin take tare da wata ƙawarta dake can wajen aikinsu ta kare daidai lokacin da Hajiya Salamatun ta bude kofar dakin ta shigo hannunta ɗauke da wata katuwar leda fara.
“Aunty Bilki Yaya Nura zai wuce yanzu.”
Ta fada tana kallonta a cikin mutanen dake dakin, da mamaki a fuskarta tace.
“A’a, tafiya kuma ba dauka zasu bari ko zuwa gobe idan komai ya natsa, naji suna zancen za’a je a taho da Kilishin.”
Sunan Kilishin da ta ambata ya rage fara’a a fuskarta kafin tace.
“Shi kaɗai zai tafi, su suna nan anjima zasu je tare da Nasir, yace shi yana da meeting din wani contaract da zaiyi a yau.”
Ta gyada kanta tana kallon ledar hannunta sai tace.
“Kaya ne nasa aka kawo masa Aunty Bilki, daga Kaduna yake kuma ashe bai zo da kaya ba.”
Ta fada tana fito da set ɗin kaya guda goma ɗinkakku da wani yaronta ya bata lambar irin wajajen ɗinkin nan na yanzu masu sunan ‘Wardrobe’ da suke da kaya dinkakku nasu kyau da zaka je ka siya.
Yadikan dukkaninsu plane masu tsananin kyau da kalolinsu mabanbanta, kowanne anyi masa ɗinki mai kyau irin sealed din nan da maza ke yayi.
“Zai daɗe ne kafin ya koma?”
Aunty Bilkin ta tambaya, sai ta girgiza kanta.
“Babu inda zai koma Aunty Bilki, tare zamu je kuma tare zamu dawo na gaya masa ne dai kawai ya kira Bashir din ya gaya masa komai.”
Ta faɗa da dukkan yaƙinin da zai iya fitowa daga cikin zuciyarta, sannan ta mayar da kayan cikin ledar da cewar zata same shi ta bashi, caraf sai Amira ta miƙe ta karɓa da niyyar kai masa, don haka sai ta samu waje a kusa da Aunty Bilkin ta zauna, tana gaya mata mutanen da suka kira ta a waya suna cewa ayi mata barka.
Sai dai sam ba fahimtar ta sosai take yi ba, ba komai take ganewa a cikin bayanin ba, zuciyarta zagaye kawai take yi taba komawa daren jiya, daren jiya da suka zauna tare da Jawad suka fayyace komai game da al’amarin, tarin bayanin da yayi nusu na yadda yaji labarin komai a cikin kankanin lokaci da ma dukkan abunda ya faru bayan nan,sai dai ba komai ne yafi tsaya mata a rai ba illa sunan Bashir da ya kira a matsayin mutumin da ya rayu a gidansa kuma yake masa kallon mahaifi tsawon shekarun nan.
Mukaminsa da ya ambata na matsayin minister shine abinda kai tsaye ya tabbatar mata da cewar Bashir din da ta sani a rayuwarta ne, kanin mijinta Ibrahim wanda yake kamar yayansa, don tun kafin mijinta yayi aure shi yake da mata uku, tana tare da Ibrahim din kuma ya kara ta uku mai suna Mardiyya, ta san shi ta san matansa sarai! Don sun yi shiri da matarsa ta biyu Yagana. Bayan abubuwa sun lalace a tsakaninsu ne sai itama ta juya mata baya kamar sauran duka danginsa.
Ibrahim yana son haihuwa, sun fara samun matsala ne tun daga lokacin da ta haifi dan da akace musu ya rasu, sannan sai abubuwa suka lalace a tsakaninsu bayan an tabbatar da matsalar da ta samu a mahaifarta, matsalolin da suka kai ga rabuwar aurensu tun a wancan lokacin, kuma cikin wani ikon Allah sai daga ita har shi babu wanda ya sake haihuwa a dukkan aurarrakin da suka yi bayan nan har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.
Tana tuna lokacin da aka gaya mata rasuwarsa, shekaru kusan ashirin da wani abu a baya, tana tuna iya zafin hakan da taji tun a wancan lokacin, zafin da bai kai wanda take ji a kirjinta yanzu ba, wanda take ji idan ta tuna cewa Ibrahim ya rasu ne yana tare da ɗansa ba tare da ya sani ba, don a bakun Jawad take ji cewa anan gidan Bashir ɗin akayi jinyarsa kafin ya rasu…
“Kukan me kike yi kuma Salamatu? Idan na murna ne ai ya isa haka, idan kuma wani tunanin ne a ranki ki kauda shi gefe dan Allah, ki godewa Allah da ya nuna hakan tun da ranki kafin ki bar duniyar, ki sa a ranki cewa ya so ki da rahama ne tunda har ya baki wannan damar… Ga ki da ranki da lafiyarki da dukiyarki har da kwarinki, ba sai a lokacin da ba lallai ki iya komai ba… Gidewa Allah zaki yi ki kara gode masa Salamatu, ba kullum ne al’amari irin wannan ke faruwa a duniyar ba.”
Sai ta sa hannunta tayi saurin goge gawayen fuskarta sannan ta daga kai alamun ta yarda hakan ne… Sannan ta dago daidai lokacin da jikokin Aunty Bilkin yayan wata yarta Muniba da itama ta karaso a lokacin suka taho da gudu suka rungume su… Ta riƙe yarinyar a jikinta tana kallon Muniban data shigo rike da karamin dan ta a hannu yayin da sauran ƴanmatan dakin suka juya suna yi mata magana, kowanne fuskarsa dauke da fara’a…
Sai kawai ta furta kalmar Alhmdlilah a fili tana kara godewa Ubangiji ya daya azurta ta da wannan damar a rayuwa.
*
Jawad yana tsaye daga cikin ɗakin, daga jikin windon ɗakin inda aka saki farar liner dake jikin labulayen ta yadda daga yadda yake a tsaye yana hango wasu motoci biyu da suka shigo gidan mutanen cikinsu na ƙoƙarin fitowa. Hannunsa ɗaya na kare da waya yayin da guda ɗaya ke rike da labulen yace.
“Wallahi mutane take ta kira Haro, daga safiya zuwa yanzu gidan ya kusa cika… They are making me feel uncomfortable, yanzu muka rabu da shi kanin nata Nasir, yana gaya min cewa idan yansandan sun iso tare zamu fita zuwa gidan ita ɗaya matar, tsakanin jiya da yau Haro na rasa ma lokacin da zan zauna inyi tunanin cikin kaina…”
Daga cikin wayar Haro yayi dariya kafin yace.
“Kace ka zama wata sabuwar amarya kawai, but I’m really happy for you man! Wallahi kayi sa’a ba kowa ne ke gane irin wannan abun game da rayuwarsa kuma ya samu mafita cikin kankanin lokaci ba… You solved everything out kafin ma mu sani, don ni sai jiya da daddare ne da muna waya da Bello na office dinku yake ce min wai ka dauki hutu a lokaci guda yana fata dai lafiya sannan na san cewar ashe baka gari ma.”
Jawad ya saki labulen ya taho cikin dakin yana kare wa kayan cikinsa kallo, a tunanin Haro komai ya faru ne cikin sauki, a lokaci guda ba tare da wani bata lokaci ba, amma shi ya sani halin da ya shiga da kuma wuyar da ya sha a iya wannan ɗan tsukin, idan za’a rarraba ta a zuciyar wani zai ɗauki watanni kafin ya iya kai ƙarshensa.
Shi kadai ya san abinda yaji shi kuma shi kadai ya san abinda ya fuskanta a cikin zuciyarsa da ma jikinsa, sannan ga tasirin dukkan abinda ya faru jiya, na yadda ya samu abinda baiyi zato ba bayan sun bashi tabbacin da shi kansa ba zai iya musantawa ba. kusan hotuna goma Hajiya Kilishi ta dauko masa na mahaifin nasa da takira da sunan Ibrahim Shanawa, kuma tun a hoton farko yaga kamar ya san fuskar kamar ya gane shi duk da cewa suna ta zuzuta kammaninsa dashi.
Sai da ya fara yi mata bayanin inda ya taso sannan komai ya fito fili, wani ikon Allah da kuma wata sabuwar isharar ta fahimtar dashi cewa a tsawon rayuwar da yake tunanin ya shafe a hannun wasu mutane, ashe ba wasu bane, a cikin danginsa yake, a tsakiyarsu ma tunda tun kafin hawan Alhaji Bashir matsayin minista gidansa yake a matsayin centre guda ta family dinsu, kusan kowa yazo zai samu wajen zama babu takura, shi yasa a yanzu da yake matsayin ministan ƴan aikin dake tafiyar da al’amarin gidan su kansu wajensu daban.
Bai kira kowa ba, bai kira su Hajiya Mardiyya ko kuma wani a gidan ba har yanzu, yafi son sai ya gama tara hankalinsa waje guda tukunna, yafi son sai ya saita iya abinda ke gabansa a yanzu, don ya sani gaggawa ba zata haifar masa da komai ba.
Ya ajiye wayar hannunsa a gefen gadon dakin sannan ya nufi ƙofar toilet ya buɗe… wanka yake so yayi ya canja kayan jikinsa shi yasa yake ta jinkirtawa don ta gaya masa cewa zata sa a kawo masa wasu, hoton fuskar Zainab ya gifta a ransa a lokacin, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha wanke masa toilet, ta haka ya fara gane ta, ta haka ya fara gane cewa an canja masa mai gyara masa daki kafin ma ya fahimci wacece ita.
Ya cije lebbensa kadan yana ƙoƙarin tuno ɗaya zagayen halin da yake ciki, sai dai hakan baiyi nisa ba lokacin da aka kwankwasa kofar ɗakin, sai ya saki ta toilet ɗin da yake riƙe da ita sannan ya matsa gaba ya buɗe.
Wata yarinya ce, tun safe ya ganta a gidan bayan ya tashi daga bacci, don bayan an kawo masa breakfast ma ta zo daga baya ta kawo masa lemo da kuma Pringles tace ya kara, bai ma san wacece ita ba, bai san matsayinta ba,yaji dai kawai suna koran sunanta da Ameera.
Bakinta ya tale da murmushin da yayi daidai a fuskarta.
“Yaya J, hope dai ban katse ka kana wani abun ba?”
Ya zura wayarsa dake hannu a aljihu sannan ya girgiza kansa yana kallonta.
“Kar ki damu I’m fine.”
Sai ta sake wani murmushin sannan ta gyada kanta.
“Toh Alhmdlilah… Kaya ne Aunty tace in kawo maka.”
Ta fada tana nuna ledar hannunta da yatsanta daya mai dauke da wani zobe dake kyalli a cikin fitilar wajen.
“Nagode.” Ya fada yana mika hannunsa fon ƙarba amma bata miko din ba sai tace.
“Can I choose a colour for u? Wanda zaka sa yanzu?” (Zan iya zaɓar maka kala?)
Jawad ya ƙara kallonta, zuciyarsa na kokarin gaya masa wani abu da ba shine ransa ba yanzu, sai kawai ya sake miƙe hannunsa yace.
“Kar ki damu zan ɗauki duk wanda yake a sama ne kawai.”
Yayi zaton zai ga canji a fuskarta, amma sai jawai ta ƙara yin murmushi mai fadi tace.
“Shikenan, muna jiranka.”
Da haka ta miƙa masa kayan sannan ta tsaya tana cigaba da kallonsa da murmushin a fuskarta ba tare da ta juya ba. Wani abu da ya ratsa zuciyarsa kenan yasa duk yadda ya kai ga jinsa wani iri sai da wani guntun murmushin ya sauka a lebbensa.
“Nagode.”
Ya faɗa yana rufe ƙofar, ta kaɗa masa yatsu biyu a gefen fuskarta tana cigaba da murmushin kafin ya rufe ƙofar a fuskarta.
Ya rufe kofar daidai lokacin da wayarsa dake cikin aljihu ta shiga kara, hannunsa ya jawo ta da sauri ya duba, sunan Nura ya baiya na tar a jiki don haka ba shiri ya daga ya kara a kunnensa tare da sallama.
Daga cikin wayar Nuran ya amsa da sautin muryar da ya sanya zuciyarsa tsalle tun kafin Nuran ya kai ga faɗin abinda ke bakinsa.
“Yallabai an samu matsala, wallahi yau da safe da muka tashi ba mu ga yarinyar nan ba, tun safe ake nemanta har yanzu babu labari….!”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
