Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Mammy bata ce wajenki zan zo ba…”
    Hamida ta faɗa tana kallon Amina dake gabanta, tashinta kenan daga bacci kuma sai da Aminan ta sha faman tambaya kala-kala kafin ta samu a yanzu tayi maganar. Maganar da a lokaci guda tasa Amina yin murmushi don in har ce wani abu to komai zai zo da sauki, saboda haka ta gyada kanta a hankali tana murmushin sannan tace.
    “Na sani, wajen Daddy tace zaki zo ko?”
    Sai ta gyaɗa kanta alamun ta ƙara warewa daga baccin da ta tashi.
    “Daddy ya fita yanzu Hamida, amma zai dawo anjima kadan kinji.”
    Bata ce komai ba ta cigaba da kallonta kawai, sai tace.
    “Zaki ci abinci kafin ya dawo?”
    Yanayin idonta ya canja da cewar maganar tayi tasiri akanta amma duk da haja sai da taji ta sake tambaya tukunna sannan ta daga kanta a hankali.
    “To taso muje a wanke fuska tukunna tunda daga bacci kika tashi ko?”
    Wannan karon a lokaci daya ta gyada kai sannan ta miko mata duka hannayenta biyu alamun ta dauke ta, Amina ta sake yin murmushi ganin hakan kafin ta mika hannu itama ta ɗauke ta a jikinta.
    Kamshin turaren ta mai daɗi ya shiga hancinta a take, daga gani tabbas tana samun kulawa don haka tunanin dalilin da yasa suka kawo ta kamar yadda su Ma’aryf keyi ya ɗarsu a ranta, suka shiga toilet din dakin har a lokacin kallonta kawai Hamida take yi.
    Ta ajiye ta a kasa tana fadin bari adebo ruwan kafin ta samo dauko kofin dibam ruwa ta taro mai dumi kadan daga fanfon. Ta tsugunna a gabanta har ysnzu tana murmushi tace.
    “Muyi wasan ruwa?”
    Ga mamakinta sai ta girgiza kai.
    “Mariya tace babu kyau wasan ruwa.”
    Sai murmushinta ya karu tana daga kai tace.
    “Good, ashe kina da ƙawa mai hankali.”
    “Mariya tsohuwa ce, ba ƙawata bace”
    Sai da Amina ta dan tsaya kafin tace.
    “Babba ce?”
    Ta gyda kai tana cigaba da kallonta. Sai ta girgiza kanta.
    “Ba sunanta Mariya ba ai Hamida.”
    Alamun mamaki da kuma tsoron laifi suka nuna fuskarta kafin tace.
    “To ai haka su Mammy ke ce mata.”
    Amina ta sake girgiza kanta.
    “Su Mami sun manta ne amma Mama Mariya sunanta, watakila ma idan kinyi bacci suna fada baki sani bane kawai.”
    Bata ce komai ba, sai ta kara yin wani murmushin da tace.
    “Tana da ƴan yara ksmar kibharda mnya ma kamar su Mammmy da ni kinga ai ta zana Mama ko?”
    Sai ta gyada kanta a hankali alamun ta gane amma bata ce komai ba, Amina tayi murmushi ta wanke mata fuskar sannan suka taho kitchen, acan yna ta dinga janta da ƴar hira a hankali har sai da ta fahimci ta dan fara sakewa da ita, duk da cewa tana ta tambayar inda Ma’aruf ya tafi da kuma lokacin dawowarsa, har Surayya da ta kawo ta ta tambaya tace mata itama zata dawo.
    Ma’aruf ya fita a ɗazu ne bayan yasa Faruk ya turo masa da direba yazo ya dauke shi da motar Oficce kuma duk kawaicinta sai da taui kokarin nuna masa cewa bai dace ya fitan ba saboda yanayin jikinsa, amma ya gaya mata cewar fitar tasa ta zama dole ne don abinda Faruk din ya samo, wani abu ne da a yadda yake jin kansa ya san ba zai iya barin kansa bai fita ba, sannan kuma du Baffa ma zasu dawo a yau, wanda ka’ida duk sanda suka yi tafiya doguwa irin wannan da sun dawo a kamfanin suke fara sauka tukunna kafin gida.
    Don haka babu yadda ta iya dashi haka ya shirya ya fitan, bayan ya roke ta da Allah cewar tayi masa tuwo da miyar wake, don haka aikin da take tayi kenan yayin da Hamida ke zaune tana cin abincinta da kuma tea din da ta hada mata.
    “Kema Daddyna daddynki ne?”
    Taji ta tambaya lokacin da take kokarin wanke naman da ta fito dashi daga fridge, ta juyo ta kalle ta da murmurshi sannann ta ɗaga mata kai, amma sai Hamidan ta kara haɗe ranta.
    “Ni bana son inyi sharing Daddyna da ke.”
    Murmushin ta ya karu sosai don maganar ta bata dariya, sai ta gyada ksnta sannan tace.
    “Toh shikenan na bar miki Daddynki ke kadai, ni zan dinga dafa muku abinci kawai kuna ci ko?”
    Ta daga kanta da sauri a jere alamun ta yarda sannan tace.
    “Kuma ki dinga min English, Mammy tace bata so bana yi.”
    “Insha Allah Princess.”
    Yadda ta fadi hakan kai tsaye kuma ta kira ta da Princess yasa karo na farko Hamidan ta danyi murmushi itama sannan ta juya ta cigaba da cin abinta, itama ta koma aikin ta. Bayan ta wanke naman ta dora, ta sake duba tukunyar farar shinkafar da tayi ƙal a cikin tukunyar kafin ta rufe ta ɗauko wayarta.
    Kamar yadda take ta gwadawa tun safe, nambar Amma ta kara dannawa amma ssi bata shiga, Allah yaso ta kira Babba dazu sin gaisa yace mata watar ba caji ne amma ya baro zata bawa Maryam ta kai mata, don haka ta tabbatar ba’a karbo ba kenan, ga shi ta fatima ma ta samu matsala da ta kira ta ita suyi magana da Amma tana nan.
    Idonta ya kara kallon wayar, sabuwa ce dal kirar Samsung don ɗazun nan kafin fitar wani mai delivery ya kawo su guda biyu, ya dauki daya ya bata daya sannan ya karɓi tsohuwar ta hannuta wadda ya fita da ita, don sabuwar ma tana ɗaki yace sai ya fara yin welcome back na sauran layikan nasa tukunna, kuma kyan wayar yasa take ganin har yanzu kamar ba tata bace.
    Ta maida ita jikin caji wanda ta jona a kitchen din sannan ta cigaba da aikinta, tana yi tana juyawa tana kallon Hamida dake cin abincin har yanzu a hankali, kamar ba zata ci ba… Har tean ta san ya gama yin sanyi yanzu, a ranta ta kudirce cewa zata gyara wannan cin abincin nata.
    “Finished.”
    Taji muryarta lokacin da take tuka tuwon, ta juyo ta kalle ta, ta dora habarta akan table din ta harde hannayenta daga kasa kuma tana shilla kafafunta, haka kurum ranta yayi daɗi ganin plate ɗin babu komai ta cinye.
    “A taimake ni da plate din a cikin sink Princess din Daddy.”
    Ta kalle ta alamun bata gane me tace ba sai tayi murmushi tace.
    “Ki kai min su plate din cikin sink Princess din Daddy.”
    Watakila sunan ne kawai yayi mata dadi, don kamar bata yi niyya ba sai ta mike a hankli ta dauki kofin da kuma plate din, da taje wajen sink din sai da tayi dage sannan ta iya cilla su a ciki.
    Amina tayi murmushi sannan ta juya ta cigaba da aikinta, ƙasa da minti daya bayan ƙarar da Hamida ta ƙwalla ta cika koina a gidan, bata san lokacin da ta saki tuwon ba ta juyo.
    Daga can karshen kitchen din ta ganta a tsaye, rike da wani dan karamin bowl da ta zuba soyayyen msnjan da ta rage a ciki.
    “Mammy jini, Mary! Mary!”
    Amina bata san wa take kira ba ta karaso ta karbi bowl din sannan ta shiga ƙoƙarin kwantar da hankalinta tana gaya mata cewar ba jini bane, mai ne kawai, amma ko kadan ba saurararta take yi ba, don haka ta dauke ta gabadaya kawai suka yi toilet.
    Ta cire mata kayan ta ajiye su a sink sannan ta saka ruwan dumi ta shiga dauraye wajen da manjan ya taba ta, daga baya ma sai suka yi wanka kawai gabadaya, kuma ba su fito daga toile din ba sai da Hamida tana kyalkyala dariya saboda yadda ta dinga tsokanarta da ruwan fanfon shower.
    Kuma a lokacin da suka fito ne abin ya faru, a lokacin da ta ɗauko jakarta don samo mata wasu kayan, ta dauko su har ma ta sanya mata, gyara su kawai take yi zuciyarta na kiyasin adadinsu da tunanin dama sun kawo ta ne da niyyar zama lokacin da idonta ya kai kan wata bakar leda a can kasan kayan, har zata maida su sai taji cewa bari taga meye a ciki.
    Hannunta ya ɗauko ta yayin da ta saki duka sauran kayan, ta taɓa wani abu kamar kwalba a ciki don haka ta zaro ta yi a hankali, kwalbar ce kuwa ƴar karama, baƙa kamar ta turare, ta kalli Hamida a lokaci guda da taji zuciyarta ta buga.
    “Turarenki ne?”
    Yarinyar ta girgiza mata kai itama tana kallon kwalbar, sai kawai tayi tunanin budewa taji wane iri ne sai dai tana taba kan taji ya ɓalle, idonta ya leka ciki, yana tabbatar mata da cewar ba turaren ne a ciki ba wani farin abu ne kamar takarda, ta tsaya tana wani tunani na sakanni kafin tace da Hamidan.
    “Bari naje na dawo, ki zauna anan.”
    “Inyi kwalliya?”
    Muryarta ta tambaya tana mikewa, idonta ya kai kan dressing mirror da take nunawa, sai kawai ta dawo ta dauke dukkan abinda ta san zata iya ɓata jikinta dashi tasa a drawer ƙasa ta ƙulle sannan tace mata tayi
    Can waje ta fita bayan kitchen ɗin nan sannan ta ɗauko intelock guda daya a gefe ta fasa kwalbar da shi, kuma abinda ta gani shi yasa a lokaci guda zuciyarta ta shiga rawa tun kafin hannayenta su fara yi…
    Laya ce… Laya fara ƙal!
    An nannade ta gabdaya da farin zare!
    ***
    *Bayan Magriba.*
    M’aruf bai san iya mintunan daya kwashe kofar dakin yana kallonsu ba, gabadayansu sun juya masa baya ne yayin da suke jera kayan Hamida da suka baje a dakin cikin wardrobe din dashi take kallo daga inda tsaye.
    Ya gaji, gajiyar da har da rashin komawar jikinsa daidai, amma duk da haka yaji yana son ya cigaba da tsayawa a wannan wajen har zuwa karshen inda lokaci zai kai su. Wani irin abu mai dumi yake ji yana bi cikin jijiyoyinsa gabadaya, tun daga farkonsu har karshe.
    Tun daga ranar da ya fara ganin Hamida yana jin wani irin abu yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar dake sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake
    ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A yanzu kuma da hotonta ya hadu dana Amina a gefenta, sai yaji komai yana ninkuwa, adadin komai ɗin na karuwa a cikin ransa da yawan da bai san ta yadda zai fassara shi ba.
    A lokacin da yake tare da Rukayya, lokacin da Hamida tana ƴar ƙarama, baya jin ranakun da ya dawo ya ganta a hannunta zasu wuce kirgensa, kullum zata ce masa tana wajen mai aikinta sai dai in a karbo masa ita daga baya, don haka a yanzu bai san da wane sikeli za’a iya auna abinda yake ji a zuciyarsa ba.
    Ya yarda har cikin ransa cewar cikar kowannen namiji yana karkashin kulawar mace ta gari! A yau kadai, sa maganar da yayi mata kadai, ta karbi Hamida cikin rayuwarta gashi tun ba’aje ko’ina ba alamu sun nuna masa cewar ita kanta yarinyar ta fara sakin jikinta da ita.
    “Wannan da wannan da wannan Uncle Jawad ne ya siyo min.”
    Hamida ta faɗa tana nuna wasu kaya har da wanda Aminan ke sakawa a wardrobe din.
    “Wanene Uncle Jawad?” Muryarta ta tambaya a hankali, wannan muryar tata mai taushi. Sai yarinyar ta girgiza kanta.
    “Kawai wajen Mammy yake zuwa.”
    Sai Aminan ta gyada kai sannan tace.
    “Allah ya saka masa da alkhairi.”
    Shirun da Hamidan tayi yasa ta juyo ta kalle ta.
    “Baki ce Amin ba.”
    Sai da ta sake wani shirun sannan tace.
    “Ameen.”
    “Yawwa Princess din Daddy.”
    Idanunsa suka sake tsayawa akan Amina da kuma murmushin fuskarta. Ta canja kayanta zuwa wata riga ƴar kanti kalar yellow, a zaune take don haka bai san tsawon rigar ba, amma kalarta ta haska wajen gabaɗaya kamar ranar dake kwallewa a sama, babu dankwali akanta sai wannan gashin nata mai laushi data daure karshen sa da katon ribbon baƙi. Kuma bai sani ba ko hasashensa ne kawai, amma daga inda yake kadai yana jin kamshin turarenta irin wanda yaji a jikinta da safe.
    Ta saka kwalli a idanunta wanda ya fito raɗau ya fito da kamanninta yana haska fuskarta da tayi fayau a cikin hasken ɗakin, shi kansa bai san tasirin da shigar tata tayina ransa ba, ga san dai kawai numfashinsa ya kara yin nauyi a kirjinsa yayin da yaji wani abu kamar gumi na tstsafowa daga tafin hannunsa, sai dai kafin yayi wani tunanin ta juyo ta kalle shi, idanunta suka sauka akansa, gashin samansu mai tsawo har yana tabo girarta, lebbenta ya tale da murmurshin da yaji kamar yana narka zuciyarsa.
    Sai dai kafin yace wani abu ko ita tace, Hamida ta juyo ta kalle shi, kuma a lokaci guda ta taso da gudu ta taho tana fadin .
    “Daddy!”
    Sai ya rasa wanne a cikin biyun nan zai dauka ya bawa alhakin narkewar zuciyar tasa, ya san dai kawai a wannan lokacin ya manta dukkan bayanan da ya tattaro a cikin kansa na Office ya karbi abinda lokaci ya bashi, saboda haka sai kawai yayi ƙasa ya durƙushe akan gwiyoyinsa yayin da Hamida ta karaso da sauri ta shige cikin hannayensa.
    Amina ta miƙe tsaye a hankali, tana kallonsu, kuma a lokacin ne idon Ma’aruf ya sauka akan ƙarshen rigar, iya gwiwa ce… Ya salam!
    “Kin tashi daga baccin Baby girl?.”
    Ya kira ta da sunan da yake gaya mata tun a creche din nan wanda ya sata murmushi.
    “Har tea na sha ma da chips.”
    “Really? Kince kinyi karfi kenan.”
    Ya faɗa suna mikewa tsaye, ta kyalkyale da dariya tana ɗaga masa kai. Amina ta matso gabansu kadan.
    “Sannu da zuwa, ya aikin?”
    Ta faɗa muryarta na saukowa kamar wani fiffiken dake saukowa kasa a hankali yayin da Idanunta ke kallonsu da nata kalar sha’awar da bata san da ita ba.
    “It was fine, ba laifi an samu abinda ake so.”
    Ta gyaɗa kanta.
    “Alhmdlilah.”
    Sai kawai ya kasa daurewa zuciyarsa yace.
    “You look breathtaking Doll, kamar idan na kalle ki da yawa zan daina numfashi.”
    Da dan guntun murmushi a lebbanta ta cigaba da kallonsa, ya gyaɗa mata kai yayin da Hamida ta juyo tana kallonsu. Wani abu yake ji a lokacin kamar wuta ya harba daga tsakiyar bayansa zuwa kafafunsa, yaji yana so ya rungume ta kamar yadda yayi wa Hamidan, kuma kai tsaye zai iya yin hakan amma bai san yaya zata karbi hakan ba a yanzu.
    Ta juya ta koma can wajen wardrobe din rike da rigar nan a hannunta sanda Hamida ke cewa.
    “Daddy, wannan Auntyn tace ta bar min kai ba zamu yi sharing ba, kawai zata dinga dafa mana abinci.”
    “Haba dai?” Ya tambaya da sauri da kuma alamun mamaki, sai kuma yace.
    “Wasa take miki, kice wasa kike mata dan Allah Doll.
    Yadda muryarsa ta fito, yadda amonsa ya furta wannan sunan da kuma taushin muryar tasa ya taba har fatar kunnenta ba ma can ciki ba, ta juyo ta kalle shi tana dariya kuma kafin shi da ita su sake cewa komai, Hamida tace.
    “Sunanta Doll?”
    Ya gyada kansa yana cigaba da kallon ta.
    “Eh mana amma ba wanda kika sani ba, wannan special one ne.”
    Sai ta gyada kanta itama alamun ta gane kuma daga wannan ta shiga tambayarsa yaushe zai sake maida ita wannan creche din da ya ɗauko ta, tana gaya masa cewa su je kitchen taga irin bowl ɗin da ake zuba mata abinci a creche din, kuma da haka ta ja shi suka bar dakin tana ji taba gaya masa cewa wai jini ne a cikin bowl din har ya bata mata kaya.
    Sai ta hadiye wani abu da bata san sunansa ba a maƙogwaronta, har yanzu ta kasa samun Amma a waya, Allah-Allah kawai take anjima tayi ta kira Baba idan ya koma gida, don duk da ta ƙona wannan layar dazu a bayan fulawoyin gidan har yanzu hankalinta bai kwanta ba, har yanzu zuciyarta bata nutsu ba.
    Ta zazzage dukkan kayan Hamidan yafi sau biyar tana sakewa, tun tana tambayarta me take nema har ta gaji ta tsaya tana kallonta kawai, sai da ta gaji ta tabbatar babu wani abu da ta sake gani sannan ta zauna suka shiga ninke su suna saka su a kasan drawer.
    A yanzu ta riga ta sami amsar da kowa bai sani ba, ta gane dalilin da yasa suka kawo yarinyar haka kwatsam bayan faruwar komai, akwai wani abu da suke son cimma ne wanda bata san takamaimai asirin akan waye ba, amma duk da haka bata jin cewa ya dace ta sanar da Ma’aruf tun a yanzu, shi yasa take son samun Amma a waya ta shaida mata komai don ta san yadda zata ɓullo musu suma, don ta yarda idan har zasu yi yunkurin cin galaba akan Kilishi to wannan ma ba komai bane, kawai tsoronta shine kar ya zamo da wani abin da bata sanshi ba ko kuma bata yi daidai ba wajen ƙona layar nan.
    Lokacin da ta gama ta koma falon, Hamida na zaune ita kadai tana kallo, don haka ta fahimci Ma’aruf yana dakinsa kenan, sai kawai ta koma kitchen ta debo dukkan kayan abincin data hada ta fito dasu falon, Hamida tace ba zata ci tuwon nan ba, don haka tayi mata wata ƴar jollof din taliya da kifi. Kuma tana miko mata ta karba ta fara ci,ta fahimci yarinyar tana son abinci kawai dai bata iya ci da sauri bane.
    Sai dai tana fara ci din tace a cire mata ƙayar kifin, don haka ta bar sake kokarin kiran su Amman da take yi tazo ta zauna daga gefenta a kujera tana kokarin cire mata ƙayar tsakiya na kifin da fork din da take ci. Kuma a lokacin ne Ma’aruf ya fito, ya canja zuwa wata gogaggiyar jalallabiya kalar milk data fito da ɗan hasken fatarsa kadan, yayi fresh din da ba sai yayi bayanin daga wanka yake ba, amma duk da haka Hamida ta tambaya.
    “Kayi wankan?”
    “Yes, nayi wanka.”
    Ya amsa yaba tahowa idonsa akan kafafunta da ta rasa me yake gani a jikinsu yake kallo, jallon da yasa zuciyarta tayi fayau a kirjinta.
    Ya ƙaraso a hankali ya tsugunna a daidai gabanta hannunsa riƙe da wani abu da bata gani sosai ba, kuma tun kafin yace wani abu Hamida ta sake fadin.
    “Daddy naku tuwo ne kai da Auntyn, ni bana ci shi yasa nake cin wannan.”
    “For real?”
    Ya dawo da ganinsa kan Aminan, don shi har ga Allah ya manta da zancen tuwon da yayi.
    “Da gaske na samu tuwon nan?”
    Tana murmushin yadda yake tambayar ta gyada masa kai, sai ya zura hannunsa daya a cikin gashinsa yana kallonta ba tare da yace komai ba.
    Sai kawai tayi murmushi ta mike zuwa wajen da ta ajiye food flasks din tana gaya masa cewa har da na dumame ma duk zai samu, yayin da Hamidan ta shiga tambayar meye ɗumamen.
    “Eeeewwwww!” Ta fada da karfi bayan Ma’aruf yayi mata bayanin.
    Suka yi dariya dukkansu kafin Ma’aruf ya taso zuwa wajen da take zuba masa abincin, kamshin miyar ya ratsa hancinsa yana yaba girkin tun kafin ya kai bakinsa don ko daga yadda miyar bata yi mai sosai ba ma hakan ya burge shi, kamar ta san yadda yake son komai.
    Ya tankwashe ƙafafunsa a gabanta yana kallonta yana kallon yadda take zuba miyar, yadda take komai… Allah ya sani baya jin gar ya bar duniya zai taba manta wannan alkhairin na Mami na kawo masa Amina cikin rayuwarsa.
    Wannan wani alkhairi ne da yake tunanin har a kabarinsa zai tuna shi.
    ****
    “Ƙarfe tara da rabi.*
    Hamida tayi bacci a lokacin, kuma har a sannan Amina bata sami damar samun su Amma ba don wayar Baban shima bata shiga yanzu.
    Ma’aruf ya shiga cikin gida wajen Baffa, kusan awa guda kenan, tun daga masallacin isha’i yace mata zai wuce. Ya gama cin abincin yayi santi kala-kala da tun tana daurewa har ta dinga dariyarta a fili, kuma bayan hakan ya gode mata lokacin da ta kwashe kayan zuwa kitchen.
    A cikin kunnenta ya dinga raɗa wasu abubuwa da ita kanta idan ta tuna yanzu sai ta runtse idonta don kunya, Ba wai maza ta sani sosai ba amma ta yarda Ma’aruf daban ne, shi da kansa yau ya gaya mata cewar baya ji, kuma itama ta yarda da hakan.
    Babu wanda zai yarda zai aikata dukkan abubuwan da yake yi, idan ka ganshi a fuska very responsible and so stiff akan dukkan abinda ya yanke, amma yafi kowa sanin tarin hanyoyin da zai ruɗa mace a lokaci guda.
    Kamar kullum wajen da ya riƙe ta har yanzu tana jin kamar shatin yatsunsa a wajen, kamar lokacin da ya riƙe ta yatsunsa sun ƙona wajen ne sai a yanzu iska ke kaɗawa tana son dawo da fatar tata daidai.
    Ta ajiye abin sallar da ta idar da isha’i a lokacin, gyaran kitchen din da tayi ta kuma tsaya yiwa Hamida Brush da canja mata kaya tana gyangyadi shi ya cinye lokacinta sai yanzu ta samu na sallar.
    Ta tafi zuwa gaban mudubi ta dauko wani kwando tana kwashe dukkan abinda ta san Hamida zata iya sawa a ido ko ta bata jikinta dashi, tana yi tana yabawa kanta yadda tayi kokari wajen kula da yarinyar da kuma sawa ta sake a gidan ysu daya kawai, Surayya na cewa sati guda, idan ta shigo gobe zata sha mamaki.
    A lokacin ne kuma kofar dakin ta bude, ta dago da idonta ta cikin mudubin tana kallon Ma’aruf din da ya shigo, fuskarta ta haska da murmushi tana masa sannu da zuwa.
    Ya karaso a hankali yana zuwa inda take, kuma ba tare da ya jira komai ba ya rungumeta ta baya, kansa ya sauka a gefe wuyanta sannan ya karkato da kansa gefe yayi kissing kumatun ta kafin yace.
    “Har guda nawa zan dinga samun wannan sannu da zuwan ne?”
    Tayi kokarin tsaida numfashinta a hankali.
    “Duk lokacin da ka fita ka dawo, kana da guda daya?”
    Sai ya gyada kansa sannan ya ƙara karkata shi zuwa cikin wuyan nata, ba shiri ta damke kwandon nan dake gaban mudubin, tana jin kamar wannan karon kusan tayi yawa.
    “Yaya jikin naka?”
    Ta tambaya a hankali don ji take yi kamar har yanzu da ɗumi a jikin nasa. Yayi shiru jamar ba zai amsa ba tsawon wucewar sakanni sannan yace.
    “I’m sorry Doll.”
    Mamaki ya dan kamata.
    “Na me?” Ta tambaya.
    Sai kawai ya mike tsaye sosai ya juyo da ita tana fuskantarsa, sannan yace.
    “Sorry da nake saki damuwa akaina.”
    Ya sunkuyo a hankali ya sake kissing daya gefen fuskar tata sanan ya sake cewa.
    “Sorry da zuwan Hamida.”
    Ya sake kissing gefen bakinta.
    “Sorry da dukkan flaws din da kika zo kika tarar a rayuwata.”
    Wannan karon saman bakinta ya sake kissing sannan ya ɗan matsar da fuskarsa baya kaɗan yana kallon idanunta yace a hankali.
    “Sorry da na bata miki dukkan rayuwar da kike tunanin zaki samu idan kinyi aure…”
    Kafin ya ƙarasa, kafin ya sake cewa wani abu tasa hannunta da sauri ta rufe bakinsa sannan ta girgiza kanta.
    “You don’t have to be… Babu abinda na taba tsarawa a rayuwata a wannan stage din, babu wani hasashe da na taba yi, so dukkan abinda ke faruwa a yanzu shine duniyata kuma shine fantasy dina.”
    Ya rike hannunta da ta rufe bakin nasa dashi, yayi kissing cikin tafin hannun nata kafin ya janye shi a hankali.
    “Ban gane ba Amina, ki kara yi min bayani sosai.”
    Sunanta da ya fito daga bakinsa da kuma yadda sautin muryarsa yake yasa jikinta yin rawa kadan, ta hadiye wani abu a makogwaronta har yanzu tana kallonsa sannan bakin ta ya furta.
    “Ma’aruf Mansour Bakori, kai ne duniyata kuma kaine duk wani fantasy dina a yanzu, I really love you so much and I mean it.”
    Kuma da haka bata jira komai ba ta kara tsawon kafafunta tayi kissing gefen bakinsa kamar yadda yayi mata dazu,da farko bai ko yi motsi ba, yana tsaye ne kawai kamar baya numfashin amma tana kokarin maida kafafunta ta koma taji ya furta kalma guda biyu rak!
    “Ya salam!”
    Kuma da haka bai jira komai ba yasa duka hannunsa biyu ya jawo ta jikinsa.
    “I love you.” Muryarta ta kara fada a fuskarsa, yayin da a cikin zuciyarta take mika dimbin godiya ga mahallicinta jalla wata’ala daya kyautata rayuwar ta da mutum kamar Ma’aruf.
    Kafin tayi tunanin komai, hasken dakin ya tafi gabadaya, kuma daga wannan gaɓar bata ƙara gane komai ba, abinda ta sani kawai shine ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa da yardar ubangiji daga wannan lokacin, Ma’aruf ya daina sanin wani ɓacin rai a rayuwarsa sai dai idan har abu yafi ƙarfinta.
    Dukkan wadannan matsalolin da yake fuskanta da sannu zata buɗe masa su daya bayan daya, don in dai har a wajen Hajiya Kilishi matsalar take, tayi imanin zata warware masa su ne hankali kwance ba tare da ita kanta Kilishin ta fahimta ba kamar yadda Amma ta gaya mata a wayar da suka yi ta ƙarshe.
    _”Mun riga mun gama haddace dukkkan wani takun matar nan Amina, don haka dasu zamu yi amfani daya bayan daya wajen kassara ta, ba zata taba tunani ba, ba zata taɓa hange ba saboda tana da yaƙinin hakan tunaninta ne ita kadai kuma saboda mun saka mata imanin cewa ke baiwarta ce, baki da wata mafita ko dabara sai tata kawai!”_
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!