Maleeka Malik – Chapter Eighteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
…………….Karfe goma da yan mintina Saleem ya shiga da motarshi cikin dan karamin flat din gidanshi,megadinsa ne ya rugo da gudu yana mishi barka da zuwa,bayan ya gaida Malika data ke Fitowa daga mota,tana bin dan karamin gidan nasu da kallo,duk da gidane daidai na talaka,ammh kuma ya burgeta sosai.
Saleem da kanshi ya daukan mata akwatinta zuwa cikin gidan,mai dauke da Babban Falo da 2 bedroom sai kichen,shikenan,ammh duka dakunan akwai kayan more rayuwa aciki,Dayan bedroom din ya kaimata kayan nata,bai mata mgana ba,shi kuma ya Shiga wanda Tun dama nan ne dakinsa,Bai dade ba ya Fito ya Fice daga gidan gabadaya bayan ya sanar da ita ta shiga ciki Shi zai Fita.
Malika ta dade zaune afalo tana bin ko”ina da kallo kafin,tatashi ta shiga dakin daya nuna mata,shima din ba laifi,Tunda yana malale da wani makeken cafet,ja sai Gado da wardrope sai dressing morrior dinshi,sai Kofar tiolet,Dakin duk yayi kura sosai alamun andade ba”a Shigo shi ba,hankalinta ne yatashi ta rasa ta ina zata fara gyara dakin ita daba komai ta iya ba,Ta tuna sanda tana Asalin malikarta,wlh ko baranta bazai zauna awannan gidan ba,ammh gashi rayuwa ta juya da ita,itace zatayi rayuwa awannan gida,kuma batare da wasu yan aiki ba.
Hawaye suka cika mata ido,tayi zaune gefen gado tana goge hanci,ganin zama ba nata bane,cuz Malika bata son zama cikin kazanta mikewa tayi tafara kakkabe dakin tana gyarawa,sai gashi har kayanta ta zazzage daga akwati ta jera cikin wardrope tanayi tana hutawa,tana tunawa da merry da Dose,tana gode musu aranta,wanda ko dauko kaya batasan wahalanshi ba,
Koda tagama gyara dakin wanda harda tiolet ta wanke,don bazata iya wanka dashi ahaka ba,bayan ta ya kage,dakyar take mikewa,Falo kuwa sai da tayi hawaye wajen shareshi,kichen dai ko kallonshi batayi ba da dakin Saleem don koda tagama tafita hayyacinta,wanka tashiga tayi,saboda tsabar jigata azaune tayi sallah Azahar da la”asar alokaci daya saboda jirin data ke gani,Ashe harda yunwa sai lokacin ta tuna duk Wunin yau bata ci abinci ba,Jingina kanta tayi jikin gadon dakin tana tsiyayan hawaye,tana tuna yau fa in kaine to ka tabbatar da zuwa gobe waninka ne,Itace fa *MALIKA MALIK* abaya mace ce,mai aji da jinkai,ilimi da takama,In tagama sai tace bazataci abinci kasar Nageria ba kuma ta zaunu,Bata cikakken sati a kasa daya,ammh sai gashi yau ankoma itake rabe awannan gidan tana kukan Yunwa da gajiya,wayyo rayuwa kenan..
Haka take ta zencen zucci har barci yafara kwasheta babu Saleem ba dalilinshi,kiran wayartane ta farkar da ita daga barcin data fara nan kan Darduman,Zabura tayi ta mike ta dauki wayan wanda ke kan Stool din gadon tana neman Dauki,sunan Daddylove dinta tagani yana kiranta da hanzari ta dauka,tana gaisheshi amsawa yayi cikin murna da Farinciki kafin ya tambayeta iyayen mijinta da shi mijin nata,amsa mai tayi duk suna nan lafiya,nan take sanar dashi yau suka zo zamfara,yaji dadi sosai yayi ta sakamata albarka,jikinsa ta tambaya da kuma hajiya,yace komai lafiya,kafin yabama Hajiyar waya suka gaisa,tana kara jadaddamata data kula da kanta da Abunda ke cikinta,gyada kai take cikin zuciyarta tana kukan zucci.
Bata karajin kuka ya ciyota ba,sai da Daddy ke tambayanta taci abinci,wasu hawaye ne masu zafi suka ketomata,bata samu zarafin sharewa ba,tabarsu suna ta sauka bisa hijabin dake jikinta,dakyar ta furta eh taci saboda batason Ta fadi wani Abunda zai tadama Daddynta da hankali wanda bata da kamarshi duk Duniya,domin shine gatanta yanzu,koda suka yi sallama Daddy yaso ya fahimci wani abu game da ita,ammh ta tabbatarmai da lafiyanta kalau kuma babu Abunda take bukata.
Itako Zuru tayi bayan sunyi sallama,tana tuna lokacin tana gida,sai taga dama ma takecin abinci,in bataci ba ko Daddy ya dinga rawan jikin lallashinta taci abinci,in ko iskacinta yatashi sai tace duka abincin basu mata ba,sai ansake dafamata wani,Watarana ma ko andafa sai tace bataci ta dauki mota taje wani Restaurant taci abincin data ga dama,ammh gashi tana neman abincin ma taci basai ta jira an lallasheta ba,ammh bata samu Ba,Saleem yayi tafiyarshi ya ma manta yazo da wata halitta wai Malika.
Shiko Saleem Tunda ya Fita bai zarce ko”ina ba sai headquater su,meeting din daya tara suka shiga,sai wajen 3 suka Fito yafada office, yana shiga office ya tarda tarin Cases cases,kala kala nan yazauna yana dubasu kwata kwata bai samu sukunin kanshi ba banda sallah babu Abunda ke tadashi,kwata kwata ya manta da wata halitta malika,sai da Ummi ta kirasa tana tambayan ko sun isa lafiya,kuma ya turomata nombar Malika zata kirata ta mata Allah huta gajiya.”Sai alokacin ya saki salatin aranshi yana dafe kai,koda ya duba agogon Shidda saura na yammah,da hanzari ya Fice daga office din yana jin ransa babu dadi in bai manta bata karyaba gwarashi ma dayazo Office yasha tea,ammh itafa bataci komai ba,Tun safe ga kuma ciki,kai ya illah nan da nan yaji bai kyauta ba, gaskiya.
Agurguje ya isa wani Restaurant yayi mata take away din Fride rice,da ferfesun kayan ciki,sai lemon hollandian da Viju,don yaga ko agidansu tafi sonsu sosai,koda ya isa gidan Abun gwanin ban tsausayi,ashe da yunwar ta isheta Sai ta tuna da dambun namanta wanda Ummi ta bata,shi ta dauko ta dinga ci babu kama hannun yaro,toh shine ma man Gyadan suyan Dambun naman ya dinga Taso mata,sai amai tun tana iya tashi ta Shiga bayi har daga karshe takoma tana kelayashi akasan cafet din dakin,koda ya Shige ya isketa kwance cikin amai tana maida Numfashi ga dambun naman ne agefe aroba taci fiye da rabi da kwata,Hankalinsa tashe ya duka gabanta yana Fadin”innalillahi,ke me kika ci haka..’,?
Yafada yana binta da kallo,nan idonshi yabashi amsa,ganin robar dambun naman,ido ya zaro daya tuna yawanshi ammh saura kadan,Dawo da kallonshi yayi kanta ganin yadda hawaye ke Fita idanuwanta sai da yaji tsikar jikinsa ya tashi,Cikin wani yanayi ya Furta'”Dole kiyita amai kalli uban Dambun da kikaji haba,shikenan bazaki dinga kiyaye lafiyanki ba,Tunda kinsan halin dakike ciki..”
Bata iya dagowa ba,dakyar ta iya Furta”Yun..wa…Na..ji..”,Tafada tana Sharbe majina,Wani tsoro ne ya shigeshi ganin tana kara dago ido sama kamar zata shide,da hanzari ya ijiye lodojin daya shigo dashi ya kama hannunta ya ciccibeta tsab ajikinsa ya nufi hanyar Toilet da ita yana Fadin”Am srry sam na manta dake,koda naje office na tarar da tarin ayyukane,su suka daukemin hankali,ammh da kika jini Shuru why not kikirani ta wayata..”,Tanajinsa bata iya bashi amsa saboda wani Haushi ma,daya kamata ita ina taga nombarshi balle ta kirashi,Kalmar ya manta da ita tafi komai bakanta mata,ita take sata kwallah tanayi tana Sharewa da hannu.,sauke ta yayi tayi saurin dafa bango ta tsaya kan kafafunta.
Da kanshi ya hadamata Ruwan wanka,ganin ya Nufota,da hanzari taja baya tana fadin”Zan iya yi da kaina..”Bai damu ya tabe baki yana Fadin”Ok..”Daganan ya Fice daga bayin,yana Fita tabi bayanshi da kallo tana Sakin Siririn kuka,Tanajin takaichi yadda yanzu komai na yaron yake burgeta,tanajin gwara ta zauna dashi Fiye da kowa ayanzu,dakyar ta iya shiga bath din ta gasa jikinta,ammh tanayi tana kukan makomar rayuwa,yanzu balle ma nan gaba.
Sai gashi Saleem ya nadadde kafan wando hannun Riga,shi ya goge aman datayi Tas,kamar bata bata wajen ba,Duk da babu wanda ya kaishi kyamkyamin amai,Aranshi yasa ne kawai don shine silan Shiganta wannan Halin ya barta da yunwa,da kar wani abu ya sameta Abbi da Ummi su tsinemai yabi Duniya,shiyasa ya zage ya gyara ko”ina,koda ta Fito bashi adakin ammh ya barmata sakon Take away dinta,kallo daya tayi ma take away din ta kauda kai domin Duk wani abinci ya Fitar mata aka yanzu,mai ta shafa tazo ta shimfida sallaya,ta nada mayafinta akai,Tunda hijabin ya lalace tayi sallar mangariba,bata tashi daga wajen ba,sai datayi sallar isha”i kana ta rarrafa ta hau gado ta kwanta tana ji kamar bayanta zai cire,Dakyar tasamu barci ya kwasheta.
Shima saleem ya dakinshi yakoma yayi wanka yayi alwala ya fita masallaci nan gaban gidan ne,shima bai dawo ba,sai da yayi sallar isha”i,ya shigo mata da kaza kasassiya koda ya leka dakinta tayi barci duk ta kure,Ya dade tsaye yana kallon Fuskarta yadda duk ta rame kwana biyu,bai san dalili ba kawai sai yana jin tsausayinta yana Shiganshi duk da bayason tasirin hakan ya shigesu sosai,kauda kai yayi zai Fita,sai idonshi yakai kan Lodojin take away din daya yimata,ganin bata taba bane,yasa ya dauka duka harda kazan ya kaimata kichen ya bude fridge ya sakamata aranshi yana Fadin”Zaki nemeshi gobe,in baki ci yau ba..”
Shima dakinshi ya shiga yayi shirin barci yafada gado,sai alokacin ya kara duba wayarsa,wacce ya bari agida misseds din Zahra ba adadi kai ya dafe aranshi yana Fadin”Allah ya hadani jaraba,kai yarinyarnan in mayyace takama mutum sai Allah kuma..”Tsaki yaja afili kafin ya latsa nombar ya marwan wanda hardashi a cikin wadanda suka kirashi baya kusa.
Washegari Saleem bai yarda yabar Malika da yunwa ba,12 nayi yaje yayo mata take away yakai mata,Tunda dai ba’iya girkin zatayi ba,koda ma zata iya yi bata iya dafa komai ba,so ko ma yace tayi zai batama kanshi lokaci ne,balle bata da wani issshiyar lafiya sosai,shiyasa ya dauki Nauyi kullun yayo mata takeway sau uku arana.
Basu samu daman cigaba da karatu ba,sai da suka kwana biyu da zuwa kana yake dora mata da daddare,da asuba kuma ta biyamai,babu laifi Tafara sanin addininta da abubuwan daya kamata tasani,Kayan sawanta kuwa Sargent musa yayima mganar yanason Siyan Atamfofi da lesuna,da hijabai,da kuma inda za”ayimai dinkuna masu kyau,nan yacemai ai baya da mtsalan wannan matarshi tana Sana”ar Saida Atamfofi,gabadaya kwangilan Siyan kayan da dinkin ya tura mata ta acccoun dinta ita kuma ta siyan mata atamfofi da lesuna,aka dinkamata dinkin Riga da sikat,da masu zani,ko masurement dita,shi ya fasalta yadda take,saboda yana ji aranshi ba wani wawan Telan da zai bari yazo ya saka tep ya gwadamai matarshi.😂
Nadira kuwa tacika alqawari domin takira Saleem,ammh itama sai da tayimai 3 missedcalls,kafin ya daga lokacin yana office yana aiki,kanshi ya dau zafi,koda ya daga kiran Bai yi mgana ba ganin bakuwar nombace,Tunkafin yace komai Nadira ta gabatar da kanta amtsayin Cousin Sister din Zahra,yamutsa Fuska yayi yana asking dinta wacece zahra kuma? Amsa ta bashi da Fadin”Zahra bukar mada,sai lokacin ya tuna da mayyar yarinya,Tsuke baki yayi yana jin bayanin Nadira tana sanar dashi irin halin da Zahra ta shiga saboda shi,wai harda kuka baki ya rike yana Jinjina Abun,aranshi yana Fadin”Lalle yarinya kin zake dayawa..”Hakuri yabama Nadira yana sanar da ita Aiki ne yayimai waya baya samun lokacin kansa,ammh tabari zuwa anjuma in ya koma zai kirata insha Allahu,daga haka sukayi sallama ya kife wayar yana jan tsaki,haushi duk ya kamashi Afili ya Furta”,Nayi kuskuren bama Yarinyarnan Digit dina wlh..”Yafada yana Sosa kunnenshi da pen din dake hannunshi.
Itako Zahra agabanta Nadira ta kira Saleem, bayan ta saka wayar aspeaker,tana jin sanda yace zai kirata ta koma gefe tana tsallen murna,Suna gama wayar ko,ta daka tsalle ta Rumgume Nadira tana mata godiya,itako tana binta da dariya bayan ta zaunar da ita tana bata Wasu karin Sirrinka da zata kama zuciyar Saleem dashi itako tana gyada kai murna duk ya cikata,kamar ance gobe ne bikinsu.
Shiko Saleem aranar bai koma gida ba,sai araound 10:39,yakoma agajiye Takeway din Malika ya kaimata fridge,saboda ya iske har tayi barci,Wanka kawai yayi dakyar yayi shafa’i da Wuturi,ya haye gado zai kwanta,wayarsa ya dauka zai kashe,sai yaga sakon zahra na yawo bisa saman wayarshi,yana ganin sakon bai kai ga Shiga ba alqawarin da yayi mata ya fadomai arai,bai karanta sakon ba ya lalubo nombarta wacce bai adanata ba,ammh tsabar nacin kiranta yasa ya ke gane Nombar.
Zahra ko tana zaune dirshan akan gado tayi tagumi da hannu bibbiyu faskekiyar wayarta ne agabanta ta zura mata ido,fuskarta tana nuna tsantsan damuwar datake ciki,Nadira dake gefe kwance ta dago tana kallonta kafin tace”Wai don Allah best baki kwanciya kibar wannan damuwar..?
Bata kalleta ba tace cikin Sanyin murya kamar zata fashe da kuka,..”,Toh bai kirani ba best..”Ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi mgana wayar Zahra dake gabanta ta dau tsuwa,koda ta kyallah ido taga Sunan Saleem wanda tayi Saving da *COOL EYES* da wani uban zabura da chakuma ta damko wayar ba inda jikinta baya rawa take Fadin”Best..best gashi yana kirana..”Mikewa zaune Nadira tayi tana Fadin”Dallah to ki dauka,kin zauna kina rawan jiki,har sai wayar ta katse..”Tana jin haka ta dauki wayan tana karawa akunne cikin sanyayyiyar muryanta ta Furta..”Hello…”
Gyara kwanciya yayi yana Fadin”Hello kina lafiya..”Ya fada kai tsaye,Washe baki tayi kamar zatayi dariya,Hararanta Nadira tayi tana Mata mgana da hannu,da hanzari ta gyara muryanta tana Fadin”Lafiya lau,Fatan kaima kana cikin koshin lafiya kamar yadda nake..”,Fuskarsa ya dan saki kafin yace”Normal…”Shuru ne ya biyo bayan kafin Saleem ya kauda shurun da Fadin”Dazu cousin Sis dinki ta kirani,duk da am very Sure,kina wajen ta kirani,so tayimin complain din kina kirana bana picking,do u know what..? Girgiza kai tayi kamar yana ganinta kamar yasani ya cigaba da fadin”Ban cika son yawan takura ba,ni mutum ne jama”a,kuma ina kokarin kare hakkin kasata,da kuma Tsoron rantsuwan danayi wajen sanya kakin yan sanda,so plz nd plz kidaina damuna da kiranki kina Shiga uzuri na sosai,ki bari ni dakaina in na samu lokaci i promise u i will call u..”Wani yamm Zahra taji idanuwanta suka ciko da kwallah,Ta juya tana kallon Nadira,wacce taji komai domin Zahra ta sanyamata aspeaker.
Alamu tayi mata da hannun data bashi hakuri,Maida kwalarta tayi kafin tace”Ayyh am srry bansan cewa kulawar danayi dakai zai zama laifi ko takura ba,buh insha Allahu korafinka ya karbu za”a kiyaye..”Tana Fada tana yaken karfin hali,mirmishi yayi mai sauti ganin kamar mganarshi ta sosa mata rai,sai yadan saki ranshi yana tambayanta mutanen gidan,kafin ya gangaro yana tambayanta karatu,nan zahra ta tankwashe kafa tana bama Saleem lbrin matakin karatunta,dayake ta iya lankwashe murya,duk bawasu kalamai ta iya ba,Nadira ce ke dorata bisa hanya,Tunda ta Fita budewar ido.
Sai gashi hira tayi dadi tsakanin zahra da Saleema,sai wajen 12 suka kafin suyi sallama,shima bawai don Zahra ta gaji ba,sai don Saleem ya nuna yana jin barci saboda Fita aiki gobe,itako Nadira tun tana jinsu sama sama har barci ya kwasheta,sai da zahra tatasheta tana ihun murna,tana sanar da ita yamzu suka gama waya da Saleem,Nadira ta rumgumeta tana ihu,wanda gar Momi dake dakin Abbansu,ta Fito tazo kofar dakinsu tana tambyansu lafiya,sai lokacin suka dawo hayyacinsu,Nadira ce tace wai Ya Nazir ne yayi musu kyautan 50k ta account yanzu,tsaki taja ta wuce tana Fadin”Allah ya Shiryeku kuyi dai ahankali yanzu dare ne..”
Sai gashi duk dare sai zahra da saleem sunyi waya da juna kafin su kwanta,duk da yanzu ta rage kiranshi,ammh kuma ta chanza taku takoma turamai sakon soyayyah masu sanya zukata,wanda Nadira ke Rubuta mata tana turamai,na safe dabam na rana dabam hakama na dare shima dabam,kuma kalamai so sexy and Romantic,shiyasa lokaci kadan Zahra ta fara burge saleem,har baya iya barci sai yaji muryanta,duk da wani lokacin yana basar da ita,bayason soyayyarsu tayi zurfi kuma yazo yace zai aureta Abbi ya dakatar dashi.
*BAYAN WATA DAYA*
Wata daya kenan da zuwansu zamfara,Alhamdulillah kawai malika zatace domin abubuwa suna Tafiyan mata yadda Yakamata,duk da akwai abubuwan da ba haka taso ba,bangaren karatunta kuwa Tuni tayi nisa son Saleem bai yi mata da wasa,koyar da ita yake kamar yadda ya dau alqawari,bata aikin komai sai gyara dakinta da Falo in yayi kura,da yan kwanuka in ta bata,Mganar abinci kuwa Saleem yadauke mata wannan Nauyin nayimata takeaway kullum sau uku arana,kuma babu laifi yana bata kula sosai abangaren cikinta,ga kuma kayan daya kawo mata kamar za”a bude shago,ta dade bata iya daura zani ba,sai da ya dinga koyamata,ko daura dankwalin ma,shike amsa yana gwada mata yadda zatayi har tasamu ta iya dan sagala shi,ganin Riga da zanin na bata wahala sai takoma sanya masu sikat kawai saboda sunfi mata saukin sawa,duk tafi sati kafin ta saba da saka kayan,da farko damunta sukeyi ba kadan ba,sai hijabai wajen kala ashirin da masu hannu da marasa hannu,kuma duka yadi uku da rabi rabi ne,in tasaka har kasa suke kaimata kamar wata zulumbiya😂
Satinsu biyu da zuwa gidan ta samu ziyarar wata makociyarsu wanda gidansu ke kallo nasu,MAMAN ABBA,Nurse ce tana aiki general hopital Zamfara. Mijinta kuma manajan bankin First bank ne,danta daya Isma’il suna kiranshi Abba,Ta shigo suka gaisa da malika,nan take sanar da ita ga gidanta nan kusa da nasu,tun sadda Acp ya sanar da Baban Abba,cewa yazo da matarsa takeson Shigowa ammh kuma bata samu lokaci ba sai yau,fatan zasu dinga zumunci….
Murna ta cika Malika rana ta farko Tun bayan Shiganta wannan Halin ta samu wani akusa da ita,cikin Fara”a da sakin Fuska ta karbi Maman Abba,wanda suka dade suna hira kafin tayi mata sallama tatafi,da saleem ya dawo jikin Malika na rawa ta sanar dashi zuwan Maman Abba,tace kuma ya barta itama ta Shiga wajenta,murtuke Fuska yayi yace bai yarda ta Fita konan da kofar gida ba,Dole ta hakura duk da ranta baiso ba ammh bata nuna mai, ba,Wannan Abun yana sa Kimarta yana karuwa a idon Saleem sau tari zai kuntatamata da gangan ammh ko a fuska bata nuna taji haushi ko ranta yabaci,sai dai shi yadaga baya yaji bai kyauta mata ba sam.
Maman Abba batayi Fushi ba dataga Malika bata Shigo ba kamar yadda tace sai ita ta Shiga wajenta,suka kara gaisawa,nan take kara lura da cikinta har ya Fito,ada kamar bazata tambayeta sai kuma ta tambayeta ko ta fara zuwa awo..? amsa mata tayi da”a”a.Nan,Maman Abba tace aiko yakamata kifara zuwa awo,saboda daga ganin cikin jikin ya kai 4month in ma baifi ba,Mirmishi kawai malika tayi tana sunkuyar dakai,don azahirin gaskiya bazata iya dora komai kan cikin jikinta,game da Saleem ba,don bata ga yana wani damuwa dashi ba balle dokinshi,balle har yagane ya isa zuwa awo.
Bata mai mganar ba,sai da aka kwana aka Wuni,bayan sun gama karatun dare,take mai mganar zuwa awon da Maman Abba tayi mata ya dade yana kallonta domin shima satin daya Wuce Ummi ta kirashi take tambayanshi Malika ko tafara zuwa awo..?karya ya zabgamata yace eh kafin ya gyada kai yana Fadin”Yaushe ne tace zaki fara zuwa awon..?Kanta na kasa tace “Bansani ba,sai in ta shigo na tambayeta..”Mikewa yayi daga tsaye yana Fadin”No gobe da Safe ki Shirya ki shiga gidan sai ki tambayeta,ko goben zaki fara sai ki sanar dani..”Gyada kai tayi tana Fadin”ngd..”Bai kulata ba ya Fice daga dakin zuwa nashi,yana kokarin amsa wayarshi wacce zahra ce ke kira.
Haka ko akayi da safe bayan ya tafi tayi wanka ta saka atamfanta dogowae riga da dogon Hijabinta ta Shiga gidan Maman Abba ta sameta tana Shiri zata asibiti yau Dutyn safe gareta,nan suka gaisa cikin Fara”a Shine take sanar da ita Abunda Saleem yace,Maman Abba tace “Toh ai Faduwa tazo daidai da zama,gobe ne ranar Zuwa awon ,sai ki koma ki sanar dashi,gobe in zan Tafi sai mutafi tare,Allah barshi bayan an miki scaning da sauran abubuwa,ni sai na cigaba da dubaki agida.
Haka ta sanar da Saleem da daddare bayan ya dawo,bai yi gardama ba yabata kudi 10k yace taje dashi,da kanshi ya dauki wayarta ya saka nombarshi yace takirashi in ance ana bukatar wani abu,Murna takama malika ranar batayi barci ba tana murnan yau itama zata asibiti ta shiga sawun iyaye mata masu ciki,koda 8 tayi sun tsufa ageneral ita da Maman Abba,wacce ta tukasu asabuwar motarta 306.
Sakamakon zuwanta da wacce take da sani awajen Bata wani jima ba,aka bude mata Fayel likita ya dubata kafin aturata dakin awo,Shima din bata jima ba Tafito,Aka bata sati hudu ta dawo,batayi amfani da kudin da Saleem ya bata ba,saboda asibitin ta gwannati ne,sai dai ta siya magungunar da’aka Rubuta mata na karin jini,Maman Abba da kanta takara tukota ta maidata gida tana ta mata godiya.
Saleem yana office ammh kuma rabin hankalinsa na kan Malika yana so yaji ya ake ciki,gashi bai karbi nombarta ba,Ganin har wajen yammah bata kirashi ba,kuma yau bashi ya kaimata abinci ba, Sarger musa ne,ammh ya tabbatar mai da megadi yace ta dawo Zahra ce ta kirashi ta daukemai hankali da hirarta tana mai kukan Shagwaban yaki yazo ya ganta,Shikuma bayaso yayi mata alqawari ya saba ne,yau dai ya tabbtar da mata data jirashi zai zo dis weeked insha Allahu,Murna kamar zata kashe Zahra tayi ta murna tana tsalle ita da Nadira,wacce itace ke dorata adukkan hanya data kama Saleem yanzu ahannunta,duk da bai gama kamuwa duka ba.
Shiko Saleem yanajin aransa zai iya maneji da zahra,domin yana cikin wani mayuwacin hali na bukatar mace akusa dashi,bayaso yaje ga malika tadauka yafara sonta ne,Ko ana Farko yayi mata hakane don tagane kuskurenta,yanzu kuma sai yakoma..? Abun da kunya gaskiya bayason yarinyar ta rainashi sam,ammh kuma yakasa Fuskarta wani abu koda zai ga mata awaje koda ko da wani irin banza Shiga ne basa burgeshi kuma bayajin hankalinshi ya tashi,ammh da zarar ya dawo gida yaga Malika,sai kawai yaji yanayin jikinsa ya chanza,ko dakinsa tazo karatu haka zai dinga jinsa konai nasa na chanzawa,In ya kalli cikin idanuwanta tsausayinta da sha’awarta na kara Tsumashi balle yanzu yadda ta cika sosai kirjinta da kugunta sun kara Fitowa,haka Fatar jikinta tayi kyau Fuskarta tacika da kumatu ta kuma kara haske Fata,koda kuskure jikinsu ya hadu da juna,ranar haka zai kwana mafarki sai Da asuba yayi wanka Kafin ya tafi mssallaci,Yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa,Sai kawai ya yanke shawarar yayi aure,Tunda dai bazai iya kara Tunkarar malika ba,gwara ya neman ma kanshi mafita duk da yana tsoron kada Ummi da Abbi su dakatar dashi.
Koda ya koma gida,gim da rai yayima malika,yana ijemata takeaway dinta ya Shige daki,ya kulle koda tazo da littafan karatunta taji kofarshi akulle,sai kuma taji jikinta yayi mata sanyi Ranar dukkansu ba wanda yayi barci,shi yana Mukurkusun Ciwon mara da fama da sha’awarta,ita kuma tana juye juyen damuwar da Saleem yake ciki,kwata kwata hankalinta yaki kwanciya,Har da safe ma daya Fito data gaisheshi dakyar ya amsa yana wani cin mgani,Tana so ta sanar dashi Abunda yafaru a asibiti ammh kuma tana jin tsoro,shine da kanshi ya tambayeta,cikin faduwar gaba ta sanar dashi,Harara ya zabgamata yana mata fadan meyasa bata kirasa ta gayamsa ba..? saboda ta rainashi ko? toh in tagaji da zama dashi ne,toh shima ya gaji zai maidata wajen mahaifinta bazai iya karban amanar ba,ta inda yake shiga batanan yake Fita ba,Zuru tayi tana digan hawaye,hakuri takeson bashi,ammh ganin yana cikin zafi shiyasa ta kyaleshi har ya Fice daga gidan yana ta bata rai,shiko aranshi baijin dadin Abunda yake mata,ammh haushin shi daya shine ita tajamai yake kwana yana Fama da tamkewar mara,shiyasa sai ya sauke komai akanta,Kuma Abun takaichi sai yayi mata fada,yakoma yana Fama da damuwa,duk da bazai iya bata hakuri ba,ammh babban Abunda ke dafamai zuciya shine Kukan Malika.,Kukanta na bala’in dagamai hankali barin ma ta kalleshi tana share hawayen,sai yaji jikinsa yayi sanyi kamar ya Rumgumota yayi ta lallashinta,ammh jin kai yahanashi.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
