Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    A bakin titi ne, daidai bayan dogon banki wajen da Babu mutane sosai musamman a safiya irin haks, motar da Hajiya Kilishi da kuma Awwalu take tana daka fake a gefen titi an zuge duka gilasanta da bakin tint mai duhun gaske, don musamman don wannan fitar Hajiya Kilishin tace da Awwalu yaje ya saka tint ɗin.
    A cikin motar, Kilishin taja tsaki tana kallon agogon tsakiyar dashboard kafin tace.
    “Mutanen nan sun fara vata mana lokaci Awwalu, saninka ne fa ko Baffa bai san na fito ba.”
    Awwalun dake gaba mazaunin direba ya gyada kai shima yana kallon titin yace.
    “Ki bari kawai, ni kaina ina da aji ƙarfe takwas ɗin nan, kuma wallahi mai muhimmanci ne.”
    “Aji?” Da mamaki a fuskarta ta tambaya.
    Sai ya juyo ya kalle ta.
    “Au na manta ban gaya miki ba, na koma makaranta fa, Bayero na samu ina yin English saura shekara ɗaya ma na gama.”
    Kilishi taji ranta ya kara baci, har tana shirin bude baki tayi masa korafin ta yadda har ya shekara biyu a University ba tare da ta sani ba sai kuma taga meye damuwarta a ciki? Rayuwarsa ce, zata hana shi ne idan har hakan ba shafarta zaiyi ba, kuma ma tun asali ta san Awwalu mai son karatu ne, don tun yana yaro farkon zuwansa almajiranta da kudinsa yasa kansa a makaranta har ya gama firamare kafin daga baya kakarta ta shiga tallafa masa, kuma shekaru biyu bayan ta gama shima ya fita daga sakandiren, don haka karatunsa bai kamata ya dame ta ba.
    Ta juya tana kokarin kallon wani mai teburin shayi daga can nesa dadu dake ta kokarin hada wutar itacensa, amma itacen yaƙi bashi hadin kai duk kuwa da iskar sanyin da ake hurawa a lokacin. Ba shiri taji murmushi ya subuce a bakinta, zuciyarta ta cika da jin dadin yadda dattijon ke ta goho yana firfita wutar, tana son irin wannan abin, tana son taga wani nata wahala akan neman bukatunsa har sai zuciyarsa ta ƙeƙashe ta daina rauni, shi yasa ko kallo bata cika yi ba, don bata ganin amfanin yadda mutane ke tsara finafinan su cewa mai kirki ne zai ci galaba a kodayaushe.
    Taja tsaki bayan wutar ta kama babu daɗewa, ta dawo da idonta cikin motar tana ƙoƙarin lalubo wayarta, sai kuma ta tuna ai ta kashe ta don kar ma a neme ta, kuma a daidai wannan lokacin sai ga wata mota katuwa ƙirar jeep Prado tazo ta sha gabansu, nesa kadan tayi fakin ta tsaya.
    “Ina ga gasu nan Hajiya.”
    Cewar Awwalu yana kallon motar.
    “Fita zanyi kenan?”
    Ya gyaɗa kansa.
    “Ai bana tunanin shi ne zai fito.”
    Sai ta kuma jan wani tsakin.
    “Mutanen nan suna cin alfarmarta da yawa Awwalu, ba don dole Jamal ya bar duniyar nan ta hanyarsu ba, bubu abinda zai hana ni zaba musu irin tasu ƙaddarar su ma.”
    Awwalun ya juyo yana kallonta.
    “Haƙuri zaki yi Hajiya minti biyar ne ba su isa su sake ganin fuskarki ba har abada, harbin tayar mota tana gudu ba aikin kowa bane banda irinsu da suka san duk wani tactis na abin….”
    Bata ko jira jin ƙarshen zancen nasa ba ta sauke nikabin da ta daura a fuskarta sannan ta janyo wata ƴar madaidaiciyar jaka dake gefenta tare da wata farar takarda ta bude kofar motar ta fita.
    Kanta tsaye ta isa wajen motar ta tsaya daga daidai ƙofar baya, kuma daga inda Awwalu ke zaune yana hango sanda aka zuge gilashin ita kuma tasa hannu ta sake ɗage nikabin nata.
    Wani mutum ne zaune a ciki, fari tas dashi irin farin da yake komawa tamkar zabiya, sannan ilahirin fatarsa kaf, koina akwai wani ɗigo-ɗigon bakin wani ciwo da ya fito ya warke. Idanunsa na sanye da wani katon gilashi baƙi ta yadda ba’a ko ganin kwayar idanunsa, a lokaci guda yayi wani murmushi da ya baiyana jerin haƙoransa wanda rabinsu suna rufe da ƙarfe ne irin wanda ake cewa hsƙorin makka kalar ruwan gwal don haka sun haska tar a cikin hasken safiyar.
    “Barka da zuwa Hajiya, sai haƙuri da irin aikinmu na gaya miki ni bana mu’amala da jakada, shi yasa kika ganni nima da kaina.”
    Hajiya Kilishi bata yi murmushin ba, tana kallonsa idanunta a tsaye tace.
    “Tun da har ka ganni anan ai ka san wannan maganar ta wuce kuma.”
    Sai ya ɗaga mata girarsa daya cikin duniyanci irin nasa sannan ya nuna jakar hannunta yace.
    “Sune wadannan?”
    Sakan ɗaya biyu tana kallonsa hankalinta na kokarin danne takaicin dake yawo a zuciyarta kafin ta ɗago jakar ta miko masa, ya kuwa karɓa ya zura ta cikin motar sannan ya buɗe, idanunsa suka yi nazarin kuɗin dake ciki.
    “Kince yau da misalin karfe tara zai fita sannan shi kadai ne a motar ko?”
    Ta gyada kanta sau ɗaya sannan ta mika masa wannan farar takardar hannun nata.
    “Ga lambar motar koda wancan text ɗin ya gige.”
    Ya karbi takardar ya kalla sannan ya sake ɗagowa ya kalle ta.
    “Hajiya zan so ace babu magana biyu a cikin wannan al’amarin namu, zamu ƙirga kudin nan idan sun cika zaki ga aiki, idan kuma akwai matsala, to kuwa za’a sami matsalar da gaske.”
    Sai da ta ɗauke kanta gefe cike da takaicin yadda yake mata maganar sannan tace.
    “Idan kuma har babu matsalar ta yaya zan tabbatar da cewar zaku yin?”
    Ta dawo da idonta kansa lokacin da yake sake wani murmushin.
    “Tabbaci kike nema?”
    Bata amsa ba, shima kuma bai jira amsar ba, sai kawai ya ɗaga yatsansa ɗaya a iska yana cigaba da murmushi.
    Kuma bata gama tunanin me Ke shirin faruwa ba lokacin da ta wata irin ƙara ta baƙunci iska, tsananin karfin ƙarar yasa duk dauriyarta sai da ta firgita, kafafunta suka yi baya yayin da tasa hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta lokacin da idonta ya kai kan wasu maza da suka juya da gudu bayan sun karyo kwana, sannan ta hango wannan mai shayin ma ya kwanta a gaban teburinsa yana kakkarwa, tabbas ƙarar ta bindiga ce ba wani abu ba.
    “Wannan shine tabbacinki Hajiya, yarana basa wasa da aikinsu, hannu kawai nake ɗagawa shikenan duk abinda nace zai wakana ko akan waye kuwa.”
    Bayaninsa yazo daidai da lokacin da idonta ya sauka akan tayar motarsu ta gaba, gabadaya ta dagargaje ta kuma wargaje a lokaci guda, motar ta tuntsira tayi gefen titi, yayin da Awwalun dake ciki ke kokarin buɗe kofarsa don ya fito kar ta kara hantsilawa dashi.
    “Na barki lafiya.”
    Ta sake jin muryar mutumin kuma ko kafin ta juyo ta kalle shi, direbansa yaja motar sun yi gaba da wani irin saurin da har sai da tayar motar ta gurzu da titi ta bada wata irin ƙara.
    Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Hajiya Kilshi karo na farko a wannan safiyar, tabbas ta bakin Awwalun ne, mutanen nan sun iya aikinsu, rainin hankalinsu ne kawai a gefe. Taji murmushin nata na sauka har cikin zuciyarta da tunanin cewa ba za’a samu akasi ba, a yau Jamal zai bar duniyar nan, ai ta gaya masa… ta gaya masa lokacin da ya juya mata baya zai tafi.
    _”Na so zan yi dukkan shirina in bar cikinku ba tare da na taba wani ahalin Baffa ba, nayi maka katanga mai yawa Jamal, na daɗe ina kange ka daga sharrina, amma ka rufe idonka ka tsallako ka iso… Ina jiye maka takaicin barin duniya da ƙuruciyarka, ina taya ka alhinin barin duniyar nan a lokacin da ya kamata ka fara cin ganiyarka, don daga yanzu ni da kai, mutane ne da baza su taɓa iya rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.”_
    Ta sake wani murmushin tana cije leɓɓenta, zata so ace zai tuna wadannan maganganun nata a lokacin yake bin ruhinsa da kallo zuwa sama. Awwalu ya karaso wajenta a lokacin da nasa murmushin shima, fuskarsa na ɗauke da yanayin da ko bai furta ba ta san me zaice.
    _”Me na gaya miki? Mutanen nan zasu iya aikin ki.”_
    Sai kawai ta juya ta kalli motar tasu a lokacin da Jama’a suka fara taruwa suna ƙoƙarin zagayeta.
    “Zaki yi waya a kawo mana wata motar ne?”
    Ya tambaya, ta girgiza kanta.
    “Baka da zurfin tunani Awwalu, ta yaya hatsarina zai zo rana daya dana Jamal? Tsaftataccen aiki nake yi a kodayaushe ka sani, bana yin sajacin da zan bari ko da ɗigon baki da zai kawo zargi a zuciyar wani na.”
    Awwalu ya gyaɗa kansa yana cigaba da wani murmushin kafin yace.
    “Na yarda dake wallahi Hajiya.”
    “”Kaje ka siyo wata tayar, a daura sai mu tafi.”
    Kuma wadannan kalaman nata na lokacin sune tushe, shine sanadin faruwar wasu abubuwan da har a yau ba’a warware su ba, don Awwalu ya dauki tsawon lokaci kafin ya iya samo sabuwar taya da kuma mai daurata kasancewar safiya ce lokacin, don haka kafin su koma gida matafiyan nan sun tafi.
    “Mami, Ya Ma’aruf ya shigo yace ya kira wayarki a kashe, yace idan kin dawo in gaya miki ya bi Ya Jamal zuwa Abujan, zaku yi waya idan kin dawo.”
    Kalaman da Salma ta faɗa mata kenan bayan ta koma gida da misalin karfe goma saura na wannan safiyar.
    Kuma a tarihin rayuwar Kilishi kaf! Idan zata misalta kalmar tashin hankali, zata kwatanta ta ne da wannan ranar, ranar da zuciyarta ta buga a kirjinta, kafafunta suka zube gar a ƙasa yayin da idonta ya shiga hasko mata gawar Ma’aruf din da bata tsara a lissafinta ba tare da ta Jamal!
    ***
    *Present Day.*
    “Halima.”
    Alhaji Sulaiman dake zaune a cikin ɗakinsa ya kira sunan matarsa dake shirin sa kai ta fita bayan ta ajiye masa flask din ruwan zafin da ta dafa a dawowarsu yanzu da safen.
    Tsintsiya ce a hannunta wadda ta dauka don zuwa ta kara share falo inda aka kwantar da Aminun, taso ace tun jiya su Maryam sun zo sunyi sharar kafin su dawo, amma haka kurum ta kasa kiran iyalan gidan Kawu Malam inda su Maryam suka tafi da wannan umarnin, tana da kawaici akan ƴaƴan ta kowa ya sani, abinda mutane basu sani ba shine tana ajiye wannan kawaicin a gefe idan har aka zo gabar da za’a cutar mata dasu.
    A kofar dakin ta saki tsintsinyar sannan ta juyo ta dawo ciki, don daga yanayin amon muryar Baban ta san magana ce mai muhimmanci zasu yi.
    Ta sami waje gefensa ta zauna yayin da idanunta farare irin na Amina sak ke kallonsa, kallo na saurare da kuma jiran umarni.
    “Jiya na hango ki kina waya da ƴarki.”
    Ta gyada kanta sau ɗaya bayan ta gane cewa Amina yake nufi.
    “Akwai wata matsala ne da take fuskanta a gidan?”
    Mamakin tambayar tasa ya kamata, sai kawai ta sunkiyar da kanta kasa a hankali, a shekarun zamanta dashi kaf! ya sani ko da sau ɗaya bata taba zuwa ta bashi labarin wata matsala ba walau ta danginta ko kuma ta wani da ya shafe ta ba kuma shima baya taba tambayar abu makamancin hakan ba sai idan har zancen ne yazo a dole su fade shi, don haka abinda ba’ayi a baya ba, ba za’a fara shi yanzu ba.
    Amina yarsa ce, ta san yana da hakki akanta amma a tunaninta ya riga ya gama taka rawarsa akanta, yayi ruwa yayi tsaki wajen kaita rayuwar da babu ta hanyar da bata kalubalance shi ba. Shi da kansa ya fada cewa ba zai iya tuna ranar da tayi masa musu akan wani abu ba, amma bai ko duba wannan kawaicin nata na tsawon shekaru ba, da yake shi namiji ne ya rufe idonsa ya juya mata baya, ya dora yar tasa a wani mizani da dole nasa umarnin zata dauka.
    A yanzu anyi hakan, komai ya wuce ba tare dacta nuna fushinta ba, kuma gashi sun fara fuskantar kalubalen da ta guje musu shi, to don me yasa zai tambaye ta kuma?
    Ta fahimci har yau Sulaiman bai gama buɗe halayenta ba, don da ya san wacece Halima da bai ɓata bakinsa ma wajen tambaya ba, bata gori, bata cewa ‘dama na fada…’ zata yi iya kokarinta ne a farko don ganin ta kawar da matsala daga karasowa gare ta, idan kuma ta kasa, sai ta fara shirin tunkararta ta hanyar da zata iya kawar da ita, wannan shine babban abinda ke riƙe da zaman lafiyar gidanta dama zamanta tare dashi. Shi kansa idan zai tuna yana da zafi da kuma zuciya a lokacin kuruciyarsa har zuwa aurensu, amma da wannan halayen nata ta canja shi a lokacin da bai ma sani ba.
    Don haka sai ta gyara zamanta kawai a hankali sannan ta girgiza kai.
    “Babu wani abu, wata yar matsala ce kawai tamu ta mata.”
    Ya kalle ta tsawon wasu mintuna kafin ya sake kiran sunanta.
    “Ina fata a yanzu kin daina ganin laifina Halima, don kowa shaida ne daga ganin yarinyar nan an san tana cikin nutsuwa.”
    Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Amma, mazan kenan! bata jin har abada za’a zo lokacin da kwakwalwar kowanne namiji zata bude game da al’amarin mata, suna ikirarin sun san komai a kullum, amma tarin abubuwan da ake lullube su a ciki suna da yawa, wanda hakan na ɗaya daga cikin abubuwan dake juya duniya, don da zasu san kowacce kissa da dabara irin ta matan to da zaman auren ma zai gagari kowa ce ƙabila a duniyar nan.
    Tun a lokacin da aka jawo kayan kefen Aminan kallo ɗaya tayi wa akwatunan da aka zuba kayan kwalliya zuciyarta ta ɗarsa mata wani abu da sai a yanzu take ganewa. Kilishi ta narka maƙudan kuɗaɗe na gaske wajen siyan tsadaddun kayan gyaran jikin da zasu karbi fatar Amina, ta yadda a waje kowa zai sanya ta cikin layin nutsuwa da kwanciyar hankali da kallo daya, yadda komai zurfin da zuciyarta zata yi babu mai iya gano hakan don za’a shagala da kallon canjawar fatarta maimakon damuwarta, gashi kuwa hakan ya fara aiki har akan mahaifinta da ya kawo ta duniyar nan, wai sau nawa ne zata fada? Kilishi mugun ice ce da gaske!
    Sai kawai tayi wani murmushi a hankali sannan ta gyada kanta tace.
    “Haka ne.”
    Shima ya gyada nasa kan.
    “Sai dai mu bisu da addu’ar dorewar zaman lafiya.
    “Tabbas kuwa.”
    Amman ta sake fada tana jin wani abu kamar raha na ratsa zuciyarta, tana ƙara yarda cewa mata duniya ne, Allah ya basu damar juya namiji duk girma da tsufansa a tafin hannunsu, kawai da yawa ne basa amfanin da danarsu.
    “Mun yi waya da Kawu Mallam yanzu, yace za’a rako su Maryam din anjima, tunda kike ta kallo na a hanya na san abinda kike so kice in tambayo miki kenan.”
    Ta girgiza kanta.
    “Ni ban aike ka ba, idan zasu kara kwana ma ba zan damu ba.”
    Kice zaki iya bacci babu Hafsatu a gidan nan?” Ya tambaya
    “Kafin in same ta fa?”
    “Kina da Amina.”
    Sai kawai ta mike tana dariya, ta ɗauki tsintsiyarta ta fita. Alhaji Sulaiman ya bita da kallo yana jin zuciyarta wani iri, kamar bai gama yarda da kalamanta ba, amma kuma babu yadda zaiyi, matarsa daban ce a cikin mata ya sani, halayenta wani abu ne da ba zai taba iya kwatanta su ba, juma abinda bai sani ba shi e matarsa iri daya ce da kowacce mace, natan ne kawai basa gane cewar nutsuwar zuciyarsu a kowanne fanni na rayuwarsu taba zaune cikin ƙwaƙwalwar su.
    Awanni biyu bayan hakan ya baro cikin gidan, Ya fito ya nufi titi don tafiya ga sana’arsa.
    Daidai lokacin da Awwalu dake zaune cikin motarsa a can gefen layin ya tada motar shima yabi bayansa.
    ****
    *A wannan safiyar.*
    Ma’aruf ya tako cikin gidan a hankali, hannunsa daya na sanye cikin wandon shaddar dake jikinsa kalar ruwan toka yayin da ɗayan ke rike da wayar dake kare a kunnensa, kayan jikinsa kalar ruwan ƙasa ne wanda ta haska cikin safiyar, ƙafafunsa na tahowa cikin falon a hankali yayin da yake saurarar bayanin da Faruk ke yi masa a cikin wayar.
    “Mutumin nan sh*ge ne B, Ƙarfe biyun dare ya kira ni wai shi daga sannan yake amsa waya, wallahi har na zata yan fashi ne suka shigo mana.”
    Yayi murmushi kaɗan.
    “Baka da hankali Faruk dan fashin ne zai fara kiranka a waya ya gaya maka cewa gashi nan zai shigo tukunna? ka gaya min yaya kuka yi dashi kawai?”
    “Yes, ya karba. But sai mun bashi wani abu tukunna, kuma ka san shi cash yake baukata, kuma gayen yana da matsala wallahi don yace dole yau yake bukatar kuɗin, shi yasa tun farko ni raina bai kwanta da mu saka shi cikin al’amarin nan ba.”
    Ma’aruf ya girgiza kansa.
    “Kar ka damu, zanje na ciro kuɗi anjima sai ya gaya mana inda zamu same shi.”
    “Shikenan, I will talk to him zuwa yamman, zan gaya maka.”
    Da haka wayar tasu ta kare, daidai lokacin da Ma’aruf ya shiga hanyar koridon zuwa kitchen, inda ƙarar motsin kwanuka ke tabbatar masa da cewar tana ciki.
    Da gaske yake abinda ya faɗa mata jiya cewa tana ƙara ƙawata duniyarsa, don duk da har yanzu bata gama sakin jikinta dashi ba, ya sani cewa shigowarta cikin rayuwarsa ya fara samun wata nutsuwa da shi kansa baya gane mata, abinda kawai ya sani shine abinda yaji tun daga ranar da ya fara ganinta shi yake jan ragamar sa akanta.
    Tsakanin jiya da yau kaɗai yana jin sunyi sabon dashi da Ruƙayya basu sami hakan a ɗan kankanin lokaci ba, ya nuna mata cewar da gaske yake wajen gyara alakarta dashi, kuma hakan bai bashi wuya ba don da gaske ne yarinyar bata da matsala, tana da hankalin da bai san da me zai kwatanta shi ba, tana da hankalin da ya fahimta sosai a cikin dukkan amsoshin da ta bashi don sunyi hira sosai a jiya, yayi mata tarin tambayoyin daya fahimci kusan rayuwarta gabadaya a dunƙule.
    A lokacin ne kuma ta juyo ta kalle shi, hannunta daya rike da plate din da take wankewa a cikin sink, lbakinta yayi masa murmushin nan nata dake tafiya har cikin zuciyarsa. Wani abu daya lissafa shi cikin nasarorinsa na kwanakin nan kenan, yana gaya masa cewa da gaske yayi kokarin da ya fara rusa wasu abubuwan dake tsakaninsu, shi yasa a jiya ya daure yayi mata tambayar da yake fatan amsar da zai samu amsa daga gare ta, amsar da yake fatan ta zama abu na karshe da zai cire duk wani hijabi a tsakaninsu.
    “Sannu da zuwa” Muryarta ta fito a hankali.
    Bayan asuba ya sake fita wajen ƙarfe bakwai na safe, ya tafi can yamadawa inda ya halarci janaizar wani abokin Baffa da ya rasu a daren jiya, da Baffan suka yi waya a jiyan ya gaya masa cewa yaje ya wakilce su shi da Baba Usman tunda basa gari, sai gobe ne suke shirin dawowa daga Kadunan.
    Don haka can ya tafi kuma har bayan an kai mutumin sai da ya sake komawa gidan don bai shiga ciki yayi musu gaisuwa ba, ya san matarsa guda ɗaya, don a shekarun baya kafin ya auri Rukayya daga ita har mijin nata sunyi kokarin hada shi da wata ƴar su Nafisa, kuma shima saboda hankalinta ya so yarinyar a lokacin amma sai naci da kuma dagiyar Rukayya ya tsallake nasu.
    Yanzu ma da yaje yaga yarinyar, tana zaune a gefen mahaifiyar tata riƙe da wani yaro mai kama da ita sak wanda hakan ya shaida masa cewar tayi aurenta itama, kuma sunji mutukar dadi na ganin nasa, don bai san me yasa ba kai tsaye yake iya fahimtar farin ciki da kuma yabawa a fuskar mutane, kamar yadda a jiya ya fahimci daɗin da Amina taji a lokacin da yake godiya da kuma yabawa girkin da tayi masa.
    Ya karaso cikia hankali sanda da ta kashen famfon tana rike da kofi na karshe a hannu ta.
    Ya tsaya a gabanta.
    “Anyi jana’izar?” Ta tambaya bayan ta kalle shi ta sunkuyar da kanta. Ya daga nasa kan kafin ya amsa.
    “Anyi tun ɗazu, makabartar babu nisa da gidansa.” “
    Yaga kamar ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.
    “Allah ya jikansa.”
    “Ameen.”
    Ya amsa yana cigaba da kallonta, kuma abinda yake gani a fuskar tata bai tafi ba, don da alama mutuwar ta ɗan taɓa ta duk da bata san mutumin ba, yaga hakan a fuskarta tun daga lokacin da ya gaya mata inda zai je da safe bayan ya shiga dakinta ya same ta zaune akan dardumar ta har a lokacin.
    Kayan dake jikinta a yanzu wata doguwar riga ge ta atamfa Green, kuma akwai wani abu a cikin kalar rigar da yayi mata kyau yake kunna wani abu kamar wuta daga ƙasan zuciyarsa tun sanda ta shigo kitchen din.
    “Har kinyi breaskfast?” Muryarsa ta tambaya da wani irin amonta mai sanyi yana katse shirun dake son faruwa.
    Ta girgiza kanta a hankali sanin cewa kofin hannunta yake kallo.
    “A’a, nayi amfani dashi ne.”
    Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kalli lokaci.
    Ƙarfe goma har da kwata.
    “Dama ba kya cin abinci da wuri?”
    Ta sake girgiza kanta.
    “A’a ya danganta kawai.”
    Sai taji yayi wani abu kamar murmushi kuma kafin ta ɗago ta kalle shi ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata yace.
    “Ya danganta da lokacin da na dauka a waje kina jirana kafin na dawo?”
    Wani irin abu ya lullubeta a lokaci guda tun daga kai har ƙafa, ta dago ta kalle shi idonsa yana kanta kamar yadda ta sani.
    “Ki gaya min gakskiya dan Allah ba zan fadawa kowa ba… kawai ce miki zanyi nagode.” Ya roje ta a hankali.
    Bata san lokacin da tayi wani guntun murmushi ba sannan ta daga kanta sau daya tana cigaba da kallonsa.
    Wani abu da yasa a lokaci guda Ma’aruf yaji wasu abubuwa kamar chemical concoctions na zubewa a cikin zuciyarsa.
    “Now I feel like posting it on my Facebook wall.”
    (Naji kuma yanzu kamar inje in rubuta a shafi na na Facebook.) Ya fada muryarsa can ƙasa.
    Sai kawai tayi wani murmushin mai fadi sannan ta juya, ta nufi wajen da take ajiye kofunan a kitchen din ta ajiye na hannunta sannan ta debo wasu containers da ta juye su Madara da Milo a ciki ta juyo, ya jingina da gefen sink ɗin har yanzu yana kallonta, kamar yana son yace wani abu.
    “Sauran kayan suna falo.”
    Ta fada tana nufin sauran kayan breakfast din, kuma da haka ta taho zata wuce ta gabansa, amma kamar yadda zuciyarta ta ayyana mata zai faru, sai ya tsayar da ita, ya riko hannunta ya dawo da ita gabansa.
    “Baki bani amsata ta jiya ba Amina.”
    Kai tsaye ya fada yana karbar kayan hannunta ya ajiye su akan sink din.
    Sai ta kasa kallonsa wannan karon, ya riko hannunta ɗaya sannan muryarsa ta cigaba da magana a hankali.
    “yunda na tashi da safe tunanin da nake yi kenan har naje na dawo, ko aikina da tarin mutane ke karkashina baya damuna kamar yadda a yanzu jiran abinda zaki ce ya dame ni, I always have the last and final say a kamfaninmu, but zuciyata bata damuwa da abinda zan fada kamar yadda a yanzu ta damu da abinda zaki fada min, so Please save me from this boredom and just say it now. Na gaya miki ko a yaya amsarki tazo zan karbe ta a hakan ba tare da wani tunani ba, I just want to hear your mind out.” ( So nake kawai inji abinda yake a zuciyarki.)
    A lokaci guda Amina taji makogwaronta ya bushe, taji tana shakar wata busashshiyar iska tana wucewa har cikin cikinta yayin da maganganun da ya fada mata jiyan ke dawowa cikin kanta.
    “Amina ban san tunanin ki gane dani ba har yanzu, auren mu daban ne da irin wanda kowa yake yi, ban taba ganinki ba sai a ranar da kika zama matata kuma na san kema haka, kowanne mu bai san yaya ɗaya yake ba balle halayensa har aka haɗa rayuwarmu tare, bamu da wannan sanin ko kuma fahimtar junar da mutane da yawa ke samu kafin aure.
    Sai a yanzu ne muke fara gina tubalin da muka baro a baya, kuma ba zan boye miki ba I think I have started falling in love with you since from day one da na ganki a cikin gidan nan, ban san me yasa ba I just did… Kuma a yanzu da na ƙara sanin ki nake sanin komai game dake Amina, zuciyata ta bani tabbacin cewa da gaske ne ina son ki ba tunani nake yi ba, zuciyata tana godewa Allah a kodayaushe da ya zamo kece wacce Mami ta zaba min a matsayin matata.
    Saboda da bake bace Amina da labarin zai canja, ko sau ɗaya kar kiyi tunanin cewa da kowacce mace aka kawo cikin gidan nan zan karɓe ta kamar yadda na karɓe ki. Na san me nake so Amina na san abinda bana so, kuma ina da tsarina a kowanne ɓangare.
    Don haka kema ina son inji tunaninki game dani, bana son in matsa miki da komai Amina, idan zamu gyara alakarmu mu cire komai a tsakaninmu ina so ya zama da yardar dukkaninmu ne, bana so ya zama don ni ina so ke kuma ya zane miki dole, so nake mu ajiye duk wani tunani a gefe tare mu karɓi junanmu da zuciya daya, I want us to ignite our hearts together and get lost because we wanted to, shi yasa a jigawa nace miki not there, not then, sai lokacin da zuciyarki ta amince kuma kika bani dama Amina.”
    Allah yaso a jiyan da yake fada mata hakan cikin duhu ne, lokacin da bai nemi shawarar ta ba ya shigo dakinta bayan ta barshi a falo yana kallon zancen wata siyasar America, tayi masa sallama da cewar sai da safe zata je ta kwanta, kuma ya amsa mata suka yi sallamar Allah ya tashe su lafiya, sai gashi minti goma bayan hakan ya shigo dakin bayan yaje ya canja kayansa zuwa na bacci.
    Ta rufe idanunta alamun bacci take yi har sanda taji ya hawo gadon, amma lokacin da babu zato taji ya naɗe hannunsa daya waist dinta kafin ya jawo ta cikin jikinsa a hankali, babu shiri ta bude idanunta tana kallonsa, kuma a lokacin ne ya gaya mata wannan maganar, a yanzu kuma da safiyar Allahn nan yake neman amsarta.
    Kuma abinda take ji a yanzu ya wuce duk yadda zata iya fassara shi, yadda ya rike hannayenta duka biyu kadai tana jinta ne kamar wani kwan fitila da ya kama tar! Sannan tana jinta kamar tana shawagi a iska, kuma cikin hakan ne taji lokacin da ya saje cewa
    “Duk abinda zaki fada ina son kiyi considering cewa ba kowa ne zai baki irin wannan damar ba Amina, Allah ina da kirki sosai.”
    Bata san lokacin da wani murmushi mai kama da dariya ya subuce a bakinta, yace ya bata damar da zata fadi ra’ayinta amma kuma ya fara yiwa kansa campaign tun bata ma ce komai ba. Sai ta dago tana kallonsa sanda shima yake murmushin. Shima ya sani ai, amsarta ba zata canja daga abinda yake fata ba, ya riga ya gama daure ta da jikyoyinta, kamar ya sace zuciyarta tun a farkon zamansu ya kulle ta a wani keji, kuma bai bude ta ba sai da ta gama sabawa dashi ta yadda a yanzu da ya baya muƙullin da kanta don ta bude kanta ya san ba inda zata iya zuwa… Dole da ta fito ta tashi zata dawo ne ta faɗo cikin hannayensa.
    Don Allah ya sani ko ba ita ba, bata ga macen da zata iya kallon Ma’aruf a wannan lokacin tare da kyawawan halayensa tace bata son sa ba, idan kuwa har an samu yo tabbas ko waceve za’a iya jeranta ta cikin masu karancin sa’a a duniya.
    Don haka a wannan lokacin Amina ta daure dukkan wani tunani a zuciyarta, ta ture komai gefe, a karo na farko a rayuwarta tayi wani abu kai tsaye da zuciyarta ta gaya mata ba tare da tunanin komai ba, don a wannan lokacin ta ma manta kowa ɗin kuma ta manta komai, babu wani kokonto a ranta ko kuma tunanin hakan bai dace ba, abinda ta sani kawai shine Ma’aruf ya tambaye ta abinda ke zuciyarsa ne kuma zata fada masa gaskiyar zuciyar tata.
    Shi kansa bai yi zato ba sanda ta tattaro dukkan dauriyarta a hankali ta ƙara tsawonta kaɗan ta hanyar miƙewa kan kafafunta sannan ta kai fuskarta daidai kunnensa, muryarta ta fito ne a hankali da kalaman da ita kanta sai a wannan lokacin taji su.
    “You’re the piece of me I didn’t know was missing untill now.”
    (Kaine wani ɓangare na da ni kaina ban san bani dashi ba sai yanzu.)
    Ta sauke ƙafafunta a hankali tana kallon fuskarsa dake ɗauke da tsananin mamakin da ita kanta take jin yana lulluɓe ta, taga yadda ya haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronsa kafin ya gyaɗa kansa a hankali.
    “Nagode Amina, insha Allah ba zan taɓa sawa kiyi dana sanin sanina a rayuwarki ba, zan kare dukkan hakkokin ki da Allah ya rataya min a wuya na, ba zan taba cutar dake ba, ina da tabo mai girma a cikin rayuwata, ina da abubuwa da yawa da ba zaki so saninsu ba, I’m a mess just like I told you, amma idan kika bani dama nayi miki alkawarin komai zai tafi daidai Insha Allah.”
    Kuma bai bari ta sake wani tunani ba ya haɗe tazarar dake tsakaninsu, ya rungume ta a jikinsa da wata irin shiga da taji kamar yana son kange ta ne daga dukkan wani hargitsi na duniyar nan, wani abu daya dawo da ragowar hankalinta jikinta yana tuna mata da zagayen halin da take ciki, fuskar Amma da kuma ta Hajiya Kilishi ta haska cikin kanta a lokaci guda, dukkanninsu suna kallonta da jiranyen da ta san yana zagaye da ita, sai dai Ma’aruf bai bar hakan yayi nisa ba lokacin da ya sake riƙe ta a jikinsa sannan a hankali ya lalubo kunnenta ya raɗa a cikin kunnenta.
    “Thank you so much Doll, I was dying to do this…”
    Kuma bai ɓata lokacin wani tunani ba, lokacin da ya dawo da fuskarsa saitin tata sannan ya hade dukkan wata tazara tsakaninsu, his lips were rough and urgent, sannan tana iya jin dukkan wani sakon da yake bata a cikin hakan, kuma cikin wannan sakon ne Amina ta samarwa kanta mafita itama, wata mafita da a lokaci guda ta haska a cikin kanta, wata mafita da zata jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya!
    Tsuntsu biyu, ba guda daya ba!
    *****
    Aka kwankwatsa kofar ɗakin sau daya, biyu, uku….
    “Who the hell is that?”
    Muryar Jamal ta daka tsawa daga ciki yayin da yake naɗe cikin bargon makeken gadonsa.
    Zainab, ƴar aikin gidan dake tsaye cikin uniform dinta na masu aikin gidan ta zabura kaɗan tayi baya saboda yadda muryar ta firgita ta, ta saba a lokuta da yawa irin haka idan tazo dama da sigar da take samun amsar sa kenan, amma ta kasa sabawa har yanzu, ta kasa sabawa tun sanda ta fara aiki a gidan.
    “Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka.”
    Ta fada da karfi kaɗan yadda zai jiyo ta. Jamal yaja tsaki yana shafa kansa da duka hannayensa duka biyu. Ya tsani yarinyar nan, ya tsane ta har cikin ransa, matan mahaifinsa uku ne, suna da ma’aikata fiye da hamsin a gidan kuma kusan rabinsu arna ne, idan ma akwai musulman to babu bahaushe ko ɗaya a cikinsu.
    Don haka ya rasa dalilin da yasa mahaifiyarsa ita kadai ta fita zakka ta ɗauki irinta aiki, shi baya hausa ma tare da ƴan aiki amma akan yarinyar nan ya fara. Kuma tun daga ranar da ya fara ganinta a ɓangaren mahaifiyar tasa, sanda suka ci karo ta zuba masa miyar data dauko a kwanon hannunta yaji ya tsane ta har cikin zuciyarsa.
    Har ya buɗe baki zai bata amsa ya tuna ko yayi turancin ma sai yazo ya fassara, don haka zata cigaba da tsaiwa a wajen tana kara maimaita masa abinda ta fada, ilai kuwa kafin ya gama tunanin yaji da wannan shakakkiyar muryar tata ta sake cewa.
    “Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka.”
    Wai wa ya gaya mata cewar Sunan Mamah Hajiya ne ma?
    Ya ja tsaki kafin yace.
    “Ina zuwa.”
    Shirun da yaji bayan wasu sakanni yasa ya fahimci cewa ta tafi, don haka ya kara jan wani tsakin kafin ya jawo wayarsa a gefe, karfe sha ɗaya da rabi na safe, laifin me aka cewa Mamahn ya sake yi da zata turo a tashe shi da sassafen nan? Missed call ɗin Haro ya gani har guda tara don ya saka wayar a silent, gayen bashi da hankali wani lokacin.
    Yana shirin sake maida wayar ya ajiye sai ga shigowar wani kiran nasa na goma. Ya ɗauka ya ƙara a kunnensa.
    “Ina ka shiga ne J? Ka bar gari ne?”
    “Yes, ina gida.”
    “Dole ka baro Abuja yau Jawad, don na gano hanyar da zamu lalata yarinyar nan?”
    Ba shiri Jawad ya miƙe zaune yana sake rike wayar a kunnensa, kusan bakinsa na rawa yace.
    “Me ka samo? Me zamu yi?”
    Daga cikin wayar Haron ya ƙyalƙyale da dariyar shakiyancinsa kafin yace.
    “Ma’aruf Mansoor Bakori!”
    **
    _Me kuke tunani ya zama karshen hatsarin nan shekaru goma da suka wuce?_
    _Wace mafita kuke tunanin Amina ta samo?_
    _Ga dai Awwalu can na bin Baba…_
    _Me ya Haro yake nufi da sunan Ma’aruf a matsayin hanyar da zasu hukunta Ruƙayya?_
    _After all this, what do you think about the love Birds??_
    _I’m here singing Confession Song by Omah lay…_
    _Ku shirya ganin wasu Confessions ɗin daga MMB…😅_
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!