Farar Huta 2 – Chapter Eleven
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“What?”
Ma’aruf ya faɗa da tsananin mamaki yana kallon fuskarsa a cikin mudubin ɗakin dake fuskantarsa.
“Baka ji ni bane ba? Nace maka auren Munaya nazo nema.”
Mamaki ya nuna tar akan fuskar sa yana shafa gashinsa ta baya.
“Wallahi da na iya zagi zan ɗura maka wanda zaka kwana kana juyi Ishaq.”
Daga cikin wayar Ishaq yaja tsaki sannan yace.
“Ai na gaya mata raini zata jawo min, amma tace in fara tambayarka tukunna, da wallahi sai dai kaji zancen.”
Ma’aruf ya girgiza kansa.
“Let’s talk serious, me kake nufi wai?”
“Da gaske nake B, ina son kanwarka, zan aure ta, kuma na gaya mata itama ta yarda, da Baba Usman zan gayawa amma wai sai tace in fara gaya maka tukunna, ban san me yasa yaran nan suke girmama ka har haka ba.”
Tsabar mamaki bakinsa ya kasa rufuwa, sai kawai ta sake girgiza kansa sannan yace.
“Wallahi ban san baka da kunya ba sai yanzu Ishaq, ni kake tambaya wai kazo neman auren Munaya Ishaq?”
“Allah ya tsinewa kunya in dai taka zanji Ma’aruf, kai kanka ina ka ganta da za’aji maka? Maimakon ka fara godewa Allah ma kun samu mutumin kirki kama ta sai ka fara aibata ni? Ni dama na san wallahi raini Peaches zata jawo min kawai don tayi insisting ne.”
Ma’aruf ya gyaɗa kansa.
“Wato Peaches Ishaq, Munayan ce Peaches? Ƴar mutane ce fa…”
Dariyar da Ishaq yayi a cikin wayar, dariya ce da ya dade baiji yayi irinta ba kafin yace.
“Kai ta gidanka ba ƴar mutanen bace ba? Malam in zaka shige min gaba muje wajen su Baffa kayi magana.”
“Ba zanje ba, baza’a baka ba.”
“Nagode Babban Yaya, Allah ya ƙara girma.”
Da haka ya kashe wayar, Ma’aruf ya cije lebbensa yana jinjina al’amarin a cikin kansa, yana jin kamar ba gaske ba, wani iri, kamar a labari cewa wai Ishaq ne ke son Munaya, yarinyar gabadaya shekararta nawa? Shekara ta biyu take fa a Jami’a, kuma a ɓangaren karatun da take yi na densistry bai taɓa zaton cewa zaiji wannan al’amarin a kusa ba, Allah kaɗai ya san yadda akayi Ishaq ya hure mata kunne.
Sai kawai ya zura wayarsa a aljihu sannan ya fita daga dakin da niyyar zuwa gobe yaje ya same shi suyi maganar hankali.
Tun daga korido yake jin maganganu alamun ƙaruwar wani a gidan, don haka ya karasa a hankali tafin kafarsa na taka tiles ɗin wajen, ya ƙarasa daidai lokacin da Amina ke kokarin ajiye tiren ruwa da lemo a gaban wata mata yayin da matar ke kallon Hamida tana faɗin ta taho wajenta, ya tsaya daidai inda su baza su ganshi ba amma shi yana gano su.
“Au ba zaki zo ba sauraniyar Mama? Ba tafiya zanyi dake ba, kinga kaya ne nan ma Mammy tace in kawo miki.”
Hamida ta matse kafadarta daya tana cigaba da kallonta ba tare da tace komai ba.
“Haba Princess din Daddy, Mama Mariya ce fa… Har labarinta fa kika bani.”
Cewar Amina da murmurshi a fuskarta, amma duk da hakan Hamidan ta matse kafadarta.
“Ai shikenan kyale ta, da kanta zata zo,ni kujera ce ai.”
Dukkaninsu suka yi dariya kafin Amina ta koma ta sami waje a kujerar da Hamidan ke zaune, suka gaisawa da matar da har a lokacin Ma’aruf bai gane daga ina take ba.
“Ai maman tata ce tace inzo in kawo mata wasu kaya da aka manta ba’a hado dasu ba, har da na wasanta ma.”
Ta faɗa tana miƙo wata jaka dake gefenta.
Kuma yana ganin yadda Amina bata karɓi jakar ba, amma fuskarta da murmushi tace.
“Ai kuwa ƙika tana kewar kayan wasan nan, don tunda tazo kallo kawai muke ta sha.”
Matar ta sake dariya kafin tace.
“Sai kuma wata mantuwa da akayi, a cikin waccan jakar tata wai akwai wani kayanta data manta shine take son in taho mata dashi yanzu.”
Mariyan ta fada har yanzu da murmurshi a fuskarta, murmushin dake tsayawa iya fatar bakinta kawai ba tare da ya ƙarasa ko’ina ba, don a wannan lokacin tana jin muryar Rukayya tana amsawa a cikin kanta da umarnin data bata kafin tahowarta, umarnin da ta bata bayan tasa ta shafe hannunta da wani bakin ruwa.
_”Idan kika gaya mata haka ta dauko miki jakar, zip din farko zaki bude, akwai wata bakar leda a ciki. Kina zaro ta sai ki bude kamar zaki tabbatar da abinda ke ciki, budewar kawai nake so kiyi Mariya, da kin bude shikenan kin gama cika aikin ki, sai ki kulle ta kawai ki dawo, ki dawo min da ita ki karbi kudinki. Cif dubu hamsin babu ragi.”_
Tana iya tuna yadda zuciyarta ta cika da murna a lokacin, ta cika da wani irin ɗoki da kuma farin ciki, albashinta dubu ashirin ne kowanne wata idan an cire alkhairin da take samu a gidan, kuma ta kwashe shekara da shekaru tana aikin, don haka idan har ba adashi ta ɗauka ba, ƙarya ne ta tuna ranar data riƙe dubu hamsin a lokaci guda ta kanta.
_”Zip ɗin baya zaki bude ledar tana ciki, babu mai ganinta sai ke da kika wanke hannunki da wannan ruwan don haka kar ki tsaya komai, kina budewa zaki ganta ..”_
Maganar da Hajiya Nafisa ta sake jaddada mata ta shiga kunnenta. Sai tayi saurin gyada kanta lokacin da Aminan ke miƙewa da niyyar zuwa ɗauko jakar.
“Who’s she?”
Ma’aruf ya tambaya lokacin da ƙafafunta suka tsaya a gabansa, fuskarta na nunawa da mamakin ganinsa da tayi a wajen. Sai kawai ta matso dab dashi sannan a hankali tace.
“Daga gidansu Hamida take, saƙo ta kawo.”
Tana faɗin haka kawai ya girgiza kansa.
“Dan na kawo miki Hamida bance har da Family ɗinta ba, babu ruwanki dasu, don me yasa zaki buɗe mata kofa?”
Yadda yayi maganar yana ƙoƙarin ɗaga muryarsa yasa tayi saurin dago da hannunta ta rufe bakinsa. idanunta na haskawa da wani abu kamar mamaki, wani abu da yasa shi fahimtar cewa ransa ne ke ƙoƙarin ɓaci, don haka sai kawai ya girgiza kansa yana riƙe hannunta data fora akan bakinsa sannan yace.
“She’s leaving.” (Tafiya zata yi.)
Tafiya? Saboda me? Ta yaya zai ce yace mata ta tafi? Sai dai kafin tayi magana yace.
“I have my plans against mutanen nan, babu wanda zai sake ganinta for the meantime a cikinsu, don haka kar ki sake buɗewa kowa kofa idan har kin san daga nan suke.”
Muryarsa ta fito ne da wani irin kauri da kuma ikon da bata taɓa ji ba yayin da fuskarsa take ɗauke da wani irin yanayin da har yanzu bata san shi ba. Sai ta gyaɗa kanta, amma duk da haka ta daure tace.
“Yanzu zata tafi, amma dan Allah ka bari in ɗauko mata sakon tukunna, ɗauka kawai zata yi sai ta tafi.”
Idan har bai bari ta ɗauko mata jakar nan ta duba taga cewar babu abinda suke nema ba, bata san me zata ƙirga a matsayin nasararta da kuma sakonta da zai isa gare su ba, ya tsaya kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya gyada kansa a hankali yace.
“Ki ɗauko ta tafi, I’ll be out in two minutes, idan na fito ganta zan mata duk abinda yazo kaina wallahi.”
Tana jin haka tayi saurin gyaɗa kanta sannan ta saki hannunsa da sauri ta karasa dakin, bata ko tsaya rufe wardrobe din ba ta dauko jakar ta fito, ta samu baya wajen don haka kai tsaye ta karasa cikin falon.
“Ai tace saƙon itama ba nata bane, wai can Adamawa za’a kai, sai da aka zo tafiya dashi ta duba taga yana nan wallahi.”
Cewar Matar tana ƙarɓar jakar har yanzu da murmurshi a fuskarta, ta miƙa mata da nata murmushin itama sannan ta zauna a kujerar dake fuskantar ta tana cugaba da murmushin dake nunawa tar a fuskarta.
_…wasa da hankalin mutane yana daya daga cikin abubuwan mafiya daɗi a duniyar nan, ina jin dadi duk lokacin da na koma baya na kalli fuskokin mutanen da na ɗaure su tamau da hannayena ba tare da sun sani ba._
Wannan na daya daga cikin maganganun da Kilishi tayi mata ranar da ta fara bude mata ko ita wacece, amma ta manta su, basu sake zuwa cikin kanta ko sau ɗaya ba sai a yanzu, sai a yanzu da take kalllon fuskar Mariyan dake bayani tana kokarin neman zip din da aka kwatanta mata, da sanda ta gane shi, da sanda ta buɗe, da kuma sanda hannunta ya shiga ciki kafin yanayin fuskarta ya canja a lokaci guda jin babu komai.
Sai kawai wani murmushi mai faɗi ya ɓalle daga bakinta, tabbas mata masu wayo dole ne su ji da kansu.
***
“Tunda bank statement dinki za’a bayar, dole za’a haɗa da affidavit da kuma I.d card dinki wanda yake dauke da signature.”
Muryar Muhd, wani ma’aikaci a wajen da ake harkar shige da fice na visa ya fada cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Kilishi.
Hajiya Kilishi ta nisa sannan tace.
“Babu damuwa Muhd, duk zasu taho dasu, idan nasa kudin da zasu isa a cikin account din shikenan komai zaiyi daidai ko?”
“Eh, amma idan da hali Hajiya ki dan bar wani abu ko da dubu dari ne.”
“Shikenan babu matsala, nagode.”
Da haka ta katse wayar, tana tashi ta dauko wata jaka da ta fito da ita a gefen wardrobe din dakin, ta koma kan gadon ta zauna sannan ta fito da dukkan takardun ciki, a cikinsu ta dauko wata ƴar karamar takarda mai dauke da rubutun nambobi ta kwafi nambobin masu shaida wata account number sannan ta tura iya adadin kudin da ta san zasu isa a komai da komai na tafiyar su Aminu har kuma da dorin da muhd ɗin yace.
Ta tura kuma bayan an turo mata da sakon kwasar kudin, bata san sanda tayi murmushi ba ganin yadda wani ɗan mitsitain adadi ne kadai ya sauka akan zunzurutun kudin dake cikin wannan account din.
Jiya ta turawa da ƴanuwanta kudin da take basu a karshen kowanne wata suma, amma duk da haka gani take kamar bata taba kudin ba… Kudin da take da yakinin ko Baffa bashi da adadinsu a yanzu, bama shi ba, kamfaninsu gabadaya da suke takama dashi na Bakorin bata jin adadin da suke dashi ya kai jimlar na accounts dinta gaba daya.
Ita kanta ta sani cewa tayi kokari kokarin da ba kowacce mace irinta ce zata iya shi ba, ganin tsawon shekarun da aka dauka tana cika rantsuwa da kuma burin data daukarwa kanta tun zuwa gidan nan, tun bata da komai sai zuciyarta da tanadinta, gashi har an rufa shekarun da ta tara manya-manyan ƴaƴan da har ta aurar da biyu a ciki.
Wani abu ya ratsa zuciyarta na cewar ƴaƴan da take wa rabin wannan hidimar ma har yanzu basu da masaniyar komai, matsalarta kenan, wajen da take ganin faduwarta kenan… A kokarin binne komai don ta tafi a tsaftatacciyar hanya, bata taɓa nunawa waninsu kalarta ba, har gwara Salma, a kwanakin baya ta kan gaya mata cewa tanadin da take yi musu mai kauri ne, don haka idan har akwai wani abu da zata iya kira da ƙalubalen da take shirin fuskanta, shine na yage su Samirah da zata yi daga wannan gidan da kuma mahaifinsu.
Ta nisa a hankali, tana lissafi a cikin kanta. Komai yana tafiya daidai, ta riga ta gama da dukkan wata harkar kashe kuɗi a shirye-shiryen tafiyar mahaifin Amina da kuma ɗanuwanta Aminu, so take su tafi har su isa can a fara yi masa aikin kafin ta tunkari Amina da hodar da Awwalu zai karɓo mata a lagos, don ta haka ne Aminan zata sami kwarin gwiwar yi mata aikin.
Da taga komai ya fara kuma, zata san ta yadda zata yi ta siya musu gida, wannan zai bawa Aminan ƙwarin gwiwar cigaba da yi mata aikin, sai kuma ta biya musu kudin aikin hajji ta kuma basu adadin kudin da zasu iya buƙata, idan tayi hakan ta tabbata babu makawa Amina zata cigaba da yiwa yarinyar amfani da hodar har lokacin da idanunta zasu rufe gabadaya.
Ta gama wannan tsarin ta ajiye shi a gefe sannan ta jawo na ɓangaren sauran adadin kudin da take son ta lahanta kamfanin Bakori dasu.
Gobe litinin, Ma’aruf zai koma aiki, ta san zai cigaba da bincike akan mutumin nan da ta tabbata yanzu an gaya masa kamanninsa kuma sun fara nemansa, baza su taɓa ganinsa ba kamar yadda har yanzu basu iya gano inda wannan Mr. Okafor yake ba don haka a ajiye hakan a gefe, ta san Ma’aruf, ta san cewar wannan abin ba zai sa ya tsaya da aikinsa ba, zasu cigaba da aiki ne kamar wancan lokacin kuma suna cigaba da binciken su, don haka meye kwangilarsu ta gaba?
Ta jawo wani file ta buda cikinsa, ta dauko takarda ta karanta, sunan wani kamfani mai suna Rotel& Co ta shiga idanunta, sai tayi wani murmushi mai fadi, ta san kamfanin don lokaci bayan lokaci suna yawan yin aiki dasu Baffan, kuma basa wasa da harkar biya ko shi Baffan ya gaya mata.
Lissafinta yayi kwana zuwa wani lokaci na gaba, lokaci mai zuwa, lokacin da har su Ma’aruf zasu gama yi musu aiki azo gabar karbar kudi, idan zata lissafa ba zai fi cikin wata guda mai zuwa ba, don haka me zata yi a wannan lokacin da zai dauke hankalin su kudin su shigo hannunta?
Wace hanya zata bi ta karbi kudin kuma wace hanya zata bi ta fara karkato hankakin ƴaƴanta don ta sami wannan kudin ta san ta kassara kamfanin Bakori kenan har abada, babu ta yadda za’ayi su iya tasowa tunda bata sani ba amma zata iya rantsewa cewa a yanzu da ragowar kudin Ma’aruf zai yi amfani wajen karbar wannan kwangilar, to idan suma suka narke me kuma zasu sake samu suyi wani aikin.
Ta ajiye wannan lissafin a gefe ta shiga lalube a cikin kwakwalarta wajen neman mafita, a lokacin wani tunani ya haska a cikin kanta cewar zata iya samowa kanta hanya guda ɗaya da zata cimma wadannan abubuwan guda biyu, hanya daya da zata dauke hankalin kowa kudin nan su shigo hannunta kuma hanya guda da zata sa ko ƴaƴanta baza su ja da ita ba idan lokacin tafiyarsu yayi…
Hanya daya,
Daya kacal!
Jifan tsuntsu biyu da dutse daya…
Hanyar da zata ƙarkare komai kuma zata kawo ƙarshen komai…
Hanya ɗaya…
Jigo kuma ginshiƙin komai…
Bango…
Meye Bangonsu?
Meye Bangon da zai jijjiga kowa?
Me zai rikito da komai?
Meye abinda zai taɓa kowa ya ɗauke hankalin kowa?
Meye zai taba har zuciyar ƴaƴanta su yarda cewa basu da wani zabi banda nata?
Idan har za’a je ƙarshe, to dole ne ta tabo komai tun daga tubali.
Meye tubalin?
Meye mafari kuma ginshiƙinsu?
Meye Bangon da kowa ke jingina a jikinsa?
Baffa….!
Tabbas Baffa!
Alhaji Muhammad Mansour Bakori.
Mutuwarsa zata zo daidai da rikicewar kowa a gidan kuma daidai da samun nasararta!
Mutuwa…
Ta ɗan tsaya tana nazari a cikin kanta amma kuma sai wani tunanin nata ya kore wannan nazarin, ta taɓa sonsa ne? Tun da suke tare taba jin wani abu mai kama da son sa koda kuwa ɗan burbushi…
Mutum ɗaya zuciyarta ke so, mutum ɗaya zuciyarta ta taɓa russuna akansa, kuma mutum ɗaya ne ruhinta ya taba kallo da wannan sigar, Ma’aruf…
Amma kuma son nasa yazo mata ne ta haramtacciyar hanya, haramtacciyar hanyar da duk kaifin basira da kuma wayonta bata isa ta mallake shi ba. Da wannan karyayyiyar zuciyar take rayuwa a kodayaushe kuma da ita take ganin yadda wasu saɓanin ita ke samunsa.
Shi yasa take yin duk abinda ta san zata faranta masa kuma zata zauna a zuciyarsa, kuma take kore dukkan wani abu da zai ɗara matsayinta a ransa. Ta yarda da wannan, ta yarda iya shi kaɗai zata samu, ta yarda shi kaɗai ne nata, shi yasa take kare hakan da dukkan iyawarta.
Ba zata taɓa bari wani abu a duniyar nan ya keta ta a cikin zuciyarsa ba… Duk sanda ta tashi tafiya kuma zata barshi ne da ragargajajjiyar zuciya irin tata ta yadda ba zai taɓa samun wata dama da wani abu msi kyau zai sake tasiri a ransa ba.
Zata kashe mahaifinsa,
Zata nakasta ƴarsa,
Zata kassara jarin kasuwancin da suke taƙama dashi,
Zata raba shi da Aminar da yaga kamar hankalinsa ya fara karkata zuwa kanta.
Idan tayi haka, me ya isa ya sake ratsa cikin zuciyarsa kuma?
Dole ne kowa ya biya bashin rashin samunsa da ba zata yi ba.
Hannunta ya ɗauki wani biro a gefe, a saman takardar Rotel&Co ta rubuta talatin ga watan yuli.
30th July.
Wasu abubuwan zasu fara kafin wannan ranar, wasu abubuwan kuma zasu faru ne a wannan ranar.
Abinda Kilishi bata sani ba shine, wani lokacin Bawa da hannunsa yake rubuta lokaci da kuma ƙaddararsa!
***
“Ni ba jahili bane Sadik, na gaya maka nafi shekara goma ina tanadi akan matar nan. Da ni take shirya komai, na san duk irin butulci da kuma cin amanar da take shiryawa makusantan ta, to ni waye da zan yi tunanin cewa zata ware ni?”
Awwalu ya faɗa yana kallon abokinsa Sadik, suna zaune ne a tsakiyar falon gidan Awwalun, inda a kodayaushe Sadik ɗin ke zuwa suna hira.
“Me kake tarawa? Kana tunanin abubwan da kake tarawa sun isa su tozarta ta a idon mutanen nan, kai da kanka fa kake bani labarin irin yardar dake zuciyarsu game da ita.”
Awwalu ya jinjina kansa, ya dauki kwalbar lemon dake gabansa ya kurɓa sannan yace.
“Ina da CDs na recording ɗin bayanan da take yi min sun fi guda ashirin Sadik, dukka a cikinsu bayanai ne masu mutukar muhimmanci na abubuwan da tayi, a wayata nake recording sai in bayar a mayar min dasu cikin Cd, sannan ina dasu a duka computers dina ma.
Kuma na dade da sanin cewa sune sanadin arzikina, don ni ba mahaukaci bane da ina kallo zata sami waɗannab maƙudan kuɗaɗen kuma in tsaya kawai ta gutsirar min wani abu a ciki? wane tabbaci ma nake dashi na cewar zata bani ɗin? So hanyarta take gyarawa kawai nima ina gyara tawa.”
A lokaci guda Sadik ya ɗuro wani zagi yana dariya, sannan ya jinjina kansa yana faɗin.
“Sh*gen duniya! To amma baka tsoron idan kayi mata wannan barazanar ta saka a far maka kaima?”
Awwalu ya kalle shi sosai sannan yace.
“A wannan ɓangaren matar nan dakiƙiya ce Sadik, don duk wadanda ka san suna mata aiki ni nake nemo su. Shi yasa nayi mamaki a yanzu da har ta sami wasu a Mexico tayi cinikin hodar nan dasu ba tare da na sani ba, kaga hakan ya nuna min cewar ta fara shirin juya min baya da ta sami wani connection ɗin.
Allah yaso dama zuciyata a tsaye take tun daga lokacin da ta shigo da yarinyar nan cikin wannan al’amarin, don na sani babu ta yadda za’ayi mu’amala mutum uku dole sai biyu sunfi jituwa… Kaga kenan da banyi wa kaina wannan tanadin ba ai na shiga uku.”
Sadik ya jinjina kansa kafin yace.
“To me kake so? Fiye da abinda zata baka?”
Wannan karon dariyar ta Awwalu ce, ya ƙyalƙyala ta iya son ransa sannan ya dago ya kalle shi.
“Duka abinda ta tara Sadik, Duka!”
Ya fadi kalmar karshen yana daga murya.
“A irin abinda ta shuka, cin amana da kuma butulcin da tayi, bata cancanci taci kuɗin nan ko ƙwandala ba Sadik, ban ma san me zata yi dasu ba, matar nan ta tsufa sannan ƴaƴanta duka mata ne, ub*n me zata basu da zai fi ta aurar dasu, kawai dai an halicce ta ne da wani irin son zuciyar da ban san ta yaya zan misalta shi ba.
Ni namiji ne, yanzu zan fara rayuwata, aure zanyi in tara iyali, don haka ka gaya min wa yafi cancanta da wadannan kudaden?”
Sadik ya jinjina kansa yana cije lebbensa kafin yace.
“Kaine, kai zaka ci su, kuma nima dole in taya ka mu same su ko ta wace hanya ce, don nima in samu abinda zan samu!”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
