Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Hajiya akwai matsala fa, motocin ƴansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba….”
    Muryar Sadik din ta faɗi kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taɓa jinsa ba.
    Bugun zuciyar tata ya cika kunnuwanta a lokaci guda da sauran bayanin Sadik din ya ɓace daga cikin kunnuwanta, ba shiri dukkan jikinta ya shiga rawa yayin da ta nemi gefen gadon nata ta zauna, hannunta daya da baya rike da wayar ya kamo zanin gadon don neman tallafi.
    “Kana ina yanzu Sadik, ka bar wajen?”
    Ta tambaya da sautin da taji kamar ba nata ba saboda ƙarar buguwar zaciyar tata da shi kaɗai take iya ji har a yanzu. Tun da rana da ta daga labulen dakinta ta kula da gajimaren da ya baibaye sararin sama, ya rufe ta kusan bakidaya saboda haka babu kadawar iska sosai, amma bata tabbatar da hakan ba sai a yanzu da take jin gumi ko tawanne ɓangare na lulluɓe ilahirin jikinta.
    “Ina daga gefe Hajiya, na leƙa layin ne sai na dawo daga baya nake kiranki.”
    Wannan karon, muryar Sadik ɗin ta amsa tar a cikin kanta.
    Sai ta mayar da wani abu dake shirin tasowa daga makogwaronta kafin tace.
    “Motocin ƴansanda ne kaɗai a wajen Sadik?”
    Ya girgiza kansa.
    “A’a akwai wata karamar mota kirar Accord.”
    Accord. Accord… Kalmar ta rangaɗa a cikin kan Kilishi ta sigar tashin hankalin da ba’a saka masa rana ko lokaci. Accord motar Ma’aruf ce! Me yake shirin faruwa? Ta yaya zasu gano Awwalu? Ta ina? Ta ina tunaninsu zai iya samo Awwalu? Ba shi yaje ya miƙa kansa ba ta tabbata, don idan haka ne a ƙofar dakinta waɗannan motocin ƴan sanda ya kamata su tsaya ba’a gidan Awwalu ba.
    “Sake komawa Sadik, sake komawa yanzun nan ka karanto min lambar karamar motar…”
    “Hajiya…” Sadik ya furta muryarsa na shaida fargaba.
    “Laifi ba’a manne yake a goshi ba Sadik, babu wanda ya sanka kuma babu wanda zai gane ka, ka koma ka karanto min lambar.”
    Yadda muryarta ta fito a kausashe tana shaida tsananin tafasa da kuma rudanin da take ciki yasa Sadik haɗiye maganar dake bakinsa sannan yace.
    “Shikenan, bani minti biyu…”
    “Kar ka kashe wayar…”
    Ta katse shi da sauri, don bata sani ba idan har kofofin hancinta zasu iya shaƙar iska tsawon lokacin da zata jira shi. Tana jin ƙarar takunsa, zuciyarta na bugawa tare dasu har zuwa lokacin da ya isa wani waje da hayaniyar mutane ta shiga kunnenta a lokaci gyda, taji shi yana ratsawa ta cikin mutanen kafin muryarsa ta fito da harafan nambar motar Ma’aruf cikin amon muryarsa da Kilishi ta sani cewa har bayan ranta ba zata taɓa mantawa da ita ba. Don a wajenta, a bangarenta wannan lokacin shine mafarin komai, shine mafarin wata rayuwar da a yanzu bata santa ba.
    ***
    *Current Situation…* *( Halin da ake ciki.)*
    “Ta farka?”
    Sune kalamai na farko da suka fara shiga cikin kanta, sune abinda ta fara ji kuma cikin amon da yake mafifici a wajenta, amon muryar da take tunanin ko a bayan kasa take babu ta yadda za’a yi ta kasa tantamce shi. Ma’aruf. Ma’aruf…
    Zuciyarta ta biya sunan sau biyu kafin wata murya a cikin kanta ta ƙwallara kara, Ma’aruf? Me ya kawo Ma’aruf inda take? Me yazo yi a wajenta a wannan lokacin? Tsaya wane lokaci ne ma? Sannan a ina take tukunna? Tayi yunkurin bude idanunta amma kai tsaye sai wata zuciyar ta hane ta da hakan kai tsaye don haka ta fasa a daidai lokacin da muryar wata mace ke cewa.
    “Gashin idonta yana motsi, da alama yanzu zata farka…”
    “Tun ɗazu abinda kike fada kenan, just go and call the Doctor.”
    Taji Ma’aruf ya sake fada yanayin muryarsa kamar a hasale.
    “Yallaɓai na san aikina fa, idan da bukatar kiran likitan ai…”
    “Ni zaki gayawa kin san aikin ki? Kin san aikin ki tun 8 kike zirga-zirga anan ta tashi ne?”
    “B, Calm down ta san me take yi mana…”
    Muryar Ishaq tayi saurin katse shi.
    “Wannan tabe-taben banzan ne ta san abinda take yi Ishaq?”
    Ya sake faɗa muryarsa na cigaba da ɗagawa cikin fushin dake fitowa karara, kuna matar bata yi shiru ba ta sake cewa.
    “Amma dai ka san mu bamu isa mu tashe ta ba idan har…”
    “I don’t f*cking care! Idan har me?all I know is mun kawo ta nan ne don ta sami lafiya.”
    Ƙarar sakin wani abu ta cika iskar dakin kafin muryar matar ta sake cewa.
    “Then ga ka nan gata ai, sai ka bata lafiyar.”
    Da haka taji matar ta juya karar takunta na yin nisa daga inda Kilishi take a kwance yayin da maganganun su Ishaq ɗin ke ƙara shiga kunnenta, sai dai ba su Hajiya Kilishi ke saurare a wannan lokacin ba, tunaninta yayi baya ne yana tarewa ga abinda ya faru jiya don ta fahimci abinda ke faruwa yanzu.
    Abinda ya faru bayan Sadik ya kira mata lambar motar Ma’aruf a ƙofar gidan Awwalun, cewa tayi ya jira ta a wajen gata nan zuwa. Don a lokaci guda kwakwalarta ta gaya mata cewa tunda har ƴansanda suka zo neman Awwalu basu same shi ba, to tabbas dole ne ita ta fito su san yadda zasu yi su nemi inda Awwalun yake a wannan daren ita dashi don ta gama da babinsa kafin komai ya caɓe mata.
    Don haka tayi saurin yin transfer wasu kudade daga bankinta na ajiya zuwa na amfaninta da kowa ya sanshi da ita sannan ta debi kayan waɗannan allurorin ta zuba a leda ta fita, ta fita a lokacin da kusan duk jama’ar gidan ke ɓangaren Hajiya Maimuna na murnar dawowar Abdurrahim, ta fita babu wanda ya ganta don ko Maigadi bata samu a gate ba shima.
    Da kafarta ta taka har bakin titi inda ta samu wani mai keke napep ɗin da ya sauke ta a shagon wani mai POS ta ciro dubu dari biyar daga account din ta zuba su a wannan ledar don ta riga ta gama shirya yin asarar ko nawa ne a jiyan don samun inda Awwalu yake.
    Tana iya tuna yadda zuciyarta ta dinga bugawa a kirjinta a lokacin, tana iya tuna yadda ta kasa zama waje guda cikin keke napep ɗin zuciyarta na cikowa a ƙirjinta,
    har ƙoƙarin tsugunnawa tayi ta kuma yi ƙoƙarin tashi tsaye, daga baya ma taga kamar mutumin baya gudu sosai don haka tace dashi ya tsaya, ta sauka ta bashi kudinsa sannan ta tsaya neman wani, tana tsaye tsabar ruɗewa da kuma yadda kanta yake juyawa sai taga kamar daya barin titin an fi samun keke napep ɗin da babu kowa.
    Kuma a lokacin ne abin ya faru, a lokacin da tazo tsallakawar ne motar ta buge ta, taji lokacin da ta tashi sama, numfashinta na biyo ta sannan taji lokacin da ledar hannunta ta suɓuce, tana gaya mata cewa kuma abu na ƙarshe da zata iya tunawa kafin numfashinta ya yanke shine taji hayaniya da kuma salatin mutane da yawa a saman kanta.
    A yanzu a asibiti take kenan, asibiti ne daga maganganun da taji suna yi a saman kanta…. Salatin da bakinta ba zai iya ba shi zuciyarta ta karanto ta kuma sake karantowa, ina ledar dake hannunta ina kuma wayarta? Me yake shirin faruwa ne? Wane irin mummunan mafarki ne wannan? Ta yaya Allah zai jarabce ta da hadarin da har zai kai ga kwanciya a asibiti a wannan halin da take ciki? Ina ledar hannunta ina wayarta? Inalillahi wainna ilaihir raji’un… zuciyarta ta ambata tana sakewa, don abu na ƙarshe da zata so yanzu shine ace ledar hannunta dama wayarta tana hannun da bai dace ba, hannun da zsi iya tona asirinta ba tare da wata wahala ba.
    Tayi kokarin yin motsi kaɗan, a lokacin ne taji yadda kanta ke juyawa kotawanne ɓangare, jikinta yayi tsami kamar anyi mata duka.
    “Har yanzu akwai ƴan sanda a ƙofar?”
    Taji muryar Ishaq ya tambaya, tambayar da ta haddasa dokawar ƙirjinta a lokaci guda, bugawar da ta nemi dagargaza zuciyarta, bakinta ya sake karanto kalar wani salatin da bata taba sanin ta iya shi ba… Ƴan sanda? A ina?
    “Suna nan baza su tafi ba ai, Baffa yace babu yadda baiyi dasu ba, amma har sun tura maganar sama, don haka babu yadda za’ayi a rufe case din tunda shi DPO din da ya kade ta ma yaki saurarar Baffan su sake magana.”
    DPO? DPO’n ƴan sanda ne ya kaɗe ta? Kuma yaga abinda ke cikin ledar hannunta? Yaushe duniya ta tsuke har haka?
    Muryar Ma’aruf ta fito da kaushi, kaushin dake shaida tsananin ɓacin rai mai haɗe da tashin hakalin da baya ɓuya. A cikin kanta ta kintaci cewa ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa.
    “There must be a mistake dole Ishaq, me Mami zata yi da allurar ƙwaya irin wannan? Sannan har da kudi five hundred thousand a cikin leda? Na yarda framing dinta kawai wasu ke ƙoƙarin yi tunda ko Baffa ma bai san da fitar ta ba… Kuma ban san me yasa ba amma jikina yana bani cewa wannan al’amarin yana da alaka da case ɗin da muke yi, shi yasa nake so ta farka tayi bayanin komai waɗannan ƴan i*kan su bamu waje.”
    A wannan lokacin ji tayi kamar ta miƙe zaune ta girgiza kanta, ta gaya musu cewa ba zai yiwu ace komai ya caɓe mata a wannan lokacin ba…
    Ba zai yiwu ba, tana da sauran lokaci, damarta bata taba karewa ta sani, tsarinta kullum daidai yake tafiya don haka ko a yanzu da take iya jin tsananin damuwa daga muryar Ma’aruf ta sani zaren bai ƙare mata ba, tana nan a Mamin da take a idanun kowa abunda ya rage kawai shine ta bude idanunta ta ture wannan ƙalubalen ta cigaba daga inda suka tsaya… Zata san yadda zata yi ta fidda kanta ta sani… Sun ga ledar a hannunta amma hakan ba zai basu tabbacin komai ba tunda babu wayarta.
    Wayarta, babu wayarta, basu same ta ba, don haka ba shiri ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, komai da sauki, komai zai zo da sauki kenan, ba’a kama Sadik ba, tana da sauran fata ta san yadda zata yi komai ya tafi daidai, ta sani…. Ita Kilishi ce kuma ko a wani hali tana da mafita…
    “Ka cire tunanin wadannan mutanen a ranka B, babu inda zasu je idan har ba umarni aka basu daga can ba.”
    Ishaq ya faɗa daidai lokacin da ya daga wayarsa kuma ba sai yayi wani bayani ba daga gaisuwa kawai Kilishi ta fahimci cewa da Hajiya Maimuna yake magani.
    “Mami baza su barku ku shigo ba, mu ma da I.D cards ɗinmu muka yi amfani, yanzu ma so muke mu samu ta farka watakila komai zaiyi sauki…”
    A lokaci guda hankalin Kilishi ya dugunzuma ya ƙara tashi, ak’amarin ya kai har a hana nakusantan ta ziyartar ta? innalilahi wa’inna ilaihir raji’un! Ta ina zata fara neman mafita idan har al’amarin ya kai haka? Me zata fara kamawa a yanzu? Ta ina zata fara bayanin inda ta samu allurar da kuma wajen da zata je? Wannan wane irin mummunan tashin hankali ne? Me yasa komai zai ɓare a lokacin da bata shirya ba? Me yasa sai a wannan nisan sannan ƙalubalenta zai zo? Don ta yarda har yanzu wannan ƙalubale ne, babu ta yadda za’ayi ace wannan shi zai kawo ƙarshen ta, tana da mafita a komai na rayuwarta, tana da ita ta sani! Kawai zata fuskanci wahala ne kafin ta daidaita komai.
    “Hajiya ce, wai su Samirah ne har da kuka zasu taho…”
    Taji Ishaq ya faɗa bayan ya ajiye wayar da yake yi.
    “Babu wanda zai zo, su bari mu san me ake ciki ma tukunna, idan sun zo me zasu yi?…”
    Cewar Ma’aruf yana jin tasirin abinda ke zuciyarsa na yin yawa, kuma Ishaq din bai ce konai ba, shiru ya ratsa dakin kafin wayarsa tayi kara, kuma yana jin ya dauka ya fara waya zuwa office ɗinsu, sai kawai ya miƙe, ya miƙe tsaye ya nufi kofar ɗakin, kuma bai kira komsi ba ya kama hanya ya fita.
    Missed call ɗin Faruk guda biyar ne, duka bai san lokacin da ya kira ba sai kuma na Amina guda biyu.
    Amina ya fara kira kafin Faruk ɗin, kuma sautin muryarta, wannan sassanyar muryar tata, shine abu na farko da ya tuna masa da irin tarin wahala da kuma gajiyar dake jikinsa, wanka kawai yayi a jiya lokacin da Baffa ya kira shi da zance mafi tashin hankalin da hafi ba zagayen halin da yake ciki, cewar wani dan sanda ya kira shi da cewar ya kade Mami akan titin hanyar gidan Gwamna, sannan sun tsinci wasu miyagun kwayoyi a cikin ledar dake hannunta.
    Yana iya tuna magiyar da ta dinga yi masa a lokacin, magiyar cewar ya fada mata abinda ke faruwa, amma bai iya ba din,rigar da take miko masa a lokacin ya karɓa kawai ya zura a jikinsa sannan ba tare da ya damu da taje barbajajjen gashin kansa ba ko kuma ya shafa mai ya dauki mukullin motarsa kawai ya fito, ya fito ya barta ita da Hamidan dake binsa a baya da nata tambayoyin da kuma kwanukan tuwon nan da yaci burin huce gajiyarsa dashi kamar me…
    “Babydoll….”
    Muryarsa ta fito a hankali bayan ya shige cikin motarsa. Kuma maimakon ta amsa sai tace.
    “Ya jikin nata? Hajiya tace har yanzu bata farka ba.”
    Hannunsa daya ya miƙa cikin barbajajjen gashin kansa sannan ya rufe idanunsa gabaɗaya yana jingina da kujerar motar.
    “Bata farka ba, amma soon insha Allah.”
    Amina ta gyada kanta, tana zaune ne akan kujerar falon gidan tare da Hamida tmda tayi bacci akan cinyarta, basu dade sosai da dawowa daga cikin gida ba, don kamar kowa suma kusan a zaune suka kwana ana jimamin abinda ya farun, a yanzu ma ta dawo ne ta yiwa Hamidan wanka ta kuma bata abinci, wanda bayan ta gama ne bacci ya dauke ta.
    “Kana tare da ita ne?
    Ta sake tambaya a hankali. Ya girgiza kansa a hankalin shima.
    “Na fito,ina mota yanzu.”
    “Dan Allah ka dawo gida kafin ka tafi wani waje… Baka ci komai ba fa..” ta fada ksmar zata yi kuka.
    Yayi shiru kaɗan kafin yace.
    “Kina ganin zan iya cin wani abu yanzu?”
    Ta gyaɗa kanta a hankali.
    “Zaka iya Sugar, saboda babu abinda zai faru insha Allah, komai zai tafi daidai kawai jiran sakamakon ne mai wuya…”
    Ya gyaɗa kansa a hankali.
    “Na sani Noor, da wuya sosai… Mami kamar mahaifiyata ce, ina jin ta har cikin raina wallahi hankalina ba zai taɓa kwanciya ba ace wasu sun saka ta a cikin wannan halin, babu abinda ya same ta amma har yanzu bata farka ba Amina, bamu san meye matsalar ba har yanzu, amma kuma duk da haka ace gaan saka ƴan sanda suna gadinta sun hana kowa shiga…”
    Ƙwallar da ta cika idanun Amina ta gangaro zuwa kumatun ta, Allah ya sani tsoro take ji, tsoro take ji sosai na ranar da Ma’aruf zai san wacece Kilishi, don bata san yadda za’ayi zuciyarsa ta iya daukar masa hakan ba, bata sani ba ma idan har zai iya daukan…
    Sai ta share su da bayan hannunta ɗaya sannan tace.
    “Babu abinda zai faru Insha Allah Sugar, alkhairi kaɗai Allah zai azurta rayuwarmu dashi insha Allah.”
    “Insha Allah.” Ya faɗa a hankali yana buɗe idanunsa sannan yace.
    “Zan aiko direba ya karɓa min abincin, ba zan iya dawowa gida yanzu ba Babydoll, ayyukan dake jira na a office suna da yawa, yanzu ma na ga missed call din Faruk kusan biyar ban dauka ba.”
    Ta cije lebbenta kaɗan na ba hakan ta so ba, amma tasirin uzirin da ta san dole ne tayi masa ya danne son ran nata don haka tace.
    “Shikenan Allah ya kaimu yazo ɗin…”
    “Kar ki sake yin komai, ki bar min ɗumamen tuwon nan kawai.”
    Tayi murmushi jin daɗin cewa har yanzu bai manta da tuwon ba sannan ta gyada kanta a hankali.
    “Insha Allah Habibi albi.”
    Ma’aruf ya sake lumshe idanunwansa yana jin tasirin muryarta da kuma sabon sunan a jikinsa. Yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba, itama tayi shiru bata sake cewa komai din ba, kuma a cikin shirun yake yake jin kamar dukkan gajiya da kuma damuwarsa suna bin iska ne, sai dai hakan baiyi nisa ba sakamakon shigowar kiran Faruq da ya sake shigowa, ya ɗago da wayar ya kalla kafin ya sake maida ita kunnen nasa.
    “Babydoll ki min hakuri please, zan ɗauki kiran Faruq.”
    “Ba komai, kaje kayi aikin ka kawai, amma dan Allah ka turo direban da wuri.”
    “Insha Allah thank you so much for ur care.” ( Nagode sosai da kulawarki.)
    “Aiki na ne Sugar.”
    Ta faɗi abinda ya saka shi murmushi ba shiri, murmushin da yake ɗan mitsitsi amma ya taɓo har cikin zuciyarsa.
    Kiran Faruq ɗin ya ɗauka ya kara a kunnensa.
    “Faruq…” Ya furta muryarsa na fitowa yadda take.
    “Ma’aruf kana ina?”
    “Ina asibiti. Har yanzu bata farka ba.”
    Ya faɗa yana kallon rubutun ‘Amenity 4’ ɗin dake can gabansa kamar yana son ya tabbatarwa kansa da hakan.
    “Kazo office yanzun nan Ma’aruf, ga Brothernka anan yana buɗe mana aiki…”
    Ba shiri ya miƙe zaune sosai yana buɗe idanunsa.
    “Wane brothern? Waye? Me ake yi?”
    Ya jero tambayoyin a lokaci guda harshensa da ma muryarsa na ƙoƙarin karyewa wajen tambaya.
    Daga cikin wayar, Faruk yayi murmushi mai sautin da ya ji shi kafin yace.
    “Brothernka da ya dawo jiya Abdurrahim, yaron nan wuta ne B, kazo ka ga aikin da yake yi, gabadaya forensic department din da muke dasu baza su iya ba B… Walkahi kowaye a bayan aikin nan, alƙiyamarsa ta tsaya!”
    Faruk ya faɗi hakan a lokaci guda da kwakwalar sa ta tuna masa abinda Baffa ya gaya masa da safoyar yau.
    _”Abdurrahim ya fita yace zai fara zuwa kamfani, inaga daga nan zai zo ya ganta shima idan zasu bari ya shiga…!”_
    ***
    A ƙofar wani ƙaton Gidan ƙasa Jawad ke tsaye a jikin motarsa, idanunsa na kan ƙifar gidan ne wanda tarin mutane ke ta fitowa ta cikinta kamar gidan tururuwa.
    Har yanzu lissafi kwakwalar sa kawai take yi na yadda abubuwa ke faruwa dashi bi-da bi, yadda duniyarsa ke tsukewa tana waje guda tarin abubuwan na bayyana gare shi, ɗaya bayan ɗaya kuma kowanne baya yin nisa da guda.
    Kusan minti talatin kenan a dazu da Zainab ta gaya masa cewa garinsu ya kawota, garinsu,inda gidansu yake kuma inda mahaifiyarta take. Mamakin hakan ya harba cikinnkwakwalwarsa da tasirin wani abu da bai san shi ba, tsayawa kawai yayi yana kallonta yayin da hannunsa ke kan sitiyarin motar yana kokarin juyawa, bayan sun rabu da Nura ne, wannan saurayin da yayi masa rakiya har gidan da ya samo lambar da bai tabbatar idan zata amfane shi ba.
    A lokacin har sun sauke Nuran ya juya kan motar suna shirin barin garin, kanta yana ƙasa tana wasa da yatsunta, sai kawai ji yayi tace.
    “Dan Allah zaka kaini gida kafin mu tafi?”
    Muryarta ta fito ne tana rawa, tana rawa sosai ta yadda da ƙyar ya gane me take cewa, ku.a ba shiri a lokaci guda ya tsayar da motar, Allah yaso ba gudu yake har a lokacin ba, ya juyo ya kalle ta har a lokacin kanta yana ƙasa,
    “Me kika ce?”
    Ya tambaya da sauri yana kallonta.
    “Gidanmu, a can hanyar yake babu nisa, dan Allah ina so in ga Naani.”
    Ta sake faɗa wannan karon hannayenta na rawa fiye da ɗazu. Kuma kalmar Naanin ta haska a kansa da wata ma’ana da ya taba sanin cewa ya rike a cikin kansa cewar haka take gayawa mahaifiyarta. Don haka ba shiri yace.
    “Gidanku? Anan garin kike dama?”
    Ta daga kanta.
    “Nan ne garinmu, da muka zo nayi zaton gida Hajiya tace ka kawo ni, sai kuma naga ba haka bane… Wanda ya nuna maka gidan da kuka je sunansa Nura, shima na san shi, a gidan da mamana take aure yake.”
    Ba shiri hannunsa ya kai saman kansa yayin da bakinsa yake a buɗe, kuma a lokaci guda ya tuno da ranar da ya fara tambayarta sunanta da kuma inda take…
    _”Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake.”_
    Haka ta fada muryarta tana rawa, sai kawai ya gyada kansa yace.
    “Zainab kin san shi? Amma ya akayi baki yi magana ba shima kuma baice komai ba?”
    Ta kai hannu ta share kwallar da ta cika idonta a lokacin, sannan ta girgiza kai har a lokacin bata kallonsa.
    “Bai gane ni ba, bai sanni sosai ba, lokacin da na tafi ma baya garin ance ya tafi ci rani.”
    Sai kawai ya haɗiye wani abu da bai san sunansa ba a makogwaronsa yana kallonta, yana kallon yadda take sunkuye da kan ta da kuma yadda take share hawayen fuskarta, bai san kukanta na meye ba amma ya fahimci tsoro take ji, tsoron tambayarsa take yi don taje ta ga mahaifiyarta, shi ɗin da ba kowa bane har yanzu a rayuwarta, wani abu da yake ji kamar ya fi tausayi girma shi ke gilmawa a zuciyarsa a lokacin haɗe kuma da mamakin yadda abubuwa ke kasancewa bi da bi a rayuwarsa.
    Ya murɗe kan sitiyarin motar suka juya, kuma yana tambayarta da kwatance har zuwa ƙofar gidan da a yanzu yaje tsaye yana jiran fitowarta, yana jiran yayin da kwakwalwarsa ke cike da lissafi da kuma tarin tunanin abubuwan da bai san adadinsu ba.
    A karo na ba adadi hannunsa ya sake danna wannan lambar da aka bashi, kuma ta shiga har zuwa bugu na ƙarshe kafin ta katse kamar kodayaushe, tunda ya tsaya a wajen yake kira, zai iya ƙirgawa kiran ya tafi kusan sau goma daga lokacin da ya fara zuwa yanzu, sai kawai hannunsa ya shiga bangaren sako ya rubuta abinda ya san ko waye zai karanta ba zai dauki neman da yake yi masa da wasa ba.
    Kuma sai da ya tura sannan tunanin ko bai kwafi lambar daidai ba ya haska a ransa, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan takardar, ya kalli lambar jiki da kuma wadda yake kira yaga daidai ne sai kawai ya duƙunƙune ta yayi wulli da ita gefe, yayi wulli da ita daidai lokacin da ƙafafun wani dattijo suka fito daga cikin gidan.
    Sanye yake da riga da babba ƴar ciki wadanda suke daban-daban, fuskarsa a murtuke take babu alamun fara’a ko kaɗan, kuma da kallo ɗaya da yayi masa ya fahimci wanene shi, Mijin mahaifiyarta, mijin mahaifiyarta wanda tace shine sanadin tahowarta aiki, naganganu da kuma hoton wannan ranar da ya fara tambayarta sunanta ya sake dawowa cikin kansa.
    _”Waye ya kawo ki nan?”_
    _”Abokin babana ne.”_
    _”Ina baban naki?”_
    _A hankali tace._
    _”Ya rasu.”_
    _”Ina babarki?”_
    _Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace._
    _”Tana nan, matarsa ce ita yanzu.”_
    _Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ƙiyasinsu._
    _”Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?”_
    _Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan._
    _”Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba.”_
    Wadannan maganganun suka dawo cikin kansa a lokaci guda, a cikin sakannin da mutumin bai kai ga karasowa inda yake ba, don haka zuciyarsa ta ɗauke shi ta ajiye shi a wani mazauni na daban daidai lokacin da mutumin ya ƙaraso har zuwa gabansa ya tsaya kuma kai tsaye tambayar bakinsa ta fito.
    “Yawwa, nace kaine Jawad ɗin?”
    Jin haka yasa shi gyara tsayuwarsa kadan sannan ya amsa, yana ƙoƙarin ture abinda ke cikin ransa.
    “Eh ni ne, Barka da fitowa.”
    Sai ya gyaɗa kansa ba tare da ya amsa ba sannan yace.
    “Ni ne mahaifin wannan yarinyar Zainab da ka kawo…”
    Ya faɗa yana kallonsa don yaji me zai ce, amma baiyi maganar ba sai kawai ya cigaba da kallonsa, don haka shima ya cigaba.
    “Ta gaya min tare kuke daga can gidan da take a Habujan… To an gode madallah zaka iya tafiya yanzu.”
    Kallonsa kawai Jawad yaje yi daga inda yake tsaye yana jin maganganun na shiga cikin kansa suna fita ta ɗaya gefen,kuma sai da ya kai karshe sannan ya girgiza kansa.
    “Nima nagode Baba, amma a yadda na sani mahaifinta ya rasu, kuma ni ban kawo ta ne don ta zauna ba, hasalima wani abu daban ne yazo damu nan kafin in san cewa anan mahaifiyarta take.”
    Mutumin ya sake kallonsa a sheke sannan yace.
    “To ni nake auren mahaifiyarta kuma shi din wanda ya haife ta abokina ne don haka ka gaya min ta yadda ban zama mahaifinta, sannan a wane hurumin zamu sake daukan yarinya yanzu mu baka? Tunda dai ta zo gida ba shikenan ba, dama ita Deluwa da ta kai ta ai ta gaya mana cewa uwargijiyar tata,ta gaji da halinta tace zata dawo da ita gida…”
    Jawad ya sake girgiza kansa yace.
    “Ba gajiya suka yi da ita ba, zasu dawo da ita ne kawai saboda ni, saboda sun fahimci cewar ina son in aure ta, kuma da gaske nake ba da wasa ba…”
    Dariyar da mutumin yayi ita ta katse shi daga kasa ƙarasawa, ya tsaya a lokaci guda yana kallonsa.
    “Ai Zainaba tana da mijin aure tuntuni, itama ta san da wannan zancen, tun ubanta yana da rai muka hada su da ɗan waje na Nura, baya zaman gari ne shi yasa itama muka tura ta don ta tara kuɗin kayan aikinta kafin ta dawo….”
    Nura, Nura. Nura…. Sunan ya ɗarsu a zuciyar Jawad tare da hoton saurayin da suka sauke daga farkon garin yanzu, wannan saurayin da yake sanye cikin wasu dukunannun kaya riga da wando yana washe baki a lokacin da ya miƙa masa dubu biyu, sai kawai ya girgiza kansa yana kallon mutumin, wannan wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ba zai taɓa faruwa ba koda kuwa bayan babu ransa… Zainab tasa ce, tasa ce har abada, me yasa kowa baya ganin tambarin hakan da shi yake gani a tare da ita?
    Ya sake girgiza kansa ya a kallon mutumin kafin yace.
    “Kayi hakuri Baba, amma bana tunanin a yanzu kana ɗaya daga cikin mutanen da zasu hana ni aurenta, saboda…”
    “Saboda me? Nace saboda me? Ita bata gaya maka da alƙawari akanta bane tuntuni? To bari in gaya mska kaf dangin uwarta babu wanda ya damu dasu da nace zan auri uwar tata ma gode min suka yi don babu wanda yake bukatar nauyinsu sai ni da nace na ji na gani.
    Dangin ubanta kuwa babu inda zaka same su, ko wuka ka dora akan uw*r tata ba zata iya gaya maka ba, daga ci rani yazo arewa bai koma ba… don haka bari in gaya maka babu wanda yafi ni iko da Zainaba a yanzu a duniyar nan don haka ka kama hanya ka bar min kofar gidana, ta gode da alherin da kuka yi mata acan da kuma wanda kayi niyya.
    Yarinya ta dawo gida ba fitowa zata yi ba, kai bari in ƙarƙare maka ma ita da sake fitowa daga gidan nan sai idan zata tafi gidan Ɗana, ɗin mahaifiyar tata ma da take taƙama da ita, ta mutu yau kwanaki takwas kenan!”
    “Ta mutu yau kwanaki takwas kenan!*…
    Waɗannan kalaman sune ƙarshen abinda Jawad yaji kafin fuskar Zainab da kuma tunanin halin da take ciki a yanzu ya cika idanunsa bakiɗaya!
    *****
    “Aunty… Aunty… Aunty.”
    Amira ɗiyar Yayar Hajiya Salamatu wadda ke yawan ziyartar ta idan tana gari ta faɗa tsaye daga bakin kofar dakin baccinta. Tana sanye ne da wata matsatstsiyar riga fitted gown data bi fukkan lunguna da kuma tudun jikinta yayin da ta sangala ɗan karamin mayafinta daga gefe ɗaya na kafadar, daya hannunta navrike da jakarta da take ƴar mitsitsita kamar ita.
    Hajiya Salamatu ta yaye bargon da ta lulluɓe jikinta dashi, ta ɗago kaɗan tana kallonta ta gefe.
    “Na tafi.” Cewar Amiran.
    “Yau ma da karatun ne?” Ta tambaya muryarta na fitowa a disashe.
    “Eh Aunty, 2-4 ne lectures din, za’ayi na 4-6 ma amma ba zan tsaya ba.”
    Sai ta gyaɗa kanta.
    “Daga can zaki wuce gida?”
    Ta gyada kanta.
    “Eh, amma idan kina gari zuwa jibi zan dawo.”
    Sai ta mike zaune a hankali kafin tace.
    “Ina nan, bana jin daɗin jikina, bana tunanin zanyi tafiya kwanan nan…”
    Ta ɗan tsaya kadan tana kallonta kaɗan.
    “Momi me ya same ki wai? Sadiya tace jiya ko abinci baki ci ba…”
    “Na sha fruits, bana jin daɗin jikina ne kawai Amira, kije sai kin dawo.”
    Kuma daga hakan Amiran ta san cewa babu wani bayani da zata sake yi mata don haka sai kawai ta tabe bakinta kaɗan cikin siririyar muryarta tace.
    “Bye-bye.”
    Sannnan ta juya tana jan hannun kofar da siraran hannunta da kusan dukkaninsa yake a waje. Hajiya Salamatu ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta dafw kanta da duka hannayenta biyu.
    Bata jin dadi, abinda take fadawa kowa kenan tun a kwanakin da suka wuce,haka take gayawa kowa, daga wadanda suka kira ta don cinikayyar kaya har ma da wasu daga cikin ƴan uwanta.
    Kuma ba karya tayi ba, da gaske bata jin dadin, bata ji dadi tun daga wannan ranar da Awwalu ya furta mata maganar da ta darsa wani irin fata a zuciyarta, wani fata da ya zabge tarin shekarunta na duniya, ya mayar da ita zuwa wani lokaci na can baya, lokacin da take ɗauke da cikin ɗanta, lokacin da take jin abinda kowacce uwa ke ji a lokacin da abinda ke cikinta ya kusa karasowa duniya, wannan hanƙoro da kuma ɗokin, zata rantse irinsa take ji tun daga ranar da Awwalu ya bata sabon fatan da bata taɓa lissafawa dashi a rayuwarta ba.
    Ta miƙe a hankali bayan ta yaye bargon dake jikinta, wayarta da ta ajiye akan mudubi ta jawo tana kunna ta, 10 missed calls daga wata sabuwar lamba ya nuna tar akai, sai kawai ta ajiye ta sannan ta nufi toilet, minti kusan ashirin a ciki tayi wanka hade da wanke bakinta sannan ta fito.
    Bayan ta shirya ta ƙwalawa Sadiya kiran ta kawo mata abinda zata karya sannan ta koma kan wayar tata ta ɗauko ta, ba tare da tunanin komai ba hannun ta ya danna wannan lambar da ta tarar da kiran nata…
    Ta shiga har sau biyu ta tsinke ba’a dauka ba, don haka bata sake kira ba, sai dai kafin ta kai ga ajiye wayar wani kiran ya shigo, lambar Salma ce ƴar gidan Kilishi, mamaki ya ɗan kamata kafin ta ɗauka, ta kara ta a kunnenta haɗe da sallama.
    “Salma kuna lafiya?” Bakinta ya furta hakan kai tsaye.
    “Aunty Mami tana asibiti, bata cikin hayyacinta tun jiya.!”
    Saƙon ya fito tare da bugawar zuciyarta a lokaci guda, ba shiri ta karonto salati tun daga farko har karshe a bakinta.
    “Gani nan Salma, gani nan zan zo gidan yanzu.”
    Ta faɗi hakan tana jin sauran hayaninyar dake tashi a cikin gidan kafin Salma ta kashe wayar,cgirman sakon na lulluɓe zuciyarta, har yanzu Kilishi aminiyarta ce, bata samu wata hujja da zata yi watsi da ita ba har yanzu, Awwalu baiyi nasara ba… Tana son ta ƙaryata shi duk da cewar zuciyarta tafi son ta bashi gaskiyar, amma har yanzu ba komai, bata da wani abubda zai nuna mata gaskiya ko akasinta…
    Ta sauke tata wayar daga kunnenta daidai lokacin da idonta ya kai kan wani sakon da bata lura dashi ba sai a yanzu, saƙon text message ne, daga wannan lambar… lambar da ta kira a yanzu ba’a dauka ba. Idonta ya sauka akan harafan saƙon, harafan da suka canza rayuwarta da na duniyarta a lokaci guda!
    _Assalamu alaikum, an bani wannan lambar ne da fatan zan samu bayanin wata mata mai suna Hanne, iyaye na nake nema a wajenta, please idan saƙon nan ya shigo contact me._
    ***
    Ƙarar iskar dake kadawa ta shiga idanun Awwalu a lokaci guda da mutumin dake tsaye akansa ya kwance ƙullin da aka rufe fuskarsa dashi.
    Ya rufe idanunsa saboda tasirin iskar da kuma na ƙasar dake tashi a wajen yayin da mutumin ya sunkuya yana kokarin kwance wayar da aka ƙulle hannayensa da ita ta baya, jijiyoyinsa suka saki bayan an kwance hannun ya shiga mutsikka su duka a lokaci guda, sannan ya murza idanunsa kagin ya buɗe su a gaban motar dake fake a gabansa.
    Ya kalli kowanne gefe a inda suke, cikin daji ne mai fili gaba da baya, bishiyun da yake iya hange tsilla-tsilla ne.
    Ya juyo da kallonsa zuwa cikin motar dake gabansa ƙirar Odessy sabuwa, idonsa ya sauka akan Ɗantaron dake zaune a kujerar tsakiya wadda aka zuge zuwa baya, gajeren wandon da yake sanye dashi tun jiya shine a jikinsa har yanzu, sai kuma baƙar T-shirt.
    Yasa hannu ya zare gilashin fuskarsa sannan ya kalle shi.
    “Ni ba ɗan i*ka bane Awwalu, ba zan zauna tare da kai ba alhali na san ƴan sanda suna nemanka ba, ina da ƙura a lamurana, idan na bari mutanen nan suka risko ni ba zan ji dadi, don haka ga ka nan na sake ka… Idan kun gama daidaitawa dasu, idan har baka mutu ba zan dawo gare ka don haka ka tanadar min kuɗina kafin nan!”
    Yana faɗin haka yayi wani guntun murmushi sannan yaronsa ya rufe kofar motar ya zagaya zuwa gaba ya shige, cikin abinda yake kasa da minti guda motar ta tashi… Suka bar wajen suna tayar da ƙurar da ta bade fuskar Awwalu baki ɗaya.
    Sai dai wannan ba shine abinda ya dame shi ba, ba shine tunaninsa ba… tunaninsa ɗaya ne, he’s free at last! Don haka ta ina zai fara??
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!