Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    A cikin asibitin, daga cikin wani dogon korido mai ɗauke da kofofin kala-kala, Hajiya Kilishi na tsaye ita da Faruk yayin da daga gefenta kan kujerar masu jira na asibitin Amina ce ke zaune suna sauraren bayanin da Faruk din ke yi.
    “Wallahi Mami mun gama duk abinda zamu yi, munyi sallama lafiya kalau da shi har ma da wanda muka hadu dashi din, kowa ya hau mota muka rabu a wajen round about din nan, to ni nayo gaba kawai sai go slow ya tare ni kafin inyi nisa, anan naji wasu mashin da suka karaso suna hirar fadan da suka baro ana yi a baya, daya yana cewa wai ai ya san mai dukan sunansa Ma’aruf yana aiki tare damu a kamfani, naji yana bawa abokinsa labarin daya incident din a ya faru dashi da Daniel.
    Da kyar na fita da go-slown nan na koma, kuma lokacin da naje ma har an raba su an dawo da Ma’aruf din motarsa mutane suna ta rike shi, ina masa magana amma kamar bai gane ni a lokacin ba, shine na kira Ishaq, sai da ya karaso sannan da kyar yasa shi ya yarda ya baro wajen, amma tunda naje abu daya yake ta fada wai a barshi ya karasa kashe mutumin yana da sakon da zai bashi.”
    Hajiya Kilishi tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace.
    “Kuma ko bayan fitar tasa ma munyi waya sai kuma na kira shi daga baya bai dauka ba.”
    “Ai Mami gabadaya wayoyin nasa ma da wallet da komai an kwashe, da yake bude motar kawai yayi ya fita a lokaci guda, to a wannan hayaniyar ɓarayi suka samu dana suka kwashe komai, har mukullin motar sun tafi dashi, ita kanta motar ma don baza su iya dauka a lokacin bane.”
    “Tana ina yanzu?” Kai tsaye ta sake tambaya.
    “Tana wajen, nasa wasu dai sun tura ta zuwa gefen titi, sannan na basu kudi su kwana a ciki saboda ban ma san inda za’a nemo spare key dinsa a dauke ta ba.”
    Duk wannan bayanin da Faruk ke yi, Amina dake zaune daga kujerar baya ta masu zaman jira a asibitin idanunta na manne ne da kayan Faruk din, farar shadda ce a jikinsa wadda gabadaya gabanta ya ɓaci da jini har zuwa kowanne hannun na rigar, zuciyarta na bugawa da motsin dake shaida girman laifinta da a yanzu take ganinsa karara, yayin da kalaman ke yawo a cikin kanta, tana yarda da kowacce kalma ɗaya bayan daya dake maimaitawa daga cikinsu.
    Suna gaya mata cewa tabbas babu abinda dan adam zai samu a duniyar nan cikin sauƙi, sannan kuma babu wani abu da mutum ya kamata ya fito yayi takama dashi a duniyar nan, don ana zuwa gabar da rayuwa ba zata baka zabi ba, zaka zo kayi wani abu da ko a mafarki ba zaka taɓa tunanin aikata shi ba.
    A baya zata rantse da Alkur’ani wajen karyata duk wanda zai zo ya shaida mata cewar zata iya aikata wani abu najamancin wannan, amma sai gashi a yanzu da hannunta ba tare da tursasawar kowa ba tayi abinda take jin tambarinsa ya ɗarfanu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taba goguwa ba, don idan har za’a lissafa da sunanta a cikin wanda suke da kamasho a yau wajen faruwar wannan tashin hankalin, wajen zama sanadin da har mutane biyu ke kwance a asibiti, da kuma fitar jinin da take kallo har a jikin Faruk yanzu, to kuwa ta tabbata bata da kalaman da zasu wanke ta ko a gaban waye.
    “Ka ce bai ji ciwon sosai ba ko?” Sai a wannan lokacin muryar Mamin ta shiga kunnenta, tana tambayar Faruk din da ya gama amsa wata waya wafda da alama fuk akan abinda ya shafi al’amarin ne.
    Ya daga kansa sau daya.
    “Ba sosai ba, na wancan mutumin ne yafi yawa, tun a can muke fatan Allah yasa bai fasa masa ido ba, don dukansa yayi tayi Mami, yana cewa a kyale shi ya kashe wai yana da sakon da zai bashi.”
    “Inalillahi wainna ilaihir raju’in… Bari na kira Baffa.”
    Ta faɗa amon muryarta na fitowa da tsananin damuwar da babu wanda zai kasa shaida hakan, Amina ta bita da kallo baya ta juya ta bar wajen, kuma a wannan ya lokacin ne wata Nurse dake cikin ɗakin da suke jira a kofarsa ta fito, hannunta dauke da farantin kayan dressing wanda ya cika fal da tarin auduga mai jini.
    Idanun Amina ya sake bin hannunta da kallo har ta ɓacewa ganinsu, abinda take ji a ranta yayi yawa a lokacin don haka sai kawai ta damƙe hannayenta biyu duka waje daya ta a shirin kore kwallar dake taruwa a idanunta. Munaya wadda suka taho tare da ita ta karaso daga fitar da tayi tana gama waya da Hajiya Maimunan da ta sake kira tana tambayar halin da ake ciki.
    Taji sanda ta zauna a gefenta bayan tayi sallama da Hajiyan don haka ta juyo ta kalle ta.
    “Za’a barmu mu ganshi yanzu?”
    Sai ta girgiza kanta.
    “Wallahi ban sani ba, amma ko sun ce ma ai inaga Mami ce kadai zata shiga.”
    Idon Amina ya nuna da mamaki kafin ta tambaya.
    “Saboda me?”
    “Saboda idan yana wannan yanayin bai kamata aje kusa dashi ba, Mami ta fada mana hakan tuntuni.”
    Bakin Amina ne ya bude a lokaci guda, mamakin dake idonta ya karu tana kallonta.
    “Waye yake kula dashi kenan?”
    “Yaya Ishaq ne, yawanci ma ba anan suke zama ba, akwai asibitin da yake ganin likita a London, can suke tafiya sai ya sami sauki tukunna. Amma lokaci kadan ne, da mood din nasa ya dawo zaki ga koma daidai.”
    A lokaci guda sai taji hankalinta ya kasa ɗaukan maganganu da Munayan ke faɗa, kallonta kawai take yi yayin da take jin kamar kwakwalwarta na washewa, komai yana gogewa, don bata san yadda zata dauki wannan al’amarin ta ƙara akan sauran tarin abubuwan dake kanta ba.
    Tunaninta ya kasa lissafa wace irin zuciya ce da Hajiya Kilishi, a kowanne irin ma’auni na duniya ta rasa a wanne iri za’a dora zuciya irin ta Kilishi tayi kama da ta mutane… Abubuwan da ta aikata a rayuwarta kaf idan za’a tara su waje ɗaya bata jin duk raunin imanin mutum a duniyar nan za’a sami wanda zai kalla bai ji zuciyarsa ta motsa ba.
    Ta shigo cikin rayuwar mutanen nan da ƙarfi da yaji, ta gurgunta mahaifiyarsa, ta ƙwace shi daga gare ta, ta shuka tarin ƙananun abubuwa a cikin rayuwarsu da watakila ita kanta ba zata iya lissafawa ba, kuma duk da bata sani ba tana tunanin wataƙila itace sanadin ciwon nasa ma amma duk wannan bai ishe ta ba sai ta daƙile shi kuma a dukkan ɓangare na kulawa irin wannan.
    Bata san irin ciwon Ma’aruf ba, bata san komai game dashi ba, amma tayi imani cewar babu wani ciwo a duniyar nan da baya bukatar kulawa, ko da na hauka ne kuwa, to ta yaya za’a ce ayi nesa dashi a lokacin da yake tsananin bukatar kulawa?
    Farkon zuwanta gidan tana ganin komai ne daidai, tana sha’awar mu’malarsu da komai shaƙuwarsu na mata yawo a ido kodayaushe, amma sai a yanzu take ganin tarin ramukan dake gewaye dasu, sai yanzu take fahimtar cewa ba daidai komai yake tafiya ba kamar tunaninta.
    Mutane ne su masu hankali, ƴan boko kuma masu ilimi, amma Kilishi ta dauke su gabaɗaya ta sanya a wani rami da babu mai iya haurowa, tana daga sama sai iya amon muryarta da kuma umarninta kawai suke ji, suna yin dukkan abinda ta furta ba tare da sun sani ba, ba tare da sun san ma me saka su ba. Taji zuciyarta ta matse a lokaci guda wani abu a cikin kanta yana gaya mata cewa wannnan yana daya daga cikin abubuwan da zata fara canjawa.
    Tana jin Munayan na cigaba da waya da wata classmate dinta a lokacin, tana jin suna tattauna wani abu da ita ba fahimta take yi ba har sanda Mamin ta dawo, ta shiga gayawa Faruk da ya dawo cewar yaje gida ya canja kayansa, don mutanen dake wajen duk wanda zai wuce sai ya kalle shi, amma yace mata bari likitan ya fito tukunna su ji abinda zai ce, don har ga Allah baya jin zai iya tafiya ba tare da ya san halin da ma’aruf ke ciki ba.
    Zuciyarsa ta yage har karshe tun daga lokacin da yaga yadda yake rike Ma’aruf a wajen nan yana yi madmsa magana amma babu alamun ya a gane shi alhsli yanzu-yanzun nan suka rabu lafiya, lokacin da al’smarin Daniel din nan ya faru a Office zuciyarsa tana bada wani kamashon laifin ga Daniel din, yana ganin har da laifinsa wajen tunzura Na’aruf din, amma abinda ya gani yau, yafi karfin dukkan wani tunaninsa.
    Don haka yana tsaye har lokacin da Ishaq ya bude kofar wajen ya fito, kayan jikinsa kalar maroon ne amma duk da haka ana ganin inda ya samu nasa rabon ɓacin jinin shima.
    “Ishaq me ake ciki? Me suka ce?”
    Mami ce ta fara jero tambayoyin cikin zaƙuwa. Kuma da muryarsa a hankali kamar kodayaushe yace.
    “Mami ki kwantar da hankalinki, ciwonsa ne dai ya tashi, dama munyi sa’a ne kwana biyu mood din nasa ya saisaita, kuma ban san me ya tada shi yanzu haka a lokaci guda ba. Sai dai na yi musu duk bayanin da suka bukata kuma sun bude file sun rubuta hakan, yanzu an bashi alluran bacci yana hutawa.”
    “Abinda zasu iya yi masa kenan?” Ta tambaya.
    Ya gyada kansa.
    “Mami ai ko irin magungunan nasa na basu dasu anan, guda daya kawai aka samu, so na gaya musu zamu taho da na wajenmu zuwa gobe su kara duba su tukunna, ina tunanin insha Allah iya nan komai zai tsaya, ba sai mun koma London ba. Don allurar da suka yi masa ma iya ta zuwa gobe ce.”
    Hajiya Kilishi ta gyaɗa kanta alamun fahimta sannan ta sake furta kalmar inalillahi wainna ilaihir raji’un fuskarta na nunaea da abinda za’a kashe wani akansa cewar damuwa ce.
    “Likitan ya fita, yanzu zasu kaishi ɗakin da zai huta, sunce nambar dakin C0-9.”
    Mamin ta gyaɗa kanta.
    “Zamu je mu ganshi kafin mu tafi….”
    “Mami zan zauna.”
    Babu zato muryar Amina ta katse abinda Hajiyan Kilishin ke shirin fada. Dukkaninsu suka juyo suka kalle ta a lokaci guda, wani guntun mamaki ya haska a fuskar Hajiya Kilishi kafin tayi saurin kore shi da murmushi.
    “Toh shikenan, sai ki zauna zuwa gobe.”
    Ishaq ya gyaɗa kansa shima.
    “Zanje in ɗauko masa wasu kayan da za’a canja masa don waɗannan na jikinsa sun ɓaci. Sannan zuwa gobe zan dauko reports dinsa gabadaya na asibitin don na san familyn wancan mutumin zasu iya shigar da kara, dole ne mu sami backup a hannu.”
    Faruq ne ya fara gyaɗa kansa kafin yace.
    “Allah ya kaimu, I need to talk to you please kafin in wuce.” (Ina so muyi magana kafin mu wuce.)
    “Okay toh muje.” Cewar Ishaq din suna yin gaba.
    “Kin tabbata kina son ki zauna?”
    Munaya ta tambaya tana kallon Amina lokacin da wata Nurse ta karaso tana mikawa Hajiya Kilishi wasu takardu na ɗakin da aka kai Ma’arf ɗin, kuma tana jin wani abu kamar damuwa na yawo a cikin muryar tata.Sai ta gyada kai tana kallon hannayenta.
    “Babu abinda zai faru Munaya Insha Allah, bai kamata a barshi shi haka shi kaɗai bane ba.”
    Hajiya Kilishi ta juyo riƙe da takardun nan a hannunta ta miƙowa Munaya su.
    “Munaya je ki fara dubo mana dakin gamu nan.”
    Wannan karon muryarta ta fito da sanyi kalau, kamar na iskar wajen dake hurowa daga A.c, kuma Munayan bata yi tunanin komai ba ta mike tsaye ta karbi takardar amsawa da Toh.
    Hajiya Kilishi ta bita da kallo har ta bace a dogon koridon wajen sannan ta juyo ga Aminan da har yanzu kanta ke sunkuye a kasa tana wasa da yatsun hannunta.
    “Naji dadin abinda kika yi fiye da tunaninki Amina, na baki wannan aikin ne don in gwada hankali da kuma tunaninki ba wai don ba zan iya ba kin sani, kuma ba zan boye miki ba zuciyata ta yaba da irin hikimarki, musamman a yanzu da nazo naji cewa daga Mai gaskiya har wadannan abokan nasa basu san komai ba, shi kansa bai san cewar ya sha magani ba balle har ya dora zargi akanki.
    Na san zaki iya Amina, na san zaki iya tun daga ranar dana fara ganinki a duniya jikina ya bani hakan, shi yasa nayi amfani da Aminu na zaburar dake don ki fahimci cewa zaki iya din ba tare da kin bata min lokaci ba, amma kamar yadda na nuna miki ne, komai zai wuce kamar ba’ayi ba, zan sa ki manta da abun da ya faru dashi kwanan nan insha Allah.
    Shima Ma’aruf din zai tashi, kwana biyu ne dama wanda kafin nan na gama dukkan abinda zanyi akan RTL, don haka abu daya nake so dake yanzu, ki rage wannan damuwar dake kan fuskarki, kin riga kin shigo cikin tsarina Amina, kuma ni bana tafiya ina barin shaidar takuna a baya, ina wucewa ta cikin sahara ne ba tare dashi kansa yashin wajen ya san na taka ba. Kin fahimce ni?”
    RTL! Sune kalaman da Amina ta fara rikewa a cikin kanta kafin maganganun Amma su gufta cikin kanta.
    _ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba…_
    Me ya same ta ne? Me take shirin yi? Tayi saurin tambayar kanta, tayi komai, ta samu yardar Kilishi a yau kadai tun ba’aje ko’ina ba, sannan kuma a yau din tana neman tayi wasa da haka? Yawu ya zarce cikin maƙogwaronta babu shiri, Amma bata nan, hasali ma zata iya kirga iya lokutan da ta taba ganin Hajiya Kilishi a rayuwarta, amma kamar ta karance ta ne tsawon shekaru, dukkan maganganunta suna zuwa akan kowacce gaɓa na tunanin Kilishin. Saboda haka sai tayi saurin girgiza kanta sannan tace.
    “Mami, damuwata ba akan abinda ya faru take ba, tunanin nake yi idan har da gaske kike game da abinda kika fada akan Aminu, ina son ƴanuwana fiye da komai Mami, kuma zanyi komai kamar yadda kika fara gani yanzu indai akansu ne, shi yasa nake ta fatan samun saukin sa kamar yadda kika fada.”
    Ta fadi hakan bayan ta ɗago tana kallonta, kuma ga mamakinta sai kawai tayi murmushi mai kyallin dake tabowa har cikin idanunta kafin tace.
    “Kar ki damu Amina, kin riga yarda dani amma baki gama tabbatarwa bane, abinda nake so kawai shine ki kwantar da hankalinki, duk wata gaggawa bata ɓullewa ga nasara, don haka mu bi komai a hankali. Ina tabbatar miki da sannu zaki fahimci wacece Kilishi da kuma hukuncinta!”
    Amina ta kalle ta da nata guntun murmushin da a dole ya sauko kan sannan ta daga kanta kawai.
    _Ina tabbatar miki idan kika tsallake matakan farko Amina, komai zai zo miki bi da bi kuma saukake, yardarta kawai muke nema a yanzu._
    Tabas! kalaman Amma gaskiya ne, gwara da ta daure zuciyarta ta bi umarninta, don tun a yanzu ta fara fahimtar cewa babu wahala juya tunanin Kilishi,
    Taji zuciyarta na ƙara yarda da kalaman Amma na cewar kissa da dabara sune makamin kowacce mace a duniyar nan, ba namiji kadai ba, hatta mace ƴaruwarta yanzu zata ci galaba akanta da waɗannan abubuwan duk kuwa da irin takama da ikonta, ya danganta kawai daga yadda macen ta yarda ta bude kwakwalarta, ta yarda cewa Allah ya halitta mafitar kowacce matsalarta a cikin kwakwalwarta, kuma idan ta dogara dashi ta yarda cewar zaki iya ɗin, shikenan ta rusa dukkan wata katanga dake gabanta.
    Kuma lokacin da suka isa ɗakin, kwata-kwata su Mami basu fi minti biyar ba suka tafi bayan Mamin ta furta kalmar Allah ya sawwake sau daya, wadda ta san itama ta fada ne saboda Munayan dake tsaye, wadda ita kuma ta kasa dauke idonta daga kan Ma’aruf din tun bayan shigarsu, tana kallonta har sanda suka zo fita sai da ta waiwayo ta sake kallonsa.
    A wanan lokacin ne kuma zuciyarta ta kasa iya auna irin don da Hajiya Kilishi ke ikirarin taba yiwa Ma’aruf, duk da cewar ita kanta shaida ce, tana kaunarsa ta wata siga da babu mai iya kwatanta ta cikin hankali, don babu hankalin da zai yarda da so da kuma cuta a lokaci guda, ta yaya za’a yarda tana sonsa amma zuciyarta bata jin komai wajen cutar dashi? Ita gabadaya saninta dashi na yaushe ne, amma da yaya ta daure zuciyarta ta aikata komai kuma yanzu yaya take ji a ranta?
    Sai ta matsa a hankali zuwa gaban gadon bayan fitarsu, kuma da kowanne taku tana jin kamar tana tafiya ne da nauyin laifukanta a gabansa, laifukan da a yanzu zuciyarta ke shan alwashin gyaransu ta duk hanyar da ta san zata iya, tunda ta riga ta fara yin mai wuyar.
    Kafafunta suka tsaya a gaban gadon tana kallon fuskarsa, kuma yanayin yadda fuskar tasa tayi so innocent ya daki zuciyarta taji tana ƙoƙarin hadiye wani abu da ya kasa barin makogwaronta.
    Wasu abubuwan suna faruwa ne ba’a yadda bawa ya tsara su ba, wasu nasarorin suna samuwa bayan ka daure zuciyarka wajen aikata wani abu da kake da yakinin samun nasararsa a gaba.
    Gashin kansa a barbaje yake sosai, sannan fatar bakinsa ta rabu da ƴaruwarta ta yadda tana iya jin fitar numfashinsa ta duka hanci da baki daga inda take tsaye, sai ta tsugunna a hankali idanunta na cigaba da kallonsa.
    Kuma bata san ta yadda zata hana kanta ba sanda hannunta ya sauka akan gefen fuskar tasa, yatsanta daya ya taho a hankali daga gefen fuskarsa zuwa karshe, kumatunsa ba cikakken bane kuma ba ramamme ba kawai dai wani abu ne a tsakiyar hakan, da sauri ta janye hannunta ganin ta karasawa kusa da bakinsa sannan ta mike tsaye.
    Wayarta da ta ajiye akan kujerar dakin tun bayan shigowarsu taje ta dauko, missed din Amma har guda biyu ya shiga idonta. Bata san lokacin da ta kira va don wayar ta shiga silent,kuma dama ko bata kira din ba, ita take shirin kira don tun safe ya kamata ace sunyi wayar amma hayaniyar dawowar Inna Danejon nan ta ɗauke hankalinta.
    “Assalamu alaikum.”
    Muryar Amman da ta fito a hankali kuma cikin sanyinta kamar kodayaushe tasa ta jin kowacce tsigar jikinta na tashi, tasirin al’amarin na da kuma abinda tayi na kara kamata, ta rufe idanunta a hankali kafin ta iya tattaro dauriyarta ta fara gaishe ta, wanda bayan hakan ne dukkan sauran hirarsu ta biyo baya.
    Hirar da a cikinta kalaman Amman da kuma umarninta ya kara inginza zuciyarta, suna buɗe mata wani sabon kwarin gwiwar da bata san tana dashi a baya ba!
    ***
    *Washegari.*
    *07:30am.*
    “Doll…”
    Muryar ta shiga kunnenta a hankali, ta jiyo amonta kamar daga can nesa, kamar a cikin wani fili da ita take ƙarshensa muryar kuma tana daya karshen, don haka bata motsa ba ta tsaya a hankali tana saurare ko zata kara jinta,bdon bata yarda cewar wanda take tunani zai kira ta da hakan a halin da yake ciki ba. Ilai kuwa bayan sakan daya biyu kuwa sai amon ya sake cika kunnenta da wannan sabon suna da a duniya kaf ta san mutum daya ne ya taba gaya mata.
    Babu shiri ta bude idanunta, amma hasken da ya shiga cikinsu a lokaci guda ya hana ta ganin komai, sai da ta maida shi ta rufe tasa hannunta ta mutsikka sannan ganin nata ya dawo daidai, a cikin ɗakin asibitin nan ne, don kafar gadon da take fuskanta itace abu na farko da ya tuna mata cewa tana kwance ne akan carpet din dakin tun bayan da tayi sallar Asuba kuma ta gama yiwa Ma’aruf dukkan addu’o’in da Amma ta shaida mata jiya a wayarsu.
    “Doll…”
    Muryar Ma’aruf da ya kira ta yasa idonta ya kai kansa a lokaci guda, yana kwance irin yadda take ta gefe daya a saman gadon, idanunsa duka a buɗe suke kallonta.
    Mamaki ya ratsa ilahirin jikinta gabaɗaya don bayan dawowar Ishaq jiya da daddare yace mata likitocin sun ce ba lallai a yau ma a samu ya farka ba don allurar tana da karfi sosai, sai kuma ta tuno addu’o’in da tayi har bacci ya dauke ra, a lokaci guda tajintana kara yabawa ƙudira da kuma ikon ubangiji, don haka ba shiri ta mike zaune kuma bata jira komai ba ta ja ƙafafunta ta ƙarasa gabansa.
    “Why are we here?” (Me yasa muke anan?)
    Ya tambaya amon muryarsa na fitowa a hankali yayin da yake kallonta, gashinsa a barbaje kamar yadda yake tun jiya sannan idanunsa ke lumshewa alamun fada yake yi da kansa wajen bude idon. Tausayinsa da ta kwana dashi a cikin zuciyarta ya sake tasowa a ranta, taga idonta na nuna mata cewa kamar ya rame daga jiya zuwa yau kaɗai.
    Tasa hannunta a hankali ta gyara dankwalinta da yayi baya da yawa, ta jawo shi ta rufe gashinta sannan tace.
    “Baka da lafiya, jiya su Ishaq suka kawo ka.”
    Taji muryar tata ta fito kamar wani yana karta farce akan katako don haka ta shiga kokarin yin gyaran murya kadan sanda ya girgiza kansa a hankali.
    “I don’t want to be here.” (Bana son zama anan.)
    Ta daga kanta a lokaci guda.
    “Tohm, bari nayi wa Nurses din magana su zo sai mu tafi gida.”
    Ta fadi haka da niyyar mikewa amma a lokaci guda ya kamo hannunta, taji yatsunsa da suka dauka dsuka da sanyin A.cn sun ratsa sun nad hannun nata, numfashinta ya dan katse a kirjinta kafin ta dawo ta tsugunna akan gwiwoyinta sanda idanunsa sun sake rufewa.
    “Kar ki kira su.”
    Bata ce komai ba, yayi ƙoƙarin sake bude idonsa sannan yace.
    “Ina wayata?”
    Tambayar tasa a lokaci guda ta tuna abinda Faruk ya fada a jiya cewa an dauke duka wayoyin nasa har dasu wallet, don haka sai kawai tace bata san inda take ba, ya sake yin shiru yana kallonta, lumsassaun idanunsa suka tsaya akanta ba tare da yace komai ko kuma ya kifta su ba, zuciyarta ta shiga tsere a kirjinta, don duk da ta san rashin lafiya ce tasa idanunsa suka koma hakan, tana jin tasirin yanayinsu har kasan zuciyarta.
    “Kin goge numbers ɗin nan?”
    Ya sake tambaya a hankali, tayi shiru na wasu sakanni tana son ta tuno wadanne nambobi yake fada kafin ta tuna ranar da yace mata ta kwashe wasu nambobi daga wayar da ya bata zuwa ta hannunsa lokacin da suna hanyar dawowa daga jigawa.
    “A’a suna nan a cikin wayar har yanzu.” Ta faɗa a hankali, kamar idan ta ɗaga muryar tata tana tsoron zata fama masa wani ciwon ne.
    Kuma saboda kokari sai da ya daga kansa sau biyu sannan yace.
    “Akwai number Ishaq a ciki, ki kira shi kice masa yazo ya fitar dani daga nan.”
    Ta daga kanta sau daya sannan tayi kokarin zare hannunta daga cikin nasa a hankali kafin ta mike yayin da ya maida idanunsa ya sake rufe du.
    Akan kujerar dakin ta ajiye wayar tun bayan da alarm din Asuba ya tashe ta, don haka ta dauko ta ta shiga nenan nambar Ishaq din. Bugu daya biyu, uku aka dauka.
    “Ma’aruf…”
    Taji muryarsa ta kira sunan da manaki da kuma kuma kokwanto bayan saurin dske cikinta. Sai idonta ta koma kan Ma’aruf din da har yanzu idanunsa ke rufe sannan tace.
    “Ba shi bane, amma dai ya farka.”
    Jin muryar tata yasa taji kamar yayi ajiyar zuciya kafin ya sake tambaya.
    “Kin tabbata ya farka?”
    Ta daga kanta.
    “Eh, shi yace in kira ka ma kazo ka maida shi gida, yace baya son zama anan.”
    “Kin kira Nurses din wajen?”
    “A’a kai yace in fara kira tukunna.”
    Yayi shiru na wasu daƙiƙai kafin yace.
    “Bashi wayar.”
    Sai ta taso a hankali ƙafafunta na taka laushin carpet ɗin wajen kafin ta isa ta tsugunna daidai gabansa, kuma kamar yaji ta ya sake buɗe idanunsa wannan karin sosai a cikin nata.
    “Zaiyi magana da kai.” Bata san lokacin da fatar bakinta ta fadi hakan ba.
    “Kin gaya masa abinda nace?”
    Har yanzu sautin muryarsa a hankali yake fitowa, ta daga kai tana kasa janye idanunta daga cikin nasan, sai yace.
    “Ki kashe wayar kawai.”
    Ta dan tsaya kaɗan don ta tabbata Ishaq din daje cikin wayar yaji, amma ga mamakinta sai kawai taji shima yace.
    “Rabu dashi gani nan zuwa.”
    Daga haka bai kara cewa komai ba kiran ya katse. Ta ajiye watar a gefe tana ganin yadda fatar idanun nasa ke sauka a hankali girmansu na kara raguwa, amma kuma duk da haka ita yake kallo.
    “Zaka ci wani abun? Ko tea?” Ta tambaya tana ganin wautar ta, don a yanayinsa kowa ya kalle shi ya san bai gama dawowa haiyacinsa ba, kuma sai ya sake girgiza mata kansa sannan yace.
    “Just stay Amina…”
    Abinda ya fada kenan kafin idanun nasa su ƙara rufewa a lokaci guda, ta tsaya kusan sakanni biyar tana kallonsa kafin tajo tana son sake rike hannun nasa, don bata san me zata yi ba ma idan ta tashi.
    Don haka haka ta miƙo shi ta riko nasa a hankali, kuma ga mamakinta sai taji ya kara rike su shima, yana ratsa yatsunsa tsakanin nata sanyin dake jikinsu ya ratsa farar ta kamar dazu, sai kawai ta matso da kanta ta kwantar dashi a gefe gadon itama, tana kallon fuskarsa yayin da idanunta ke ƙiftawa a hankali.
    ***
    *Awanni biyu bayan hakan.*
    “Mami ni na san Ma’aruf, wallahi idan ya farka ya sake ganinsa a wajen nan abinda zai biyo baya zai fi muni akan wanda ya faru jiya.”
    Ishaq ya fada lokacin da yake tsaye a kofar dakin, yayin da daga ciki wasu Nurses ne guda uku matsbiyu da namji daya ke kokarin dora Ma’aruf akan wani gado mai taya da za’a fita dashi.
    Amina na tsaye daga gefensu riƙe da jakar ƴan kayayyakin da aka kawo musu idonta yabi hannun ɗaya Nurse din da ta riko kansa da kallo, tana kallon yadda hannunta ya nutse cikin gashin kansa, wani abu ya motsa a cikin zuciyarta.
    Sai kawai ta juya tana sauraren Ishaq ɗin dake cigaba da yiwa Mami bayanin da yasa dole ya nemi sallamar wa Ma’aruf, yana rokonta akan ta kira Baffa tayi masa bayani akan cewar ya bari a dawo da Ma’aruf gida don yanzu suka gama waya dashi yan fadan cewar don me ya biyewa Ma’aruf ɗin yace a sallame shi, saboda kawai yace baya son zama a asibitin.
    Kuma bai sani bane amma ita kanta Mamin bata so hakan ba, da zata sami dama nata ƙorafin zata yi itama. Don kamar yadda ta faɗa mata a yau ne zata aiwatar da koma meye kudirinta, kuma abu na karshe da zata so shine ace Ma’aruf baiyi nisan daga gare ta ba ta yadda ba zai iya kawo mata giftawar wata matsala ba komai kankantar ta.
    Ta maida wayarta jaka lokacin da Nurses din nan suka shiga tura gadon da suka ɗora Ma’aruf ɗin dake bacci har yanzu, don tun bayan wannan farkawar, bai kara bude idanunsa ba.
    “Amina.”
    Muryar Ishaq da ya karaso cikin ɗakin bayan fitar Nurses fin tasa ta dawo dq hankalinta kansa.
    “Bai ce miki komai ba bayan sakon da kika bani lokacin da ya farka?”
    Ta girgiza kanta a hankali.
    “Cewa kawai yayi in gaya maka kazo ka fitar dashi, kuma bayan kiran ya katse ma bai sake cewa komai ba.”
    Ta gyada kansa yana maida wayarsa cikin aljihu.
    Shiru ya ratsa na dakika biyu kawsi kagin ymuryarsa ta sake fitowa.
    “Mun gode sosai da abinda kika yi Amina, this is the first time da wani ya taba zama da Ma’aruf a irin wannan yanayin bayan ni.”
    Bata san me zata ce ba, don haka ta gyada kanta a hankali tana kallon jakar hannunta da ta rike. Ya juya ya fita daga dakin har a lokacin bata dago ba, rayawa take a zuciyarta cewa idan har daga yanzu za’a fara yi mata godiya akan duk abinda zata yi, watakila za’a zo lokacin da za’a rasa wajen ajiye godiyar ma.
    ****
    Hajiya kilishi ta tsirawa sakon da ya shigo wayarta ta nambar Awwalu ido, ta karanta ta sake karanta yadda yake gaya mata dukkan tsarindu ya tafi daidsi lokaci kawai yske jiracda kira ta kafin wani irin murmushi ya subuce a bakinta.
    Me yasa take mantawa ne wai? Itace fa, itace wannan Kilishin da ba ta taba saka abu a gaba bata cimmasa ba, to don me kuma a yanzu take iya saka kokwanto a ranta? Me yasa take yiwa komai tunani biyu bayan gashi Aminar ma ta riga ta sami kanta.
    _Saboda faruwar komai yana sauri da yawa…_
    Wani gefen tunaninta ya ambata mata amma sai tayi cilli dashi gefen da ya fito a lokaci guda, ai yarinyar ta gama tsorata da ita ta sani, ta gaya mata cewar taɓa dan’uwanta da tayi ba karamin abu bane da ba za ta so a sake irinsa ba, don haka ta riga ta gama yarda da ita, tunda har ta iya aikata wannan umarnin da ta bata a kudundune, umarnin da yaci sunan lauje cikin nadi, amma kuma tsaf cikin hikimarta ta ware nadin ta fidda laujen cikin sauki.
    Don haka bata da sauran matsala ta sani, ko an dawo da Ma’aruf gidan umarni kawai zata bata na cewar kar ta sake ta bari ya fito, da wannan ta san zasu iya gama komai ita da Awwalu kafin jibi, tunda ko Baffa sai gobe zasu dawo suma.
    Ta sake wani murmushin a hankali tana hango lissafinta. Tazarar fa kaɗan ce, saura kaɗan su ƙarasa ga ƙarshe inda komai zai fashe, taji tana taya Amina murnar shigowa cikinsu, don wahalar da zata yi kadan ce, ita da Awwalu sun daɗe suna tsarawa da gina komai bi da bi.
    Wayarta tayi kara a lokacin, Awwalu ne, ta dauka ta kara a kunnenta,
    “Hajiya ki fito yanzu komai ya kammala.”
    Ta gyada kanta ba tare da ta amsa a fili ba.
    Ta kashe wayar tana wani murmushi sannan ta jawo mayafinta, ita da dawowa gidan kuma sai lokacin da ta kammala kaso mafi yawa na cikar burinta.
    Abinda bata sani ba shine, ubangiji ya kadarta tafiyarta a wannan lokacin ne don faruwar wani abu da tunaninta bai taba hango mata ba.
    ****
    *Karfe biyar da rabi na wannan ranar.*
    Karo na farko a rayuwar Ma’aruf da ya taɓa bude idanunsa cikin irin wannan yanayin yaga ƴanuwansa zagaye dashi fal, Awa kusan uku kenan tun bayan farkawarsa amma har yanzu zuciyarsa ta kasa ƙarasa yarda da ganinsu gabadaya tare dashi kuma ba a ko’ina ba a cikin gidansa.
    Samira ce ta gaya masa cewar Amina ce ta sanar dasu an dawo gida don haka tun da rana kafin ya farka suka zo har dasu Salma, Shukra da Safiyya wanda suka zo a ranar, ga dadin dadawa Inna Danejo da itama Mama Rabi ta rako ta tun daga cikin gidan har nan.
    Tana zaune daga gefensa inda aka kwantar dashi a falon tana ta karanto tarin addu’o’i daga cikin carbin ta take ja tana gaya masa cewar rubutu zata sa ayi masa na Alkur’ani gabaɗaya don ita ta gaji da yawan maganin asibitin da har yau bata ga amfaninsa ba.
    Kuma tun da Ma’aruf yake a rayuwarsa, tun daga lokacin da ya sami ciwon nan, idan har bashi da lafiya ya sani cewar sai dai ya farka ya ganshi a London asibiti ko kuma tare da Ishaq a gefensa.
    Ko lokacin da yana tare da Rukayya baya bude idonsa ya ganshi a gida kuma ko shi a baya bai taba ganin wani abu game da hakan ba, don idan ba zai manta ba a cikin hira Mami tasha gaya masa cewar hakan shine daidai, bai kamata ya dinga mu’amalantar kowa ba har sai yanayinsa ya sauko ya daidaita.
    Shi yasa a karo na farko da ya farka a yanzu yaga mutane zagaye dashi sai yake jin wani iri a zuciyarsa, wani irin yanayi da bai san dame zai fassara shi ba, kallonsu kawai yake yi tun bayan da ya bude idanun nasa, kowanne da murmushi a fuskarsa suna tambayar lafiyarsa da kuma yadda yake ji.
    “Ya MB kace min ka warke dan Allah, ni ban san haka ciwon ka yake ba wallahi, ban taba ganinka a haka ba.”
    Shukra ta fada tana gyara glasses din dake fuskarta tana kallonsa. Kuma sunan da ta kira shi dashi ya tuna masa da dadewar da yayi bai gansu ba tun bayan aurensu, ya san dai kowaccensu ta kira shi sau daya sun gaisa amma bai kara jinsu ba bayan hakan, dukkaninsu sun canja, musamman Safiyya da tayi wata irin kiba a watanni biyu kawai tana gaya masa cewar da wuri zasu tsufar dashi idan ska kalle su aka cewa su kannensa ne.
    Kuma maimakon ya bata amsar abinda ta tambaya sai kawai yace.
    “Ya project work ɗin naki kuwa Kin gama?”
    “This is your answer ya warke kenan, don ni na tabbata da yace miki da sauki to wallahi Yaya bai warke ba.”
    Cewar Salma tana karasowa rike da kwanon furar da Inna Danejo tasa taje har bangarenta ta dauko shi. ta zubo wani potate ɗin dankali a ciki daga kitchen, tana karasowar kuwa Inna Danejo dake gefensa ta karba tana fadin.
    “Muhammadu juyo nan kasha wannan, na gaya maka ni ban yarda da wannan she*gen ruwan da ake sawa ba ace wai shima abinci ne, gashi nan tunda ka farka ai kake ta shan ruwa da yana aiki ai ko shi ba zaka nema ba.”
    Ya juyo ya kalleta, ta debo abincin da niyyar bashi, sai kawai ya girgiza kansa yace.
    “Ni ba haka matata take bani abinci ba.”
    Su Salma suka kyalkyake da dariya ba shiri yayin da kafin Inna Danejo ta kai karshen salatin ta Surayya ta shigo tana fadin cewar ga wani likitan nan ya karaso da sakon cewar Baffa ne ya turo shi, don a dazu bayan farkawarsa sun yi waya da Baffan har ma da Baba Usman suna tambayar yaya jikin nasa, kuma a cikin muryarsu kaɗai ya fahimci su ma sunji dadin yadda wannan karon ciwon nasa bai tsawaita ba.
    Inna Danejo ta ajiye farantin hannunta tana fadin ace masa ya shigo, Ma’aruf ya juyo yana ce mata ta bashi furar tace ai kuma yayi wa kansa kenan ya zauna da yunwar cikinsa idan matar tasa tazo ta bashi.
    A lokacin ne kuma yadso ya tambayi inda Aminan take don tun bayan lokacin da ya farka sau daya ya ganta sanda da ta kawo masa ruwan farko da ya tambaya, amma kafin ya bude baki Shukra ta matso tana dariya ta ɗauki plate din tana faɗin ita zata bashi.
    A lokacin ne kuma Zahra da Sahla da suka fito daga hanyar koridon dakunan gidan.
    “Ina Aunty Amina?”
    Suka tambaya a tare muryarsu na shaida murna.
    “Me kuka je kuka yi mata a daki?”
    Safiyya ce mai tambayar tana kallon hannun Sahla data boye a baya.
    “Babu komai, kawai tambayarta zamu yi wani abu.”
    Salma ta kalle su tace.
    “Makaryatan banza ai idan bincike ne kun iya shi, na gaya muku duk ranar da zaku zo gidana walkahi ku gaya min kulle koina zanyi ku zauna a falo.
    Munaya dake zaune a gefe ta kalle ta.
    “Har yanzu baki san abinda ke tsakaninku da Samirah bane, shi yasa kike ganin na wadannan yaran wani abu suke yi.”
    Da sauri Salman ta juyo tana rokonta ta gaya mata abinda Samiran ta daukar mata amma tace ita ba zata fada ba ba, ta bari duk ranar da Allah ya tashi tona mata asiri zata gani da kanta yayin da Inna Danejo ke fadan hada husuma babu kyau.
    “Wai ina Samiran ne ma, ni tazo in bata sakon cupcakes.”
    Safiyya ta tambaya daidai lokacin da Surayya ta shigo tare dasu Faruk da kuma likitan nan, hannunta na dauke wani dan karamin yaro da a lokaci guda Ma’aruf ya gane cewar Aarif ne ɗan gidan Faruk, kuma bai gama tunanin ba Shaida natar Faruk din ta shigo biye da sauran ƴaƴansu biyu mace da namiji.
    “Yaya, su Aunty Shaida ne duka zo.”
    Cewar Surayyan kasancewar dama ita tun da ta san Shaidar don yayar ƙawarta ce.
    Kowa ya amsa sallamar su da fara’a yayin da Munaya ta taso a lokaci guda tana kokarin daukar Aarif din dake ta mika hannu zai koma wajen mamansa alamun kyuiya yake yi.
    Shahida ta karaso har gaban Inna Danejo tana gaishe ta yayin da likitan nan ke kokarin cire allurar drip din daje hannun Ma’aruf din, shima ta gaishe shi sannan ta gaya masa cewa Faruq din yana waje tare da Ishaq wanda shima ya karaso a lokacin.
    Da haka ta juya wajensu Safiyya tana gaishe su da tambayar Yaya mai jiki. Tambayar da tasa sai a lokacin hankalin kowa ya lura cewar Amina bata wajen kuma kowa ya tabbatar da cewar bai ga lokacin da ta fita ba.
    Sai dai kafin hakan ya kai ga nisa, kofar falon ta bude, kuma Aminan da ake nema ta shigo a lokacin tare da Samiran da suka fita tare, sai dai duk wanda ke ɗakin basu yake kallo a lokacin ba.
    Wadda ke zaune akan kujerar da Samira ta turo zuwa cikin falon a hankali ce… Hajiya Maimuna.
    Shiru ne ya ratsa ilahirin falon a lokaci guda kafin kowannesu ya rufe da kiran sunanta, hatta Inna Danejo sai da tayi murmushi tana kallonta, don a tarin jama’ar gidan kaf, kowa ya san kawaici irin na Hajiya Maimuna, ba karamin kokari Amina da Samira suka yi na sawa tazo ba, tunda tun rana ta san inda dukkaninsu suka taho amna bata ce zata zo ba.
    Ma’aruf ya kasa rufe bakinsa a lokacin da yake kallon Hajiya Maimunan dake Samirah ke turota tana karasowa gabansa. Keken tayar ya hawo har kan carpet din ta iso daidai gabansa da kuma Inna Danejo wadda ke fadin taso Baffa yana gari yau yaga Maimuna a gidan Ma’aruf, don ko sanda yana tare da Rukayya har suka rabu bata taba takawa gidansa ba.
    A lokaci guda wani abu kamar kwallar da bai san dalilinta ba ta cika idanunsa lokacin da Hajiya Maimunan ta gama gaishe da Inna Danejo ta juyo tana tambayar yaya jikin nasa, bai ma san da wadanne irin kalamai ya amsawa tambayarta ba, ya san kawai a wannan lokacin idanunsa na kallon Amina ne dake can tsaye a baya da murmushi a fuskarta tana gaisawa da Shahida tana kuma kokarin daukar Aarif da ya gudo daga hannun su Munaya ya koma wajen Shahidan.
    Zuciyarsa yaji tana gaya masa cewa ko da iya wannan alkhairin nata na yau kaɗai, zai kyautata duniyarta da dukkan iyawarsa.
    ***
    *Ƙarfe tara da rabi na dare.*
    Kowa ya tafi a lokacin, hatta su Ishaq bayan ya takura musu sun shaida masa dukkan abubuwan da yayi missing dinsu a ranar, farko shine shari’ar Hamida da shi kansa ya manta da ita a yau,Ishaq din ya gaya masa cewar yaje ya dauko yarinyar ya tafi da ita kotun, kuma duk iya kokarinsa a gaban Alkalin, ba’a je koina ba alkalin ya yanke hukunci da cewar yarinyar ta koma wajen mahaifiyarta idan yaso tunda ya bada uzurin mahaifin nata bashi da lafiya, ya yanke hukunci cewar duk sanda ya warke zai iya sake shigar da kara sai a zauna a sake tattaunawa.
    Na biyu kuma shine zancen haduwarsa da mutanen RTL din nan, Faruq ya gaya masa cewar babu yadda baiyi yayi contacting mutanen ba amma ya kasa samun su kuma suma basu ce masa komai ba. Sannan Ishaq ya shaida masa cewayasa snyi deactivating gabaɗaya cards dinsa da aka ɗauke kuma barayin basu sami danar fitar da komai ba.
    Har suka tafi Faruk yana ta kokarin ya kwantar da hankalinsa akan cewar ya san ba wani issue ne babba ba amma har suka kammala zancen suka tafi jikinsa bai bashi haka ba, kawai ya ajiye zancen ne a gefe sanin cewar idan ya saka a ransa tabbas abin zai hadu ya dame shi tunda wancan case din ma har yanzu basu karasa shi ba, don haka ya hakura ya barwa karin samun saukinsa komai.
    A yanzu gidan daga shi sai Amina ne, kowa ya tafi, su Salma tare suka koma cikin gida tare dasu Inna kuma ya san zuwa yanzu ma duk sun tafi. Kuma Hajiya Maimuna da har ta tafi fara’ar fuskarta bata ɓoyowa, kuma yana jin sanda taje ta addu’a da sawa Amina albarka daga can bakin kofa inda suke sallama.
    Hatta Faruk sai bayan da suka yi sallar Isha ma sannan suka tafi don suna ta hira tare da Ishaq, yayin da Amina ke tare da Shahida a kitchen don dukkaninsu basu tafi ba sai bayan da suka ci abincin dare, har Samira ta dawo daukan wayarta da ta manta tana ta korafin me yasa basu kirata ta taya su ba.
    A yanzu fitowarsa kenan daga wanka yanzu tunda ya samu a dazu sunyi jam’in sallah tare dasu Ishaq.
    Yana zaune daga bakin gadon dake dakinsa, safa yake kokarin sakawa a ƙafarsa saboda sanyin da yake ji yayin da zuciyarsa ke kara hasaso dukkan abinda ya faru a yau yana ganin kamar a wata guda akayi komai ba yau kadai ba.
    Kofar ɗakin ta buɗe a hankali, ya juyo da kansa lokacin da Amina ta shigo hannunta dauke da wani dan madaidaicin tray a hannuta.
    Tun bayan tafiyar kowa bai ganta ba, kuma tun a adibitin nan da ya farka yace ta kira masa Ishaq basu kara magana ba, jayan jikinta suka shaida masa cewa itama tayi shirin ba ci don doguwar riaga a jikinta wadda bara sauka sosai, ba, wani abu acikin kansa ya shiga gaya masa cewa yana missing wadannan siraran kafafun nata kamar me.
    Ta karaso gabansa a hankali, idanunsa na kallon kowanne takunta, kaginnya maida su fuskarta.
    “Yaya ka kara ji da sauki?”
    Muryarta ta tambaya kamar wani abu dake tashi sama a hankali.
    Kuma baiyi tunanin komai ba yace.
    “Ke kike ta bani reason din da nake jin saukin ai.”
    Sai kawai tayi murmushi kaɗan sannan ta tsugunna a gabansa, ta durkushe kafafunta daga ganinsa, hannunta ya buɗe plate guda ɗayan dake kan tray din tana fadin.
    “Na san yanzu zaka iya cin wani abu ko?”
    Bai amsa ba ta sake cewa.
    “Inna Danejo tace kar in bari ka kwanta haka baka ci wani abu.”
    Ta karasa sanda ta saka cokali a cikin plate din hadadden potate din dankali da alaiyahun dake ta ƙamshi a hancinsa.
    Ta dago ta kalle shi, har yanzu idanunsa na kanta, kuma ga mamakinta sai taga kawai ya sauko kasan shima ya zauna daidai gabanta, sannan ya riko hannunta daya da bata rike plate din dashi ba, kamar koyaushe ya ratsa yatsunsa a tsakanin nata. Ta kalli hannun nata daya rike ba tare da tace komai ba sannan ta ɗebo abincin ta shiga bashi, yana ci tana gaya masa yadda akayi kafin likitocin asibitin nan su sallame shi.
    Kuma bayan sun gama ne yace ta dauko masa wasu magungunan gargajiya da ya taba siya ya ajiye a saman drawer dakin, kamar zata iya sai da taje gaban drawer sannan taga da saura dosai kafin tsawonta ya Kai, don haka ta shiga neman abinda zata taka, amma kafin ta motsa tajinsanda ya karaso daidai bayanta sannan kai tsaye hannayensa duka biyu suka zagayo ta kasan cikinta kuma kafin ya hade su waje daya tana jin irin rawar da suke yi alamun har yanzu jikinsa bai gama kwarin da zai tsaya haka ba.
    Don haka bata san lokacin da ta juyo ta fuskance ba da sauri idanunta na haskawa da mamaki.
    “Me yasa ka taso? Zan iya daukowa fa…”
    Sai ya girgiza kansa yana sake rike ta a jikinsa.
    “I want to talk to you.”
    Har yanzu ji take yi kamar basu gama tsayawa daidai ba don haka tasa hannunta duka biyu ta rike gaban rigarsa kadan tana cigaba da kallonsa, kuma bata ce komai ba ya cigaba.
    “I’m sorry game da abinda ya faru Amina, I’m sorry for how you saw me, (Ki yi hakurin yadda kika ganni) Na gaya miki dama I’m a mess…”
    Sai tayi saurin girgiza nata kan itama tana cigaba da kallonsa.
    “You dont need to be, lafiya da rashinta ba mallakin kowa bace, Allah yana bamu ita ne a lokacin da ya ga dama ya kuma karɓe ta a lokacin da yake so don wanke zunubanmu, saboda haka ba kaifinka bane, ba laifin kowa bane, don kowan bai wuce ya wayi gari shima an karbi tasa ta wata sigar ba.
    Insha Allah abinda ya same ka kaffara ne ga wasu abubuwan da ba lallai ka san dasu ba ma. Don haka daga kai har mu ba abinda zamu yi da ya wuce addu’a kamar yadda kowa da ya taru anan yayi tayi maka…”
    Tayi shiru tana kallonsa kafin ta karasa a hankali.
    “… abinda kake bukata kenan.”
    Taji hannayensa sun sake rike ta sosai kafin ya karadso da fuskarsa a hankali ya dora goshinsa akan nata.
    “Ban san me zan ce miki ba Amina, duk abinda kike yi, duk kike fada yana wuce dukkan tunanina, bana jin a duniyar na bayan Mami akwai wanda yake fahimtata yanzu sama dake.”
    Ambatar sunan Hajiya Kilishi da yayi yasa numfashinta yin rawa kafin ta rufe idanunta a hankali, tana jin nasa numfashin shima na sauka akan fatarta, sai kawai ta tatraro dukkan dauriyarta tace.
    “Nima bana son kowa yafi ni fahimtarka, nafi son na zama mutum ta farko da zaka nema a kowanne lokaci walau na ɓacin rai ko farin ciki.”
    Bata sani ba ko kallonta yake yi amma taji sanda ya kara rike ta a jikinsa yana gaya mata dukkan wasu kalaman godiya, sai kawai ta ture dukkan wani tunanin a cikin kanta a lokacin ta mika hannunta daga saman kirjinsa zuwa bayan wuyansa, ta rike shi kwatankwacin yadda shima ya rike ta. Wani abu da ya bashi mamaki don taji sanda ya dantsaya a cikin hannayen nata kafin ya kira wannan sunan nata a hankali.
    “Doll…”
    Kafin tama yi tunanin amsawar yace.
    “Wannan ma yana daya daga cikin amsata na ranar?”
    Ya rufe bakinsa daidai sanda ta daga kanta alamun amsa, taji yayi wani murmushin mai sauti sannan ya matsar da fuskar sa kadan daidai saitin kunnenta ya rada abinda a lokaci guda ya sata dunƙule yatsun kafarta akan tiles din dakin.
    “I want to kiss you again dan Allah…”
    Ya faɗi hakan sannan ya janye fuskarta daga tata, yayi baya sosai yana kallonta. Amina taji lebbenta ya shiga rawa tare da hannayenta sai kawai ta ƙara tsawon kafarta a lokaci guda, ta kai fuskarta daidai gefen tasa kuma ba tare da jiran komai ba tayi pecking gefen kumatunsa.
    Ta sake jin sautin murmushinsa kafin ya kara sunkuyowa cikin fuskar tata ya kwaikwayi sak abinda tayi yayin da take jin murmushinsa akan fatarta, kuma sai da ya matso dab da bakinta sannan ya tsaya, wani abu da yasa a lokaci guda ta buɗe idanunta tana kallonsa.
    “I want to ask you something? (So nake in tambaye ki wani abu.)
    Kafin ta amsa yace.
    “Naga kin fara kwarewa a wannan karatun, shekarar ki nawa? ‘Cox I don’t want us to stop, bana so mu tsaya kuma bana so a kama ni da laifin child abuse.”
    Amina bata san lokacin da bakinta ya subuce da wata irin dariya ba, ta rufe idanunta gabaɗaya sautin dariyar na fitowa tare da tsananin kunyar da maganganun dake lulluɓe ta.
    ****
    _Wani abu yana shirin konewa anan.😅🥰🤩_
    _Ina kuke tunanin Hajiya Kilishi ta tafi ne?_
    _Me suka shirya ita da Awwalu?_
    _Ruƙayya da mahaifiyarta sun samu nasara, Hamida ta koma wajensu, kun tuna mataki na biyu a tsarinsu?_
    _Yaya kuka ga kokarin Amina na farko wajen hada kan gidan Alhaji Muhammad Mansour Bakori?_
    Sai naji dukkan sharhinku..🥰😍🙏
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!