Maleeka Malik – Chapter Twenty-three
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Abangaren gidansu Zahra ne Shirye Shiryen yafi yawa saboda itace uwar gayyah,Tun ana saura sati daya biki Hajiya Saratu momi ta dauko hayar wata Falmata mai gyara amare daga maiduguri,wacce zata gyara Zahra ciki da bai kafin ranar bikin yazo,Hakika bakaramin burgeta momi tayi ba,haka takasa boye murnata afili dama ita burinta taje ta rikita Saleem wanda zai manta da kowa da komai sai ita shalele Fatimatul zahra’u.
Bangaren gidansu Saleem kuwa Abbi shima ya saki aljihu ana ta Shiryen shiryen biki,Tunda daga kano Abuja za’a kawo zahra sai ta kwana washegari su Wuto zamfara da ita,wannan Auren na musamman ne,domin yazoma Saleema akan gaba,sun gama Final Exams dinsu ta tararro ta dawo gida aka Shiga shagali da ita tayi alqawari sai ta chusama Malika haushi Sosai da sosai,Balle ma Da Sadiq ya sanar da ita itama Zahran ba baya ba akwai kyau ga iya kwalliya da Iya tsara kalamai,Kawai sai taji lokaci ta burgeta saboda neman suna harda karban nombarta ta kirata suka gaisa.
Itako Zahra an samu nayi ai sai aka zare an samu kanwar miji abagas,abun takaichi ma Saleema bataji kunya sanar da Zahra duka sirranka auren Saleem da Malika wanda batasan dasu ba,yazamana Family issues ne,itako zahra kanta ya fashe harda daukan ma Saleema alqawarin sai inda karfinta yakare game da mallakan Saleem,harda ikirarin sai malika ta barmata gidan🤔.,Saboda munafuncinsu yazo daya,sai ga Saleema ta Shirya kayanta tsab tatafi kano gidansu zahra tace chan biki zai fi dadi,Allah barshi in Za”a kawota sai ta biyosu su dawo tare,Ummi da Abbi basu zargi komai ba sun zata dama kila chan kawayene suna da kyakyawan alaqa duba da itama Saleema zamanta yafi yawa akano,basu san ko kullewan ta munafunci bane.
Duk wannan Abun Saleem bai san dashi ba don babu wanda ya sanar dashi,Dayake ma Saleema yanzu bata gabanshi Tunda sukayi karon nan da ita agida yadaina mata dariya,gabda bikin yaga kiranta ammh sai ya Shareta bai daga kiran ba kuma bai calling dinta back,sai ana gobe biki yana Shirin tahowa Abuja inda zasu hadu anan gidan Abbi su Tafi daurin Aure,Zahra ta kirashi tana rokonshi don Allah ya iso kano yau ya hallarci Dinner dasuka Shirya,kawai sai yaji kamar muryan Saleema cike da mamaki yake tambayan Zahra murya wa yakeji kamarta kanwarsa Saleema..?Zahra na mirmishi ta sanar dashi itace,gabansa ya fadi hannunsa bisa bakinsa,yana jinjina al”amarin na Saleema tsoro ya darsu ranshi rai bace yace zahra tabata waya nan akaba Saleema waya ta karba tana gaisheshi bai iya amsa gaisuwanta ba ya kira sunanta a kakkaushe..
“Saleema,Don ubanki uban me kikazo yi gidan su Zahra..? Tana tabe baki tace”Yo laifi ne don nazo gidansu matar da zaka aura,Don mutaru muyi shagalin biki tare..? yana Numfarfashi ya tare ta yana Fadin”Ke rufemin baki munafuka,kinsan Allah Saleema kinsan dai nasan halinki wlh tallahi in naji wata mgana ta Fito to nasan daga bakinki ne,Kuma sai naci ubanki na kakakkrya ki shegiya Mai dogon baki kawai..”Yafada yana huci ya yanke kiran,Tabe baki Saleema tayi kafin tace acikin ranta”Ni ba munafuka bace..”Tafada tana murguda baki kamar tana gabanshi,Nadira ce ke tambayanta ko lafiya,sai ta barsa tace bakomai..,”
Abangaren Malika ma,Joda da Maman Abba suna ta gudanar da Shiryen Shiryen zuwa amarya ta ango,Maman Abba da kanta ta karbi kayan Malika wajen kala biyar taba telanta ya tsaro mata dinkuna na gani na fada,kuma saleem yabada kudin da kanshi,kuma zahirin batu dinki sun Fita sosai,Gashi yayi mata masu yalwar saboda cikin jikinta.
Duk da Malika na boye kishinta bata bayyanashi ammh yau kam takasa control din kanta,balle dataga Saleem ya Shirya kayansa Zai Wuce Abuja bazai dawo ba sai jibi in sun taho da amarya,tana zaune agefen gado sanye da doguwar rigar Atamfa cikin dunkunan da Maman Abba ta dinkomata,tayi mata kyau sosai balle da cikinta yakara tsufa,sai ta dan kumbura kadan fuskarta ta cika sai takara kyau,tagumi ta zabga hannu biyu tana kallonshi yana kokarin saka botir din gaban wani yadinsa Fari ammh Shara shara ne,domin hatta Farar vest dinsa ana gani,Hulansa ya dauko xanna bukar,mai adon baki ajiki domin aikin jikin rigar baki ne,Yadorata akai agogonsa baki na fatar damisa yake daurawa kafin hankalinsa ya koma kan Malika wacce idanuwanta suka fara cika da kwallah.
Yadade yana kallonta kafin ya saki ajiyar zuciya ya karisa kusa da ita,har ya durkusa gabanta bata Sani ba,sai da sanya hannu ya ciremata hannuwan datayi tagumin dasu,kana ta dago tana kallonshi ido cikin ido, Kwabe Fuska yayi yana kallonta yace”Why…? Haba Amanata meyesa kikeson Allah ya kamani ne? ehe kina tagumi abunda kikasan babu kyau meyasa kikeyi..? Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi dukar da kai tayi saboda bazata jure kallon kwayan idonshi saboda suna dauke da wasu sirranka wanda suke haddasamata wasu irin yanayi atare da ita.
Kanta na kasa tace”Na daina..”Ta fada tana sosa hanci dan mirmishi yayi kafin ya saka hannu ya dago habarta yana Fadin”Mejego..Uhmmm..Menene fadamin naji..? Yafada yana shafa lebenta da hannunshi guda daya,rikemai hannu tayi tana kokarin maida kwailarta tace”Katashi katafi kada kayi dare a hanya..”,Kwayan idonta yake son gani,ammh sai taki ta rinka kauda kai,shikuma yana binta da ido,ganin haka yasa yatashi tsaye yasa hannu ya dagata tsaye yana Kallonta cike da kulawa,bai bata zarafin mgana ba, ya budemata hannuwanta tafada,lokaci daya ta saki kukan data ke rikewa Tun dazu..”matseta yayi yana shinshinar Wuyarta cike da salo,lokaci daya yana Shafa cikin jikinta,Tunda dama ta gefe ya Rumgumeta,saboda cikin daya yi mishi shamaki.
Sai da tayi kukanta ya isheta kana tayi Shuru tana Ajiyar Zuciya,tare da sauke Numfashi,Mirmishi yayi yana Kara gyara mata daurin dankwalinta bayan ya bata Sumbata asaman tsakar kanta yake fadin”Kamar kada natafi Amanata,inaji ajikina zanyi kewarki sosai..”Da sauri ta dago kanta tana kallonshi kafin tace cikin sauri”are u Sure zaka yi kewata mallam..? Yana kallon cikin kwayan idanuwanta yace”Very Sure..Kefa zaki kewata..?Bata iya bashi amsa ba,sai kawai tayi dage ta kama lebenshi tana tsotsa da sauri rike kanta da hannu daya yayi,hannu daya kuma yakara mtseta cikin maranshi cike da salo Malika take sumbatarshi har sai da suka gaji kama suka saki juna suna maida numfashi,bisa kirjinsa ta lafe tana Fadin”Zanyi kewarka sau ba adadi mallam,kariga ka zama jinin jikina,rayuwata bazata iya tafiya ba sai da kai,ina nace maka bani son zama dakai akoda yaushe wlh nayi karya mallam,i so much luv u,don Allah karka bani ko bayan kayi aure..”Tafada hawaye na wanke mata Fuska.
Wani sanyi yaji ya Shiga cikin ransa,cike da farinciki ya damki Fuskarta da hannu biyu yana kallonta yace”Da gaske kina sona malika..”?Gyada mai kai tayi hawaye suna kwaranyomata,Bakinta ya sumbata kafin yace”Duk da yadda na lalata rayuwarki na toxartaki keda mahaifinki..? Hannayenshi ta damke tana Fadin”Da shine ma nakejin ka mamaye duka raina,kayi sanadiyar Chanza malika zuwa wata malikar dabam,in ko hakane ka taka muhimman rawa arayuwata mallam,ka koyar dani abubuwa dama,wanda ni banda bakin godemaka sai dai nayita maka addu”an Allah ya saka maka da gidan aljannah Firdausi..”
Bai samu zarafin mgana ba,illah matseta dayayi ajikinsa yana shakan kamshin Turarenta,cikin wata murya yake fadin”kinsa me? bai bata zarafin mgana ba ya cigaba da cewa”Nima sai daga baya nadinga jin Abunda na aikata gareki ban kyauta ba,mussama ranar danaje daukanki agidanku naji matukar kunyar yadda Daddy ya karbeni batare da yayi Duba da irin Tozarcin dana miki ba ya karbeni hannu bibbiyu kuma wani karin nadamar tawa yadda yabani ke batare da Gaddama ba,ranar naji kunya sosai..”Mirmishi tayi kafin tace”Ni kuma abu daya ke ban haushi a abunda kayi min in na tuna..?
Dago kanta yayi yana Fadin”Menene shi..? Gira ta matse tana Fadin”Har ka manta..”Tafada tana hararanshi,ware ido yayi kafin yace”Srry gayamin don Allah..”Yafada yana Shafa dogon hancinta zuwa karamin bakinta,Shagwabe Fuska tayi kafin tace”Yadda ka karbi Virginity na da karfin Tsiya mana..”Tafada tana Wulkamai ido cike da salo,Mirmishi ne ya Subucemai wanda sai da duka fararen hakoransa suka bayyana awaje,hannunta ya riko yana Shafawa har zuwa saman kirjinta yana mirmishi kafin ya gangaro zuwa katon cikinta,cikin husky voice yace”Ni kinga wannan daren D Unforgtable Night and moment kenan bazan taba manta wannan Daren ba..”Yafada yana Shafa cikinta yana wani munafikin dariya.
Fuska ta kwabe tana kallonshi kafin tace”Saboda mene…? Hannunsa ya dora bisa lebenta yana zagaya babban yatsanshi dashi yace”Baki sani ba..? ta gyada kai tana kallonshi Yar dariya yayi kafin yace”Dare ne mai cike da Tarihi ,dare ne da kika Shayar dani wata zuma mai dadi wanda banta zaton akwaita ba,Wlh tallahi i can Explain buh abu daya na sani ke ta dabamce domin Haryanzu kina kan Shayar dani wannan zumar,sai dai na ranar is so Sweet and special..”Yafada yana kanne mata ido daya,Dariya da kunya suka kamata,sai takaimai duka Kirji tana mai kukan Shagwaba dariya yake yana Fadin”Allah am Serious,ko zaki karamin ne,sai na kara tabbatarwa..”Wata uwar harara ta makamai kafin ta warci hannunta tana kallonshi,Juyawa tayi ta dauki yar jakarsa wacce ya sanya kaya ta rataya tana Fadin”Ni..? ai yanzu mun tsufa abari amarya tazo sai tabaka sabuwar zumar,muje na takamaka kaga dare nayi kuma,sadiq karya ga kamar ni na tsaidaka..”
Yana dariyanshi na Nishadi yabiyo bayanta tana tafe da kyar yace”Ai wlh kece kika tsaidani ko ya tambayeni haka zancemai,mganar zumar amarya kuma nidai Taki nasani ki bari in tazo na dandani tata,sai na tantance..”Yafada yana shafa gemunsa na rashin kunya cike da Nishadi tana jinsa tayimai banza ta Fito daga dakin tana mirmishi cikin ranta.
Har cikin kichen din yabi Su maman Abba yayi musu sallama,sukai mai fatan isa lafiya,da kuma Fatan Allah yasa adaura aure lafiya,Tare suka Fito da malika har haraban gidan ita da kanta budemai mota ta turashi,saboda taga bai da niyyar Tafiya sai kwakwumarta yake jakar kayansa ta sakamai akujera mai zaman banza kafin Tarufe mai kofar mota taja gefe tana dagamai hannu,Jagale yayi yana kallonta kafin ya bude murfin motan ya Fito,kawai sai ji tayi ya Rumgumeta kam kam,yana Sumbatar wuyanta,itama matseshi tayi tana kokarin maida kwallarta Sai da suka dau tsawon lokaci kafin ya saketa yana Riko hannunta yace”Ki saka ashafa miki wannan jan Abun na mata,zai yi kyau da hannunki..”Bata kalleshi ba tace”Toh..”Yana kallon Fuskarta yace”Kinji..Don Allah kiyi ko don ni kinji Amanata..”Muryanta cikin sanyi tace”Zanyi insha Allahu..”Mirmishi ya saki kafin ya duka ya Sumbaci bakinta,yana dagamata hannu ya fada mota,ya daura Set belt ya tada motan yana kallonta tana dagamai hannu,shima dagamata yayi kafin yayi Riverse da motar yazuba hon megadi yataso da sauri ya wangalemai get ya sulala waje Malika ta dagamai hannu,sai da ya karisa Ficewa megadi ya maida get ya Rufe kana ta juya zuwa cikin gidan tana Share kwallar data zubo mata.
Tana shigowa sai ta Wuce dakinta tashige tiolet taci kukanta kafin ta wanko Fuskarta ta Fito,cikin kichen din tabi su Maman Abba,wadanda ke ta aikin soye soyen miya da naman kaji bakin da zasu yan kawo amarya Tunda su ba taro zasuyi ba,Abunda yayima malika dadi da Hajiya binta ta mata waya tace Goggon daga malumfashi, da Wata zaliha wacce take ya ga Daddy zasu zo mata gobe,Ho zo kuga murna har bakinta yaki Rufuwa ko bakomai ashe dangi ma suna da ranarsu,gashi zasu suyi mata rana lalle duk wanda baisan darajan dan adam ba,yana tare da Nadama duniya da lahira.
Nan take tambayan joda wani abu ne ake sanya ma Hannu yayi ja,Mallam yace tasaka,Maman Abba da joda suka sanya dariya harda tafawa,Joda ne tace”La Anty Malika Kunshi fa yake nufi..”Maman Abba ta karbe da cewa”sha kuruminki dama nayi ma wata Mami mai lalli na kusa damu mgaba tana kitso tana kunshi,so gobe zan kawota tazo ta Chanchare min ke,yadda Acp zai ka rikice yakasa gane Amarya da uwargida..”Dukkansu suka sanya dariya suna cigaba da aikinsu suna hira ita kuma malika na zaune tana tayasu da hira,gefe daya kuma tana sakin mirmishi ita kadai.
*
Koda Saleem ya isa Abuja ya tarar da gida cike da Yan”uwansu wadanda suka zo daga kumo,maza da mata,wadanda zasu tafi daurin aure gobe,Koda yaje Sadiq ya gaji da jiransa har yayi Fushi ko takanshi baibi ba,saboda haushin dayake bashi na yadda yake wani rawan kafa,akan aure,Abun takaichi ma sai mutum yaga yadda Su Nadira suka maidashi kamar wani kakansu komai suke so shi suke kira suna rawan kafa gayamusu shi kuma yana rawan baki sanar dashi,harda mai masifan kin zuwa da Wuri su wuce kano ayau su samu Dinner dasu Zahra suka Shirya,wani dogon tsaki yajama Sadiq bai kara tankanshi ba,ya Cigaba da laluban nombar wayar Malika yana so ya sanar da ita Ya iso lafiya.
Abokan wasansu kuwa sai tsiya suke mai,suna fadin yayi rawan kafa,da Son mata ko kuma suce mai jaraba ne,Akanannan Shekararunsa har yatara mata biyu,Dariya kawai yake musu yana Fadin”Kunga alamun cewa Saleem lafiyayye ne,don da bani da karfin mazantaka da ba’a kara bani wata matar..”Rufe baki sukayi suna sunne kai sunji mganar dayafi karfinsu,Dariyan mugunta yakeyi cikin ranshi,dama da gangan yayi saboda ya kashe bakinsu.
Ya marwan kuwa da bai samu zuwa ba,ya taimaki kanshi don haka suka tasa mai tsiyan yaki aure har kaninshi yana Shirin yin na biyu raggo kawai har suna Fadin in bai lahiya ne ya sanar su neman mai mgani,dariya takama Sadiq yayi ta darawa har sai da yakira Marwan din yabashi lbrin,dariya yayi kafin yace”Kamar yasan za’a rina,shiyasa ya noke wannan karon,ammh shima insha Allah da zarar yahadu da wacce yakeso zai yunkuro..”
Washegari da karfe 11:30 na Safe aka daura Auren *SALEEM KABIR KUMO*
Da Amaryanshi *ZAHRA BUKAR MADA* akan sadaki mafi daraja Dubu Dari da hamsin,wanda aka daura akofar gidan Alkalin Alkalai bukar mada,daurin auren daya samu hallarta kusoshin gwannati dadama wanda sai dai wasu ka gansu acikin jarida ko gidan talabijin.
Bayan gama Daura auren aka Shiga gaggaisawa,musamman Abbi wanda yake ta sallaman jama’a wadanda suka zo dominshi,shiko angon Amaarya yana gefe,sanye da wata Navy blue din Shadda wacce taji aiki,riga da wando har da babban Riga,sai hulanshi zannah bukar,Shida Sadiq suka sha anko wanda Sadiq din ya Siya shaddan ya kuma dinka musu suka sanya,Sadiq ne keta hada hadar jam’a bakinshi yaki Rufuwa ammh banda Saleem,wanda ya wani hade rau,in kaga yayi dariyan yake toh anzo an bashi hannu ne,ana tayashi murna da Allah sanya alheri.
Su Abbi basu Wuce ba,sai da Bukar mada yatsayar dasu sukayi walima acikin babbann falon gidanshi,wanda sukaci suka sha,suka tashi suna fatan Allah yabada zaman lafiya,Suko su Saleem da sauran abokanshi basu bi tawagar su Abbi su zasu tsaya su taho da amarya..
Tun after 1 Saleem ke masifan Yakamata su Fito su dau hanya,saboda kada suyi dare,don shi yagaji da jira,ammh kuma tawagar amarya suka ki fitowa,Dole tasa Sadiq yajasu da sauran abokan aikinshi zuwa cikin gidansu Zahra suka gaida iyaye da baki,Amarya suna wani bangaren na gidan,sukaji lbrin Shigowar ango cikin gidan,ai zahra dake zaune ana gyara mata Fuska wacce aka Firgita Fuskarta da kwalliya kamar wata aljanna,tana sanye da wani leshi dinki riga da sikat,wanda ya Fito da Suran jikinta,saboda yadda kayan suka kamata,bata ma jira sauran kawaye ba,ta fito Mayafi ahannu,su Nadira ne suka biyo ta da gudu da jakarta suna kokarin gyara mata mayafi.
Lokacin da Saleem yaci karo da Zahra da farko ya tsorata da Fuskarta ganin yadda aka chabamata abubuwa babu kyan gani,kamar wata aljannah,Abunda yafi bashi mamaki babu kunyar Amaren zamani afalon gidansu gaban dubban jama’a ta rikoshi tana mai mgana cike da shagwaba,Sagale yayi mata ammh kuma ya chanza Annurin Fuskarshi kwata kwata ya tsani mace mara aji da kamun kai,shi Tunda kan malika yadaina ma mata kallon goro,toh ji dai malika bai taba zata zai sameta aburduwa ba,ammh sai gashi ta bashi mamaki,Ammh kalli zahra Da yake ganin tatashi cikin hausawa ammh ji Abunda take kamar ba diyar hausa Fulani ba.
Haka ta matsamai suka yi hotuna tana manne dashi,Kawayenta ma duk sunyi hotuna da Sauran abokanshi,Saleema ma tashigo sunyi hoto,ammh fa yanayi yana hararanta,saboda haushinta yakeji,ganin yadda ake Kiranta ko’ina kyace gidan ubanta ne,ko wata kanwar uwarta,Chan suka ja gefe da Sadiq suna gulmansu na fama yana kallonsu aranshi yace”Munafukai kawai…
Suna gama hotuna aka zo aka ja Zahra aka kaita wajen Babanta yayi mata nasiha daganan sai dakin Hajiya saratu momi,itama tayi mata nasiha daidai gwargwardo,acikin nasihan nata taja kunnanta kan ta rage rawan kan nan nata,da shigen Fi’ili da kuma tsiwarta,don wasu mazan basu son Rawan kai,daga karshe ta mata Fadan tabi mijinta,ta kuma zauna da abokiyar zamanta lafiya,kada taji wani baraka ya bullo daga barayinta,Zahra na dunkunkune cikin mayafi kamar ta Allah nan ko Allah Allah take asadata cikin mota don Nasihar Momi ba Shiganta yake ba,Cikin ranta fadi take”Kishiyar ne zan bi ? Hala ita ta auroni tabdijam ai kowa tashi ta Fisshine..”Take fada babu ko alamun Nasihan ya Shigeta.
Haka aka Fito da zahra,ko hawaye babu a idonta,koda na gulmar da amaren zamani keyi ita batayi ba,idonta kir,sai da Nadira ta maketa ta ja mayafinta ta Rufe mata Fuska tana mata mgana cikin kunne kana ta daina Fito da kanta waje😂,Motoci hudu ne suka tafi Abuja,Domin bukar mada yace bayason bidi’an nan duk maison zuwa daga baya yaje ganin daki,duk da dama ango yace amayar kadai yake bukata basai an kawomai wani kaya ba,toh dayake Duniya tana cike da yan boko da masu dashi,shiyasa suma iyayenta basu damu ba.
Motar Sadiq aka sanya amarya Saleem Tun da yaga ana bata lokaci yabi motar wani abokinshi Dcp Sulaiman gidado(Na kishin mata),kusan dama abokai ne😂 ,kuma halinsu yazo daya suna da Shigen jinkai da rainin wayau,suka kamo hanyar Abuja su biyu suna tafe hiransu ta abokai suna Shekewa da dariya,shi gidado shi kebama Saleem wasu dabarun zama da mata biyu,saboda shi yariga yin gaba,Hafsa da Jameela suna fafatawa dashi,duk ya da tara daya gida har yana ba Saleem shawaran duk wacce ta kawo wargi ya bata takarda ya sanda ta gida😂
Dangin mamanta biyu sai na babanta daya,sai kawayenta biyu sai Nadira da Saleema sai zahra su kenan,Suka kamo hanyar Abuja,Zahra tana ji kamar ta bude ido taga sun isa,don ma Nadira ta kwabeta da farko tafara gaddama bazata Shiga motar kowa ba,sai ta angonta wanda tuni yakara gaba,kujimin Amaryar zamani gaakiya Zahra zamanki cikin gidan Saleem akwai shan kallo…”!.
Sai bayan mangariba suka iso gidansu Saleem,nan fa kallo yakoma sama domin ganin tsaruwa na gidansu Saleem,zahra tana cikin mayafi ammh tana kokarin Fito da kai,sai da Nadira ta damketa dakyau tana mata Fada,Ummi da kanta ita da kawayenta suka Fito suka tarbi amarya da yan’uwanta cike da Farinciki da murna,suka dumguma zuwa cikin gidan inda akayi musu masauki adakin na mussaman da’a gyara domin su.
Nan da nan Aka fara jera musu abincin da ababan Sha da’aka tanadar domin su,wasun su ne suka fara gudanar da sallar kafin sufara cin abinci,ammh irinsu Saleema da Nadira sai da sukaci suyi nat,Abunda zai baka mamaki sai ganin Zahra ta cire dankwali ta Cire sikat tana zaune daga ita sai rigan Leshin jikinta da Underwears,ta Iyayen ciki suka mata mgana sai tace,zafi takeji bazata iya zama da Sikat din ba,Ai nan gidan iyayen mijinta ne,So kamar gidan Mijinta ne,Rike baki kadai sukayi suna mamakinta,basu gama mamaki ba sai gashi ta Fito da wani hadin gumbar mata tanaji,Duk kyafta mata idon Nadira keyi saboda Saleema awajen bata gane ba,Da wata kanwar Babanta ta mata mgana sai takara narke Fuska tace’Yo ni goggo Shatu,in bantashi tsaye na taimaki kaina ba,kawai sai na zauna tunda dai kun kasa,ai ni sai nayi Tunda gidan kishiya zan Shiga abun sai da tanadi..”
Tafada hankalinta kwance,daganan ba wacce ta sake mata mgana,Kowacce ta kama kanta,tunda sunsanta bata da kunya ko kadan,Itako zahra harda tafawa da Saleema tana kara zugata,Nadira dai Shuru tayi tana tsoron kada Zahra ta tafka kuskure,koda wani abu ya bullo Saleema yar”uwanshi ce, bazai taba rabuwa da ita,itafa Yana da ikon da zai yarda kwallan mangwaro ya Huta da guda…”
.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
