Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaɗe idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba….!”
    Haji Mardiyya ta fada tana dafa sink din daje gabanta a cikin banɗakin, daga cikin wayar, yayar tata mai suna Aunty Sadiyan tace.
    “Duk ba za’a kai ga wannan ba insha Allahu, yanzu dai kawai abinda nake so shine kiyi kokari ki samu ki raba shi da yarinyar kawai, idan har ta tafi sauran mai sauki ne.
    Kawai lokaci zamu ja sai idan ya takura mu samu wani kauyen mu kaishi, da mun fan sunna wa wasu a cikin garin yan kuɗaɗe sai ya same su a matsayin iyauenta kawai ace masa ta mutu, kinga wannan dole ya hakura ai, komai fa dabara ne Mardiyya, rayuwar mace gabadaya akan dabara take tafiya, idan kika iya ta ina tabbatar miki babu ruwanki da tashin hankali akan abubuwa da yawa, kina daga zaune zaki dinga gyara matsololinki hankali kwance.”
    Hajiya Mardiyya ta gyada kanta.
    “Na dade da haddace wannan karatun naki ai Aunty Sadiya, yanzu na aika a kirawo shi don haka ko yazo ma, ba zan nuna masa kai tsaye cewa ya rabu da yarinyar ba, kawai zan nuna raina ne ya baci ta yadda ba zai fuskanci komai…..”
    Kalaman ta suka gutsire a iska sakamakon juyowar da tayi a zacen nata, juyowar da tayi a lokaci guda kuma kai tsaye siffar Jawad ta shiga idanunta, yana tsaye rike da hannun kofar banɗakin, yana tsaye yana kallonta da tarin abubuwan da ba zata iya lissafa su ba a jikin idanunsa, tarin abubuwan da suka sa babu shiri wayar dake hannunta ta zame daga kunnenta ta tarwatse a ƙasa!
    ***
    A cikin tangameman ɗakin baccin, Alhaji Bashir ya sauke wayar dake kunnensa daidai lokacin da matarsa ta biyu Hajiya Yagana, kwallin idanunsa kuma shalele duk a cikin matansa uku ke miƙo masa plate din data zuba abincin a ciki tun bayan farawar wayar tasa tsawon mintuna da suka wuce
    Kallon da take masa wani kala ne, wani kala ne da duk sanda ta yin yake zabge shekarunsa da nata a zukatansu gabaɗaya, lokaci ya ara musu wata dama da a cikinta suke ɗanɗanar ruwan zumar da baya duba da yaro ko kuma babba.
    “Ayi hakuri mana Shalele, aikin his excellency ne, ni ban isa ince ba zan saurare su a yanzu ba.”
    Ya fada yana kallonta da murmushi, sai ta turo bakinta kaɗan alamun ba inda fushin nata yaje kafin tace.
    “Kwana biyu ne an shiga hakkina da yawa ranka ya daɗe, a lalace nayi kusan wata ban same ka ba, duk ranar da kwana na yazo sai tafiya ta taso ko kuma wani abu ya faru… Hatta su Amal sun fahimta.”
    Ya sake yin murmushi mai armashi yana kallonta kafin yace.
    “Kar ki damu, wannan duk labari kike bayarwa, yanzu dai ba gani ba kuma ga ki? ai zance ya ƙare kuma tsawon kwana ukun nan ni naki ne, ko office ba zan fita ba Yagana, idan ƙasar ma kike son mu bari ki zabi inda zamu je mu kwana biyu sai mu dawo…”
    Idanunta suka wulkito tana sake kallonsa yayin da dadi ke ratsawa har cikin zuciyarta, a duniyar nan bata da wani lissafi da ya wuce a kullum ta samu tarin hanyoyin kuntatawa kishiyoyinta, duk wani abu da zata yi su ji haushi shine kawai alkibilarta, don haka ta gyaɗa kanta tana murmushi sannan tace.
    “Garin masoya zamu tafi Daddy, (Paris) ina son inga hasken fitulun garin nan na haska min fuskar ka a idanuna….”
    Dariya da Alhaji Bashir yayi wannan karon mai sauti ce, dariya ce dake fitowa tun daga cikin zuciyarsa, kuma har ya buɗe baki zai yi magana lokacin da kararrawar (doorbell) ɓangaren gabaɗaya ta ɗauki ƙara, sautin ta ga mamaye ko’ina da amon da zaka san tabbas ba an danna ta ne sau ɗaya ba.
    “Waye wannan kuma…”
    Hajiya Yagana ta furta tana ƙoƙarin danne zagin da taji ya biyo bakinta. Kuma kafin ta karasa wata karar ta sake biyo baya, Sai kawai Alhaji Bashir dake gefe yayi murmushi yace.
    “Je ki buɗe ko waye na gida ne ai.”
    Kamar ba zata tashi ba, don sai dai ta kirga wasu sakanni zuciyarta na biya tsinuwar dake tafiya ga ko waye a bayan kofar nan kafin tayi kwafar da ita kadai taji ta ta mike, ta miƙe sanda Alhaji Bashir ke fadin.
    “Zan same ku anan falo.”
    Kafafunta suka dauke ta zuwa cikin falon da shi zaka fara tararwa bayan ka fito daga ɗakin, ta wuce ta isa ga falo na karshe a bangaren sannan ta kama handle din makekiyar kofar ta buɗe bayan ta murda mukullin, kuma fuskar wanda ke tsaye daga wajen, fuska ce da ta sake bakanta ranta a lokaci guda, tasa zuciyarta matsewa a kirjinta… Wai har yaushe Jawad ya fara shiga rayuwarta ne? A kodayaushe ita mantawa take dashi ma a lissafin dukkanin ƴaƴan gidan don ko zama a gidan bai cika yi ba, to don me yasa yanzu zai dawo ya saka ta a gaba kuma?
    Tayi niyyar gaya masa magana amma sai yanayin fuskarsa ya tsaida ita, don duk da ba wani sanin halinsa tayi sosai ba, ta sani cewa bata taɓa ganinsa a irin yanayin da yake yanzu ba, fuskarsa fayau take yayin da idanunsa ke haskawa da wani abu da bata san meye ba, sai kawai ta saki kofar sannan ta juya ciki ba tare da tace dashi komai ba.
    Ta juya daidai lokacin da Alhaji Bashir ke fitowa, nasa idanunsa shima suka sauka akan Jawad din dake shigowa, yana kallon yadda bai ko cire takalman kafarsa ba, balle ya rufe kofar da ya baro a bayansa.
    Kuma ga mamakin Hajiya Yagana, tana juyuwa da niyyar biyo bayansa su dawo cikin falon sai kawai ya ɗaga mata hannunsa guda.
    “Ki shiga ciki Yagana, zan shigo.”
    Ita kanta ta sani cewa a yanayin Jawad din, babu ta yadda za’ayi ya faɗi abinda ya kawo shi a gabanta, bata jin ma ko da gaishe da mahaifin nasa ne zai yi idan har tana wajen, don haka bata ce komai ba sai kawai ta juya ta koma ciki, kuma ta shiga cikin ba tare da ta rufe ƙofar ɗakin gabaɗaya ba.
    Alhaji Bashir ya ƙaraso cikin falon ya samu waje ya zauna, kuma sai da ya zauna ɗin sannan Jawad ya ƙarasa ƙarasowa cikin shima, ya sami waje a daidai jikin kujerar dake fuskantarsa ya durkushe har ƙasa kan lallausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen.
    Alhaji Bashir ya kalli yadda ya zaune a gabansa, idanunsa na cigaba da nazarin fuskarsa, zai kafa hujja da cewar tunda yake bai taɓa ganinsa a irin wannan yanayin ba, don haka sai kawai ya ajiye wayoyinsa da ya fito dasu a gefe sannan ya kira sunansa.
    “Jawad, me ya faru?”
    Muryarsa ta fito ne a hankali, cikin wani amo irin na manya, irin na manya a lokacin da suka fuskanci wata matsala game da ƴaƴansu ko kuma duk wani wanda suka san zai iya samun mafita daga gare su.
    Sai dai abinda Jawad ɗin ya buɗi baki ya fada a wannan lokacin, wani abu ne da ya shallake dukkan tunani da kuma hasashen Alhaji Bashir, wani abu ne da idan za’a tattaro dimbin abubuwan dake kansa a jera sunya tabbata ba za su taba kaiwa ga magana irin wadda ya fada a wannan lokacin ba…
    “Ƴan sanda zasu zo gidan nan, nan da minti kaɗan Daddy, babu wanda zasu taɓa kuma babu wanda zasu kama, kawai so nake ta gansu ta tsorata ta gaya min gaskiya, tace ni ba ɗanta bane ba ita ta haife ni ba, don haka so nake ta gaya min su waye iyaye na kuma meye asalina… Wannan kawai nake so in sani Daddy!”
    ***
    *Ƙauyen Garun Albasu ( Yakura).*
    *12:15Pm.*
    Awwalu ya gyara zamansa a gaban motar da suke ciki, motar dake tafiya cikin wani tsukin lungu na ƙauyen da suka shigo kusan awa gyda da ta wuce, kuma a wannan lokacin suka shafe suna faman tambayar gidan wata mata mai suna Hanne kamar yadda Awwalun yace itace wadda a wancan lokacin ta shaida masa cewar yaron da yake nema yana can Abuja, kuma a cikin awa gudar an kaisu ga gidajen mata masu sunan Hanne fiye da goma, kowacce Awwalu yana fadin ba ita bace da zarar ta fito.
    Lokacin da suka shigo cikin kauyen kai tsaye ma yace zai iya gane gidan da ya sami matar a wancan lokacin, amma tun kafin tafiyar tayi nisa, canje-canje da kuma sabbin tsarin da aka samu a koina ya shaida masa cewar abinda ya sani a wadancan shekarun da kuma yanzu daban ne, don haka suka shiga tambaya, tambayar da ta kaisu ga lissafin mutane kusan tara kafin a samu wanda ya faɗa musu cewa matar ta daɗe da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.
    Tun a hanya Hajiya Salamatu ta sani cewar zai iya yiwuwa matar ta mutu, zai iya yiwuwa su zo su sami labarin wucewar wasu shekaru da mutuwarta, ace musu ta rasu tare da labarin abinda suka zo nema, abinda shine zai zamo ginshiƙin canjawar rayuwarta da ma ta adadin wasu masu yawa.
    Amma bata san me yasa ba a yanzu zuciyarta ke gaya mata cewar bai kamata ta biyewa Awwalu rana tsaka ba, bai kamata ta yarda da wani daban akan aminyarta da suka shafe tarin shekaru tare ba, waɗannan shekarun da a cikinsu baza ta taɓa cewa ga rana guda da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, kokwanton kawai guda daya ne… idan ta tuna cewa sauran mutanen da take azabtarwa wanda suma haka zasu buɗi baki su ce.
    Sannan kuma har yanzu Awwalu bashi da wata shaida, bashi da wata shaida ko guda ɗaya da zata tabbatar mata da dukkan labarinsa, zai iya yiwuwa yazo yayi amfani da ita ne don kawai ya sanarwa kansa mafita, idonta ya sauka akansa daga gaban motar, shi kansa ba abin yarda bane, shekara nawa ya shafe yana aiki tare da Kilishin, shekaru nawa yayi yana taya ta wajen kuntata rayuwar wasu? Me yasa bai taɓa tuba ba sai a yanzu? Shekaru sun fara ja masa amma ko aure bai taɓa tunanin yi ba, bashi da wani mutunci ko kuma wani abu kwakwkwara da rana tsaka kawai zata yarda dashi.
    Sai dai idan har bata yarda da Awwalun ba, to tabbas kuwa ba zata yarda cewa Kilishi ba zata iya aikata abinda Awwalun ya faɗa ba.
    Lungun da suke bi a yanzu wani ɗan tsuki ne da ba don direban nata yace zai iya bi ba, zata ce su fita su tafi a ƙasa ne, don a yanzun ma dukkan mutane da kuma samarin dake zaune sai da suka mike suka dage bencinan da suke zaune akai don bawa motar waje, idanun kowa na binsu da kallon rashin sani kamar yadda suke gani a koina duk inda suka tsaya tambaya.
    “Wancan kwanar ce, yaron yace kwana ta farko zamu karya.”
    Awwalu ya fada yana nunawa direban kwanar dake damansu, zuciyarsa fayau take a kirjinsa, yana jin kamar allon kirjin nasa baya ɗauke da komai, kamar iska ce kawai ke yawo a cikin gangar jikinsa da take fanko, yana jin yadda bugawar zuciyar ke amsawa a cikin kunnuwan shi.
    Rayuwarsa gabaɗaya a yanzu ta ta’allaka ne ga inda zasu je da kuma abinda suka taho nema, nasararsa da akasinta tana ga irin amsar da zasu tarar ga tambayarsu, idan har bai samu gamsaahshen bayanin da zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu ba, bai san me ya kama ba, bashi da wata mafita ko zaɓi illa ya tattara komai nasa ya bar garin Kano zuwa wajen da ya tabbata Kilishi ba zata taba riskarsa ba.
    Kuma wannan ba shine babbar matsalarsa ba, ya san yana da ilimi da kuma takardun da zai iya neman aiki a koina, kuma ya san yana da yan kuɗaɗen da zai iya gina sabuwar rayuwar da zai fara a ko’ina, amma wannan ba shine burinsa ba, ba shine fatansa ba… Bashi da wani jin daɗin da zai wuce ya ga faɗuwar Kilishi, ya ga tarwatsewar ta tare da dukkan mafarkanta, yana so ko sau ɗaya ne Allah ya bashi damar da zai zama sanadin da Kilishi zata ɗanɗani ko da rabi ne na irin baƙin cikin da ta shafe rayuwarta tana jefa al’umma a ciki.
    Bayan sun shiga kwanar, motar ta tsaya a daidai gida mai bunun da akayi musu kwatance, kuma daga Hajiya Salamatun suka fito suna barin direban a ciki, kafafun Awwalu suka ƙarasa da sassarfa ya ƙarasa wajen wasu samari dake zaune a kofar gidan ya shiga yi musu bayanin abinda suka zo nema.
    Akan idon Hajiya Salamatu wani saurayi ya miƙe ya shiga cikin gidan bayan yayi wa Awwalun bayanin cewa zaiyi masa iso da matar da suke nema, tana ganin yadda Awwalun ke juyowa yana kallonta daga inda yake tsaye, sai kawai ta juyar da kanta gefe guda ba tare da tace dashi komai ba, sharadi ne sun rifa sun yi sho tun kafin su taho.
    Zata yafe masa,ba zata ce komai ba, ba zata ce komai ba,ba zata tona shi a gurin Kilishi ba, zata barshi yaji da neman hanyar tsira da rayuwarsa,komai zaiwuce kamar bai faru ba, niyyar taimakonta da yayi zata kore duk wani sharri da da zata iya shirya masa, amma idan har akasin hakan ce ta faru, komai ya tabbata zuwa gaskiya… to tabbas zata nunawa Kilishi wata sabuwar siffar cin amanar da a tsawon rayuwarta kaf! bata taba saninta ba.
    Cikin abinda yake kasa da minti biyar, wannan saurayin ya fito yana faɗin ance su shiga ciki. Awwalu ya juyo ya sake kallonta alamun ta taho kuma bata ce komai ba har a lokacin ta gyada masa kai kawai.
    Suka nufi ciki inda bayan sun wuce soron bunun ƙatuwar haraba ce irin ta gidajen ƙauye, akwai tarkace mai yawa wanda ya haɗa da tarin tirame da kuma wasu abubuwan da baza su lissafu ba, ginin ƙasa ne a ciki na ɗakuna kala-kala kowanne na fuskantar junansu yayin da wasu suke daga can gefe, mata guda hudu suka tarar a tsakar gidan, uku da hijabi a jikinsu da alamun shigowarsu ce ta sa suka sanya sai kuma wata tsohuwa daje surfe daga can gefe, dukkaninsu suka amsa sallamar su.
    Wannan saurayin da ya shige gaba shi ya jagorance su har wani daki dake can karshe, kuma tun kafin su shiga suke jin muryar dake ciki na faɗin.
    “Maraba, maraba… Sannun ku.”
    Hajiya Salamatu ce ta fara shiga ciki kafin Awwalun ya biyo bayanta, ɗakin bashi da girma sosai, akwai gado da kuma wasu kayan tarkace na kwanuka daga gefe, sai daga gaban gadon kuma aka shimfiɗa wata sabuwar tabarma, matar tana daga gefe sanye da hijabi itama sai washe baki take yi tamkar ta sansu.
    “Barkan ku dai, maraba…”
    Ta sake faɗa bayan sun zauna, Awwalu bai shigo ciki ba don ko takalminsa bai cire ba, tsugunnawa yayi kawai daga ƙofar ɗakin yana amsawa kamar yadda Hajiya Salamatu ke yi.
    “Ai Yakubu da ya shigo ya gaya min abinda ke tafe daku, yace bayanin Inna Hanne kuka zo nema ko?”
    Awwalun yayi saurin gyaɗa kansa da sauri.
    “Tabbas, indai itace Hanne, to ita ɗin muka zo nema, wani Malam Tanimu ne ya kwatanta mana nan gidan yace ke ƴarta ce zamu sami bayanin inda take a wajenki.”
    Matar da har a lokacin basu san sunanta ba ta gyada kanta sannan tace.
    “Tabbas, ai da yake ta jima da barin ƙauyen nan, tayi wani aure ne a can Hayin Shehu, wani kauye dake gabas da nan, hi isa mutane da yawa ta ɓace musu.”
    Hajiya Salamatu ta gyaɗa kanta kafin tayi magana, maganar da ta zarce ga abinda ya kawo su kai tsaye don har yanzu ita bata ga dalilin shigowar su gabaɗaya da kuma tarbar da matar ke yi musu ba.
    “Shi yaron yayi miki bayanin abinda ya kawo mu?”
    Sai kuwa ta gyada kanta a lokaci guda da amon muryarta ya canja.
    “E, yace nemanta kuka zo yi…”
    “Ƙauyen Hayin shehun kawai zaki kwatanta mana da kuma gidan wa zamu nema idan har mun je.”
    Awwalu ya faɗa yana katse abinda take shirin faɗa. Sai ta girgiza kanta a hankali idanunta na kallonsa, sannan ta faɗi kalaman da yake gudu, kalaman da yake tserewa, kuma kalamai na ƙarshe da zai iya tunanin ba da ransa akai idan har zai iya tare su daga fitowa daga amon kowanne mutum a duniyar nan.
    Kanta ne yayi sama ya koma ƙasa alamun gyadawa sannan sautin muryar tata ya fito fili.
    “Haka ne, sai dai Inna Hanne ta riga ta rasu shekaru shida da suka wuce!”
    ***
    Ƙarfe shida na yamma, Awwalu ya buɗe kofar falon gidansa, kuma bai jira komai ba ya shigo har ciki ba tare da ya ko cire takalman kafafunsa ba.
    Ya wuce falon ya tafi har cikin ɗakin kwanansa, inda ansn ma ma bai bata lokaci ba hannunsa ya janyo wani akwatinsa da yake yawan tafiye-tafiye dashi, ya shiga ya baɗe drawer ɗakin a gurguje yana kwaso gogaggun kayansa dake nibke a ciki yana jefa su cikin akwatin, kuma sai da ya tabbata ya kwashi fiye da rabi sannan ya rufe akwatin da ƙyar ya sake jawo wata jaka irin ta matafiya daga ƙasan wardrobe din.
    Ya buɗe zip ɗin cikinta ya tabbatar da tarin cd’s ɗinsa dake ciki suna nan sannan ya wawuro wata computer dake ajiye kan bedside ɗin gadon ya cusa ta a ciki itama ya shiga ƙoƙarin rufe zip ɗin.
    Wayardmsa da ya cillar akan gadon dakin ta shiga kara tana nuna wata sabuwar lamba, da sauri ya dauko ta ya kara a kunnensa.
    “Eh nine, ni ne wanda ya kira ka yanzun nan… Dan Allah ka taimaka in samu ticket din nan… Eh, na Lagos… To shikenan ina son na Lokojan… Nagode ka samar min shi ɗin kawai, gani nan yanzu zan karaso.”
    Ta fadi dukkan wannan bayanin, zuciyarsa na rawa tare da amon muryarsa, burinsa da ma fatansa ya ta’allaka ne a tanzu kawai kan barin garin nan, babu iya kokarin da baiyi ba wajen kokarin fahintar da Hajiya Salamatu iya gaskiyarsa don ta yarda da dukkan bayanin da yayi mata, amma bata saurare shi ba sam! Hasali ma ta gaya masa ne cewar zata yi masa alfarmar rufe sirrinsa a wajen Kilishi don niyyar taimakon da yayi mata, kuma bata ko sake ɗauko shi motar ta ba ita da direbanta suka juya suka tafi suka barshi tsaye a ƙofar gidan Bunun nan.
    Haka ya fito daga cikin ƙauyen nan ya samu ya isa tasha sannan ya ɗauki shatar mota guda saboda tun akan hanya zuciyarsa ta gaya masa cewa bashi da isasshen lokaci da kuma kwanciyar hankali daga yanzu, gobe ne… gobe ne ranar da Kilishi ta gama tsarinta akansa, gobe ne dukkan wannan bayanan da yaji su a matsayin labari zasu tabbata idan har bai samarwa kansa mafita ba.
    Don haka a yanzu zai dauki dukkan wasu abubuwansa masi muhimmanci ne ya var garin nan, idan yaso daga baya,zaiyi magana da dillalin da zai sayar da gidan ya kuma ɗaukar masa sauran kayansa… Burinsa da fatansa kawai shine ya bar cikin Kano a yau, yayi nisa daga inda Kilishi zata iya samunsa kafin yayi nisa daga gare ta gabadaya, nisan da ba zata taba iya samunsa ba, don idan har shi baiyi nasara akanta ba, to kuwa ba zai taba bari ita tayi akansa ba.
    Bayan ya ajiye wayar ya zaro wallet dinsa ya kalli adadin kudin ciki da kuma tarin cards ɗinsa na banki, ya tabbatar komai yana nan daidai sannan ya sake mayar da ita aljihunsa.
    A hannayensa duka biyun ya ɗauko jakar ya kuma riƙo akwatin da guda ɗaya, ƙafafunsa na sassarfa ya fito daga ɗakin ya sake biyowa ta cikin falon ya nufo hanyar fita waje inda motarsa da ya bude ke jira, sai dai da taku biyu kaɗai ya rage tsakaninsa da kofa lokacin da abin ya faru…
    Kofar falon ta buɗe da wani irin ƙarfin da yafi na hankali, kuma a cikin sakanni biyun da suka biyo baya, idanun Awwalu suka ɗaukar masa hoton mutanen da suka fado ciki…
    Ya san su, ya gane shigarsu, kayan jikinsu da kuma yanayin yadda suke rufe ba tun yau ba, ba kwanan nan ba, a shekaru masu yawa da suka wuce, shekaru goma da suka wuce…. Sai dai kafin kwakwalwarsa ta tariyo masa inda ya san su da kuma a ranar da ya gansu ɗaya daga cikinsu ya karaso da saurin da suka faɗo gidan dashi ya buga masa wani dogon abu da yake riƙe dashi.
    Wata tsawa tare da wani farin haske suka ratsa kunnuwa da kuma idanun Awwalu a lokaci guda! Yaji kamar ruwa na bi ta bayansa, kamar yana sulalewa zuwa wata duniyar daban, taji sanda kafafunsa suka yi rawa suna durkushewa a wajen, kuma kafin idanunsa su tafi su rufe gabaɗaya, yaga sanda da yawansu ke shigowa cikin gidan suna yanyame shi.
    ****
    “Kun gama?”
    Ma’aruf ya tambaya a cikin wayar dake kare a kunnensa yayin da yake zaune cikin daga office din Faruk.
    Amina dake tsaye ya gaban mudubin dakinta ta daga kai kafin tace.
    “Eh yanzu ta fita, ta gaya min duk abinda zan dan kiyaye ne kuma tace babu wani abu tunda anui scanning a asibitin babu wata matsala, kuma nace mata babu abinda nake ji.”
    Ma’aruf yayi shiru yana kallon tarin takardun dake gabansa da kuma Faruk ɗin dake can jikin windon office ɗin yana waya, an kammala dukkan wani binciken da gidan waya je yi akan lambar da suka samu ta Awwalu, sun sami tarin bayanin da tun dazu ake turowa Faruk ɗin yana printing dinsu daga computersa, a yanzu abu ɗaya kawai suke jira, so suke yi a turo musu da address din inda yake wanda aka samu daga cikin wayarsa tare da wani shekaru uku da suka wuce yana bayanin canja gidan da yayi.
    Yaron da zai turo musu da report ɗin hakan ne ya tafi wani meeting tare da sauran shuwagabannin su, don haka tun ɗazu Faruk ɗin ke rike da kan waya yana jiran dawowarsa tare da kuma samun wasu bayanan daga sauran ma’aikatan wajen.
    A gabansa kuma tarin takardu ne na meeting din da zasu shiga da kamfanin Rotel&co gobe, kwangilarsu ta gaba… Babu yadda Faruk bai yi dashi akan su daga ranar zaman nasu ba amma yace masa A’a dole zasu ajiye komai a gefe su yi hakan, don baya son bawa Baffa kowacce irin dama da zaiyi tunanin cewa suna kasawa a wani abu, sannan su kansu kamfanin sun samu kwangilarsu ne da kyar, akwai tarin kamfaninnika da yawa da suke neman samun yin aiki dasu don tabbas kowa shaida ne cewar biyansu ya banbanta da na wasu kamfanikan da yawa.
    Don haka ko yaya suka basu wata dama, kai tsaye zasu iya tuntubar wasu su manta da zancensu, fon haka ya dage cewar dole su tsaya kan alkawarinsu, amma kuma duk da
    Wadannan tarin ayyukan dake gabansa tunaninsa ya kasa mantawa da matarsa da kuma sabon al’amarin da suke ciki, gani yake kamar ba haka bane, kamar abinda ita da kuma asibitin nan suka gaya musu ba gaskiya bane, ba don komai ba sai don yadda abin yake iya tsakaninsu kawai har yanzu.
    Lokacin da yana tare da Rukayya, lokacin da ta sami ciki, zai iya cewa shi da Malam sani direba sune na ƙarshe a sani, don yayi tafiya a lokacin har aka kwantar da ita a asibiti ta kwana babu wanda ya kira shi a cikin ƴanuwanta tunda ita tana bacci a lokacin, sai da safe da Mami zata je asibiti wajenta sannan ta kira shi tana gaya masa, a lokacin suka ji tare da Malam Sanin da zai kaita.
    Kuma Allah ya sani a wancan lokacin da zuciyarsa ta riga ta gama sarewa da al’amarin Rukayya, don baya jin ko sau daya ya taɓa nuna damuwa da abinda ke cikin nata, ya san dai ya bata dukkan kulawar da zai iya, bayan haka bai damu ba da dawainiyar cikin ba kamar ita, kamar itama da a lokacin bata ɗauke shi a komai ba.
    Sai a ranar da Hamida tazo duniya, ranar da ya riƙe ta a hannunsa sannan wannan ƙaunar da iyaye ke ji a lokacin da suka kalli gudan jininsu ta mamaye komai, ta rufe wasu abubuwan ta kuma bude tarin wasu a zuciyarsa, tarin wasun da duk karfin da suka yi basu iya saita rayuwarsa daidai a lokacin ba, don ƙaunar da yake bukata, zuciyar da yake bukata ta fahimce shi tafi tafi karfin ƴar karamar dake bugawa a kirjinta.
    Amma wannan karon, haka kawai yake jin kamar komai daban ne, tunda rayuwarsa ta canja, yana cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankalin da yake ji hannayensa zasu iya buɗewa su riƙe wani abun fiye da wanda yake iya kokarinsa wajen kula dasu a yanzu, shi yasa haka kurum bayan yazo office ɗin ya kira wata likita dake aiki a asibitinsa na can Abuja, ya kira ta yace taje gidan ta sake duba ta tunda sunyi magana tace masa tazo Kano ita da Familyn ta hutu.
    Saboda haka ya sake gyara zamansa yana zura hannunsa cikin gashin kansa kafin yace.
    “BabyDoll kin tabbata babu abinda kike ji?”
    Amina ta girgiza kanta a hankali tana neman wajen zama daga bakin gadonta.
    “Ba abinda nake ji da gaske, kawai kamshin wasu abubuwan ne suke damuna ka sani…”
    Ya gyaɗa kansa yana kallon Faruk ɗin da a yanzu ya tafi can gaban teburinsa yana karanto wasu lambobi daga cikin wayar tasa zuwa cikin wayar dake kare a kunnensa.
    “Kiyi list dinsu gabaɗaya ko menene we are getting them out of the house da zarar na dawo… Kinji.”
    Ta cije lebbenta taba murmushi, don list ɗin farko da ta fara hangowa kusan rabi na turarukan da yake amfani dasu ne, sai kawai ta gyaɗa kanta sannan tace.
    “Insha Allah Sugar.”
    Yayi shiru na wani lokaci, itama tayi shiru bata ce komai ba, tana jin muryar Farouk din dake magana daga cikin wayar.
    “Kina son wani abu?”
    Ya tambaya a hankali yana katse shirun, sai ta girgiza kanta kamar yana kallonta kafin tace.
    “A’a.”
    “Ni ina son wani abu…”
    “Wani abu me?” Ta tambaya tana cije lebbenta sanin halinsa, amma sai taji yace.
    “Dan Allah ki min tuwo yau…”
    Tuwo. Kalmar ta dira akanta duk da yadda ya fade ta a hankali, ba wani jin daɗin jikinta take ba, kawai daurewa take tana gaya masa babu komai tunda ta san tarin ayyukan dake gabansa da kuma abinda yake fuskanta. Bata tunanin ma zata so kamshin kowacce miya da zai ce yana so.
    Amma ya zata yi? Ba kullum ne zata fyskanci abinda take so a cikin auren ba ma ta sani, ta sani a cikin kanta cewa wannan matakin da suke ciki mai wucewa ne ma, yau da gobe tafi ƙarfin komai, rayuwar ba tatsuniya ba ce ba, ko a tatsuniyar ma akwai lokacin da abubuwa basa tafiya daidai, tana lissafi da ranar da zata zo Ma’aruf zaiyi mata abinda zai ƙona ranta, tana lissafi da ranar da zata fara fuskantar irin hakurin da kowacce mace ke yi a gidan aurenta, saboda hakan shine auren shi yake mikewa ya cigaba da haifar da fahimtar juna da kuma shaƙuwa a tsakani, idan har babu hakuri a ginshikin aure, da tabbas duk wani nau’i na jin dadin duniya ya ƙare.
    Saboda haka sai kawai ta gyaɗa kanta a hankali sannan tace.
    “Insha Allah Sugar, kayi aikinka ka dawo, muna nan muna jiranka da tuwonmu a ƙofa…”
    Tana jiyo murmushin da yayi mai kama da dariya.
    “I love you so much Noor…”
    “Love u too.”
    “Ki saka min wannan rigar kafin in dawo.”
    “Wacce?”
    Ta tambaya girarta biyu na gadewa waje guda alamun bata gane ba.
    “Wadda ba sai na sha wuya ba…”
    Dariyar da ta kyalkyale da ita ta katse sauran maganganunsa, yayi shiru yana juya biron hannunsada nasa guntun murmushin shima.
    “Da gaske nake.”
    Sai ta girgiza kanta sannan tace.
    “Kar ka damu, zaka so wadda zan saka fiye da wadda kake tunani ma…”
    Ya girgiza kansa a lokaci guda
    “The day is rough Babydoll, and you are making me go crazy…”
    (Ranar yau sai a hankali Babydoll, kuma kina kara rikita ni….)
    Amina ta cije leɓɓenta a hankali tana murmushi, kuma sanin halinsa da abinda zai iya faɗa a gaɓa, yasa tayi saurin yi masa sallama, wayar tasu ta ƙare da hakan.
    A daidai lokacin da Ma’aruf ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da Faruk ya tsaya a gabansa yana miƙo masa takardar dake hannunsa, kuma murmushin dake kan fuskarsa shine abu na farko da ya fara shaidawa Ma’aruf abinda bai furta ba.
    “Mun same shi Ma’aruf, ga address dinsa nan, ka shirya mu tafi… ko waye wannan Awwalun yau dubunsa ta cika!”
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!