Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    ………….Malika bata samu Saukin Laulayi ba sai da cikinta yayi kwari yakai kimanin Wata Hudu kafin Tafara dawowa daidai tana kuma kokarin Maida jikinta,Ammh lokacin yana Farkon Shiganshi Malika tayi Rama Sosai kamar Wacce take ciwon Tari,ammh yanzu Alhamdulillah Tafara Maida jikinta ba kamar Da ba.

    Yau ma takama Weekend ne,ACP SALEEM yana gida bai Fita ko”ina ba,Yana daki ya kwanta bayan yagama latse latsensa ajikin laptop dinsa,malika kuma Tun Safe ta Fita Zuwa kichen Don Jiya dakyar tayi barci sakamakon kwadayin Cin Garin kwaki daya matsa mata Shiyasa tatashi da Safe zata karya dashi.

    Kwadashi tayi da Kolokuli da kuma Manja kafin ta zo Falo ta zauna kan Kujera taja Filon kujera ta Daura Bisa kafafunta bayan ta Dora Filet din kwadan garin Saman Filo,cikin Zumudi da Murna take Tura garin Daga ganin yadda takeci kasan Abun ya kaimata,don ganin yadda Fuskarta yake Sakin Annurin Farinciki,Rabin Hankalinta naga Talabijin tana kallon Gidan Badamasi atashar Arewa 24 da,Haka kurum take son Shirin Don yana Sata Nishadi.

    Merry ce ta Fito bayan ta Duka ta Gaisheta,Amsawa tayi kafin tace ta Shiga kichen ta gyara mata Shi ta gogeshi tsab,don yanzu tana kokarin sakawa a tsaftace waje ammh fa ba da kanta zatayi ba,don Malika ko Acp ya Fita Attaka yanzu😂😂.

    Yadade tsaye daga kofar dakinsu yana Kallonta,Hannuwanshi cikin aljihun Wandonsa,na barci baki mai wani Roba ta kasa,jikinsa kuma babu Riga gabadaya yalwar gashin kirjinsa wanda ya kwanta yayi luf duk ya bayyana,batason da tsayuwar mutum ba balle taji karisowarshi sai dai kawai taji ya Dauke Filet din garin yana kallonta gefe daya kuma yana yamutsa Fuska kamar yaga kashi .

    Dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kwabe Fuska tana Fadin”Kai Mallam don Allah Ka bani bafa kyau mutum na cin abnci ana katseshi kafini sani,kune malamai magada Annabawa..”Tafada tana mai yar Dariya tana kuma gyara Zaman Shegiyar Shimin datake jikinta wanda Cibiyartama awaje,kwata kwata cikin nan ya chanzamai mata fa,Yanzu malika bata iya Wuni da kayan kirki Sai tace Zafi takeji,daga ita sai Karamar Riga da Wando.

    Da kallo ya Bita kafin ya kara bin garin da kallo yana Fadin”Wai ke baki gajiya da Dura ma cikinki wannan Abun .? Baki tsoron ki haifomin bby,da Tabon garin kwaki..”Yafada yana Tamke Fuska Dariya ya bata Har Sai da ta Dara Tana Fadin”Au dama ana Haifan yara da tabon Abunda Uwa taci lokacin suna ciki ne..? Lalle ko da har dakai ka Fito da Tsiron Danwake don Ummi ta gayamin da cikinka Shine abincinta Shida Wainar Fulawa..”Ta karishe Fada tana Dariya.

    Zaro ido yayi yana Fadin”Wai da gaske…?,Dariya Malika ta Kece dashi harda Dukawa,ganin haka yasa ya Bata dankwashi akai yana Fadin”Kazamar mai ciki kawai,wato nine yau na zama cartoon dinki ko..?”Tana Sosa kanta ta kwaremai baki tana Fadin”Wayyo tsakiyar kaina ya Burma wayyo Ummi da Abbi Mallam ya Burmamin tsakiyar kai..”Ta Fada harda matse ido,kamar gaske,dariya Abun ya Bashi har sai da Duka hakoransa suka bayyana Waje…

    Kusa da ita ya Zauna yana Fadin”Yarinyarnan yar Sharri ce,dan wannan yafa danayi miki ne zaki sakamin kuka kice kanki ya burma,salon kijamin Sharri,in mazaki kukan Jini ne yarinya bamai Cetonki yau..”Jin haka yasa ta bata Fuska ta mika hannu tana Fadin”Ni dai bani Abuna..”Tafada tana kokarin amsa,shi kuma ya maida shi bayanshi yana Fadin”Anki abaki,in kina da karfi ki kwace…”Jin haka yasa ta mike zata tsallaka dayan gefe,shi kuma yayi Saurin mikewa ya daga Filet din sama yana Fadin”In mutum ya isa ya kwata din..”Tsalle ta Fara tana Fadin”Don Allah ka bani,wayyo…!”Dariya ta kamashi ya danne yana Daga mata gira yake Fadin”Au bazaki iya karba ba.? Amshi mana..”Yafada yana sauke hannunshi tayi Caraf zata kama ya dage sama yana Dariya,ganin haka yasa ta Fara Diddira kafa tana kukan Shagwaba,Tanayi yana kallonta yana jin Nishadi sosai yadda take Diran Kafafun ne,Ko’ina na jikinta na motsi yasa wata Sha’awarta takamashi Lumshe ido yayi yana Fadin”Tsaya tsaya..Gashi..”Ya fada yana mikamata Da Sauri ta dakata tana Washe Baki ta mikamai hannu,miko mata yayi ta saka Hannu kenan zaka karba ya Maida bayanshi yana fadin”Da Sharadi ammh..”Jin haka yasa ta Mele baki tana Fadin”Kayi ka Fada,don daga yanzu nadaina Biye maka,sai wahalar dani kake da wayau..”…

    Yana Dariya ya kai bakinshi Saitin Kunnanta yana Fadin”Don Allah nayi….”Da Sauri ta dago ta kalleshi kafin tace’Kayi me…? Ido ya lumshe kafin ya Shafa saman Nonuwanta har Zuwa saman karamin matashin Cikinta kafin ya gangaro Zuwa kasar maranta yana Shafawa ahankali,kafin yace”Wannan…”yafada yana Kokarin Turamata hannu cikin wandon jiknta,duk da ya kashe mata jiki,Tureshi tayi tana Fadin”lalle naki wayon,na kwada wani yanzu..”Tafada Tana Nufar hanyar kichen din,Ganin Haka yasa ya Ijiye Filet din a bisa kujera ya isa gareta da Sauri sai dai taji ya Dagata sama cak yana Fadin”Ni da Hakkina adnga min yanga,lallema yarinya..”Yafada yana Dariya,itama Dariyan take tana bugunshi akirji tana ihun ya sauketa,shiko bai Direta ko”ina sai kan gadonsu,tana kokarin Tashi ya bita ya Danne,bayan ya sakarmata Nauyinshi,Baknta take kokarin Budewa sai yayi Caraf ya Hade bakinsu waje Daya.

    *
    *BAYAN SATI DAYA*

    Aikin ginin Masallacin da makarantan Da malika ta gina Tuni ya kammallah har sun kirata sun Sanar da ita,itakuma sai ta Sanar da Saleem,shine ya bata Shawaran Asanar da jama”a Saboda su samu hallartan Taron Bude Wajen,da kuma Addu”a Ga Daddy,Malika ta yarda da Shawaran Saleem nan aka Fara Sanar da gaddamar da makranta da kuma Masallacin da Malika malik ta gina y’a marigayi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa domin Sadakatul Jariya Zuwa gareshi wanda zai Gudana agarin Malumfashi RANAR ASABAR Da misalin Karfe 9 na Safe.

    Kafin kace kwabo wannan Budaddiyar Sanarwan Hade da Gayyatan ta iske kowa yaji sai ya sakama Malika albarka domin akwai ya”yan masu dashi da yawa wadanda iyayensu ke Mutuwa su bar musu Tarin Dukiya,ammh bazasu taba Tunanin Yi musu Sadakatul jariya ba sai dai Suyi ta Facaka da kudi suna Abunda suga dama,ammh sai Gashi Malikan da ba”a taba Zato ba tama kowa mamaki,kuma wannan ba komai bane,Sila illah Saleem wanda Shine keda kaso 90% wajen Daidaita Rayuwar Malika hartazama Abun yabo da koyi awannan zamanin.

    Ranar taron Tun wajen Karfe 8 Suka isa Malumfashi ita da ACP SALEEM dinta,cngam dinta kenan,suna Sanye ne da Shadda mai Ruwan kasa,wacce akallah zatabama Dubu 50 baya Saboda Yadda take Fitar da maiko da yarari,Shi Saleem yayi dinkin Tarzace ne Dinkin Muhammed na Samarin zamani masu ji da kyau da Mukami,Da hulansa Zannah bukar wacce take Kalan,Ruwan kasa ajikinta haka takalmin kafanshi ma Rufaffe ne Mai Kalan Ruwan kasa,hadadde na Fatan Damisa,hakama agogon Fatan Dake Hannunsa,shima Kalansa kenan wanda na kamfanin Rado ne…

    Itama Malika Dinkin Jikinta Riga da zani ne,Stone work ne,Rigar harpjmp ce,domin ta sauko mata har Gwiwa,sai Babban mayafinta mai kalan Ruwan kasa,da Takalminta mai Dudu Shima mai kalan Ruwan kasa,hakama yar karamar Jakar dake Hannunta,agogon Hannunta kala daya ne,dana Saleem ammh Shi nashi is For men,ita kuma nata For women ne😂in ka gansu sai sun Burgeka kaji kana ta kallonsu baka sani ba,saboda yadda suka zama Abun Burgewa.

    Taro yayi taro wanda ya Gudana a haraban sabuwar mkranta Wacce dama masallacin ke kusa da mkrantar,Abbi da Ummi sunzo,hakama Hajiya binta tazo,hakama manyan malamai hadda Dan majalisar Dake Wakiltar Malumfashin yazo,Yan jaridu harda gidan Talabijin duk sunzo daukan gani da ido Bayan Bude taro da Addu”a inda Wasu karin bayanai suka gudana,sai kabama Malika damar mgana,wanda Tunkan aFara gabatar da Taron ta Fara Hawaye, Saleem ne yake Damke da hannunta alamun lallashi,ta Fita ta karbi Abun mgana ammh kuma ta kasa mgana,saboda Tunawa Da Daddyta datayi Abu daya ta iya Fada Bayan ta mika godiya Allah (SWA) sai ta koma mika sakon Jinjinarta Zuwa ga gwarzonta kuma bango gareta,wanda Shine Silan Faruwa komai,shi zata mikama sakon Godiyarta,kuma ta Wakiltashi amatsayin wanda Zai yi bayani Amadadinta,Awajen babu wanda baiji kwallah ba,lokacin da Malika ke Fadin ta Gina wannan mkrantan ne Fisabilla da kuma Sadakatul Jariya ga,Mahaifinta Allah yaji kansa Da Rahma,Kuka ne yaci karfinta,sai da Saleem yazo ya kamata ya Rumgumeta ya maidata wajen zamanta,,taron bai wani jima ba akayi Abunda ya kamata,Malika ta dauki Nauyin malaman mkratan da duk Abunda za”a bukata karatu takeso akoyar kyauta batare da an anshi Sisin kwabon wani ba,Anyi Addu’o’i Da fatan Allah yajikan Daddy,ita kanta Malikar tasha addu”a da Fatan gamawa Da Duniya lafiya kafin Taron ya Tashi bayan an gaddamar da Sunan masallacin *MARKAZUR UMAR BIN KHAD’DAB* Sai Shikuma Mkrantan *MADARASATUL UBAIYU BIN KA’AB*.

    Basu kwana ba Aranar suka Jiyo zuwa zamfara,Ranar dai Malika Mutuwar Daddy ta dawo mata Sabuwa don da suka Dawo haka ta kwanta akan gado tana kuka mai Cinrai,Sai da Saleem yayi ta lallashi da jikinsa da hannunsa kana ta bar kuka ta koma tana Sakin ajiyar Zuciya,koda Dare yayi zazzabi ya Rufeta Ruf ta kwana tana Nishi sai da Saleem ya tasheta ya bata mgani,kuma yasa Ruwan sanyi bayan ya Rika jiko Towel yana matsa mata jiki dashi,shine taji sauki har kuma ta Samu barci.

    ___________________

    Sannu bata Hana Zuwa sai dai Adade ba”a je ba,an kuma ce Duk Abunda aka Sanyama lokaci Toh zai zo,gashi har bikin Nadira da Dr Hambali yazo,sauran Sati daya inda Shirye Shirye ya Kamkama Aduka bangarorin,Nadira tayi gayyah sosai kawayensu na mkranta da kuma yan uwa da abokan Arzuka,Har Saleema sai dai ta kaima kati da Minti gayyata bayan kuma ta Tura mata ta waya,.

    Saleema tayi mamakin ganin Nadira tazo har cikin Asibiti ta kawo mata kati gayyatanta Zuwa wajen Bikinta,nan nema Saleem ke Fadama Nadira itama asanya lokacin Bikinsu ita da Ya Sadiq,wanda nan da Wata uku ne lokacin take gama Housemanship dinta,Tayi Mata Fatan alheri tare da mata alqawarin indai tazo bikinta itama zata Sanar da Dr tasan bazai hanata ba,sun Rabu cikin Aminci inda Saleema ta mata alqawarin zata zo insha Allah.

    Abun mamaki Nadira bata Sanar da Zahra ta gayyaci Saleema ba,shiko Saleem, Bukar Mada da kanshi ya Kirashi ta waya ya Sanar dashi,bayan kuma ya Turamai sakon gayyata ta waya,anyi haka da kwana biyu Sai ga kiran Nadira,bai da nombarta lokacin don ya Dade da Shareta da nata dana Zahra na Abba kadai ya bari,shima saboda yana kiranshi suna gaisawa ne, kada ya goge Watarana ya kirashi yace waye😂yace baida mutumci,yana dagawa bayan sun gaisa tace itace Nadira,yaji mamaki sosai nan take Sanar dashi mganar bikinta tare da cemai tana gayyatanshi Daurin aure,kuma tana son Don Allah ya Turamata Nombar Malika zata kirata,mirmishi kawai yayi mata yace kada ta damu in ya samu lokaci zai zo,mganar malika kuma ba sai ta kirata ba,Zai sanar ita ammh da Wuya ta samu Zuwa don bata jin dadi cikint jikinta yayi Nauyi..”Cike da Mamaki Nadira kema Malika Fatan Sauka lafiya kafin suyi sallama bayan tace agaisheta,shikuma yace ta gaida Momi,.

    Ya dade Shuru bayan sungama waya,yana Tunanin wani abu,Abunda yasa bai bata Nombar Malika ba,saboda shi atunaninshi Zahra na wajen,kuma zata iya daukan Nombar Malikan ta kirata,saboda shima kwanaki tayi ta kiranshi baya dauka,daga karshe sai ta koma tana kiranshi Da Rufaffiyar Nomba,Sai da ya kulleta kana ta daina Damunshi..

    Sai da yakoma gida yake sanar da Malika sakon Nadira,tayi ta mamaki harta Fadin in Saleem zai barta data jema Momi da Nadira biki suna da kirki sosai,wani kallon lalle ne ma Saleem yayima Malika dole taja bakinta tayi gum,itama din ma jnta baki ne,ammh tasan yadda Cikin jikinta yayi kato kuma Wata 6 kenan ammh kamar wanda zai Fito yau ko gobe,duk ta kumbura musamman kafafunta,Barin ma tayi dogon Zama kafin tatashi duk sai su haye,Sai Saleem ya dawo daga aikin kafin su kwanta yayi mata massges dinsu.

    Saleema ta cika alqawari tazo bikin Nadira,wanda Sai dai Zahra ta ganta kwatsam suka kama aikama juna kallon mamaki,Zahra ita tafarama Saleema mgana inda ta bata hannu suka gaisa tana tambayanta su Ummi,itako Saleema Karema Zahra kallo take yadda Rayuwa ta Horata Duk ta yi sanyi kamar ba ita ba,Ace yau Ana bikin Nadira ammh Zahra na Zaune waje daya cikin Natsuwa ba iyayi ba hayaniya ba Rawan kai,lalle Ruwa ya Daki babban Zakara kuma Gani ga wane ya ishi wane Tsoron Allah.

    Saleem bai samu Zuwa Daurin Aure ba,ammh Abbi yazo Har suka Hadu ta Saleema ta biyoshi suka koma Katsina tare,dama tana son Zuwa weeked,amota take ta bama Abbi lbrin yadda taga Canzawar Zahra,Abbi sai yayi amfani da wannan Damar ya dingama Saleema Nasiha wanda suka kashemata jiki sosai takuma yi alqawarin yin amfani dashi…

    Anyi taro lafiya an kai Amarya Lafiya,ta tare agidan Mijinta dake kusa da Asibitin murtala,,Tsakaninsu da Gidan ya Nadir Babu Nisa,Flat hudu ne Uku na matanshi daya kuma nashi ne,to cikin dayan ne aka Saka Nadira komai dai achan achan sai wanda ya gani,Sai inda ma kayi Ra”ayi ne zaka So ganin wata kishiya,ammh sai ka Wuni a Shashenka bakaga Gilmawar kowa ba,kowa na barayinshi sai ko in An hadu agaisa,kowacce cikinsu ta iya kama girmanta da kuma Salon kishinta yayinda itama Nadira ta iya jan kankanta da kuma Salon Jawo Hankalin Mijinta gareta,ammh batare data Cutar da abokan zamanta ba

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!