Farar Huta 2 – Chapter Six
by NadminA cikin harabar gidan, daga can gefe inda akayi shuke-shuken wasu bishiyu dama fulawowyi, Jawad ya shafo kan hancinsa da daya hannunsa wanda baya rike da wayar da yake yi kafin yace.
“Na gaya maka naga motar, daga can gefen inda muke ta tsaya kuma ni naga mace da namiji a ciki, fuskokinsu ne kawai ba zan iya tantance maka ba.”
“Babu ji, wannan mai sauki ne in dai har ka tabbatar number motar da ka faɗa daidai ne. Zanyi kokarin nemo bayani akan plate din sai muyi tracing , tunda na san dake zuwan nasu yana da alaka da dalilin rashin zuwan Ma’aruf wajen.”
Jawad ya gyaɗa kansa a hankali yana cije lebbensa.
A jiya bayan sun shiga Kano, tsarinsu ya tafi daidai, sun yi komai kamar yadda Haro ya tsara kuma ma sun isa wajen da suke saka ran ganin Ma’aruf inda zai hadu da wadannan mutanen, sai dai sunyi tsawon jiran da har mutanen suka zo babu Ma’aruf din babu alamarsa, kuma suna wajen har lokacin da motar mutanen ta juya suka bar wajen.
Kuma sai a yanzu Jawad ya tuna da motar da suka wuce akan titin kafin su sami wajen tsayawa, don haka ya kira Haron a waya yanzu yake gaya masa, don a jiyan bai ko bari ya kwana a Kano ba yayi booking jirgin dare ya dawo gida,yana da abubuwa da yawan da ba zai iya wasa da lokaci wajen kuɓucewaru ba.
“Kar ka damu J, ai ba ƙasar ya bari ba, muna da lokaci muna dashi mara adadi, wannan opportunity din ma don naga yayi kusa ne nace muyi amfani dashi kawai, amma yanzu damar ta fara Jawad kai ma ka sani.”
Ya gyada kansa.
“Na sani, na san akwai lokaci Sadiq, fata kawai nake ne kar Rukayya ta shammace mu.”
Haro yaja tsaki a cikin wayar.
“Haba Jawad, a cikin kwakwalwar wannan dakikiyar yarinyar har akwai abinda zata yi ne da zai fi namu? Kawai ka cigaba da harkokin ka, ba za’ayi dedewar da kake tunani ba insha Allahu, su kuma Waɗannan mutanen zan saka a nemo mana su insha Allah.”
Da haka suka gama wayar, Jawad ya kalli mintunan da duka gama fitowa a jikin screen din kafin ya kashe ta ya zura a aljihu, yayi abu guda biyu da ya ɗanawa tarko a safiyar yau bayan dawowarsa, saura na ukun wanda har cikin zuciyarsa yake jin tasirin faruwarsa, game da yarinyar nan, ƴar aikin nan.
Jiya bayan ya fito ya gan ta a wajen nan kuma ya tabbatar da cewar taji dukkan maganganunsa da Haro, baiyi mata magana ba, bai ce komai ba, don ko Haron baya son ya san hakan, abinda zuciyarsa ta gaya masa shine dole ya san yadda zai yi ya rufe bakinta kawai don baya hango yadda alakarsa da mahaifiyarsa zata kasance idan har koda wasa ne ta fadi hakan a gabanta.
Ya zura wayar a aljihu, sannan kai tsaye ya fito daga wajen ya nufi hanyar da zata zagaya dashi baya zuwa ɓangaren masu aikin gidan, bangaren dashi kansa gida ne guda mai ƙatuwar haraba da kuma shuke-shuke, ba zai iya tuna rana ta karshe da ya taka kafarsa zuwa wajen ba, kawai dai ya san kafin su kai ga tarewa a gidan da suka zo gabaɗaya tare da mahaifinsu da kuma sauran ƴanuwansa maza, sun zagaya koina har nan kuwa.
“Good morning sir… Good morning.”
Wasu ƴan aikin guda biyu dake shanya tarin kayan wankin yara suka tsugunna suna gaishe shi, ya gyaɗa kansa alamun amsawa sannan ya tsaya yana kallonsu, ya rasa ma me zai ce musu saboda ko sunan yarinyar bai sani ba, ya san dai ya taba ji Mamah ta taɓa kiranta a gabansa, watakila fiye da sau ɗaya ma amma baya jin zai iya tunawa.
“You want something sir?” ( Kana bukatar wani abu ne yallabai?)
Daya daga cikin ma’aikatan ta faɗa, sai dai kafin ya buɗe bakinsa yayi magana idonsa ya hango masa ita, ta karyo kwana ta shigo wajen, hannunta dauke da wani katon farin nokiti da ta ciko kayan miya a ciki, ko daga nesa ya san bokitin yayi mata nauyi daga yadda yake kokarin rinjayarta ta gefe guda.
Sai kawai ya juya ya nufi wajenta, kuma har ya taho bata lura dashi ba sai da ya iso daidai gabanta tukunna, da farko idanunta basu shaida shi sosai ba, watakila ko bata taba zaton ganinsa a lokacin kuma a wajen bane, amma a lokaci guda sai idanun nata suka haska da tsananin mamaki da kuma fargaba.
Yana ganin yadda ta saki bokitin da sauri zuwa kasa kafin itama ta bishi kasan ta durkushe kan gwiwoyinta sannan tace.
“Ina kwana… Barka da safiya.”
Duka kalar gaisuwar guda biyu shi kaɗai, kuma har ya buɗe baki zaiyi magana sai idonsa ya kai kan wasu mata daga ginin dake gabansu sun leƙo ta window suna hangensu, wani tunani ya gifta a cikin ransa don haka sai kawai ya maida kalaman da yayi niyyar faɗa yace.
“Me kuka dafa a bangren Mamah?”
Tambayar ta shiga kan Zainb da tsananin mamakin da ya fi na farko, don ta tabbata ba abinda ya kawo shi kenan ba, ya za’ayi ya bato bangaren ya taho tun daga can har zuwa nan don ya tambayeta kawai abinda aka dafa? Mutumin da idan hr ba fita zai yi ba kowa ya haddace cewar baya tashi sai rana ta miƙa, amma ƙarfe nawa yanzu? Tara da mintuna…
Ta yaya ne ma yake mata magana muryarsa a ƙasa, ta zata ai idan har ba tare da mahaifiyatsa yake ba baya iya magana babu hantara. Sai tayi saurin hadiye abu a bakinta sannan tace.
“Ba’a gama abincin duka ba, an dai yi wasu.”
Ya gyada kansa.
“Ki debo wanda aka gama ki kawo min.”
Da haka bai kara cewa komai ba yayi gaba. Zainab tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa kafin ta mike a hankali.
Kuma minti goma bayan hakan, ta kwankwasa kofar ɗakin nasa ɗauke da farantin kayan abincin, kallon da sauran manyan ƴan aikin gidan suka dinga binta dashi bayan ta gaya musu inda zata kai abincin.
“Shigo.”
Muryarsa ta fada daga ciki, kuma karo na farko ta murda hannun kofar ta shiga, dakin kamar yadda ta zata ne, ƙato mai cike da hadaddun kayan kamar na sauran ƴanuwansa mata, sai dai har gwara nasu ma yafi kyale-kyale akan wannan da komai tsilla-tsilla ne. Yana zaune daga gaban gadon dakin a tsakiya, ya dora hannayensa kowanne akan cinyoyinsa yana kallonta, kuma da yatsu biyu kawai yayi mata alamar cewar ta karaso.
Ta taho ɗin, amma muryarsa ta tsaida ta.
“Koma ki rufe kofar.”
Gabanta ya sake faduwa, amma babu yadda ta yi ta koma ɗin ta rufe ta a hankali sannan ta sake juyowa, tana ta tahowa bai ce ta tsaya ba, kallonta yake yi ta sani amma ita idanunta na kan farantin.
Sai da ta karaso nesa dashi kadan sannan ta tsugunna ta ajiye farantin a saitin gabansa, kuma kafin ta mike kamar yadda daga shi har ita suka san shine abu na gaba ya sake magana.
“Zauna.”
Ta hadiye wani kullutun abu a makogwaronta sannan ta gyara tsugunnon nata a hankali alamun ta zauna ɗin, tambayarsa ta gaba ta kada ƴaƴan hanjinta a lokaci guda.
“Daga ina kike?”
Sai ta dago ta kalle shi.
“Nace daga ina aka kawo ki?”
Ya sake maimaitawa, ya sake maimaitawa yana fadada tambayar da ta riga ta fahimta din kuma ta san ina take dosa.
“Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake.” Muryarta tana rawa.
Ya gyada kansa.
“Waye ya kawo ki nan?”
“Abokin babana ne.”
“Ina baban naki?”
A hankali tace.
“Ya rasu.”
“Ina babarki?”
Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace.
“Tana nan, matarsa ce ita yanzu.”
Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ƙiyasinsu.
“Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?”
Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan.
“Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba.”
Kalmar Naanin da ta fada ya fahimce itace mahaifiyarta don haka kai tsaye ya sake tambaya
“Yaya sunanki?”
Wannan karon da mamakin da yafi nasa ta kalle shi, bai san sunanta ba? Bai san sunanta ba yake tambayar labarinta?
“Sunana Zainab.”
Sai ya sake gyaɗa kansa yana kallonta.
“Zainab, I know you heard us….”
Maganar tasa ta katse tuna cewar a banza zai yi bayanin ko ta cigaba.
“Na san kin ji mu ranar nan, kinji duk abinda muka fada ni da wanda yazo….”
Ta riga ta sani dama, tasan zancen da zai yi mata kenan, ta san ta shiga uku, ta san karshen rayuwarta a gidan nan tazo tun daga wannan lokacin, Allah ya sani tana jin daɗin zaman gidan nan fiye da sauran gidaje biyu da tayi aiki dasu a baya saboda yadda mahaifiyarsa ke kyautata mata, amma tun daga ranar da ta ci karo dashi har ta zuba masa miya a kaya, tun daga ranar hannayenta suka fara lissafin kwanakin barinta gidan, sai gashi ta samu talalar wasu watannin kafin shekanjiya ta tabbatar mata cewar wa’adin kwanakin nata yazo karshe.
Don haka taji yadda iska ta wuce cikin busashshen makogwaronta kafin ta tattaro dukkan karfinta ta daga kanta sau daya.
Jawad ya gyaɗa nasa kansa shima.
“Good. Shi yasa na kira ki nan.”
Ya fadi hakan sannan ya gyara zamansa.
“Ba zaki so in zama abokin babanki na biyu ba Zainab balle kuma har in fi shi, don ina rabbatar miki zan iya kuntata rayuwarki fiye da yadda bakya tunani idan har kika zabi yin wasa dani.
Abinda kika ji sirrina ne, kuma duk da babu yardata ya iso gare ki, na baki amanarsa a yanzu, kuma in so ki barshi a cikin ranki, ki barshi kamar yadda yake a tsakanin mu yanzu, idan har shiga kunne na biyu musamman kunnen mahaifiyata Zainab…”
Yayi shiru yana cije lebbensa kafin ya fadi abinda yasa ta zare idanunta a lokaci guda ta dago tana kallonsa, hannayenta dama ilahirin jikinta gabaɗaya suka shiga kakkarwa yayin da idanunta ke haskawa da tsoron da bsta lissafa dashi ba a duk wani lissafinta na ukubar rayuwar da take tunanin fuskanta!
****
*Kano.*
*No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Quaters.*
*Ƙarfe Goma na safe.*
A cikin dakin, cikin uwar dakin Hajiya Kilishi ta dubi kawarta Hajiya Salamatu wadda isowarta kenan a wannan safiyar bayan fitar Mama Rabi wadda ta shirya musu abun motsa baki fal a wani katon faranti.
“Kinyi min nisa da yawa Salamatu, china tayi min nisa tunda ni ba harkar social media din nan nake yi ba. Na kulla abubuwan da yawa wanda babu tayawarki a ciki balle har mu kai wa tufkar ƙarshe mai daukar ido.”
Hajiya Salamatun ta cire dankwalinta ta ajiye shi a gefe, mikakken gashin kanta da yasha gyara ya shiga nuna maikonsa cikin hasken dakin kafin tace.
“Ni iyaka ta dake ai shawara Kilishi, wasu ma ba ɗauka kike ba idan na fada, to don me zaki yi kewata? Yanzu kawai ki gaya min me ya faru? Me ya faru daga inda na barki.”
Hajiya Kilishi ta juya idanunta tana murmushi sannan ta kalli aminyar tata dake zaune daga bakin gadon dakin tace.
“Abubuwa da yawa Salamatu, don haka mu kyale ƙananan ma a gefe, mu fuskanci manyan.
Na riga na gama da yarinyar nan, ta san komai kuma ta yarda da komai…”
“Haka cikin sauki?”
Salamatun ta kasa daure namakin da yasa ta katse ta wajen tambaya.
Sai kawai ta ɗauki kofi guda akan farantin, ta tsiyaya lemo a ciki ta mikowa Hajiya Salamatu kafin ta bata amsa.
“Ba cikin sauki bane, nayi abinda ba zata iya bijire min bane kamar yadda ta fada da bankinta. Kin sani Salamatu, kin san yadda bana wasa da dukkan abinda nasa a gaba, kuma kin san yadda nake bawa abinda nake so muhimmanci.”
Hajiya Salamatu ta kurɓi lemon sannan tace.
“Na sani Kilishi, ba sai kinyi wannan bayanin ba, na yarda kin samu yarinyar bayan ita kuma sai me?”
Tayi wani sassanyan murmushi tana kallonta.
“Sai burin da na ɗanawa tarko, burin cike kan wadannan kudaden.”
“An samu?”
Ta tambaya bayan ta ajiye kofin lemon.
“Kwarai, an samu Salamatu, wani ciniki suka yi na makudan kudaden da har suka fi gejin da nake nema ma.”
“Kince min ya gano waccan hanyar taku ta hacking account din kamfanin da akayi aka tura musu da alert din bogi. To wannan karon me kika yi?”
Kai tsaye Kilishin tace.
“Kwantar dashi nayi kamar yadda na saba kuma zaki yi mamaki ta hanyar yarinyar nan hakan ta faru.”
Wannan karon da mamaki Hajiya Salamatun ta kalle ta kafin ta kyalkyale da dariya.
“Irinki basu da yawa a kowanne ƙarni Kilishi, shi yasa nake gayawa duk mai takura min akan rayuwa cewa ya kyale ni kawai, da nayi niyya zan rayu a duniyar nan kamar a aljanna ne saboda ke.” (Waiyazubillah.)
Kilishi ta gyada kanta tana daukan cake guda a cikin farantin fake gabansu.
“Ni kaina na sani Salamatu ina da laushi fiye da dukkan tunanin mai zato, laushin da zan iya ruɗar ko waye a duniyar nan ya dulmiya zuwa cikin tarko na da bashi da ƙarshe. Shi yasa tun farko na gaya miki cewa ita kanta yarinyar na shirya mata, kuma gashi tun amba’aje koina bakan ta tabbata r miki da abinda na fada cewar babu wata mace da ta isa tayi tasiri a zuciyar Ma’aruf sama dani, a yanzu na gama yi mata shirin da ba zata taɓa iya bari Ma’aruf din yayi tasiri a zuciyarta ba balle har ta iya tsallake umarni na.
Na tsorata ta, kuma ta gama tsoratar akan al’amarinsa, zata ganshi ne kamar yadda na haska mata shi, zata ganshi a matsayin wani abu daban ba mijin aure ba, don ko ciki bata isa ɗauka ba.”
Salamatu tayi dariya.
“Na san zaki aika ai Kilishi, kawai dai a farko ne nayi tunanin ke kanki baki gana sanin halin yarinyar ba na jiye miki wannan tsoron, amma tunda har kin taka matakin nasara akanta tun ba’a je koina ba, mu cigaba a inda muka tsaya, ki gaya min ta yadda kika sami kudaden nan.”
Kilishi ta daga kanta sau daya sannan ta cigaba da magana.
“Kwantar dashi nayi kamar yadda na gaya miki sannan Awwalu ya sanya min yaran sa suka fara binsa tun daga lokacin da ya bar gida, muka sa wani yaje ya daki motarsa sannan kuma ya zage shi don in tabbatar idan har yarinyar nan ta bashi maganin, ilai kuwa nan da nan mood dinsa ya rikice ya kama dukan mutumin, a wannan hayaniyar wasu da muka saka suka samo min wallet dinsa har dama wayoyinsa wanda muka yi amfani dasu.”
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
“Ban gane ba, kuka yi amfani dasu ta yaya?”
Kilishi ta ajiye cake din da har a lokacin bata kaishi baki ba, ta gyara zamanta sosai tana kallonta sannan tace.
“Ma’aruf yana da wayo da dabara sosai Salamatu, na sha gaya miki tun bai kai haka ba. Don haka bayan sun gama wannan bincijen shi da wannan abokin aikin nasa, sun gano cewar tabbas alert din da suka samu na bogi ne, sai ya canja shawara, yace wannan karon cash zai karbi kuɗi ta hannun mutanen da suka yiwa aiki ba ta account ba kuma da kansa yadda zai je ya saka a banki don kar a sami ma wata matsala ba.
Abinda bai sani ba shine, tunanin Kilishi da nasa ba daya bane, a cikin maganganunsa kawai na gane abinda yake shirin aikawmtawa tun kagin ma su gama aikin a saka ranar karbar kudin, shi yasa na tsara komai, na tsara iya kwanakin da zasu ishe ni har in tunkari Amina ta gama shawararta tazo ta amince dani da kuma iya kwanakin da zata sanya masa gubar har ya kwanta kafin ranar.
Kuma na sami komai Salamatu, I.D cards da kuma wayar Ma’aruf ɗin kaɗai muka nunawa mutanen nan da kuma wani dan bayani kaɗan suka yarda suka bamu kudin a madadinsa, kuma mun karbo ba tare da wata matsala ba Salamatu, Ma’aruf kuma yana nan a kwance duk da ance min ya fara samun sauki amma wannan ba damuwata bace, ko yanzu idan ina son ya kara komawa, umarni kawai zan bata, muna zaune anan zaki ji komai ya kara rikicewa.”
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
“Ba kya tunanin idan ya tashi ya tuntubi mutanen zasu iya shaida masa abinda ya faru da kuma yanayinku? A tunanina ba kya ɗanyen aiki Kilishi.”
Itama ta girgiza kanta.
Ba tunanin kike ba Salamatu, tabbas bana danyen aiki, don wannan ɗin ma gasashshe ne. Wani saurayi muka samo daga Prison, wata na biyu Salamatu ina barar da kudi a prison din nan ina neman kafa, don kawai a ara min shi na rana guda yayi wannan aikin kuma da kyar muka samu.
Awwalu ne yayi masa I.D card din kamfanin sak a matsayin babban ma’aikaci, don haka muka tura shi a matsayin hakan ya karbo mana kudin da bayanin cewa shi maaikacin wajen an aiko shi ya karɓi sakon ne bayan ya nuna musu kayan Ma’aruf harma da wayarsa don haka nan da nan suka yarda.
Suka bashi dukkan kudin mu kuma muka bashi rabonsa tare da na iyayen gidansa muka maida shi inda muka dauko shi. Shi yasa nace miki aikin gasashshe ne Salamatu tunda kin san duk naci da binciken Ma’aruf babu ta yadda zai kamo mutumin dake cikin Prison duk kuwa iya bincikensa.”
Hajiya Salamatu ta kyalkyale da wata irin dariyar da bata shirya mata ba tana girgiza kai.
“Zama dake alheri ne Kilishi, na sha gaya miki yadda kike bude nin kwakwalwata akan abubuwa, yana bani saukin warware nawa matsalolin gabana na nima.”
Kilishi ta gyada kanta.
“Abinda na gayawa Saratu kenan ai, kowacce mace tana da irin tata dabara da kuma mafitar matsalarta a cikin kanta, yanzu da ta saurare ni ba gashi nan daga ita har ƴaƴan ta mijin ya tafi dasu Egypt din ba, amaryar da ake takama da ita da farko wata daya tayi ya dawo da ita.
Kawai jahilci ne yasa mutanen farko ke bin wasu bokaye da suke maza ma don samun biyan bukatar fa bata dorewa. Kowa ta sani cewa tunda aka halicci duniyar nan har kawo yau, ƙarya ne a samu aikin wani bokan da ya zama mai dorewa har abada.
Amma idan mace tayi amfani da dabara da kuma tunaninta wajen kwatarwa kanta ƴanci ko a wajen waye, ina tabbatar miki wannan abin ba mai gogewa bane balle har ya lalace, akwai abubuwa da yawa da suke ɗamfare da tare da halittar mu, kawai bama barin kanmu mu gansu ne.
Kwakwalwar mace kamar littafi take, dauke da tarin abubuwan da tana bude shafukan gaba tana kara fahimta, wadda bata bude ba kuma zata yi ta jallon bangon ne kawai ba tare da ta taba sanin meye a ciki ba.
Salamtu ta kara gyada kanta tana yarda da dukkan maganganun kamar yadda Kilishin ta dade tana ambata mata.
“Na taya ki murna kwarai na samun wannan burin da kika daɗe kina lissafinsa a ɗan kankanin lokaci Kilishi, kin tafi zuwa gaba kuma saura kiris ki kai ga cimma msnufarki gabadaya. Sai dai yanzu na san baza’a sake samun irin wannan aikin a kusa ba, za’a dauki tazara koda baza’ayi dadeear da nake tunanin ba. Don haka meye a gabanki yanzu?”
Tambayar ta yiwa Hajiya Kilishi dadi, me yasa ne take buɗewa Salamatu cikinta dama? Me yasa take gaya mata dukkan tsarinta duk sanda ta tambaya? Ba saboda tana gaya mata daɗaɗan maganganunn dake wanke zuciyarta suna bata kwarin gwiwa a kodayaushe bane?
“Hamida ce target dina na gaba Salamatu..”
Ta faɗa kai tsaye tana kallonta.
“… wannan yarinyar, wannan ƴar ta mai gaskiya, ina son Ma’aruf amma bana son duk wani abu da zai zana nasa, don hakan ba karamin naƙasu zai jawo min a zuciyarsa ba.
Rukayya bata taba damunsa ba shi yasa nima bata taɓa damuna ba har tayi yayinta ta tafi, amma wanna ƴar tata Salamatu, naga wani abu a cikin idanun Ma’aruf a ranar da yake riƙe da ita a asibiti, na ga wani abu da ban taba ganin irinsa tare da kowa idan ba ni ba Salamatu. Shi yasa tun awanvan ranan na rufe idanuna naso kawo karshenta, amma Allah yayi da sauran ruwanta a gaba shi yasa ban samu nasara ba, amma a yanzu ina jin cewa ko ta halin
ƙaƙa zan iya canja kaddarar yarinyar nan Salamatu. (Waiyazubillahi!)
Ta rufe bakinta daidai lokacin da kofar dakin ta bude, Samirah ce ta shigo jai tsaye hannunta rike da wata ƙatuwar jaka kalar Pink mai kyau, dukkaninsu suka bita da kallon yayin da kafin Hajiya Kilishin tayi magana Surayya kuma ta biyo bayanta, hannunta dauke da ƴar yarinyar da a lokaci guda kamanninta suka doka wata irin fargaba zuciyar Hajiya Kilishi.
Hamida ce, riƙe a hannun Surayyan ta makalkale ta yayin da take zare manyan idanunta irin na maifinta sak! akan kowannensu.
“Mami yanzun nan direban gidansu ya kawo ta, wai cewa akayi akai ta wajen Ya Ma’aruf.”
Murmushin da ya sabuce a bakin Hajiya Kilishi wani murmushi ne da ya taɓo har acikin zuciyarta… Tana son mutane masu saukaka mata ayyuka, a rayuwa, Allah ma ya sani.
****
“Inalillahi wainna ilaihir raji’un…”
Sune kalaman da suka fito daga bakin Ma’aruf a lokacin da yake zaune kan kujerar falon yana sauraran bayanin da Faruk ke masa a cikin wayar, kayan jikinsa dogon wando ne baƙi da kuma wata riga kslar ruwan toka mai haske.
“Wallahi sun nuna min evidence da komai cewa kai ka turo mutumin da ya karbi kudin, don har I.D Card dinka da sauran credit cards dinka ya nuna musu a matsayin shaida.”
Ma’aruf ya cije lebbensa.
“Na kasa ganewa Faruk, na kasa gane wanda zai sace kayana a wannan lokacin kuma har ya san ina da appointment da mutanen a wannan wajen kuma a wannan time din.”
“Saboda already sun san hakan ne, sun san kana da wannan appointment din shi yasa suka tare ka a wannan wajen kuma suka kwashe dukkan wayoyi da wallet dinka.”
“Are you thinking this is all planned?” (Kana tunanin duk wannan abin haɗawa akayi?)
“Ba tunani nake ba, ina ƙoƙarin tabbatarwa ne, don tun safe muke waya da Ishaq, ya gaya min mutumin da rigimar ta hada ku har yanzu baiyi filing case ɗin ba, tunda ka san da sun yi dole za’a neme shi, ka duba al’amarin nan ka gani hankali ba zai dauka ba Ma’aruf ace kayi masa wannan abin amma ko shi ko ƴanuwansa basu dauki wani mataki ba.”
Yayi shiru kafin yace.
“Amma har da nawa contribution ɗin Faruq, ta yaya kake tunanin zasu iya saka ni nayi abinda ban yi niyya ba, ina shan magani na cikin ƙa’ida sannan ina kiyaye dukkan ƙa’idojin da aka rubuta a wannan takardar. To ta yaya zasu iya controlling emotion dina?”
Faruk yayi shiru shima kafin ya amsa.
“Da wannan kuma B, amma zamu gano komai a hankali idan muka bincika. But there’s no way da zan yarda cewa wannan al’amarin accident ne kawai.”
Ma’aruf ya rufe idanunsa, ya dafe goshinsa da hannu daya yana rarraba ƴan yatsunsa akan goshin. Abubuwan dake yawo a cikin kansa basu da iyaka, motsin kowannensu kawai yake ji yana ihu tare da ƴanuwansa, yana jin kamar tafiya suke yi akan fatar kan nasa suna zagayawa da karfin da yafi na kadawar iska a cikin sakanni.
Me yasa ne sai su? Me yasa ko waye su ya zaba yana bibiyarsu? Me yasa ko sau daya bai taba tunanin ya barsu su huta ba? Kamar dukkan fafutuka da kuma ayyukan da suke yi na da sauki a wajensa, kamar a rana ɗaya kawai suke kammala komai ta yadda gake diban dukiyarsu hankalinsa a kwance, yana jin cewa zuciyarsa ba zata tafi da nauyin wahalarsu da ma guminsu ba.
“Na gaya maka B, na gaya maka ka bari sai ka dawo office tukunna ma tattauna, but you still insist. Gashi nan yanzu naji alama you’re changing, bana so na jawo maka wata matsalar kaima ka sani. So mayi magana kawai anjima.”
Da haka wayar ta katse kuma Ma’aruf bai sauke ta daga kunnensa ba, ya cigaba da rike ta kawai idanunsa a rufe yayin da kwakwalwarsa ke juyawa da son tantance dukkan wata kalma da ta fito daga bakin Faruq din.
Bashi da wanda zai zarga, babu wannan mutumin a cikin lissafinsa, amma ya san a yanzu zargin kamar dole ne, don ta haka ne kawai za’a iya samun hanyar da zasu fara tunanin kawo ƙarshen wannan al’amarin.
Anyi haka ba sau dayaba, ba sau biyu ba… An daɗe ana irin wannan abin a kamfanin tun kafin ya kai ga karbar wannan muƙamin, anyi a farkon fara aikinsa ma, watannin daBaffa da Baba Usman suka dora dukkan wani fatansu akansa na cewar abubuwa zasu canja da zuwansa, amma babu abinda ya canja ɗin banda adadin kudin da suka ninku wajen bata ma fiye da baya.
_Ina so ka sani Ma’aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ƙauna take ba._
Kalaman Jamal sula haska akansa tun bayan wani lokaci, a shekarun baya ya kan tuna su fiye da cikin masaki, amma da wucewar lokaci da kuma hargitsin rayuwa ya manta lokaci na ƙarshe da ya tuna su sai yanzu da suka dawo kansa a lokaci guda, yana iya tuna cewa a wancan lokacin Jamal ya gayamasa cewa bai san dalilin da yasa ya fada masa hakan ba, kawai tunani yake cewar zai iya amfanarsa a gaba…
‘Gaban’ tana da ma’ana da yawa, zata iya zama shekarun baya da suka wuce, zata iya zama shekaru masu zuwa a gaba, zata iya zama kuma yanzu, yanzun da yake jin kamar maganar tana ɗoruwa ne akan halin da yake ciki.
Ya ajiye wayar a hankali daga gefen kujerar sannan ya mike a zuwa hanyar kitchen inda ya baro Amina ya taho amsa wayar, ya san ma ta gama aikin nata a yanzu, don tun kafin ya fito ta kusa karasawa.
So yake yayi distracting kansa, so yake ya juyar da tunaninsa a yanzu gabaɗaya daga kan wannan al’amarin, ya samu wani abu da zai ɗauke hankalinsa ya manta da abinda ya gama ji, don bai san me zai faru ba idan ya cigaba da kasancewa cikin hakan a yanzu, abinda ya sani kawai shine koma waye a bayan wannan al’amarin zaiyi dana sanin da wani mahaluki bai taba irinsa ba duk ranar da yazo hannunsa.
Don haka yayi kokarin maida tunaninsa kan Aminar a yanzu, yana kuma tunawa kansa da dukkan abinda ya faru jiya, jiyan da a cikinta kadai ya kara yarda cewa da gaske ƙaunar yarinyar nan, zuciyarsa ta manta da dalilin da yasa ya aure ta don baya ko saka ranar fara wannan binciken, tunda ya taushi kansa da cewar sai ya saba da ita tukunna shikenan ya ajiye hakan a gefe.
Baya iya wani tunani sai na yadda kusan komai nata ke burge shi, halaiyarta, saukin kanta da kuma kunyarta wadda bata hana ta abinda take so, ya kara fahimtar hakan a jiya sosai, a jiyan da yaso abubuwa su fi haka a tsakaninsu, amma baya jin dadi, baya jin kwarin jikinsa kuma baya son yin komai a wannan yanayin, don bai yarda da kansa ba, bai san ta yaya ma komai zai kasance ba.
Ya karasa cikin kitchen din idanunsa na nuna masa cewa babu kowa a ciki, sai kayan girkinta da ta gama ta jera komai tsaf akan table. Karfe sha daya ne na safiya a lokacin, basu dade da tashi ba, don ita kanta ya kula ta gaji jiyan, kwanan asibitin nan da suka yi ba wani mai dadi bane, shi yasa ya sake rike ta a jikinsa bayan sunyi sallar asuba, tana ta gaya masa cewa zata tashi da wuri amma ya ture bayaninta ya kashe bakinta.
A haka wani baccin yayi awon gaba dasu su duka biyun wanda basu tashi ba sai ƙarfe goma saura, shi ya fara tashi ma, kuma yana yin motsi ta farka, shikenan sai baccin ya kare.
Kofar kitchen din ta baya da take a buɗe ta shaida masa cewa fita tayi wajen, don haka ya nufi wajen kuma tun kafin ya ƙarasa ya hango ta, ta wanke wasu ƴan kananan dusters na kitchen ɗin tana shanya su a jikin igiyar da bai san lokacin da ta ɗaura ta ba.
Wannan rigar ce a jikinta, wannan rigar da bata rufe kafafunta ba, da safen nan bayan tayi wanka ya roke ta da Allah da ta saka don zuciyarsa ta gaji da hasashen kafafun nata da yake jin kamar ya shekara bai gansu ba, kuma da kyar ta yarda ta maida kayan da ta dauko ta saka din tana fadin ita ta bacci ce, abinda yasa shi tunanin zai siyo wanda ba na baccin ba kenan.
Amina ta shanya tawul na gaba a hannunta yayin da take jin zuciyarta tayi wani irin wasai a yau, farin cikinta na karuwa da kowanne wucewar lokaci idan ranta ya tuna abinda ya faru jiya, kokarin da tayi wajen hada al’ummar gidan nan kaf a gaban Ma’aruf bayan tashinsa, ciki har kuwa da mahaifiyarsa da sai dagabaya ma zuciyarta ta bata shawarar hakan, wani abu da ta san babu wanda bai ji dadinsa ba, don ko su Shukra kafin su tafi suna ta fadin zasu tambayi Ma’aruf ya barta tazo inda suke suma, yayin da Salma ke fadin cewa zata zo su saka labule, tayi ta binsu da murmushi kawai tana amsawa har suka tafi, Shahida ma matar Faruqa a jiyan kadai ta sake da ita har sunyi exchanging numbers, musamaman da ɗan ƙaramin ɗanta Aabid yaki kowa duk a tarin jama’ar nan ta jiya sai ita da kuma Inna Danejo… Har Innan na ta tsokanarsa cewa jinin tsofaffi ne dashi don wai tana da kishiya data rasu mai suna Amina.
Sannan ga Ma’aruf ma, yadda ya dinga yi mata jiya kadai ya isa ya shaida mata irin nasa jin dadin, don har godiyar yayi ta radawa a kunnenta, godiyar ma da daga baya ta kasa tantance gabadaya ta mecece. Yanzu babban abinda ya rage shine ta roke shi ya barta taje gidansu kafin Hajiya Kilishi ta sake ɗago da wani abun ko kuma ita ta cigaba da nata takun.
Don Allah ya sani tana kewar ƴanuwanta fiye da yadda zata iya misaltawa, shi yasa ko a jiyan da suka yi waya da Fati da kuma Maryam a wayar Fatin, bata ko sake yi musu zancen zuwansu ba, don ta yiwa kanta alkawarin da kanta zata zo sai dai su biyo ta daga baya.
A wanan lokacin ne kuma Ma’aruf ya karaso ta bayanta, ta san shine don a lokaci guda ya hanayensa zuro ta gefen cikinta duka biyun ya rungumota ta baya, fuskarsa ta sauka akan kafadarta guda ɗaya yayin da ɗumin fatarsa da kuma na hannayensa suka ratsa jikinta a take… Zazzabi ne kuma ya kama shi?
Babu shiri ta juyo da sauri tana kallonsa, sai yayi mata wani guntun murmushi sannan yasa yatsansa ɗaya yana taɓa gashinta da ya fito ta gaba kamar yana karkaɗe mata wani abun, a lokaci guda taji zuciyarta kamar ta fashe a kirjinta, dumin hannayensa ya shiga ratsa fatar goshinta yayin da numfashinta ya fara rawa a kirjinta, ta zata ta fara sabawa… Sai kawai ta buɗe baki tace.
“Zazzabi kake… yi?”
Ya girgiza kansa a hankali.
“Lafiya ta kalau, na gaya miki na warke tun jiya, ko baki yarda ba?”
Ta girgiza kanta itama.
“Jikin ka da zafi har yanzu.”
Sai kawai ya jawo duka hannayenta biyu dake ɗauke da kowanne dusters ɗin nan jikakku, ya kara su duka biyun akan kumatunsa sannan yace.
“Kina jin zafin har yanzu?”
Tayi wani guntun murmushi sannan ta girgiza kanta.
Ya cije lebbensa kaɗan.
“Na so kince A’a, don ina da wasu hanyoyin da zan nuna miki cewa lafiyata kalau BabyDoll.”
“Me yasa kake kirana haka nr?”
Yace.
“Saboda kina min kana dasu, wadanannan siraran ƴantsanan da nake gani su Sahla suna wasa dasu da.”
“Zanyi kiba kwanan nan, kar ka damu.”
“Da gaske?”
Ya tambaya ysna kara matso da fuskarsa kusa da tata.
“… Me zai saki kiyi kibar?”
Tana murmushi har yanzu ta ɗauke hannyenta daga fuskars ta dan ture shi baya ta kafadunsa sannan tace.
“Idan nayi zaka gani.”
Yayi baya ya dawo sannan ya girgiza kansa.
“Ki gaya min idan akwai gudunmawata kinga sai na fara shiryawa tun yanzu.”
Yadda yake maganar ya sata yin dariya kafin tayi kokarin juyawa a hankali don karasa shanyar na hannunta, amma ya dawo da ita.
“Seriously idan kiba kike so na san ta yadda zamu samo ta, kawai ki gaya min.”
Ganin da gaske yake yasa ta kara ture shi tana dariya.
“Nan fa waje ne, beside rana tana tayi ma bamu yi breakfast…”
Muryarta ta katse sanda ya dora goshinta a saman nata, idanunta suka shiga haskawa da mamaki da kuma tsoro tace.
“Wani zai iya shigowa fa…”
Ya girgiza kansa, motsin na tafiya da nata kan.
“I don’t care, let them… koma waye ban damu ba ‘cox i’m trying to find my inner peace here.” (Kwanciyar hankalina nake nema anan.)
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da ya sinkuyo da fuskarsa cikin wuyanta yayin da tasa duka hannayenta biyu masu rike da jikakkun duskter din nan ta riƙo gaban rigarsa saboda yadda take ji jikinta na rawa kamar zata fadi.
Kuma a daidai lokacin ne, wannan kofar bayan nan dake ɓullewa zuwa hanyar cikin gida ta buɗe, Hajiya Kilishi ta fara shigowa sanye da wani dogon hijabinta na sallah sannan ƙawarta Hajiya Salamatu ta biyo baya, daga bayansu, Sameera ce riƙe da wannan jakar Pink, yayin da Surayya ke binta ɗauke da Hamida.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
