Farar Huta 2 – Chapter Nine
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“Ma’aruf…”
Muryar Amina ta fito a hankali cikin shirun dakin a hankali, ƙarfe bakwai da rabi ne na safiya, don tun bayan sun idar da sallar Asuba basu koma bacci ba. Kuma jin yayi shiru yasa a hankali ta dago da kanta ta kalle shi.
Idonta ya sauka akan fuskarsa, ya rufe idanunsa gabadaya kamar ya koma bacci amma ta san ba baccin yake yi ba, wani tunani mai daɗi ya sauka a cikin zuciyarta na tunanin cewa daga daren jiya zuwa yau ya daɗa tabbata shi mijinta ne don dukkan wahalar data sha ma da yadda take jin jikinta baya gabanta a yanzu, kawai zuciyarta na kara narkewa ne da tunanin dukkan abinda ya faru.
Daga yadda yake rike da ita kadai a yanzu tana jin cewa kamar a duniya kaf babu wani waje da zata taɓa zama a killace sama da cikin hannayensa, musamman a yanzu da ya fara bata labarin rayuwarsa, tana jin yadda kowacce kalma da yake fada ke ratsawa cikin kanta har zuwa zuciyarta.
Rayuwarsa mai kyau ce, cike take da wani irin gata da kuma jin dadin da ita bata taba saninsa ba ma, don ko a tsakanin yan uwan nasa, rayuwarsa daban ce, Hajiya Kilishi ta kyautata rayuwarsa da wani irin gata da kuma jin daɗin da a yanzu take jin zuciyarta na ƙara dasa aya kan wace irin ƙauna ce wannan da zata so shi irin haka kuma ta dinga cutar dashi.
Sai dai bayan duk hakan kuma a yanzu yazo gabar da yake gaya mata labarin yadda ya rasa ɗanuwansa Jamal, ya gaya mata yadda komai yake tsakaninsu, shaƙuwarsu dama dukkan wani buri da kuma ƙudirin Jamal ɗin bayan ya dawo daga karatu, a yanzu yana gaya mata lokacin da suka yi wata tafiya ne zuwa Bakori don ɗauko Inna Danejo, kuma duk da bsi karasa ba, tunaninta ya gaya mata cewa a wannan lokacin ne wani abu ya faru, shi yasa bayan yayi shiru bata ce komai ba, tana jinsa kawai yana cigaba da wasa da yatsunta daga kasa bargon da ya lulluɓe su, sai da shirun ya tsawaita tukunna sannan tayi magana.
Ya bude idanun nasa a hankali ya lumshe su yana cigaba da kallonta yayin da ita nata ke ware akansa. Kuma a hankali cikin rashin hasken ɗakin muryar sa ta cigaba da cewa.
“Shi ya bani tuƙin a lokacin, kuma abu na karshe da ya gaya min shine kar in kashe shi, bayan mun canja waje na hau titi bamu kara magana ba saboda ya shiga ansa call din wani abokinsa Liman, suna ta magaba ni kuma nayi focusing hankalina akan titin, wallahi wallahi banyi wani abu ba daidai ba, I was driving safely lokacin da abin ya faru.”
Ya sske yin shiru, shirun da ba sai wani ya gaya mata cewar yana shirin gaya mata cewa yana shirin gaya mata dukkan memories din dake binsa shekara da shekaru bane.
“Kawai naji sitiyarin ya ƙwace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi amma ni ban ma san me nake cewa ba, hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta sauka daga kan titi ta nufi cikin daji, daga ni har shi babu wanda yaga karyayyiyar bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa ta faso ta cikin gilashin ta soke a ko’ina na kirjinsa.”
Ya sake yin shiru, idanunsa na kallon tsakanin girarta guda biyu yayin da suke haskawa da wani irin abu da Amina ta kasa tantance shi a lokacin, sai kawai ta ɗago da hannunta daya da bai riƙe ta dashi ba zuwa gefen fuskarsa, a hankali dogwayen yatsunta suka ratsa tsakanin gefen fuskarsa da kuma wuyansa, wani abu da yasa ya sake lumshe idanunsa nasa kafin ya sake cewa.
“Likitocin sunce zuciyarsa ta fasa a lokaci guda shi yasa tun a wajen ya rasu…”
Bata ce komai ba ya cigaba.
“Ya rasu yana kallona Amina, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama’a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, don tankin mai ya fashe tana shirin kamawa da wuta, ba’a iya fito da Jamal ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa.
Ban ma san ta yaya aka zaro ni ba, na san dai kawai ban ƙara fahimtar komai ba bayan hakan sai farkawa nayi na ganni a asibiti, and that was the beginning na farawar ciwo na, I was depressed, emotionless and even out of my mind.”
Taga alamun ya haɗiye wani abu a maƙogwaronsa sannan ya cigaba.
“Kusan haukacewa nayi a wannan time din Amina, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar ita kadai take ta maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru.
Su Mami, kowa da kowa sunyi mutukar kokarinsu wajen tallafa min Amina, musamman Ishaq, Ishaq yayi mutukar kokarin da ban ma san adadinsa ba Amina, kusan shi kaɗai yake tare dani a kodayaushe, dashi muka yi ta yawon zuwa asibiti a London, shi yake tare dani a gida kodayaushe, su Mami suna zuwa duba ni amma ba kodayaushe ba, ina samun support dinsu da tarin addu’o’i.
A cikin wasa muka yi magana da Jamal cewa zan iya canja rayuwata zuwa tasa idan har wani abu ya faru, amma duk da haka bayan naji sauki sai naji ba zan iya rayuwa a matsayin Ma’aruf da wannan nauyin ba, saboda haka sai na ajiye dukkan wani buri na a gefe na fara sabuwar rayuwa.
Tun ina yaro burina ne in zama likita, kafin accident din na sami admission a wata makaranta a lokacin amma bsyan na warke ban sake bi ta kan admission din ba na dage wajen canja makaranta dama course din gabadaya, Baffa ya iya kokarinsa don hana ni amma na gaya masa cewa in dai ba karatun business ba ba zan yi karatun ba gabadaya, a lokacin ne Mami tasa Ishaq ya dawo wajenmu bayan rasuwar iyayensa muka tafi London tare muka yi karatun.
Bayan wannan abubuwan da na canja a rayuwata suna da yawa Doll, this isn’t me, mafi muhimmanci shine wannan matakin da nake kai, burin Jamal shine ya karanci harkar kasuwanci kuma riƙe ragamar kamfanin Baffa kamar yadda nake yi yanzu.”
Ya sake yin shiru yana kallon yadda ta kame gabadayanta, har yanzu hannunta na kan fuskarsa,babu abinda take sai numfashi da kuma jiran ya cigaba.
“Kin fahimce ni Doll, kina ganewa?”
Ya yanke shawarar tambaya, sai tayi kokarin ɗaga kanta a hankali tana son tayi maganar amma ta kasa, ta kasa don bata ma san me zata ce ba, ya gyada kansa shima ba tare da ya damu da jin abinda zata fada din ba, kuma tana ji yana cigaba da wasa da hannunta kafin yace.
“Bani na kashe Jamal ba Doll, ni na san bani na kashe shi ba don haka bayan abubuwa sun fara tafiya daidai sai na fara bincike akan wannan accident din, kuma sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutane biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tuƙin, da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ƙara sai kawai ta fashewar tayar.
Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin, ina living rayuwata ina kuma yin binciken don ban taba amma duk hanyar da na bi bata ɓullewa bana samun komai, kuma duk lokacin da hakan ya faru I felt emotionally high, sai ciwona ya tashi, sai inji komai ya tsaya, abu kadan yana bata min rai kuma idan ran nawa ya baci bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal.
Kuma abu daya ne kawai yake zuwa kaina cewa zan iya aika masa da sako, shi yasa duk wanda ya bata min rai, sai inji ina son in kashe shi kawai, in kashe shi in bashi sakon cewa ya gayawa Jamal abinda ya faru bani na kashe shi ba, this is crazy! I’m crazy na sani Amina, na san banbancina da mahaukaci a irin wannan lokacin bashi da yawa, amma wallahi hakan ne kaɗai abinda nake so shi yasa nake tunanin idan har na samo wanda suka yi abin nan watakila zan iya jin sauki a raina.”
Amina ta hadiye wani abu da bata san sunanshi ba a maƙogwaronta, tana jin yadda maganganun ke zagawa cikin kanta kowanne da tarin ma’anar da yake fitowa da ita, kowanne da nauyinsa kuma kowanne da tasirin da yake zama dashi a zuciyarta. Kuma bata sab lokacin da hawaye ya cika a idanunta ba sai zubuwarsa taji a gefen fuskarta.
“Wannan ciwon shine dalilin rabuwata da Rukayya, ta bata min rai a ranar da nima nawa ran yake a bace, so bana cikin hankalina sanda na karbi Hamida daga hannunta tana Baby lokacin nayi wulli da ita, ita kuma nayi mata dukan da ba don Allah ya kawo Ishaq a lokacin ba ban san me zai faru ba.
Ba zan ɓoye miki ba Amina, duk yadda nake jin zuciyata na sakewa dake wallahi ina tsoron ranar da ciwona zai iya tashi akan ki, shi yasa lokacin ayrenmu na aika miki da wannan takardar don ki fasa, bana son in sake abinda nayi tare da Rukayya …”
Ya kara kallonta sosai, yana kallon idanunta da suka cika da kwalla kafin ya ƙarasa.
“… Na yarda ƙaddarar haduwa dake itace bata sa na mutu ba tun a wancan lokacin, sabida haka idan har wani abu ya same ki ta dalilina yanzu, na tabbata wannan karon nima mutuwa zanyi, don ba zan taɓa iya sake wata rayuwa a duniyar nan ba idan har na kara sanadin rasa abu nsi muhimmanci irinki…”
Wadannan kalaman suka tada tsigar jikinta a lokaci guda, taji wani abu ya ratsa tun daga zuciyarta har zuwa bayanta. Sai kawai ta sake matso da kanta cikin jikinsa sosai, tana rike da fuskarsa har yanzu ta shiga girgiza kanta a jikin fuskarsa.
“Babu abinda zai sake faruwa, babu abinda zaka yi min Insha Allah, babu wanintashin hankalin da zai kara samunka, sauran da suka faru ma, sun faru ne saboda haka Allah ya tsara komai ya kasance, amma Allah ba zai kara kawo su cikin rayuwarmu ba insha Allah, all I care is that ba kai ka kashe Jamal ba kuma na san shima ya san hakan, da zai dawo nayi imanin zai gaya maka hakan, zai gaya maka cewa ya san ba laifinka bane.”
“Laifin waye Doll? Har yanzu na kasa gane laifin waye, ko zai dawo ɗin ta yaya zai yarda dani?…”
“Zaka sani insha Allah, nayi imanin idan ka cigaba da nema zaka sani, Allah ba azzalumin bawansa bane Ma’aruf, ya sani cewa ko su waye sun cuce ja kuma sun hargitsa rayuwarka, zai maka sakayya ta hanyar tona musu asiri insha Allah.”
Maganar ta fito tare da tahowar wani hawayen mai dumi daga idanunta, sai kawai ya sake sunkuyo da fuskarsa kan goshinta yayi kissing idanun nata duka biyu yayin da ta rufe su.
“Insha Allah Doll, fatan da nake yi kenan a kodayaushe.”
Wasu hawayen suka sake biyo bayan na baya suka fito masu ɗumin gaske. Abinda ta sani kawai a wannan lokacin shine idan har da sa hannun Hajiya Kilishi a mutuwar Jamal, to tabbas kuwa Ma’aruf ya kusa samun amsar sa.
***
*Ƙarfe tara da rabi.*
Tunda suka tashi take iya kokarinta wajen ganin tayi komai kamar yadda suka saba, yau asabar ce don haka ta san vabu inda zai je, wajen karfe takwas ta fito ta sake yin wanka sannan ta shiga aikinta, tana jiyo shi daga daki yana ta waya kuma bayan taje kai masa daya wayarsa da ya bari a falo wadda ake ta kira, ta ganshi ya fito da system har guda biyu yana ta faman dube-dube. Basu yi wata magana sosai ba amma yayi mata murmushi fiye da yadda zata kirga a iya safiyar kawai.
Ta kammala hada breakfast din tana dauraye kwanukan da tayi amfani dashi ne lokacin da ihun Hamida ya ziyarci kunnenta, ta tashi tana ta kiran sunan Mary.
Ta fahimci Mary ce ƴar aikinta da kullum suke tare, kuma takaicin da ya kasa barin zuciyarta shine na yadda sunan arniyar ya zauna a bakinta, ko mahaifiyarta bata kira sama da ita, yanzu ma ace yaro ya tashi daga bacci babu kiran sunan Allah sai wata arniya… Da sannu zata canja mata hakan a hankali.
Kuma ko da ta isa dakin har ta sauko daga gadon tana shirin fitowa, don a bakin kofa ta tarar da ita. Kuma cikin siga da dabararta sai da ta sa ta fadi addu’ar tashi daga bacci kafin su wuce zuwa bandaki inda tayi mata brush da wanka gabadaya.
Bayan sun fito ta shirya ta cikin wata ƴar doguwar rigarta mai kyau pink colour sannan suka fito falo,inda anan suka tarar da Ma’aruf har ya fito shima ya ɗebo kayan breakfast din da kansa zuwa falo ya zuba yana ci.
Yana ganinta ya fara bata hakuri cewa yunwa yake ji shi yasa ya kasa jiransu, Hamida ta makalkale shi tana gaya masa cewa tayi mafarki da Unicorn, wani shirmen mafarkinta irin cartoon din da kullum take gani.
Wannan lokacin yayi dadi a zuciyar Amina ba kadan ba, sai take ganin yadda yarinyar ta dada sawa gidan ya zama lively a tsakaninsu, har wayar Ma’aruf ɗin ta dauke lokacin da Faruk da wani Josh ke ta kira babu kakkautawa, sai da ya roƙe ta da Allah ya gaya mata cewar wani suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwanciyar nan da yayi na kwana biyu kawai sannan zancen ya dake ta da wani irin yanayi ta bashi wayoyin.
Ya fita zuwa barandar waje duk da suna jin dukkan abinda yake cewa, kuma ko kafin ya dawo Hamida tasa ta canja mata daga tashar CNN din da yake kallo zuwa Disney Junior dinta, ita kuma ta kwashe kayan nan zuwa kitchen ta shiga karasa wanke wankenta da bata gama ba.
A lokacin Ma’aruf ya shigo cikin kitchen din, ya karaso har inda take sannan ya rungumeta ta a hankali cikin hannayensa.
“Hey Angel.”
Ya faɗa a cikin wuyanta, a lokaci guda numfashinta ya katse a kirjinta kafin tayi kokarin saita kanta zuwa tambayar dake bakinta.
“Me yasa zaka fita yau weekend?”
Tayi tambayar don taji sanda yake gayawa Faruk cewa gashi nan zuwa. Taji yayi murmushi a cikin wuyan nata kafin ya lalubi daidai kunnenta yace a hankali.
“Saboda babu yadda zanyi Doll, dole ne muyi abin nan da gaggawa mu samo mutumin nan, babu wanda ya san abinda ya faru a kamfanin har yanzu, ni da Faruk da kuna Josh ne kawai, sai wadanxan mutanen daya kamfanin. Kuma bana son ayi dadewar da dole zancen zai fita balle har Baffa ya sani… Idan hakan ta faru rayuwata zata sake taɓuwa ne na sani.”
Tana jin yadda jikinta ke yi kamar ya kama da wuta, sannan tana jin murmushin da yake yi a jikinta alamun yana jin dadin rikita tan da yake yi, kuma kafin daya daga cikinsu ya sake cewa wani abu, sallamar Samirah da kuma Munaya daga falo ta shiga kunnensu.
Ba shiri tayi kokarin matsawa amma yaki sakinta.
“Su Samira ne suka zo…”
Ya gyada kansa.
“Naji su, me za’ayi?”
Ya tambaya da gaske, hannusa daya na kokarin kwance dankwalin kanta, babu shiri tasa nata hannun duka biyu ta damƙe shi sannan ta juyo tana kallonsa.
“You are busy ka manta kace fita zaka yi yanzu, suma kuma yanzu zasu shigo nema na har nan.”
Ya girgiza kansa yana ƙara jawo ta jikinsa.
“Na fasa, I want this busy yanzu more than anything.”
Ya fadi hakan idanunta na kan kofa don daga yadda take jin Samirah na kiran sunanta ta san yanzu zata shigo, sai kawai taji ya shiga kissing gefen kumatun ta yana jawo hankalinta daga kofar zuwa kansa.
“Dan Allah ka tafi kar su shigo.” Muryar ta ta fito kamar zata yi kuka.
Ya janye fuskarsa baya sannan murmushi mai kama da dariya kafin yace.
“Yanzu kike shirin roko na kar in fita yanzu kuma kina korata saboda waɗannan yaran, wai laifi muke yi ne ko me?”
Girgiza kai kawai take tana kallonsa cike da roko, kuma kafin ta iya cewa wani abun muryar Samirah ta doso kitchen din tana fadin.
“Matar gidan tana nan ne…”
Ai bata san lokacin da tasa dukkan karfinta ba ta fita daga hannun Ma’aruf ta dawo gaba ta tsaya da sauri tana kokarin daukan wasu kwalayen sugan data juye a jar ta bar kwalayen anan kan worktable din dake tsakiya, kuma kafin Samiran ta shigo tana jin sanda ya juyo shima ya sake tsayawa a daidai bayanta sannan kafin tayi tunanin komai ya sunkuyo daidai gefen kunnenta yace.
“Kina nufin in zuge miki zip din rigar? Dama wancan karon da na taya ki din nan kamar ba daidai muka yi ba ko?….”
Bakinta ya faɗi har ƙasa yayin da numfashinta ya dauke a lokaci guda, sai kawsi ya kyalkyale da wata dariya a hankali sannan yayi gaba ya wuce ta zuwa hanyar kofa, kuma sai da yaje daidai kofar sannan ya juyo yace.
“Na tafi inda kika kore ni, kiji dasu, amma akwai lokacin da bakin ki ma bai isa yayi magana ba.”
Yana fadin haka ya kifta mata idonsa daya yana murmushi sannan ya fita daidai lokacin da taji Samirah bna cewa.
“Ashe kaima kana nan Yaya…”
Sai kawai ta saki wani numfashi a hankali sannan bakinta ya tale da murmurshin da ta kasa tsaida shi.
***
*Karfe goma sha ɗaya.*
Ƙarar ƙwankwasa kofar ta karaɗe gidan gabadaya, Amina ta taho da sauri daga cikin daki inda ta bar Hamidah na ƙoƙarin taje girarta a gaban mudubi, yarinyar na son kwalliya da alama, don ko ɗazu da ta raka ta toilet tayi fitsari tana kallonta lokacin da take gyara hularta a jikin mudubin jikin sink.
Allah ya sani a yanzu tana jin son yarinyar nan yana ƙaruwa a cikin ranta, kwana biyu kawai amma duk sanda ta kalle ta da waɗannan idanun nata irin na Ma’aruf sak, sai taji wani abu na yawo a cikin ƙirjinta, don ita kanta yarinyar ta ƙara sakewa da ita sosai.
Tafiyarta a hankali saboda yadda take jin jikinta ta karaso bakin ƙofar, kuma haka kurum sai taji gabanta ya faɗi, taji farin cikin da ta tashi dashi a yau na yayewa, taji zuciyarta tayi fayau yayin da jikinta yayi shafal a lokaci guda kamar fallen takarda.
Sai kawai ta karanto hasbunallahu wa ni’imal wakil sau uku sannan ta bude kofar daidai lokacin da aka ƙara kwankwansawa.
Kuma a lokaci guda idanunta ya shiga na cikin Hajiya Kilishi dake tsaye a wajen.
***
“Me tace?”
Muryar Amma ta tambaya a cikin wayar da Amina ke yi awanni biyu bayan hakan. A hankali taji wani abu na zarcew cikin maƙogwaronta yayin da idonta ke kallon Hamida da tayi bacci a cinyarta.
Kalba take yi mata a cikin gashinta mai tsananin laushi amma kuma babu yawa, laushinsa ne kawai irin na Ma’aruf amma bai yo yawan nasa ba, saura guda daya su gama don haka ta daɗe da yin baccin don tun a farko tayi abinta.
“Me ya kawo ta Amina?”
Amman ta sake tambaya jin tayi shiru, tun dazu suke wayar, tun dazu Amman ta kira take shaida mata cewa ashe a airplane su Hafsa suka sa mata wayar tun jiya shi yasa bata same ta ba, kuma bayan ta kashe ta sake kira ne ta shiga zayyano en mata zuwan Hamida da kuma layar da ta gani a cikin kayanta.
“Kinyi daidai wajen ƙona layar,don nsyi imanin idan har ba da sunanki aka yi ba to da nasa ne, don da alama asirin kusa ne,sai yana tare da mai shi sannan zai ci, suna da tasu manufar tabbas, amma nafi danganta hakan da cewar kome take son taui ita mahaifiyar yarinyar, shi yasa suke son su jawo hankalinsa kanta ko kuma ke su kore ki, amma bamu da tabbas, don haka ki dage da addu’a, ki kuma cigaba da kiyaye dukkan wani abu a gidan.
Zasu zo, ni na tabbata zasu zo miki don asirin bai fara ci ba tukunna, ki zuba ido kawai ki saurari zuwansu, wannan matsalar mai sauki ce don nasu tunanin bashi da fadi don haka a lokaci kankani zaki gama dasu.
Amma yarinyar, ki cigaba da rike ta da wannan kulawar da na sanki da ita Amina, Kilishi ba zata kawo miki ita a banza ba amma tunda bata ce komai ba mu saurare ta tukunna, wanda kafin nan ki cigaba da rike ta da zuciya daya don wannan ba karamar kofa bace da zaki ƙara bude wata darajar taki a zuciyarsa, kar ki manta kullum ina gaya miki takamar kowacce mace a duniyar nan zuciyar mijinta ce, samun nasararki akan Kilishi dama duk wani abu da zai biyo baya ba zai kai darajar kyautata rayuwar aurenki ba.”
Da wannan suka kammala zancen Hamida da kuma batun layar nan, sannan Amman ta shiga bata labarin cewa Hajiya Kilishi ta turo da wasu mutane an dauki Baba da Aminu zuwa wajen da za’a fara musu fafutukar visa don kaishi asibiti a india kamar yadda ta shaida musu.
“Suna nan suna ta yabonta Amina, Babanku da ƴanuwansa har ma dasu Asma’u (ƙannenta) kowa yana ta sambarka, basu san cewar umarninki bane Amina, don wannan bashi da maraba da cewar umarnin hakan kika bata, umarnin da ita kanta bata sani ba.”
“Tazo ɗazu Amma.”
Kai tsaye bakinta ya fadi hakan, don a wannan lokacin ta kasa daurewa tarin hargitsin da kuma ruɗanin dake cikin kanta.
“Me tace?”
Sune kalmomi biyu da Amman ta furta wanda taji su a cikin ranta kamar baron da aka cika da ƙasa mai nauyi yake rike a hannunta kuma tana shirin hawa tudu dashi, don bata san ma ta inda zata fara ba, bata san ta inda zata fara dauko zancen ba, amma shirun wayar dake tafiya yana shaida mata jiran sauraren da Amma ke yi tasa ta hadiye abinda ke bakinta sannan tace.
“Akan Hamidan ne.”
Amma bata ce komai ba har ta ƙara haɗiye wani abun a cikin maƙogwaronta sannan ta cigaba.
“Kamar yadda kika fada tace bata kawo min ita a banza ba, bata tsallake kowa tace ni zan rike ta ba sai don tana da dalili, dalilinta kuma shine bata bukatar yarinyar ta zauna a cikakkiyar mutum, ta gaya min da farko tayi niyyar a kawar da ita ma gabadaya, amma kuma sai taga cewa gwara ta bar Ma’aruf da wani abu ko guda daya ne a rayuwarsa bayan ta tafi.
Bata gaya min inda zata je ba, amma tace daga ni har ita mun kusa barin rayuwar Ma’aruf don ta kusa kammala burin da ta shigo dashi gidan, burin da yasa tayi fafutukar auren Baffa tun a shekarun baya, don haka tace min ko bayan bata nan bata son ya zama akwai wani abu mafi soyuwa a rayuwar Ma’aruf sama da ita.
Tafi son ya zama zuciyarsa na tunawa da ita da matsayin da yafi na kowa a wajensa, don ta gaya min cewar tafiyar da zata yi ma zata tafi ne ba tare da sirrinta ɗaya ya fita ba, zata tafi ne ta barsu suna begenta har karshen rayuwarta don hakan shine babban burinta kuma ta riga ta tsara yadda zai kasance tuntuni, kawai tana jiran kammala cike abinda ke gabanta ne.
Don haka ta gaya min cewa tana so ta makantar da Hamida ne ta kuma gurgunta ta ta yadda ba Ma’aruf kadai ba, babu wani mahaluki da zai kalle ta da daraja a duniyar nan kuma zata yi haka ne ta hanyata, ta gaya min da hannu na zanyi hakan Amma.”
Muryarta ta kai ƙarshe da tsananin rawar da take fitowa kamar kuka ne ke shirin kwace mata,amma kuma duk da haka sai taji kamar ta ɗauke wani dutse ne daga kirjinta, nauyin maganganun da ta furta na barinta kamar yadda iska ke ɗiban yashi.
Kuma shirun da ya ratsa a cikin wayar, mai tsawo ne, tsawon da ba zata iya tantance shi ba don har sai da Hamida ta motsa a cinyarta ta gyara kwanciyar ta, daga bangaren layin gidan wayar kuwa, ta san bakinsu na ta washewa na ganin adadin cinikin da suke yi dasu, kuma abinda Amman ta furta bayan tsawon wannan lokacin shine.
“Alkawarin me tayi miki wannan karon?”
Ta shaki wata busashshiyar iska a cikin hancinta kafin tace.
“Na’am Amma?” Alamun bata gane ba.
“Alkawarin me tayi miki idan har hakan ya cika?”
Ta gane yanzu, amma bata gane me yasa shine abu na farko da Amman ta tambaya ba, amma duk da haka sai ta hadiye mamakinta sannan muryarta ta fito.
“Tace zata canja muku gida sannan ke da Baba zaku je aikin hajji wannan shekarar.”
Sai kawai ta jiyo murmushin Amman kafin tace.
“Ashe ina da rabo a wadanda Allah ya kira zuwa dakinsa wannan shekarar Amina.”
“Amma ban gane ba…”
“Kar ki damu zaki gane komai Amina, abinda zan gaya miki a yanzu kawai shine cewa babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!”
“Amma…”
“Kar ki ce komai a yanzu, bar ni kawai da tunani na har zuwa lokacin da zata kawo miki umarnin farko na abinda zaki yi. Yanzu ki gaya min ta tambaye ki wani abu game dashi a yau din?”
Amina ta haɗiye tarin kalamai da kuma rudanin da bata san adadinsu ba a cikin kanta sanin cewa tunda Amman ta faɗi haka babu wani bayanin da zata kara samu daga Amman a yanzu. Kuma abinda ta fada yanzu ta san shi din da take nufi Ma’aruf be, don bata taba kiran sunansa saboda haka sai kawai ta ɗaga kanta kamar tana kallonta sannan tace.
“Eh ta tambaye ni inda ya tafi kasancewar yau asabar.”
“Sai kuma me?”
“Na gaya mata cewar suna bincike ne shi da abokin aikinsa game da wani abu da ya faru a kamfanin su.”
“Me ya faru?”
“Yace min wani mutumi suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwaciyar nan da yayi na kwana biyu kawai.”
Murmushin da Amma tayi wannan karon ya amsa sosai a vikin kunnen Amina kafin tace.
“Kin fahimta? Kin fahimci wannan ne aikin da Kilishi tace miki tana son yi a wajen aikinsa wanda tace miki bata bukatarsa a sannan?”
Ta gyada kanta da sauri.
“Na gane Amma nima na fahimta, shi yasa da ta tambaye ni na gaya mata gaskiya din nsji abinda zata ce, amma kuma abinda ta fada din ban gane masa ba.”
“Me tace?”
Ta sake maimaita kalma biyun nan na ɗazu. Amina ta gyara zaman wayar zuwa ɗaya kunnenta kafin tace.
“Dariya kawai tayi, tace wai ai da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba, kuma sai da nayi tunanin sannan na gano cewa wajenta take nufi tunda ba zata taba faɗa ba.”
Amma ta sake yin shiru na wucewar wasu lokutan kafin muryarta ta sake fitowa.
“Me suka samo su game da mutumin?”
“Ban sani ba dai duka amma naji kamar suna waya da wani yana gaya masa cewa an kwatanta musu siffarsa ne kawai”
“Bani minti biyar, ina zuwa Amina.”
Abinda ta fada kenan sannan ta kashe wayar ba tare da ta jira komai ba.
Amina ta rike wayar a hannunta, tana sake niya dukkan maganganun nasu kafin a hankali kuma tunaninta ya tsaya kan abu guda daya da bata shaidawa Amman, wannan abun da tun a farko ta boye mata na zancen cewa Kilishi bata yarda da wani zance na samun ciki a wajenta ba, a yau ma ta sake maimaita mata cewar ta cigaba da yin taka tsantsan da zuciyarta akan Ma’aruf, ta kawo ta ne don tayi mata aiki ba don ta zama matarsa ba.
Kalaman da suka kara sata jin wani abu na sauka a zuciyarta yana kara gaya mata cewa wannan yakinta ne, ta ƙyale Amma a ciki ta nunawa Kilishi nata kalar kissar da lulluɓin da bata isa ta yaye ba.
Da wannan tunanin, zuciyarta ta koma wajen jiran da Amman tace tayi, fiye da komai zata so su fara samun mafita kamar yadda tayi alkawari wa rayuwar Ma’aruf, komai ya tsaya cak akanta, hatta hanyenta dake rawa a yanzu sun daina, ta kasa ko sake taba kan Hamida balle ta karasa kalbar dake jiranta, jira kawai take yi yayin da idanunta kallon wucewar lokaci a agogon wayar.
Minti goma bayan hakan wayar ta shiga gurzawa a hannunta da ƙarfin vibration din dake jikinta, kuma ba tare da ta jira komai ba, ta danna wajen amsa kira ta kara ta a kunnenta.
“Amina…”
Muryar Amman ta fito da wani irin yanayi da ta kasa fassara shi.
“Na’am..” ta amsa a hankali tana jin yadda nauyin da take murna da tafiyarsa a ɗazu ya sake dawowa kan ƙirjinta kafin kalaman Amma su fito da tasirin da yasa komai tsaya cak a cikin kanta.
“Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
