Farar Huta 2 – Chapter Seven
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“A hankali zaki kwantar da ita ta gefe.”
Amina ta faɗa lokacin da Surayya ke kokarin kwantar da Hamida da tayi baci a jikinta kan gadon a hankali.
Surayan ta sunkuyo tana kokarin ajiye ta dadai inda Amina ta sake shimfida bargo da ta ninke gida hudu akan gadon.
“Kar ki sake ta sai ta taɓa gadon.”
Amina ta sake faɗa a hankali lokacin da ta kai ƙarshe da ita kuma a hankalin Surayya ta ajiye ta sosai akan bargon sannan ta zare jikinta da kadan kadan, da farko Hamidan tayi kamar zata tashi amma kuma sai ta koma ta kwanta alamun baccin ya dauke ta da karfi, Amina ta karaso rike da wani farin mayafinta dan karami ta rufa mata a jikinta, suna kallo su duka biyun har fuskarta ta saki jikinta sosai akan bargon.
“Kar ki damu insha Allah ba abinda zai canja da zuwanta, kawaidai maganar da su Mami ke tayi alsn rashin kyautsawarsu ne da suka kawo ta da sassafen nan babu wani bayani.”
Cewar Surayyan tana cigaba da kallon yarinyar. Amina tayi murmushi itama tana kallon yarinyar kafin ta sunkuyar da kanta a hankali tana kallon yatsun hannunta, ba wai zancen Hamidan ne ya dame ta a yanzu ba, tunanin tarin abubuwan da bata gama saninsu bane game da al’ummar gidan dama Ma’aruf din kansa, sannan kuma tunanin halin da ta lura Ma’aruf na ciki tun sanda taje falon.
Tayi zaton a yau sau ɗaya zuciyarta zata tsorata kamar yadda tayi a dazu, a dazun da taji karar buɗe kofar nan ta baya, Samirah ta taba gaya mata cewar kofar tana kara ta samu mai ta saka mata, amma bata taba tunanin cewar mantawar da tayi zaiyi amfani ba sai a dazun da karar buɗewar tata ta cika wajen, wanda a lokacin guda ta ture Ma’aruf daga jikinta ta ruga ta koma cikin gidan ta kofar kitchen din dake bayansu.
Bata san waye ba amma tun a lokacin zuciyarta ta gaya mata cewa koma waye din bai dace ya gansu a wannan yanayin ba, sannan bayan rashin dacewar ma ta sani hanya ce da al’amura zasu iya cakude mata tun yanzu, ilai kuwa sai ga mutanen da bata taba zato ba, Hajiya Kilishi da kanta har da wata da ta kira Aminyarta da kuma su Surayyan.
Ta tuno yadda hannayenta suka dinga rawa lokacin da take kokarin zaro dogon hijabinta daga cikin abin sallarta bayan ta taho da sauri zuwa daki, da kuma yadda Hajiya Kilishin ta dinga bin hijabin nata da kallo bayan ta fita gaishe su, kamar tana son ɗage shi ne don ta gano wane irin kaya ne a jikinta.
Kuma kamar yadda Mamin take haka matar da ta kira kanta ƙawarta take, duk da cewa tana ta faman addu’a da sanya fatan alkhairi a cewarta bata sami zuwa biki ba, sai dai daga ita har Ma’aruf don a wannan lokacin ba jinta suke yi ba, Ma’aruf din na can tsaye a hanyar kofar fita daga falon kusa da window yana waya da Ishaq rike da yarinyar da Surayyan ta shigo da ita yayin da nata idanun ke tafiya kansu duk bayan wucewar sakan guda tana jin zuciyarta na sake yin rawa a kirjinta.
“Sunanta Hamida Amina, ƴarsa ce.”
Abinda Mamin ta fada kenan bayan lurar da tayi da kallonsu da take yi da kuma cewar wayar Ma’aruf ɗin ba mai karewa ba ce a kusa.
Tana tuna yadda zuciyarta ta doka a ƙirjinta kafin ta haɗiye wani dunƙulen abu tana wasa da yatsun hannunta.
“Nayi zaton ai a cikin surutan yaran nan sun gaya miki zancenta, tunda tun kafin bikin ku ake ta case din dawowar tata wajensa.”
Sai ta girgiza kanta a hankali yayin da Surayya ke cewa.
“Mami hirar ce dai bata taba zuwa ba idan muna tare, amma ai ko daga colander bakin Samirah zata iya ji.”
Amina bata ce komai ba har sanda Hajiya Kilishin ta sake cewa.
“Kuma shima ban ce ya gaya miki bane shi yasa duk aka taru aka manta.”
Ta fadi hakan muryarta na haskawa da wani irin yakini da kuma izza wadda wanda ya santa irin sanin da tayi mata ne kawai zai fuskanci manufar kowacce kalma dake bayan maganar tata, da kuma dabarar cewa itace mai juya duk wani al’amari da ya shafi mutanen gidan. Kuma Amina tana tuna yadda wata busashshiyar iska ta shiga wucewa ta makogwaronta kafin ta gyada kanta.
Samirah ta tafi a lokacin don tace kitchen ta baro ta taho, don haka ko da ta gama gaishe dasu bata zauna a falon ba, ta miƙe ta dawo ɗaki, a bakin gadonta ta zauna tunaninta na zarya kan tarin abubuwan da bata san yawansu ba a cikin kanta yayin da take jin muryoyinsu daga nan Ma’aruf ya dade yana wayar nan kafin taji ya gama su dawo magana dasu Mamin, tana jin muryarsu amma bata san me suke cewa ba har zaman shirun ya ishe ta, gashi wayar nantana hannunsa balle ko ba ta kira Amma don ta sanar mata ba, ta kira taji ya jikin Aminu.
Sai kawai ta fito da wasu mayafai da hijabanta da har yanzu ke cikin akwatunan lefen nan ta fara ninke su tana samo musu waje a gefen inda take sa kayanta, a haka Surayyan ta karaso ta same ta ɗauke da yarinyar da tayi bacci.
“Ki kyale Mami kawai Amina, na san Ya Ma’aruf zaiyi miki bayanin komai, ita ba lallai taga hakan a matsayin wani abu bane.”
Surayyan ta ƙara faɗa wannan karon tana kallonta, kuma ba shiri itama ta dago da fuskarta ta kalle ta.
A zagayen tunaninta kaf dama yadda ta fahimta tayi zaton ai babu mai iya ganin rashin daidain Hajjiya Kilishi balle har a su fahinta, amma da sigar da Surayyan ke mata magana a yanzu sai taga kamar tana nuna cewar bata ji dadin yadda Mamin tayi mata maga a dazu bane wanda ita ta san dalili, Ma’aruf baya zaune a wajen… ƙawarta kuma Hajiya Salamatu ta riga ta san da abin dake tsakaninsu da alama, Surayyan kuma dake zaune bata damu da abinda zata yi tunani ba.
Lokacin da suka fita zuwa falon babu kowa, su Mamin sun tafi Ma’aruf kuma bata san inda yake ba, Surayya tayi mata sallama ita kuma ta kwashe kayan lemonta da basu taɓa ba ta koma kitchen.
Zuciyarta na ta sake-sake tana maida kayan wajensu lokacin da taji shigowar Ma’aruf yana waya, kuma daga sautin muryarsa ta ji ya wuce zuwa hanyar daki don haka ta dauko kayan breakfast dinsu da ta riga ta haɗa ta taho zuwa dakin.
“Ka bar ta kawai Ishaq, ka barsu kawai… tunda ka tura musu da wannan shikenan I have my plans against them. Sun yanke wannan hukuncin, na karba, zasu ga me zai biyo baya kuma.”
Muryarsa ta fito ne a hankali da tsananin damuwar dake kwance fal a cikin ransa, damuwar da tun a dazu ta san da ita, amma yawanta a yanzu ya ninku ta yadda take jin da zata iya, zata ƙwace wannan wayar ne don kowa ya daina kiransa yana ƙara gaya masa abubuwan dake hargitsa shi.
Yana zaune daga gefen gadon ya sunkuyar da kansa hannunsa ɗaya riƙe da wayar ɗayan kuma ya zura hannunsa a cikin gashinsa yana magana. Ta karasa ta ajiye tray din hannunta akan bedside drawer dake gefen gadon.
Ya dago ya kalle ta sau daya sai kuma ya cigaba da sauraren bayanin da Ishaq din ke yi ta cikin wayar. Tana jin yadda jikinta babu nauyi kwata-kwata ta shiga kokarin hada tea a kofi guda bayan ta zuba dankali da kwan da ta soya a plate ta ajiye a gabansa, lokacin da ta gama haɗa tean ta juyo don ta miko masa ya gama wayar.
“Kin zuba naki?” Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta.
Sai ta girgiza kanta.
“Yanzu zan zuba, ka fara karɓa tukunna.”
Sai kawai ya miƙo hannunsa ya riko kofin, ya hada har da hannunta gabadaya, ya zagaye yatsunsa a jikin natan.
“Mami ta miki bayanin komai?”
Komai? Idan har komai ɗin yana cikin kalma biyun da ta faɗa cewar yarinyar ƴarsa ce to kuwa tayi mata bayanin, abinda ya rage kawai shine a fahimtar da ita don bata gane ba, babu abinda ta gane a zuwan nasu da sassafen nan har kuwa rare da Aminiyarta da kuma yarinyar da aka zo ala shimfide a gadonta, amma sai bata ce komai ba, don bata san ta yadda zata fara gaya masa tarin tambyotin dake cikin kanta ba.
Yana riƙe da hannunta da kuma kofin lokacin da ya fara maganar da a farkonta bata gane komauba.
“Rukayya kamar Family freind dunmu ce tun da dadewa, mahaifinta abokin Baffa ne, sunyi aiki tare kuma sunyi kasuwanci tare kafin kowa ya buɗe nasa kamfanin. Ita kadaice a gidansu mace tana yayye da kuma kanne maza, amma tun a wancan lokacun ba ma shiri da sauran ƴanuwan nata saboda ra’ayinmu da ya banbanta.
Ita kaɗai ce a gidansu kowa yake shiri da ita, kuma tun a wannan lokacin ra’ayinta ya karkata sosai a kaina ta yadda take kyautata min fiye da kima har sai da kowa ya fahimci cewa she’s interested in me. To sai wani abu ya faru a wannan lokacin da ya zama mafarin ciwo na, rayuwata ta canja gabadaya ta yadda na tashi daga yadda kowa ya sani zuwa wani abun daban.
Amma duk da haka bayan mun kammala karatu sai ta dage akan bakanta, and I’ve no right da zan iya cewa A’a, saboda ko Baffa a lokacin ya matsa da cewar inyi aure kuma ni ba wannan ne a gabana ba, ina wani bincike ne da nake ganin cewa zan iya gama shi a wancan lokacin saboda haka above all the girls a sannan sai Rukayya tafi kowa zama wadda ya dace na aura.
Bayan auren mu, da shekara biyu, sai zaman yazo karshe, lokacin Hamida tana Baby….”
Yayi shiru yana shafa hannunta akan kofin kafin ya cigaba.
“Na yarda na bar yarinyar a wajenta ne a lokacin saboda karama ce kuma ko baka haka ba dole a wajenta ya kamata ta zauna dama, sai dai duk da haka munyi wani sharadi a lokaci da zai bani damar ɗaukarta bayan na kammala abubuwan gabana.
Lokacin da ake shirin fara aurenmu dake, lokacin naga Hamida a wani waje da bai dace ba tare da wata Christian wai ita take kula da ita, da na dauke ta na kai ta wani creche ne tunda ba zan iya kawo ta gida a lokacin ba kuma a can ta zauna har bayan kin zo gidan nan.
Mami tace in dawo da ita nan amma banyi hakan ba saboda nafi son komai ya tafi a hankali, don ni dake ba mu gama fahimtar juna ba a lokacin, so I have my plans yadda komai zai tafi daidai amma sai gidan su Rukayyan suka kasa jira na suka kai zancen kara kotu wanda a jiyan ya kamata inje amma ban samu zuwa ba, Ishaq yaje kuma basu yarinyar kamar yadda muka san dama hakan ce zata faru.
Amma kawo ta da suka yi a yau ban san dashi ba Amina, Dukkaninmu babu wanda ya san dalilin da yasa suka yi hakan, abu daya kawai na sani shine, Hamida tazo wajena kenan Amina ba zata taba komawa hannunsu ba ko me zasu yi a duniyar nan kuwa.”
Yayi shiru yana kallon yanayin fuskarta, yadda idanunta ke nuna cewa kwakwalwarta tana daukan dukkan maganganunsa a wani ma’auni da ya kasa tantance shi, don haka sai kawai ya karasa jawo ta gabansa a hankali, har yanzu kofin na rike a hannunsu su duka biyun. Kuma saura kadan goshinsa ya hadu da nata yace.
“Doll, zaki taya ni mu rike ta?”
Muryarsa a hankali ta fito, da wani amo da kamar auna shi ne ya tabbatar zai kassara kowanne abu mai kwari a jikinta da kuma cikin kanta, numfashinta kawai take ji yana fitowa da saurin da yafi daidai, kuma ta san ya fahimci hakan amna da yake a kowanne yanayi Ma’aruf shi din ne dai sai ji tayi yace.
“Idan tunani kike zata hana mu wani abin Doll kar ki damu, I will always find a way, na miki alkawari.”
Bata san lokacin da ta ture shi baya da hannu daya sannan ta miƙe tsaye, ya rike kofin data bar masa, ya kalle ta da murmurshi a fuskarsa lokacin da wayarsa ta sake kara.
Ta juyo ta kalle shi kamar zata ce wani abin game da wayar, ya daga mata gira ɗaya yana kai kofin bakinsa, sai kawai ta kasa cewa komai din ta juya zuwa wajen wardrobe ɗinta.
“B, yanzun nan ɗaya daga cikin mutanen RTL ya sake kira, ya bamu details akan mutumin nan da yazo ya karbi kudin.”
Abinda Faruk ya faɗa kenan, bayanan layi biyu da a cikin sakanni biyu kawai da suka da suka yi ƙoƙarin goge duk wani dukkan hargitsin da ya tashi dashi a safiyar yau, bakinsa ya furta hamdalar da bai san lokacin da taji bakin nasa ba.
Yaji zuciyarsa na washewa da yakinin fawwalawa Allah al’amarinsa, a yau kaɗai ya tashi da matsaloli har guda biyu wanda suke jigo kuma manya-manya a rayuwarsa, amma sai gashi tun kafin ya kai breakfast bakinsa ya fara samun rabi na waɗannan matsalolin sun fara gushewa.
Idonsa ya sauka akan Amina data dauko wani farin abu dan karami ta karaso kan gadon daga daya gefen tana ƙoƙarin kara rufawa Hamida dake motsi kamar sanyin fankar dakin ne ke damunta.
“Alhmdlilah.”
Ya furta a hankali yana cigaba da kallon halittu biyun da yake ganin sun zama wani jigo naduniyarsa a yanzu.
Abinda bai sani ba shine, akwai wasu lokuta da bawa ke kaiwa gabar da karshen wahalhalunsa a duniya ke karewa, akwai gabar da mutum ke zuwa inda komai zai tsaya, komai din da ya danganci dukkan wani kunci da hargitsin rayuwar da ya fuskanta, akwai gabar da mutum ke girbe tarin hakurinsa da ya shuka, akwai gabar da mutum ke fahimtar cewa Allah na karbar dukkan addu’o’in sa, sannan akwai gabar da mutum ke iya canja karin maganar bahaushe da cewar…
Rana dubu ta barawo… Rana dubu ma ta mai kaya!
***
_Ina ga mun tatttaro dukkan ksn matsalar mu a yanzu, so wa shiryawa fara samun revenge?_
_Waya shiryawa ramuwar gayya da ake cewa tafi ta gayyar zafi?_
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
