Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Hannun Inna dake riƙe da cokali ya juya wani kwadon zogalen da yaji kuli-kuli da kuma su tumatir daga can tsakar gida inda take zaune yayin da a lokaci guda da Amina dake zaune a gɗaki ta sauke wayar hannunta daga kunnenta.
    Idonta ya tsaya akan Amman yayin da kalamanta na yau suka shiga dawowa cikin kanta. A dazu bayan fitar Baba, sun fi ƙarfin awa guda suna magana, magana sosai irin wadda tun bayan tafiyarta basu yi irinta ba kasancewar wannan ba’a waya bane ba, sun sake tattauna tarin abubuwan da suka gudana a baya sannan ta gaya mata cewar ta cigaba da rike Hamida hannu biyu kafin ta ga abinda su Rukayya ke shirin sake shiryawa, wanda har a yanzu ta jaddada mata da cewar kar ta bari Ma’aruf ya sani.
    “… Ki cigaba da tafiyar da al’amarin gidanki kan turba mai kyau Amina, daga shi har yarinyar kar ki basu kokwanton wani abu yana faruwa daban tare dake, ki barshi yaji da matsalar wajen aikinsa da yake fuskanta yanzu, kuma kar ki taɓa tambayarsa wani abu idan har ba shi ya gaya miki ba, don tambaya hanya ce mai ce miƙakƙiya ga zargi… Don haka ki kyale shi da dukkan wata tambaya da ta shafi binciken da yake yi, kwanciyar hankali shi yafi buƙata daga gare ki yanzu, idan har muna buƙatar wani bayanin, akwai hanyar da zamu samu abinda muke nema daga gare shi, zai faɗa miki duk abinda kike so ba sai ma kin tambaya ba.”
    Tana tuna yadda ta dinga juya maganganun a lokacin, yadda Amma ta gata mata dukksn hanyoyin da mace zata bi idan har tana son samun amsar wani abu daga wajen mijinta, ba tare da shi kansa ya fahimci tambayar tata da kuma abinda take nema ba.
    “Rayuwar mace gabaɗaya dabara ce da kuma kissa Amina, idan da har bayan ibada kowacce mace zata ɗauki waɗannan abubuwan guda biyu ta riƙe su a kowanne fanni na rayuwarta, da tabbas mata da yawa zasu sami rabin aljanarsu ta duniya.”
    “Kin san ranar nan kuwa Jamila tazo nemanki?”
    Maryam dake zaune a gefenta riƙe da Hamida wadda ta ɗane kan cinyarta tana zana mata fulawa da abin Rani ja kan fararen hannunta ta fada.
    Amina ta kalle ta, tana tuno Jamilan da take fada, wata ƙawarta ce da a islamiyya ce da babu gaira ba dalili ta tsiri daina yi mata magana, har Amma sai da ta shiga cikin al’amarin a lokacin wajen tambayarta abinda ya faru amma tace babu komai.
    “Da gaske? Me tace kuma?”
    “Wai taji labari ance kinyi aure ne shine tazo yin murna, wai a rakata inda kike ku gaisa.”
    Amina tayi murmushi tabya jinjina kanta alamun mamaki kafin Maryam din ta cigaba.
    “Amma tace wai ai sai ta saka rana tazo a raka ta, shine ta karbi nambar wayar Amman wai zata kira, ni kuwa na bata wrong number, ranar da ta gaji ta tako ƙafarta tazo, kwanciya zanyi ince bani da lafiya?”
    “Saboda me?” Amina ta tambaya tana dariya.
    “Dan Allah ki rako ta ko kuma ki bata namba ta, kinga ai a kawo karshen gabar tata.”
    Maryam ta girgiza kanta tace.
    “Wallahi Yaya wannan yarinyar ba mutunci ne da ita ba, haka kurum taje ta jawo miki wata matsalar…”
    “Haba dai, ai bata isa ta jawo min wani abu da yafi karfin wanda nake ciki ba Maryam, tunaninta bai isa yafi na mutanen da nake tare dasu ba.”
    Ta fadi hakan fuskar Kilishi na haskawa a cikin kanta.
    “Bata sake yi kiranki ba har yanzu?”
    A dazu da suke magana da Amma haka ta tambaye ta, ta girgiza kanta kafin tace.
    “Bata sake yi min magaba ba tun daga lokacin Amma, na kula kamar kwana biyu hankalinta ya rabu ne kan wani abun, tana yawan fita sannan bata maida hankali kan abubuwan gidan sosai.”
    Amman ta gyada kanta a lokacin sannan tace.
    “Watakila ta fahimci binciken da suke yi ya fara doso ta ne, watakila kuma tana da tsarin wasu abubuwan bayan sha’anin yarinyar shi yasa tayi miki shiru.
    Kilishi tana da tsari, ta san me take yi… Wasu abubuwan take saitawa kafin ta waiwaye ki, ba zata baki aikin a lokacin da ta san hankalinta baya kanki sosai ba, watakila kuma tsuntsu biyu take neman jifa da dutse ɗaya, abu biyu zata haɗa a lokaci guda. Ba lallai ki iya sani ba, amma idan kin ga alamar wani abu ki gaya min watakila zamu iya samo wani abun a cikin takunta.”
    Ta gyada kanta a lokacin sannan ta ɗago ta kalle ta sosai kafin tayi tambayar da ta daɗe tana ci mata rai a zuciyarta.
    “Amma idan har ta kawo maganin ta yaya zanyi amfani dashi? Lokacin da muka yi magana kince komai zai faru amma kuma ba abinda zai faru? Kince a idonta kawai Hamidan zata makance amma ba a gaske ba.”
    Murmushin da Amman tayi mai fadi ne a lokacin kafin tace.
    “Kar ki damu, har na fara wannan shirin Amina, na gaya miki takunta zamu ɗauka kamar yadda muka fara yanzu, zamu shammace ta ne ta hanyar da take shammatar mutane, ta hanyar da take ganin tata ce itace mai ikonta, don haka ki bari lokacin yazo zaki san komai, nafi so a yanzu ki tsaida hankalinki akan gidanki tukunna, nan ne ɓangare mai girman da yafi kowanne bukatar tallafawarki a yanzu.”
    “Wani abu kike ciki yanzu a gidan?”
    Tambayar Maryam ta dawo da ita duniyar zahiri, sai tayi saurin girgiza kanta.
    “Ina nufin tunaninta bai isa yafi na mutanen gidan da yanayin wayewarsu da komai ba, na gaya miki yadda su Samiran nan suke, yanayin rayuwarsu ta banbanta da namu ta hanyoyi da yawa.”
    Ba tare da ta fahimci komai ba Maryam tace.
    “Shi yasa bana son zuwa ai, kin san ni duk inda za’a wulankanta ni ko a raina ni ba son zuwa nake ba, wallahi ko da su Amma suka tafi Jigawa kai Aminun nan da muka je gidan Kawu Mallam baki ji yadda na dinga ji ba, na tsani a dinga min iko da abu.”
    Sanin wannan halin nata sarai yasa Amina bata ja zancen ba tace.
    “Allah ya taimake ki kar Baba ya miki irin nawa.”
    Sai ta girgiza kanta tace.
    “Wallahi ba zan iya ba Yaya, ba zan taba iyawa, nifa kinga ko kayan gidanki da na san da yawa nasu ne, zasu sa zuciyata ba zata nutsu wani ya shigo ya gaya min magana…Don ma dai Hajiya Kilishi ce, da sauki ta saba mana alkhairi, shi yasa ma banji komai sosai ba ko a wannan tafiyar dasu Baba zasu yi.”
    Amina tana murmushi tace.
    “Allah ya shirye ki Maryam.”
    A wajenta dukkan wannan abin da take faɗa tatsuniya ce kawai, don bata san tarin kalolin da rayuwa ke haskawa ɗan adam ba.
    Daga haka idonta ya jai waje inda Amma ke zaune da kwano a gabanta da kuna Hafsa da ta shigo a lokacin daga islamiyya tana tambayar.
    “Har yanzu su Yaya suna nan?”
    “Wai ina Aminun yake ne ma?” Amina ta tambaya.
    Maryam ta tabe bakinta tace.
    “Abokanansa ai ba sa kyale shi tunda ya dan ji saukin nan, yanzu zaki ji sallama sun shigo sun gara wheelchair din sun fita dashi musamman yanzu da suka san jibi za’ayi tafiyar nan.”
    Kafin Amina tace wani abu Hamida dake kan cinyar Maryam din ta taso da sauri tana nuna mata kunshin da aka gama da murnarta.
    “Babydoll yayi kyau?”
    Wani abu ya ratsa cikin kan Amina, ta rasa ta yadda zata yi yarinyar nan ta daina kiranta da haka, Ma’aruf ya vuvi kwakwalarta da yawa, kuma kagin ta amsa idon ta ya gano mata Hafsa, sai kawai tayi wajen da sauri tana fadin,
    “Aunty Hafsa come look, zo ki gani me aka min
    …”
    Mamaki ya kama dukkaninsu. Maryam ta gyada kanta tace.
    “Ina gaya miki Hafsa ta ƙar rashin mutunci yarinyar nan, yanzu wai daga zuwanku har ta san ta gaya mata sunanta Aunty Hafsa…? Bari Adam yazo kuma mu ji Uncle Adam.”
    Dukkaninsu suka yi dariya Amina na fadin,
    “Ni na san kamar fuska kawai muke yi da Hafsa ai, amma ina zan iya da halinta.”
    Maryam tana mikewa tace.
    “Yarinyar nan zata kunyata ki a cikin mutane watarana, gwara ma ki gaya mata ba sunanki BabyDoll ba…” Ta dan yi shiru sai kuma tace.
    “…Amma kuma ya iya zabar suna.”
    Dardumar dake gefenta Amina ta ɗebo ta cilla mata tana faɗin.
    “Ranki zai ɓaci wallahi…!”
    Wayarta tayi kara a lokacin, Fatiman da take ta jira ce.
    “Haba Fati, wai bokiti guda ake soya mana ne?”
    Daga cikin wayar, a gaban ƙawarta dake soyar waina Fatiman tace.
    “Kin san mutanen da aka tsallake ake yi mana ne kike ta kwala min kira, to wallahi ko sun zo daukar ki ne sai sun tsaya mun ci wainar nan Allah.”
    “Wa ya gaya miki tun yanzu zan tafi? Ni kawai na ƙagu ne, bakina sai tara yawu yake.”
    Fatiman tayi dariya tace.
    “Ki cewa ɗan Baban yayi hakuri, gani nan a hanya.”
    A lokaci guda kalaman Fatiman suka tafi cikin kan Amina dake zaune suka buga wani abu, wani abu da taji dirarsa har cikin ƙirjinta, wani abu da yayi mata kama da tashin hankali a lokaci ɗaya, taji ma’anarsa na yin fadi a cikin zuciyarta tana so tafi karfin kalmar kokwanto.
    Hannunta ya kai kan cikin ta a lokaci guda da kalmar Fatiman ta furta akan lebbenta, kwana biyu bata jin dadin jikinta sam, tana ta yin komai ne amma bata fahimta ba sai da ta fara jin tashin zuciya, haka kurum take ji kwana biyu bata son kamshin wasu abubuwa,ko a yanzu ma zogalen da Amma ke haɗawa ne yasa ta kasa tashi taje wajenta, tun daga nan take jin cewa bata son ƙamshinsa, sannan kuma yadda take ji kamar wani abu a cikin cikinta na rawa na jiran wainar fulawar da Fatiman ta tafi siyo musu, yafi karfin yadda take son wainar a kodayaushe.
    Amma tsaya, haka da wuri komai yake faruwa? Kai tsaye kawai? Idan zata tuna lokacin da Aunty Ma’u ta sami cikinta na farko ba irin wahalar da ita da mijinta da kuma Amma basu sha ba.
    Don ta kusa sati uku kwance a asibiti, kuma Amman ce mai kwana da ita a lokacin, to ta yaya ita yanzu tana zaune komai zai faru ba tare da ta ma sani ba? Sai kawai ta ture zancen Fatima a gefe ta mike ta fito daga falon lokacin da ta kula Amma ta rufe kwanon zogalen.
    “…. Suna gidanmu gabaɗaya, zaki zo? Har da Barbie nake da.”
    Ta jiyo Hamida na lissafowa Hafsa kayan wasan ta yayin da take zare ido cike da ɗoki tana kallonta. Tana juyowa suka haɗa ido da Inna dake kallonta tunda ta fito daga falon sai dai kafin tace komai Maryam ta fito daga ɗaki da hijabi tana fadin ta tafi.
    “Ina zaki je?”
    “Kuɓewa zata siyo anan bayan layi gidan su Aisha, ita kaɗai ce ba’a samo ba a kayan naki.”
    Amma ta faɗa tana jawo wata leda mai yalo da baƙi da aka cika taf da kullin bakaken leda.
    “Ga Kuka anan, wannan kuma busashshen zogale ne ga yajin sannan ga dakakkiyar citta da tafarnuwa anan…”
    Ta shiga lisaafin kowacce leda daga ciki yayin da Amina ke kallonsu, zuciyarta na bajewa da wani daɗi da kuma ganin daraja ta girman Uwa, tabbas dole ne wanda ya rasa ta yayi kuka da idanunsa kullum a duniya, don ƙarya ne ka sami mai kulawa da kai tun daga ƙasan ruhi a duk duniyar sama da ita, sai dai kuma ubangiji kan ɓoye wasu tarin hikimomin nasa ga rayuwar wadanda ya karbi tasun, hukuncinsa daidai ne a kodayaushe.
    Ɗazu kafin ta tafi gidan kitson a hira kawai take tambayar idan har yanzu gidan wata mata mai suna Salamatu akan layin nasu tana sayar da kuɓewa, tace duk bata dasu sai gashi har Amman ta tanadar mata komai a yanzu. Da murmushin da godiyar ba zata misaltu ba tace.
    “Madallah, Allah ya saka da alkhairi.”
    Amman ta amsa da Ameen sannan hannunta ya dauko kwanon zogalen nan ta miƙo mata, bata ko bude murfin ba, amma ƙamshinsa ya tafi a tsaye har cikin hancinta, ba shiri ta juyar da kanta da sauri, sannan ta shiga girgiza kanta.
    “Amma madallah, Fati zata kawo mana wainar fulawa yanzu.”
    Amman ta kalle ta na wasu sakanni kafin ta dauke kwanon tace.
    “To ita zaki iya ci?”
    Da murmushin ta ta kalle ta tace.
    “Amma wainar fulawa ce fa.”
    “Wannan ma ai zogale ne kuma kina cin sa a da.”
    Fassarar da Amina ta yiwa kalaman Amma daban a cikin kanta, don haka a lokaci guda idanunta suka kaɗa ta shiga sake girgiza kanta.
    “Wallahi Amma ba wani abu nake nufi ba, kawai ji nayi bana son ƙamshinsa, ya za’ayi in ƙi ci haka kawai…”
    Amman ta gyada kanta tana katse ta.
    “Na sani ai, na san da lalurar shi yasa na tambayeki… Kin fada masa ma tukunna? Don ban ga alamun kun je asibiti ba?”
    “Asibiti?…”
    Amina ta tambaya kai tsaye tana kallon mahaifiyar tata, idan ka shigo a wannan lokacin ka kallesu, su biyu zaune akan tabarmar nan, zaka yarda an ƙirƙiri wani mudubi ne dake zabge shekaru yana kuma ƙara du a lokaci guda, don kamarsu daya sak, yanayin sirantar jikinsu da idanun da hancin, dama yawan gashin kan mai laushi duk da na Amina ne kawai a buɗe, banbancinsu kawai shine shekaru da kuma hasken fatar da Aminan tafi Amman a yanzu.
    “… Lafiyata kalau fa Amma ba abinda ya same ni…”
    Murmushin da Amman tayi shi ya katse ta daga sake magana, ta juya da kanta bata kalle ta ba sannan tace.
    “Baki san kina da ciki ba?”
    A lokaci guda tambayar ta janye Amina daga gangar jikinta, ta jita tana tashi zuwa wata sama mai nisa, tana barin gidan, tana batin unguwar, tana barin garin tana barin ƙasar, tana barin nahiyar ma gabadaya… tana ganin kowa da kuma komai a cikin kanta kafin ta faɗo a lokacin guda, ta taho tun daga wannan lulukin a tsaye, babu wani hijabi har inda take zaune, kuma ƙarar dirar tata ya cika kunnwanta bakidaya!
    ***
    A cikin motar dake tafiya, Ma’aruf ya kalli Faruk dake zaune a gefensa bayan ya ajiye wayar da suka yi da wani jami’in ƴan sanda yace.
    “Yana da wayo Faruk, ko waye Awwalun nan yana da wayo, tunda har daga wadannan mutanen har Mr. Okafor bai taba waya tare dasu ba.”
    Faruk ya girgiza kansa yana komawa da baya ya jingina sosai da kujerar da yake zaune kafin yace.
    “Shi yasa na gaya maka zama zamu yi sosai kawai mu fara sabon bincike, gobe dole ka fito early, sai mu ga ta inda zamu fara.”
    Dawowarsu kenan daga Police headquarters na Bompai inda aka garkame duka mutane hudu ma’aikatan prison din dake da sa hannu akan fitar wannan mai laifin, inda har a yanzu daga mutumin har da mutanen kowannensu ya tsaya akan rantsuwar wani mutumi mai suna Awwalu kawai suka sani akan al’amarin, a yanzu haka an sami nambar da suka yi magana da shi Awwalun a lokacin, an mika ta hannun IT department, kuma zuwa gobe suke sa ran samun bayani daga wajensu idan har za’s iya tracking wani waje da za’a iya samun Awwalun ko kuma wani bayanin da zai ksi su gare shi.
    Ma’aruf ya dunkule hannunsa akan bakinsa kafin yace.
    “Kana tunanin mu shigo da Yakubu wannan ɓangaren shima?”
    Faruk ya girgiza kansa.
    “Yakubu ya iya aiki B, amma ka san yana da nasa matsalolin… Yana aikin ne tare da mutane da yawa kuma ban san me yasa ba amma haka kurum jikina yake bani cewa neman Awwalun nan yana bukatar sirri, sannan ya gaya maka cewa akwai aikin da yake yi yanzu haka shi yasa har zai cigaba da kula da wannan Mr. Okaforn, ka ga we have no time da zamu jira shi kenan.
    Kawai kaje gida ka huta, gobe early in the morning mu san ta inda zamu fara kafin mu sami bayani daga IT members din, zan taho da ƴan bayanan da na hada sai mu gani.”
    Ma’aruf ya gyaɗa kansa sau biyu kafin yace.
    “Gobe Abdurrahim zai dawo and I think ni da Ishaq zamu dauko shi daga airport, but insha Allah zamu yi komai.”
    “Wow! Allah ya kawo shi lafiya…” Cewar Faruk ɗin kafin ya cigaba.
    “Da safe kafin in kira ka, munyi magana da mutanen Rotel&co (kamfanin da zasu yi aiki dashi na gaba) na gaya musu ranar da muka yi fixing zamu zauna dasu… Amma yanzu da wannan abubuwan da suka taso, ina ji kamar a kira su mu ƙara ɗagawa…”
    Ma’aruf, ya sake girgiza kansa.
    “Let them, zamu iya Insha Allah Faruk, kar ka manta duk wannan fafutukar da muke yi Baffa bai sani ba, so abinda kawai zai sani shine idan muka tsayar da aikin mu, har zuwa karshen shekarar nan fa bamu da wata kwangila a gaba, wannan ce damu kawai, may be idan muka yi aiki mai kyau, zamu iya sake wani contract da wasu.”
    “Haka ne.”
    Cewar Faruk ɗin kafin wayarsa ta fara ƙara, ya dauka ya kara a kunnensa ya shiga waya da makanikensa wanda zai zo ta dauki motarsa data mutu a ƙofar Prison din nan da suka fara zuwa.
    “Canja ta zanyi kawai Aminu, kawai dai a fara gyarawa mu gani tukunna…”
    Faruk ɗin ya shiga magana, sai kawai ya dunƙule hannunsa guda dunkule akan bakinsa yayin da har a lokacin yake kallon titi.
    Wani iri zuciyarsa ke masa, wani iri yake ji a dukkanin jikinsa gaba daya, kowannan tukin ymda yake yi ji yake kawai kanar a cikin wani zagaye yake tafiya da idan suka yi gaba suna sake, tunanimsa yq kasa hango masa waye wannan Awwalun da kuma dalilinsa na kassara su, yadda yake amfani da kwakwalwa dana kudinsa don ganin kawai ys tarwatsa su.
    Zai rantse har da Allah dalilin wannan abin bai taru kawai akan kuɗi ba, dole akwai wani labarin dake ƙarƙashin komai.
    A haka har suka karasa kofar gidan Faruk din ya sauke shi.
    “Ka huta sosai B dan Allah idan kaje gida, ka barwa gobe komai, let your mind rest.”
    Abinda Faruk din ya fada kenan bayan ya fita ya tsaya daga wajen motar, kuma da ya kalle shi sai yaga kamar yana kallon mudubi ne wanda ke hasko masa irin tarin gajiyar dake tattare dasu, idanun Faruk din kadai sun kada kamar nasa, don banda ruwan da suka siya bayan sunyi salkar La’asar babu wani abu da ya shiga cikinsu a tsayin ranar yau din.
    Sai dai kafin ya buɗe baki ya bashi amsa, kofar falon gidan daga can barandar dake fuskantarsu ta buɗe, yara biyu mace da namiji suka fito da gudu suna ihun.
    “Daddy! Daddy!”
    Kafin matarsa ta baiyana itama riƙe da hannun karamin ɗansu Aarif wanda ya fara tafiya, sai kawai yayi masa murmushi sannan ya ja motar zuwa can gate inda maigadin dake tsaye bai rufe ba kasancewar ya gaya masa yanzu zai iso. Da a yau bashi da inda zai je ya huta gajiyarsa kamar Faruk, baya jin zai iya hana ciwonsa tashi kotawacce hanya.
    *
    Siraran hannun Amina suka kwankwasa kofar bandakin a hankali, idanunta na kallon tiririn daje saman ƙofar inda wajen glass ne maimaikon katakon dake kasa.
    “Come in…”
    Muryar Ma’aruf ta faɗa daga ciki, sautinta ya fito lazily kamar yadda yanayinsa yake tun lokacin da ya shigo, ta tsaya kamar ba zata bude ba sai kuma tasa hannunta daya da baya riƙe da ɗan karamin towel din da ta riƙo, ta murda handle din a hankali, kofar ta rabu da wata ƴar siririyar hanya amma sai ta kasa karasa buɗewa, ta tsaya rike da handle din kawai tana shakar daddadan dimin dake fitowa hade da ƙanshin sabulunsu.
    Baifi sakanni biyar ba Ma’aruf yaja kofar daga ciki ya buɗe ta gabadaya, yana tsaye daga shi sai towel din dake jikinsa na wankan da yayi, gashin kansa a jike yake gabadaya ya barbaje wasu kuma sun manne da fatarsa, tana kallon idanunsa da suke a lumshe sosai don kusan rabinsu je kawai a buɗe kanar mai jin bacci, sai kawai ta karaso ta rufe takun biyun dake tsakaninsu, tasa towel din hannunta akansa sannan ta shiga goge masa gashin a hankali da duka hannunta biyu.
    Ya rufe idanunsa duka biyun a lokaci guda da hannayensa suka zagaye ƙugunta yana rike ta sosai a jikinsa… Yana jin yadda siraran yatsunta ke motsi a cikin gashin nasa ta jikin towel ɗin. Sai kawai tayi ɗage da kafafunta ta ƙara tsawo daidai shi sannan ta dora goshinta akan nasa, ta janyo hannayenta daga saman towel din ta zura su ta kasan sa, numfashinsa ya kara nauyi akan fuskarta sanda yatsun nata suka shiga cikin gashinsa gabaɗaya, tana jin yadda ya ƙara riƙe ta a jikinsa, ɗumin jikin nasa da kuma ƙamshin sabulun na mamaye ta gabaɗaya.
    “Are you feeling better?”
    Muryarta ta fito a hankali, a hankalin da shi kansa da yake jikinta can kasa yaji ta sosai.
    “Abinda nake ji yafi karfin Better Babydoll, you are healing me…”
    Kalaman suka sata murmushi, suka kuma bata kwarin gwiwar yin ɗage da kafafunta a hankali kafin tayi kissing dinsa, bai ce komai ba da farko sai da yaji da gaske take sannan bakinsa ya furta.
    “Damn it!”
    Da haka ya sake riƙe ta sosai a jikinsa yana tuna mata da banbancin dake tsakanin abinda zata iya da kuma wanda shi zai yi, tsawon mintuna kafin ta janye zuwa baya a hankali tana kallonsa.
    “I love you.” Muryarta ta fito kamar wadda ta tsaya a tsakiyar gudu.
    “I love you too Noor.”
    Ya fada tasa muryar hankali kwance. Sai tayi murmushi mai fadi jin sabon sunan da ta samu kafin a hankali ta janye towel din daga kansa ya fado zuwa wuyansa sannan ta saka hannunta na dama ta shiga gyara gashinsa zuwa baya a hankali.
    “Da zan iya tsaida lokaci zan tsayar da wannan daren yayi ta sake faruwa Sugar, har sai ka dawo daidai, sai na tafiyar da gajiya da kuma damuwarka gabadaya, this is our own happy place, ni da kai kawai.”
    Ta fada idanunta na kan gashin nasa da kuma yadda take gyara shi, ya sake rike ta a hannunsa kafin ya gyada kansa a hankali sannan muryarsa ta fito.
    “Nima haka BabyDoll, I wanna see the sun rise on your skin kullum, amma kar ki damu da nayi settling abubuwan da ke gabana we’re going on a honeymoon, somewhere far away, just me and you.” (Da na gama da abubuwan da dake gabana zamu tafi yawon amarci, wani waje mai nisa daga ni sai ke kawai.)
    Ta gyada kanta tana kallonsa da murmurshi a fuskarta, sai ya sake cewa.
    “Yaya kika bar su Amma?”
    Su Amma, sunan ya tuna mata da gida da kuma dukkan abinda ya faru a can, sai taga kamar taje wata duniya ne ta dawo, rayuwarta a can da kuma a wannan gidan tana da tarin banbanci, a gidansu a gaban iyayenta da kuma ƴanuwanta, ita Amina ce, Aminar da kowa ya sani Aminar da ita kanta ta san kanta a ita, amma idan ta dawo gidan nan sai taji ta koma wata daban, wata suruka a gidan ƴan gayu da kuma ɗan gayun mijin dake sawa taji kamar sune ma’aurata mafi sa’a a duniya, bata jin kanta a komai sai a matsayin Babydoll din da yake kiranta. Fuskar Hajiya Kilishi ce kawai mai ruguzo da ita tana tuna mata cewa ba’a aljanar duniya take ba.
    Amma kuma bayan hakan a yanzu, karo na farko sai taji cewa kamar an ƙulla wani zare ne da ya haɗe waccan duniyar tata da wannan, kalaman Amma, bata tabbatar ba, ba wai bata yarda ba… Kawai kokwanto ne a cikin kanta har yanzu…
    Kokwanton da ta kasance a cikinsa tun daga wancan lokacin, don bata sake cewa Amma komai ba, basu sake maganar ba gar suka taho, kawai dai kowa ya san yanayinta ya canja, tunanin ya cika kanta, tunanin da a cikinsa babu komai sai na yadda zata gayawa Ma’aruf hakan, fon a tsarin da tayi, a tsarin da tayi na kokarin boyewa kowa, kowan da Hajiya Kilishi ta zamo sila babu Ma’aruf, hasalima shine daya hannun da zai talkafa mata wajen cimma dukkan abinda ta tsara din, tsarin da ko Amma bata san shi ba…
    Amma kuma tun kafin tazo gaban nasa, sai ta rasa ta yadda ta yadda zata iya harhado kalaman da zasu tashi ma’anar da zata gaya masa, ta kasa tunanin konai, tana jin kwakwalarta dama zuciyarta fayau, don haka ko a yanzun babu abinda ta iya cewa sai kawai ta shiga bashi labarin gidan nasu da kuma yadda Hamida ta sake da ƴanuwanta.
    Har ya shirya suka koma falo inda ya cika cikinsa da abincinta kafin Hamida ta cika kansa da nata surutun, har suka yi bacci, tana rungume a jikinsa tana jin numfashinsa a hankali kafin ya koma mai nauyi alamun gajiyar dake jikinsa tafi ƙarfinsa.
    Har Asuba da tayi, ya fita masallaci ya dawo ya same ta akan tata sallayar, tana zaune gaban Mahaliccin data idar da ibadarta yayin da zuciyarta ke karanto tarin addu’o’in da basu da ƙarshe.
    Daga bayanta ya tsugunna akan gwiyoyinsa, sannan ya zuro hannayensa duma biyu ya kara su a bayan nata, ya tsayar dasu yadda ta yi wa nata wajen addu’ar sannan ya ɗora haɓarsa a saman kanta.
    Tayi murmushi a hankali tana jin ƙamshin sabon turaren da ya fesa a jikin sallayarta na shigar mata har cikin kai, ƙamshin mai sanyi ne, amma ita tana jin ƙarfinsa har cikin kanta, ta kai ƙarshe a addu’ar kuma yana ganin ta motsa hannunsa ya haɗe su da nasa gabaɗaya suka tafi kan fuskar tata.
    “Ameen ya Allah Noor.”
    Ya faɗa daga saman kan nata sannan ya juyo da ita gabaɗaya tana fuskantarsa, a lokacin ne ta rasa dukkan wani tunanin kanta, yadda yake kallonta a cikin duhun dakin ya warware dukkan wani lissafinta, a lokacin ne bakinta ya furta abinda ya zama mafarin bude wata sabuwar rayuwa a tsakaninsu.
    “Ma’aruf…”
    Bakinta ya furta sunan ba tare da ta san ma me ta fada ba, kuma kafin ya amsa sauran kalaman suka biyo baya, bi da bi, wani na tunkude wani akan lebbenta.
    “I think we’re pregnant….!”
    ( Ina tunanin muna da ciki…!)
    ****
    *No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
    *Gidan Hajiya Salamatu.*
    “Kar ki damu Hajiya, gobe-goben nan zan sako miki su a mota, an riga an haɗa sun cika cif, laces guda talatin da biyu ne, atamfa arba’in, sai materials ɗin guda takwas Nylon da kuma cotton guda goma…”
    A cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Salamatu take wannan bayanin, tana zaune ne a barandar gidanta, daga ƙasan rumfar yayin da iskar yammar ke kadawa a kowanne ɓangare na harabar gidan.
    A gabanta akwai wani dan karamin tebur da ta ajiye jotter da kuma biron da take karanto adadin kayan da take lissafawa a ciki, bayan jotter akwai jug mai garai-garai yana ɗauke da lemo kakar yalo tar da kuma kofinsa wanda aka zuba lemon a ciki.
    Ta kai ƙarshe a wayar tata, sannan ta sauke wayar, kuma kai tsaye hannunta ya lalubo nambar Hajiya Kilishi wadda taji shigowar nata kiran a lokacin da take waya.
    “Ina tare da mutane na ne ranki ya daɗe…”
    Ta fada kai tsaye bayan Kilishin ta ɗauki waya daga nata ɓangaren.
    “Na sani ai shi yasa ban takura ba… Saratu ta kira ni da safe take gaya min cewa zasu dawo kasar nan kunyi waya?”
    Hajiya Salamatu ta gyaɗa kanta tace.
    “Mun yi tun jiya, nake cewa komai labari ne, yaushe take ta daga hankalinta akan yaƙi tafiya da ita gashi har ya dauke ta da ƴaƴan nata kuma zasu zo hutu.”
    Hajiya Kilishi tayi murmushi mai kama da dariya kafin tace.
    “Da ta biyo ta hanya ta ba, a baya ta tashi hankalinta a banza, amma da ta fahimce ni ta ja da baya ta zama macen kanta ba gashi yanzu komai ya dawo hannunta kishiyar tata ma ta kama gabanta ba.”
    “Wallahi kuwa…” cewar Hajiya Salamatun kafin ta canja zancenta da cewar.
    “Kin samu kayan ne?”
    Hajiya Salamatun ta tambaya tana kurbar lemon hannunta.
    “Wai sai Jibi zasu iso, abinda nake ta tunani kenan Salamatu, karo na farko da zuciyata ta kasa kwanciya akan wani abu, haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru.”
    Hajiya Salamatu tayi dariya kafin tace.
    “Ki kwantar da hankalinki Hajiya, kin san hausawa sun ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, gangarar kawai kika zo shi yasa kike jin haka, ban da abinki ma daga ni sai ke fa muka san wannan abin da kike shirin yiwa Awwalun nan, kuma ni dai kin san ko yanka ni akayi baza’a iya fitar da sirrinki daga cikina ba ko?”
    Kilishi ta gyada kanta.
    “Na sani Salamatu, kawai ban san me yasa ba bana gane komai ne a yanzu sai na fara gamawa da Awwalun nan, ɗazu munyi waya da Maigaskiya yace min yana office abubuwwa sun yi masa yawa, bai ce min komai bayan hakan ba amma na fahimci kamar binciken nan suke yi kuma sun gano wani abu Salamatu, da ba Awwalu na dora akan harkar nan ba da na bari ko sau daya ne dun ganni da tuni inaga abubuwa sun canja kala daga yadda nake kallonsu.”
    Salamatun ta girgiza kanta itama.
    “Ki daina wannan tunanin, ki fuskanci abinda ya rage kawai bayan Awwalun, zancen yarinyar nan tasa Hamida sai kuma mutuwar shi mai gidan naku da har yanzu baki tsara yadda zata kasance ba.”
    “Na tsara komai Salamatu, zan gaya miki da zarar mun hadu, a yanzu bayan wadannan biyun kuma ina so da Amina idan ta gama yi min aiki akan yarinyar in raba ta da mai gaskiya itama, a fuskokinsu kawai zaki gane kamar rayuwa na tafiyar musu daidai, ba zan iya basu wannan farin cikin ba Salamatu… Ba zan iya barin Ma’aruf da wani abu mai haske a rayuwarsa ba, so nake har ƙarshen rayuwarsa ya dauwama yana tunanin ni kaɗai ce haskensa.”
    Hajiya Salamatu ta taɓe bakinta kaɗan kafin tace.
    “Ba zaki canja tunaninki akan yaron nan ba Kilishi, amma wannan ɗin ma daidai ne, ai bai ɗara daga cikin aikin ki ba, sai dai tsaya… Wane tabbaci ma kike dashi cewa har i yanzu yarinyar nan bata ɗauke da wata hamidar ko kuma Hamidu?”
    Kilishi tayi murmushi mai fadi kafin tace.
    “Na dade da bata magani Salamatu, kuma a yadda yarinyar nan ta yarda dani ba zata saba min alkawari ba, abinda zanyi musu ma idan ta gama yi min wannan aikin na Hamidan zai rufe musu ido ba zasu ga komai a rabuwar tasu ba daga iyayenta har ita din. Kuma yadda zan raba sun babu wuya, ni na san abinda zanyi, na san abinda zanyi yadda Mai gaskiya ba zai sake kallon yarinyar nan a duniya ba.”
    Hajiya Salamatu ta gyada kanta.
    “Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya… Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waɗannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ƙare, don haka kar kiji komai.”
    Da haka wayar tasu ta ƙare.
    Hajiya Salamatu ta ɗauki jotter da kuma bironta sannan ta miƙe tare da wayarta ta shiga ciki tana barin jug ɗin lemon anan, kuma shigarta kenan bata ko yi minti biyar ba, wata ƴar aikinta mai suna Sadiya ta shigo, ta durkusa har kasa tace.
    “Hajiya kinyi baƙo, yace wai mai karbar kaya ne shi yasa maigadi ma ya barshi ya shigo.”
    Ta ɗan kalle ta tsawon wasu sakanni tana son tuna wadanda suka yi alkawari dasu a yau cewa za’a zo a karɓi kaya, bata tuna ɗin ba don haka sai kawai tace.
    “Je ki shigo dashi.”
    Ta tashi ta juya ta fita, idonta yabi ta da kallo har ta fita daga ƙofar falon nata da yake na biyu a jerin tsarin gidan.
    Minti guda bayan haka Sadiya ta dawo, biye da ita Wani ne da bata ga fuskarsa a karo na farko ba kasancewar ya saka riga irin ta sanyi mai hula ya rufe kusan rabin fuskar tasa, don haka bata sallami Sadiya ba ta tsaya tana kallonsa, idonta akan kofin lemonta wanda ta baro a waje dake rike a hannunsa yanzu, kuma kafin tayi magana yasa hannu ya cire hular zuwa baya, a lokaci guda fuskar Awwalu ta baiyana a gabanta.
    Yana murmushi ya kai kofin bakinsa ya kurɓa, sai kawai ta ɗagawa Sadiya hannu alamun ta sallame ta, Sadiyar ta juya ta tafi shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar dake gefen tata.
    “Me ya kawo ka wajena Awwalu?”
    Ta tambaya fuskarta a hade tana kallonsa, da murmurshi a fuskarsa ya sake kurbar lemon sannan ya taso ya fuskance ta sosai yana rike kofin da duka hannayensa biyu.
    “Ni ba mutumin banza bane Hajiya, na san ƙawarki, na san Kilishi tun bata da komai a duniyar nan sai ku biyu ke da ɗayar da bata magana Saratu… Yau sati guda kenan Kilishi bata kira ni ba, tun bayan da na karbo mata wannan hodar a Lagos, don haka dole na san akwai abinda yake faruwa kuma na san ba zan sami bayani a ko’ina ba sai a wajenki ko kuma wajen wannan ɗayar yarinyar da ta shigo da ita cikin al’amarin.
    Don haka zuwa nayi ki gaya min ta inda Kilishi ke shirin kashe ni…”
    Hajiya Salamatu ta kalle shi tsawon sakanni, cike da mamakin yadda akayi yasha jinin jikinsa game da Hajiya Kilishin tunda ta gaya mata cewa bata bashi wata dama da zaiyi tunanin cewa tana shirin juya masa baya ba… Kuma ko mutumin da ta saka ya kusance shi mai suna Sadik bai bada damar da zai zarge shi ba har yanzu. Sai kawai ta haɗiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.
    “Ban san komai ba Awwalu, ka tashi ka fitar min daga gida.”
    Ta ƙarasa tana nuna masa hanyar kofa, sai kawai ya saje wani murmushin yana kallonta, ya girgiza kansa sannan ya sake kai kofin lemon bakinsa, wannan karon ya shanye shi tas! Sannan ya ɗago ya sake kallonta.
    “Na gaya miki ni ba mutumin banza ne bane Hajiya, ina da abinda zaki miko min Hajiya Kilishi yanzu ba sai anje koina ba.”
    “Me kenan?”
    Ta tambaya tana kallonsa cikin ido. Ya sake wani murmushin yana kallonta cikin ido shima kafin bakinsa ya sake motsi.
    “Kina da labarin inda ɗanki yake?”
    Mamaki ya bayyana tar a fuskarta, mamaki irin wanda ke sauka a fuskar mutum lokaci guda, ba shiri bakinta ya furta.
    “Wane ɗan nawa?”
    Awwalu yana sake wani murmushin da shi kadai ya san ma’anarsa kafin yace.
    “Ɗan da kika haifa tare da mijinki na farko, wanda ya mutu a asibiti ranar da kika haife shi!”
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!