Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    ………………..Koda ya Fita Fuu,haka ya Bude motarsa ya fada yana sauke Numfashi,sama sama jingina kansa yayi da jikin kujeran motana yana sakin wani Huci mai zafi,kansa yafarawa shafawa zuwa sumar sajensa,lokaci daya yana tsigen gemunsa wanda ya fara taruwa,duka idanuwansa suna Rufene

    Ya dade ahaka kafin ya bude idanuwansa yana cija lips dinshi na kasa,Abunda yafimai bakinciki shine cewar da Abbi yayi wai yaje yabama Malika hakuri? to uwarta yayi mata da zai bata hakuri? Shi ba”a ce ta duka har kasa ta bashi hakuri ba,sai shine za”ace ya bata hakuri,Durun uwa ne ma..? yafada yana sakin wani dogon tsaki kafin ya gyara zamanshi yana kokarin Daura Set belt yake fadi abayyane.

    “Zanje dai na taho da ita kamar yadda Abbi ya bukata,ammh mganar bata hakuri wlh Uwarta bata haifeta bama,wacce zan ba hakurin gaskiya..”Yake Fada yana kunna motar nashi Afusace yayi mata kwana kafin ya shiga sakarma megadin hon ba sassautaawa kamar zai cirema mutane kunni,koda ya budemai get din a guje ya Fice yana kara sakarma motar Speend kyace zai tashi sama ne.

    Ransa amatukar bace yake kwarara gudu bisa Kwalta,yadda zuciyarsa ke tafasa haka yake tuka motar,cikin abunda baifi awa uku ba,sai gashi yana zuba hon makeken get din gidansu Malika,koda aka wangalemai get din afusace ya danna kai gidan,har yana kusa takema megadin yatsun kafa,da kallon mamaki yabi motar sanda take gyara parking.

    Sai da ya daidata kanshi kana ya Fito daga motan,ammh Fuskarsa tamau babu alamun Fara”a ko kadan,Megadin ya, ya Fito da hannu,wanda dama yake tsaye yana kallonshi cike da tsoro,jikinsa na rawa yazo yana Fadin”Brka da zuwa yallabai..”giransa ya hade yana Fadin”Ka shiga ciki kace ana mgana da mai gidan..”Kallon mamaki megadin ya bishi dashi,yana so yace mai ai Alhaji baya da lafiya bai Tafiya yanzu,ammh yanayin Saleem din yasa dole ya Wuce sumu sumu jikinsa na rawa.

    Megadi Hajiya binta ya sanarma da sakon,wacce ta kalleshi cike da mamaki tana Fadin”Waye shikuwa..? baisan Alhaji baida lafiya bane..”Yace”ina ga hajiya…!”

    Tabe baki tayi tana Fadin”koma waye sanar dashi ya shigo ciki Alhaji baida lafiyan da zai Fito ya sameshi..”Jikinsa na rawa ya Fice da hanzari,koda yazo ya iske saleem jingine jikin motarsa yana faman latse latsen waya,rankwafawa yayi yana Fadin”Yallabai hajiya tace ka shigo ciki,don Alhaji kam bai da lafiyan da zai Fito ya sameka..”Sai alokacin ya tuna ance fa Alhaji Abdulmalik ya samu shanye barin jiki,Basarwa yayi kafin ya wuce kai tsaye bayan ya tusa wayarsa cikin aljihu lokaci daya yana Tura duka hannuwan nasa,cikin aljihun cikin takunsa na isa da takama ya nufi kofar da zata sadashi da babban Falon gidan.

    Da sallama ya shiga Falon lokacin da wani sanyi hade da kamshi ya dakeshi,ga taushin wani shigen grass cafet dake malale afalon,Tabe baki yayi yana bin Falon da kallo,nan ya cikaro da taftafkan hotunan Malika akowani kusurwa na bangon Falon,Yatsine yake kallonsu kafin yay tsaki aransa yana kara jin tsanarta,Yana nan tsaye sai yaji motsin Ana saukowa daga saman Bene,Dama aleeady yabama Steps din baya ne,so sai ya waiwayo daidai lokacin da Hajiya binta ta karisa Saukowa,idonta karaf akanshi tana karemai kallo.

    Duk da sau daya Tak ta ganshi,ammh ta shaidai shi,shiko ganin yadda ta kureshi da ido ne yasa,ya dan rankwafa yana Fadin”Ina yini hajiya…”Ta amsa da “Lafiya lau,sannu da zuwa,kamar Saleem ko? mijin Malika..”Wani haushine ya kamashi,nan da nan ya hade giransa kafin ya dan saki yake yana Fadin”Eh…”Daga haka ya tsuke bakinsa,yana kallon gefe.

    Baki ta washe tana Fadin”Ah!Masha Allah sannu da zuwa yaushe ka dawo,domin kamar naji ana zencen baka kasar ko.? Fuskarsa ba Fara”a yace”Eh wlh jiya na dawo..”Juyawa tayi tana Fadin”Allah sarki,biyo muje Alhajin yana sama ne..”Tafada tana Taka Step,shima ya bi bayanta yana zabgamata harara sai kace ita ta kirashi Dole.

    Suna shiga Falon sama,inda Daddy yake zaune kan kekenshi yayi Shuru yana Tunanin Rayuwa,Sai yaji hajiya binta ta Shigo tana Fadin”Alhaji kayi bako..”Waiwayowa yayi yana Fadin”Bako kuma..? Ya fada da sigan Tambaya,Eh tace kafin ta cigaba da cewa”Saleem ne Mijin malika…”Tafada daidai lokacin da yake saka kanshi cikin dakin bayan ya cire takalminsa.

    jin Abunda Hajiya binta ta Fadane yasa Daddy ya washe bakinsa duka yana Fadin”Masha Allahu….”Yake Fada sanda Saleem ya kariso gareshi shikuma ya danna Abun tafiya da keken atare suka tarbi juna,Saleem yayi saurin yin kasa yana bin Daddy da kallo,ganin yadda lokaci daya y koma kamar wanda ya Shekara yana ciwo.

    Hannayensu sarke ana juna Daddy yake Fadin”Saleem sannu da zuwa,yaushe ka dawo kasar,don Kumo ya sanar dani daga wajen aikinku an turaka wani karatu ko…”?Kan Saleem na kasa kunya duk ta kamashi,bai taba zaton wannan karban mahaifin Malika zai mai ba,sai gashi yaga sabanin Tunaninshi,Kasa hada ido yayi dashi kansa na kasa ya Furta..”Eh Daddy jiya na dawo..”Daddy yace”Masha Allah,an samo Abunda akaje nema ko..”?Kara sadda kai yayi yana Fadin”Insha Allahu Daddy…”

    Gyada kai yayi kafin yace”Allah ya bada nasara,ya kuma dafa maka…”Kasa amsawa yayi da Ameen,saboda nauyi da nadama,yana jin zuciyarsa na kara Rauni,kafafun Daddy yake kallo,yana Tuna sanda yazo da kafarshi ammh yau sai gashi zaune baya iya takawa ko nan da chan,Wani imane yakara kamashi,yana Tunanin iyaye irin Daddy sun kare,wanda za’a yima yarka wannan Cin zarafin da tozarcin,ammh kuma ka hadu da wanda ya aikatama haka,kuma ka karbeshi da duka hannuwaka..? Lalle yaji kamar ya maida hannun agogo baya.

    Daddy ne ya kalli Hajiya Binta yana Fadin”Binta samomai Abun shama,kinsa fa ya yo Tafiya..”Gyada kai tayi zata Fice yayi saurin cewa”A”a Daddy abarshi bana jin kishi…”Girgiza kai Daddy yayi kafin yace”A”a kar muyi haka dakai,kafa sha hanya,dole kana bukatar Ruwa,maza binta kawomai don Allah…”Da hanzari ko ta Fice,shiko saleem duk ya kasa sakin jikinsa,ballema ya dago kanshi Daddy ne ya kalleshi yakuma karanci yanayinsa mirmishi kawai yayi kafin yace”Ya ka barosu Abbanka,ya kuma su Hajiya da Umminka..? Kansa na kasa yace”Duk suna gaisheku..”Ya amsa da “Muna amsawa….”

    Daga haka Shuri ya biyo baya har Hajiya ta dawo dauke da tire shake da kayan sanyi,ta jiye agabanshi kafin ta sake Ficewa,Hannunsa Daddy ya saki yana Fadin”Sha ko Ruwane Saleem ka jika makoshi…”Baiyi gaddama ya dauki roban swan mai sanyi ya Tsiyaya akofi yana sha kadan kafin ya ijiye yana sauke ajiyar zuciya,so yake yayi mgana ammh kunya da Nauyin Daddy sun hanasa wani motsi.

    Gajiya yayi da sadda kai,ya dago yana kallon Daddy kafin yace”Armm Daddy dama Dalilin zuwana Abu daya ne zuwa biyu,na farko domin na baka Hakuri bisa Abunda ya faru,don Allah Daddy kada ka rikeni ka yafemin ajizanci ne na Dan Adam,da kuma sharrin Shedan sai na biyu don na sanar dakai na dade da maida Malika amtsayin matata,yanzu haka nazo neman izininka ne zan tafi da ita,muje mu zauna muyi zaman Aure na hakika..”

    Har ya gama mganarsa Daddy na mirmishi kuma yana jinjina kai,Bai katseshi ba sai da ya gama kafin yace”Saleem…” ya kirasa da muryansa cikin taushi da kulawa dagowa yayi yana kallonsa Kai Daddy ya kada mai yana Fadin”Taso kazo kusa dani kaji…”Bai yi gaddama ba,yaja jiki zuwa kusa Da daddy,wanda ya kama duka hannuwanshi ya rike gam,yana kallonsa ido cikin ido kafin yace”Bantana rike ka araina ba Saleem,saima Dadin Abunda ka aikata Naji,ko banza kafara Daidaita rayuwar malika,ni kuma kasa na gane gaskiyan dana gaza ganewa shekara da shekara,Hakika zuwanka Rayuwar Malika Saleem haske ne,kuma Rahama ne,dama aikinka ne kai kafara kuma kai zaka karisa,Malika zata bika,duk inda zaka sanya kafa zata saka Domin na bar duka amanarta ahannunka ne Saleem…”Ya fada kwallah tana cikamai ido …

    Gabadaya gwiwan Saleem tayi sanyi yama kasa mgana,ya bude baki zaiyi mgana kenan hajiya binta ta dawo dakin tana tambayan Saleem ko akawo mai lunch ne,girgiza mata kai yayi batare da yayi mgana ba,Daddy ne ya kalleta yana Fadin”Binta taimakeni ki kiramun Bby,ki kuma umarci yan aikinta da su hadamata duka Abunda zata bukata acikin akwatunata,,ga mijinta nan zai wuce da ita yanzu…”Yafada daidai sanda kwallar dayake rikewa ta zubomai,Hajiya binta bata ce komai ba ta juya tafita,Shiko saleem yana ganin sanda hawayen Daddy ke diga bisa hannunshi,ammh yakasa kwakwaran motsi saboda kalmar nan da Daddy ya Furta na yabashi duka *AMANARTA*…”

    Hajiya Binta zaune ta iske Malika tana cin abinci tashinta daga barci kenan,sakon Daddynta ta sanar da ita,bata bar dakin ba har sai da malika ta mike sanye da doguwar riga baka na kamfanin Armani,wanda bakin Siririn gyalen dake kanta ta sakaloshi zuwa wuyanta,kallo daya zakamata ka Fahimci tana da shigar karamin ciki,kodon ganin yadda tayi wani danya sharaf da ita,sai da ta Fice zuwa Falon na Daddy kafin Hajiya Binta ta Umarci su Dose da su hadama Malika duka kayanta na anfani cikin manyan akwatunanta,amsa mata sukayi da toh kafin su Shiga ciki su fara hada mata kayan.

    Bata da masaniyar zuwan saleem,domin Tun safe tana daki bata Fito ba,shiyasa kanta tsaye ta shiga falon ko sallama batayi ba,don ba halin malika bane shiga waje da sallama,Bata lurama da Saleem dake durkushe gaban Daddy ba,wanda duka hannuwanshi ke hannu Daddyn kamar mai rokon wani Abu.

    Tana zuwa ta duka ta bashi peck agoshi tana Fadin”Dadylove ya jikin ka..? Hajiya tace kana kirana hop dai ba wata damuwa ko..? Tafada tana kokarin dukawa kusa dashi,sai ji tayi cinyarta ya gogi Gwiwan kafar wani azabure ta kalli inda taji Abun yatabata,shima daidai lokacin ya dago suka ko Hada Four eyes dashi.

    Dam!Dam!Dam! gaban malika ya buga bayan ya amsa lokaci daya,ko mutuwa tayi ta dawo bazata taba mantawa da wannan muguwar Fuskar ba,wacce bata cike da komai sai mugunta da zalunci uwa uba rashin imani,Ai sai ga Malika saboda tsoro da razana tayi baya zata Fadi Allah ya taimaketa ta rike karfen keken Daddy,ta zauni da duwawunta dabas akasa,ko”ina na jikinta babu inda baya rawa kafin kace me ta kamkame jikinta hawaye ya Shiga wanke mata fuska,Shiko saleem kallo daya yayi mata bai kara,don in ya cigaba da kallon Fuskar shegiya zai iya tashi ya zubamata marunka da zatayi hawaye mai dalili gaban Ubanta,kauda kai yayi yana jan Allah isa Aransa,sai daga bayama yake Tunanin me ma yasa ya dawo kasar? kai gaskiya Abbi bai mai Adalci ba.

    Daddy daya lura da yanayin malika Sai ya saki hannun Saleem guda daya ya mika mata yana Fadin”Taho Babby,mijinki ne yazo tafiya dake…”wani yam! taji lokaci daya kanta ya sara da karfi Dafe kirji Tayi kafin tace”No Daddy…..No…”,Take Fada tana sharan kwallah gwanin ban tsausayi

    Girgiza mata kai yayi kafin yace”A”a Babby karki ce haka,plz come closer kinji…”Yake Fada yana mikamata hannu,shiko saleem aransa addu”a yake Allah yasa kartace zata bishi,ammh sai addu”arsa bata karbu ba,jikinta na rawa ta matso ga Daddy kafin ta damkamishi hannunta kwara daya hada hannunta yayi dana Saleem waje daya ya damke,dukkansu sai da sukaji wani Shock yajasu,tare dukkansu suka saki ajiyar zuciya suna Runtse ido.

    Daddy ya kalli Saleem yana Fadin”Saleem ga Malika nan,Na damka amanarta da amanar rayuwarta a hannunka na har abada,kai ne, uwarta kai ne ubanta yanzu,Saleem ina da kyakyawan Shaida akanka,don Allah kada ka bani kunya kayimin alfarman tsayawa tsayin daka wajen kula da tarbiyan Malika,ka koyar da ita ko kadan ne daga cikin Abunda ka sani,kazamo wa gareta,ka zamo mata kani,bayan kazama mata shafin wani kawa ko aboki, Don Allah don darajar iyayenka kada kabar rayuwar Malika ta sake lalacewa akaro na biyu,bata da wani gata anan Duniya yanzu sai kai,ni yanzu tawa ta kare,ba lalle bane na sake daura wasu shekarun araye …”Ya fada kuka ya kwace mai,Wani kuka ne yazoma ma Malika da karfin gaske ta fada jikin Daddy tana saka kanta bisa cinyarsa tana gunjin kuka take Fadin

    “plz Daddy Don’t let me go…”plz….”Take Fada tana kuka mai cinrai,hannayensu ya saki kafin ya kama kan,Malika yana tashafawa alamar lallashi muryansa cikin karaya yake Fadin”Am srry Babby kidaina kuka kinji ko,ko bani na tabbata saleem,da mahaifansa baza su barki kiyi kukan maraici ba,Ki bishi sau da kafa,kiyimai biyayyah,ki kuma guji Abunda bayaso,Don Allah Malika kibi mijinki Duk Abunda yace kiyi kiyishi matukar bai sabama shari”a ba kinji ko..”Gyada mai kai takeyi tana kuka kamar zata Shide shima hawayen yake.

    Saleem dake gefe shima kamar yayima Daddy kwallah,saboda yadda suka bashi tsausayi,baisan sadda yasaka Tattausan hannunshi yana Sharema Daddy kwallah ba kafin ya koma ya dago Malika yana kallon cikin idanuwanta cike da wani yanayi wanda Shikadai ya barma kansa,sani itako,runtse idanuwanta tayi tana jin wani Fargaba acikin zuciyarta Hannaunta ya damka ya damke da karfi yana Fadin”Na karbi Amanarka Daddy da zuciya daya kuma nayi maka alqawarin ni Saleem kabir kumo zan kula da Malika Fiye da yadda zan kula da kaina,zan tarbiyarta da ita kamar yadda uwa zata tarbiyarta da yarta,zan bata kulawa tamkar yadda yaya zai kula da kanwarsa,Sai dai Abunda na gaza zan barma Allah sauran..”Ya fada yana hada duka hannunsu su uku ya damke atare.

    Daddy na hawayen Farinciki yana ma Saleem godiya kafin ya kalli Malika yana Fadin”Ki tashi kije ki Shirya babby,daganan ki tahomin da mukallayen gidan nan dana motocin nan,tare da takardan sakamakon likita game da cikin da kike dauke dashi…”Dam!Gaban saleem ya buga,da rawan baki ya kalli Daddy yana Fadin”,Ci..ki….Ma…Li….Ka…..Ke…Da…Shi….”?

    Yafada bakinsa na rawa,gyada mai kai Daddy yayi yana Dafa kanshi daidai lokacin da Malika ta mike tana shesshekan kuka ta Fice,Wani yanayi Saleem yaji sai ya samu kanshi da kurama bayan Malika ido,yana Jin wani iri acikin ranshi,ciki kuma? kai yanzu wai har ya isa yin ma mace ciki…? Bai gama mamaki ba,yaji Daddy na gayamai jikin da malika takeji,gyada mai kai kawai yakeyi yana kiyasta abubuwa da dama cikin ransa,gefe na zuciyarsa na Farinciki ammh kuma wani shashe na fadin”Koda cikin sai ta ci ubanta,ai babu daga kafa yarinya…”

    Ba Malika takawo makullyan ba,Hajiya binta ta kawo,shiko Daddy ya hada duka ya damkama Saleem yana Fadin”Duka kyautar danayi maka,da zuciya daya nayi maka shi,saboda haka gasunan na maida maka,sai dai in bakaso ka kyautar dasu,duka mallakinka ne..”Girgiza kai yayi yana bin takardan sakamakon Cikin Malika yana Fadin”Bazan kyautar ba Daddy,ko wanchan karan dana dawo dashi rashin sani ne,ammh wannan karan na karba kyautan naka da hannu bibbiyu Allah ya saka da alheri ya kuma baka lafiya..”Da Ameen ya amsa yana ta sakamai albarka.

    Malika ko tana chan tana ta kuka kamar za”a zareta ma rai,Hajiya binta ke ta lallashinta,bata chanza kaya ba da wannan bakar dogowar rigar hajiya ta riko hannunta suka nufo dakin Daddy,yayinda da Su Dose suka fara Fita da manyan akwatunanta guda uku suma jikinsu duk yayi sanyi na Tafiyar madam dinsu,wanda suna zaton wannan karon bada su za”a tafi ba.

    Gaban Daday da saleem ta durkusar da ita tana Fadin”An gama hada komai,sun Fita da kayan zuwa waje…”Saleem najin haka ya mike yana duba agogon hannunshi,biyu saura na rana,Kallon Daddy yayi yana Fadin”Toh shikenan Daddy mu zamu Wuce kada muyi dare bisa hanya..”Kallonsa Daddy yayi yana Fadin”Haba Saleem kamar na koranku kubari kuci abinci kuyi sallah sai ku dau hanya ko..”Saurin cewa yayi “No Daddy karka damu zamu tsaya bisa hanya muci abinci muyi sallah,bani so muyi dare ne…”

    Shuru Daddy yayi kafin yace”Shikenann Saleem Allah ya kiyaye hanya,ngd sosai ka gaida su Kumo din Allah ya kaddara saduwa…”Da Ameen ya amsa yana mikamai hannu suka sake musabaha kafin yafara taku zai Fice daga Falon,da hanzari Daddy yafara tura kekenshi zuwa cikin bedroom dinsa yana fadin cikin wata irin murya..”Binta ki Fita da Malika daga dakin nan,bani son ganin tafiyarta don Allah…”Yafada yana tsiyayan hawaye,Jin haka yasa malikar kwace jikinta dagana Hajiya binta ta bishi da gudu ta rumgume bayanshi tana Fadib”Wayyo Allah!Daddy na…..”Take Fada tana kuka kamar zata shide,bai saurareta ba,yana share kwallah,ya cigaba da tura keken zuwa cikin bedroom dinshi yana Fadin”Kije Babby,insha Allahu nan gaba zaki zama Abun alfaharin ya”yanki da al”ummah baki daya koda bana raye,kije Allah yayimiki Albarka yakuma zaunar dake lafiya agidan mijinki…”Yafada yana wani kuka na zuwarma,tura kofar bedroom din nasa yayi ya shige yana Rufe kofar….

    Zuciyarsa ke bugawa da karfi tana Fat!Fat!Ammh kuma gefe daya Farinciki yake na ganin ya sauke wannan Nauyin dake kanshi wanda ke damunshi Shekara da shekaru,na damka amanar Malika hannun wanda zai gyara mata rayuwarta daga Duhu zuwa haske,kuka yake yana Fadin”Allah na tuba Allah ka yafemin ya Allah..Astagafurrillah.!”Yake Fada yana daga hannunshi sama hawaye suna zuraromai..!

    _Wayyo Allah!wlh Sai da nayi kuka😭Wannan page din ina rubutashi inaji yana tabamun zuciya sosai…Kai Allah kadamu da kyakyawan kaddara,ka kuma bani damar yin Nadama cikin lokacin irin na Daddy,ba sai lokaci ya kuremana ba kamar Fir’Auna..,Allah ka tsaremu Ameen_

    Nan wajen Malika ta Fadi tana gunjin kuka,Hajiya binta ne ta kamata tana lallashinta ita ta rikota har suka sauko Falon kasa inda Su Atika da Dose suke tsaye suna share kwallah tsausayin Madam dinsu da kewarta,Kallonsu takeyi sai taji yau sune fa yan”uwanta don dasu ta saba,tayi musu tsawa,tayi musu Fada,ta wulakantasu,ta dakesu,ammh sai gashi yau suna kuka don zata rabu dasu,ashe ba Farinciki zasu yi ba,don zasu rabu da ita ba..? batasan sadda tatafi da gudu ba ta fada jikinsu tana kuka ba,Suma kamata sukayi suka Rugume suna Fadin,”Plz madam we are going wit u”

    Girgiza musu kai takeyi kafin ta dago tana share musu kwallah dukkansu kafin tace”No,stay here…buh i promise u zan zo na tafi daku insha Allahu kunji,stop craying Sweetheart ,and tanque very much For u Time,May god bless u Ameen…”Wani kuka ne ya kwace mata tayi baya da Sauri tana daga musu hannu.

    Gaban Hajiya taje ta durkusa tana Fadin”kiyafemin *MOMMY*…”Take Fada kanta sunkuye tana kuka,Wani tsausayi da sanyi ya kama Hajiya ta duka ta dagota tana Share mata kwallah tana Fadin”Bakomai yata,dama banta ba rike ki ba,Kisani tamkar yata joda haka na daukeki,shawarata gareki Shine kibi dukkan Abunda Mijinki ya umarceki,komai kike bukata ga iyayen mijinki nan,ki tambayesu komai kike bukata zasu baki shi, Abu na karshe ga waya nan,zamu dinga kiranki muna tambayanki lafiyanki,daga karshe don Allah malika ki kula da kanki da kuma cikin dake jikin yanzu dai baki da kowa sai Allah sai mijinki kinji ko? .

    Fadawa jikinta kawai Malika tayi tana kuka take Fadin”Naji Mommy,kuma insha Allahu zanyi amfani da shawaranki Nagode sosai..”Take Fada tana share kwallah,Megadi ne ya shigo yana sanar dasu Yallabai yace Madam ta Fito su Tafi,jikinta ba kwari ta daga kafa ta fara tafiya tana karama Falonsu kallon Sai watarana,ahaka har ta Fice bata waigo ba itama hajiyar sai taji kwallar na silalo mata,Su Dose ko faduwa sukayi suka kamkame juna ita da merry suna kukan tsusayama madam dinsu,don daga ganin fuskar mijin nata baida imani,balle sun tsorata dashi Tun kusa kashe musu madam dinsu da yayi.

    Cikin kukan ta Fito tanayi tana sharbe kwallah,nan ta iske joy da peter tsaye suna zare ido,kallonsu kawai tayi sai tasamu kanta dayi musu mirmishi tana daga musu hannu,saleem na tsaye jingine jikin motarsa yana kallonta wani wawan tsaki yaja kafin ya kauda kai,jikinta asanyaye ta kariso gabanshi tana rawan jiki,kallon sama da kasa yayi mata kafin ya bude baki yace.

    “Ke…”Afirgice ta dago idanuwanta da sukayi jawur saboda kuka tana kallonshi Ware mata ido yayi yana Fadin”Uban wa zaki bi da wannan dan Figigin mayafin…? Yafada yana jefamata wani banzan kallo,baya taja tana saka hannu tana goge kwallar da suka zubomata takasa cewa komai,ganin ta maidashi wani mahaukaci ne yasa ya daka mata tsawa yana Fadin”Ke bada ke nake mgana ba,dont force me to mention my First statement,wlh bazaki ji da dadi ba..”

    Yafada yana kada mata yatsunsa,Bakinta na rawa Tace”Ba..ni…da..wa…Ni….”Harara ya sakarmata yana Fadin”Au baki da wani ko? kodayake banyi mamaki ba,saboda ba addinin aka sani ba,comon jare,ki koma ki sako hijabi ko na waye kizo mu tafi in ba haka ba,i swear bazaki shigarmin mota da wannan Shigar ba,ba dan iska bane ni…”ya fada yana zagayawa bangare Direba da hanzari.

    Batayi gadddama ba,da hanzari ta koma cikin gida.bata ga kowa afalon ba,dakin hajiya kawai ta shiga ta bude wardrope dinta taci karo da wani Farin hijabinta,dauka kawai tayi ta saka tana Ficewa daga dakin Da hajiya sukaci karo,wacce ta kalli malika da mamaki kafin tayi mgana Malikar ta rigata da cewa”Yi hakuri mommy na Ari hijabinki ne..”Tafada tana mata mirmishin yake.

    Baki Hajiya ta washe tana fadin”,Masha Allah…Maza Allah ya kiyaye hanya kai madallah da samun Surikiin kwarai yau Malikar Daddy ce harda Hijabi..? Tafada tana Mata dariya,mirmishi kawai tayi kafin ta juya Ta fice,hajiya ta bita da kallon mamaki tana mai jin dadi sosai na gamin yadda komai zai tafi kan lokaci

    Hajabin yadi uku ne,itama hajiyar Joda ta dinkamawa,so bai kai mata kasa ba,ammh tayi kyau sosai kamar ba malika ba,don yau itace rana ta farko data taba saka hijabi haka,Tun daga nesa yake hangota sakin baki yayi yana kallonta aransa yana Fadin So cute ashema hijabin yafi mata kyau,tana kariso ya riga daya bude mata gaban motan,shiga kawai tayi,shikuma yana kokarin tada mota dama alreday ya daura Set belt,tana jinsa yana karanta addu”ar matafiya kafin ya tada mota,suyi kwana, hon ya zubama megadi da hanzari ya wangale musu get suka sulala waje su peter na daga musu hannu.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!